KASAR WAJE CHAPTER 11 BY MARYAM DATTI
KASAR WAJE CHAPTER 11 BY MARYAM DATTI
Koda ya Yusuf ya isa masallaci ga mamakinsa masallacin da mutane da motoci a harabar masallacin da su escorts a hankali ya karasa ya musu sallama Hamzad yace masa ya karasa+
Sosai gaban Yusuf ya fadi kodai wani abu ya faru za a koreshi aiki karasawa yayi ya kara gaishesu ya zauna can gefe
Hamzad ne ya dubi wani kyakyawan dattijon balarabe ya nuna Yusuf yace wannan shine “Yusuf Suleiman shugaban ma’aikatanmu na Masallaci”..
Balaraben yayi murmushi ya kalli Yusuf yace ya taso yazo kusa da shi, Yusuf cikin tsananin gitmamawa ya mik’e ya karasa saidai still bai iya zama daf da shi ba. Kallon Yusuf yayi yace ” muna rabon sadaka ko wani Ramadan domin talalfawa y’an uwanmu musulmai da ke ko wani sako na wannan garin na mu bawai farare kawai ba harda y’an uwanmu da suka fito daga kasashen Africa bamu tab’a yin matashi jagora na wannan masallacin ba sai a kanka shiasa na keso ka jagoranci tafiyar a wannan shekarar
d’an ajiyar zuciya Yusuf yayi bai iya magana ba… Minista yaci gaba za kuyi tafiyar a jibi sannan zaku iya yin sati ko fiye da haka zaku shiga duk wasu k’auyuka su drebobinmu sunsan duk inda aka saba zuwa kai kuma zaka jagoranci rabon…
Shi Yusuf hayfa da supermarket ne fargabarsa yaya zaiyi da su…. Yaji muryar minista ka ansa wannan kaje kafara shirin tafiyar jibi IA..
Jiki babu k’wari Yusuf ya ansa yayi godiya ba tare da ya iya furta komai ba sai godiya tare da mik’ewa yayi musu sallama ya wuce d’akinsa na gadi domin ya shirya
Sunkai 12:38am kafin suka gama har gaban motar minista da escorts d’insa Yusuf ya masa sallama suka fita masallacin kamar ba minista ba cukin sirri duk suka watse sai gamzad shima Yusuf ya masa sallama shima ya wuce ganin dare yayi.
Hayfa ma aiki duk ta gaji ga yunwa amma Armando sai gyaran aiki yake yana qara turo mata sannan ga shi ta nema Yusuf shiru saidai shi Yusuf lokacin da ya shiga nasallaci ganin mutane ya kashe wayar sai yanzu ya kunna ya jefa layinta….
Cikin d’an baccin da ya kwasheta ta d’aga wayar saidai ba tayi magana ba wai tana fushi
Cikin muryarsa mai shiga jikinta ya furta “Sorry baby ina tare da manyana shiasa na kashe waya kin neme ni ko”?
Ajiyar zuciya tayi tace “eh kawai”.. Yace pls 4give me ya gida?
Ajiyar zuciya ta sake yi tace “lafiya yace baby bari na barki ki yi bacci in na dawo za muyi wata magana kinji”?
“Toh” tace yace Love u baby
dukda tana cikin fushi dashi wai duk na kashe wayar da yayi itama ta bashi ansa “love u too”.. Su kayi sallama ya koma aiki ta koma itama ganin wai Armando ya dawo mata da aikin cewa bata fayyace adadin daliban da ake sawa a ko wani class ba a makarantun gomnatin Nigeria
Mugun ciwo kanta ke mata wlh tagaji ita ina zata iya sani itada tayi private school, saidai da sauri ta Tuna mominta wayarta ta d’auka ta jefa layin Ammah
Ammah ana kamfani da ma’aikata kasancewar lokacin rana ne a Nageria sabida Ammah ta ajiye aiki ta maida hankali kan bud’e kamfaninsu da ta k’awatashi sosai Office d’inta kamar falon wani attajiri a matsayinta na CEO
Ganin number Hayfa da sauri ta matsa gefe ta ansa ‘yan matana ya akayi?
Hayfa cikin shagwab’a tace mominmu kuna lafiya? Ammah tace lafiya qalau, ya d’an albarka? Haka take kiran Yusuf hmmm duniya Allah ya kyawta
STORY CONTINUES BELOW
Hayfa tace lafiya! Mominmu pls kamar students nawa kuke sawa a class?
Ammah tanbayar ta bata mamaki tace “mai yasa kike tanbaya”?
Hayfa tayi d’an shiru ta rasa mai zata ce can tace “dama wata k’ungiya ce anan mu ke ciki zamu kawo tallafi Nageria shine aka sani lissafi..
Ammah cikin tsananin farin cukin yadda suka d’aukaka wai yau sune rayiwarsu ta koma haka a k’asa da 2yrs sun zama shaharrarun masu kud’i dukda rashin haihuwar hayfa ya fara damunta domin kuwa gaskiyar Adda suwaiba idan har yanzu da bata haihu suna samun kud’i haka jikin Yusuf to inta haihu ay sai Allah gaskiya gara taje gurin malam akan maganar haihuwar hayfa dole tayi komai domin hayfan ta samu ciki… Muryar hayfa taji mominmu pls fadamin..
Da sauri tace ” tace kamar 22 xuwa talatin ma.. Hayfa tace to mominmu sai da safe suka yi sallama ta koma aiki dukda bacci ta keji sosai kuwa…
Bayan gama wayarsu Ammah ta kira malam cewa tana zuwa yanzu. Koda suka gama da ma’aikatan direct u/dosa ta wuce a motarta cike da fatan samun mafita a gun malam
Koda ta iso suka gaisa tayiwa malam bayanin har yanzu hayfa shiru babu ciki malam yayi bugun k’asa yadda ya saba ya kuma ga gskyr abinda hayfa ta yiwa kanta saidai shi har yau yayi alkawarin bazai tab’a fad’awa ammah gsky rayuwar hayfa da Yusuf idan har ita hayfa bata gaya musu lallai bataso su sani don haka shi bazai b’atawa kansa hanyar zukarsu ba yadda yanzu haka kawai ma ammah saita tura masa kudi tab
Kallon Ammah yayi yace aiki ne zaayi amma gsky saikin kashe kud’i… bayan ta samu ciki Zaki biya 500k ayiwa mutanenmu sadaka, yanzu kuma kibada
Ammah cikin zak’uwa tace ko nawa ne malam zan kashe.. Murmushi yayi yace 300k sabida har saniya zan yanka, ko b’ata lokaci babu ammah ta masa transfer inda malam ya kudirce b’ata d’aurin mahaifar hayfa domin ya k’ara zukar Ammah haka su kayi sallama malam cike da farin ciki domin jini kawai zai sakarwa hayfa a yau yadda bayan sa mahaifarta zata koma daidai sai ciki anytym
Kusan 4:11 ta gama aikin ta turawa Armando da shima a lokacin ya gama had’a komai ya tura saudia ya kwanta itama hayfa ta d’an kwanta kafin shigowar Yusuf
Koda ya iso gida tana kwance gefen system d’inta a hankali ya zauna gefe ya d’aga kanta zuwa cinyarsa dukda shima a gajiyen yake ga bacci saidai bazai iya yi ba sabida yanason zuwa supermarket da wuri yaga manager suyi magana akan tafiyar sa ga hayfa baisan ya zai tunkareta da maganar ba.
Ganin aikin masallacin kansa har yanzu ta kasa sabawa kullum zai tafi sai tashiga damuwa
d’uminsa da k’anshinsa ya sanyata bud’e idanuwanta a hankali idanunta suka fad’a cikin nasa d’an lumshe idanun yayi ya mata murmushi
Shafa fuskarsa tayi a hankali ta d’ago ya mata peck a goshi yace “sorry na tashe ki ko”?
Shiru tayi tana kallon yadda idanunsa sunyi k’anana sun d’anyi ja tsabar rashin bacci da Hutu
Hawaye taji suna sauka mata a hankali ta furta “pls ka d’an d’auki hutu a azumi in kula da kai kaji”?
Murmushi yayi shima ya shafa fuskarta yace “baby wani hutu munada buk’atar kud’i kafin mu rayuwa mai mutunci”..
Ajiyar zuciya tayi kamar tace masa inada kud’in da zamu iya yin rayuwa mai d’an sauqi amma ta yaya zata iya fad’a masa ita d’in “Model ce” yadda Ya keda kishi
Kwantar da kanta tayi k’irjinsa tace “pls ka gwada neman hutun koda kafin sallah mu k’ara azumi a gida kaji”?
IA yace! baby tashi muyi magana tafiya ce ta kamani gobe IA
Mugun fad’uwa kirjinta yayi tace zuwa ina? Nan ya mata bayani tanata hawaye
Yace kinga kina iya zuwa gun Clara har na dawo sabida ta d’ebe miki kewa kinji?
STORY CONTINUES BELOW
Hawaye kawai take yana lallashi. kusan 10mnts yana lalashinta kafin da k’yar ta tsaida hawayen saidai still idanunta cike su ke da k’wallan ya rik’o hannunta ya saka mata envelope…
Kallonsa tayi a hankali da alamar tanbaya.. d’an ajiyar zuciya yayi yace an bani ne wai na shirin tafiya ki tsara yadda za muyi da su..
wani irin kallonsa take tanajin kamar ta shigar da kanta jikinsa a hankali ya shafa fuskarta yace “Baby bari nayi wanka muyi sallah lokaci ya tafi” rik’o hannunsa tayi tace ka bari to mu tsara kafin ka wuce aiki..! Murmushi yayi ya dawo ya shafa fuskarta yace “baby kiyi yadda kike ganin ya kamata kinji”?
Kallonsa take tana mamakin yadda kwatakwata baya damuwa da komai hatta da kudin da yake nema da kansa…
Peck ya mata ya shige bayin ya barta zaune a dole ta ajiye envelope d’in itama ta mik’e taje had’a masa brk kan ya fito suyi sallah, kwai ta soya musu da brd da waken gongoni tana gamawa ta ganshi ya fito yace “kije kiyi alwala” fitowa tayi kantar ta wuce tana wucewa yasir ya iso shima bayan ta fito sanye da dogon hijabin sallarta suka tayar yasir yayi liman suka yi sallah suka karya suka fito duka saida suka hau train ta dawo gida cike da tunani itama dama saura 4dys tafiyarsu ga Yusuf to ya za tayi bari ta kira Armando..
Tana shiga gida ta jefa layinsa yanata ringing kafin ya ansa “yace Queen ya har kin tashi”? Gaisheshi tayi tace “eh”!
Tace wai da gaske nan da 4dys za muyi tafiyar? Dariya yayi yace eh mana queen.. Akwai matsala ne? Ah ah tace ta masa bayanin tafiyar Yusuf
Ajiyar zuciya yayi yace da kyaw kinga mun huta da yi masa k’arya ba.. “Tace kamar yaya”?
Yace za muyi tafiyarmu sabida mu ma 5dys kawai za muyi sannan in mu kaje sai ki saya sim da zai b’oye no da komai yadda bazai san a ina kike ba ko kuna waya har mu dawo ke zan maida tafiyarmu ma ranar da shima zaiyi tasa hankalinki ya kwanta..? A hankali tace eh tana sakin hawaye sosai Yusuf take jinsa yanzu kamar rayiwarta sam bata jin dad’in yaudararnan da take masa… Muryar Armando ta jiyo mu had’u yau da 3 muyi shopping na tafiya..
Toh tace su kayi sallama ta aje wayar tanata hawaye sai lokacin ta d’auko envelope d’in Yusuf ta bud’e $3000 ne a hankali tayi ajiyar zuciya kaya za ta siyo masa da kud’insa..
A train Yusuf ya ke bawa Yasir labarin tafiyarsa sosai yasir yayi murna da yi masa fatan alkairi har suka sauka kowa ya kama hanyarsa ta aiki.
Malam ya gama bugun k’asa ya k’ara tabbatar da abinda ya saba gani a duk sanda su Ammah suka sashi bincike akan hayfa da Yusuf saidai shi ya gano dayawan abubuwa da bai fad’a musu gudun yanke alak’arsa da su sanann a wani b’angare sosai yake mamaki akan wani boyayyen al’amari da ya gano akan Yusuf d’in da hayfa wanda ya gano su Kansu Yusuf da hayfa basu san hakan ba
Ajiyar zuciya yayi kafin ya fara aikinsa cikin k’warewa a shed’anci ya gama aikin tas yana mutmushi domin tabbas shi zai fara sani idan cikin ya shiga ya sanarwa Ammah yadda zai k’ara buk’atar wasu mak’uddai a gunta..
Koda Yusuf ya isa Supermarket Manager bai iso ba nan ya fara aiki sai wajajen 9:25am manager ya Iso inda Yusuf ya nufi office d’insa cike da fargabar yadda zasu k’are
Bayan ya k’wankwansa manager ya masa izilnin shiga
Bayan sun gaisa Yusuf ya masa bayani cewa ya samu uzuri ne na family zaiyi tafiyar 8dys
Kallonsa manager yayi babu walwala sosai yace “yanzu ya kake so a yi”?
Yusuf ya k’ara rusunawa cikin girmamawa yace “idan ma za a cire a kud’ina na amince amma inaso a taimakamin tafiyar tanada matuk’ar muhimmanci “…
Ajiyar zuciya baturen yayi yace gaskiya saidai in zaka kawo wanda zai karb’ar maka har ka dawo in ba haka ba saidai na sallameka gaba d’aya in ka dawo tafiyar ka nema wani aikin
da sauri Yusuf yace ah ah zan nemo wanda zai karb’a..!.
Manager yace “ok” sai ka kawo shi su kayi sallama Yusuf ya fito cike da tunanin wa zai saka alhalin yasir busy pool da club
da sauri ya tuna yasir yace masa Albert na club ya bar club shima wai yana karatu online wayarsa ya d’auka ya kira yasir
Yasir yace ya akayi “Dude”?
Yusuf yace kace Albert ya bar aiki tiffun ke aikinsa yanzu?
Yasir yace eh kasan yana online classes ne kuma wai da dare suke 8 to 10pm
Yusuf yace ya samu aikin rana ne? Yasit yace No yana nema dai tukuna….
Yusuf yace turomin number d’insa yanzu pls
Yasir bai iya tanbayar Yusuf ba lura da yayi Yusuf d’in kamar a gaggauce yake.. Yace OK bari na turo maka su kayi sallama…
Ko 3mnts basuyi da sallama text ya shigo Yusuf ya kwashe ya jefa kiran
Albert ganin number ya ansa…
Yusuf ya gaisheshi…
Albert cike da mamaki sanin Yusuf sam baida son mutane kamar yasir ko mai ya faru Yusuf d’in yau ya kirashi
Yusuf ya masa bayanin buk’atarsa da cewa zai bashi ma complete kud’in watan amma ya kama masa aikin na 10dys
da sauri Albert ya amince nan suka yi sallma akan sai 4:pm Albert zaije Yusuf ya gabatar dashi sannan gobe ya fara aikin..
Saida hayfa tayi azhar sannan ta d’auko na ta envelope na interview ta jefa jaka dana Yusuf ta fito taxi ta hau zuwa kamfani inda zasu shiga gari da Armando..
Tana isa company Armando ya fito suka shiga mota driver ya tayar inda suka je wani babban mall
B’angaren kaya ta wuce na maza inda armando ya wuce b’angaren kayan yara zai fara order kayan da zasuyi rabo a kauyukan da zasu..
Kaya designed na pencil jeans na maza masu kyaw da tsada kala goma ta d’ibarwa Yusuf sai takalma loafers kala goma suma sai riguna polo kala sha biyar da shirts biyar, Sai t.shirt masu kyaw suma biyar da ke tasan yanada wanduna babu laifi kusan goma a gida ta saya masa manyan perfume da lotion na kamfanin Nivea ta gama aka had’a mata lissafin $37000 haka ta biya aka kai kayan mota kafin ta koma b’angaren Armando inda shima yayi kaya kwali 10 domin an turo da kudin sayayyar da na tickets d’insu nan ya kalleta cikin tsokana yace
Wai duk wannan dad’ewar a b’angaren kayan maza kike…? d’an kunya taji dukda zuwa yanzu ta fara sabawa da tsokanar da ya kanyi mata akan Yusuf..+
Kallonta yayi jin tayi shiru yace ni fa tunda naji ki shiru na zab’i kaya da kaina iya abinda zan iya kin gama kema mu wuce..?
Eh tace suka fito suna ci gaba da tattaunawa inda yake tanvayarta wane tym su Yusuf zasu wuce..? Tace kamar 6:am gobe
Yace OK mu zan yankar mana ticket d’in yamma, “toh” tace suka ci gaba da fitowa saida suka shiga mota driver ya kawo hayfa ta d’an kalleshi tace “Ni zan sauka ne a gidanmu”…
Dariya ya d’an saki yace OK queen ni zan sauka a hotel amma dai kada kije kina shagala gida ki manta abinda ya kawo mu.. Dariya tayi itama kafin tace
Ah ah ba zanyi haka ba..
Yace gud ba’a hada aiki da komai kullum abinda na ke so ki gane kenan sai ki samu nasara mai ban mamaki a rayuwarki ki maida hankali kina aiki tukuru
Ita hayfa dai shiru domin ta rigada ta saba kullum maganar Armando kenan “aiki tukuru”..
Saida suka tsaya kamfani suka k’ara y’an ayyukansu wajejen 5:pm ta fito kamfanin inda tama ki driver ya maidata sanin zasu iya haduwa da Yusuf tana cikin taxi msg d’insa ya shigo..
Hi Baby
Pls tuwo na ke so miyar kuka hop gimbiyata za tamin..? Nagode
Murmushi tayi ba zata masa reply ba sabida yau tanaso suyi dare na musamman na bankwanar Tafiyarsu duka..
Saidai tun kan ta iso gida wani mummunan ciwon mara mai had’e da zazzafa ciwon kai ya Kawo mata farmaki kamar wasa ta fara wani irin numfashi sama-sama a taxi inda shima mai taxi ya d’an tsorata yana tanbayarta ta ma kasa amsa masa har suka kawo k’ofar gidanta da k’yar ta iya fitowa taxi d’in domin mai taxin yaso rik’eta ya taimaka mata ta k’i a dole ya k’yaleta ya kwaso kayanta ya shigar mata har falonta ta sallameshi ya wuce nan ta zube falon wani jiri da taji mai k’arfi ko k’ofar bata rufe ba
Numfashi take fitarwa sosai cikinta na wani irin azababen murd’awa na fitina nan ta fara kuka sosai tana murk’ususu tsakar falon..
Yusuf da suka gama magana da manager da Albert akan gobe ma Albert zai fara sabida yau zaiyi shirin tafiya ya kamo hanyar gida bayan sunyi waya da yasir wai sai after Ishaa zai k’araso ya tsaya ana party a pool zaici bulus
Yusuf na taxi ma Hamzad ya kirashi cewa ya kwana yau gida yayi shiri da kyaw sai ya fito 6:am zuwa masallaci abokan tafiyar na jiransa da motoci sosai Yusuf yayi farin ciki at least za suyi kyakykyawan sallama da gimbiyarsa cike da murna ya iso gida
Sai dai tun kan ya fita taxi hankalinsa ya tashi ganin k’ofar a bude da sauri ya sallami mai taxi ya fito hankalinsa ya gama tashi
Ganin hayfa a sume ga jini da take kwance da sauri ya k’arasa ya rik’ota yana jijjigata yana kiran sunanta ya ma rasa mai zaiyi sai kawai ya ciccib’eta a haka ya nufi waje ya jawo k’ofar yayi sa’a ga wani taxi ya tsaida ya bud’e baya ya kwantar da ita ya shiga ya d’aga kanta ya d’ora cinyarsa yacewa mai taxi ya kaisu asibiti ko inane
Ba b’ata lokaci a k’arshen layinsu ma ya ajiyesu wani private clinic inda aka shiga da hayfa cikin gaggawa Yusuf ya zauna bencin hankalinsa duk ya gama tashi
STORY CONTINUES BELOW
Kusan 50mnts Dr ya fito yace Yusuf ya biyoshi office ya mik’e suka je inda Dr yayiwa Yusuf bayanin kamar hayfa wai tayi miscarriage ne na d’an k’aramin ciki wanda kuma ba haka bane shi kansa bai gane dalilin b’allewan jinin bane shiasa yace haka domin koda suka shiga da ita jinin da kansa ya tsaya inda suka mata wankin ciki suka kaita d’akin Hutu. Ajiyar zuciya Yusuf yayi yace “yanzu yaushe zamu koma gida”..? Dr yayi mutmushi yace ko yanzu ta farka zaku iya tafiya ay ga magunguna da zata rik’a sha yanzu babu wani damuwa kuma
Yusuf yayiwa Dr godiya ya fito ya nufi d’akin da Dr yace Ankai hayfa tana kwnce da harta d’an fad’a zama yayi kusa da fuskarta yana kallonta duk tausayi ta bashi ya shafa fuskarta tare da rik’o hannunta yayi kissing na farin cikin ta fara cire masa damuwar shirun da ya damu na rashin samun cikinta dukda bai tab’a nuna mata ba
Tunani yayi yanzu ma bazai bari tasan miscarriage tayi ba kada hakan ya sanyata cikin damuwa gashi shi yafiya zaiyi bare yayi ta lallashinta
d’an bacci ne ya kamashi sai a sannan ya tuna da yasir ya kira shi ya fad’a masa amma yace kada ya zo ma suma zasu dawo da ta farka
Yasir yace pls ka kula da ita da kyaw
Yusuf yace IA..Nagode sosai
Suka yi sallama shi yasir dama tuni yana club da tsammanin shima Yusuf yana masallaci shiasa bai kirashi ba
12:28am Hayfa ta farka Yusuf dama idanunsa biyu shafa fuskarta yayi yace “sorry baby” ya jikin?
Mirmushi tayi tace lafiya sosai mu koma gida..
d’an murmushi yayi yace kin tabbata bakyajin komai..? Eh tace tana kallonsa danna wata kararrawa yayi nurse tazo ta k’ara duba hayfa da kyaw ta basu magingunansu da recit domin Yusuf bai biya ba tace masa ya dawo 7:am ya biya a reception domin akwai address d’in gidansu Yusuf da na supermarket komai a jiki so yace zai biya ta accnt supermarket..
Karb’a yayi yayi mata godiya ta fita ya rik’o hayfa ta sakko gado ya taimaka mata ta cire rigar asibitin ta maida rigarta ya rik’ota suka fito inda suka samu taxi suka wuce gida
Koda suka iso sai lokacin Yusuf ya lura da tulin jakunkunan shopping na kamfanin Dolce gabana kusan hud’u
Wucewa suka yi ya shiga kanta ya d’ora mata ruwa ya zaunar da ita bayan ruwan yayi ya Kai mata bayi ya had’a yazo ya rik’ota suka je da kansa ya mata wanka ya had’a mata wani a k’aramin bucket tayi tsarki sosai taji ta warke ta fito tuni ya had’a mata coffee da d’umamen macaroni kallonsa kawai take
Y’ar rigar sanyi tasa iya gwiwa da hula sai suck tayi kyaw sosai ya zaunar da ita jikinsa ya fara bata abincin taci ta k’oshi tasha coffee ta gama ya dawo yana kallonta yace “baby ya za muyi? 6: zan wuce.. d’an ajiyar zuciya tayi tace “zan wuce gun Clara kamar 10:am
Ajiyar zuciya yayi yace pls ki kulamin da kanki sosai kinji? Girgiza kai tayi ya mata peck a goshi ya mik’e yace bari na fara shirya kayana kada nayi latti
A hankali ta mik’e itama tace ni zan shirya maka.. Yace baby ke da bakida lafiya..? B’ata fiska tayi tace na warke fa
OK yace ta fito falo ya kwaso jakunkunan ta d’auko akwatin laifenta d’aya ta juye kayanta kan gado ta zazzage kayan jakunkunan zata fara shiryawa a kwatin taji muryarsa.. Daga ina wannan kayan..?
d’an d’agowa tayi taga babu alamar walwala a fuskarsa ta d’an tsorata amma ta dake tace “nayi shopping ne da kud’in da aka baka duka”..
Kallonta yake sosai da alamar tanbaya kamar bai yadda ba ganin yawan kayan da kuma ganinsu masu tsada ne designed duka barin takalman
K’ara tsorata tayi amma ta k’ara dakewa tace dama akwai kudin café da nake tarawa duka sai na had’a amma bashi na baka duk sanda ka samu kud’i sai ka biyani
Dariya ce ta kub’uce masa domin tsaf ya gano rigakafi tayi masa kada yayi mata fad’a.. A hankali ya rik’ota ya mannata da k’irjinsa ya nutsar da idanunsa cikin na ta yace “baby na saki aiki ne domin buk’atunki da na y’an uwanki idan ya tashi ba don buk’atuna ba kinji”? Bata ce k’ala ba yaci gaba pls ki daina in bakyaso nayi fushi da ke..
Hawayen shagwab’a ta saki tace shikenan to zan daina aikin in bakaso ina taimakawa kaina… da sauri yace pls ba haka nake nufi ay sabida ki taimakawa kanki na saki aikin ya zaki ce banaso..? Cikin shagwab’a tace ay taimaka maka shine taimakawa kaina..!
Wani irin jinta Yusuf yayi da baisan sanda ya rungumeta ba har k’wallah ya saki bai bari ta gani ba bai tab’a tuna zata zo ta sakko haka ba amma duk da haka zai dage yana neman nasa kuma IA zai maida mata kud’inta kada tana k’arar da d’an nata a kansa
d’agota yayi yana kallonta ya furta “Allah yayi miki albarka”
Amin tace suka k’arasa gyaran kayan tare ganin kusan 3:11am lokacin suka kwanta da saka alarm 5:30 sosai suke manne da juna nan da nan bacci ya d’auke su.
5:30 alarm ya kad’a da k’yar suka farka duka inda hayfa jininta na fita kad’an-kad’an Yusuf ya shiga wanka da sauri-sauri ya fito yayi sallah ya shirya cikin d’aya daga cikin kayan da hayfa ta siyo pencil jeans da polo dark blue yasa bak’in takalmi yasa agogonsa wani irin mugun had’uwa yayi kamar wani half cast suka fito falo suka karya suna jiran yasir ya iso suyi sallama shi zai raka Yusuf har masallaci kafin ya wuce pool
Suna falo 5:46 yasir ya iso ko zama baiyi ba ya d’auki take away da hayfa ta masa ya fita Yusuf ya k’ara janyota jikinsa yana kallonta tuni tafara hawaye a hankali yasa hannunsa yana share mata ya fara kissing d’inta sosai ta rik’eshi kusan 5mnts suna manne suna tsotsar juna kamar kada su rabu kafin da k’yar suka saki juna ko wannensu har ya fara fita hayyacinsa
Hannunta ya rik’o yayi kissing yana lumshe idanunsa itama haka kafin ya d’ago ya mata peck a goshi ya wuce kawai bai k’ara juyowa ba yana fitowa suka shige taxi suka wuce hayfa na tsaye inda ya barta tanata hawaye
Suna isa masallaci motoci har hud’u Yusuf kawai ake jira suka yi sallama da yasir ya wuce pool suka tayar suma Yusuf da abokan tafiyar su hud’u a mota d’aya sai saura motocin pick-up van cike da kayan abinci ..
A hanya ne Yusuf ya kira innarsa sunata hira sauran na kallonsa da mamakin yaren da ya keyi kusan 40mnts suna waya da innar kafin su kayi sallama tafiya ta fara nisa sosai bacci ma ya keji
Hayfa ma tasha kuka kafin ta koma bacci sai kusan 11 ta tashi tayi wanka ta sake karyawa tayiwa yasir girki har kala kusan shida tasa masa a fridge kafin itama ta shirya kayan tafiyarta ta kira Armando cewa tana gidan Clara..Clara dama sunyi da Hayfa key na gun mak’ociyar Clara wata mai suna “Fabiola” y’ar Colombia duk sa’oi suke da su hayfa+
Qonqosa mata k’ofa hayfa tayi Fabiola ta fito suka gaisa inda ta gayyaci hayfa ta shiga gunta hayfa ganin batada isashen lokaci tace tayi hak’uri wani lokacin zata shiga
Fabiola tace na biyoki bashin shigowa ko? Cikin murmushi hayfa tace “eh” promise..! Ita fabiola mayyar model ce tanason itama ta shiga kuma tun aikin hayfa na biyu taga magazine d’in tana ma da duk yawancin aikin hayfa don haka tun lokacin da Clara ta fad’a mata tasan hayfa ta keta rok’on Clara ta had’a su
Bayan hayfa ta ansa key tayiwa fabiola sallama ta shiga b’angaren Clara kan kujerar falon 3sitters ce d’aya da dinning mai hud’u sai y’an tarkace da computer console da sauransu zama tayi kan kujerar ta bud’e jakarta ta d’auki wayarta ta fara neman Yusuf
Yusuf bacci ne mai d’an nauyi ya kwasheshi sabida motar range Rover ce ubansu sitt d’inta akwai laushi ga abin d’umama mota sun kunnawa kasancewar lokacin sanyi nan da nan kuwa bacci ya kwashe Yusuf ga wayarsa tun bayan gama waya da innarsa yasata silente
Kusan kira hud’u dole ta hak’ura itama ta d’an mik’e da tunanin ko baya tare da wayar ne, itama d’an bacci ya kwasheta sai cikin d’an baccin ta fara mafarki da innarta da tazo mata cikin yanayin damuwa sannan ta tsaya nesa da ita.. A hankali hayfa ta kalleta cikin damuwa itama tace inna mai yake damunki na ganki haka..?
Inna ta kalleta tace “rayiwarki ke damuna”.. Hayfa cikin rashin fahimta tace inna kamar yaya? Innar tace Mamana kina wasa da rayiwarki.. D’an shiru tayi kafin taci gaba inaso ki sani aure ba abin wasa bane sannan ba kasuwanci bane ba kuma abin nishad’i bane “Aure Ibada ne”.. Inaso kiyi k’ok’ari ki sanja manufarki akan aure ki gyara zamantakewarki da mijinki ki kuma tsarkake zuciyarki da imaninki kiyi zaman aure tsakaninki da Allah domin Allah ya fiki sanin dalilin da ya k’addara miki auren “Yusuf”..
Hawaye hayfa ta fara ta d’an matsa kusa da innar da niyar fad’a mata dalilinta na yin aikin da ta keyi Innar tace “kiyi abinda duk na fad’a miki tun kafin lokaci ya k’ure miki Yusuf matsayinsa na da yawa a rayuwarki kinji”..?
Tana shirin furta magana Innar ta b’ace bata saurareta ba farkawa tayi itama cikin tsananin firgici tana kiran “Inna Inna” tana hawaye tare da kama kanta tana ci gaba da kiran sunan Allah.. Tabbas daga anyi Gala koda contract d’inta bai k’are ba zata ajiye aikin nan tunda mominsu tace sunada napep 4 golf mai Kaduna Kano 2 ga gidajen haya 2 ga kamfani sannan akwai kud’ad’e a banki ita gaskiya daga Gala zata daina aiki ta zauna gida k’ark’ashin mijinta komai talaucinsa ta hak’ura su zauna tana sonsa haka kuka take tana duk wannan tunanin wayarta ya fara ringing d’an tsagaita kukan tayi ta kalli wayar Armando ne ta d’aga yace queen ki shirya 5:40 zamu wuce airport
Toh tace kawai ta kashe wayar taci gaba da kukanta..
A hanya ma su Yusuf sun iso kauye na farko sun isa masauki nan ya fidda wayarsa ganin yawan mclls d’in hayfa ya d’an fito waje kafin ya jefa kiranta
da sauri ta d’aga ganin shine saidai ta yi shiru
Ajiyar zuciya yayi kafin yace sory baby bacci nayi a mota ya kike..? Cikin muryarta da ta d’an dishe sabida kuka tace ..lafiya kun isa lafiya..? Yace baby mai ya samu muryarki? Shiru tayi
Yace kuka ki kayi..? da sauri tace kaina ne yake ciwo..! Ajiyar zuciya yayi bai yadda ba amma yace kinsha magungunanki? “Eh” tace yace to ki k’ara bacci zuwa yamma zai warware IA mu zamu fita bayan munyi sallah bansan yaushe zamu dawo ba in dare yayi dayawa sai gobe za muyi waya kinji..?
STORY CONTINUES BELOW
Toh tace tana share hawaye tunawa da tayi itama daren tana jirgi hanyar Nigeria jinta shiru yace pls baby banason yawan damuwannan kinji?
A hankali ta saki kuka da ta kasa had’iyewa.. Ya salaam ya furta baby kinaso nayi fushi da ke..? cikin kukan tace “pls 4give me”.. Yace toh ki daina sau nawa ina fad’a miki banaso..
A hankali tayi shiru “yace gud girl” ki kula da kanki zanje nayi wanka nayi sallah Na gaji sosai tafiyar na da tsawo
Sorry tace “yace kinsan abinda zai saka na samu nutsuwa a nan?” Ah ah tace a hankali yace sanin cewa kina cikin aminci da farinciki pls ki barni ni kad’ai cikin zuciyarki kada ki shigar da ko wani irin damuwa da zai iya yimin illa na kasa zama cikin masarautata kinji”? Ajiyar zuciya tayi tare da lumshe idanunta tace “zan daina IA” yace gud bari na barki duk sun gama ni suke jira ki kula kinji babyna..? Eh tace yace “Love u so much baby”..
Me too tace su kayi sallama..!
Tana shirin kwanciya Clara ta shigo shap-shap itama sabida Zata koma café
Hayfa tace wai ina kince zaki ajiye aikin full tym?
Clara tace eh amma kinsan nace miki Sandrine ta haihu shiasa ban ajiyeba sai ta dawo.. Hayfa tace lallai yaushe ta haihu? Clara tace yau 5dys kinsan ke yanzu tauraruwa ce ganinki sai rabo sau nawa nayi miki wpp babu reply kai Khadija..?
Hayfa tace sorry wlh aiki ne sam banada ko tym d’in kaina bakinga jiya ma msg na miki ba na zuwana inason kiranki amma bana zama
Clara tace ay shiasa ni bazan tab’a aikin model ba ko sabida takurawa irin na manajojinsu ance kamar y’an k’wallo kuke komai sai manajanku ya yadda za kuyi abinci da k’aida komai ance yadda ba ‘ason y’an k’wallo na yawan sex idan sunada wasa a gabansu haka kuma kuma wai koda kunada aure ni wallahi bazan iya takuraba diba kema duk kin rame kin koma kamar mai 15yrs
Tunda Clara tafara magana hayfa ke hawaye gaskiyane ita kanta tagaji da aikin ko sabida yadda yanzu sosai take son mijinta batason taje ta rasashi sabida aikin
Dafata Clara tayi tace sorry khadija amma kinsan ni da ke bamu b’oye-b’oye shiasa na fad’a miki gaskiya da zarar kin d’an tara kud’i ki ajiye aikin kiyi karatu ki fara normal lyf sabida wlh da aikin nan wata rana ko yawa kamar ni ba zaki iyaba za a fara biyoki ana son hoto sannan komai kike papparrazi suna bibiyarki suna yad’awa a labarai bakida sauran sirrin rayuwarki
Hawaye hayfa take sosai tunda tafara aikin babu wanda ya tab’a fad’a mata bad syd d’in aikin sai yau Clara kuma bayahudiya amma tasan wai mutunci da sirri
Kallonta hayfa tayi tace Nagode sosai Clara kuma zanyi anfani da shawararki ko sabida “mijina”..
Cikin tsananin mamaki Clara ta kalleta tace “mijinki”..? Hayfa tace “eh” Clara tace dama kinada miji..? Hayfa tace eh shin..Clara ta katseta da cewa “Yusuf”..? Hayfa tace eh
Cike da mamaki Clara tace amma mai yasa da baki tab’a fad’amin ba..? Hayfa tace babu komai.. Clara ta dafa ta tace gaskiya kinyi sa’a Yusuf ya had’u da inata tunanin ki taimakamin na sameshi ashe na kine ma wow yanada kyaw gaskiya ki kir’eshi da kyaw in ba haka cikin sauk’i za a sace miki shi
Mutmushi hayfa tayi tace nagode sosai Clara.. Agogo suka kalla lokaci ya tafi itama hayfa da sauri ta mik’e ko kafin ta motsa kiran Armando ya shigo cewa ta sakko. Tace toh.. Suka fito itada Clara inda zasu sauke Clara café in hayfa ta dawo Nja gidan Clara zata koma har Yusuf ya dawo shima su tare sabon gidansu..
Suna saukowa suka shiga driver ya tayar da motar da gudu yake tuk’in sun kusa makara airport suka ajiye Clara suka wuce ko airport…
7:23pm jirginsu hayfa ya d’aga zuwa Nigeria inda take ta hawaye kawai Armando yana ta baya yana karatun jarida..
STORY CONTINUES BELOW
Koda Yusuf suma suka gama abubuwansu a waje kusan 11:52pm suka dawo gida ya nema layin hayfa off yayi tunani tayi bacci ya mata msg shima ya shirya ya kwanta domin kowa da d’akinsa da bayi a ciki gone gobe suma da wuri zasu fita su fara aikin da ya kawosu ance akwai wasu kananun kauyuka makota duk zasuje rabon haka ya kwanta cike da kewa da so da tunanin matarsa..
6:28am jirginsu hayfa ya sauka abuja inda ko b’ata lokaci ba suyi ba suka d’auka shatar motoci uku zuwa Kaduna na kaya biyu sai nasu.
Wajajen 9:17am agogon Nageria su Hayfa su ka shigo Kaduna inda ta fad’awa driver address d’insu a Kuse rd ya wuce da su..
Duk yadda hayfa take tsammanin gidansu da Ammah ke bata labari da suka iso gate d’in kawai tafara mamaki hon su kayi mai gadi yana lazimi da sauri ya mik’e yazo ya bud’e motarsu hayfa ta danno kai cikin gidan mai gadin ya k’arasa domin sanin ko bak’i ne a kayi daga nesa saidai ganin hayfa ya fara mik’a gaisuwa kasancewar bai tab’a ganinta ba amma makeken hotonta da ke falon gidan ya sashi ganeta shi ya bud’e mata k’ofar b’angarenta ta fito duk tayi laushi kafin Armando shima ya fito sosai gidan ya burgeshi yanata kallo ya juya ya kalli hayfa yace Queen gidanku ya burgeni sosai…. Tace Nagode mai gadi ya fara kwasar kaya yana shiga dashi inda Hayfa ta k’ara kallon Armando tace.. Pls karka manta banaso su san komai game da aikina.. Murmushi yayi yace to gimbiyar Yusuf naji.. d’an murmushi tayi suka nufi k’ofar falo gidan bud’ewa tayi ta ma Armando izni ya shiga
Wow yace ganin yadda falon ya had’u sosai yace Queen babu wani hotel da zani ina gidan nan.. Cikin d’an dariya tace “toh” tana haurawa sama ganin shiru gidan sai motsin laraba a bayan kiching da alama yara duk sun wuce school d’akin farko a saman ta tsaya da tunanin tabbas nan ne d’akin mominsu a hankali ta tura k’ofar Ammah na zaune itama da system tanata aiki taji an bud’e k’ofa ta d’auka laraba ce ta d’ago saidai cikin tsananin mamaki taga hayfa da sauri ta mik’e “y’an matana yaushe kika shigo”? Hayfa ta k’arasa ta rungumeta harda hawayen farin ciki ganin yadda ammah tayi wani irin kyaw da haduwa da k’iba dama ammah fara ce wahala da yasa hasken ya dishe gashin kanta kuwa yasha k’ananun kitso tayi kamar wata mai 25yrs
d’agowa hayfa tayi tana kallonta tace mominmu ina Daddy..? Ammah tace yana Lagos can aka bashi aiki tun bayan da ya gama course d’insa yana zuwa ne kawai ko wani 2wks
Hayfa tace mominmu ya gida..? Ammah tace lafiya..! amma maiyasa baki fad’amin zuwanki ba na miki shiri? Ke kad’ai kika zo..? Hayfa tace ah ah ni da wani abokina da muke k’ungiya d’aya wanda na fad’a miki rannan.. ammah tace yana ina shi..? Hayfa tace yana k’asa in mu ka karya zai wuce hotel
da sauri ammah ta jawo hijabi tace kin cika shirme shine kika barshi haka shi kad’ai..? Muje babu wani hotel zai sauka d’akin k’asa kawai suka nufi k’asan tare
Armando na duba wayarsa yaji muryar ammah tanata masa sannu da zuwa nan ta zauna suka fara gaisawa inda take fad’a masa babu maganar hotel akwai d’aki bayan falon a k’asa sai ya sauka ciki yayi mata godiya ta kira laraba cewa maza taje su fara gyara dake d’aya mai aikin tana b’angaren su goggo tana musu shara da moping
Nan aka gyara masa d’akin dama akwai komai ya shiga tare da ce musu zaiyi bacci tukuna.. Bayan shigarsa ammah ta kalli hayfa tace ya d’an albarka? Hayfa tace lafiya shima yayi tafiya..! Ammah tace OK muje ki gaida su goggo kizo kiyi wanka ki kwanta kema ki huta kinji..?
Hayfa tace to suka mik’e.. Babansu na kan dadduma a baranda goggo da mai aiki na kiching suna dama Koko sabida inna nada bak’i daga Maiduguri y’an uwan babansu hayfan su biyu mata shiasa bata jira sai angama na b’angaren ammah take had’a musu abinci da wuri
Ganin hayfa babnsu yayi kamar bai ganeta ba ganin yadda ta zama kamar wata afroamerica ta goge sosai fatarta tayi kyaw sosai saidai ba k’iba
da sauri hayfa ta k’arasa ta rungumeshi tana hawaye kafin ta d’ago yana shafa kanta shima yana kallonta ” ina kwana tace”? Yace lafiya lau auta”..? Ya mijinki..? Tace lafiya.. Goggo alje ce taji muryarsu ta fito itama cike da mamaki da murna da sauri hayfa ta koma gunta ta rungumeta sun dad’e kafin duk aka baje a barandar inda hayfa ta gaisar da bak’in da tagani nasu sun dad’e anata hira tana gajiye amma dole ta hak’ura k’arshema nan tayi wanka ta karya ta kwanta amma ta koma domin tanada appointment akan lasisinsu na kamfani da zata ansa yau d’in da k’arfe goma da rabi..
Hayfa cikin bacci take mafarkin da Yusuf ta ganshi cikin tsananin damuwa tana tanbayarsa mai ya faru.. Ya kalleta cike da damuwa yace mai kike b’oyemin..? Bata yi magana ba yaci gaba zan iya yafe miki komai banda cin amanata..! tsabar tashi da hankali ta matsa kusa da shi za tayi masa magana ya b’ace cikin mugun tashin hankali ta ke kiran sunsa tana kuka goggo da bak’inta suna can wajen masu gyaran ciyayi sabida ana shukawa goggon zigale da lemon grass da aloe verra Abba ne ya jiyo hayfa da sauri ya nufi d’akin yayi kanta still ma baccin take tanata kiran Yusuf saidai kukan har a zahiri ma ta keyi kusan minti uku yana kallonta da tunanin tabbas akwai abinda yarinyar ke b’oyewa game da rayuwarta da mijinta saidai zaiyi k’ok’ari ya gano kafin yasan matakin d’auka a hankali ya fara yoga mata addu’a kafin ya dafa goshinta yana kiran sunata “Hadiza”..? bud’e idanunta tayi da suke ta zubda hawaye ta ga babanta da a hankali ta d’ago.. Yace tashi babu kowa muyi magana..tashi tayi ta sunkuyar da kanta kwata-kwata kwanan nan ta dena samun nutsuwar zuciya da ta k’wak’walwa.. Kallonta yake sosai yana karantarta ya kuma gane tsab akwai muhimmin sirrin da take b’oye musu wanda har da mijinta hakan yasa take ganinsa har cikin mafarki domin itama b’oye masan na damunta+
Kiran sunata ya k’arayi “Hadiza” kin sani duk duniya bakida wanda ya fini ni babnki ne dukkan damuwarki tana wuyana na sanshi koda banida k’arfin taimaka miki zanyi miki addu’a kuma addu’ata zata karb’u a kanki IA domin Allah yayi alkawarin ansa addu’ar iyaye akan yaransu.. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali.. Yaci gaba ki fad’amin na miki alkawari ko y’an uwanki in bakiso su sani bazan tab’a fad’a musu ba kinji..? Kuka ta saki sosai shiru yayi yana tunani tabbas wani al’amari ne mai girma mik’ewa yayi ya je ya kulle k’ofar barandarsu yadda in su goggo suka dawo zai sani ya dawo ya zauna yana kallonta tayi kukan sosai kafin ta tsagaita… Ya sake cewa mai yake faruwa..? A hankali ta fara bashi labari tun daga ranar da Ammah ta bata waya suyi magana da Yusuf zuwa tafiyar ta kawo yau..!
Ajiyar zuciya yayi sosai ya ke mamakin abinda ya faru saidai tabbas dole hayfa ta bar wannan aikin kafin aikin ya zame mata hatsari tunda ko babu komai sunci riba ay zuwa yanzu saidai abin takaicin har yanzu burin y’an uwanta su zama fitattun masu kud’i a Kaduna da ma kewayen Kaduna sabida tsabar rashin godiyar Allah..
Kallonta yayi yace..kinason ci gaba da rayuwa da mijinki..? Mantawa tayi ma da babanta take magana ta bashi ansa da “har in mutu”.. Murmushi yayi yace to daga yanzu ni zan rik’a tsara miki yadda zaki yi komai kin amince..? Girgiza kai tayi alamar eh.. Yace maza kije ki kirawomin Driver yazo ya samomiki sim mara number ki kirashi kuyi magana kada ki bari ya gane komai a tare da ke kinji..? Ta girgiza kai yace maza tashi kije kada su zargi wani abu
A hankali jiki babu k’wari ta mik’e at least ta d’anji dama a zuciyarta a hanya ta had’u da su goggo alje suna dawowa ta k’ara gaishesu kafin ta wuce ta tsaya ta fad’awa driver da ta ganeshi shine ganin yanata wankin babbar motar kai yara makaranta ta gaisheshi shima haka cikin girmamawa sanin ta a hototunan gidan ta fad’a masa sak’o Abba ta wuce inda b’angarensu shiru babu kowa sai laraba da mairanjo sunata aikinsu suka gaisheta ta tanbayesu Armando ya tashi? Suka ce ah ah ta haura sama d’akin mominsu ta koma can aka kai mata kayanta dukda akwai d’akinta da dama ammah ta gyara tasa komai harta da kayan kallo abcewarta duk sadda hayfan tazo Nigeria ko hutu ko haihuwa ko taro tanada d’akinta
Kwanciya tayi a gadon ta lumshe idanunta tana tunaninsa, kewarsa ta fara ji sosai tana addu’a Allah ya bud’a masa ya taimaki kansa da y’an uwansa da haka ta kuma komawa bacci mai cike da tunani..
Tun bayan fitar hayfa babanta ya fad’a duniyar tunani tabbas dole ya fitar da ita daga wannan rud’ani koda mai zai faru dukda bayani da tayi masa na cewa in akayi contract ba’a janyewa har sai ya k’are in ba haka ba kamfanin zasu shigar da ita k’ara.. Ajiyar zuciya ya k’arayi yana mai tausaywa yarinyar na dagewarta akan taimakon rayuwarsu duka don ganin sun fita daga talauci saidai dole aikin ya tsaya a yanzu itama ta fara gina ingantacciyar rayuwa mai amana da gaskiya tsakaninta da mijinta duba da har yau ya kasa gano mata danginta mijinta kad’ai a yanzu yake danginta baya ga shi da y’an uwanta..
Wayarsa ya d’auka ya nema layin dreban gidan.. Suna Abubakar Gumi market ya ga kiran Abba da sauri ya d’aga yana masa sallama..
Abba yace kaje d’auko yara ne.. ? Yace ah ah Hajiya tace zata d’aukosu mun fito ne da bak’on Hajiya Hadiza..
STORY CONTINUES BELOW
Abba yace to zan fito yanzu da keke sai na kiraka mu had’u da ku zan gana da bak’on kuma bance ka fad’awa hajiyarka ba.. Yace IA alhaji koma nazo na d’aukoka..?
Abban yace ah ah ganinan zuwa da kaina babu damuwa.. Yace to sai kazo suka yi sallama ya kashe wayar ya mik’e goggo suna baje a can tsakar gidan kan tabarma ya musu sallama ya fita..
Hayfa bayan ta saka sim ta duba da register da credit na 5k a ciki cikin farin ciki ta kullo k’ofar d’akin ta koma gefen gadon ta zauna ta jefa layinsa..
Sun idar da ishaa kennan yana zaune duk hankalinsa baya tare dashi na rashin samunta ya kira yasir baya kusa bare yaje café ya duba ta ko lafiya ko jikinta ne ya sake tashi ga k’auyen ma akwai matsalar ntwk.. Yana cikin tunanin yaji wayarsa na ringing da sauri ya d’auka yana kallo saidai ga mamakinsa babu number an rubuta “unknown” mamaki yayi saidai yawan matsalar ntwk d’in inda suke yasa yayi tunani k’ila ntwk d’in gun ne ya b’oye number a hankali ya ansa..
Wani irin nannauyan ajiyar zuciya ya sauke jin sallamarta ya furta “Baby mai ya faru wayarki bata shiga”?
Ajiyar zuciya itama tayi tace sorry d’an problem na samu da wayar.. d’an shiru yayi itama haka kafin yace “ya jiki”? da sauk’I ta furta a hankali sai kuma ta k’arayin shirun..
Yace mai kike yi yanzu..? Mugun bugawa k’irjinta yayi ta d’ago wayarta ta duba lokaci a Toronto kusan 8:30pm ta maida wayar kunnenta tace ina shirin bacci ne.. Yace ina Clara..? Tace ta fita..! Yace pls ki rik’a kulamin da kanki kinji..? A hankali ta furta IA tana sharar hawaye wlh ta gaji da wannan k’arerayin..
Jinta shiru yace mu ma aikin ba sauk’i gaskiya k’auyukan sunada yawan mutane da unguwoyi sosai haka muke shiga ko wani layi amma alhdl muna samun nasara a yau muka fara amma munyi aiki dayawa a yau d’in.. Ajiyar zuciya tayi tace “Allah yasa ku gama lafiya” amin yace
Bari na kwanta baby gobe ma 7 daidai zamu bar gida kinga ana sa ran jibi a d’auki azumi..tace Allah ya kaimu yace yanzu ina layinki..? Tace na ajiye kafin Clara ta raka ni a duba ina anfani da wannan na ta ne..
OK yace kenan ke zaki rik’a kira kinga baya nuna komai bare na kira ki.. Eh tace IA haka suka yita firarsu har kusan 35mnts kafin su kayi sallama ya kashe wayar bacci kawai ya keson yi yayinda hayfa ta k’ara fad’awa tunani suma gobe zasu fara aikinsu tsakanin kafancan, ancau, kubau, kudan k’aura sauran k’auyukan sai foundation ya kafu zasu shigar da su lokacin sun samu ma’aikata a nan Nigeria na foundation d’in..
Koda Abba ya isa kasuwa ya kirasu dreban yace suna Chiking republic da ke kan amadu bello way Armando na yin launch Abba ya k’arasa ya same su
Armando na ganin Abba ya gane shine baban hayfa sabida kalar fatarsu da tsawon hancin ya mik’e ya k’arasa ya mik’awa Abba hannu suka gaisa kafin Abba ya zauna inda tuni driver ya fita ya basu guri.. Kallon Armando Abba yayi baisan ya za suyi suyi magana ba a dole Abba ya juya yana kallon matasan da ke gurin ya kira wani matashi da gani bahaushe ne koda ya k’araso tebur d’insu Abba
Abba yace ka zauna magana zanyi da wannan baturen ina fad’a maka kana fad’a masa yana fad’a maka kana fad’amin
Y’ar dariya ce ta kub’ucewa matashin Abba ya kai masa rank’washi yace “gidanku” ka nutsu..
Tsaida dariyar yayi yana kallon Abba shidai Armando kallonsu yake baisan mai yake faruwa ba..yaga Abba ya farawa matashin magana kamar haka.. ” inaso ka tanbayeshi Hadiza ta fad’amin komai na aiki da take yi da su dole ne sai contract d’inta ya k’are zata daina aiki da su”?
Shi matashin bai gane ba amma ya kalli Armando ya fad’a masa abinda Abba yace.. ajiyar zuciya Armando yayi yace “eh in ba haka ba kamfanin zasu iya kaimu k’ara ni da ita sabida na nema mata alfarma dayawa a kamfanin baya cikin tsarin kamfanin idan akayi contract da su ayi aiki a waje komai k’ank’antar aikin amma ita na nema mata wannan damar aka bata domin ta samu kud’i da shahara don haka idan a yanzu ta ce zata ajiye aiki tabbas zasu kaimu k’ara har manyan cotunan duniya wanda zamu iya kashe fiye da kud’in da muka samu na aiki a gunsu..
Matashi yayi ajiyar zuciya ya juya yana yiwa Abba bayani tas na abinda Armando ya fad’a masa sosai Abba ya zaro idanu amma yace “kuma gaskiya ne ko haihuwa bata iyayi yayin aikin..?
Matashin ya fad’awa armando .. Armando yace eh sabida lokacin da tayi contract ko aure bamusan tanada shi ba a yanzu kuma idan haka ya bayyana shima hukunci zamu fiskanta sosai ni da ita ga masu kamfanin..
Matashin ya fad’awa Abba abinda Armando yace.. Innalillahi Abba yake fad’i tare da fatan Allah ya gaggauta kawo k’arshen contract d’in.. Ya k’ara kallon matashin yace yaushe ne contract d’in zai k’are..? Matashin ya fad’awa armando, Armando yace nan da watanni hud’u zuwa biyar.. Matashi ya fad’awa Abba, Abba yace inaso muyi a rubuce kaga mu addininmu da al’adarmu wannan aikin bai kamaci koda mara aure ba bare mai aure ka taimakamin daga ya k’are kada ta sake yin wani nagode ta fad’amin yadda ka taimaka mata nagode sosai amma banson wannan aikin
Koda matashin ya fad’awa Armando abina Abba yace shiru ya d’anyi saidai yayi tunani suna Nageria hayfa na Canada inma taci gaba da aikin ya zasu sani don haka yace “babu damuwa idan har itama tace ba zata k’ara yin aikin ba babu damuwa
Abba bai gane manufar Armando ba yayi masa godiya tare da bada labarin maraicin hayfa wanda wannan ya k’ara sawa Armando yaji dole ta taimaka mata ta shahara sosai a duniya shi kansa babanta zai zo yayi alfahri da ita don gaskiya zai ja kud’i da hayfa ba vyadda za a yi ya batta ta bar aiki bata yi koda 5yrs ba a aikin..
Haka matashin ya mik’e Abba ya bashi 3k ya masa godiya ya koma bakin aikinsa Armando kuma da Abba sai murmushi suka fito driver ya tayar suka nufi gida ..
Hayfa na falo yara suka dawo duk aka rungumeta anata tsalle gashi ita bata yiwa kowa tsaraba ba suna falo duk sunata fira Ammah da suwaiba suka shigo suma da gudu hayfa taje ta rungume suwaiba kafin duk suka koma su da yara duk anata hira surayya kusan girmansu d’aya da hayfa yanzu bayan hayfa ta bata kusan 2yrs