KAINUWA CHAPTER 3

KAINUWA CHAPTER 3

Sosai Barde ya ba Sani tukuici sannan ya kamo hanya. Shikam Hisham tun da suka isa masauki ya kasa zaune ya kasa tsaye can ya gaji ya koma ya zauna tare da bubuga ‘yatsarsa a guda d’aya a kasa alamar yana cikin dogon nazari ba shakka dolene ya d’au mataki sai dai ta ina?kuma ta yaya? Ganin yaron ma yasa hankalinsa ya kara tashi matuka, ba shakka in har Mai Martaba yaga yaran nan to fa su tasu ta kare, tunda shi jininsa ne. In mun tafi a hanya in jefar dasu a tsakiyar daji ne? Abinda ya fara fad’o mai kenan a zuciya, kai ya girgiza da sauri yace in nai haka kuma ai zasu koma gidan a hankali tunda da kafarsu kuma zasu iya samun taimako. Insa a je gidan a kashe su yau? Kai ya girgiza yace na tabbata in nai haka sai an zargeni tunda dai ina garin. Idanunsa ne ya kada sosai na bakin ciki, gashi dare yayi bare ya tafo daura gun mai magani. Ko guba zan……. Kai ya kada da sauri alamar rashin gamsuwa, idanunsa ya rufe cikin bakin ciki, jiyai daga wajen d’akin da yake wasu na hira “wlh jiya ai munga abin mamaki, tas fa wutar nan ta cinye gidan daga mata da mijin har yaranta biyu ba wanda ya tsira.” Zumbur ya mike yace wuta…..Wani murmushi ya saki na gamsuwa da shawarar data zo mai a yanzu. + Turawa yai a kiramai wani bawansa wanda ya sa aka bashi matsayi a gidan sarauta saboda tsabar yardar da yamai, bawa ne wanda baya ko tambayarsa dalili in ya saka shi abu, baya taba musa mai ba kuma ya neman sanin dalilinsa na sashi abun. Yana zuwa ya jashi cikin kuryar d’aki ya sa bakinsa a saitin kunnensa alamar rad’a ya fara mai bayani wanda ni da nake tsaye a gun ma bansan mai ake cewa ba. Itakam Basira da Babynta bayan Magrib suna kwance akan gado Lantana na kasa tana ninke kayan data wanke tana ta shirya musu jaka matar Yayanta ta shigo. Basira na ganinta ta fara kokarin mikewa, da saurin tace ” koma ki kwanta.” Itakam Basira mikewa tai ta zauna, kallan Lantana matar tai tace “Lantana d’an bamu guri.” Da sauri Lantana ta mike tai waje. Kallan Basira tai sannan tace ” Basira.” Yanda ta kirata yasa Basira ta tattara hankalinta gaba d’aya kanta. Ta cigaba ” Wani irin zama kukeyi da Yayar wanda yazo?” Basira tace ” zaman mutunci mukeyi.” Ido ta kura mata sannan tace ” gaskiya nakeso ki fadamin.” Basira taja numfashi sannan tace ” wlh da gaske nake tana kula dani nidin ce zuciyata taki yarda da ita.” Meyasa? Abinda taji ta fada kenan. Basira tai shiru kafin can tace ” gabana fad’uwa yakeyi in na ganta.” Shiru tai sannan tace ” ki nutsu kiji mai zance, tun bayan zuwansu hankalina yaki kwanciya da yanda naga yayanta yana kallan yaron nan, kallo ne na tsana tsantsa.” Basira tai murmushi tace ” kedai kila baki fahimceshi bane amma……” Katseta tai da cewa ” Basira zaman gidan sarauta ko ba’a fada ba kasan ba wai zama bane wanda kowa zai soka, bare ke da kika haihu, ki kasance mai hakuri sannan kar ki bari ko kad’an a cutar miki da d’anki.” STORY CONTINUES BELOW  Murmushi Basira tai tace ” ki daina damuwa ba komai insha Allah.” Sun dade a d’akin kafin ta mata sai da safe ta fito. Wajen karfe 1 na dare Basira ta farka sakamakon kukan da Jaririn yake mata, kuka yake sosai ta mike tana bashi mamma, Lantana ta amsheshi tace kawoshi na fita dashi na lallabashi ki samu ki kwanta. Nan ta amsheshi tai waje dashi, kamar wasa tana jijashi taga hayaki sosai yana tasowa daga wajen d’akin Amadu. Cikin tsoro ta koma ciki dayakr ta kofar baya ta fito a kuma nan d’akin Basira yake, Basira ta gani tana ta tari cikin bacci. Nan ta fara tashinta, dakyar ta samu ta tasheta, ganin yaron nata tari shima yasa Lantana tasa zani ta goyashi. Basira cikin tsoro tace ” menene hakan?” Lantana tace bansani ba nima sai dai hayaki na tasowa daga can. Da sauri Basira ta mike ta nufi ciki, tana bud’e ‘yar karamar kofar da zata sadata da wajen su Amadu, da yake gini ne irin namu na da, kowa da inda yake sai dai shi yayi dabarar ginewa tsakanin nasu da inda Basira take sai yar ‘yar kofa a gun. Basira na bud’ewa taga wuta sosai tana ci ta b’angaren su Amadu, ihu sosai ta kwalla wanda yasa Lantana tahowa da sauri. Ganin yanda wuta ke cin b’angarensu Amadu har ta fara gangarowa inda suke yasa ta saki ihu itama, daga waje sukaji mutane an fifito, Basira kam neman cusa kai takeyi b’angaren su Amadu, ganin yanda ta fita hayyacinta tana ihu tana kiran yayanta da matarsa yasa Lantana ta fara jan hannunta. Fizgewa tai da karfi ta kara nufar ciki, Lantana ta kara riketa tana ihu akan a kawo musu a gaji, nan wasu maza sukai tunanin bi ta baya, suna shiga sukaga yanda Lantana ta kankame Basira tana ihu, nan fa suka kamo Basira sukai waje da ita, ihu take sosai akan a taimako mata yayanta. Suna kaiwa waje gidan ya kara kamawa sosai ihu sosai Basira take ana ririketa, can ma kawai sai gani akai ta suma. Mahaifin Sani wanda yazo gun yasa aka kaita gidansa, sosai ranar anga tashin hankali a unguwar, daga Amadu har matarsa sun kone a ciki, dan da alama bacci suke wuta ta taresu. _Nace Allah ya jikansu Ameen_ ******* Itakam Basira sai wajen asuba ta fardo, kuka kawai takeyi, sai wajen hantsi bayan anyi jana’iza mahaifin Sani ya kalleta cikin tausayawa yace “Basira ya akai wuta ta kama haka?” Kai ta shiga jijigawa akan bata sani ba, shiru yai sannan yace ” da matsala.” Kallansa tai cikin mamaki tace name?” Yace ” Basira wanda suka zo gidanku jiya masu rawani dan bansan matsayinsu ba.” Kai ta gyad’a alamar ta sansu, yace “kinsan ko jana’iza basu zo ba, kawai tambayata yai akan kina raye? na sanar dasu kina raye kina gidana, sai ya tambayan yaron fa? Ni kuma sam banga yaro ba alokacin sai nace mai ban sani ba gaskiya dan nima a rikice nake, abinda yaban mamaki yanda naga idanunsa sunyi alamar bakin ciki na kasa gane bakin cikin namenene a ciki, na rashin mutuwarki ne ko na rashin sanin halin da yaron yake ciki.” Zatai Magana Lantana ta zo da sauri tace ” Ranki ya dade nima naga Kafilu(wannan bawan na Waziri) a lokacin da muka fito sai dai abinda yaban mamaki daga nesa na ganshi ina kallo ya juya yai gaba ba tare da yazo inda muke ba.” Basira ta kalleta tace “ya akai kika san shine bayan dare ne?” Tace ” akwai hasken farin wata sannan akwai hasken wuta da take ci.” Basira bata sake magana ba ta mike zata fita, jitai yace ” ni zan fita gun amsar gaisuwa.” Basira ta mike ta koma ciki, kallan Abu Turab tai sannan tai shiru tana tunani, randa ta zubar da jini sosai har ta d’auka tayi b’ari shine ya fara zuwa mata, ba shakka ranar abu d’aya taitacu wato tuwon da Magajiya ta kawo mata, sannan ansha sanar da ita akan ta kiyayi Magajiya da Yayanta dan hatta Mahaifiyarsa sai datace mata tai a hankali da Magajiya. Tuno maganar matar Yayanta tai, zumbur ta mike idanunta duk sun kumbura. Hijab ta zura tai waje, tana gani yanda mutane suka taro a waje amma da yake idanunta sun gama rufewa yasa tai gaba. Gidan Hakimi ta nufa inda Hisham yake, basu tsaya mata wasu tambayoyi ba suka mata izini ta shiga wani ya mata jagora, sai da suka kusa zuwa d’akin da yake sai wanda ya mata jagorar yace ” bari na kirashi.” Nan yai gaba, daga lungun dake bayanta taji ana magana kasa kasa, jitai ance ” ina kallansa ya fita da daddare ni kuma da gulma sai dana bishi wlh a idona ya d’au kalanzir da ashana yai gidan.” Nidai tsoro yasa na juyo, ni dama nayi mamaki sosai danaga Waziri kamar bai damu ba da haihuwar nan bayan kuma kowa yasan abokin takara zai zamewa d’an Magajiya nan gaba.” Jikin Basira ne ya fara rawa, da sauri ta juya cikin kid’ima, tana shiga gida ta kalli Lantana dake cikin mutane alama ta mata da hannu akan tazo, d’aki suka shiga, Basira cikin rikicewa tace ” Lantana ke Baiwa ta ce ko?” Kai ta d’aga, tacigaba ” kin yarda da duk abinda zanyi?” Nan ma ta d’aga kai, Basira tace ” zan fara fita, zan tsaya a karshen layin nan in nai minti biyar ki biyoni. Ba tare da tambaya ba Lantana ta amsa da to, Basira ta kalli Abu Turab tace “Dolene in kareka, nayi rashin yayana da matarsa akan shirme da rashin wayau na dan haka bazan yarda inyi rashinka ba a wannan halin, hawaye ne suka shiga zubo mata, lalai bazata taba yafema Hisham ba in har da bakin Magajiya itama bazata taba yafe mata ba, sannan zata kare d’anta har zuwa lokacin da zai girma ya daukar mata fansar abinda aka mata. Cewa tai Lantana ta fita, Lantana na fita ta had’e kai da gwiwa ta saki wani irin kuka mai tsananin ban tausayi. ******** Da yake yaran da suna dadewa kafin ma su dinga bud’e idansu sannan ko sun bude ma ba alokacin zasu fara gani ba shi yasa sam Basira batai tunanin an ma d’anta wani mugun abu ba. ********** Yanda suka tsara hakan ce ta faro, ta goya d’anta ta fita, ta dade da fita sannan Lantana tabi bayanta……. To fa abin babba ne🙊 ( Abu Turab an haifeshi a shekara ta alif dubu d’aya da d’ari tara da saba’in da d’aya, shikuma Abdulmajid an haifeshi a alif dubu d’aya da d’ari yara da saba’in, karku manta farkon labarin a shekara 1970 aka fara wanda ya kasance ranar sunan Abdulmajid, a kuma shekarar ne Sarki ya auri Basira har ta samu ciki.) _Wannan tuni ne_ ******** Hisham ya fito sai dai baiga kowa a waje ba, ciki ya koma cikin halin ko in kula dan shi babbar damuwarsa bai wuce ya d’au mataki a kan Basira da d’anta ba dan tuni aka sanar dashi suna raye, ba shakka inya sake wani yunkuri za’a gano bakin zaren shiyasa yake tunanin in suka tafi a hanya ya zama dole ya san yanda zaiyi kafin su karasa garin. ********* Magajiya tun bayan tafiyar Hisham ta rasa inda zata sa kanta, ya zama dole ta fitoda wata sabuwar hanya ta yanda zatai in har d’an ya dawo, ita ta kasa yarda da komai ma. Mamaki ne ya kamata jin sallamar Jakadiya, ta dade sosai kafin ta bata izini, Jakadiya ta shigo tare da washe baki, ta matso kusa da Magajiya ta zauna a kasa sannan ta kalleta ta mata jinjina tace ” Sai ke Sarauniyar da babu irinta, ba aiba kuma baza’ai irinki ba, kinci dubu sai ceto takawarki lafiya matar sarki, takawarki lafiya mamar sarki, takawarki lafiya Haj…….”+ Wani banzan kallo Magajiya ta mata tace ” me kike aikatawa yanzun?” Jakadiya ta washe baki tace ” wato Ranki ya dade matsala aka samu ai yayatace bataji dadi ba shi……” Wani mugun murmushi Magajiya ta sakar mata tace “Babu ruwan kwai da aski, abinda nakeso naki shine ke din wacece?” Yawo ta had’iya sannan tace “taki ce sai dai……” Magajiya tacigaba ” waye ya baki wannan matsayin wanda kike takama dashi?” Jakadiya tai zuruzuru da ido, da kyar tace ” kece.” Magajiya tai wata ‘yar bazawarar dariya tace ” kinsan da haka ke har kin kai matsayin da zakiyi tunanin yimin karya?ke d’in wacece da har….” Da sauri Jakadiya ta sa gwiwowinta a kasa tace ” Magajita tuba nake, sai dai kafin ki yanke hukunci yakamata ki duba yanda nake miki biyayya, nasani sarai Yarima ba…….” Gaban Magajiya ne ya fad’i ta kalli Jakadiya a tsorace, dama Jakadiya tasan wannan ce kadai hanyar dazaisa ta tsira inhar ta nuna mata ta san sirrinta. Jakadiya tai saurin rufe bakinta tana waige waige tace “tuba nake ranki ya dade, wannan sirri ne da zan rikeshi har kabari na, tuba nake da subutar baki.” Magajiya ta danyi kifikifi da ido sannan ta daure tace ” me kike san cewa?” Jakadiya tace ” tuba nake Ranki ya dade ai sirri ki nawa ne, baza’aji wannan zance daga gareni ba.” Ganin tabbas Jakadiya tasan wani abu sai dai da alama batasan duka ba yasa ta daure tace ” tashi kije ni ina bukar hutu.” Nan Jakadiya tai waje da sauri.1 Tana fita tai dariyar mugunta tace ” ni da gidan nan da matsayina mutu ka raba.” ********* Sarki ya kasa zaune ya kasa tsaye, yau ya kamata su Hisham su dawo sai dai yajisu shiru hakan yasa da kansa yai tattaki zuwa b’angaren Magajiya. STORY CONTINUES BELOW  Zagi(wanda yake ma sarki iso sannan yake zama a gaba duk inda zaije ya sanar da isowar Sarki.) Mikewa Magajiya tai cikin mamaki, masu kula da ita ne suka shigo suka kara sanar da ita, nan ta fito dan tarbarsa. Sai daya shiga ya zauna, sannan ya kalleta yace ” Hisham fa? Bayau zai dawo bane?” Kallan mamaki tamai wato abinda ya kawoahi b’angarenta kenan?so yake yaji zancen matarsa da d’ansa kenan.” Murmushi ta saki duk da bakincikin da take ciki tace ” mai zaisa hankalin Mai Martaba ya tashi bayan na tabbata yanzu suna hanya?na tabbata ka matsu kamar yanda nima na matsu inga d’ana.” Sarki ya d’an kalleta yace ” niba saboda haka nake tambaya ba, akwai abinda nakeso najine daga bakin Waziri.” Murmushi tai tace “Angon Karni ai ba sai kayi kara ba, nima d’a na ne.” Kallanta yai yana mamaki, sai dai yana jin dadi sosai na yanda takesan d’ansa. Yace ” Ina AbdulMajid?” Tace ” d’azu Uwar Soro( Mahaifiyar sarki, ko yayarsa ko gwaggonsa. ko uwargidansa, wadda ta wanke shi. wadda ke iya gaya masa duk abin da ake jin nauyin gaya masa, ita ake kira uwar soro.) Amma ita Mahaifiyarsa take nufi dan a lokacin nasu ita ake kira da Uwar Soro. Murmushi yai sannan yace ” ni zan koma.” Kallansa tai a ranta tace ka gama abinda ya kawoka kenan? Amma a fili tace ” ina godiya da wannan ziyarar Ranka ya Dade.” Yana fita ta d’anyi kwafa cikin takaici tace ” ni zaka wulakanta?” ************ Basira kam tana gaba Lantana na baya ta kasa mata magana ganin kawai tafiya takeyi da alama batama san inda takesa kafarta ba. Abu Turab na bayanta, ko da Lantana tai yunkurin ansarsa Basira taki. Sunyi tafiya mai uban nisa dan Lantana harta gaji, itakam tafiya kawai take dan hankalinta baya jikinta, tunanin yayanta da matarsa sun mata yawa, sai da taji Abu Turab ya sa kuka sannan hankalinta ya dawo jikinta. Kallan inda suke tai daji ne sosai juyowa tai ta kalli Lantana sannan ta nemi guri ta zauna ta kunto shi daga bayanta, Lantana ta zo kusa da ita ta tsuguna sannan tasa hannu ta fara danna mata kafarta dataga ta kumbura. Basira kam shayar dashi kawai take ko magana batayi, idanunta ya kafe kaf ta kasa ko hawaye bare taji sanyi a ranta. Sai da Lantana ta danna mata kafa sosai sannan ta kalleta tace ” bakici abinci ba ranki ya dade.” Basira kai kawai ta girgiza mata, ganin ya koma barci yasa ya fara neman goyashi, Lantana tai saurin amsarsa ta sashi a bayanta suka cigaba da tafiya. “********** Shikam Hisham da yamma yai tunanin zuwa gaisuwa sannan ya sanar da ita tafiyarsu gobe, dan ya tabbata in bai je ba sai gulmar abin ta bazu a garin killa ma dogarawan da suka zo su kai gulmar har masarautarsu. Bayan sunzo gidan ne, ya nemi a kira masa Basira ya mata gaisuwa, sai a lokacin aka farga da rashin su a gidan. Tashin hankali nan fa aka bazama naimansu, ganin Basira bamai yawo bace sannan ba Lantana ba kuma d’anta, wannan ya kara tadama mutane hankali, tun azahar ake nemansu amma ba labari…. Hisham kam hankalinsa ya kara tashi har ya fara zargin kila ko ta samu mota ne ta tafi Zazzau, wannan al’amari ya kara tada mai hankali sosai da sosai…… ********* Basira kam sai da ta fara hakki sosai sannan ta samu ta zauna, dan tafiya kawai suke sai dai in Abu Turab yayi kuka su tsaya yasha sannan su ci gaba da tafiya. Lantana ta matso tace “Ranki ya dade dan Allah ki samu ki huta?” ita kanta Lantana hakki take sosai ga magrib ta kawo kai dan rana saura kiris ta fad’i. Kallan inda suke tai, wani kauyeni da ba mutane sosai, nan suka karasa kauyen. Wani tsoho suka gani a zaune yana wanke alo da alama rubutu yai, lantana ta gaisheshi tace ” Baba dan Allah ka taimaka mana da gun kwana zuwa gobe.” Kallansu yai ya kalli Basira wacce ke tsaye kamar zata fadi, yace ” ku shiga ciki kafin wannan ta samu ta kwanta. Lantana ta shiga mai godiya, Basira kam jiri ne yake d’ebanta, tsohon yace “kuyi sauri ku shiga.” Da kayar Basira ta daure tace “Mun gode.” Sannan suka nufi ciki. Sun shiga ciki sukaga ba kowa a tsakar gidan, nan suka tsaya suna sallama, Basira kam jingina tai da bango. Wata matace ta fito daga bayan gida rike da buta a hannunta ta amsa sallamar tana kallansu, nan Lantana ta gaisheta ta amsa, Lantana zatai magana sai taji muryar tsohon nan ta bayanta yana cewa ” ‘yata basu guri su huta sai suyi alwala ki basu abinci.” Ba tare da musu ba ta amsa da to, sannan tace ” ku shigo.” Sun shiga wani d’aki wanda da alama nata ne d’aki ne an sa gadu guda biyu d’aya nai rumfa kato sannan sai d’an karami a gefe, sannan ancika d’akin taf da jere na samiru da ‘yan china. Akan tabirma data shimfid’a musu suka zauna, sannan ta zauna itama suka gaisa(wannan shine halin mutanen mu na da basa yarda ayi gaisuwa a tsaye ko me suke yi sunfiso suna daga zaune a gaisa)+ Nan ta mike tai waje, Abu turab ya d’an fara abin kuka, hakan yasa Lantana ta kuntoshi daga bayanta ta fara jijigashi ganin ita kanta Basira yunwa takeji ina zai sami ruwan nonon da zaisha? Itakam tana tausayin Basira ganin tana tafe da d’anyen jego. Matar ce ta sake shigowa rike da fitilar kwai ta ajiye musu sannan ta mike zata fita, kallan Abu Turab tai cike da sha’awa tace ” Tabarkalla masha Allah sai dai da alama ba’a dade da haifarsa ba.” Lantana tai murmushi tace ” yau fa kwanansu biyu.” Cikin tsananin mamaki ta kallesu tace “da jego haka d’anye kukai tafiya?” Lantana tai shiru batace komai ba, kallan Basira tai wanda ganin yanda ta galabaita yasa ta fahimci itace Uwar, waje tai da sauri ta karasa murhu ta kada miyar kuka wanda dama ta saka komai kadawa kawai zatai. Tana gamawa ta kawo musu tuwon dawa miyar kuka tasha manshanu. Nan fa suka fara cin abinci, sosai Basira taci abinci. Sai da suka gama sannan Lantana ta tashi tai sallah tunda Basira tana fashin sallah na jinin haihuwa. Sunyi shiru a d’aki shikam Abu Turab bacci kawai yakeyi. Basira tunani duk ya isheta da bakin cikin yanda rayuwa ta risketa. Daga waje sukaji kamar ana dan fada, Lantana ta kalli Basira, jisukai ancigaba da fada ” wlh yau bazan bar gidan nan ba sai Shehu ya biyani kud’ina kaf dan kuwa na gaji da wannan rainin wayan.” Hakuri sukaji ana badawa amma kamar zuga matar ake sai kara masifa takeyi da k’ak’aji. Basira ta daure ta mike ta fita wajen, Matar da ta kula dasu ta gani zaune a gefe tana kuka, sai kuma wani mutumi a tsaye kusa da ita, ga matar nan da take ta masifa a tsaye a kansu. Wata matace ta fito daga wani d’aki daga gefensu ta saki wani gud’a cikin farin ciki tace “Allah kasheni saboda farinciki, lalai yau take sallah a gurina, anje anci bashi anyi aure gashi an kasa biyan kudin da aka ranta, yo dama ina za’a iya biya tunda an auro mai farar kafa?” Basira ta kalli matar yanzu ta gane inda abin ya dosa, da alama waccan din uwar gida ce, mijin yaci bashi ya auri wannan gashi kuma ba damar biyan kudin?” Mai kudin ta kara zak’ewa tana ta zabga masifa, Basira ta fito ta zo kusa da matar sannan ta zare sarkar dake d’aure a wuyanta, sarka ce ta azurfa wanda a waccan lokacin kudi ce sosai, cikin mamaki matar ta kalleta sannan ta amsa ta shiga dubawa, tabbas azurface mai kyau da tsada wacce kana gani kasan sai mai hali sosai shine zai sa ta. STORY CONTINUES BELOW  Shehu ya kalleta cikin mamaki sannan ya kalli matarsa yace ” wacece?” Hawayene ya zubo mata, zatai magana matar tace ” kina nufin kin bani duka?” Basira tace ” ki saidata kid’au kud’inki ki ba matar nan ragowar.” Wannan d’ayar matar mai guda ta matso da sauri tace ” baiwar Allah ked’in wacece?” Basira ta juya ba tare da ta amsata ba ta koma ciki, Dattijon nan wanda ya kawo kai daidai lokacin da Basira ta mika azurfa ya share kwalla da ta taru masa, ba shakka dama yaji ajikinsa alhere ne su yana kallansu ya kalli yaron. Matar ta kalli Shehu tace ” Shehu ina ka samo wannan?wlh ka bincike ta in har ba matar wani hamshakin d’an kasuwan bane to tana da dangantaka da sarauta, inba haka ba a wannan zamanin waye zai baka wannan shamfad’ed’iyar azurfar?” Shehu ya fizge azurfar daga hannunta yace “uwar san banza kud’inki dana ranta ko rabin wannan baikai ba, inyaso gobe kizo muje mu sai data inbaki kud’inki.” Haushi ya kamata, haka tanaji tana gani tai waje. Uwargidansa ta matso da sauri tace “Shehu kawo na ajiye ma,kasan na iya ajiya.” Harara ya maka mata yace “kingama gud’ar?” Kallansa tai cikin zolaya tace “kai bakasan wasa ba?” Tsaki ya ja sannan ya mikama Amaryarsa azurfar yace ” ajiye tukunna sai na nemi shawar Baffa.” Yana fad’a yai hanyar waje, a tsaye yaga Mahaifinsa, tsayawa yai kusa dashi kansa a kasa. Mahaifinsa yace “biyoni ciki.” Nan yai gaba shima ya biyoshi. A tsakar gida ya tsaya, nan Amaryar tai saurin shimfid’amai tabirma, ya kalleta yace “sannu ‘yata, d’an shiga ki kiramin bakin nan.” Nan tai ciki da sauri, sun fito sun zauna a kan wata tabirmar, nan ya kalli Shehu yace ” Zauna kaima.” Nan ya zauna matansa ma duka suka zauna. Shiru ne ya biyo bayan kafin yace ” Bismillahi Rahmani Rahim, ita bismillah ana san a fara ta akan duk abinda mutum zai aikata, dan haka yana da amfani mutum ya dinga yinta akai akai.” Kai suka jinjina sannan yacigaba ” Baiwar Allah ya sunanki?” Basira! Abinda ta fada kawai kenan kanta na kasa, yacigaba ” daga ina kuke?” Tace ” katsina.” Yace ” bazan tambayeki rayuwarki ba da yanda kikayi ta da abinda ya fito dake ba sai dai inaso inji abu biyu, na farko wannan yaron ta wani hanya kika sameshi?” Lantana zatai magana Basira ta rike mata hannu sannan tace ” Allah shine shaidata aure nai na sameshi.” “Alhamdulila!” Abinda ya fada kenan sannan yace ” tambayar karshe, Yanzu da kuka fito ina zaku?” Basira tace ” ni kaina bansani ba, na rasa yayana wanda shi kadai ya ragemin sannan dole ne in taimaki d’a na.” Shiru yai kafin yace “Shehu.” Da sauri yace “Naam Baffa.” “a guara musu bangaren mahaifiyarka su zauna.” Ya amsa da to, sannan yacigaba ” ku zauna anan har iya lokacin da kukaji zaku koma, ni limami ne a nan garin kar kusa komai a ranku ku zauna anan kamar kuna gidanku.” Godiya suka shiga yi, Shehu ya mika mata azurfarta, yace ” karki damu zan….” Kai ta jijiga sannan tace ” karka damu nayi ne dan Allah da kuma darajar taimakon da aka mana, nima bani akai dan na bada kuma ba wani abin bane.” Da wannan aka tashi. Amarya wato ( Kubra) ta mike tai b’angaren mahaifiyar shehu wacce ta rasu wata 5 da suka wuce, b’angarenta daban ne dan sai ka d’anyi tafiya kadan ka shiga kofa sannan zata sadaka da b’angarensu. ************ Tashin hankalin da Hisham ya shiga baya misaltuwa haka suka isa Zariya duk ya gama rikicewa, suna isa yai fada da sauri, Mai Martaba kam ana cewa Hisham ya iso hankalinsa ya kasa kwanciya saboda tsananin farin ciki, kofa kawai ya kurama ido yana jiran shigowar Hisham. Ganin Hisham ya shigo yasa yai ajiyar zuciya, nan Hisham ya matso duk ya birkice ya gaidashi ya d’auka zai haushi da fada akan yabar matarsa ta taho ita kadai, sai jiyai Sarki yace “Hisham ka dawo lafiya? Sannu da kokari ba shakka ka sha tafiya.” Hisham ya share zufa cikin tsoron abinda zai faru, Sarki yace ” ka je gida ka huta kasha tafiya.” Nan Hisham yai godiya yai waje. Mai martaba yai murmushi, yau zaiga Basira da d’ansa, burinsa na sa wannan suna yayi. Bazai taba mantawa ba tun sanda mahaifinsa ya bashi labarin sunan a lokacin da ya ganshi ya kwanta a kasa, ya sa aransa sai ya sa sunan nan. (_Sunan Abu Turab sunane wanda Manzon Allah ya sawa Sayaddina Ali a yayin da ya ganshi ya kwanta a kasa, yai murmushi yace Abu Turab wato Father of Soil.” Murmushi ya sake yi. Shikam Hisham na fita yai gun Magajiya da hanzari. Tana tsaye ya sameta dan itama hankalinta ya tashi jin ance Hisham ya dawo amma shi kadai ne ba tare da Basira ya dawo ba. Yana shigowa ta tareshi da cewa ” Yaya meke faruwa?” Hisham ya rikice yace ” Magajiya muna cikin matsala.” Matsala?tame kenan?” Nan ya kwashe komai ya sanar da ita, kanta ta dafe cikin tashin hankali tace ” yanzu kenan bamusan a wani hali take ba daga ita har d’anta?” Yace ” tuba nake.” Wani tulu dake gefenta ta buga da karfi hakan yasa ya fashe, cikin tsoro Hisham ya kalleta, idanunta sunyi ja cikin fada tace ” meyasa baka aiki da hankali? Me kake tunani zamu cema Sarki? Bamusan ta mutu ba ko tana raye, in mukace mai ta mutu ta dawo fa? Muce me? In kuma mukace tana raye to tana ina? Me yasa Hisham sam wani sa’in kanka baya aiki? Ni kaji daga bakina nace ka kona musu gida? Waye ya baka damar aiwatar da abinda ban umarce ka ba?” Hisham takaici ya kamashi, me wannan yarinyar take nufi? Cikin fad’a tace ” jeka banasan ganinka sannan kar ka shigo gidan sai nan da kwana biyu ni zan san yanda zanyi.” Jiki a sanyaye yai waje, wani dogon tsaki taja ta d’aura hannu akai cikin takaici yanzu ya zatai? Shiru tai ta shiga dogob nazari…….. _Hmmmmm_ Ana Magrib Magajiya ta kintsa tsaf sannan ta aikama da Sarki zuwanta, alokacin hankalin Mai Martaba ya gama tashi dan yana tasowa daga fada ya aika wani bafaden sa akan ya dubo masa lafiyar matarsa da d’ansa kafin yazo sai dai abin mamaki dawowa akai aka sanar dashi rashin isowarsu gidan.+ Magajiya ta iso a lokacin shi kansa ya matso ya ganta dan yana san jin abinda ke faruwa. Bayan ta shigo ne ta zauna a inda ta saba zama wato d’an nesa dashi kadan, sannan ta numfasa cikin isa da kuma nuna alamar damuwa tace ” Ranka ya dade muna cikin matsala fa?” Kallanta yai cikin mamaki sai dai bai amsa ba, itama ta kalleshi sannan tace ” Basira bata dawo ba.” Kallanta ya sakeyi nan ma bai tanka ba, idanu ta runtse cikin alamar kunar zuci na tausayi tace ” gobara ce ta kama da gidansu a daren jiya.” Lalai wannan kalma ta d’agamai hankali wanda bai san sanda ya mike tsaye ba, Magajiya ta kalleshi cikin kulawa tace ” Yayanta da matarsa sun rigamu gidan gaskiya.” Sarki a tsaye yake kawai dan hankalinsa ya kai koluluwar tashi, ta cigaba tare da share idanu kamar irin mai kwallar nan, tace Basira da d’anta dai ba abinda ya samesu sai dai firgita datai da abin yasa ta fita da gudu wanda har safiyar yau ba wanda ya ganta. Hankalin Sarki ya kara tashi ya koma Ya zauna dabas kamar ba sarki ba. A hankali ta taso tazo inda yake tasa hannu ta kamo nasa hannun tace ” nasani sarai hankalinka ya tashi sosai kamar yanda nawa ya tashi, shiyasa na rasa mai zance maka, Hisham tun safe yake nemanta amma ba labari wanda hakan ne yaga dole yazo ya sanar dakai asan abinyi.” Kallanta yai ji yake kamar ya saki wani irin ihu na bakin ciki, Magajiya cikin murya taban tausayi tace ” Basira ba yarinya bace na tabbata zata dawo hankalinta ne ya tashi har yasa tai wani hannu sai dai fatan Allah yasa ta fad’a hannu na gari.” Sarki ya d’ago cikin tashin hankali wanda tunda Magajiya take bata taba ganinsa cikin wannan yanayin ba, kallanta yai cikin kakkausar murya yace ” inasan kad’ai cewa.” Kai ta jinjina alamar to, sannan ta mike ba tare da tace komai ba tai waje. Tana fita ta kalli kofar d’akin tai wani murmushi tace ” kai da Basira sai a lahira dan duk yanda kaso ko ita taso baku isa ku kara zama tare ba bare har kaga d’anka ka fahimci menene d’a na jini.” Juyawa tai tacigaba da tafiya ana take mata baya cikin kasaita da tak’ama. ************ Shikam tana fita ya runtse idanunsa kam jiyai hawaye ya gangaro mai sau d’aya, mikewa yai yaje jikin tagar d’akin ya bud’e ya kurama taurari ido,jiyake kamar zuciyarsa zata fashe ga zuciyarsa ta fara masa sake sake mara amfani, yana tsaye yana kallan taurari sai dai a zahiri tunani ne fal ransa, nan ya shiga tunanin rayuwarsu da abokinsa da kuma matarsa ga kuma bai taba ma ganin d’ansa ba,kasa jure abinda ke ransa yai ya tsugunna a gun tare da dafe kansa wanda ya fara sara mai…. A wannan ranar Mai Martaba ko gadonsa bai hau ba bare ya samu danar rintsawa. ************ Basira ma bataga bacci ba a wannan ranar, tunani ne kawai ke mata yawo a ranta, ido ta kurama d’anta tana ji wani abu na taso mata, ya zatayi? Zama zatai tayi anan saboda tsoron kar wani abu ya samu d’anta? In tai hakan kenan ta raba d’anta da mahaifinsa, sannan auranta fa?” Wad’annan tunanukan sun mata yawa fal aranta wanda sukasa idanunta suka kafe kaf. STORY CONTINUES BELOW  *********** Magajiya ta sanar da Hisham yanda sukai da Sarki sannan ta sashi yaje ya nema ayima Basira magani akan karta waiwayi gida, a mata maganin da zaisa taji sam batasan gida.” ******** Tun bayan tasowar Abu Turab suka kula da rashin ganinsa, da farko sun d’auka lokacin ganin nasa ne baiyi ba sai dai ganin ya kai wata 4 yasa suka fahimci akwai matsala da idanunsa, haka ya taso ba idanu sai dai Allah ya bashi hazaka wanda ko zama kai dashi na awanni sai ka fahimci hakan, yanada baiwa sosai ta fahimta da rike abu. A duk sanda Basira tai tunanin komawa gida sai taji zuciyarta ta kuntata, hakan yasa ko maganar batasan a mata, Lantana kam ko da wasa bata taba tambayarta ba, haka mutanen gidan. Abu Turab har yakai shekara 5, Baffa shi yake koya masa karatu, yana tsananin san yaron saboda san karatunsa da hazakarsa, Basira ta d’aurashi a kan tarbiyya mai tsananin gaske, ko laifi ya mata wanda bai kai ya kawo ba haka zatasa shi a tsakiyar rana gashi bashida ido sai yayi kusan awa uku a tsaye, gashi bai isa yai kuka ba, dan kuwa in ya kuskura yai to fa lalai zai gamu da hukunci mai tsananin gaske, a haka in ka kalleshi bazaka taba cewa baya gani ba dan kuwa idanunsa garau suke, bata bari a taimaka mai har sai intaga yana neman faduwa ko yana neman taimakon sosai, komai da kansa yake yi, zakasha Mamaki in har kaga yanda Basira take tsananta tarbiyar d’an nata. Abu Turab ya taso mai tsananin jarumta gashi dama magana bata wani dameshi ba dan ko abokai bashida shi sannan yaro ne wanda in yana abu dole ka kalleshi domin jinin sarauta na yawo a jikinsa yana da jinkai sannan ko magana yakeyi zakasha mamaki. Shigarsa Shekara bakwai ga tsufa ya kara kama Baffa, yanzu ko fita zaiyi sai an taimaka masa, a yau ya tashi da zazzab’i wanda yasashi zama a d’aki, Abu turab na zaune kusa dashi yana mai karatu kamar yanda Baffa ya sashi. Bayan ya gama ne Baffa yace ” D’ana(haka yake cemai.) kiramin Mahaifyarka.” Abu Turab ya mike rike da karamar sandar da yake tafiya da ita ya isa b’angarensu, A waje yaji muryarta hakan yasa ya matsa kusa ya sanar da ita sakon baffa. Mikewa tai ta zura hijabinta ta fita, Lantana na zaune tana sana’ar mangyad’a wanda dashi suke rayuwa, ya matsa kusa da ita dan yanajin sautin aikin datake, zaiyi magana yaji tace ” Ka zauna.” Tai maganar tare da tashi a kan kujerar ta ta nuna masa gun zama. Shiru yai hakan yasa ta rike hannunsa ta zaunar dashi. Murmushi yai yace ” Lantana baki tab’a kiran sunana ba tunda nake dake.” Kasa tai da kai a ranta tace ” ina na isa?” Murmushi ya sakeyi yace ” Kujerar da kike kai kika bani ko?” Batai magana ba sai dai a ranta tace ” dole na ne ai.” Mikewa yai ya nufi hanyar cikin d’aki.” ********* Basira zaune kusa da Baffa wanda ya ke a kwance, Baffa ya kalleta yace “Banso na miki magana da kaina ba sai dai inaji a jikina lokaci na ya kusa hakan yasa dole na kiraki.” Kallansa tai sannan ta maida kanta kasa, Baffa ya cigaba” Basira ya kamata ki koma gidanki inhar akwai aure akanki to fa lalai kina d’aukan zunubi ne.” Kallansa tai idanunta suka kad’a sosai ga mamakinsa hawaye yaga tana zubarwa. Kallanta yai cikin tausayawa yace ” ba tillasta miki nake ba sai dai shawara nake baki, in har da aure akanki nace nima ba wani abu ba.” Hawayenta ta share sannan tace “Sunana Basira……….” Kaf abinda ya faru da ita ta sanar dashi. Baffa hawaye ne ya gangaromai saboda tausayi, shiru ne ya biyo baya a d’akin domin kuka sosai takeyi miken dake binne a zuciyarta ya tashi. Sun dade a haka kafin Baffa yahau addu’a, sannan yace” nayi zargin wani abu sai dai rashin sanin labarinki yasa ban tab’a sanar dake ba, sai dai yanzu zargin da nakeyi inaji ajikina hakan ne.” Kallansa tai cikin rashin fahimta, Baffa ya cigaba ” D’ana, wato Abu Turab banaji a haka Allah ya halliceshi.” cikin mamaki tace ” kamar yaya?” Yace ” sihiri baya taba zama daidai da kaddarar Allah.” Idanu ta zaro tace ” kana nufin…..” “kwarai da gaske, bazan rantse ba kuma bazan miki alkawari ba sai dai kafin Allah yad’au numfashina in dai har sihirine to ni zan karyashi da yardar Allah, sannan inaso kimin Alkawari In har d’anki ya warke zaki koma gun mijinki, Allah ne kadai yasan halin da yake ciki na rashin ku.” Basira tace ” Nagode kwarai sai dai Baffa na rasa dalili sam banasan ai zancen komawata gidan.” Hannayensa ya had’e ya shafi fuskarsa yace ” dole ki cire tsoro a ranki ki taimaki d’anki, ba wai dan ya hau mulki ba a’a sai dan tsira da rayuwarsa, kina tunanin taimakonsa kikai na kawoshi dajin nan? Ko kina tunanin zaki iya canza abinda Allah ya kaddara a kansa ne?” Kai ta girgiza alamar A’a. Baffa ya cigaba ” Abu Turab inaji a jikina yaro ne wanda za’ayi alfahari dashi nan gaba, kada ki kuskura ki rabashi da mahaifinsa, ki zamanto mai yarda da kaddara mai kyau da mara kyau.” Hawaye ta share sannan tace ” na maka alkawari inhar sihirine yana warkewa zamu koma in kuma ba shi bane ma zan maidashi gun Mahaifinsa.” “Alhamdulila, nagode da amfani da shawarata da kikai sannan inkinje ki turomin d’ana sannan ki bashi kaya kala uku a guna zai dinga kwana, yaro ne mai hazaka da ilimi wanda a shekara 7 ya haddace izu 30 wanda tunda nake ban taba ganin yaro mai wannan baiwar ba, ni dashi zamuyi yakin ganin mun warware komai.” Godiya sosai Basira ta shiga yi.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE