KAINUWA CHAPTER 9

KAINUWA CHAPTER 9

Hisham ya iso Zariya cikin tashin hankali, ana magrib yana shiga bangaren Magajiya. Zaune take gefenta kuma Khadija ce tana duba mata wasu kayayyaki, Abdulmajid kuma na gefenta na hago. Hira sukeyi da Abdulmajid sama sama, itakam Khadija bata sa musu baki a zaune kawai take tana aikin da aka sata. Can cikin hirar tasu ne Abdulmajid ya kalli Khadija yace ” ke dama inada magana dake.” Kallansa tai batace komai ba. Fuskarsa a had”e yace ” haryanzu baki daina zuwa b”angaren Abu Turab ba ko? Kina mace ko kunya.” Magajiya ce ta kalleta tace ” Khadija me kenan?” Kanta ta maida kan kayan tace ” meye amfanin ma in naje tunda ba kulani yake ba?” Dariya Abdulmajid yasa yace ” kinji kunya wlh, kina mace kina bin namijin da baya sanki.” Zatai magana Hisham ya banko kofa cikin hanzari. Jin yanda a ka bugo kofar yasa duk su ukun suka maida ha kalinsu kan kofar. Hisham na shigowa ya kalli Khadija yace ” bamu guri.” Mikewa tai tsam dan dama ba san zaman takeyi ba sai dai jikinta ya bata ba maganar arziki zasuyi ba. Tana fita ta tsaya a jikin kofar d”akin. Hisham ya kalli Magajiya cikin tashin hankali yace ” Magajiya!” Ita kanta hankalinta ya tashi ganin ita data aikashi maganar aure kano? Ya dawo mata a haka?” Kallansa tai tare da tattara hankalinta kansa. Yawo ya had”iya sannan yace ” yaran nan yana gani Magajiya.” “Yaro? Wani yaro kake nufi kenan?” Yace ” yaron nan mana da baya gani.” Idanu tad”an juya tace “wai wani yaran kake nufi? Nibansan wani yaro ba.” Abdulmajid ma yace ” wani yaro kake nufi Kawu?” Hisham yace ” Yarancan Abu Turab.” Dariya Magajiya tai tace ” Waziri? Ko dai gajiya ta fara ratsaka ne? Me kake san fada takamaimai?”+ Hisham ya kallesu cikin wani yanayi yace ” Wlh da gaske nakeyi, yarancan Abu Turab idanunsa garau suke.” Abdulmajid ya mike tsaye yace ” ni wlh na dauka maganar arziki zaka fada ashe tsokana kazo da ita, ni nayi masallaci.” Hisham ya kalli Magajiya yace ” Magajiya na taba miki karya akan harkar dana san bazata amfanemu ba?” Wannan lokacin kam ta kalleshi kallan nutsuwa, Abdulmajid ma ya ja ya tsaya. Khadija kam da baya da baya ta juya tai waje cikin tashin hankali, me kenan? Hisham ya kalli Magajiya sannan ya kalli Abdulmajid yace ” dayaje kano a garau yaje musu.” Magajiya ta kanne idanuwanta tace ” ban fahimta ba.” Nan Hisham ya zayane mata kaf abinda ya faru na zuwansa. Tashin hankali karara ne ya bayyana a idanun Magajiya, kallansu tai cikin tashin hankali tace ” ku bani guri.” Nan suka mike suka fita. Abdulmajid ma bangarensa ya wuce cikin d”emuwa da rashin sanin abinda zaiyi. Shi kuma Hisham yai waje. Magajiya ta kasa zaune ta kasa tsaye ba shakka in har hakan ne lalai kaf duniya ba wanda ya taba rainamin hankali irin yaran nan. Kwallawa wata mai kula da ita tai, cikin hanzari ta iso. Bata ko juyo ta kalleta ba tace ” kiramin Abu Turab.” To tace kawai tai waje itama. Abu turab yana zaune kan sallaya tilawa yakeyi cikin daddadan muryarsa, yau ko masallaci bai je ba dan bayasan ganin kowa.1 Garzali ya mai sallama, sai daya kai aya sannan ya amsa mai. Garzali ya matso ya tsugunna sannan ya sanar dashi sakon Magajiya. Ya dade kafin yace ” ace mata ina zuwa.” Nan yai waje. Sai dayai sallar isha”i sannan ya mike ya fito, Garzali ya mikamai Sandarsa wacce Lantana ta kawo. Amsa yai sannan yai gaba Garzali yabi bayansa. Bayan an mai iso ya zauna a kilisarta sannan ta shigo cikin takamarta. Idanu ta kafa mai har ta zauna shikam fuskarsa a had”e take yana zaune kansa a kasa. Bayan ta zauna ne ta kalleshi tace ” Abu Turab ka iso?” “Barkanki da warhaka Umma Babba.” Murmushi ta sakarmai sannan bata amsa ba tace ” kiranka nai in baka wani labari.” Shima bai amsa mata ba dan lalai ji yake bazai iya kallanta ba saboda tsananin tsana. Magajiya tacigaba ” Wani dan tsakone kurma ya taso karkashin kulawar kura, ita kurar dama tanada nata d”an hakan yasa ta had”asu duka ta rike, a kwana a tashi sai kurar nan ta tsufa, ta fahimci dole tana bukatar barma d”anta mukaminta a daji. Kasan abin mamaki?” Abu Turab ya d”ago suka had”a ido, bai d”auke idanunsa daga cikin nata ba yace ” bazai wuce wannan d”an tsakon kurma yace shi yake san aba wannan mukamin ba.” Ta kuramai ido itama tace “Haka! Ashe ka harbo jirgin, sai dai kasan wani abun tsoro a labarin?” Kallan ban fahimceki ba ya mata tace ” Tun daga sanda Kurar nan ta fahimci kudurin wannan d”an tsakon har yau ba wanda yasan inda wannan d”an tsakon yake.” Wani lalausan murmushi ne ya bayyana a fuskar Abu Turab yace ” sai dai ban fahimci abu d”aya ba a labarin, d”an tsakon dama can kurma ne ko kuwa yayi hakan ne da saninsa ya noke bakinsa?” Idanun Magajiya ne suka d”an canza sai dai da sauri ta maida fuskarta cikin yanayin hankali a kwance tace ” hmm wannan shine abinda ya sa kurar nan dana sani.” Gani tai ya saki wata yar karamar dariya har hakwaransa suka bayyana ya kalleta yace ” Tuba nake Umma Magajiya, na saki a duhu danai na nuna miki nidin bana gani.” Wannan karan kam duk yanda taso ta b”oye bacin ranta ta kasa, karara ya nuna a fuskarta. Abu Turab ya rangwadar da kai yace ” umm ya zamuyi yanzu?” Tace da me kenan? Yace ” dan banaji zan iya yafemiki.” Kallo tamai cikin mamaki tace ” bakaji xaka iya yafemin kamar ya kenan?” Fuskarsa ce ta canza idanunsa sukai jaa, ya kalleta yace ” bazan taba yafe miki ba daga ke har yayanki, abinda yama yayan mahaifiyata da matarsa da ke da kika umarceshi a sanadiyar kokarin rabani da duniya da kukai kuka jamusu mutuwa, ni Abu Turab in har Basira da Abdussamad sune suka haifeni sai na sa an muku hukunci daidai da laifinku.”2 Wata muguwar dariya ta saki, wanda ya sashi tsayawa yana kallanta tace ” kai a suwa kenan?” Yace ” a wanda yake da damar zama Sarki.” Ta ja tsaki tace ” Shekaruna d”aya da mahaifinka, hakan na nuna nid”in batayau bace, ba kai ba hatta mahaifinka bai isa yaja dani ba.”2 Abu Turab ya d”an juya bakinsa sannan ya had”a lab”ansa yace ” well, shi daban nid”in daban, mu zuba mu gani.” Tace ” shikenan mu zuba mu gani, na baka sati biyu kacal, ina zaune anan zakazo gwiwowinka biyu ka nemi gafarata.” Yace ” ina fatan hakan ta kasance.” Kallan juna sukai, kansa ya saukar kasa ya juya kansa gefe tare da d”aukan sandarsa yace ” Umma Babba nagode ni zan wuce, ki huta lafiya.” Kallan mamaki tamai, gani tai ya sa sanda a gaba kamar makaho. Idanu ta kuramai har ya fita, ta murmusa tace ” hmm a kashi 100 na baka 40, ba laifi ka iya b”oye fuskarka da abinda ke ranka, ko dayake d”an Abdussamad ne.” Fuskarta ta kuma had”ewa tace ” kai har ka isa? Kamar ni? Kamar ni Magajiya ka rainan hankali?” Kwafa ta saki. Abu Turab kam na fita ya juyo ya kalli bangarenta sannan ya juya ransa a b”ace. ********* Itakam Khadija ta shige d”aki ta kwanta akan gado, me ke faruwa? Ya Turab yana gani? Anya kuwa? Ta yaya? Yaushe? Itakam ta kasa yarda da abinda taji, ba dai wani sharrin zasu kullama bawan Allah ba? Da sauri ta mike zaune tace ” dole in fadama Yaya gobe akan abinda sukace.” Washegari.+ Da safe zaune yake a gaban Mai Martaba a cikin Turakarsa. Mahaifinsa ya kalleshi cikin kulawa yace “Turab me yasa ka dawo tun jiya? Sannan tundaka dawo baka zo ba.” Fuskarsa a d”aure take dan sam ba fara”a a cikinta kallansa yai yace ” Dama zuwa nai na sanar dakai zan auri Bilkisu yar gidan Sarkin kano.” ” Alhamdulilah nagode kwarai na kuma ji dadi daka fahimceni.” “Bayan umarnin auranta daka bani a yanzu auranta yana tattare da amintata, a da auranta zanyi saboda umarninka, sai dai yanzu zan aureta ne dan kaina.” Fuskar mai martaba ta kara fadada da farinciki yace “naji dadi yanda kuka fahimci juna.” Kallan Mahaifinsa yai yanajin wani radadin takaici a ransa, yace ” zan koma.” “Abu Turab!” Komawa yai ya zauna sannan ya kalli Mahaifinsa dan yanda yaji ya kira sunansa yasan yana bukatar nutsuwarsa. Mai Martaba ka kalleshi cikin kulawa yace ” Abu Turab me yasa kake so ka b”oyemin abinda ke ranka? Me yasa bakasan mudinga raba damuwar dake zuciyoyinmu?” Shiru yai sai dai zuciyarsa tadan raunana. Sarki yace ” Meke damunka?” Shiru ya kuma yi sai dai a wannan karan ya d”ago ya kalli mahaifinsa da idanunsa da suka canza launi. Sarki ya cigaba” Shikenan mubar maganar inhar zuciyarka bata san inji.” Abu Turab yace ” zan koma Abba.” Mai Martaba ya murmusa yace ” to Turab.” Mikewa yai ya fito daga bangaren mahaifinsa, ba shakka yanasan ya sanar dashi damuwarsa da kuma neman shawararsa sai dai ba yanda zaiyi domin kafin ya kasance mahaifinsa sarki ne shi a wannan garin dole kuma yai abinda ya dace a matsayinsa na sarkin garin. Bangarensa ya nufa rike da sandarsa yana gana Garzali da wani na gefensa. Sunsha kwanar da zata kaisu bangarensa yaji muryar Khadija tace ” Ya Turab.” Haka kawai ta samu kansa da kin tsayawa dan abinda Mahaifinta sukamai bayaji ko ganin Khadija yana kaunar yi a wannan lokacin. Ganin bai tsaya ba yasa ta kara sauri, har tazo inda suke, tace “Ya Turab.” Tsayawa yai sai dai bai juyo ba. Gabansa ta dawo ta kalli Garzali tace ” dan Allah kudan matsa kadan zanma Ya Turab magana.” Nan suka gaisheta suka matsa. Kallansa tai tace ” Yaya.” Bai kalleta ba sai dai yace ” ya akai?” Tace ” yaya kana ganina?” “Me kike nufi da hakan?” Ta kara matsows tace ” Yaya ninasan baka ganina, sai dai na rasa dalilin Abba na na zuwa ya fadama Magajiya wai kana gani.” Kallanta yai, ta kalleshi hakan yasa ya kauda idanunsa, tace ” Yaya Please ka kula da su wlh sam hankalina ya kasa kwanciya dasu, na tabbata da abinda suke shiryama.”3 Jitai yace ” yanzu kinaso ki cemin zuwa kikai kiban shawara akan kula da Mahaifinki? Ko kuwa zuwa kikai ki sanar dani Mahaifinki zai cutar dani?” Cikin rashin fahimtar kalamansa tace ” Ban fahimceka ba.. ..” ” in mahaifinki zai cutar dani tayaya nake da tabbas din ke bazaki cutar dani ba?” Kallansa tai a zabure cikin tsananin mamaki tace ” Yaya.” Yace ” da mahaifinki da ni wanene mafi kusanci dake? Wanene wanda yake jininki? Tayaya zan yarda zaki juya ma mahaifinki baya akan wani makaho wanda bakuda hadi dashi?” Gaba daya ta ma kasa magana dan batada amsar da zata bashi, tana neman amsar da zata bashi taga ya fara tafiya. Idanunta ne suka ciciko a hankali wasu zafaffan hawaye suka xubo mata, me yaya yake nufi? Gani tai ya tsaya a jikin kofar bangaren Mahaifiyarsa da alama magana yake da wani, gani tai ya saki fuska ba kamar yanda ya cukule mata ba. A hankali ta tako har gefen da suke. Mairo ta gani a tsaye a gun rike da kula suna magana, juyawa tai zuciyarta sam ba dadi. A bangaren sa kuwa, bayan ya taho daga gun Khadija zai wuce yaji tace ” Ya Ina Kwana?” Juyowa yai ya kalleta yace ” Mairo kece?” Tace ” nice, Umma ce ta sani in kawo mata abu yau da safe.” Murmushi yai yace ” Mairo kinaji da Umman nan.” Ta kalleshi tace ” Da cemaka akai Ummanka ce kai kadai?” Kallanta yai yace ” Yar gidan Umma ce ke dama ai.” Zatai magana yace ” ki gaisheta.” Tace ” bazaka shiga ba?” Kallanta yai fuska a sake yace ” Later.” Daga nan yai gaba. Kallansa tai cikin mamaki dan taga ba haka suka saba ba. ************ Abdulmajid ne zaune gun Magajiya yace ” Umma ya kukai Jiyan? An bincika yana ganin?” Magajiya ta kalleshi tace ” Abdulmajid, ka nutsu sosai kaji abinda zan fada ma.” Kallanta yai sannan yace ” inaji.” ” Ka shiga hankalin sosai da Abu Turab ka daina masa kallan wanda bashida wayau ko bai san komai ba, wlh wnnan yaran hmmmm” Tai shiru sannan tacigaba ” kadai bi a hankali karka kuskura ka fada tarkwansa.” Abdulmajid ya dan tabe baki yace ” ni Umma har wannan yaran ya kai in shiga hankalina a kansa?” Ta kalleshi cikin isarta sannan ta ce ” Abdulmajid kenan.” Kara tabe baki yai yace ” ni Umma dama maganar aurena nazo muyi, nace tunda dai Bilkisu an riga an hadata da Turab mai zai hana mu juya akalar auran kan Mairo.” Ya karasa maganar yana dan sosai keya. Kallansa tai tace ” Mairo? Wacece hakan?” Yadanyi kasa dakai yace ” Mairo “yar gidan Barde.” Barde?bakada hankali ne?” Yace ” Umma to….” Katseshi tai cikin fada tace ” nimeyasa baka tunani ne a al”amuranka? Abu Turab zai auri Gimbiya Bilkisu kai kuma dan hauka kacemin wata Mairo? Me yasa ne bazaka dinga abu da tunani ba?” Fuska ya hade dan maganar ta batamai rai, Magajiya ta cigaba ” kada ka kuskura ka karamin wannan banzan zancen.” Tana kaiwa nan ta maike tai ciki. Kallo ya bita dashi da alama zai je gun Sarki ya fadamai kuwa dan shi kam Mairo yakesan aura ko ta wani haline kuwa, dan kwanan nan har mafarkinta yake wai sunyi aure. 🤣 ************** Kwana biyar da dawowarsu kuwa Mai Martaba Sarki Shu”aib mahaifin Bilkisu ya aiko mutane daga Masarauta akan amincewa da aure da sukai. Wannan labari ya tadama Khadija hankali, sai dai duk yanda taso ganin Abu Turab abin ya faskara, itadai ba dama ta shiga bangarensa dan ya bada umarnin hana kowa shiga bayan Mahaifiyarsa, sannan ko a waje tadaina ganinsa. Mairo ma wannan labarin ya d”aga mata hankali, sai dai ba yanda zatai dan dama ta riga tasan komai. Yau ta gama aikin gida kenan tana “yan kukuninta na takaicin abinda ake sata yi, wani yaro ne yazo ya sanar da ita ana san ganinta a waje. Hijab dinta ta ja ta saka dan bata kawo saurayi bane ko wani na kunya ba. Mamaki ya kamata kwarai ganin Abdulmajid a tsaye a jikin soron gidansu. Kallansa tai cikin mamaki sannan ta karasa gunsa tace ” Malam lafiya?” Abdulmajid ya kallesta kalleta yace” Mairo ina kika shiga ne? Sam na daina ganinki dole kika sani na zaro jiki na fito.” Kallan sa tai tace ” ban fahimci inda ka dosa ba.” Yace ” Kin manta me nacemiki ne? Na dauka na sanar dake kedin matata ce.” Dariya ta saki tace ” Matarka? A yaushe kenan akai hakan? A iya tunanina ban amshi sadakin ka ba.” Idanu yadan rage yace ” An kusa ai indai wannan ne, inkuma kinaso in baki yanzu to.” Ka bani yanzu? Da alama tunanin ka ya fara tafiya ko? Matsowa yai a zuciye hakan yasa ta matsa da sauri sannan ta nunashi da hannu tace ” Stop Malam! Tsaya anan karka kuskura ka tabani.” Kallanta yai rai a bace yace ” Mairo.” Tace ” kwarai kuwa sunana Maryam wacce ake cewa Mairo yar gidan Barde kanada magana ne?” Kwafa yai sannan yai murmushin mugunta yace ” ina tausaya miki yarinya randa kika zo hannu.” Baki ta murguda tace kafa zanzo ba hannu ba. Ta juya tai ciki ranta a bace.1 Murmushi ya sakeyi sannan ya juya. Wata yarinyace wacce bata wuce shekara goma sha hudu ba ta, kana ganinta kasan yarinyace da take aiki a gidan duba da yanayin kayan jikinta. kwankwasa kofar tai mai kula da kofarsa ya bude tare da tambayar ta me ya kawo ta. Yarinyar mai sanyi ce kana ganinta kuma kaga shiru shiru, kanta a sunkuye tace ” Yarima Turab ne ya umarceni da inzo.” Yace ” to, shiga.” Nan ta wuce ta shiga, yanata mamakin abinda ya kawota da magrib din nan.+ Ka idar rayuwar Abu Turab in yai sallar Magrib to sai yayi Isha”i yake tashi, sannan kwanan nan saboda bayasan haduwa da kowa yasa ko masallaci ma ba zuwa yake ba, sai dai yai sallah a gida yai tilawarsa.1 Yarinyar nan tana shiga ta zauna a cikin falon da ba kowa sai shi dake zaune daga can gefe kan sallaya yana karatu. Falon ba wani haske gareshi ba, in ba gabansa dake d”auke da fitila kusa da al_qur”anin sa ba, ya kashe fitilun ne saboda kar a fahimci idanunsa yana gani, sannan karatun ma bada karfi yake yi ba. Yarinyar tana zaune a bakin kofa har sai dataji kiraye kirayen sallar isha”i sannan ta mike ta fito, sam Abu Turab bai ma san da zuwanta ba, balle fitarta. Haka yarinyarnan ta d”au kwana hud”u tana wannan zuwan, kullum kuwa ana magrib take zuwa. Mai gadi kofar kam kullum yana mamakin wannan abu, sai dai bashida ta cewa dan da Abu Turab bai yarda da zuwanta ba tabbas da ya haneshi da barinta ta shigo sannan da ita kanta ya koro ta. Yau ne kwanan ta na hud”u da fara zuwan, kamar yanda tasaba zama a kofar yau ma haka tai, sai dataga an dade da sallar magrib sai ta tsiri rage kayayyakin jikinta. Ta rage daga ita sai wata yar bes sai zanin dake jikinta, kara ta saka tare da fad”uwa kasa. Abu Turab dake karatu ya mike da sauri tare da tahowa inda yaji karar, ganin mace yai a kwance tanamurkususu sam bai kula da jikinta ba ganin yanayin da take ciki, da sauri ya karaso ya d”agota yana tambayarta abinda ke damunta, juyi kawai take tana wash wash. Masu kula da bangarensa kuwa suna zaune suna hira sukaji wannan karar nan suka taso da sauri. Shigowa sukai ganin duhu yasa Garzali ya kuna fitila dan sun dauka wata matsalarce ta faru jin yanda Abu Turab ke cewa lafiya? Ita kuma tana kiran wash. Haske ne ya bayyana a d”akin me zasu gani? Abu Turab ne rike da yarinya, gashi cikin duhun nan yarinyar tai amfani da damar ta ballemai botira guda biyu na saman rigarsa. Gaba d”aya turus suka tsaya cikin tashin hankali me zasu gani? Meke faruwa? Abu Turab ne ya kallesu sannan ya kalli yarinyar dan sai a lokacin ya kare mata kallo. Sai kuma a lokacin ya fahimci sharri ne akazo a kula mai. Mikewa yai tare da hankad”e yarinyar, ita kuma ta hade kafafuwanta tasa kanta a ciki tasa wani irin kuka. Zaiyi magana sukaga an bud”o kofa. Abdulmajid ne, gefensa kuma Galadima. Kallan sa Galadima ya shiga yi cikin mamaki da tsana yace ” ashe dama abinda ake fadamin da gaske ne? Lalai ka zubar da mutuncin masarautarmu.” Abu Turab ya kalli Abdulmajid wanda yad”an juya yana dan murmushin mugunta. Galadima ne yacigaba da cewa ” Yanzu Ka kyautama mahaifinka da mahaifiyarka? Kana makaho? Ace har da neman mata? Wa”iyazubillah, dolene gobe a zauna saboda kai, ko kuma yanzu ka wuce muje gun Mai Martaba tun kafin magana ta fita.” STORY CONTINUES BELOW Abu Turab ya jujuya sannan yace ” Galadima?” Inajinka. Abu Turab yace ” ina neman alfarma.” Tame kenan? “Inaso ka taimaka muje gun Mai Martaba a wannan lokacin, sannan mu tafi da yarinyarnan, a kuma taimaka a kira mahaifiyata da kuma Umma Magajiya dan su zama shaidar abinda zai faru.” Galadima yace ” dama ai canzamu yanzu, ya kalli Garzali yace ” jeka kira Magajiya da Mamansa.” Nan yai waje. Galadima yace ” muje.” Haka suka isa gun Mai Martaba lokacin yana zaune bayan ya dawo daga masallaci. Bayan Zagi ya nemarmusu uzuri sun shiga. Mai Martaba ya kalli galadima yace ” Galadima lafiya?” Kallan Abu Turab yai sannan yace ” ba lafiya ba sai dai muna jiran isowar shaidu kafin a fara shari”a.” Sun dan dade a zaune kafin Basira ta fara isowa sannan Magajiya wacce hankalinta kwance ta iso dan dama jiran kiran take in kuma ba”a kirata ba tana jiran labarin korar Abu Turab ko kuma killaceshi da hanashi fita daga bangarensa, a kuma hana kowa ganinsa. Bayan kowa ya hallara Galadima ya sanar da duk abinda ya faru ga Mai Martaba. Tashin hankali ne karara ya bayyana a fuskar Basira. Magajiya ta kalli Galadima tace ” Galadima me kake san kafad”a? Kana tunanin Abu Turab keta mata hadi yai ko me? Na san halin Turab bazai yiwu ba abinda ka fada sannan ta ina ma zai fara yin lalata bayan idanunsa ba gani suke ba?” Abu Turab ya saki wani murmushi yace ” Haka ne Umma Babba ba gani nake ba tayaya zan kama yarinya ta karfi in keta mata hadi?” Abdulmajid ya kalleshi yace ” bayan kamaka da mukai?” Abu Turab yace ” ina yarinyar?” Nan Galadima ya kirata. A jikin bango ta takure kana ganinta a ido kaga salaha. Abu Turab yace ” ba gani nake ba sai dai ina fatan yarinyar tana nan?” Sarki yace ” tananan me zaka ce mata? ” Abu Turab yai kasa dakai yace ” Tuba nake ranka ya dade sai dai ina bukatar yi mata tambayoyi.” Nan Sarki ya bashi dama. Abu Turab yace ” baiwar Allah ya sunan ki?” Tace ” Zulaika.” Yace ” Zulaika kin san ni?” “Eh yarima Turab sunanka.” ” Me yake kawoki bangarena?” Kuka ta saka tace “kaine ka ce indinga zuwa duk bayan magrib.” Abu Turab yace ” gaskiya ne, amma a ina muka hadu na fada miki haka?” Tace ” a waje ranar ka fito.” Allah sarki me nake miki in kinzo? Kuka ta saka hakan yasa Sarki yace ” karki damu sanar dani duk abinda yake miki. Tana kuka tace ” tatabani yakeyi ya cire min…. .”kuka ne yaci karfinta hakan yasa tai shiru. Abu Turab yace “Galadima a ina kaga yarinyar nan da ni?” Galadima yace ” a falon ka mana.” Abu Turab yace ” waya taba neman mata na lalata a sarari? To ko mata tace ya kamata a ganni da ita a falo?” Galadima yai shiru, Sarki ya katseshi da cewa ” in idanun ka ya rufe da alfasha fa?” Kai ya jinjina yace ” haka ne sai dai inada tambaya ga yarinyar, ni ba gani nake ba wanda kowa yasan da haka, ta ina zan iya janyota? Ko ince ta ina zan iya mata karfi?” Sarki ya kalli yarinyar yace ” bashi amsa.” Tana kuka tace ” kirana yake yi.” Abu Turab ya ce ” Umma babba yi mana shari”a aa nan an ganmu a farko farko gaba da kofa kadan sannan tace kiranta nakeyi me zakice?” Magajiya wacce tunda ya fara tambayoyinan ranta yake a b”ace tsananin mamakin rainin hankalin dayake musu yasa tama kasa magana, makaho? Wanda kowa yasan da hakan? Kallansa tai jin tambayar daya mata tace ” gaskiya ne wannan abin dubawa ne galadima.” Abu Turab yace ” Umma babba dan Allah inada tambaya, in har yarinyar nan ta karfi nake mata me yasa ba”a taba jin kararta ba sai yau?” Magajiya ta kalleshi zuciyarta fal bakin ciki amma a fili tai murmushi tace ” Gaskiya ne Turab wannan ma abin dubawa ne.” A ransa yace “Hajiyar Poker Face.” Abu Turab yace “Galadima in har lalata nake da yarinyar nan ta yaya za”a ganta a nuste ina nufin kayanta da kuma d”an kwalinta, banda rigarta data cire, inasan in tambayeta wani irin lalata ne wannan.” Galadima ya kalli yarinyar yace ” ke dan kwal uba……..sanar damu gaskiya ko kuma wlh daga nan sai dai ki sameki a gidan horo.” Idanunta ta zaro a rikice, Abu Turab yace ” ke na taba lalata dake? Wannan shine tambayata ta karshe dake in baki fadamin gaskiya ba……” Sarki ya karasa ” ni kadai nasan hukuncin da zan mata.” Da sauri ta zube a kasa tace ” tuba nake ranka ya dade.” “Tuba? Name kenan?” Magajiya ta saki wani lalausan murmushi tace ” yaro yaci galaba a dokan farko, bari muga na biyu.” Dan tasan ko za”a kashe yarinyar nan batasan wanene ya umarceta da wannan aikin ba, kudi da kaya aka kaimata sai umarnin aikin dazatai da wata ta fada mata, wacce ta fada mata kuwa bama a gidan take ba. Kuka take sosai yarinyar tana neman gafara. Abu Turab ya kalli Magajiya yace ” Umma Babba na gode da aminta dani da kikai.” Daga nan aka wuce da yarinyar dan mata hukunci da tambayoyi akan laifin data aikata. Abu Turab suna fita ya karasa da saurin gun Magajiya wacce take tafe Abdulmajid na bayanta. Yana isa ya sha gaban ta yace “Umma ina kara godiya fa.” Kallansa tai tace ” karka damu d”ana ina laifi in uwa ta taimaki d”anta?” Ya kalli Abdulmajid yace ” ba dai anyimin wannan wasan kwaikwayon bane dan labari yakai masarautar kano?” Abdulmajid ya makamai harara yace ” Wa kake tambaya?” Abu Turab yace ” ba tambaya nake ba, shawara dai nazo badawa, in har za”a hanani auren Gimbiya Bilkisu ko kuma a sani in nemi gafara da gwiwowina bana tunanin wannan wasan yaran zaici galaba a kaina maganar gaskiya na fahimci ashe Babbar tamu ba iya babban game tai ba.” Yana kainan yai gaba. Magajiya ta kalleshi tai dariya tace ” Abu Turab! Nayi laifin farawa da mafi kankanta daga cikin shiri na.” Abdulmajid ya kalleta yace ” Umma kefa yake nufi ko?” Tace ” kwarai zamu gani ai.” Jakadiya dake tsaye tana kallan abinda akeyi ta sheke da dariya tace ” Magajiya kin hadu da daidai ke, na kosa inga idanunki a lokacin da yaran nan ya fahimci shi kadai ne jinin sarauta Abdulmajid ba d”an Sarki bane.” Takara sa dariya sannan ta juya cikin farin cikin ganin an wulakanta Magajiya.+ Magajiya na shiga d”aki ta rufo kofar sannan ta zauna tare da kurama kasa ido, ranta yau inyayi dubu ya b”aci. Abdulmajid kuwa bangaren Abu Turab ya nufa, daidai lokacin shima yana kokarim shiga cikin nasa gidan. Turab. Abinda Abdulmajid ya fada kenan. Abu Turab ya tsaya sannan ya juyo ya kalleshi, matsowa yai inda yake yace ” Kana tunanin kaci riba ko?” Abu Turab yace ” a wasan yara ba.” Abdulmajid ya matso daf dashi sosai yace ” Karkai tunanin kaci riba, karkuma kai tunanin nidin soko ne, ba damuwa nai da auranka da Bilkisu ba,dan ni Mairo nakeso kuma zan aura, mulki kuma wallahi kaji na rantsema baka isa kahau kujerata ba in har kuwa kaga ka hau to wlh sai dai in mutuwa nai.” Abu Turab ya saki wani murmushi har hakoransa suka fito yace ” Malam Yarima, ita d”in Mairon sanka take?” “So? Wannan kuma ai kai kasanshi, in dai harni ina santa?” Abu Turab yamai wani kalo shekeke yace ” Indai har kana santa? Me kake tunani?” “Me kuwa nake tuna? Nine magajin sarki auranta kuma dole ne a garine.”1 Mamaki ya kama Abu Turab yace ” banda neman matan da kakeyi, bayin gidan nan, haka kakeso ta kunshi bakin cikinka?” Yace ” Neman mata ai iyawa ne sannan bakin ciki kuma wannan damuwarta ne in har ina zaune da ita ni ba ruwana, gargadi na a gareka karka kuskura kai tunanin shiga tsakanina da yarinyar nan.” Juyawa yai zai tafi, da sauri Abu Turab yasa hannu ya fizgo hannun Abdulmajid sannan yace mai ” in kuma na aureta fa?” Wani irin mugun kallo Abdulmajid ya bugamai, kishi ne karara ya bayyana a idanunsa, Abu Turab yace ” ni ina mamaki, na d”auka ma Khadija zakace kanaso ganin kunfi kusanci da ita sann……” Dunkule hannunsa yai ya naushi kuncin Abu Turab wanda baiyi zato ba, hakan yasa bai karasa maganarsa ba.1 Abu Turab sai daya kusa kaiwa kasa, gefen lebensa ne a fashe kadan, Abu Turab ya kalleshi zaiyi magana, Abdulmajid ya nunashi da yatsa yace ” Gargadi zan maka, wlh kar insake ji kace zaka auri Mairo ta wannan shine kashedi na na karshe dakai.”1 Ya juya a fusace yai gaba, Abu Turab ya kalleshi sannan yace ” ayya Malam kace Mairo ce weakness dinka.” Juyawa yai ya dan furzar da iska. Basira kam sosai hankalinta ya kwanta ba shakka ta samu d”a, tana kuma kara godema Allah da kuma rokonshi ya kare mata shi. ************* Washegari na sassafe ya nufi bangaren mahaifinsa bayan ya gaisheshi ne ya d”ago yace ” Abba zuwa nai nuyi wata magana. ” Sarki ya kalleshi yace “Ina jinka.” “Me zai hana a kaini asibiti a matsayin an kaini amin aikin ido inyaso ko zuwa sati d”aya inyaso sai ace na warke.” Sarki ya jinjina kai yace ” hakan yayi, ko dan saboda maganarka da Gimbiya Bilkisu dole ne mutane su gane kana gani, to gwara kafin abu yai nisa a fahimci kana gani, ko dan ka kwaci kanka.” Abu Turab ya kalleshi sannan ya sunkuyar da kansa yace ” Tuba nake nasan jiya…..” Kayi daidai Abu Turab, naji dadi abinda kai, hakan ya nunamin ko a wani hali kake zaka kqaci kanka, yanzu yaushe zaka tafi asibitin?” Abu Turab yace ” yau ko gobe, dan gwara mu hanzarta kafin a samu matsala.” “Ka yi tunani, a asibitin Ahmadu Bello akwai wani tsohon abokina na sirri director ne a asibitin in ka sanar dashi komai zai san abinda ya dace.” Abu Turab yace ” nagode Abba.” Sun dade a zaune shiru kafin Abu Turab yace “Nasan ban kyauta ba abinda nai jiya, kamar rainuwa ce nama Umma Magajiya, nasan zakai tunanin haka.” Sarki yai murmushi yace ” ko kadan Abu Turab, nasan Magajiya sosai da sosai nasan kuma sharrin ta da izzar ta, sai dai fatana ka kula da kanka kar su maka illa, ni nasan abinda nakeyi, bawai banasan Abdulmajid bane ko ina fifitaka akanshi sai dai dolene in kare masarautata da garina, inhar Abdulmajid yahau mulki tabbas mulki ya koma gun Magajiya da Hisham da ahalinsu.”2 Abu Turab yace ” nifa…..” Basai ka ce komai ba, na sani na kuma fahimci me zakace, bawai san mulki kake ba, sai dai nasan akwai lokaci da zakaso mulkin, shiyasa nake rokonka daka bar komai a ranka harzuwa lokacin.” Haka ya taso ya fito, Jakadiya tana ganinsa ta taho da sauri ta gaisheshi amsawa yai ba tare da ya kalleta ba. Ta bishi da kallo tace ” inama kana gani ai sai kunfi fafatawar da Magajiya, mu kuma “yan kallo mu kwashi namu rabon.” ************* Washegari Basira da Lantana suka rakashi asibiti, nan magana ta fito akan antafi yimasa aiki saboda isowar wani kwararen likitan ido a asibin na Abu. Magajiya kam tayi dariya sosai dajin wannan rainin hankali, sanda akazo mata da maganar kuwa tana zaune Khadija na cire mata jan lalen data mata, mai kula da ita ta shigo da sauri tace “Ranki ya dade yanzu naji labari akan Yarima Turab ya tafi asibiti.” A zabure Khadija ta mike tace ” meya sameshi?bashida lafiya ne?” Kallan mamaki matar ta mata sannan tace ” a”a aikin ido za”amai.” Magajiya ce tasa dariya tace ” aiki? Lalai yaran nan.” Gani tai da gudu Khadija tayi waje. Sauri take sosai daga can gun shiga mota ta hangosu, sauri take sosai sai data kusa isa daf sai ta hango Mairo a gefen wajen boot din motar rike da kula. Turus tai ta tsaya tana kallanta. Gani tai Abu Turab din ya matsa kusa da Mairon batasan me suke cewa ba. Shikuwa gunta ya karasa yace ” Ke kuma waya fadamiki?” Tace ” Umma na mana ko kamanta nidin “yar gidanta ce?” Kai ya jinjina yana murmushi yace ” na d”an manta kadan.” Kula ta nuna mai tace ” gashi kaci inkaje can, Goggo ce tace in kawoma, nasan in mace zan bika hanani zakai.” Kallanta yai yace ” akwai maganar ma danakeso muyu dake, kizo mu tafi tare, in kuma da abinda zakiyi kizo ko zuwa gobe ne.” Kallansa tai cikin mamaki tace ” yaya? Wai da gaske kake?” “Me kika gani?” Zatai magana ta hango Khadija a kusa dasu kad”an ta kura musu ido. Mairo ta kalleshi tace ” yaya anzo gunka.” Juyawa yai ya kalli gun, sannan ya juyo yace ” zamu tafi sai na ganki.” Mota ya bud”e ya shiga. Dama su Basira sun shiga tasu motar. Nan aka jasu shi da Garzali, Basira kuma da Lantana. Yana kallan Khadija ta glass har suka wuce. Ba shakka har zuciyarsa yanajinta, balle yanda yaganta a tsaye tana kallansu ya tabbata taji ba dadi na ganinsu tare. Motarsu na wucewa Khadija ta karaso gun Mairo ta kalleta jiki a sanyaye tace ” wani asibitin zasu?” “Me yasa baki tambayeshi ba?” Khadija ta kalli Mairo tace ” Mairo menene tsakaninki da ya Turab?” Mairo ta kalleta cikin mamaki, ita ya kamata ta mata wannan tambayar, zatai magana taji ta kara cewa ” ko da yake bake ya kamata in tambaya ba.”1 Juyawa tai zata tafi, Mairo ta kalleta tace ” wani abu ya hadaku da Yaya ne?” Khadija ta juyo sai dai batace komai ba. Mairo tacigaba ” Kinaso kicemin bakisan wa yaya yake so ba?” Khadija ta kwakwalo murmushin takaici tace ” na sani yanzu, nasani ni kadai nake bilayi na.” Mairo zata sake magana taga Khadija tayi gaba. Kallan mamaki ta mata tace ” Wai batasan ita yaya yake so ba?” Juyawa tai itama ta fita….

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE