KAI KAFI CHAN CHANTA CHAPTER 8 BY JAMILA UMAR TANKO
shi yasa hira ta dake ba ta dadewa domin daga an fara labari sai ki fara maganganu ki na koke-koke dan haka ni yanzu zan bar miki gidan idan kin gama kukan can bayan sallar isha’i zan dawo.
Ya juya zai fita, ta sake zubo da hawaye.
Ta ce “ashe daman zance ka fara zuwa shiyasa jiva ba ka yi sallar magaruba da isha’i a masallacin kofar gida ba? ka je ka dawo da wata-shadda ashe ita ta ba ka. Ai ba a nan kasar ka ke siyan shaddar da ka ke sawa ba.” Tsawa ya daka mata wacce ta razanar da ita ko tari bata sake yi ba, ya fara magana cikin fushi. Ya ce “ya ishe ni haka, ba na son ki gara daga wannan maganar, labarin da na ke niyyar baki na fasa kuma kar kisake tambayata.”
Ya juya a fusace ya fice, ya zabi dankareriyar mota
wacce ba ta jiya- ba ya shiga ya tafi. Bai tsaya a ko ina ba sai a kofar gidan malam Yakubu. Kamar jiya yauma anan suka yi Sallar magaruba suka yi karatu sannan su kayi sallar isha’i sannan kowa ya watse. Sai Malam da Bakura su na ta zuba hira.
Yahuza ya fito dauke da farantin abinci ya ajiye a
gabansu, languna ne na tuwo da miya, Yahuza ya durqusa ya gaishe da Bakura cike da fara’a da tsananin saka ran yau ma zai sami wata dari biyar din. Ya sami gefe ya zauna ya ci gaba da tsurawa aljihun Bakura ido.Malam Yakubu ya gallawa Yahuza harara ya fada. cikin tsawa “tashi ka shiga gida. Waye ya ce ka zo ka zauna anan?” Da sauri
Sum-sum Yahuza ya miqe har ya wuce zaure ya fito da
Yace “ah Baba na manta Sajida ta ce ka ba ni kudin igiyar leko(mosquito coil) in siyo ma ta.”
*”‘Malam Yakubu ya b’ata rai kai kace ruwan zafi aka watsa masa. Ya ce “ba zan siya ba, ai na fada mata jiya, igiyar lokon kwana biyu ne, domin guda biyu na ba ta amma ta qi ji ta kunna dukka biyun jiya, daya a wajen kanta wata a wajen gafarta wai ita isasshiya. Igiyar lekon biyu naira goma sau biyu a rana daya sai ka ce buga kudin nake yi. Dama guda shida na siyo jiya na miqawa Sajida biyu, na ce ma ta jiya daya yau daya.Na miga ma ka guda biyu, na kai biyu dakinmu muka kunna daya, yau zamu kunna daya. Ko kaima dukka biyun ka kunna jiya?”
Yahuza ya zabura. Ya ce “a’a ni saura daya da rabi da
-asuba na tashi na kashe dan kar ta qare.”
Malam yayi murmushin jin dadi. Ya ce “yauwa ka ji
yaro mai tattali haka ake so ka ga kai kwana hudu za ka yi kana kunnawa, ita kuwa Sajida yau idan za ta mutu don cizon sauro babu mai ba ta maganin sauro a gidan nan. Ka je ka ce ma ta ba zan siya ba, ai ta kwana biyu na ba ta kuma kar ta sake damuna.”
“Bakura ya ciro kudi naira dubu zai bawa Yahuza malam ya hana. Ya shiga roqar Malam, ya na yi masa magiya ya taimaka ya bari Yahuza ya siyo shaltos, malam ya fisge kudin daga hannun
Bakura ya tura masa a aljihun gaban rigarsa.
Ya ce “Bakura ba za mu yi musu da kai ba ko jayayya
tunda na ce ka bari ka bari, Sajida zúma ce sai da wuta ta na da taurin kai da rashin jin magana. Kuma laifin mahaifiyarta ne, ita ta shagwabata ba’a kwabarta, ada muna gamin kamar yarinta ce sai da ta girma naga tsiwar ta yi yawa sannan na tabbatar tantiriya ce sannan na fara saka mata takunkumi.” Bakura ya yi shiru kawai ya zuba tagumi.”
Malam ya dubi Yahuza ya daka masa tsawa. Ya ce
“tsayuwar me kake yi ne har yanzu? Na ce ka je ka fada ma ta ba zan siya ba.”Yahuza ya shiga gida da sauri. Malam ya ce “shi kuma Yahuza bashi da matsalar rashin jin magana ammo fa akwai shi da kwadayi da son kudi kamar wani quda idan ya ga koko haka ya ke wajen kwadayi.”
• Bakura ya kwashe da dariya ya ce “haka yara suke ako’ ina ma, sai dai fatan Allah Ya shirya mana zuriyarmu baki daya.”
Malam ya ce “amin summa amin.”
“Bakura bismillah ga abinci fa an fito mana da shi, tun jiya na ce daga yau abincin mutum biyu za’a dinga zubawa ni da kai.” Malam ne ya fada.
Bakura ba zai iya cin abincin gidan Malam ba, ga kunyar malam da nauyinsa yana ji.
Malam ya jawo farantin abinci ya bude tuwon dawa ne
da miyar kuka ta sha daddawa da wake amma ba nama. Babu shakka Bakura ma’abucin son miyar kuka ne, to amma tambayar
-ita ce ta yaya aka sarrafa miyar shine bai yarda ba, ma’ana tsaftar mai girkin, da tukunyar miyar da ruwan da aka dafa miyar, da tsaftar dan aiken da ya siyo kayan hada miyar shine babban tashin hankalinsa. Domin Bakura mutum ne mai tsaftar gaske ga yawan tsantsani. Sannan miyar kukar da ake yi masa a gidansa ta sha bamban da irin wanna kasancewar sai an jefa kaji biyu ko uku a cikin ruwan miyar sun dahu luguf, gashin ya sallube sannan atsame gashin sai a kada kukar a kai.
Malam ya sake maimaitawa “Bismillah Bakura ga abinci, kuma kar ka ce min ka koshi domin anan mu ka yi magriba ka ga kenan ba ka ci abinci a gida ba. Sai dai idan ba za ka iya cin abincin almajirai ba marar kaji da naman talo-talo.”
Bakura ya yi dariya ya ce “haba malam miyar almajirai, nima ai almajiri ne sai dai kawai na ci abinci da yamman nan na koshi.”
Malam: yayi turus da alama bai ji dadi ba. Ya ce “bari
na kira Yahuza ya karbo ma ka balangun naira dari a zuba maka a miyar ko dan ka ga babu nama shiyasa ba za ka ci ba.”
Bakura ya zubura ya ce “a’a malam ka bari kawai, ba dan rashin nama ba ne.” Gaban Bakura yayi mummunan faduwa saboda har ga Allah ko ba’a bude kwanon abincin ba ya san ba zai iya ci ba.
Ya ci gaba da cewa, “wallahi ba rashin nama ba ne.Ni
waye da zance dole sai da nama a abinci zan ci, nawa rayuwar duniyar take? Na koshi ne kawai.”
Malam ya yi zugum kamar mai tunani da alama bai ji dadin qin cin abincin da Bakura ya yi ba. Can ya dubi Bakura.Ya ce “ba zan boye maka ba d’ana, amma ban ji dadin qin cin, abincin nan da ka yi ba, ai sai ka saka albarka ko ba za ka ci da yawa ba. Ni da na ke ganin ka zama dan gida, zá ka iya zuwa ka ce min Malam yau abu kaza nake so a dafa min, in saka Sajida ta dafa maka ko menene ma.””Bakura ya tambaya cike da zumudi.”Sajida ta iya girki ne?”
Malam ya ce “ai fiye da shekara biyar Sajida ta hutar da mahaifiyarta, girkin dare da rana, safe da yamma ita takeyi sai dai idan ta tafi makaranta a lokacin da take zuwa makaranta kafin a cire ta. Ita mahaifiyarta ta na fama da abincin siyarwa yaushe za ta samu damar dafa mana abincin gida. kwalla-kwallar kunu da
daro-daron dan wanke take dafawa ta sayar a rana.
Babu abinda Bakura ya tuna da akace masa Sajida ce ta dafa sai lokacin da Zuhuriyyarsa take dafa masa turo miyar kuka sai yaji kamshin miyar kuka iri daya da na Zuhuriyya. Bai san sanda ya sa hannu suka fara cin tuwon ba, a idonsa ya na tuna yadda Zuhuriyya take kada miyar komai a cikin tsafta don haka bai sake jin kyamar miyar da yake ci ba. Malam ya ji dadin ganin yadda Bakura ya ke loma ba tare da kyama ba: Sai ci suke har sai da su ka kusa cinyewa. Sannan Bakura ya cire hannunsa. Malam ya cinge tas ya sude kwanon sannan suka wänke hannu, bayan sun taba ‘yar hira Bakura ya ce da Malam zai koma gida sai küma gobe idan Allah ya kaimu.
Yauma kamar jiya Malam ya tsayar da Bakura ya shiga gida ya fito dauke da turare. Ba laifi ya ‘na da kamshi amma ba irin designer da Bakura yake fesawa ba ne shi da iyalinsa.
Bakura zai ki karba, malam ya ce ba zai yiwu ba sai ya
karba dole. Bakura yayi godiya ya karba ya tafi zuciyara cike da mamakin halin kyauta irin na Malam Yakubu. Tabbas ko ba’a fada ba malam Yakubu ya na matukar kaunar Bakura a ransa, Bakura ya shiga sake-saken shin shi kuwa wacce irin kyauta zai yiwa wannan bawan Allah don ya fitar da shi da iyalinsa daga- cikin kangin talauci da wahala?.
- Amma kuma can a cikin ransa ya na son ya jira zuwa wani lokaci mai tsawo don ya sake tabbatarwa shin Malam saboda Allah ya ke kaunarsa, yake yi masa wadannan kyaututtukan ko don ya linka masa ne a gaba?
Samira ta lura yau ma Bakura ya shigo da leda a
hannunsa ya wuce dakinsa don haka ta sake tabbatarwa lallai maigidanta ya Shiga sabuwar rayuwa ba irin tasa ta da ba. Idan hankalinta yayi dubu ya tashi, sai zagaye take cikin gida ta rasa
Hmmm