KAINUWA CHAPTER 2

KAINUWA CHAPTER 2

Ganin yanda takeyi yasa Magajiya tace a maidata b’angarenta, nan kowa ya mike ya fita sakamakon sallamarsu da tai. Suna fita ta aika a kira mata yayanta Hisham, bai dade ba ya shigo nan ta sanar dashi komai sannan ta d’aura da cewa ” yanzu in Mai Martaba ya tambayeta ta fadamai tirsasata nai zaiyi zargin wani abu kasan halinsa sarai.” Hisham yai shiru sannan ya ce ” bari na kira mai magani ya dubata.” Wani mugun kallo ta bugamai wanda yasa yace ” tuba nake ashe fa babu namijin da ya isa shiga b’angaren matan sarki ba tare da izini ba ko an sanshi ba.” Kanta ta d’auke daga inda yake tace ” Ka fad’ama Turaki ya tambayar mana kaninsa ko akwai maganin da zai warkar da ciwon tunda naga kanin nasa yasan kan magani.” Nan ya amsa da to sannan ta kara kallansa zatai magana yai saurin cewa “na fahimci komai kinaso kice shi Turakin ya rike maganar a sirri.” Murmusawa tai kad’an sannan ta juya kai.+ Hisham ya mike ya fito yana fita waje yai d’an kwafa tare da kallan inda ya fito sannan yai gaba. Basira kam kwanciya tai ta shiga bargo saboda sanyin dake ratsata itakam batasan gidan nan sam ita duk rayuwarma ba dadi take mata ba inta itace har gwara can inda ta fara zama akan nan dan a kalla a can gidan bayi insuna hira suna sata dariya amma nan kam tanaji tunda ta shigo haryau batai dariya ba. Tana nan kwance aka aiko mata da magani, ko kallan maganin batai ba dan itakam ta sab ciwonta inta kwana washe gari zai baje. Bayan tayi isha’i ne wasu bayi suka shigo suka tsaya a inda take, babbar cikinsu wacce suka zauna da ita a can ne, ta matso kusa da Basira tace “Ranki ya dade wanka zaki tashi kiyi.” Basira batai musu ba ta mike saboda a can an sanar da ita yin musu laifi ne kuma yana jawo a rage ganin girmanta. Ban d’aki ta wuce, ruwan zafi ne aka saka a katan baho an saka abubuwan kanshi kala kala, kina shiga b’an d’aki wani dadad’an kamshi ne zai bugeki, nan ta sata a ruwan zafin. Bayan sun gama wankan ne suka bata wasu kaya masu kyaubta saka sannan wannan matar ta miko mata wani ruwa a kofi ba musu ta amsa ta shanyi, maganin ba dadi bata koma san dame akayishi ba sai dai tasan akwai zuma a ciki. Tana gama shiryawa wata mata ta shigo mai d’an jiki haka, tana shigowa suka gaisheta jin suna cewa Jakadiya yasa ta fahimci wacece. Jakadiya ta kalleta sannan ta gaisheta tace “Ranki ya dade muje ko?” Basira batai musu ha tabi bayanta. Sun d’anyi tafiya kad’an kafin su shiga wani b’angare, sosai an tsara b’angaren gashi kato ita da tana tunanin b’angaren Magajiya yafi kyau sai dai yau ta gane wannan yafi, ga girma ga kyau,kofar wani d’aki suka isa sannan Jakadiya ta kwankwasa, daga ciki akace shigo. Jakadiya ta kalli Basira nan Basira ta shiga dan ta gane hakan ake nufi. Katon d’aki ne sosai ganinsa yasa tai saurin maida kanta kasa, murmushi ya saki sannan yace ” Amarya karaso mana.” A hankali Basira ta karasa inda yake ta tsugunna nesa dashi sannan tace “Barka da dare.” Alama ya mata da hannu akan ta matso kusa dashi, idanu ta d’an zaro kad’an tana tsoron kar ta matsa ya kula da bakinta da ya ke ciki da kuraje har kan d’an leb’enta. STORY CONTINUES BELOW Ganin yanda yake kallanta yasa ta matsa kadan, hannu ya kara nuna mata akan ta kara matsowa, Basira ta rasa yadda zatai a hankali ta matsa sai dai ta sunkuyar da kanta. Abdulsamad yasa hannu ya jawota kusa dashi yace ” bakiga me ke gabana bane?” Sai a lokacin ta kalli gun, abincinsa ne a gun da ‘ya’yan itatuwa. Ya kalleta yace “Zubamin.” D’agowa tai ta kalleshi wanda hakan yasa ya kalli bakinta, mamaki ne ya kamashi yace “Menene hakan a bakinki?” Da sauri ta rufe bakin, matsowa yai ya fizge hannuta sannan ya ce bud’e bakinki, tsoro ne ya kamata dan Allah ya bashi kwarjini, bud’ewa tai cikin tsoro. Idanunshi taga sun canza cikin fada yace “meye hakan?me ya faru da ke? Ai sanda kike can ba haka kike ba.” Bakinta ne ya fara rawa, cikin tsoro tace “banashan ruwan zafi ne sai dazu tsautsayi yasa nasha na dauka na warke.” Kallanta yau cikin kokwanto da sauri tace “tun ina karama na daina sha sam na dauka na daina.” Ta dauka zaiyi fada sai taji yace ” kidinga kula yanzu bari nasa a samo miki magani.” Kai ta girgiza tace ” ai gobe zai warke.” Jakadiya wacce ke makale a kofa ta saka kunne tana jin komai da sauri ta juya ta fara tafiya cikin sauri kamar zata kifa. Shikam Sarki daga wannan matsowa ya shiga wani al’amarin daban ya manta da abinci……Lol! Jakadiya kam bata tsaya ba sai a b’angaren Magajiya tana isa ta nemi izini ta shiga. Zubewa tai a kusa da Magajiya nan ta zayyane mata komai. Murmushi Magajiya tai tace “da alama tanada hankali.” Jakadiya tace “nima na kuka da hakan.” Magajiya tace ” ya ya? Ya kusanceta?” Jakadiya tsoro ya kamata itakam sam ta manta ma aiki biyu aka sata ta ji me zatace da kuma ko Sarki ya nemi Basira. Kallanta Magajiya tai tace ” menene?” Yawo Jakadiya ta had’iya tasan halin Magajiya sarai ba tada kyau ko yayanta ba raga mai take ba hatta Sarki in ranta ya b’aci sai ta san yanda tai ta kona mai nasa ran ita kuwa ina ita ina yi mata laifi? Amma itakam tana ganin me zaisa Sarki ya kusanceta bayan ragowar Matan ma sai ya dade bai kusancesu ba? Magajiya ta kafeta da ido. Jakadiya ta saki murmushi tace “ina fa? Yana gama tambayarta yai kwanciyarsa dan ko abinci baicibama. Magajiya ta saki wata bazawarar dariya tace ” nikaina jikina yaban haka saboda Basira yarinyace bata wuce 16 zuwa 17 ba shi kuma na sanshi sarai bayasan kusantar yara ko ya auresu yafiso sai sun girma.” Jakadiya ta sake dariya tace”Ai Mai Martaba ke kadai ce a gabansa Hajiya Magajiya mahaifiyar Yarima Amdulmajid Magajin Sarki.” Kanta ta juya tana murmushin kasaita, nan Jakadiya ta mata sallama tai waje. ******** Magajiya ta yanke shawarar daina ba Basira shayin nan saboda taga abinda ya faru sannan taji Mai Martaba bai fara nemanta ba hakan yasa ta sa Hisham ya samo mata wani wanda ba sai a ruwan zafi ba, dan gwara a samo mata ta ajiye kafin Mai Martaba ya fara tunanin kusantarta. Jakadiya kam bayan ta dawi ta tambayi wata baiwa wacce take ta hannun daman ta ce, ita ta bari a gun dama ta tafi kai gulma akan ko wani abu ya faru. Baiwar ta fada mata ai tana tafiya akai abun. Shiru Jakadiya tai tsoro fal ranta sai can tad’anyi tsaki tace “to ai ba abinda zai faru ma dan inaji Sarki Juya ne inba haka ba matansa nawa haryanzu ba haihuwa? Da ya kwanta dasu da kar ya kwanta duk d’aya ne.” Baiwar tace ” wani juya kuma bayan Magajiya ta haihu.” Jakadiya tai dariya a ranta tace ” sai dai a rainawa dolo hankali amma ni da nake zuwa gunta banga wani alamar ciki ba, wanda nake gani kuwa baimin kama da ciki ba sannan menene dalilin turani tafiya zuwa Masarautar Kano a daidai watan haihuwarta? Ni nasan akwai wata a kasa. Murmushi tai a ranta, ganin komai ya zo mata daidai. ********** _Bayan wata hudu_ Basira kam duk ta rasa me ke damunta bata iya cin abinci gashi shiru ba al’adarta sai dai bata kawo komai a ranta ba haka kuma tana kokarin yin komai daya kamata wanda hakan yasa ba wanda yai tunanin komai. Sai dai a ‘yan kwanakin nan ta fara zargin ko ciki ne ganin yanda cikinta yai tauri sannan ya dan fara tasawa kad’an. Magajiya kam nasan Basira yanzu tunda taji abinda ya faru, haka zatai ta aika mata da abubuwa, itakam Basira har yanzu ta kasa sakar zuciyarta da matar. Matsala ta fara faruwane daga sanda kanwar mahaifiyar Magajiya tai tattaki na ziyara ta kawoma ‘yar yayarta, wanda a lokacin matan sarki duk suna zaune kwasar gaisuwa. Kallo d’aya tama Basira tsoro ya kamata dan ta fada dashewa irin na masu cikin nan. Ido ta kurama Basira wanda har tasan akwai matsala, da sauri Basira ta dauke idanta daga kan matar. Suna fita Kanwar Mamanta wato Aunty Lami ta matso kusa da ita tare da cewa ” Magajiya nikam waccan wacece?” Ta fad’a tare da nuna inda Basira ta zauna, murmushi Magajiya tai tace “Ahhh Basira? Kema ta burgeki ne? Bansan meyasa ba amma yarinyar ta shiga raina.” Aunty Lami tai d’an shiru tana tunanin ta inda zata fara, can tace ” amma dai ba matar Sarku bace ba ko?”. Had’e rai Magajiya tai tace ” wace irin tambaya ce wannan? Baki ga kayan jikinta bane? Ko akwai masu sa kayan Sarki bayan matansa?” Aunty Lami ta dafa kai, kanta na kasa tace “amma dai ba ciki ne da ita ba ko?” Kallanta Magajiya tai cikin halin ko in kula ta girgiza kai cikin takaici sannan tace ” da alama tsufa ya fara miki illa.” Lami ta d’ago ta kalli Magajiya tace ” Magajiya wlh ba haka bane lalai ki binciki ‘yar nan, kina me har ciki ya zauna a jikinta haka? Da alama ma cikin nan ya kai wata hudu in bai fi bama.” Kanta ta juya ba tare da ta bata amsa ba dan ta kula nema take kawai ta kona mata rai. Lami ta kara matsowa tace ” wlh Allah da gaske nake, Magajiya kinsan dai da yanda nake, indai naga mace da ciki ko wata d’aya ne sai na gane.” Tasan da wannan sarai sai dai tayaya zatace ciki bayan yarinyar haryanzu Sarki bai fara…….. Tunaninta ne ya tsaya ta tuno sanda ita kanta waccan satin taga yanda tai haske har take tsokanarta akan lalai gidan sarauta ya amsheta ganin yanda take kyau haka. Zumbur Magajiya ta mike cikin firgici ta shiga kwallama wata baiwarta kira, nan ta karaso da sauri. Baiwar ta zube a kasa, Magajiya tace ” jiku shirya zani b’angaren Basira.” Mamaki me ya kama baiwar dan tasan Magajiya bata zuwa b’angaren kowa hatta bangaren Mahaifiyar Sarki sai ta shafa watanni bata ko leka ba. Basira kam tana dawowa daga gun Magajiya ta hau amai dan abincin dataci acan sam kawai dai ta tura ne amma bawai dan ranta yaso ba, kwanciya tai akan gado dan wani irin jiri takeji. Mai kula da ita tana kusa da ita tana tambayarta akan ta kira mata mai magani na gidan? Kai Basira ta jijiga zatai magana sai jin kirarin isowar Magajiya tayi ana yi a kofar ta. Da sauri ta mike ta d’an gyara fuskarta sannan ta fito. Magajiya ta gani a zaune tayi zama irin wanda ta saba, tun da ta taho Magajiya da Lami suka kura mata ido har kafarta ce ta hard’e ta kusa fad’uwa. Da kyar ta karaso, Magajiya ta kalleta cikin dabara tace ” ya akai? Bakyajin dadi ne?” Kai ta girgiza alamar a’a, baiwar dake kula da ita ta matso ta zube a kasa tace ” Magajiya dan Allah a kira mai bada magani ta duba Uwar gijiyata wlh ba lafiya ce ta isheta ba.” Gaban Magajiya ne yai wani wawan fad’uwa amma dayake isashiyace sai ta maze cikin gadara tace ” je ki kirata.”+ Da sauri ta mike tai waje, Magajiya ta kalli Basira tace ” na d’auke ki kamar kanwata ashe ke ba haka bane?” STORY CONTINUES BELOW Basira ta d’ago a hankali itakam tana tsoron matar nan, daurewa tai tace ” ba wani abun damuwa bane kawai dai naci abinci dayawa ne a gunki.” Magajiya ta kafeta da ido, tsoro da fargaba ya cika mata ciki taf. Suna zaune anan mai bada magani ta shigo. Nan Magajiya ta bata umarnin duba Basira, hannunta ta kama ta bud’e tafin hannunta ta zuba musu ido, ta sake ta sannan ta bud’e idanunta na hago, nan ma ta saki ta sake bude na dama. Tana gamawa ta zube a kasa tare da cewa ” ina tayaki farin ciki yake Magajiya, babu wani gabanki ba wani bayanki, kece fitila wacce take haskaka gidan nan……” Katseta Magajiya tai tace ” ya isa ni fadamin meke damunta.” Mai magani tai murmushi tare da kara dukufar da kanta tace ” Yarima Abdulmajid ya kusa samun kani ko kanwa ima tayaki murna Magajiya.” Ai ba Magajiya ba kowa na gun sai da ya zaro ido, itakam Basira kasa kawai tai da kanta. Mamakin daya rufeni, gani nai Magajiya ta mata alama da hannu akan ta matso kusa da ita, nan ta taso ta iso, tana zuwa Magajiya ta jawota ta rungumeta tsam tace ” Masha Allah! Lalai kinyi abin kwatance a wannan masarauta ba shakka ked’in ta dabance.” Basira kam addu’a kawai take dan gabanta sai fad’uwa yakeyi. Magajiya ta saketa ta kalli Mai Magani tace ” ki biyoni ki amshi tukwicinki mai tsoka. Nan ta mike ta fito. Abinda zai baka mamaki kan kace me? Labari har ya cika gidan, Jakadiyar Sarki kam tana jin wannan labarin ta garzayo gun Basira sai data tabbatar sannan ta tafi gunsa yana fada ta sa a sanar mai. Magajiya kam tana shiga d’akinta ta dafa kanta wanda ke sarawa, idanunta sunyi jaa sosai lalai dabadan tun tana karama an hanata kuka ba lalai yau da sai tayi, sai dai itakam batasan kuka ba, ko da mahaifinta ya rasu batai ba. Lami ta kalla tace a kira Ya Hisham. Nan Lami tai waje da sauri ta aika a kirashi. Hisham na fada ya samu sakon kanwarsa da sauri ya mike ya nemi izini ya taho, a waje yaga mai magani hakan yasa yai tunanin ko batada lafiya ne. Murmushi yai sannan ya shiga, a tsaye ya ganta ta juya baya. Nan ya canza fuska cikin kalar damuwa ya matso kusa da ita ya zauna yace ” Magajiya lafiya?” Juyowa tai cikin takaici ta zauna a gun zamanta sannan ta kalleshi tace ” ciki gareta.” Cikin rashin fahimta yace ” wa kenan?” Lami tai caraf tace ” Basira Amaryar Sarki.” Tashin hankali Hisham ya mike da sauri cikin tsananin mamaki da tsoro yace ” ban gane ba? Magajiya ba kince bai kusanceta ba?” Sosai ya damu dan babban burinsa bai wuce yaga d’ansa akan mulki ba, Magajiya ta runtse ido cikin takaici tace Jakadiya ce ta fadamin. Shiru sukai kafin daga bisani Hisham yace ” ya zama dole a zubda cikin kafin yai kwari.” Magajiya tai shiru sannan tace a kira mata mai magani. Mai Magani ta shigo cikin farin ciki, gaban Magajiya ta tsugunna. Magajiya ta kalleta yace ” shekararki nawa kina aiki a gidan nan?” Cikin zumud’i tace “40.” Magajiya tai murmushi tace ” muhallin zama fa?” Tace ” a wani d’an daki muke takura nida mijina da ‘ya’yana.” Magajiya ta kalleta tace ” Zubar dashi.” D’agowa tai da sauri tace ” me fa?” Hisham yace ” ke kika dubo tana da ciki hakkinki ne kisan yanda kikai kika zubar dashi, in har kinasan ki cigaba da aikinki kuma kinasan muhallin zama mai kyau ke da iyalanki.” Cikin tsoro tace ” Waziri tuba nake amma tayaya zan zubar da kwan Sarki?” Hisham yace ” ruwanki ne ki zubar ruwanki ne ki barshi sai dai ‘ya’yanki ina tabbatar miki zasu fuskanci gararin rayuwa dan ko aure basu isa suyi ba in har sun zauna da ransu kenan.” Cikin tsananin tashin hankali ta d’ago ta kalli Hisham. Lami tace ” kinaso mahaifiyarki dake kwance ba lafiya ta rasa inda zata zauna? Ke kuma ki rasa sana’arki?” Kai ta shiga girgizawa, Lamibta cigaba ” in har kinaso bakin ciki ya kashe mahaifiyarki kar kiyi abinda aka saki.” Ganin ta rikice tana roko yasa Magajiya tace ” kwana bakwai, kwana bakwai kacal na baki ki tabbatar kin kawon magani mai karfin da zai tafi da cikin, kar kuma kiyi tunanin bazan gane ba dan sai nasa ankai gun mai maganni ya tabbatar da hakan.” Kanta ta shiga d’agawa nan aka sallameta. Tana fita Lami tace ” zatabi umarnin mu?” Magajiya ta juya kai batace komai ba. Magajiya tasa a nemo Jakadiya sai dai sama ko kasa an nemeta an rasa bat ta bata dan bata gidan sam. ********** Sarki kam yana tasowa daga fada yasa a kiramai Basira, dan da shi yaso zuwa ma sai Barde yace in yaje za’ai tunanin yafi san Basira ne wanda hakan zaisa matan su fara tsanarta. Farincikinsa ma yau kwanan ta ne, tunda yai sallah ya kasa tsaye ya kasa zaune sai jeka ka dawo yakeyi, yana nan a tsaye har ta iso. Tana shigowa tun bata karasa ciga cikin d’akin ba ya karaso ya rungume ta tsam wani irin nishadi da jin dadi na ratsashi. Bayan ta zauna ya sa hannunsa akan cikinta cikin tsananin murna, itakam kanta na kasa tana murmushi, cikin tsananin farin ciki yace ” in Allah ya saukeki lafiya in har Mace kika haifa zan sa mata suna Fatima Zahra wato ‘yar Manzon Allah in har kuma Namiji ne zan sa mai ABU TURAB.” Cikin muryarta mai sanyi tace ” Har ka zabi suna?” Yana murmushi yace ” sunayen dana fi so kenan haka kuma fatana in ga na saka wad’an nan sunayen.” Murmushi tai sannan tace ” meyasa baka sama d’an ka na farko ba?” Yace ” ai shi magaji ne shiyasa na samai Abdulmajid, tun daga kan mahaifinmu ake sa ma Magaji Abdul a gaba.” Murmushi tai sannan ta kara sadda kanta kasa. Dadi ne ke ratsashi hakan yasa ya kara jawota jikinsa lalai baiji haka ba sanda Magajiya zata haihu, yau jinsa yake daban lalai yana cikin farin ciki. Magajiya tasa Aunty Lami akan duk wani magani datasani ko wani mai bada magani data sani ta je ta amso mata maganin da zai kawar da wannan cikin, babu makawa sai ta sa cikin nan ya bi shada dan itakam bataga wanda ya isa ya haihu ba a gidan, dan kuwa bazata tab’a iya jurar ganin yaro na yawo a gidan ba a matsayin d’an wani ba, ba nata ba. Basira tana kwance a d’aki tun safe ta kasa cin abinci, sallamar baiwar ta ce wato lantana yasa ta mike zaune, Lantana ta karaso ta gaidata sannan tace ” Ranki ya dade Magajiya ta aiko miki da magani da kuma abinci.” Basira tace ” nakoshi Lantana sam banajin cin abinci.” Lantana ta matso tace ” Kinsan bazataji dadi ba in taji bakici ba kinga na jiya ma data aiko bakici ba sai dataji ba dadi.” Basira tace ” to ke kici mana?” Idanu Lantana ta zaro tace ” so kike a yanken hukunci mai karfi? Magajiya ce fa ba wani ba.” Zata sake magana sai ga Aunty Lami ta shigo ba ko neman izini, tana shigowa ta matso kusa da Basira fuskarta a sake aosai tace ” haba ‘yata tashi ki daure kici mana, ko so kike hankalin Mai Martaba ya tashi?”+ Da sauri Basira ta jijiga kai alamar a’a, Aunty Lami tasa aka kawo abincin da kanta ta bata sai dataga taci sosai sannan ta bata maganin da aka kirashi da sunan maganin dazaisa taji karfin jikinta.” Ta dade a zaune ganin Basira ma baccinta take shara yasa ta fita daga d’akin. ******* Zaune take gaban Magajiya wacce itama shiru tai tana tunani, can Aunty Lami tace ” amma Mai maganin nan na kan tudu ya rainamin hankali, sai fa daya tabbatarmin cikin minti 15 zata fara fitsari akai akai in har naga haka inbata kwana d’aya cikin zai zube dan dama nacene ya bada wanda zai dan d’au lokaci kafin cikin ya zube kar a gane.” Magajiya tai tsaki tace ” mai Yaya yakeyi?” Da sauri Lami tace “ya tafi Daura anso wani maganin.” Magajiya tace ” itafa matar nan ga gidan nan?” Lami tace ” ita kuma tace a bata zuwa gobe.” Magajiya tai d’antsaki tace nifa banasan jan abin nan dan ji nake kamar akan bushiya nake a zaune.” Lami ta matso tace ” karki damu ‘yata…..” Wani kallo Magajiya ta mata wanda yasa tai shiru, kanta Magajiya ta juya gefe sannan tace “kayan abincin dana aika ya karene?” Lami ta d’aga kai, Magajiya tace ” zan aika da wani amma sai hankalina ya dawo jikina.” dan dama ta sani da zarar taji Lami ta fara cewa ‘yata tasan abu take nema. Basira kam ta fahimci Magajiya ce kawai ke santa a matan sarki dan su kiri kiri suke nuna mata kishin cikin nan, dan haka duk abinda aka aiko mata daga bangaren Magajiya bata wani kokonto take ci. Mahaifiyar Sarki wacce ta tsufa itama bata gazawa gun aikoma Basira kayan marmari. Shikam gogan wato Sarki kullum sai yayi aike sau uku akan a dubo lafiyarta, wannan al’amari ya kara dugunguza hankalin Magajiya dan kuwa an sanar da ita, to ita ke yasa sanda akace tana da ciki baya mata wannan aiken? Tsanar Basira da abinda ke jikinta ya kara tsananta a ran Magajiya. Yayanta ya dawo d’auke da magunguna kala kala nan ya zauna yama Lami bayanin komai, nan ita kuma ta shiga yin hidimominta. A ranar da aka fara bata maganin an saka mata shine a cikin miyar kubewa d’anya, san tuwo da takeyi yasa taci tuwon nan sosai, sai dai me? Tunda ta kwanta bacci ta ke juyi a kan gado, tsananin ciwo da mararta keyi yasa tai ta murkusus, da sauri Lantana ta fita ta karasa b’angaren Sarki nan ta aika a sanar mai. Ranar kwanan matarsa ce ta biyu, ai ko fadamata baiyiba yai waje da sauri, sun iso bangaren Basira lokacin ciwon ya mata yawa dan ta fad’o ma daga kan gado, jini ne ya fara zubo mata wanda hakan yasa hankalinta yai tsananin tashi. Sai dai tsananin ciwon da takeji yasa ta kasa magana, shigowar Sarki ne yasa ta daurw ta fara kokarin mekewa, da sauri ya karaso ya rungumota jikinsa, hawayene kawai ke zubo mata a hankali take cewa “shikenan cikin nan ya tafi shikenan nikam na baka kunya….” Hannu yasa da sauri ya toshe mata bakinta sannan ya kara jawota jikinsa, d’aya daga cikin bayin Basira wacce Magajiya ce ta turota b’angaren dan kai mata rahoto. Da sauri ta zame jikinta tai bangaren Magajiya. Tana shiga ta zayannema Lami halin da ake ciki, da sauri Lami ta shiga ciki ta sanar da ita, ajiyar zuciya Magajiya tai tace ” yau da alama zan samu bacci mai dadi.” Lami ta saki dariya tace ” nikuma gobe za’a sallameni ko?” Kanta ta juya gefe bata amsa mata ba sai murmushin jin dadi data saki. Basira kam tana jikin Sarki ganin ciwon ya lafa yasa ya kira Lantana yace ta taimaka mata ta gyara jikinta. Basira tana mikewa Lantana taga yanda jini ya zuba sosai, salati ta shiga yi, Sarki ya kalli gun dan harshima ya b’atashi, Lantana ya kalla ya mata alama da ido akan tai shiru hakan yasa tai shiru itakam Basira hawaye kawai take yi. Shiru yai bayan sun shiga b’and’aki, ji yai idanunsa na neman canzawa, kallan jinin yai yanajin wani abu na tasomai na bakin ciki, ba shakka yasa rai sosai akan cikin nan, yana nan a zaune Lantana ta fito ta debi kaya ta koma. Can sai gasu sun fito, kuka sosai Basira takeyi wai tana bashi hakuri, mikewa yai yaje kusa da ita ya jawota jikinsa yace ” karki damu Allah zai bamu wani.” Shiru tai batace komai ba, ya daure yai murmushi yace ” kishirya gobe insa a maidake gida gun Amadu inkin warware sai insa azo a d’aukeki. Kallansa tai cikin mamaki tace ” akan me?sakata kai?” Dariya yai sannan yace ” wani irin saki kuma? Ai ba saki a auranmu cewa nai dai kije inda zaki samu kulawa sosai sannan za’a dinga d’ebe miki kewa, sai ku shirya ku tafi da Lantana.” Murmushi tai sannan ta sunkuyar da kanta kasa. Magajiya kam an tabbatar mata ciki ya zube shine ma dalilin tafiyarta gida, nan ta aiko mata da kaya kala kala wai ta kai gida, masu murna nayi masu bakin ciki na yi na tafiyar cikin nan. Sarki ya cika musu mota da kayan abinci ya kuma bata kudi sosai yace ” zai zo sai dai bai san yaushe ba.” Sun shirya sun kama hanya. ********** Matar Amadu kam bata yarda cikin nan ya tafi ba ita kanta basira ganin cikinta na kara tasowa yasa tasan cikin nanan, sai dai ba yanda zatai ta sanar da Sarki tunda dai ba salula babu kuma wanda zata aika, sai dai ta zauna zuba ido akan sanda zai zo. Matar Amadu dashi Amadun tunda sukaga cikin Basira nanan suka d’aura himma sosai na kula da ita hakama Lantana sosai take kula da Basira. _Wannan kenan Shiru shiru ba sarki ba labarinsa wanda hakan ya kara d’agama Amadu rai gashi lokacin Basira cikinta yakai wata 9, ganin kar Basira ta haihu ba tare da sarki yasan komai ba yasa Amadu ya shirya tsaf ya nufi garin Zariya a akuri kura. + Sai yamma liss suka isa, gidan Sarki ya wuce. A b’angaren Mai Martaba kuwa aiyuwa sun cab’e mai a fada wanda ya rasa yanda zaiyi, yaso ya aika aje q dubo Basira sai dai Barde ya bashi shawara akan ya kara jinkirtawa ganin kar a gane tsananin san da yake mata wanda kan iya jawo mata tsangwama in ta dawo. Yau ma kamar kullum yana zaune a fada ana ta fama kawo kara yana hukunci, wasu kuma neman taimako suka zo yi wasu kuma sulhu da dai sauransu, ganin yamma tayi sosai yasa ya sallami kowa akan a dawo gobe, shigowar bafadansa ne yasa ya kalleshi, bafadan ya sanar dashi zuwan Abokin nasa kuma sirikinsa, nan ya bashi izini da sauri. Amadu ya shigo kansa na kasa sai daya gaidashi tukunna, Sarki ya nemi a basu guri, suna fita ya kalli Amadu yace ” Amadu ka jini shiru ko? Wlh al’amura ne suka c’abe min gaba d’aya. Amadu yace bakomai sannan ya d’ura da cewa ” dama zuwa nai na sanar dakai Basira ta shiga watan haihuwa.” Mamaki ne ya kamashi wanda sai da ya bayanna a kan fuskarsa yace “Haihuwa kamar ya?” Amadu yai murmushi yace “ai cikin bai zube ba.” Mikewa yaga Sarki yayi da sauri ya shiga matse hannayensa yama rasa mai zaiyi can ya matso jusa da Amadu ya d’agashi tsaye ya rungumeshi kam yace ” Basira ta kusa haihuwa kenan?” Amadu yai murmushi yace “kwarai kuwa dan tama shiga watan, haihuwa yau ko gobe, nima sai da Matata ta sanar dani ta kula Basira ta kusa haihuwa sannan nace to ya zama dole yanzu kam inzo in sanar dakai.” Abin mamaki kwalla ne ya taru a idan sarki hannu ya d’aga ya shiga godema Allah. Abin mamaki fadawa da bayinsa dake waje nan a ka fara zamewa kadan kadan an tafi kai gulma (lol…..) Sarki yace “aikam yanzu dakai zamu tafi muje in d’aukota.” Amadu yai dariya yace ” kai da kake fama da aiki sai dai ka tura kawai a d’aukota.” Shiru yai yana tunani can yace ” ka kwana anan zuwa gobe zansan yanda za’ai.” Magajiya na zaune zance ya zo mata, tashin hankalin da ba’a kwatantashi, ba shakka tashin hankalin data shiga ya wuce duk yanda mai karatu zaiyi tunani tana tsaye jitau jiri ma na neman d’ebanta, Hisham kam ba kanta dan kuwa magana ra baci, tsantsan tashin hankalin da ya shiga ya wuce misali. Gun Magajiya ya taho a sukwane, sunyi jugum jugum su biyu a d’aki, can Magajiya tai d’an ajiyar zuciya sannan ta kalli Hisham tace “duk laifinka ne, kaine ka tabbatarmin maganin nan ba karya ko wasa a ciki.” Hisham yai shiru can yace ” duk ba wannan bane abinyi yanda zamuyi yanzu shine abinyi.” Magajiya tai shiru tana tunani, Hisham yace ” bafa zai yiwu mu bari a haifi yaron nan ba in ma mace ce da sauki to amma ina muka sani?” Magajiya cikin kufula tace ” aikin gama ai ya riga ya gama kanaji ance ta shiga watan haihuwa?” Da sauri Hisham yace ” to sai me? Ai ko haifarsa tai sai mu halakashi.” STORY CONTINUES BELOW Kura mai ido tai can tace ” kisa kake so muyi kenan?” Hisham ya share zufa sannan yace ” ai da din ma kisa ne, in kuma kina ganin ba wani abu to shikenan kinfi kowa sanin Abdulsamad haka kawai bazai ba Abdulmajid mulki ba dan yana na fari ko yana d’anki ba.” Shiru tai tana tunani kafin tace ” banasan irin wannan maganar ka fita ka bani guri in na gama yanke hukunci zan kiraka.” Mikewa yai ya fita rai a b’ace. Magajiya ta dade tana tunani kafin daga bisanj ta mike ta fito. B’angaren Sarki ta nufa, yana turakarsa banda farinciki ba abinda yakeyi, neman izini da akai akan isowar Magajiya yasa gyadan had’iye abinda ke fuskarsa. Magajiya ta shigo cikin tafiyarta ta isa,zama tai a inda ta saba zama sannan ta kalleshi tace ” ina cikin tsananin farin ciki Mai Martaba, nasan ban kaika ba amma natabbata ina bayanka.” Murmushi ne ya bayyana a fuskarsa na tsantsan farinciki yace ” nagode Magajiya.” Murmushi itana tai sannan tace ” ka gode dame? Abinda za’a haifa kamar d’ana ko ‘yata ne zan kula da abinda aka haifa kamar nice na haifesu.” Kallanta Sarki yai sai dai yau idanunsa ya rufe har ransa yake jin dadin maganar ta. Magajiya ganin ta kamo lagonsa ta cigaba ” shine nake tunanin kai ka zauna saboda hidimar dake gabanka inyaso waziri sai yaje ya taho da ita.” Sarki ya kalleta zaiyi magana tace ” menene amfanin waziri? Dole ne ya wakilceka ko ya taimaka maka alokacin da kai kake wani abun, banaso mutane su fara tunanin kafinsan matarka a kan talakawa da mutanenka.” Shiru yai yana tunani ba shakka hakan data fa’a shine gaskiya, ya kalleta yace “haka ne sai dai bakya tunanin Hishan zaiji ba dadi ganin kishiyarki ce?” Kai ta jinjina tace ” zaiji mana, sai dai ai a karkashinka yake, sannan in munaso mu girmama Basira shi din ya kamata a tura.” Sosak Sarki ya gamsu haka kuma ya amince da wannan shawara. Bayan Magajiya ta dawo b’angarenta tasa aka kira Hisham, ta kalleshi tace ” gobe ka shirya kai zaka taho da Basira sai dai inaso ka sani banaso inga Basira a gidan nan daga ita har abinda zata haifa.” Tana gama fadar haka ta sallami Hisham ba tare da ta jira abinda zai ce ba. ********** Washegari kuwa da sassafe Mai Martaba yasa suka kama hanya, mota biyu sukau saboda in an tashi d’aukota yace a taho da Matar Amadu saboda ta kula da ita inta sauka, ganin ita ta gidace ba wai dan baza’a bata kulawa a gidan nasa ba. A can garin Katsina kuwa Basira tun dare take nakuda mai azabar wahala, banda juyi ba abinda takeyi duk sun jigata daga ita har abinda ke cikinta har matar Amadu, sai asuba ta sauka, ta haifi d’anta santalale mai tsananin kama da Mai Martaba, duk da dai ance jariri ba’a gane kamarsa sai dai wannan kam kallo d’aya zakamai ka san ba Basira bace. Tana haihuwa wani nannauyan bacci yai gaba da ita, Matar Amadu ta gyara d’an tas sannan ta gyara gun, ganin yaron ya tafi bacci yasa ta zo ta tashi Basira ta gyara ta, sannan tace ta koma ta kwanta bayan ta d’anci dumame. Shiru Matar Amadu tai tana tunani, ga Amadu bai dawo ba gashi Basira ta sauka, ganin zaman ba shine mafita ba yasa ta mike ta fito tai gidan yayanta dake nan kasan layinsu. Babban d’an yayan ta samu tace maza yaje ya samu motar da zatai Zariya ya hau, ta bashi sako akan yaje gidan Sarki ya nemi Amadu in bai ganshi ba yace a sanar ma Sarki Basira ta sauka ta haifi Namiji. Sai dataga ya hau motar sannan ta juyo gida, kazarta ta kama ta yanka ta shiga gyarawa, Lantana na aikin gida. Rashin sani sam itabatai zaton Amadu na hanya ba. Su Amadu sun iso wajen azahar nan ya tarar da abin farin ciki wanda ya kasance na babban bakin ciki ga Hisham, sai ma da aka miko mai yaron yana bacci ganin katon yaro nau kama da AbdulSamad yasa hankalin Hisham ya kara tashi, jiyai kamar ya shake yaran ya mutu. Matar Amadu ce ta kawo musu ruwa da abinci ganin yanda Hishan yake kallan jaririn ne yasa ta tsorata ba shakka kana gani kasan kallo ne na saka mugun abu a rai. Hisham jin motsin ajiye tire yasa yai saurin kallanta sannan ya canza fuska, itakam tana ajiye wa ta juya tai ciki, zuciyarta fal da tunani. Bayan yaci abinci ne yace zaije ya samu hakimin nan garin ya kwana a gunsa zuwa gobe tunda bai kamata su kama hanya yau ba. ******* A can kuwa Sani ya isa Zariya ya sauka ya gangara masarauta, a bakin kofar shiga dogarai suka tambayeshi inda zashi, nan ya sanar dasu gun Kawu Amadu yazo wato yayan Basira wanda yazo jiya, nan suka sanar dashi ai ya koma katsina yau, jiki a sanyaye ya juya, har ya d’anyi nisa sai kuma ya dawo yace ” ku sanar da Mai Martaba dama Yafendo ce ta sauka yau da asuba, an samu d’a namiji.” Kallan mamaki dogaran sukamai suka ce Yafendo?wacce kenan?” Sani cikin halin ko in kula yace “Basira.” Kallan juna dogaran sukai sannan suka kalleshi sukace ” da gaske ta haihu?” Kai ya d’aga alamar eh, gani yai sunyi ciki da sauri ko kulashi basu sake yi ba, tsayawa yai yana mamaki, ganin ba kowa a kofar shikam ya shige ciki. B’angaren Magajiya sukai tana zaune a kilisarta dan ko abinci ta kasa ci, bayan sun nemi izini ne suka shiga ciki suka zube a kasa suka kwashe komai suka sanar da ita, zumbur ta mike cikin tashin hankali sai dai ganin su waye a gabanta yasa ta daure ta saki fara’a tace ” Alhamdulila kun sanar da Sarki?” Sukace “munje baya fada shiyasa muka garzayo nan.” Tace ” dakyau ba sai kun fadamai ba bari ni na sanar dashi da kaina, ko kuma dukanmu kar mu fadamai sai dai kawai mu bari in ta dawo gobe ya ganta da d’a lalai zai sha mamaki.” Kai suka jinjina alamar gamsuwa sannan ta basu tukuici ta sallamesu. Shikam Sani ciki kawai yai ta shiga har ya ganshi a wajen wasu mutane, a tsatsaye a waje da alama magana mai nahimmanci suke tattaunawa kuma yaga duk wani mutum akewa maganar. Gun ya karasa ya gaishesu, kallansa sukai cikin mamaki,Barde wanda ke tsaye ya kalleshi yace ” Lafiya?” Sani ya kara sanar dashi yanda ya fadama dogaran. Barde cikin zakuwa yace ” ka tabbata?” Yace ” sosai nidin ai d’an yayar matar Kawo Amadun ne.” Barde ya kama hannunsa cikin sauri sukai gaba. Gun Mai Martaba ya kaishe yace ya tsaya a waje shi kuma ya shiga ya sanar da Sarki. Sarki kam wani irin dadi ne yake ziyartarsa ji yake kamar zaiyi me dan dadi, nan ya bada umarni a ba Sani tukuici mai tsoka. Magajiya ta rasa abinda zatai da sauri ta aika a kira mata Inna Lami(sry zamusa Inna Lami tunda a lokacin ba Aunty.) Lami tana shigowa ta tsinci labari a sama yana yawo akan haihuwar Basira. Cikin hanzari ta juya tai waje, gun malaminta ta nufa ta sanar dashi komai. Kallanta yai sannan yace ” yanzu me kikeso ayi?” Tace “an riga an haifeshi ni kuma ban taba kisa ba kuma itama Magajiya nasan bazataso muyi kisa ba dan haka so nake a nakasar dashi. Kallanta yai yace” Nakasa wace iri?” Tace waccece zata hana mutum yai tunanin hawa mulki? So nake a nakasar dashi a yau yanda in sukazo gobe za’a dauka a haka aka haifeshi.” Dariya yai sannan yace ” na baki ko na ido? Sune babban nakasu da zasuma mutum.” Lami tai shiru can tace ” ido, a hanashi gani yanda ko uwarsa bazai sani ba balle ubansa sai dai muryarsu, tunda munyi iya yinmu akan karyazo duniya amma sai da ya zo.” Tana zaune anan ya gama abubuwansa sannan ya bata wani yace ta binne, nan ta bashi sallama ta mike ta fito cikin farin ciki. Sai daya gama komai sannan ta shiga gun Magajiya ta sanar da ita. Magajiya ta kalleta tace “kina ganin zai kama?” Tace kwarai kuwa kuma nina fada miki gobe ba ido zaizo gidan nan. Ajiyar zuciya Magajiya tai cikin damuwa…… _Hmmmmmm_

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE