KAINUWA CHAPTER 8

KAINUWA

CHAPTER 8

Khadija bangaren Magajiya ta isa, tana shiga ta taddata a zaune, karasawa tai ta gaisheta, Magajiya ta kalleta cikin kulawa tace ” Khadija sannu, ina nan hankalina a tashe ina tunanin yanda jikinki yake, Khadija ya akai haka? Duk kin rame.”
Khadija ta d”ago ta kalleta bata bata amsar tambayarta ba sai jitai tace ” Umma an tura wani ya dubo Inna Lami?”
Magajiya tad”an tabe baki kadan sannan ta kalleta tace ” na tura, sunce jikin da sauki.”+

Hawaye ne ya zuboma Khadija tace ” Umma me yasa bakwasa tausayi a ranku?”
Hade rai Magajiya tai tace ” KHADIJA!”
Khadija tana kuka tace ” makociyar Inna Lami ba ta aiko a sanar daku jikinta yayi tsanani ba?”
Magajiya tace ” a yaushe akai hakan?”
Khadija tace ” amma tace ai ta sanar da Yaya, Umma Allah ya d”auki ran Inna Lami, ita kanta bata sani ba tunda ita tasan ta sanar da Yaya ta dauka anje an dauketa, ita kuma a ranar tai tafiya, sai jiya da ta dawo ta shiga gidan ta ganta duk ta kumbura da alama ma ta dade da rasuwa, nan tasa aka kira mutane aka mata sallah aka kaita, d”azu da naje take sanar dani……”

Kukanta ne ya tsananta sanda tazo karshe.
Tace “Umma Inna Lami fa kanwar Mahaifiyar ku ce, tayaya zaku…”
Ya isa haka!
Abinda Magajiya tace kenan, d”agowa Khadija tai ta kalleta, dan tayi maganar ne da kakkausar murya.
Magajiya tacigaba ” Ya isa haka Khadija, Inna Lami ta rasu Allah ya jikanta, zansa aje gidan, ke kuma jan maganar ya isa, ba kuma na san ki kara tada maganar nan.”
Kallanta Khadija ta shiga yi cikin tsananin mamaki, Magajiya ta kalleta tace ” ki tashi ki koma gida zan aiko miki da magani da abubuwan bukata, banasan ki dinga kwanciya ciwo akan abinda bai kai ya kawo ba.”
Sam ma ta rasa me zatace sai kallan mamaki kawai datake binta dashi.
Ganin batada niyyar kara magana yasa Khadija ta mike ta fito daga d”akin.
Ba shakka yau taga abin mamaki ace d”an uwanka na jini? Sannan harda wani wai batasan taga tana kwanciya akan abinda bai kai ya kawo ba? Kenan abinda sukama Turab da wannan rashin kula da Inna Lamin da sukai ba wani abin bane a gunsu?
Samun kanta tai kawai da bin hanyar da zata kaita gun Abu Turab.
Sai dataje kofar shiga ta tsaya tana tunani me zatace mai?
Tabbas ganinsa ne kadai zaisa taji saukin wannan abin.
Tura kofar tai a hankali, Mai kula da gun ne ya taso ya gaisheta, a hankali ta furta Ya Turab nanan?
Yace ” eh yana ciki, a sanar mai da zuwanki?”
Tace ” bari na shiga ai kasan ni ko?”
Kallanta yai yace ” na sani amma taya…..”
Gani yai kawai tayi gaba batama san yanayi ba.
Falo ta duba ganin bayanan yasa ta tsaya taba kallan falon, idanunta ne suka kara zubo da wasu kwallar sannan a hankali ta nufi kofar d”akinsa kwankwasa wa tai daga ciki yace ” waye?”
Shiru tai sai kuma ta kara kwankwasawa.
Mikewa yai ya bud”e kofar.
Kallanta yai sannan yai saurin kauda kai ya kara cewa ” waye?”
Kallansa ta shiga yi hawaye na zubo mata, a zuciyarta tace “Yaya ina cikin wani hali, su Umma Magajiya, Yaya, da Abbana sun fara bani tsoro, banaji suna da digon tausayi a zuciyoyinsu, Yaya ya zanyi in canza su? Ya zanyi in nuna musu hanyar gaskiya?”
Hawayenta ta shiga sharewa, jiyai zuciyarsa na kuna ya tsani yaganta tana kuka, gashi yaga ta rame sosai da alama rashin lafiya tai, daurewa yai ya juya da nufin komawa ciki, jiyai tace ” nice Yaya.”
Juyowa yai yace ” Khadija? Me kike a nan?”
Ta daure tace ” ganinka kawai nazoyi, ya hannun naka?”
Fuska ya had”e yace ” me zaisa ki damu da ciwon da baikai ya kawo ba, bayan kece kike bukatar kulawa?”
Daurewa tai tace ” yaya ya warke?”
Labansa yadan ciza yace ” Khadija meke damunki? Me yasa bakya fahimtar abinda nake nufi? Kina tunanin in kika nuna damuwarki akan ciwona kika wulakanta naki lafiyar zanji dadi? Me yasa kike san ki dinga sani cikin damuwa?”

Kallansa tai fuskarta cike da mamakin kalamansa, tace ” Yaya.”
Idanu ya d”an runtse yace ” please in har kinasan ki nuna kulawarki a kaina to ki kula da lafiyarki.”
Juyawa yai ya koma ciki, ya rufo kofar.

Shiru tai sai hawaye da suke zubowa daga idanunta, jingina tai da jikin kofar, shikansa yana shiga ya jingina da jikin kofar.
Idanunta a lumshe tace ” Yaya.”
Bai amsa mata ba sai dai yana jinta, tacigaba ” Kayi hakuri yaya, kayi hakuri da rashin sanar dakai tafiyata fa banyi ba, kasan ina zaune a gunka lokacin da aka aiko inje, ina zuwa aka sani a mota ko gida ban shiga ba, kayi hakuri da rashin nemanka dabanyi ba, tunda naje garin ba”a kara barina na zo ba sai wannan dawowar.”
Iska tadan furzar sannan tace ” Yya kayi hakuri na abinda su Umma Babba sukama, sannan kayi hakuri na rashin baka hakuri da sukai.”

Ransane ya bace ya bud”e kofar da karfi, hakan yasa tai saurin gyarawa ganin ta kusa faduwa, a fusace yace ” meyasa kike bada hakuri? Me kikai? Me yasa kike bada hakuri a koda yaushe? Bayan wadanda ya kamata su bada hakurin basusan ma sunyi laifi ba? Me yasa Khadija? Meyasa kike neman tadamin hankali?”
Kai ta shiga girgizawa har ya gama fadan sannan tace ” Yaya na san…..”
Katseta yai yace ” Khadija meyasa bazaki fahimceni ba? Banasan kina yawan bani hakuri hakan na sa inji kamar nine nake miki laifi.”

Daurewa tai tace ” Nadaina yaya.”
Yace ” Khadija please…..”
Murmushi ta kakaro tace ” na daina Yaya, nazo ne dan ina cikin wani hali zuciyata bata kawo min kowa ba sai kai, shiyasa nazo.”

Kallanta yai yace ” me ya sameki?”
Murmushi tai tace ” hmm inama Yaya kana gani? Da kaganni ina ma murmushi.”
Shiru yai baice komai ba, tace ” Haryanzu addu”ata kenan, Allah ya bud”ema idanunka.”
Murmushi taga yayi, itama murmushin tai sannan tace ” Ahh da alama zuciyata tayi sanyi,duk da hankalina haryanzu bai kwanta ba.”
Yace ” me ya faru kuma?”
Tace ” Inna Lami ta rasu.”
Yace ” yaushe?”
Kallansa yai tace ” ba”a san yaushe bane.”
Kallan mamaki ya mata, ganin zata d”ago yasa ya kauda kai yace ” ban gane ba.”
Zama tai a kasa a jikin bango, ta kama rigarsa tace ” Yaya zauna plz.”
Zama yai dan ya kula tana bukatar mai lalashi.”
Zayannemai komai tai.

Hankalinsa ya tashi, lalai mutanen nan basuda imani, wato abin ma harda jininsu?
Khadija ta d”ora da cewa ” Yaya in kaine me zakayi?”
“Hmmm in nine ba abinda zanyi.”
Tace ” ba abinda zakai?”
Kai ya d”aga alamar eh yace ” me zanyi to? Abin nan dai ya riga ya faru, sannan mutanen na basu nuna tausayawa ko dana sani ba, ni da nake d”a me kike tunanin zanyi? Sai dai….”
Shiru yai hakan yasa tace ” sai dai me?”
Yai ajiyar zuciya yace “sai dai dole girma da darajarsu zai ragu a idona.”

Tace ” na fahimceka Yaya na kuma gode.”
Mikewa tai tace ” yau naji dadin dana dade banji ba duk da wata zuciyar tana tausayawa Inna Lami, sai dai wata zuciyar tana farin cikin zama tare da kai danai wanda na dade ban samu ba.”
Baice komai ba, tace ” nagode yaya.”
Ta fada tare da tafiya.
Kallo ya bita dashi sannan ya mike a hankali ya koma ciki.

Ya zaiyi? Ya zaiyi? Ba shakka yanasan Khadija sai dai yana ganin auransa da ita ba mai yiwuwa bane, tsanar Magajiya da ahalinta ne suka kara shigarsa jin labarin da khadija ta bashi.

Kansa ya dan shafa yace ” Ya zanyi?”

Wajen karfe sha biyu na rana ya fito daga bangarensa sanye da shadda mai kyau da tsada da yake kayan mu na da masu kyau ne da quality kai ka dauka sabuwa ce, yayi kyau sosai sannan ya zuba wasu kayan a cikin yar karamar jaka tunda Mai Martaba yace kwana biyu zasuyi a can din.

Sabi”u ne ya zo kusa dashi yana dan tafi yace ” Yayai Ango ai da alama Bilkisu takace, ta ina zatai wasa wannan saurayin ya wuce ta?”
Fuska ya d”aure tamau yace ” zaka fara ko?”
Sabi”u yazo gefensa yace ” Nadaina Ango.”
Abu Turab yace ” matsalarka ce wannan, mikam mu tafi.”
Su biyu suka fito dan ko Garzali bai dauka ba, dan Mai Martaba yace zuwan nasu kano ya zama sirri.
Bangaren Mahaifiyarsa yaje ya mata sallama, duk da ranta baiso sai dai tamai fatan alkairi, ta kudura a ranta in har Bilkisu ta aminta dashi to fa yana aurenta zatasa ya auri Mairo, in kuma bata amince ba to dama ita hakan take so.

Ya fito suka shiga motar da Mai Martaba ya umarcesu suje, suna fita daga kofar gidan ya ga Mairo jikin katangar gidan a tsaye, sun hada ido sai dai da sauri ya dauke na sa idan, ya tabbata fitowa tai dan taga tafiyarsa, shikam tausayinta yake, yana kuma mata fatan samun miji na gari.
Sunyi da nisa, jefi jefi suna dan taba hira, sun danyi shiru kafin Sabi”u yace ” Abokina!”
Turab yace ” ya akai kuma? Dan nasanka sarai wannan Kiran kira ne na tambaya.”
Sabi”u yace ” tun jiya nakeso nai ma tambayar sai dai na rasa ta inda zan fara, ba kuma nasan mu samu sabani saboda ita.”
” ina jinka.”
Sabi”u yai shiru kafin ya dan kalli titi sannan yace ” me kake nufi da a makaho zanje mata?”
Abu Turab bai ko kalleshi ba bare yaga alamar mamaki a tambayarsa, Sabi”u yana tukinsa yace ” ba wai naso naji maganarku bane da mai martaba sai dai jin maganar nai daga inda nake tsaye.”
” Ina gani.”
Abinda Abu Turab ya fada kenan, cikin tsananin mamaki Sabi”u ya gangara gefen titi yai parking, Abu Turab ya kalleshi yace “meye abin tsorata? Harda tsayawa?”
Sabi”u yace ” ban gane kana gani ba?”
Murmushi Abu Turab yai yace ” Kaya ruwan toka ne a jikinka ka sa hula baka, sannan kaidin fatsi ne, kanaso in cigaba?”

Sabi”u idanunsa a waje yace ” Yaushe ka warke?”
Abu Turab yai murmushi yace ” that”s not important, ka wuce muje.”
Jiki a sanyaye Sabi”u ya tada mota, da kyar ya iya furta amma me yasaka pretending?
Shiru Abu Turab yamai, jin haka yasa yasan bazai amsa mai ba, sun dade a haka kafin Abu Turab yace ” sanar dani halayenta da akace ka binciko.”
Sabi”u yace ” Bilkisu ita kadai ce mace a gun Sarkin Kano, yarinyace mai kyan gaske, dan kowa yana fadan irin kyan datake dashi, mace ce mai tausayi ayanda aka fada tanada saukin kai, ko kadan batasan a tozarta wani.”
Shiru yai hakan yasa Abu Turabya kalleshi yace ” shi kenan?”
Kallansa Sabi”u yadanyi yace sai dai tanada matsala d”aya.
Abu Turab ya kalleshi yace ” na me kenan?”
Sabi”u yace ” batasan a komenene a hadata da wani, wannan dalilin ne yasa taki aminta da duk mazan da suke kawo mata hari, a yanda naji ita kishi ko na menene batasan tayi dan tanada zafin kishi.”
Tsaki Abu Turab yai yace ” zancen banza takeyi kuma kenan baya yarda da kanta ba, in har tanaji da kanta tana ganin komai nata yayi 💯 banaji ya kamata ta dinga wannan shirman, wannan alamace na akwai abinda take lacking.”

Sabi”u ya girgiza kai yana dariya yace ” lalai Turab bakada kyau, yanzu kishin ma sai ka fassarashi? To ita kishin in hallitarta ce fa?”
Baki yadan tabe yace ” sai ta danne shi tunda ba ita tai kanta ba.”
Sosai yaba Sabi”u dariya, haka sukai ta zancen Sabi”u na kara dariya, sun isa kano da la”asar gidan Sarki suka wuce direct, Mai Martaba sarkin Zariya ya riga ya sanar da Sarkin kano akan zuwan nasu, suna zuwa aka wuce dasu ma saukin su, aka kuma turo musu bayi guda uku masu kula dasu.

Sunyi wanka sunyi Sallah sannan aka kawo musu abinci.
Abu Turab ya kwanta akan gado tare da daure hannunsa kan goshinsa kamar yanda ya saba, Sabi”u ya kalleshi yace ” Malam Makaho sauko muci abinci.”
Murmushi yadan mai yace ” fara ci.”
Sabi”u ya matso kusa dashi yace ” kodai ka kosa ka ganta ne? Dan na kula tunaninta kake yi.”
Abu Turab ya juya mai baya yace ” kasan ni din ai ba kai bane.”
Saida Sabi”u ya kusan gana cin abincin sannan shima ya sauko dan kadan yaci ya mike ya fito wajen harabar gidan.
Wata yarinya ya gani wacce batafi shekara 12 ba tana leko shi.
Alama ya mata da hannu akan tazo, tsayawa tai tana wasa da yatsun hannunta, Abu Turab ya tako har inda take ya dan rusuno yace ” yan mata me kike anan?”
Kallansa tai tace ” Kaine Yarima Turab?”
Cikin mamaki ya kalleta yace ” kin san ni ne?”
Kai ta girgiza tace ” Aunty na ce ta aikon inganka.”
UmmaBilkisu?kina nufin Gimbiya Bilkisu?”
Kai ta daga alamar eh, sannan tace ” amma karka fada mata kaji.”
Murmushi yai yace ” naji kedin wacece to?”
Tace ” babana shine Yarima Nazir magajin sarki.”

STORY CONTINUES BELOW
Kai ya jinjina zaiyi magana yaga ta juya da gudu, mamaki ne ya kamashi ya juya bayansa, ganin Sabi”u yasa ya fahimci ganinsa ne yasa ta gudu, murmushi yai sannan ya juyo.

Sabi”u ya karaso yace ” Kai da waye?”
Abu Turab ya juya yace ” bakowa.”
Sabi”u ya matso yace ” an turo wai bayan Magrib zamuje.”
Harararsa yai yace ” Zamuje ina?”
Sabi”u ya matso wajen kunnensa yace ” Zance mana.”
Abu Turab yace ” dakai zanje zancen?”
“Eh mana, da kai da wa?”
“Sry Malam ni kadai zanje.”
Sabi”u yace “Mai Martaba cewa fa yai in bika.”
Kafadarsa ya dafa yace “sry mutumina amma ni kadai zani.”

*******

A can kuwa Bilkisu ce xaune a d”aki, Munnira tana shigowa ta kalleta tare da mata alama da hannu akan ta matso, sannan ta sallami masu kula da ita, kallan Munira tai tace ” Munnira ya?”
Munnira tace ” Nikam Yamin UmmaBilkisu dama kibarmin shi.”
Harararta Bilkisu tai tace ” abinda na aikeki kiyi kenan?”
Munnira ta turo baki tace ” Nidai shi zan aura.”
Bilkisu ta harareta tace ” ni tashi kiban gu bansan kayan haushi.”

Bayan Magrib bayinta suka kara shigowa aka gyarata sosai,wasu kaya ta saka sun mata kyau sosai, karan miski ne an mata doguwar riga, dashi an sanye wasu duwatsu faga tsakiyar rigar, tayi kyau sosai, alkyaba aka sa mata a saman kayan.

Abu Turab kam ya hade rai sosai ganin Sabi”u ya nace akan sai ya bishi, haka Sabi”u ya hakuri shi kuma ya fito bayin da zasu sadashi da inda zasu hadu suna gaba.
Sai da sukaga ya shiga ya zauna sannan suka fito.
Bilkisu kam Jakadiya ce ta kawota, ta kwashi gaisuwa agun Turab sannan ta fita.
Kan Bilkisu na kasa bayan ta zauna, Abu Turab ya d”an kalleta kadan, tabbas tanada kyau sai dai shi wannan bai dakeshi ba.
Bayi ne suka shigo da tire dauke da kayan marmari suka jere a gaban Turab.
Har suka fita ba wanda yace ufan a cikinsu, ta gefen ido take kokarin san ganinsa sai dai ta rasa me yasa takejin wata irin kunya.
Kallanta yai yace ” bako iya gaisuwa bane?”
D”agowa taita kalleshi, maganar da zatai ne ta tsaya mata sakamakon hada idon da sukai.
Kasa tai da kanta batace komai ba.
Shima shiru yai, sun dan dade a haka kafin yace ” da alama bacci ne ya kamaceni.”
Kallansa tai tace ” da wuri haka?”
Yace ” to me zan miki? Kinyi shiru, nima nayi shiru to me zamu jira?”
Baki ta d”an turo kadan tace ” Barka da isowa.” A hankali tai maganar
Yace ” ni banji me ma kikace ba.”
Dan Murmushi ne ya bayyana a fuskarta tace ” Da alama kanada mita.”
” ni ba mace ba mai zai hadani da mita?”
Tad”an tabe baki tace ” mata ne kadai ke mita?”

” ban sani ba, wannan kuma ke za”a tambaya ai.”
Kallansa tad”anyi zatai magana ta d”aga girar sa duka biyun yace ” baki gama kallan nawa bane?”
Idanta ta d”auke da sauri tace “wa yace ma kallanka nake?”
“Yarinyar da kika aiko na d”auka ta sanar dake kamannina da yanda nake.”

Kanta ta juyar gefe, cikin kunya tace ” wace yarinyar kenan?”
Kafada yadan daga yace ” bansanta ba.”
Shiru tai a ranta tace ” Shi wannan haka ake zancen? Neman fada? Ita ta saba duk wanda yazo gunta tofa wasa ta zaiyi tayi itakuma tana dauke kai.
Jitai yace ” kina tunanin wani irin zance nakeyi haka ko?”
Kallansa tai batace komai ba, yace ” baki sanni ba, nima bansanki ba yauce ranar da muka fara ganin juna, bazan yabeki akan abinda ba haka ba, ba kuma zan kusheki ba akan abinda ban sani ba, banida tabbas zamu kara haduwa da juna kinga kuwa bazanso in bar tarihin karya ko dadin baki agunki ba.”
Kallansa tai ta kasan ido, ba shakka kalamansa sun mata dadi.
Kanta na kasa tace ” Amma ai ina gani ya kamata ka nunamin ko na maka alamar so ko aminta da hadin da akai.”
Murmushi yadanyi kadan yace ” Bana sanki!”
Cikin tsananin tashin hankalin jin wannan kalmar yasa ta d”ago ta kafeshi da ido, iska yadan furzar yace ” kina sa ran daga ganinki sai in fara sanki?”
Idanunta tai kasa dasu batace komai ba, yace ” Bilkisu!”
Kallansa ta karayi, yace ” kina da kyau na tabbata kowa na fada miki haka, kinada mulki wanda ke kanki kinsan haka, sai dai inaso ki sani karkiyi tunanin hakan zai na soki, ba wai dan abinda kike dasu baimin ba sai dai dan ni ban yarda da wadannan sune abinda ya cancanta ba a so, sannan ban yarda da love at first sight ba.”

Jiyai tace ” sai me ka yarda dashi?”
Murmushi ya mata yace ” sirri ne.”
Shiru ne ya ratsa na “yan dakiko.
Jiyai tace “Nagode.”
Kallanta yai cikin mamaki yace ” name fa?”
Tace ” Na gaskiya daka fadamin.”
Yace ” Ina miki fatan alkairi a rayuwarki, ana tabbata ba lalai mu kara haduwa ba.”
Mikewa yai zai tafi, jiyai tace ” in kuma na bukaci hakan fa?”
Juyowa yai cikin mamaki ya kalleta bai amsa mata ba.
Wani sansanyar murmushi tamai tace ” Ban taba had”uwa da mutumin daya fadamin gaskiya ba sai kai, da fari na fara jin haushi sai dai a hankali na fahimci gaskiya dama d”aci gareta.”
Kallanta kawai yake baice mata komai ba.
D”agowa ta kara yi ta sakar mai murmushi tace ” Da alama kai zaka gaji masarautar Zariya.”
Cikin mamaki ya kalleta sannan yace ” me kike nufi?”
Tace “sani ne bakai ba ko kuma bakasan ne na fahimceka? Na tabbata ka san cewa bazan auri wanda bashine zai gaji sarauta ba, sannan tunda mahaifinka ya turoka nan alamace ta kai yakeso ka mulki masarautar sa.”

Gabansa ne ya fadi cikin mamaki yace ” aurenki haka yake nufi?”
” Da farko ance mana baka gani sai dai daga baya aka kara aikowa akan ka samu sauki.”

Idanunsa ne suka dan rage girma ya matso kusa da ita yace ” waye ya sanar daku hakan?”
Murmushi tamai tace ” na sani sirri ne dan nima ni kadai Mahaifina ya sanar ma hakan, da farko abin yaban haushi dan a gaskiya wannan dalilin ne yasa na tura Munnira ta ganka, sai dai yanzu na fahimci kanada dalilinka nacemin baka gani da alama da bakaso zuwa ba.”

Wato da bayan sunyi bincike sunji labarin baya gani, amma mai martaba ya aiko da sakon yana gani.
Mikewa yai daga tsugunnan dayai a gabanta, baice komai ba yai waje ransa a b”ace.
Kenan saboda dalilin nan aka turoshi? Shikuma harda kokarin yi mata sauki dan bin umarni?

Ba shakka ransa ya bace na biyomai ta bayan gida da akai…
Yana fita Jakadiya ta matsu gunsa da sauri tace ” Ranka ya dade Mai Martaba nasan ganinka.”
Kallanta yai yace ” Yana ina?”
Nan ta nuna mai hanya, tana gaba yana binta a baya zuciyarsa fal take da tunani kala kala.+

Wani katon d”aki ne ba komai a cikinsa, capet ne a shimfid”e sai “yan tum tum.
Sallama yai ya shiga kamar yanda Jakadiya tace ya shiga.
Zama yai nesa da Mai Martaba sannan ya tankwashe kafofinsa, sannan ya gaisheshi.
Tunda ya shigo shikuwa Mai Martaba yake kallansa, cikin yaban nutsuwa da zatinsa.
Cikin mulki ya amsa sannan yace ” Abu Turab Barka da zuwa Masarautarmu, ina fatan komai ka sameshi yanda ya kamata.”
Kansa na kasa yace ” ina kara godiya da karamcin da muka samu.”
Shiru ne ya d”an ratsa kafin Mai Martaba yace ” Ammm Abu Turab”
Abu Turab ya nutsu, Mai Martaba yacigaba ” Kaga Bilkisu?”
“Naganta Ranka ya dade.”
Me kake tunani game da ita?
Abu Turab ya d”ago sannan yace ” Ina kara jinjina ma na tarbiyantar da ita dakai da sai dai fatan Allah ya kyautata rayuwarta.”
Murmushi Mai Martaba yai yace ” Ba shakka kai din jinin Sarauta ne ko daga yanda kake bani amsa cikin fasaha ba tare da na zargi wani abu ba.”
Abu Turab yai kasa dakai yace ” ina godiya da yabon da kamin.”
Shiru suka kara yi kafin Mai Martaba yace ” bari na gyara tambaya ta to, mai kake gani game da auranka da Bilkisu?”
Sarai yasan abinda yakesan ji kenan sai dai shi bashida ansar wannan tambayar dan kuwa shi dai ba santa yake ba, ba kuma zai iya kallan idan mahaifinta yace baya santa ba, sannan a xahiri gaskiya bai kuma tsaneta ba.
Kansa na kasa yace ” Ranka ya dade ai wannan tambayar tana hannun Bilkisu, duk abinda ta yanke shine daidai.”
Kallansa yai cikin yabawa da nutsuwa da kaifin tunaninsa yace ” duk da haka inasan ji xaga gareka, Bilkisu ita kadaice “yata, duk da ina sha”awar ta auri mai mulki sai dai abin da nafiso shine inga ta auri wanda zai kularmin da ita.”
Abu Turab ya nisa sannan yace ” Ran ya dade ka gafarceni amma mune muka nemi had”in auran nan hakan ai yana nuna muna so ne.”

Cikin jin dadi yace ” nagode da jin amsoshinka, Allah yamana jagora.”
Ameem ya fada.
Shiru sukai kafin Abu Turab yace ” Zan koma gobe in sha Allah, in munji daga gareku xamu damu dawo da yardar Allah.”
Duk da baiso tafiyarsu gobe ba saboda yana san yaga sun kara fahimtar juna, sai dai bazai iya hanashi ba.
Yace ” Allah ya kaimu.”
Sallama yamai sannan ya mike ya fito, a falo ya tadda Sabi”u yana zaune sallama kawai yai ya wuce shi ya shiga ciki, Sabi”u cikin mamaki ya kalleshi zaiyi magana yana fuskarsa a had”e yasan ko yamai magana ma ba lalai ya amsa mai ba.
D”aki ya shiga ya yazauna a bakin gado tare da dafa kansa.
Tunanin maganar da Bilkisu ta fadamai yakeyi, me mahaifinsa yake tunani? Anya kuwa abinda take tunani haka ne? Shiru yai yama rasa ta inda zai fara ba ma kansa amsa.
Washe gari kuwa da safe yace ma Sabi”u ya shirya zasu koma, Sabi”u bai musa ba dan yaga yanda yake tun daren jiya.
Sun sanar da tafiyarsu haka aka kawo kayan tsaraba kala kala daga bangaren Fulani wato maman Bilkisu da kuma bangaren Mai Martaba aka basu.
Sunje shiga mota Munnira ta taho da gudu, ganin zai shiga yasa tai sauri cewa ” Uncle Turab!”
Abu Turab ya tsaya sannan ya waiga, ganin Munnira yai ta karaso da gudu, ya kalleta yace ” Munnira ya da gudu?”
Tana haki tace ” UmmaBilkisu ce ta aikoni naga kuma zaku tafi.”
Kallanta yai yace ” aiken me kenan?”
Wata yar karamar jaka ta mikomai tace ” Gashi.”
Amsar jakar yai sannan yace ” ki mata godiya.”
Tace to.
Mota ya shiga Sabi”u yaja.
Suna hawa kan titi Sabi”u yace ” da na dauka itace ta bata maka rai, amma ganin sakonta yasa nasan ba ita bace, me ta kawo mana ne?”
Abu Turab ya bud”e jakar, wani kwalbar turarene mai kyau yana bud”e kwalbar wani kanshi ne ya bud”e motar, rufe turaren yai ya ajiye shi sannan ya jinginar da kansa kan kujera tare da rufe idanunsa.
Ganin haka yasa Sabi”u yai gum….

*********
A can kuwa Zariya yau da sassafe aka kawo musu gulmar zuwan abu Turab can.
Tashin hankalin da Magajiya ta shiga baya misaltuwa, cikin sauri ta aika a kira mata Hisham ko wanka lokacin baiyiba haka ya fito dan ancemai kiran na gaggawa ne.
Sun shiga can kuryar d”aki ta kalleshi cikin yanayinta na isa da san boye damuwarta tace ” Hisham mai martaba ya biyomana ta bayan gida.”
Kamar ya kenan?
“Ya tura d”ansa ganin “yar sarkin kano.”
Hisham yace ” ita zai aura?”
Ranta ya b”aci tace ” kai ni meyasa kwakwalwarka kamar ta kifi take?”
Kallanta yai cikin tsananin kunar rai sai dai tsoro yasa yace ” Magajiya ban fahimceki bane.”
Kallansa tai tace ” “yar sarkin kano fa na fada maka, wacce nafadama xamu hadata da Abdulmajid kai bakasan me auranta yake nufi ba?”
Hisham yace ” Au matar da kikace za”a tura?”
Tak tsaki tace ” Bakasan halin Mai Martaba ba kenan, ba kuma kasan me yake tunani ba.”
Hisham ya kalleta da nufin san karin bayani.
Tace ” ya fara shiri akan d”aura Abu Turab mulki.”
Idanu Hisham ya zaro yace “Mulki kuma? Makahon?”
Idanu tadan kanne na bacin rai tace ” shine abinda na kasa fahimta, me zai sa Sarkin Kano ya aminta da makaho a matsayin siriki? Me yake tunani akan aura ma yarsa kwaya d”aya makaho?”
Hisham yace “au ya amince ne?”
Tace ” majiyata ta sanar min da alamar amincewa dan kuwa ancemin har kiransa yai daga baya sai dai ba wanda yasan me sukai a ciki.”
Cikin tashin hankali Hisham yace ” ai kam bazai taba yiwuwa ba, mulki na Abdulmajid ne haka kuma yarinyar dole ne mu san yanda zamuyi.”
Magajiya tace ” tashi zakai yanzu ka je Masarautar kano, ka samu Hajiya Karama kawata wato Amaryar sarki ka tambayeta komai, sannan ka san yanda zakai su tsani Abu Turab ni zan shiryama duk abinda zaka fada.”
“Hakan yayi Ranki ya dade, yaushe ya kamata in tafi?”
Tace ” a yau zakaje dan da zafi zafi akan bugi kirji.”
Hisham yace ” na fahimceki amma in suna can fa?”
Shiru tai sannan tace ” sai yafi ma, yanda za”a katse auren a basu sallama.”

Dariya yai yace ” ko banza naga idan d”an jakar uba.”
Murmushi tai sannan tace ” ai shi mugunta wani sa”in alheri yake sama, in har shi yana tunanin mugunta yamana dole ne mu maidashi abinda zai amfanemu in yaso sai muga yanda xaiyi, kuma Wallahi zaisan niyama haka, zai kuma san Makaho da mai gani ba karfin su d”aya ba, da MAGAJIYA yake zance.”

Hisham yasa dariya yace ” wa ya isa dama yaja dake?”
Tai d”an tsaki tace ” Abdulmajid inyaso yazo ko zuwa jibi ne.”
Yace ” Hakan yayi.”
Sallama ya mata akan zaije ya kimtsa.

*************
Khadija tayi kwalliya ta fito da nufin zuwa gidan wata “yar uwarsu a cikin gari, tana tafe cikin sanyinta dan dama mai sanyi ce.
Ita kuma a tsaye take a jikin wani shago tana amsar sakon da aka aikota ta amsa, juyowa tai cak idanunta suka hango Khadija wacce take nufo gunta.
Kura mata ido tai cikin waswasi dan kuwa an dade rabon data ganta, ta kusa da ita taxo wucewa, cikin rashin yarda da abinda take tunani tace ” Khadija!”
Kallo gun Khadija tai tare da tsayawa, Mairo ta kalleta tace ” Khadija!”
Khadija ta matso gunta fuskarta d”auke da murmushi tace ” Naam.”
Mairo ta matso tace ” Khadija ce ta gidan Waziri?”
Khadija tai dan dariya tace ” nice dai Mairo, da ban ganeki ba sai da kika matso daf.”
Gaban Mairo ne yadan fadi dan itakam tasan ita Abu Turab yake so, daurewa tai tace ” yaushe kika dawo?”
Khadija tai murmushi tace ” Ban dade ba, Allah dai bai had”amu bane.”
Mairo tace ” ikon Allah! Kuma kina shiga gidan Sarki?”
Tace sosai ma, ko shekaran jiya ma naje.”
Mairo ta daure tace ” Ya Turab fa? Kun had”u?”
Gani tai Khadija tayi kasa dakai tana murmusawa, sannan tace “mun had”u sosai ma.”

Mairo tai dariyar yake tace ” bari naje aike na akai kar aga na dade.”
Khadija tace ” to, sai mun sake haduwa.”
Juyawa yai ta amshi sakonta ta juya da sauri ta fara tafiya, jitai gaba daya jikinta yai sanyi, ba shakka Abu Turab zai mata wuyar samu yanzu a da tana tunanin kila tanada chance amma yanzu kam ta tabbatar ya mata nisa, balle ga Bilkisu, ina ita “yar gidan wani Barde ina takara da manya?
Haka ta isa gida jikinta duk ya gama yin sanyi, tana shiga ta ajiye sakon ta shiga d”aki ta kwanta, a hankali taji wani zazzafan hawaye yana zubo mata ta kuryar idanunta….
Magajiya ce xaune a kilisar Mai Martaba, ta umarci kowa ya bargun, sun dade a zaune kafin cikin kasaitarta tace ” Ranka ya dade ashe Abu Turab yana kano?”
“Eh.” Abinda yace kenan yai mata shiru.
Kallansa tai fuskarta dauke da murmushi tace ” Daren jiya na aika yazo mu gaisa sannan yaci abincin dare a guna akacemin ai yayi tafiya.”

“Ha ka.” Nan ma daga fadar haka taji bai ce komai ba, sosai ranta ya b”aci ammabta daure tace ” Dama zuwa nai in fadama wata magana.”+

“Inajinki.”
Ta nisa sannan tace ” tunanin hada auran Abdulmajid da Gimbiya Bilkisu nakeyi.”
Yace ” hmm shawarace mai kyau hakan sai ki aika musu da takarda.”
Kallansa tai cikin mamaki tace ” ai kai ya kamata ka aika Ranka ya dade.”
Kallanta yai sannan yadan murmusa yace ” fadamin kikai ai ba shawara kika zo nema ba, kinga kuwa banida abin cewa.”

Kallansa tai sannan tace ” Ranka ya dade ka taba nuna cikakiyar kulawarka ga Abdulmajid? Kana sane lokacin auransa yayi amma sam banga kana nema masa wacce ya kamata ba.”

Kallanta yai yace ” kin taba bani girmana na uba a kan al”amuransa?”
“Me kake nufi da kalamanka?”
“Inkin gama inaso in runtsa kafin na fita fada.”
Ya fada tare da dan lumshe idanunsa.
Ba shakka ranta yayi tsananin baci ace kamar ita Magajiya ita mai martaba zai wulakanta?
Kallansa tai rai a bace, mikewa tai ta tako a hankali har inda yake ta tsugunno inda yake ta sakar mai wani sansanyan murmushi tace ” Takawa kardai ka manta da Abu Turab idanunsa basa aiki, Abdulmajid shine kadai wanda zai kula dashi, ina ganin ya kamata ka kara karfafa zumuncin dake tsakanin “yan uwan biyu, ganin Abdulmajid shine babba kuma magajinka.”
Kallanta yai kawai, itakuma ta mike cikin salan tafiyarta, babu wanda ya isa ya juyata ko kuma ya nemi wulakantata, dolene abi abinda takeso inhar ana bukatar zaman lafiya a wannan gidan.

Mai Martaba kam bayanta yabi da kallo sannan ya girgiza kai har ta fita yana kallanta, a fili yace ” nine sarki ba ke ba, sannan da Abdulmajid da Turab karkashin ikona suke da ke kanki, tabbas zan nuna miki kashin namiji da mace ba d”aya bane.”4

*********

Abu Turab kam suna isowa ya wuce b”angaren Mahaifiyarsa, mamaki ne ya kamata da Lantana tace mata ta fito ga Abu Turab nan ya dawo.

Zama tai a saman kujera, shi kuma yana zaune a kasa ya lankwashe kafafunsa.
Bayan ya gaisheta ne ya nemi a basu guri, nan su Lantana suka fita.
Kallanta yai yace ” Umma me mai Martaba yake nufi da auran Bilkisu?”
Kallansa tai sai dai babu mamaki a idanunta tace ” Mahaifinka yana san ka gaje shi.”
Yace “in gajeshi? Ban fahimta ba.”
Basira tadan yi yake tace ” Ni kaina bansan me yake nufi ba.”
Mikewa yai waje.
Yana fita Lantana ta shigo da sauri, tace ” Tuba nake ranki ya dade, banyi da nufin jin abinda kuke cewa ba sai dai na taho kawoma Uban gidana ruwa naji abinda yake cewa.”
Basira tace ” ba komai Lantana.”
Lantana ta ce “Amma Bakya ganin hakan shine ya dace? Ko kin yafe musu abinda suka aika tama Yayanki?”

Abu Turab wanda ya dawo domin sanar da ita kartama Mai Martaba maganar tukunna yana tsaye jikin kofar yaji wannan kalaman na Lantana.
Ji sukai yace ” Me kike nufi da kalamanki?”
Basira ta kalleshi a d”an razane,itakam Lantana jikinta rawa ya shiga yi.
Takowa yai har inda suke, Lantana ta mike da sauri ta koma ciki.

Zama yai daf da mahaifiyarsa gwiwowinsa na kasa yace ” Umma meke faruwa? Dama ni nasan akwai abinda kika dade kina b”oyemin sai dai nayi alkawari bazan taba fara miki magana ba.”

STORY CONTINUES BELOW
Jiki a sanyaye cikin sanyin murya tace ” Tabbas akwai abinda nake b”oyema, a koda yaushe in nai yunkurin sanar dakai sai inji bazan iya ba saboda tsoron kar in sa ma d”aukan fansa a ranka.”

Yace ” Umma dan Allah ki sanar dani tun daga farkon rayuwarki.”

Basira ta numfasa sannan tace ” Sunana Basira………………………………………………………………”
Haka Basira ta zayyanemai kaf abinda ya faru da ita tundaga fyaden da aka mata zuwa auranta da Mai Martaba ba da sanin matansa ba, har zamanta a can gidan da kuma zaman da tai anan gidan, da matsalolin data samu bayan ta samu ciki har zuwa haihuwar tashin hankalin da ta fuskanta na zuwan Hisham da jin maganganunsu.

Tana kuka tace ” Kaji dalilin dayasa muka taso a gidan Malam”

Idanun Abu Turab sun kada sunyi wani mugun jaa, ita kanta bata taba ganinsa cikin wannan yanayin ba, fuskarta ta canza bakinsa kawai yake motsawa ta ciki, sai dai kaga alamu ta waje.

Handkerchief ya zaro daga aljihunsa ya mika mata baice komai ba ya juya ya fita.

Tabbas tasan ya shiga cikin tashin hankali, sai dai ita kanta mikin daya fara dishashewa a xuciyarta ne ya tashi.

Sam ko sandar ma bai d”auko ba, yana kokarin shiga b”angarensa yaji muryar Abdulmajid “Kai Blind man.”
Wani mugun kallo ya juyo ya wurgamai sannan ya bud”e kofa ya shiga ciki.

Abdulmajid ya juya ya kalli masu kula dashi cikin tsananin mamakin abinda ya gani yace ” kunga idanun Abu Turab? Ba kallona yai ba kuwa?”

Sukam basu gani ba sukace ” Tuba muke ranka ya dade amma bamu gani ba.”

Cikin fada yace ” karya kuke munafukai, xakuce baku gani ba, anya kuwa idanun makaho ne wannan?”

Abu Turab kam yana shiga d”aki ya kule ya zauna a kan gado, sai dai ba wanda yasan me yake tunani yake kuma sakawa a ransa, daga shi sai mahallicinsa.
**********

A kano kuwa Bilkisu da kanta ta sanar ma Mahaifinta tana kaunar Abu Turab hakan yamai dadi dan shi kansa ya mai.

Shi kuwa Hisham ya isa kano bayan azahar, bangaren Gimbiya Sadiya wato Amarya ga mai martaba, bayan an masa iso.

Bayan sun gaisa ne kansa na kasa yace ” Gimbiya nazone dauke da sakon Gimbiya.”
Murmushi tai tace ” Magajiya ikon Allah wani sakon ta aikoka dashi?”
Yace ” Maganar auren Gimbiya Bilkisu da Yarima Abdulmajid”

Kallan mamaki tamai tace “Me kake nufi? Na da”uka ai an bar wannan maganar ganin yau d”innan Abu Turab yabar gidan nan, kuma inada labarin Bilkisu ta amince dashi.”

A razane ya d”ago yace ” Gimbiya ta yaya Yar sarki guda zata amince da Makaho? Na tabbata asiri suka mata.”
Kallan rashin fahimta tamai tace ” waye makahon kenan?”
“ABU TURAB mana.” Ya fada kansa tsaye.
Tace ” ban fahimta ba, a iya dai sanina banji ancemin yaran nan makaho bane.”
Murmushin jin dadi yai yace ” kisa a tambayo miki gimbiya.”
Tace ” in kuwa hakane na tabbata Mai Martaba bazai aminceba.”
Nan ta aika a kira mata Jakadiya.

Bayan Jakadiya ta gaisheta ne Gimbiya Sadiya ta kalleta tace ” Nikam ya Abu Turab yake ne? Yanada wani nakasu ko abin kushewa a tattare dashi?”

Jakadiya tace ” ban fahimceki ba Gimbiya.”

Gimbiya Sadiya tace ” hakkinane a matsayina na matar Sarki intambayi wanda Bilkisu zata aura.”
Jakadiya tace ” Tuba nake ranki ya dade, amma Yarima Turab bashida wani nakasu a jikinsa.”

Da sauri Hisham yace ” idanunsa fa?”
Tace ” idanunsa kuma? A iya sanina bashida wata matsala na gani da idanunsa.”
Hisham ya kalleta yace ” Jakadiya ki tuna da kyau, baki ganshi da sanda ba?”

Kallan mamaki tamai tace ” Na kasa fahimtar wannan tambayar taka, ni dai a iya sanina bashida wata sanda kuma sunyi magana ta fahimta da Gimbiya, ya kuma shiga gun Takawa.”

Gimbiya Sadiya ta kalleta tace ” tashi kije Jakadiya.”
Zufa ne ya shiga ketoma Hisham tsananin tashin hankali, kasa yarda yai da wannan zancen ya mike yace ” bari naje gun Mai Martaba mu gaisa.”
A ransa kuwa so yake yaje ya dan tambayeshi a dabara.

Yana mikewa yaji kafafunsa sun mai nauyi, da kyar ya iya d”agasu.
Haka ya garzaya fadar sarki.
Bayan ya shiga ne suka gaisa da Mai Martaba.
Sarki ya kalleshi yace ” Waziri ba dai biyu Abu Turab kai ba?”
Hisham ya dan yi yake yace ” a”a na dai shigo garin ne naga ya dace inzo mu gaisa.”
Sarki yace ” hakan yayi, Abu Turab sun tafi yau.”
Hisham yace ” ai na d”auka ma sai zuwa gobe zasu taho, ko dai abin bai yiwu bane?”

Sarki yai murmusa yace ” zamu aiko da amsa cikin wani satin.”
Hisham ya rasa ta inda zaiyi tambayar ganin yanayin Sarki alama ce ta gamsuwa da yai da Abu Turab.
Sallama yamai sannan ya mike ya fito.
Sai da ya kara tambayar wasu fadawa kowa ya tabbatar mai ba sanda a hannun Abu Turab sannan ya juya ya shiga mota.
Jiyai kansa ya dau wani zafi yana rasa ta inda zai fara tunani.
Me ke faruwa?
Kenan kallansu kawai yake?
Tabbas lalai yau yanada mumunan labari, suna mai kallan dan tsako ashe kura ne?????
Nace Daga Baya kenan Hisham….😝

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE