KAINUWA CHAPTER 1
KAINUWA CHAPTER 1
*Shekara ta 1970* Gidan ya cika taf da mutane duk inda ka duba wasa ake yi, wasu na wasan dokuna wasu na wasan shad’i wasu busa suke yi, wasu waka suke yi, haka wasu wasan kidan kalangu sukeyi. Hidima dai kala kala irin ta wasan ninmu na hausa na da, kowa ka gani fuskar nan tasa a washe take alamar tsantsan farin ciki. Bayi sai murna sukeyi dan irin wannan sha’ani shi ke sa su su fito haka, maroka sai tasu hidimar suke yi. Gidan sarauta na kasar zazzau kenan wato Zariya. Zazzau na daya daga cikin manyan masarautu a Najeriya. Masarautar taci kasashe da dama da yaki, Girman kasar Zazzau ada ta kai har Suleja a Jahar Niger.+ Masarautar Zazzau ita ce tafi kowace masarauta a yankin Afrika ta yamma yawan makarantun zamani da na addini, shiya sa ma ake mata taken Zazzau, birnin Ilimi.2 Zazzau yana d’aya daga cikin Hausa bakwai wanda Bayajidda ya kafa, gari ne na sarauta. A wannan shekara ta Alif dubu d’aya da d’ari tara da saba’in karni ne na sarautar Abdulsamad wanda ya kasance d’a ne ga sarki AbdulJalal wanda ya mulki kasar shima daga gun mahaifinsa. Abdulsamad yana shekara 20 kacal aka daura shi akan mulki sakamakon rasuwar mahaifinsa, suna da yawa a gun mahaifinsu sai dai shine ya kasance d’an sarauniya Kubra sannan yaro ne mai hankali da ilimi hakan yasa mahaifinsa ya bada wasiyyar shi yakeso a nad’a. An aura ma Abdulsamad mata a wannan lokacin wace ta kasance ‘ya ce ga waziri wato ” Safina” wacce ta kasance tun tana yar shekara uku mahaifinta ya bada umarni a koyar da ita tarbiya ta matan sarki, hakan yasa ta taso mace mai tsauri da tsananin jan aji, abinda zai baka mamaki ko Abdulsamad sai ya sara mata a gun ji da kai da mulki. Safina ta auri Abdulsamad tana yar shekara 15, wacce aka nad’a a matsayin sarauniya, ta kuma bada umarnin a dinga kiranta da *MAGAJIYA*. Yayanta Hisham shine ya gaji mahaifinsu, wanda aka nad’a sarautar waziri. Auran Abdulsamad da Safina babu soyayya a ciki sam aurene na umarni, sai dai ita dama Magajiya sam babu soyayya a tsarin rayuwarta abu d’aya aka nuna mata ta auri sarki ta haifar masa d’a wanda zai gajeshi, itadai d’anta kuma jininta ya zama Sarki. Wannan shine abinda iyayenta suka daura ta akai. A wannan lokacin shekarar Sarki Abdulsamad da Magajiya 20 da aure sai dai har yanzu Allah bai azurtasu da haihuwa ba. Sarki ya cike mata 4 sannan yana da kwarkwara 9 amma har yanzu ba labarin ko da batan wata. Wannan abu na matukar damun Sarki da Magajiya, tayi magani harta gaji har yanzu babu labari. Sai dai alwashi ne tasha babu mai haifar ma Abdulsamad magaji sai ita in har ba ita ba kuwa to lalai bataga wacce ta isa ba. _Wannan kenan_ Kwatsam Magajiya ta fara abin laulayi haka kuma tace ai likita ya bata umarnin zama a d’aki ba tare da fita ba har sai ta sauka, sannan ya hana mijinta kusantarta saboda mahaifarta batada karfi. STORY CONTINUES BELOW Sam wannan bai damu Sarki Abdulsamad ba shidai farin cikinsa shine zai samu magaji. Magajiya sam ta daina fitowa haka ma bayinta sai wadanda ta yarda suzo gunta a haka har watan haihuwa tai, nan tace itakam gidansu takesan komawa. Kasancewar Sarki Abdulsamad bai isa da itaba yasa ta shirya ta tafi. Har ta sauka sannan aka aikomai da cewa ta haifi namiji. Fadar farincikin da Hisham yake ciki ma b’ata lokaci ne, wanda ya kasance yau ne ake hidimar sunan d’an nasa wanda aka samai suna Abdulmajid. Anata hidimar suna a waje sai dai daga kuryar d’akin Magajiya itace zaune akan kasan carpet gewaye da tintin sannan d’akin anyi jere sosai na kayan karfe masu maifar kyau da tsada, tana zaune cikin shigarta ta matar Sarki, gefenta kuma Hisham ne a zaune, su biyu ne kacal a d’akin sakamakon sallamar bayinta datai. Kallan Hisham tai cikin isa da mulki tace ” Yaya baka manta da abinda na fad’a ma bako?” Dariya yai yace “in banda abinki Magajiya ai ba wanda zai ji wannan sirri dan kuwa ita kanta Sauda(matarsa) na ja mata kunne akan ma karta kuskura ko da wasa tazo gidan nan inkuwa tazo to lallai karta bari su hadu da Abdulmajid. Murmusawa tai kadan sannan tace ” daga Abdulmajid na rufe haifar wani d’a a gidan nan, babu macen da zata haihu bare ma har a fara tunanin wanda za’a daura akan mulki.” Hisham yai murmushin mugunta yace ” Magajiya gaskiya kwakwalwarki tana aiki ya akai kika zo da tunanin karyar ciki? Sanda na sanar dake Sauda na da juna biyu?” Wani murmushin kasaita tai sannan ta sa hannu akan lab’anta alamar shiru sannan a hankali tace ” Yaya kenan ai na fad’a maka tabbas d’ana shine zai gaji sarautarnan, inhar bazan haihu ba dole ne nai amfani da kai jinina.” Wani kallo sukama juna na jin dadin abinda suka kulla, Hisham yace ” Nace Sauda ta bari sai nan da wata uku sannan ta dawo.” Magajiya ta jinjina kai alamar gamsuwa tace ” gwara ta kara zama saboda kar aganta aga kalar haihuwa aga kuma ba ciki, dan ma matar nada hakuri kaga bata mana musu ba sanda muka bata umarni.” Hisham ya sosa keya yace ” inta kawo wargi ai sai ta amshi takardarta, kinsan akanki ba abinda bazan iya ba.” Murmushin jin dadi Magajiya tai sannan tace ” ka sa a kara aikomin da maganin nan dan wanda nake badawa a sa ma matansa a girki ya kare.”1 Ya dan sa dariya yace ” gaskiya Magajiya ke karshe ce, shi yasa nake baki girma da darajaki, amma bakya gani ko an daina basu maganin yanzu ba abinda zai faru? Gani nake mahaifar tasu ma ai ta gama aiki.”3 Wani murmushi tai wanda ya fahimci cewa tana nufin ta sani amma a kawo. _Nikam nace Hmmm_ Sarki Abdulsamad kam kana kallansa zakasan yana cikin tsananin farin ciki. Bayan ya dawo daga hawan doki ne ya shigo fada sai ga wani bawansa ya sanar dashi yayi bako, tun daren jiya yazo, sakamakon rashin saninsa da sukai suka hanashi shiga, sai yanzu da sukaga takiyan dai ba mai cutarwa bane. Bayan an sanar da sarki ya bada izini akan bakon ya shigo. Wa zai gani? Amininsa ne wanda suka shaku sai dai dayake shi dan Katsina ne wanda aiki ne ya kawo mahaifinsa garin Zariya, har suka shaku haka kafin daga baya su koma garinsu. Da sauri ya karasa gun sarki saboda tsananin murna, nan Sarki ya kallesu da ido wanda ya nunama dogaran akan yanaso su fita, ba musu kuwa sukai waje. Rungume juna sukai cikin tsananin farin ciki Sarki ya kalli abokinsa yace ” Amadu ashe zan sake ganinka?” Wani irin farin ciki sukeji na ganin juna, bayan sun nustu ne suka shiga hirar yaushe gamo. Can Sarki yace ” ko ziyara Amadu? Da alama yanzuma ba saboda ni kazo ba.” Sarki gani yai Amadu yayi kasa da kansa alamar damuwa, cikin kulawa yace “menene?” Ya tambaya cikin kulawa. Hawaye ne ya ciciko a idan Amadu cikin wata muryar abin tausayi yace ” Mai martaba ina cikin wani mugun hali. Na rasa wanda zan fadawa naji sauki, kai kadai ka iya fadomin.” Mamaki ne ya kama Sarki yace “Name kenan?” Ido Amadu ya runtse yace ” kanwata aka ma fyade a kasarmu, wanda hakan yasa dangina da na matata duk hankalin mu ya tashi sakamakon habaici da kyamatar mu da akeyi, ko ina muka wuce zinden mu ake.” Cikin tsananin tashin hankali Sarki yace “kanwar ka badai Basira ba?” Amadu ya jinjina kai cikin takaici sannan yace ” ita kuwa shiyasa naga zamanta acan bazai yiwuba dan ko fita bata iyayi shine nace bari inzo in rokeka ko zaka tambayarmin yayarka Aunty Babba ko zata zauna agunta ko da kuwa na wata d’aya ne, bani da wanda na sani bayan kai a kasar nan, gashi duk samarinta sun gujeta, in komai ya lafa sai ta dawo.” Cikin tausayawa Sarki yace ” amma garin yaya?” Amadu yace ” da daddare matata ta aiketa siyo maganin zazzabi dan bawa d’ana da bashida lafiya, nikuma bana gari, a hanyarta ta dawowa aka tareta aka mata fyade, duhu yasa batasan waye ba bare ta nunashi, abin takaicin ma maza uku ne biyu suka riketa…..” ya karasa maganar cikin tsananin rauni. Sarki yai shiru yana nazari, Amadu yacigaba ” Mai martaba in kuwa kanada wani dogari ko bawa da kake tunani ka hadata dashi a musu aure dan kuwa babban abin kunya ne a ma mace fyade ka san bazata taba samun miji ba sai dai wani iko na Allah gashi ta girma shi yasa nake tunani ko wanene ma kawai ka bata a daura auren kafin nan sai ta zauna gun Aunty Babba.” (da yake a wancan lokacin babban abin tashin hankali da kunya ne a ma mace fyade ko ta je gidan mijinta ba tare da budurcin ta ba) Sarki yai shiru, tausayin rayuwar Basira yakeyi, yarinya ce wacce ba ruwanta ga hakuri. Bayan dogon nazari ya kalli Amadu yace ” kaunar da mahaifinka yakema nawa, da wanda kaima kake min yasa na yanke shawara ni zan aureta sai dai inaso karka bari zancen fyade ya fito a ko ina, mu birne ta a nan inba haka ba kyamatarta za’a dingayi a gidan nan.” Tsananin mamaki yasa Amadu ya kasa magana sai dai wani zazzafan kwalla daya gangaro masa, kai ya girgiza yace ” nagode dajin haka sai dai bazan yarda ka auri macen da aka taba a waje ba.” Sarki yai dan murmushi yace” Amadu kenan menene amfanin abotar? Kana tunanin akwai mai rike ma sirrinka bayan nidin? Yanzu in muka mata aure da wani bawan ko dogarin daga yaje ya ga ba cikakiya bace shikenan sai wulakanci, haka ma in sanar dashi mukai bazai fasa wahalar da ita ba.” Amadu yai shiru, Sarki ya dafa shi yace “karka damu a goben nan ma zan aureta sai dai bazan bari a sani ba tukunna har sai ‘yan taro sun watse saboda hidimar suna da akeyi.” Amadu ya zube yana godiya, Sarki yace ” ka koma kasarka gobe da safe zanyi shigar burtu na zo ba tare da sanin kowa ba sai wanda na yarda dashi.” Amadu wani dadi ya kamashi ya hau godiya sannan yace ” nidai zan jiraka mu tafi tare sabida tsaronka.” Sarki yai murmushi yace ” idan ka tsaya kuma waye zai sanar dasu maganar auran? Sannan nima banaso asan zanje har can din, sannan ka bari in sa akaika a mota dan nasan a irin a kori kurar nan ka zo.” (A waccan lokacin in har kaga mutum da motarsa to fa lalai d’an wani ne sannan motar ma mu a wannan lokacin tsohon yayi muke daukanta irin mai shafaffen booth din nan ce..) Sun dade suna tattaunawa kafin Amadu ya mike yamai sallama, godiya da jindadi kam yayi ba adadi. Nikam nace hmm wata sabuwa…. Shiru Sarki yai yana nazari bayan fitar abokinsa, baiyi zato ba sai jin muryar Aminin nasa yai a kusa dashi alhalin ya dauka ya tafi. Amadu yace ” Amma Mai Martaba ba matanka hud’u ba?” Idanunsa ya bud’e ya saukesu akan Amadu sannan yace ” Amadu kaje ka sanar da Barde ya kaika gida, ni kuma gobe zanzo.” Jin haka yasa Amadu ya fita jiki a sanyaye, Mai martaba yai shiru tare da maida idanunsa ya rufe, ya dade a haka kafin ya bud’e idanunsa sannan ya kira wani bawansa ya sanar dashi akan ya kira masa kaninsa wanda suke uwa da uba daya.+ Bai dade da fita ba sai gashi ya dawo shi kuma kanin nasa Kamal na biye dashi a baya. Yana shiga ya saki fuska tare da cewa ” Mai Martaba ina can ina hawan doki ka aika a kirani, Allah yasa ba matsala bane.” Abdulsamad ya tattara hankalinsa kan kaninsa yace ” Kamal yanzu ace na baka mata zaka aura?” Kai ya d’aga mai alamar eh sannan yace “ko ma wace iri ce in har ba mara da’a bace ko wacce ta lalata tarbiyarta da darajarta a waje ba.” Sarki yai shiru kafin yace ” in kuma d’aya daga cikin wacce ka lissafo baka so ne fa?” Kamal yai murmushi kafin yace ” maganar gaskiya zan aureta in har umarnine daga bakin Sarki sai dai in har umarnine daga bakin yayana bazanyi ba gaskiya.” Ya dade yana kallan Kamal kafin ya saki dan kasaitacen murmushi yace ” ya! kaje gun d’an naka?” Kamal ya washe baki yace ” Abdulmalik yana can yana bacci amma yau kam zai yi kwanciyar gajiya, ai yau kowa na cikin farincikin magajin sarki.” Sarki ya kara fad’ada murmushinsa yana jin dadin kasancewarsa uba kafin ya sallami Kamal. Bayan fitar kamal ne yai shiru yana tunani ( _a yanda tarihi yake mata guda hudu ne kamar yanda musulunci ya umarta mana sai dai akwai kwarkwara wanda suke zama matan sarki in anci garinsu da yaki ko kuma makamancin haka sannan su wad’an nan basu da gadon sarki in ya mutu_) Lalai yau ya yanke hukunci ba tare da yasan mafita ba sai dai yayi hakan ne saboda tunanin kare mutuncin aminin nasa. Matarsa ta karshe ko ince Amaryarsa wacce ya aura a waccan shekarar ita yake tunanin rabuwa da ita badan komai ba sai dan rashin san auransa da takeyi shi kansa yasan tauye mata hakki mahaifanta sukai gun bashi ita, yarinyace ‘yar shekara 9 mahaifinta yayane ga sarkin Daura wanda sunyi hadin auren ne a san ransu, ace shi yana shekara 40 amma an bashi yar shekara 9 ai kowa yasan hakkinta aka tauye shi yasa ko tunanin nemanta bai taba yi ba. Da wannan shawara ya mike tare da ba bayinsa izini akan yanasan a kira Magajiya zuwa turakarsa ********** Magajiya kam tana zaune sai shigowa ake yan suna ana mata barka, ba amsa wa take ba sai kai kawai da take kadawa cikin isa da takama, tayi shiga na alfarma dan Magajiya ‘yar gayu ce, ta iya kwalliya ta kuma iya sa kayan alfarma. A ranta wani irin nishad’i takeji tabbas tana cikin tsantsan farin ciki dan saura kiris burinta ya cika, wannan burin nata kuwa bai wuce ace d’anta Abdulmalik ya hau mulkin garin na Zazzau ba. Wata baiwar ta ce ta iso kusa da ita ta rada mata a kunne sakon Sarki, idanu ta juya tare da d’an yin karamin tsaki a ranta, itafa batasan takura akan mai shi baxai zo inda take ba sai dai ace wai taje? A duk sanda akace mata taji turakar sarki ji take kamar tafi karfin a dinga sata a bu. STORY CONTINUES BELOW Tafi minti talatin kafin ta mike ta fito. Turakarsa ta nufa yana xaune akan kilisar dake shimfid’e a gun, nan ta shiga kanta tsaye. D’agowa yai ya kalleta ta iso ta zauna d’an nesa dashi kadan cikin isa da takama ta zauna sannan tace ” gani ranka ya dade.” Kallanta yai yace ” Magajiya na tasoki kina cikin taro ko?” Kallansa tai ta danyi murmushi tace ” da alama kanada magana mahimmiya ne.” Ajiyar zuciya yai sannan yace ” ana cikin farin ciki sai dai zan sanar dake wata magana ne.” Kallansa tai tare da tattara hankalinta kansa. Yacigaba ” so nake in ba Rabi’atu takardarta ina tunanin zallintar da mukema yarinyar nan ya isa haka.” Kallansa tai cikin mamaki tace ” ban gane ba? Ka taba gani inda sarki ya saki mace?” Yace ” yau xa’a fara a kaina.” Tace ” in ka saketa kana tunanin akwai mai auranta?” Abdulsamad yace ” zan saketa ne amma bazan bari tabar gidan nan ba, ni zan rike ta har sai ta samu wanda takeso in aurar da ita.” Kallansa tai har zatai magana ta fasa dan itakam yanzu babu wani abu da zai dameta d’a ne ta samu yanzu dan haka komai ma zai faru sai dai ya faru. Ganin tayi shiru yasa ya fahimci ta amince nan ya rubuta takardar saki d’aya ya mika mata yace ” ki sanar da ita sai ta koma bangarenki da xama ko bangaren Hajiya Umma (mahaifiyarsa) Jiyai tace ” sai dai bangaren Umman dan nikam banasan tarikice.” Sarai maganar tad’an kona ransa sai dai bai nuna mata ba, takardar ta amsa sannan ta mike ta fita. Itakam Rabi’a bayan Magajiya ta aika tazo ta sanar da ita halin da ake ciki sam bata damu ba sai ma dadi da taji ta kuma ji dadi kwarai da akace zata zauna anan, dan dama tsoronta mahaifinta. Suna yayi dadi an kashe kud’i, ‘yan gari sun sha kalo, anyi hawan doki sosai, jaruman maza sun sha wasa da takubba, masu wasa da kura sun sa mutane nishad’i da sauransu. Da haka kowa ya koma gida, Magajiya ta dauko unguwar zoma mai kula da ita. ********* Washegari Sarki Abdulsamad bayan yayi sallar asuba yakira bawansa wanda ya aminta dashi haka kuma shine dama yake jansa a mota ya sanar dashi zasuyi tafiya, suna sallar asuba ya fadama fadawansa akan zai dan yi zagaye cikin gari dan ganin halin da mutanensa ke ciki. Kasancewar kowa yasan dama al’adarsa ce yasa ba wanda ya kawo komai a ransa, suna fita suka dau hanyar katsina. ******* A can katsina kuwa Amadu ya sanar dasu akan gobe za’a daura ma Basira aure da zarar anyi sallar azahar a masallaci. Basira kam batada bakin magana dan ita tun bayan faruwar wannan lamari sam ko magana ta daina yi, ko tambayar mijin batai ba ta mike ta koma ciki. Matar Amadu ta shigo ta ganta a zaune a bakin irin gadon nan na karfe, ta kalleta tace ” Basira bakyaso ne?” Kai basira ta jijiga mata alamar A’a. Numfashi ta ja sannan tace ” Basira ya kamata ki cire abin nan aranki yau wata d’aya da sati biyu kenan da faruwar wannan al’amari, daga ni har ke rabon da muyi fira a waje kenan, sai dai ke ko magana ba yi kike ba sai in ta kamaki dole, bakya gani lokaci yayi da zaki cire wannan a ranki? Ki amshi kaddarar da Allah ya miki? Murmushin dole tai sannan ta mike, ga mamakin Aunty Karima gani tai ta shiga had’a kayenta a akwati, mikewa tai jiki a sanyaye tai waje, ba shakka tana tausayin yarinyar nan gashi Amadu ya ki fada mata waye mijin itakam tana tsoron kar akai yarinyar nan inda zatasha wahala, dan ma dadinta d’aya ciki bai shiga ba sanda akai fyaden tunda har tayi al’adar ta. Basira kam kayanta kawai take sawa a akwati tana gamawa ta shiga tai wanka tare da kwanciya akan gadon d’akin, ta rasa me yasa ko tunani ma ta kasa yi idanunta kawai ta rufe. Bacci ne ya dauketa mai nauyin gaske. ********** Wajen karfe 12 suka iso dan motar wannan lokacin sam ba gudu ne da ita ba kamar ta yanzu ba, hakan yasa suka dade sosai a hanya. Basu san gidan Amadu ba hakan yasa suka shiga neman kwatance dan ma ya sanar dasu unguwar dan lokacin ba a sa sunan layi. Sun dan sha wahala kafin su gane gidan, abin takaici ma na mutane sai sunce gidan su Basira sannan suke ganewa. Hakan yasa Sarki yasan lalai abin ya yado dayawa, mutane nata mamakin me zai kai mutum mai mota gidansu Basira? Ko baisan labarinsu bane? Wajen karfe d’aya suka isa gidan lokacin Amadu na waje yana ta leken is kudu da yamma ko zai gansu. Yana hangosu ya saki ajiyar zuciya dan da ya dauka ko an samu wata matsalar ne. Abdulsamad ko ciki bai shiga ba yace muje masallaci a ayi abunda za’ai in koma dan barin fada ba tare da kwakwaran uzuri ba matsala ne. Amadu ya jinjina kai sannan suka nufi masallacin kusa dasu dama ya riga ya sanarma liman, bayan sunyi sallah ne aka daura auren Abdulsamad da Basira wanda Liman yama Abdulsalam walici shi kuma Amadu yama Basira an daura aure akan sadaki naira dari 200. Wannan kenan……. Kafin su fito daga masallaci bayan an daura auren mutane har sun cika gaban masallacin, labari har ya kai musu cewa ga wani gara can da baisan me yakeyi ba ya auri Basira. Sarki na kokarin fitowa wannan Bawan nasa ya sha gabansa ya rusuna tare da sanar dashi halin da ake ciki.+ Jikin Amadu ne yai mugun sanyi, jiyai Abdulsamad yace ” Ku fara fita in yaso ni sai in fito daga baya.” Amadu yace ” ai mai martaba bakasan gidan ba.” Yace ba komai zan biyo ku a baya ne nima ai. Jin hakan yasa suka fara fita, nan fa mutane suka saki baki suna kallan bawan, kowa da gulmar dake fada aransa, wasu cewa suke ai dole ya nemo ko ma waye ya bata da kuma alama ma fakiri ne, wasu kuma suce da alama sadaka aka bashi yaji banza shi yasa bazai iya bari ba. Haka dai kowa da abinda yake tunani, sudai sukai gaba, Mai Martaba na baya cikin mutane yana kuma jin duk abinda kowa ke fada, jikinsa ne yai mugun sanyi lalai ba shakka yayi babban taimakon na auran yarinyar nan dan kuwa da alama ba mai auranta a garin nan. Sai da mutane sukaga sun isa gida sannan kowa ya watse, shi kuma Sarki Abdulsamad ya shiga ciki. Bayan sun zauna ne matar Amadu ta kawo musu fura mai sanyi tare da dambu na tsakin massara yasha gyada, Abdulsamad ya dan ci kad’an kafin ya kalli Amadu yace ” Amadu ba zan kai Basira gidana ba yanzu.” Gaban Amadu ne ya fadi yace ” kana dana sani ko? Na auranta? Ni kai……..” Katseshi Abdulsamad yai yace ” ina tsorace mata a bubuwa guda uku shiyasa bazan kaita yanzu ba.” Yadan ja numfashi na manyan mutane kafin yace ” in har taje gidan nan a haka zatasha bakar wahala ba tare kuma da sanina ba, ko Magajiya bazata barta haka ba, ganin jiya akai sunan d’anta ace yau na kawo mata? Sannan na saki yarinya jiya ashe wani nake san sakeyi? Sannan ban sanar dasu zanyi auren ba ma sam. Kaga wad’annan dalilan sune zai sa su wahalar da Basira, gata ita kuma ko harkar gidan sarauta bata sani ba bare ta nemi kwatar kanta.” Shiru Amadu yai kafin yace ” Gaskiya ne ni kaga sam banyi wannan nazarin ba nidai dadina Basira ta auri wanda nasan ko bani da rai zai kular min da ita.” Sarki ya d’an murmusa kadan kafin yace ” Zan maka kwatancen gidana dake cikin gari, zan kuma sanar ma ma’aikatan gidan in yaso kai zuwa gobe sai ka taho da ita ka kaita can, zan tura mata bayin da zasu dinga kula da ita da koya mata abubuwan daya dace, in yaso zuwa ko sati biyu ne sai ta dawo.” Amadu ya shiga godiya, nan Sarki ya mike yace zai wuce. Amadu ya shiga kwallama Basira kira, da sauri Sarki yace ” ya isa haka, bance ka kirata ba ai, ina sauri ne in tazo naje na ganta.” Amadu ya amsa da to, sannan yamai sallama yai waje. Yana fita ita kuma matar Amadu wacce ta taso Basira da kyar tanata sharar baccinta suka fito, ganin ba kowa a gun yasa tace ” Malam ina mijin?” Basira ya kalla yace ” Basira gobe zan kaiki shi yayi gaba.” Matar tace ” a ina aka tabayin haka? Yaya shine zai kai yarinya?” STORY CONTINUES BELOW Amadu yace ” ni ai da so nai tabi mijinta ma baki alekum to amma tunda haka yace ni na kaita goben” Zata sake magana yace ” kul! Mijin Basira baya magana a canzata dan haka ki kiyayi kanki.” Mamaki ya kamata sai dai bata sake magana ba, Basira kam tana jin haka ta koma ciki tai alwala tai azahar. ********* A can gidan Sarauta kam ganin Sarki ya dade bai dawo ba yasa Hisham ya shiga amsar matsaloli da dai sauran abinda Abdulsamad ya kamata yai a ranar,dadi kuwa ya kamashi dan ba shakka yana san mulki sosai. Sai wajen shida sannan suka isa zariya. Kai tsaye wanka yai sannan ya zauna a kilisarsa aka shiga jeramai abinci kala kala da ‘ya’yan itatuwa.. Sai da ya koshi sannan yai bincike akan abinda ya faru a ranar. *********** Isar Magajiya da mulkinta yasa ta bada umarni bayan auranta dole ne duk matar sarki da kwarkwarori suzo su gaisheta da safe kafin suci abinci anan ne take sawa a kawo musu wani shayi wand sune suke tunanin shayi ne sai dai a zahiri naganin hana daukar ciki ne. ********* Amadu kam ya kai Basira inda aka umarceshi sannan ya mata sallama akan zai tafi. Kallansa tai idanunta suna neman cikowa tace ” yaya ina ne nan? Na tabbata ba mai hankali mai kudin kuma da zai aureni.” Amadu ya girgiza mata kai yana murmushi yace ” a naki tunanin kenan sai dai Basira inaso ki kasance mai godiya ga Allah dan kuaa ya baki mijin da babu kamarsa wanda baki taba tunanin ko gani ba bare aure ba.” Zatai magana taga ya juya baya yana kara kallan falon, daga nan ya kara mata nasiha ya fita zuciyarsa fes da ita. ********* Sarki kam sam ya manta da Basira sakamakon hidimomin dake gabansa, yau ya cika satinta uku kenan da zuwa garin amma ko keyarsa bata gani va, sai wasu abubuwa da ake koya mata. Gashi abin haushi komai sai ace sai dai a mata, magana wannan akwai mai nuna mata yanda zatai, itakam duk ta gaji da wannan sabon al’amarin. Yau watanta d’aya cif, Abdulsamad harya kwanta bacci ya tuno da Basira da sauri ya mike cikin tsananin mamakin kansa da takaici ya fito daga turakarsa, Bayinsa ne suka matso suna tambayaraa ko yana bukatara wani abun ne? Da sauri ya nemi bawansa Mudan ya kuma umarci bayin da wannan fitae ta zama sirri, nan yai waje shida Mudan. Kayan fadawa ya saka sannan ya rufe fuskarsa ya hau doki, ba wanda yai tunanin Sarki ne har ya fita. Gidansa ya nufa, a lokacin ita kuma an sa tayi wanka da wasu turaruka masu kamshi kamar yanda suke sata kullum wai hakane al’adar dole in zatai bacci tai wanka da wad’an nan turarukan sannan ta sha madarar shanu ta kwanta. Ta fito kenan ta zira doguwar riga tana shan madara taji sallama. Gabanta ne ya fad’i jin muryar namiji, a hankali ta amsa kamar mai rad’a, nam shi kuma ya shiga. A zaune ya ganta sai dai idanunwanta sunyi zuruzuru. Dama ya umarci bayin dake waje su tafi makwancin su, nan na cikin d’akin suma suna ganinshi suka zube suna gaidashi, nan suma ya sallamesu. Itakam idanuwanta ne duk suka fito jin suna cewa ” Mai Martaba barkada shigowa.” Batakai ga nemo amsar tambayar dake mata yawo akai ba taji yace ” Basira ba gaisuwa?” Kallansa tai sannan ta zube da sauri kamar taga mala’ika sai dai ta kasa cewa komai sai gabanta kawai dake mugun fad’uwa. Murmushi yai sannan ya matso kusa da ita ya d’agata ya, itakam kafafuwanta rawa suke hakan yasa tsayuwar ta fara neman gaggararta, da sauri ya jawota jikinsa tsoro ne yasa ta zaro idanuwa, shikam Abdulsamad yana mamakin girman yarinyar. Kamshin jikinta ne ya sa ya lumshe ido ba shakka kamshin Magajiya ya ninka nata dadi sosai sai dai baisan meyasa yakijin nata wanu daban ba, ji yake yana ratsa zuciyarsa. Bata taba tunani ba haka kuma batau zato ba taji yace ” kinyi al’ada ne?” Da sauri ta matsa daga jikinsa ta kalleshi kadan sannan ta sunkuyar dakai, taya za’ai ya mata wannan tambayar? Ko kunya?” Abdulsamad yace “dole ce ta sani yi miki tambayar.” Baya ta juya da sauri sannan ta d’aga kai alamar eh tare da shigewa uwar d’aka. Hamdala yai sannan ya shiga ciki shima. Itakam a bakin gado ta zauna tare da rike hannayenta biyu itakam wacce irin tambaya aka mata yanzu? Mijin da bata taba gani ba taya zai fara mata wannan tambayar?” Shigowarsa ne yasa tai saurin kwanciya tare da rufe ido, murmushi yai sannan ya karasa kusa da ita ya zauna, hannu ya sa a kafadarta cikin maganarsa ta isa da sanyi yace ” Basira na tambayeki ne badan komai ba sai saboda gaba.” Kallansa tai cikin mamaki yai dan murmushi yace “karki damu ni dama nasan ba matsala sai dai ya zana dole na tambaya.” Kasa tai da kanta ta maidashi kan filo, kanta ya shiga shafawa a hankali ya kwanto da kansa jikinta, tsoro ne ya shiga kamata ta tuno abinda ya faru da ita. Da sauri ta mike ta zauna tare da matse kafafuwanta. Hawayene ya shiga zubo mata, tana kuka tana girgiza kai. Sarki ya shiga mata kallan tausayi, Basira cikin kuka tace ” tsoro nake.” Matsowa yai kusa da ita ya rungumeta ta kara fashewa da wani kukan, nan ya shiga jijigata yana bata hakuri cikin salon soyayya a haka har yasa jikinta ya mutu nan shi kuma ya gabatar da abinda yake so…….. Bayan ya nutsu ne ya jawota jikinsa itakam har yanzu kuka take, hakuri ya cigaba da bata, ta dade sosai tana kuka kafin bacci yai gaba da ita. Shiru yai yana kallanta, ya sani sarai dolene gobe bayin dake kula da ita su bincika ko jinin da ya kamata ya fita a gabanta sakamakon farkon kusancin ta da maza ya fito, dan sune zasu zama shaidarta nan gaba. Dubawa yai ya samo reza ya bud’e cinyarsa ya tsaga kad’an sannan ya sa a jikin zanin gadon, sannan ya mike ya fito bayan ya dan sumbaci Basira. Wajen Sallar asuba babbar mai kula da ita a cikin bayi ta shigo dan taimaka mata tai alwala. Basira tana kwance tana bacci matar ta shigo ta tasheta, sam Basira ta manta abinda ya faru hakan yasa da karfinta ta nemi tashi, jin zafi a gabanta ne yasa ta tuna, saboda tasha wahala sosai sanda aka mata fyade dan sai da matar yayanta tai ta saka ta acikin ruwa mai zafi tana gasata tukun na, mikin daya warke ne taji ya motsa, hakan yasa ta dan ce wash.+ Matar ta kalleta tare da yayi zanin gado da sauri, ganin jini yasa ta saki gud’a, Basira kam kallan jinin tai sam bata kawo ba daga jikinta ya fito ba saboda matan da ba ruwansu da zancen nan, hakan yasa batasan sau d’aya yake fitowa ba, itakam matar ce take bata mamaki ganin yanda take gud’a. Kan kace me? Sai ga ragowar bayin sun taho da sauri, nan suka gani kowa ya fahimta, nan wata ta fita dan d’ora mata ruwan zafi, itakam matar zanin ta yayi ga mamakin Basira gani tai ta ninke ta saka a cikin leda. Bayan ruwa yai zafi ta taimaka mata tai wanka tai sallah sannan aka kawo mata abinci, Basira nasan taji wai menene matsayin wannan mijin nata wanda yazo jiya sai dai tana kunyar tambayar hakan. ********** Sarki ne zaune akan kilisarsa Magajiya na d’an nesa dashi tana cin ‘ya’yan itatuwa shi kuma yana d’auke da Abdulmajid a hannunsa yana murmushi, can ya nisa yace ” Magajiya nayi aure.” Kallansa tai cikin isa tace ” aure kamar ya kenan?” Ya dan murmusa yace ” kanwar abokina Amadu ce zata tare nan da sati d’aya zuwa biyu.” Kallan mamaki tamai sai dai isa da ji da kai yasa batace komai ba, sai dai maganar ta kular da ita sosai tayaya kamar ita za’a mata kishiya ba tare da ta sani ba?lalai Abdulsamad yazo da rainin hankali. Mikewa yaga tayi tare da kiran baiwarta, nan ta shigo da sauri, Magajiya ta kalleta tace “Amso Yarima zan koma.” Abdulsamad ya kalleta sai dai shima baice komai ba sai mika ma baiwa ‘yar yai suka fita. Tana fita ta tura a kira mata Yayanta Hisham. Zaune take a d’aki ya shigo cikin sauri, ganin yanda fuskarta take a had’e yasa yace “Magajiya lafiya?” Kofin dake hannunta ta jefo da karfi inda yake saura kiris ya jefeshi hakan yasa yasan lalai yayi laifi, da sauri ya matso cikin sanyin murya yace “kanwata………” Wani mugun kallo ta bugamai tace ” me kakeyi har Sarki yai aure ban sani ba?” Gabansa ne ya fad’i cikin tsananin mamaki yace “Aure kuma?” Wani kallo ta kara mai tace ” ba nace ka dinga kula da duk al’amuransa ba? Yaya wai meke damunka ne? Ko ka manta da wasiyyar Baba yace?akan ka dinga bin duk abinda na fad’a?” Yace “Yahkuri Sarauniya uwar Sarki duk wanda yaja dake shine a wahale, tayaya wata mata can da baki santa ba zata kona miki rai bayan ko ta shigo sahun ragowar matan zata shiga?” Shiru tai tana kallansa, yace ” menene naki na kishin wata macen bayan ba haihuwa zatai ba bare musa ran samun matsala nan gaba?” Shiru tai kafin daga bisani tai ajiyar zuciya sannan ta d’an ja tsaki tace ” ko menene dalilina na jin haka? Tunda yake aure ban taba jin haushi ba sai yau.” Hisham yai dan dariya ganin ya shawo kanta yace “kinada yarima magajin sarki sannan kina da ni waziri menene zai saki damuwa?” Murmushin jin dadi tai sannan tace ” zan baka sako ka aikama gidan matarka sannan itama ya kamata ta dawo.” STORY CONTINUES BELOW Kai ya jinjina alamar gamsuwa yace ” yanzu kam bamai gane ta haihu.” Sukai murmushin jin dadi. _nikam nace hmmmmm_ 1 Yau ranar kwanan Basira ne a yanda Mai martaba ya tsara sai dai kasancewar bata nan ya kamata ace shi kadai zai kwana, sai dai shikam da daddare ya lalaba ya fita. Tana zaune ita kadai shiru, gefenta bayinta ne suke ta hirarsu, taji sallama. Da sauri suka mike suka shiga kwasar gaisuwa sannan suka fita, ya rage saura su biyu. Zama yai daga gefenta kadan yana shirin magana tai saurin cewa “ina wuni?” Kallanta yai yace ” da alama sai na sa an d’aure masu kula dake.” Dasauri ta kalleshi idanunta sun bayyanar da tsoro tace ” me sukai?” Yace ” tunda haryanzu basu koya miki abinda ya dace ba.” Da sauri tace “Barka da dare.” Sannan ta cigaba “wlh na sha’afa ne ba laifinsu bane.” Murmushi yai sannan yace ” ke bakya magana dayawa ne?” Shiru tai batace komai ba, yana kallanta yace “kishirya zuwa jibi zaki koma gidana.” Kallansa tai batace komai ba itakam tana san jin shi d’in wanene. Jitai yace “Abdulsamad sunana sauran bayani zaki gani inkin isa jibi.” Kai ta d’aga ba tare da ta kalleshi ba, hannu yasa ya rikota suka shiga ciki. Duk da itakam tana tsoro sai dai bata isa bijire ma wanda ya taimaki rayuwarta ba. Sai da komai ya lafa sannan bacci yai gaba dashi, itakam shiru tai dan baccin ya bar idanunta ta dade tana tunani kala kala kafin tai bacci. *********** Magajiya da kanta tasa aka gyara b’angaren da zata zauna sannan tasa aka sanar da Sarki akan komai ya kammala, shikuma ya aika a sanar dasu lokacin da za’a daukosu. Da daddare aka sata tai wanka, bayan tasa kaya aka miko mata alkyabba irin masu karfin gaske da nauyi irin na da, aka sa mata, mamaki sam ya hanata magana, sarka ta zinare aka sa mata aka sa mata abin kafa da awarwaro, kasa jurewa tai ta kalli baiwar tata tace ” amma wannan shigar batai yawa ba? Ni fa na fara tsoro.” Baiwar tai kasa dakai tace ” tayaya kaya zaiyi yawa bayan haka al’adar masarautar take? ” Cikin tsananin mamaki tace “Masarauta?” Kallanta baiwar tai tace ” eh mana duk abinda muke koya miki ai abinda zakiyi ko zaki tarar acan mukeyi.” Wani abu ne ya tsaya mata a makogaro, sarauta? Ba shakka ta gane yanzu, wato abokin yaya ne wanda kusan duk labarin yaya baya wuce na Sarki Abdulsamad lalai shine ya aureta kenan, to amma ina ita ina shi? Ta ina? Ita da ba cikakiya ba? Jitai an dafata hakan yasa tai firgigit daga tunanin data tafi. Baiwar tace ” Ranki ya dade ana jira.” Dakyar ta fara d’aga kafarta suka fita. ******* Haka suka isa gidan tunani duk ya isheta. B’angarenta aka wuce da ita suna tafe ana gaidasu danma bata ganinsu saboda fuskarta a rufe take. Har suka shiga aka ajiye ta a kan bakin gado nan kowa ya fita aka barta da baiwarta guda d’aya. A ka’ida bayan an daura mata aure akwai wasu bukukuwa daya kamata ayi agidan sarautar sai dai Abdulsamad ya turo a sanar da Magajiya akan kar ayi, tayi mamakin jin haka ta aika a tambayeshi dalili ganin al’adar gidance hakan. Abdulsamad yace ” Gani yai ba’a dade da yin taron suna ba shi bayasan almabazaranci.” Magajiya tayi dariya jin haka dan tasan lalai uzuri kawai yake nema na kar ayi amma wannan ai ba hujja bace, hakan kuma ya nuna mata lalai Sarki ba san auran yake ba da alama akwai wani abu a kasa ne. Basira kam da yake mai san shiru ce zaman bai dameta ba. Yau tana tashi baiwarta Ta sanar da ita zuwa gaida magajiya. Batasan dalili ba sai dai tanajin sunan taji gabanta ya fadi, jiki a sanyaye ta fito suka nufi b’angaren Magajiya. Bayan kowa ya zauna ita da ragowar matar nan ta gaidasu kowa na mata kallan wulakanci kallan wacce ba’aso. Fitowar Magajiya yasa taga kowa ya nutsu, nan ta juya suka had’a ido kwarjini da cikar zati irin na Magajiya da isa da mulkinta yasa Basira tai saurin dauke ido, gabanta kuwa yaki daina faduwa, addu’a kawai ta shiga yi har Magajiya tazo ta zauna. Basira ta d’ago suka kara hada ido, gani tai Magajiya ta mata alama da hannu, jiki a sanyaye ta isa gunta. Magajiya cikib muryar rad’a tace “sau daya zan fada ki tsaya kiji dakyau, yau ya zama rana ta farko kuma ta karshe da zan juyo in ga idanuwanki a kaina banasan kallo.” Cikin inina tace “Tuba tuba nake.” Kowa ya gaida Magajiya sannan aka kawo abinci itakam dakyar ta ci kadab nan aka kawo musu ruwan zafi anmai had’a had’e, itakam Basira komai ya isheta a gun abincin ma da kyar taci ruwan zafi kam da kyar ta iya yin kurb’a d’aya. Magajiya ta kalleta tace ” shanyewa zakiyi ai.” Basira tai kasa dakai tace Ranki ya dade bana iyashan ruwan zafi tun ina karama.” Magajiya tai wani murmushi tace ” inkinsha ya kasheki.” Basira gabanta na faduwa da tsoro gashi harga Allah batashan ruwan zafi dan tun tana yarinya datasha tai ta amai haka kuraje suka feso a bakinta tun daga nan aka hanata, an nemar mata magani amma ba’a dace ba sam. Nan ta d’aga kofin ta fara sha kafin ta shanye kuwa sai amai ya feso, nan ta mike da sauri ta fita ta shiga kela amai kan kace me kuraje sun cika bakinta. Tsoro ya kama Magajiya gashi ranar kwanan Basira ne, ya zatai in Mai Martaba ya tambayeta dalilin hakan???????