KAINUWA CHAPTER 4

KAINUWA CHAPTER 4

Haka Baffa da Abu Turab suke wuni karatu da addu’oi kala kala sannan daga dare yashiga kashi uku Baffa yake tashinsa su shiga saloli da addu’oi, ko waje baya fita, a kwanansu na hud’u Abu Turab ya fara wasu mafarkai cikin dare yake farkawa wani sa’in da kuka sai dai daga ya tashi yake manta mafarkin. Sun dage sosai da addu’oi, karatun qur’ani da saloli. Yau satinsu d’aya kenan Abu Turab na kwance yana bacci hankalinsa a kwance, yau baccib dadi yake masa gashi ko mafarki baiyi ba, Baffa ya sa hannu ya tabashi yace “D’ana tashi lokaci yayi.” Mamaki abin yaba Baffa ganin bai tashi ba, kallan fuskarsa yai sai dai kana kallansa zakasan yana cikin kwanciyar hankali, Baffa yai murmushi sannan yai bismillah ya kara taba shi, addu’ar tashi daga bacci ya fara karantowa bayan ya gama ne ya bud’e ido a hankali duk da yasan duhu kawai zai gani sai dai me? Dishi dishi ya fara gani, cikin tsananin mamaki yace ” Baffa ido na.”+ Baffa ya dafashi yace ” menene? Me idan naka yai?” Murza idan ya shiga yi, Baffa ya shiga karanto addu’oi yana tofa mai, Abu Turab ma yanayi. Cikin tsananin mamaki da al’ajabi Abu Turab yaga tsohon dake kusa dashi, a hankali yakai hannu inda Baffa yake yace “Baffa!” Kallansa Baffa yai shima ya kasa magana sai addu’a yakeyi Allah ya taimakesu. Abu Turab ya tsugunna kusa dashi ya rungumeshi sai ya saka kuka. Baffa ma hawaye ne ya zubomai dan ya fahimci ya ganshi. Abu Turab cikin kuka yace ” Baffa na ganka, Ina ganin komai ga katifarka, ga kayanka nan a lank’aye, ga kwanan abinci nan ga leda nan a tsakar d’akin, Baffa ina ganin komai.” Idanu Baffa ya lumshe yace ” Alhamdulila lalai babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.” Tashi muyi alwala muyima Allah sujjada. Mikewa yai cikin wani jin dadi mara misaltuwa yai waje. Bayan sunyi addu’ar godiya ga mahallici ne ya kalli tsohon yace ” inje gun Ummana?” Baffa yace ” ka barta ta samu bacci zuwa asuba.” Nan ya zauna cikin zakuwa, sai kallan abubuwa yakeyi…… Ana asuba yai b’angaren da gudu jin kofar a bud’e ya shiga bugawa, Basira ta mike a d’an tsorace ta matso tace “waye?” Cikin jin dadi Abu Turab yace ” nine Umma.” Mamaki ne ya kamata da sauri ta bud’e, ya matso da gudu ya rungumeta yana kuka yace ” yau Allah yayi na ganki.” Idanunta ne suka ciciko da kwalla, ya saketa sannan ya kura mata Ido yace ” Umma na ganki, Umma naganki.” Rungumeshi tai itama tace Alhamdulila. *********** Satinsa d’aya da warkewa Baffa ya kara kiranta ya mata maganar tafiya nan, tace nan zuwa kwana uku zasu tafi. Zaune take a d’aki tana kan gado Lantana na kasa haka shima D’an nata. Kallansu tai tace “inaso duk ku bani hankalinku, akwai abinda nakesan sanar daku masu mahimmanci guda biyu.” Tai d’an ajiyar zuciya sannan tacigaba” na farko zuwa jibi zamu tafi Zariya.” Da sauri Lantana ta kalleta shikam baisan me hakan yake nufi ba shiyasa bai wani damu ba. Tacigaba ” abu na biyu wanda yafi komai mahimmanci shine inaso Lantana kada ki kuskura ko da wasa ki nuna Abu Turab na gani.” Cikin mamaki ta kalleta, Basira tace “wannan umarni ne ba shawara ba.” Da sauru Lantana tace ” angama Ranki ya dade.” Basira ta kalli Lantana tace ” d’an bamu guri.” Da sauri tai waje. Basira ta kalli d’anta ta mikamai hannu hakan yasa ya mike tare da zuwa inda take. Basira ta zaunar dashi kusa da ita sannan ta rike hannayensa biyu tace ” nagode kwarai da baka tab’a tambayata mahaifinka ba.” Kallanta yai sannan yai murmushi, ta cigaba ” ka nutsu sosai da abinda zance maka.” Kai ya d’aga alamar to sannan ya kada nutsuwa, tace ” zamu koma gidan da mahaifinka yake wato gidanku sai dai ina tsananin tausaya maka, da farko inaso kada ka nunama kowa kana gani, hatta mahaifinka ka zama makaho a gaban kowa, ka zama mai ido agabana kad’ai.” Cikin mamaki yace ” me…..” Kallan datai mai yasa yai shiru, tacigaba ” banaso ka tambayeni dalilin hakan dan kuwa inka mallaki hankalin kanka na tabbata dakanka zaka sanar dani komai, domin zaka samu cikaken amsar tambayarka.” Kai ya d’aga alamar to,tace ” Abu Turab!” Yanda ta kira sunansa da kakkausan murya yasa ya kalleta jiki a sanyaye, tace “kamin alkawarin zakai wannan abin?nasan kasan me alkawari yake nufi a muslunci ka kuma san hukuncin wanda ya karya.” A hankali yace “na miki alkawari ko mai zai saman bazan nuna ina gani ba.” Ajiyar zuciya tai na jin dadin baiwar da Allah ya mata wato na azurtata da wannan yaron, tacigaba ” gidanku ba kamar gidajan daka sani bane, dolene ka nutsu kaji me zance, da farko duk yanda ranka yaso da b’acci banaso ka nuna, sannan abu na biyu banaso ka zama ragon yaro.” Kallanta yai baice komai ba, ta riga tasan wannan sai dai ya zama tuni amma tun yana karami ta horar dashi akan haka, ita dama matsalarta shine taurin kansa dan inbaiyi niyyar abu ba ko za’amai dukan dazai kasa tashi tofa bazaiyi ba, wannan hali nasa shi take jiye masa. Ta riga ta d’au alwashin sadaukar da komai nata dan ta kare d’anta. Sun dade rike da hannu juna tana mai fada a karshe tace ” in muka koma gun Mahaifinka banaso ka yawaita cewa komai sai ni, dolene ka rage nuna damuwarka akaina, kallan mamaki ya mata a ranta tace (in aka fahimci nice komai naka to lalai za’a nemi yin amfani dakai da sunana wanda nikuma ba lalai in iya kwatarka ba daga hannun makirai.” Abu Turab zaune kusa da Baffa yana jin nasiharsa sun dade suna hira kafin Shehu yazo su zauna, Abu Turab yanajin hirar tasu har bacci ya d’aukeshi. Sukam sunyi hira sosai, da shehu ya mike zai tafi sai yasa hannu zai d’auki Abu Turab akan kaishi b’angarensu. Baffa yace ” barshi anan so nake na kwana dashi.” Nan Shehu ya ajiye shi ya tafi, Baffa ya d’auko rubutun daya wanke ya tashi abu turab yace ya wanke fuskarsa har zuwa kansa, yana magagin bacci ya wanke sannan ya kwanta, Baffa ya dinga mai addu’a sannan ya kwanta. Jin kiran Sallah yasa Abu Turab ya mike, mamaki ne ya kamashi ganin Baffa a kwance yana bacci, kusa dashi ya matsa ya shiga tashinsa, hankalinsa ya tashi ganin ko motsi bayayi. Da gudu yau cikin gida b’angaren Shehu, a waje ya sameshi yana alwala matarsa na tsaye kusa dashi. Abu Turab ya kalli Shehu yace ” Kawu kazo Baffa yaki tashi daga bacci.” Inalilahi wa ina ilaihi Raji’un wannan kalma ita Shehu yai ta ambata, dan ko ba’a fada ba ko bai gani ba yasan me hakan yake nufi….. Allah ya jikan Baffa da Rahama Ameen…….. ********* A ranar da akai uku su kuma suka shirya tafiyar tasu. Sun shirya tsaf ba kaya suka d’auka ba dan komai nasu anan tabarma matan gidan saboda tasan inda zasuje. Shehu shi ya kawosu inda zasu hau mota dan a wannan shekara wato ta 1978 (shekarar Abu Turab 7 sannan shekararta takwas da aure.) a wannan lokacin an sanu cigaban wata yar kurkurar mota bayan akuri kura da motar itace, sai da suka shiga sannan Shehu ya musu sallama ya juya ya tafi, matansa sunsha kuka dan kuwa Basira ce silar zaman lafiyansu.+ A hanya Basira sai kara jaddadama d’anta takeyi akan abinda takesan yayi. Daga baya bacci yai awun gaba dashi, Lantana ta kalleta sannan tace ” Ranki ya dade inasan tambaya duk da dai ba hurumi na bane.” Basira ta kalleta alamar tana ji, Lantana tai ajiyar zuciya sannan tace ” me zakice ya hanaki komawa? Dan ina tsoron kar a miki wani sharrin.” Basira tai murmushi tace ” Lantana kenan, a da na yarda ni sukuwa ce wacce bata tunanin abinda zai faru, sai dai yanzu inada abinda nakesan karewa dolene in canza daga sukuwa zuwa nai dabara, karki damu.” ta karasa maganar tare da dafata. Sun dade suna tafiya kafin a d’an tsaya saboda wasu yaran na mota najin fitsari, nan fa aka fifita hardasu Abu Turab, bayan an dawo ne aka ci gaba da tafiya. Sai yamma lis suka isa garin na Zariya. Basira bayan sun sauka ta kalli Lantana tace “zaki iya gane gidan da na fara zama?” Kai ta kada mata alamar eh, ta d’aura da cewa “sosai kuwa.” “Can zamu wuce.” Ba tare da tambaya ba Lantana ta amsa da to, Abu Turab ya rike sandarsa kamar yanda mahaifiyarsa ta umarceshi, dayake dama idanta a bud’e yake tarau a da d’in ma sai ance miki baya gani tukunna dan in kika ganshi haka bazakiyi tunanin rashin ganinsa ba. Haka sukai ta tafiya har suka isa gidan, dan ma ba nisa sosai. Suna isa suka karasa bakin kofar da fadawa biyu ke gadinta, Lantana ta kallesu sannan ta musu gaisuwar da take nuna alamar a masarauta take, sannan ta d’aura da cewa ” Matar Mai Martaba ce Gimbiya Basira.” Kallan juna sukai alamar basu fahimta ba, dan kuwa su basu santa ba, ba’a dade da kawosu nan ba, sannan ko da ace ma sun santa ai shekarun dayawa dan kuwa mutane dayawa sun manta da ita, wasu sai da insun tunata susa dariya, wasu kuwa suyi tunani ko tana raye? Basira ce ta kallesu tace ” bud’e mana, shiga zamuyi sannan d’aya ya zauna dan ya tabbatar da mudin ba da wani nufi mukazo ba, sannan d’aya yaje Fada ya sanar da Mai Martaba yayi baki na sirri anan.” Kallan mamaki suka mata, Basira ta kalli na hannun dama tace ” naga kamar kai bazaka iya mana komai ba in ma munzo da wani nufi ne, ganin yanayinka, dan haka so nake kaje ka samu sarki in ba hali ka samu Barde kace ya sanar da Sarki a kwai bakin sirri a gidansa na cikin gari.” Kallanta yai yana kokonto, Basira tace ” kada ka kuskura ka sanarma kowa sai mutanen nan biyu, ganin kafin kaga Sarki abin zai zama mai wuya ina shawartarka ka sanarda Barde, kada ka fadama kowa inba shi ba.” To, ya fada yanzu kam ya fara yarda da sunsan mai Martaba duk da dai bai yarda matarshi bace sai dai gani kamanni iri na Abu Turab yasa ya san tabbas akwai hadin jini na sarki a jikinsa. STORY CONTINUES BELOW  Nan yaja d’ayan yace “ka kula dasu kafin naje na dawo.” Nan ya fara tafiya, sukuma suka shiga ciki. Suna shiga Basira tasa d’anta yai wanka sannan ta bashi rigar data taho mai da ita kala d’aya. Itama wankan tai Lantana ta d’auko mata kaya tasa, dan kuwa dana akwai ajiyayun kayayyakin datai amfani dasu. Nan Lantana ta shiga kitchen dan sama musu abin ci. ********** Bafaden nan ya dade kafin ya samu ganin Barde nan ya sanar dashi sakon, mamaki ya kamashi bakon sirri? Ya kalleshi yace “sanar dani abinda ya faru tundaga farko.” Nan ya kwashe komai ya fad’amai sai dai ya manta sunanta shidai yasan ance matar sarki ce sannan yaganta da yaro.” Barde mamaki ya kamashi yace “shikenan koma gidan zan sanar dashi.” Har Bafaden ya juya Barde ya kirashi, ya karaso da sauri, Barde yace ” yaron shekararsa nawa?” Kai ya girgiza alamar rashin sani sannan ya dora da cewa “bazai wuce dai shida ko bakwai ba.” Gaban Barde ne ya fadi sai dai yai saurin girgiza kai a fili yace ” bazai kasance ita bace kar na tadama Mai Martaba hankali.” Bafaden na tafiya shima ya koma fada, ko minti goma baiyi ba magrib tai, nan mai Martaba ya mike aka shiga takamai baya fadawansa. Turakarsa ya shiga, yana kokarin shiga makewayi dan kama ruwa da alwala jakadiya ta fara sallama. Amsawa yai tare da cewa ” ya akai?” Ta kalli Zagi sannan ta kalli Barde tai kasa dakai tace “Barde ne ke neman iso Ranka ya dade, a gafarceni.” Mamaki ya kama Sarki ganin Barde baya biyoshi, nan yai gyaran muryar dayake nuna alamar ya shigo. Nan tace “Godiya yakd Takawa.” Nan ta kalli Barde tace ” bismillah.” Barde ya bud’e kofar ya shiga, a zaune yaganshi nan ya karasa ya zauna a kasa kansa na kasa yace “Tuba nake Takawa na katsema lokacin al’amuranka.” Mai Martaba ya kalleshi yace “ya akai?” Barde yai dan huci yace “wai baki ne na sirri suke jiranka a gidanka na ciki gari.” Cikin mamakin zancen yace ” na sirri kuma? Me kake san cewa?” Barde ya kwashe komai shima ya sanar dashi, a zabure ya mike yace ” Barde Basira ce! Basira ce.” Barde yace “Mai Martaba kayi a hankali kasan bangon gidan sarauta akwai ji (azancin magana yai – yana nufin ya kula akwai masu lab’e.)” Sai alokacin hankalin Sarki ya dawo dan jin ance Basira ba karamin tadamai hankali akai ba, cikin murya kasa kasa yace ” ka shirya ka fara zuwa gidan ni zansan yanda zanyi na fito.” Barde yace “an gama Takawa.” Su Jakaddiya kuwa an baje kunne ana san jigo gulma ko dayake ba ita kadai ba wasu fadawan ma hankalinsu duk yana d’akin, sai dai ba wanda yaji me akace sai dai sunji kamar an ce Basira kamar kuma Barira kamar dai wai suna ake fada da ya fara da Bas, abinda yasa ba wanda yai tunanin Basira saboda ganin tsawon shekarun, na farko shikansa sarki ba kiran sunanta yake ba bare suyi tunanin wani abun. ********** Mai Martaba kam wasu kayan yasa a jikinsa ana sallah ya samu ya wuce tare da bafadensa na kusa, sannan ya umarci d’ayan akan yace ya koma turakarsa ya kwanta sakamakon kansa dake sarawa. STORY CONTINUES BELOW  Sun samu sun isa gidan tun a hanya yaketa add’ua akan Allah yasa sune. Bayan ya shiga cikin gidan ya nufi kofar ya sa hannu kamar zai murd’a sai kuma ya fasa, karatun qur’anin dake tashi ya tsaya ji, can ya daure yai sallama, Basira tana zaune akan sallaya tanata addu’a akan Allah ya bata ikon shanye komai ya kuma sa komai yazo da sauki. Abu Turab na gefenta yana karanto suratul Rahman cikin kira’arsa mai dadi. Shiru Mai Martaba yai yana sauraron karatun. Gaban Basira ne ya fad’i jin sallamar muryar da ta kasa b’ace ma kunnuwanta, mikewa tai a hankali tazo bakin kofar ta bud’e gabanta nata fad’uwa. Kallan juna suka shiga yi cikin tsananin kewa da tausayama juna, a hankali hawaye ya zuboma Basira, Mai Martaba ya sa hannu ya riko nata hannu jin yake kamar a mafarki, ba shakka muryar d’ansa ne kenan yake karatu? Hakan yasa ya kamo hannunta ya shigo inda take a tsaye. Cak ya tsaya yana kallan yaron dake zaune kan sallaya yana karanto Suratul Rahman cikin kira’arsa mai dadin gaske, zuciyarsa ce ta karye ya juyo ya kalli Basira sannan ya nuna yaron da hannu ya kuma nuna kanshi da hannu alamar ( wannan nawa ne?)” Hawayenta ne ya gangaro sosai ta kada mai kai tana zubo dasu kamar ana zugo kukan. Sakar hannunta yai ya karasa inda yaron yake a hankali dan jikinsa duk ya gama mutuwa, Zama yai a gaban yaron kan sallaya, Abu Turab ya kura mai ido amma bai daina karatunsa ba, yana kallansa. Hannayensa Sarki ya kamo,hakan yasa yai sadakallahul azim. Sarki yace “ya sunan ka?” Ko kifta ido baiyi ba haryanzu yace “Abu Turab.” Kalla. basira yai cikin jin dadi. Sannan ya nuna kansa yace “ka gane ni?ah ba haka zance ba, kasan ko ni waye?” Tunowa da alkawarin dayama Mahaifiyarsa yasa yad’an kalli gefe kad’an ya girgiza mai kai alamar a’a. Sarki yace “ina dama zaka sanni? Ni kaina sai yau na tab’a ganinka.” Kai Abu Turab ya sake girgizawa yace ” ba haka nake nufi ba, ba na gani ta ina zan ganeka?” Basira wacce ke tsaye tsoro duk ya kamata ganin yanda d’an nata ya kurama mahaifinsa ido ta d’auka ya manta alkawarinsu sai dai jin abinda yace yasa tau ajiyar zuciya. A zabure ya kalli Basira, ganin yanda idanunsa sukai yasa ta daure ta d’agamai kai tana hawaye tace ” tun yana jariri idanunsa basa gani.” Zuciyar Sarki ta kara karaya jiyake kamar ya sa kuka, da sauri ya jawo d’an nasa jikinsa ya kankameshi kam. Sundade a haka kafin ya sakeshi. Shiru ne ya biyo baya a d’akin, yana zaune kan kujera rike da hannun matarsa ya d’aura d’an nasa kan cinyarsa. Basira ta kalleshi tace “in wani ya ganka fa?” Murmushin yake yai ya shafa kan d’an nasa yace ” duk laifinane, da bance kije gida ba d…….” Kai tai saurin girgiza mai tace ” ko kad’an ba kaifinka bane.” Kallanta yai sai dai baice komai ba.. Sun d’anyi shiru kafin Basira ta kalli d’anta tace “koma can ka zauna zamuyi magana da mahaifinka.” Nan ya mike ya koma can gun ‘yan tumtum ya zauna sai dai hankalinsa na kansu. Jiyai Mahaifin nasa yace ” basira ina kuka shiga?hankali na yayi matukar tashi.” Murmushi tai tace ” ka yafeni nasani nayi babban laifi sai dai ba komai bane ya hanani dawowa sai d’ana, ina tsoron rayuwar da zaiyi a gidan sarauta ba ido, ina tsoron wulakanci da gulma da habaici da zai fuskanta, nafarko ni ba wata mai matsayi ba sannan ga d’ana ba ido, tsoron wulakancin da za’amai yasa na kasa dawowa, sai dai tunanin raba d’a da mahaifi da kuma raba kaina da kai yasa na dawo.” Tunda ta fara magana yake kallanta yauce rana ta farko da ta saki jiki take mai magana haka, murmushi yai sannan yace ” na fahimcike na kuma gode da kika dawo gareni baki bari na mutu banga d’ana ba.” Shiru suka d’anyi kafin yace ” ku zauna anan in har kina ganin zaman can zai ma d’ana wahala.” A ranta tace da kenan, yanzu in har na zauna anan wayasan me zasumin a bayan idanka?ai in kana tsoron kura ba inda yafi maka saukin zama irin raminta, domin duk abinta bazata taba kawo akwai wanda ya isa shigar mata rami ba bare tai farauta a ramin nata. Murmushi tamai sannan tace ” a’a nafisan zamana kusa da kai sannan in na zauna anan yaushe Abu Turab zai dinga ganinka? Sannan in akaji labarin zamana anan baka gani xai jawo ma da ni kaina matsala? Kallanta yai yana kara mamakin yanda ta canza……… Mai Martaba ya juya ya kara kallan d’an nasa zuciyarsa a raunane, ba shakka kam d’ansa na bukatar kulawa ji yake kamar laifinsa ne yasa yaron ya makance. Basira ganin yanda yake kallan d’an nasa yasa tace ” Ba laifinka bane, kaddararsa ce babu makawa sai hakan ya faru ko da kuwa a gunka muke.” Kai ya jinjina cikin tausayawa, tai murmushi tace ” ka koma tun kafin mutane su farga da rashinka.” Yace ” haka ne, kiyi hakuri zuwa wasu ‘yan kwanaki zan san yanda zanyi ku dawo ba tare da mutane sunyi zargin komai ba.” Ta lumshe ido sannan ta murmusa tace ” na yarda dakai.” Mikewa yai a hankali yaje kusa da d’ansa ya rungumeshi kam sannan yace “sai da safe d’ana.” Abu Turab ya d’aga kai. Haka ya fito tana bayansa, a tsakar gida taga Barde nan ya gaidata sannan ta juya ciki, su kuma suka tafi.+ Abu Turab ya matso inda take idanunsa fal kwalla sai dai ya rasa mai zaice, ya kuma rasa dalilin jin yana san yai kuka, kallansa tai tace ” me kake shirin yi?” Yad’iye kukan yai sannan yace ” bakomai.” Ta mike ta wuceshi ta nufi cikin d’aki, zama yai dabas yanzu yana ganin mahaifinsa ba dama yace ya ganshi? Shikam ya kasa gane mai mahaifiyarsa take nufi da hakan. ********* Sarki ya kasa bacci sam sai juyi yake akan gadonsa, tayaya zai b’ulowa mutane da matansa? Mai zai fada wanda mutane bazasuyi zargi da korafi ba akan matarsa da d’ansa? Sam ya rasa amsar tambayarsa sai juyi kawai yakeyi. ********* Washegari da sassafe sarki yasa bafaden nan nasa ya tuko mota ya kawo musu kayan abinci sosai, duk wani abun bukata ya kawo musu sannan ya aiko da kudi akan a siyoma Abu Turab kaya da wasu abubuwan bukata. Wajen karfe 10 suka shirya itada Lantana da Abu Turab suka fito dan zuwa kasuwa siyo kaya. Suna tafe suna ‘yar hira itada Lantana jikin wani shago ya tsaya dan shi sam bayasan shiga mutane da alama hakan ya faru ne saboda inda ya taso. Yana wajen shagon su kuma sun shiga ciki, kallan wata kantanga yake wacce akai mata zane da wasu rubutu wanda bai taba gani ba, ido ya kurama rubutun yanasan sanin namenene? Wasu yara ne su uku suka fito daga ciki sanye da fararen kaya riga da wando da hijabi, basu wuce shekara 5 ba, su biyu ne mata d’ayan kuma namiji ne. An tashi tara. Suna tafe kamar masifa biyun babbar macen da namijin, d’ayar wace take karama itakuma da alama kuka takeyi, kura musu ido yai yana neman amsar tambayarsa, daga ina suke hakan? Wata ce yaga ta fito da gudu ‘yar karama bata wuce shekara hud’u ba, daga inda suka fito tazo ta d’akama babbar cikinsu duka ta kara zurawa da gudu, inda yake tsaye take yowa mamaki ya kamashi ya tsaya yana kallan ikon Allah, yana nan tsaye yaga tana nufoshi shi dai bai matsa ba sai kallan ikon Allah yake. Da gudunta kuwa ta cigaba, kai ya girgiza ya juya ya kalli inda Mahaifiyarsa take, yana juyawa yaji an wani irin hankad’eshi iya karfinta, dukansu suka fad’i a kasa tim, shikam ya fita jinjiki dan sar da hannunsa na hagu ya kurje, cikin fad’a ya d’ago dan ya mata magana, mamaki ne ya kamashi ganin ko a jikinta kad’e jikinta tai tana shirin kara sa wani gudun. Da karfi yasa hannu ya fizgo hijab d’inta ya dawo da ita inda yake. Kallansa tai sannan ta kalli wacce ta daka tace ” dan Allah yahkuri ka sakeni karta kamani.” A ransa yace wasa kike yarinya, saurin kauda kansa yai daga kallanta sannan yace ” malama bakya gani ne?” Kallansa tai taga yasa hannu yana neman gefenta yana jujuyawa kamar irin neman inda fuskarta take yakeyi. Kusa da fuskarsa ta matsa ta kalleshi sannan ta mai gwallo, ganin baice komai ba yasa tasa hannu ta toshe baki tana dariya wato da alama baya gani. Hannu tasa ta fara kokarin zare hijab dinta alamar zata cire hijab din ta gudu ta barshi, jitai ance ” me ya faru Abu Turab?” Kallan matar datai magana tai ta ciji leb’e cikin takaici ga waccan ta karaso daf, ganin yana neman sanar da matar yasa ta fizge hijab dinta iya karfinta, ta sakar mai gwalo tace “makaho kaje ka nemo sanda.” ta kara falawa da gudu kamar zata kifa. Juyawa yai yana kallanta cikin takaici, yanaji d’ayar tana binta tana cewa ” Mariya wlh ko me zakiyi sai na rama gwarama ki tsaya.” Daga can itama ta juyo ta jefo mata dutse tace ” ki kamani in kinada karfi.” Yaja tsaki yace ” Umma amma waccan batada hankali, bigeni fa tai kiga yanda naji ciwo amma ko hakuri bataban ba.” yakarasa maganar yana nuna hannunsa. Basira ta matso ta duba hannunsa tace ” da alama daga makarantar boko suke amma wannan yarinyar kwai fitinaniya, kaga yanda taketa gudu ko ajikinta?” Abu turab yai kwafa ahankali yace ” Allah yasa inganta watarana.” Basira tace ” me kace?” Kai ya girgiza yace bakomai. Lantana tace ” inba dan yanayi ba inama ta isa ta ganka a haka? Bare har ta tureka?” Basira tace ” muje nikam.” Sun gama siyayarsu sannan suka koma gida, Abu Turab sai dayaga sunyi salla sunci abinci sannan yace ” Umma menene boko?” Tace ” makarantace da ake koya karatu, menene?” Kai ya girgiza alamar ba komai. Kallansa ta sakeyi tai murmushin dan ta fahimci abinda yake nufi. A waccan lokacin ba kowa bane ya damu da karatun, yawanci zakaga yara ba zuwa suke ba, wasu kuwa iyayensu ne malaman makarantar, wasu kuma turasu ake bawai dan sai sunyi karatun ba. ********* Magajiya zaune a kilisarta tanacin inibi, gefenta d’antane Yarima yana zaune kusa da ita shima yanacin ayaba, ta kalleshi sannan ta kalli Jakadiya dake zaune tace ” jiya ina Mai Martaba yaje?” Jakadiya tace ” ba inda yaje.” Wani kallo Magajiya ta mata tace ” me kikeso kice?karya na miki ko me?” Dasauri ta rusunnar da kai tace ” tuba nake Magajiya ni kaina bansani ba daga gun sallah ne bai dawo ba.” Ta bud’e baki zatai magana wata yarinya yar shekara hud’u ce ta shigo da gudu ta zo ta fad’a jikin Magajiya. Fara’a ce ta karfafa a fuskarta ta d’agota tace “wa nake gani haka kamar uwata?” Yarinyar ta d’ago tana murmushi tace ” nice Aunty.” Kallan d’an Auntyn nata tai wanda ke zaune ko kallanta baiyi ba, ta taboshi tace ” Yaya bakaganni bane?” Kallanta yai yace ” Yaushe zaki girma ne Khadija? Sai ki dinga gudu kamar wata…..” Magajiya ce ta katseshi tace ” a mata afuwa Yarima yarinya ce, sannan na tabbata inta ganni ne take haka ko Uwata?” Baki ta turo sannan ta d’aga kai. Magajiya na tsananin san Khadija wacce take ‘yace ga Hisham, wanda yanzu ‘ya’yansa hud’u itace ta uku, duk da dai ‘ya’yansa a matsayin uku suke tunda ba wanda yasan Abdulmajid d’ansa ne. Har mamaki mutane suke yanda ta sakar ma yarinyar fuska, ko dan sunan mahaifiyarsu ne? Haka ta sa Khadija a kusa da ita tana tambayarta ‘yan gida da karatun ta. Jakadiya kam ganin haka yasa ta samu ta sulale dan itakam taji dadin ganin Khadija. Yau da sassafe kafin Mai Martaba ya tafi bada a aika a kira masa Magajiya. Zama tai irin yanda ta saba sannan ta kalleshi, ba sai an fada mata ba ta fahimci magana yakesan yi mai mahimmanci. Ya dade baice komai ba kafin ya ja numfashi yace ” Magana nakeso muyi, ko ince abu nakesan fada miki.” Kallansa tai sannan ta maida kanta inda take kallo da. Sarki ya nisa yace ” akwai abinda na b’oye miki ko ince akwai abinda ya kasance sirri na ne da ba wanda ya sani.” Bata juyo ba dan bata taba kawo wani abu ne babba ba, Sarki yacigaba ” Matata da d’ana zan maido gidan nan zuwa gobe.” Da sauri ta juyo ta kalleshi tana mamakin kalamansa dan sam bata fahimci ina ya dosa bama. Sarki ya cigaba da cewa “Matata da ke zaune a cikin gari d’aya daga cikin gidajena, uzuri ne yasa take zaune acan saboda d’an data haifa ya kasance yanada lalura, wanda hakan yasa ta naimi zama acan dan ta kula dashi, ba wai dan tana tunanin nan din bazai samu kulawa ba a’a sai dan lalurar tasa babbace wacce take bukatar kulawa.”+ Tunda ya fara maganar take bin bakinsa da kallo dan ta kasa aminta da abinda kunnenta ke ji. Daurewa tai tace ” aure kai bamu sani ko me? Nifa na kasa fahimtar inda ka dosa.” Kallanta yai yace ” Basira nake nufi da d’ana Abu Turab wanda suke gidana shekara bakwai kenan.” “me kace? Basira da d’anta?sannan suna zaune a gidanka shekara bakwai? Takawa mai kake san cewa ne?” Mikewa yai yace ” ana jira na a fada, sannan na tabbata zakiji abin banbarakwai sai dai gaskiyar kenan.” kasa magana tai saboda tsananin mamaki, tana kallo ya juya ya fita. Shikam ya sani in har ya mata lago lago tabbas sai ta bulomai da wani abun. Ta dade a zaune kafin Ta mike tai bangarenta. D’aki ta shiga ta rufe, tafiya ta dinga yi a d’akin cikin tashin hankali, me ke faruwa? Meke faruwa? Ta dade kafin ta aika a kira mata Hisham. Hisham kam ya taho ko a jikinsa dan dama yanasan ya mata magana akan a nad’a dansa matsayin Yarima mai jiran gado sai kuma ta aika a kirashi. B’angaren d’ansa ya fara zuwa, yana shiga yaji alamar fasa abu, da sauri ya shiga ciki hankali a tashe. Abdulmajid ya gani a zaune ga bayinsa sunsa gwiwowunsu a kasa suna bashi hakuri, a hasale Abdulmajid ya kallesu yace ” ba nace banasan a kawomin ruwa a irin wannan kopin ba?” Hakuri suke bashi hankalinsu a tashe, ya wani juya kai irin ba saukin nan yace ” bazai yiwu ba Ummana zan sanarwa ta d’au mataki a kanku.” Nan suka shiga rokonsa, Hisham yai dariya ya juya ya fita yana jinjina kai, murmushi ya saki yace ” haka akeso ai, gwara ya nuna musu a kasan sa suke hakan zaisa inya zama Sarki a dinga tsoronsa.” A zaune ya tadda Magajiya sai dai kana kallanta kasan tana cikin tashin hankali, nan Hisham ya d’an tabe baki kadan yace “wa ya tabo wannan zakanyar?” Kusa da ita ya karasa ya zauna yace ” Magajiya menene?” Ta kalleshi cikin tashin hankali sannan ta bada umarni a basu guri, kallanta yai sannan yai dan dariya yace ” menene? Khadija tace a gaisheki.” STORY CONTINUES BELOW  Hucci ta saki tace “ina amsawa amma ba wannan bane a gaba yanzu, kasan Basira ta dawo kuwa? Ko ince wai ashe tana nan?” Kallanta yai yace “Basira? Wa ke……..” ido ya zari sakamakom tunowa dayai yace ” Basira dai?” Ido ta runtse tace ” ita mana, ba ita kadai ba ma harda danta.” Mikewa Hisham yai da sauri yace ” ban gane ba? Basira tana nan a ina?” Magajiya ta kwashe komai ta fada mai, shiru yai sannan ya zauna a kasa dabas ya dafe kai cikin tashin hankali. Magajiya ta kalleshi tace ” naji maganar Mai Martaba sai dai ban yarda da duk abinda ya fada ba.” Hisham yace “ban……” Tace ” kana tunanin Basira tana garin nan shekara bakwai amma sarki bai nuna alama ta zargin haka ba? Ko na fita? Ko na aika abinci ko wani sako?” Hisham ya kalleta yace ” haka ne kuma.” Magajiya tai wani murmushin takaici tace ” kwanan nan ta dawo.” “kwanan nan?” Tace ” haka zuciya ta da kwakwalwata ke sanar dani, nasan hali Takawa, nasan yanda yakesan Basira da abin cikinta, na tabbata bazai taba kyalesu ba batare da ya dinga binsu ba.” Hisham yace ” gaskiya ne,to yanzu meye nafita?” Tace “nayi tunani sosai bayan naji abinda yace sai dai nasan babu abinda zamu iya yi, na farko bazamu sa ta koma ba sannan ba zamu kashe danta ba, sai dai akwai kafita.” Hisham ya kara matsowa, Magajiya tace ” da farko mu nuna masa ba komai, sai dai ni zan sanar dashi akan in har yanaso in nuna dawowar matarsa ba komai bane har sai ya amince da bukatata.” Hisham yace “kina ganin zai yarda?” Tai wani murmushi tace ” yafi kowa sanin in na tsani matarsa zaman gidan nan gagararta zaiyi hakan zaisa ya yarda.” Hisham ya kata jinjina yace ” haka ne, amma meye bukatar taki?” Tace ” ya rubutamin alkawari akan ba mai gadar sarautarsa sai Abdulmajin wato d’ana.” Hisham ya washe baki yace “kai Magajiya da ke namiji ce tabbas da kin taimaki kasar nan da kwakwalwarki.” Kai ta juya tace ” sannan basai na damu da d’anta ba tunda yace min yanada lalura duk da banmasan lalurar menene ba.” Hisham yace “lalura?” Ta tabe baki tace “oho musu sai dai dolene muyi amfani da dawowar yarinyar nan mu amshi takarda a hannun sarki. Murmushi sukai na farincikin ganin sun warware matsalarsu…. _Nikam nace hmm ba giringirin ba dai…….._ ********** Mai Martaba ya sanar a fada akan dawowar matarsa da kuma zamansu a can, mutane dayawa sunyi mamakin wannan al’amari da kuma san suji lalurar d’an nasa. Sannan ya aikama Basira akan su shirya dan kuwa gobe ne ranar komawarsu. ********* Basira yau tace Abu Turab yazo su kwanta tare a kan gado, sun kwanta shiru, ta kamo hannunsa tace ” yauce rana ta karshe da zamu kwanta tare duk dadai mun dade bamu kwana tare ba.” “dolene ka zamanto mai kauda kai sannan mai gudun rigima in ka koma gidan mahaifinka, zakaga mutane kala kala masu hali daban daban sai dai fatana ka nutsu ka karanci ko wani hali na d’an adam din daka gani.” Kai ya d’aga mata alamar to, tai mumushi tace ” kada ka kuskura ka nuna ma mutane kana gani, wannan alkawarinmu ne wanda nakeso ka rike har sai sanda nace ma ka nuna musu.” Ya kara d’aga kai, tace ” zan zamo mai zafi a gareka, zan ki bin bayanka, zan ki nuna ma kulawa, sannan zan nuna rashin damuwata akanka sai dai inaso kasani hakan gata ne wanda zanma, a yanzu bazaka fahimta ba sai dai nan gaba kai da kanka zaka fahimci dalilina nayin hakan.” Abi Turab ya kalleta idanunsa sunyi raurau, ba komai yake fahimta ba a kalamanta saboda yarinta sai dai ya san abu d’aya tana nufin akwai dalili dazaisa ta daina nuna mai kulawa. Kallansa tai, batai magana ba yai saurin had’iye kukansa, daurewa yai yace ” nikam banasan gidan.” Kansa ta shafa tace ” Allah ya albarkaci rayuwarka ya karemin kai, wannan itace addu’ata a ko da yaushe.” Shirun da sukai ne yasa bacci yai gaba dashi, ta dade tana kallansa zuciyarta na tsananin tausayama rayuwarsa. _nikaina tausaya d’an yaron nan nake cewar Kanwata Yar Fara(Meema White)….Lol_😅

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE