KASAR WAJE CHAPTER 3 BY MARYAM DATTI
KASAR WAJE CHAPTER 3 BY MARYAM DATTI
Www.bankinhausanovels.com.ng
Bacci ne ya d’an kwasheta duk kuwa da zafin da jikinta yayi ga rawar sanyi tana d’anyi kad’an saidai ta lullub’a da hijabinta na sallah ga safa da ta gani gefen gadon ko damuwa ba tayi ba da sanin mai shi ta saka
koda ya iso gidan magrib tayi bai ko damu da rashinta a falon ba yasan tana d’aki
shiga yayi bayi yayi alwala ya fito bayin ganin yadda take k’udundune sannan ga d’an rawar sanyi tana yi da d’an hanzari ya k’arasa gadon yana ya d’an yaye mata rufar ya tab’a wuyanta
Tana jinsa bata ko motsa ba
Sosai ya tsorata jin mugun zafin da jikinta yayi da sauri ya mik’e ya maida takalminsa ya fita zuwa pharmacy da k’afa ma ya taka babu nisa da gidansu
Bayani ya musu na yanayinta aka bashi magunguna da yadda zata sha sannan aka ce taci abu mai d’umi tukuna ta sha
Yana isowa gidan ya kunna gaz ya d’ora taliya ya mata jolof da sardin da d’an ruwa-ruwa ya juye ya had’a mata coffee ya d’auki maganin ya nufa d’akin
Ajiye plate d’in yayi a k’asa ya d’an shafa hannunta a karon farko yana kiran sunanta HAYFA ga magani ki tashi ki sha
runtse idanunta tayi sam bata jin dad’in jikinta jin magani ne a dole ta tashi domin tana so ta warke ta nema mafitar halin da ya saka su ita da y’an uwanta
d’ago tray d’in yayi ya d’ora mata kan cinyarta ya mata bayanin yadda zata sha magani ya mik’e ya bar d’akin
Bin bayansa tayi da harara tana ayyana auren nan sunansa mafarki dole ne kuma ta farka daga mafarkin
Sallah yayi a falo shima ya d’iba taliyar yaci kusan 1hr yana zaune yana tunanin inama ya bar wayarsa yana son kiran innarsa
Ganin bai ga wayar ba ya mik’e a kujerar da tunanin k’ila d’aki take ya d’auka da safe kan ya wuce aiki baya son shiga d’akin dukda yana jin son jiyarta da kansa amma dole ya hak’ura ya kwanta zuciyarsa cike da kewar y’an uwansa da mahaifiyarsa.
Sosai kamal ya haukace a gidansu ya kulle k’ofarsa yana huci dole ko waye yayi kuskuren rabashi da hayfa yayi maganinsa
Yana kwance bacci mai nauyi ya kwashe shi inda hayfa bayan ta d’anci taliyar ta shanye coffee d’in tasha magani itama jikinta yayi nauyi ta kwanta in ta farka dare sai ta maida sallah
tun 4:56am Yusuf ya tashi yayi wanka yayi alwala ganin yadda hayfa ke bacci kamar jaririya yasa hankalin Yusuf kwanciya cewa taji sauk’i ya fito d’akin
Sallah yayi ya ci bread da tea ya bar gidan!
Yana train yana tunanin yadda zasu yi rayuwar aure a haka tun ba’aje ko inaba sun fara samun Matsala da tunanin har ya iso pool.
Wajajen 6:11am ta farka da salati cikin hanzari ta mik’e ta d’auro alwala tazo ta fara sallah
Bayan ta idar ne tana kan dadduma tayi tagumi tana tunanin yadda zata b’ullowa matsalarta
Tunani tayi bai kamata ta fad’awa aunty ammah yanzu ba saidai zata k’ara tunani ta bari ayi koda wata yaso ta nema kamal su tsara yadda zata samu admission ta koma cikin university da zama kafin su fad’awa aunty ammah ta rabu da Yusuf sabida yaudararsu yayi shi ba mai kud’i ba ne
da wannan tunanin taji hankalinta ya d’an kwanta ta mik’e taje ta d’aga fillow ta d’auko wayar ta kunna ta shigar da number salma baita tayi saving kafin ta kira salman directly bata tsaya magana ba tace ki hau wpp yanzu
STORY CONTINUES BELOW

Salma tana d’akinta dama kallo take ta kunna data tana tsokanar hayfa “amarya bakya laifi”!
Tsaki hayfa tayi tace lallai
Salma tace wannan na profile shine mijinki?
Hoton Yusuf ne zaune kujerar pool yana d’an kallon sama yana tunani yasir ya masa hoton sai hoton ya bada wani irin burgewa na musamman kamar wani babban star ko model
Tsaki hayfa tayi tace “eh” kawai
Wow salma tace “gaskiya bacin ina yinki over da wallahi nayi miki snatching d’insa ya had’u kamar shi yayi kansa
Hm hayfa tace ay ko na baki ke da kanki zaki bawa wata
Salma tace mai yasa kika ce haka?
Hayfa tace kyan d’an maciji ne babu komai a bayan kyan
dariya salma tayi tace pls indai da gaske kike ki bani shi ni ko baida alherin komai na duniya ina so haka
shiru hayfa tayi cike da mamakin salma
Emoji salma ta turo mata na gwalo tace ay nasan wasa kike, kedai zanga ranar da zaki daina jiji da kai ke yanzu har mijinki ma kina masa?
Wlh sis ki kiyaye mijinki ya had’u k’arshe ni ace ni na sameshi ko baida kobo ko baida ilmi zan aureshi in godewa Allah bare ke yanada komai gashi a kasar waje duba lefenki ko na Mardhiya Abubakar gumi da Yusra shamsuna Ahmad munje biki mun gani ke shaidace duk basu fi naki ba
Ajiyar zuciya hayfa tayi bata iya magana ba salma taci gaba
ni yanzu na samu admission a Al-azhar Egypt jiya aka bani kuma kuma kinsan burina nayi university a gidan mijina pls ki godewa Allah ki rik’e mijinki
Haka salma tayi ta yiwa hayfa nasiha domin salma babnta tsohon ES ne NEITI dake presidency amma sosai tafi hayfa sauk’in kai su katsinawa ne tanada yayanta da yayi aure yana aiki NHIS yaso hayfa tak’i sabida ita bayan jiji da kai tafi k’arfin ta auri mai mace dukda salma taso abin sosai dole ta hak’ura sanin halin wulak’ancin hayfa kada taje tana wulak’anta mata d’an uwa ya shafi k’awancensu
Kusan 2hrs suna chart da salma kafin su kayi sallama hayfa ta kashe data ta kwanta cike da tunani tanason kiran kamal tana tunani saidai ta yanke hukuncin kiransa
Mik’ewa tayi a hankali ta shigar da number sa ta jefa yana office ganin number waje yanada friends da ke waje amma duk number su da suna
Hayfa zuciyarta ke bugawa ta sani sarai tayi islamiyya tasan duk hakkokin miji akan matarsa tunani tayi koda mai ke taakaninsu da Yusuf bai kamata tayi magana da wani namiji ba tana matar wani
kamal na d’aga wayar ta tsinke tayi shiru tana hawaye
Ganin haka kamal ya maida kiran tana kallo yana ta ringing tak’i d’agawa sau uku yayi ta k’i d’agawa ya hak’ura ya kashe cike da tunanin wa ke kiransa daga Toronto sabida ya ga information ta trucllr
Tunani yayi da sauri ya jefa layin auntynsa Luba k’awar ammah
Tana office taga kiran ta d’aga tana d’an tsokanarsa “hala d’ana yayi mafarki da ni”?
Dariya yayi suka gaisa kafin yace “pls aunty ina ne hayfa tayi aure”?
Tsaki tayi tace haba kamal wai haukacewa za kayi?
Ka manta yarinyarnan ka riga ka rasa ta sannan da wuya ku k’ara had’uwa domin ko zasu dawo Nigeria ba yanzu ba yayarta tace sai bayan hayfa ta gama masters ma zasu dawo
Pls ka manta da ita Allah ma ya tausaya maka ya kaita har Canada domin ka mant….. Kamal ya katse wayar domin ya gane hayfa ce ta kirashi, da sauri ya sake jefan kiran saidai yayi ta ringing hayfa na kallo ta kasa ansawa tunani yayi sai kawai ya mata txt
STORY CONTINUES BELOW

Salaam. Ya bae ya kike? Pls ki hau wpp muyi magana!
Tana ganin msg d’in ta kunna datar ta shiga saidai ba tace k’ala ba
Kamal ya fara tanbayanta ya take mai ya faru tayi aure ko fad’a masa ba tayi ba ya k’ara
Bae ina alk’awarin da muka yi na kasancewa da juna na bae kinsan irin son da na ke miki mai yasa kika min haka
Tunda ya fara turo msg hayfa bata ce komai har yanzu
Ci gaba yayi ya fini kud’i shiasa ko?
Iyayensa sunfi nawa kud’i ko?
Ya fini ilmi ko?
Babu ansar da hayfa ta bashi yaci gaba
Kinsan na fad’a miki na fara aiki da masters ne sbd na banaso daddy yaci gaba da hidimata inaso na k’arasa ratuna da kaina kuma tare da ke a k’asar da kike so zanyi karatu iya yadda kike so har professor
Kamal ba duk wannan ba ne “hasali ma ni ko a haka da kake ka fiyemin wannan mijin
Emoji ya turo na alamar da gaske?
Itama emoji ta tura masa na eh
Yace to mai yasa kika yi aure kika barni?
Nan ta fad’a masa yayyunta suka zab’a mata mijin kuma ba tada wani hukunci bayan na su saidai inaso kaci gaba da addu’a IA wannan auren dole zan barshi
Ajiyar zuciya yayi hankalinsa ya d’an kwanta domin ya san hayfa bata da k’arya in za tayi abu yi take in ba zata yi ba ba mai sata dole ko yayyunta rarrashinta suke
Nan yace toh tanan zamu rik’a magana?
Tace ah ah wannan wayarsa ce
Yace to ki bani na ki…
d’an shiru tayi kafin tace banada waya tukuna…
Yace ki bani address d’inku yanzu zan turo miki waya
“Toh” kawai suka yi sallama ta kashe wayar
Ta dad’e zaune tayi shiru kafin daga bisani ta mik’e ta fita wajen gidan ta bud’e d’an akwatin ajiye note na k’ofar gidan ta kwashe address d’in ta dawo ciki
Falo ta zauna ta masa msg.
Kamal da tunda suka gama waya yake jin duk damuwarsa ta gushe, Yana ganin msg d’in ya shiga wani babban kamfanin saida wayoyi na Toronto ya saya mata k’atuwar IPhone11 ya biya harda kud’in sim ya bada address d’inta duka online ya gama yana cike da murmushin farin cikin dawowar hayfa gare shi
Tana zaune tana d’an tunane-tunane taga kira na shigowa dubawa tayi taga suna Ahmad
Bata d’aga ba domin tasan wannan kiran Yusuf ne, barin wayar ma tayi gurin ta mik’e ta shiga kanta ta bud’e fridge sauran slide bread ta d’auka tasa a tuster ta had’a tea ta shiga d’aki taci tana tsaki ko abinci duba kamar a kayyade yake
Yau ma Yusuf saida ya isa pool ya tuna ya bar waya gida takaici duk ya isheshi haka ya wuni aikin yau duk babu dad’i sama-sama suke hira da yasir
Bayan hayfa tayi zuhur wajajen 3:pm bacci ne ya kwasheta a d’aki inda ta manta wayar Yusuf falo
Da yamma yau 4:25 Yusuf ya kamo hanyar gida bacci yake son yi da yamma zai fita neman wani aiki ko a café ko mall da tunanin ya iso saidai yana isowa ma’aikacin kamfanin waya ya kawo sak’on hayfa
Gaisawa suka yi da Yusuf ya fad’awa Yusuf ya kawo sak’o ne Yusuf cike da mamaki sak’o
Saidai ma’aikacin ya bashi kwalin da ke nannad’e cikin takarda mai ruwan k’asa ya bawa Yusuf Biro yayi signing ya ya mik’a masa ya wuce
STORY CONTINUES BELOW

Koda ya shigo falon jin shiru yasan tana d’aki ya zauna ya fara karanta d’an taller da ke manne jikin kwalin
Kamal Tijjani Nadabo first bank Kaduna Nageria!
Sosai ran Yusuf ya fara b’aci ya yake takardar ya bud’e kwalin yaga waya ce zungureriya y’ar ubansu iPhone11 goldin
Maida wayar yayi cikin kwalin ya fad’a tunani yaji tasa wayar tana ringing nema ya fara yi sai yaji ashe cinyarsa na kan wayar ya d’aga saidai ga namakinsa number Nigeria kuma bak’uwar number
Kamar ba zai ansa ba ya d’aga
Kamal jin an ansa bai ko jira ba yace “bae kinga sak’on”?
Ajiyar zuciya Yusuf yayi cikin dakiya yace “kai yanzu baka jin tsoron Allah”?
Kamal na jinsa bai yi magana ba..
Yusuf yace “kana musulmi baka san hukunci mu’amala da matar aure ba”?
Cikin takaici kamal yace auren dole? to bari kaji hayfa zata dawo gareni koda zan k’arar da dukiyata da ta iyayena wajen ganin hakan ya tabbata ya kashe wayar
Sosai ran Yusuf ya k’ara b’aci da hayfa saidai baima san wani mataki zai d’auka ba domin shima yanzu ya fara zama confused akan dalilin da yasa ta aureshi
Call ya shiga yaga yawan call d’in da kamal yayiwa hayfa
Number kanninsa Ahmad ya jefa suka gaisa
Ahmad yace yana waje yace dama innace take son magana da kai in na koma gida zan maka flashing
Yusuf yace ya jarabawar Ku?
Ahmad yace mun samu jamb mu duka
Yusuf cikin farin ciki yace alhamdulillah
Kai mai ka samu?
Yace pharmacy a Kaduna state university
Yace gud Qassim fa?
Yace English shima a Kaduna state university
Yusuf yace shikenan IA zan fara muku shiri amma kuje ku fara neman accommodation da wuri zaifi mana sauk’i yaso sai muga yadda zamu tsara komai cikin sauk’i IA
Toh Ahmad yace suka yi sallama.
Shiga wpp Yusuf yayi saidai yayi mamakin ganin number kamal a wpp ma bud’ewa yayi ya fara karanta duk chart d’insu da hayfa
Ba k’aramin b’aci ransa yayi ba sosai zai saita yarinyarnan ba zai d’auki sangarta ba ko baida komai wallahi bazan yadda da cin kashi ba, Mik’ewa yayi ya fara girki yunwa yake ji ko da safe bai karya ba sai sandwitch da suka ci shi da yasir a pool
motsinsa ne ya farkar da hayfa ta tashi tana tsaki da takainci mai ya dawo da shi yau da wuri ta wuce bayi tayi wanka ta d’auro alwala tayi asar ta saka wata tsinaniyar doguwar rigar material ya matseta iya matsa d’inkunata duk na tsiya na y’aran masu kud’in Kaduna dama telanta gagararre ne shagonsa na Kinshasa road U/Rimi
Falon ta fito neman abinci yunwa take ji sai ganinsa tayi yana aikinsa ko k’ala bata ce ba ta juya zata koma taji muryarsa “ke”
Banza tayi dashi zata shige yace wallahi kika wuce ban baki izni ba zan baki mamaki
Hayfa na da tsoro don haka ta tsaya saidai bata juyo ba tunani tayi kada yaje ya mata duka babu mai k’watarta
Fitowa yayi daga kantar yace “waye kamal”?
Juyowa tayi da sauri tana kallonsa
yace “tanbayarki na yi”?
Still ba tayi magana ba..
Har gabanta yaje yace karki damu na gane d’aya daga cikin karnukan ki ne da suka saba yi miki biyayya
Kina ji na ga wayar da kika buk’ata ya kawo miki “amma wallahi ko da wasa ba zaki yi anfani da ita ba haka zaki zauna har ranar da na samu kud’i na miki Nokia da zaki rik’a gaisawa da iyayenki
Hawaye kawai hayfa ta keyi tana ayyana gaskiya Yusuf baida mutunci ita wani irin k’addara ne ya had’ata dashi
Yaci gaba sannan wallahi ko wayata na k’ara mantawa kika d’auka kika yi anfani dashi ba da izni na ba na gano haka zaki ga yadda zan hukunta ki
Kuka ta fara yace “ki b’acemin a gabana mara tsoron Allah da aurenki kina magana da gardawa a waje sabida shegen son abin duniya!
Sosai hayfa ta saki mugun kuka ta durk’ushe a gurin
Yace aiki na dawo inason hutawa kuma amma sabida iskanci ko girki baki iya ba ki tashi ki bani guri nace
Mik’ewa tayi ta shiga d’akin ta zauna gefen gadon tana kuka sosai kamar ranta zai fita
Koda ya gama girkin yaci ya mik’ewa yayi a kujerar saidai tunanin aikin na biyu da zai nema ya sashi mik’ewa ya saka takalminsa ya fita
A k’afa yake d’an takawa yana kalle-kalle hagu da dama
Bayan fitarsa hayfa sosai tasha kuka tana tanbayar kanta burinsu ya koma haka?
Hawaye ta share babu wani dalili da zata zauna da Yusuf gashi mugu ga talauci ga bak’in hali gashi bata sonsa dole ne zata kashe auren ko ta wani hali IA ta fara university d’inta a gurin saita gama ta koma Nigeria lokacin kamal ya k’ara hab’aka da kud’i suyi aurensu
Yusuf na dawowa ya shiga wani café na kusa da layinsu ya tanbaya ko akwai aiki
Suka ce eh ammah wanke-wanken kayan coffee da goge su kuma safe da dare da gudu Yusuf yace yana so nan suka bashi zai fara aikin kullum kafin ya wuce pool sannan bayan pool 7:pm yayi na dare da haka ya nufo gida cike da farin-ciki
Ya iso yayi magrib ya d’anyi karatun qur’ani kafin yayi ishaa ya idar ya kira Ahmad
Ahmad na gani ya bawa innarsu wayar
Nan Yusuf ya fara gaisheta tana tanbayrsa hayfa yace tana bacci “tace toh aure dai hak’uri ne ka rik’e amanar y’ar mutane kaga yarinyar da alama y’ar babban gida ce domin ba kaga uban garar da suka mana ba kamar shago za’a bud’e kasuwa goggonku ce da alhaji suka ce na sayar da rabi rabin ayi rabo na dogon daji mun basu sosai an tafi dashi alhaji ya biya babbar mota ta tafi dashi, sai nawa anan shinkafa buhu 3k da kaya sosai kwalaye sunkai 25 to mun saida rabin kayan kwalin za muyi hidimar karatunsu sai suma su tafi da kayan abincin kaga daga ni har kai zamu samu sauk’i sosai
Ajiyar zuciya Yusuf yayi yace inna hakan yayi Allah ya k’ara rufa mana asiri
Amin tace Allah ya baku zaman lafiya ka kira alhaji kayi masa godiya sosai yayi zumunci
Yusuf yace toh innah suka d’anyi hirarsu kafin suka yi sallama tace ya gaida hayfa
Shiru yayi yana tunani daga abinda ya fara fahimta wato hayfa ta amince da shine da tsammanin shima d’an masu kud’i ne kamar ita
Rik’e kansa yayi why duniya ta zama haka? Mutum duk kyawun d’abiunsa da asalinsa in bayada abin duniya ba’a ganinsa da daraja Sosai abin ya dameshi amma a k’arshe ya share yayiwa Aliy flashing ya kunna data suyi fira ya kwanta da wuri gobe zai fara sabon aiki.+
Yau Yusuf ya gama aikin café yana pool ammah ta kira ya gaisheta cikin girmamawa domin baisan komai ba akan hayfa illa ammah ce mamanta ikon Allah
Tanvayarsa tayi hayfa? Tace naji shiru tun rannan da tayimin txt na d’auka ma baku k’asar shiasa ban kira ba sai yau ganin kwanaki sun matsa
Ajiyar zuciya Yusuf yayi lallai da gaske sun d’auka shi d’an masu kud’i ne
Cikin girmamawa yace bana gida ne in na koma zamu kira IA
Ammah da ke lallab’a Yusuf kamar k’wai tace toh babu damuwa sai kun kira nagode suka yi sallama Yusuf ya fad’a tunani da mamakin al’amarin shi tunda suke chart da hayfa bai tab’a ce mata shi wani bane ko d’an wani
Hayfa yau ganin kayanta sun d’an taru tayi tagumi tana tuna Uthman mai wankinta da guga ko su pant da bra d’inta ammah ke wanke mata tas ta goge ta zuba mata a drawer ta
A dole ta mik’e ta shiga bayi ta zuba kayan a d’an k’aramin washing machine d’in ta dawo ta zauna gefen gado tana tunani tana gyaran gado ta canza bedsheets ta saka wancan a washing machine ta share d’akin tas ta d’auko d’an injin share tas tayi goge sosai tana yi tana hawaye har ta gama wardrobe ma ganin kayan Yusuf baida yawa ga sauran layi biyu na kanta space ta fitar da dogayen riguna kusan kala talatin ta jera su a gurin da hijaban sallah biyu ta gyara akwatunan ta maida su yadda Yusuf ya jera mata tun ranar da ta iso
Tana gamawa ta kwashe kayan wankinta taje ta baya inda taga Yusuf na shanya ta shanya ta dawo tayi wanka ta dafa shinkafa da stew d’in sardin da albasa kawai ta d’an ci ta koma d’aki ta zauna tayi shiru sosai take missing Aunty ammah tanata hawaye har magrib tayi sallah tana zaune kan dadduma har isha tayi ta hau gado saidai ba bacci take ba duk ta gaji jikinta ciwo yake mata ko wankinta ta manta bata kwaso ba
Bayan Yusuf ya gama da café kusan 9:34pm ya nufo gida a gajiye yana shigowa ya hango kayan hayfa a shanye sosai yayi mamaki sannan ya d’anyi murmushi yak’i kwaso mata ya shigo
Ya tsaya kitchen yaga jagwalgwalon miyarta da tayi a haka ya d’iba ya ci kafin ya shiga tana kwance ya tsaya yana kallonta ya fito da wayarsa ya jefa layin ammah yace “ke”
Ki ansa mamanki ce saura ki k’ararmin da credit dukda anan k’asar kira na da arha sosai ammah ni bamai kud’i bane taka tsantsan nake da credit d’ina sabida kullum ni kudin da nake d’an samu a lissafe suke
Tana jinsa bata motsa ba yaji ammah ta ansa tanata sallama yasa speaker bayan ya gaida ammah hayfa ta mik’e daga kwance ta fara gaisheta
Shigewarsa yayi bayi ta cire wayar daga h/free ta d’ora kunnenta
ammah tace ya gajiya?
Tace lafiya mominmu ya su muhsin da Yasmin da khairat?
Ammah tace duk lafiya sunata missing d’inki
Hayfa ta d’an share hawaye tace nima haka sosai…
Ammah tace karki damu da kin kwan biyu zaki warware bare in kin shiga dad’i mantawa ma zaki fara yi da mu gashi yanzu ma sai ni na nemo ki
da sauri hayfa tace Allah mominmu don banada waya ne..
Ammah tace bai saya miki ba?
Hayfa tace dam… Yusuf ya fito bayin ta d’ago tana kallonsa ta kasa k’arasawa
STORY CONTINUES BELOW

Wucewa yayi falo ya barta ajiyar zuciya tayi tace mominmu ni… Ammah ta katseta wai hayfa yaushe zaki rage jiji da kai? Wlh in kina haka zaki b’ata mana k’ok’arin da muka dad’e muna yi kinsan yadda mu kayi kafin wannan auren na ku ya tabbata pls ko ba da sauri ba ki rik’a sakin jikinki dashi ko so kike mutane su mana dariya?
d’an kuka hayfa ta saki sam ta rasa ya za tayiwa ammah bayanin gaskiya
Kinga yanzu wlh ko genetor na shekaran jiya na saida muka k’ara biyan wani bashin masu girkin biki ki …… Hayfa ta saki kuka sosai ta shiga uku
Yusuf na kan dadduma da sauri ya nufi d’akin hannunta na rik’e da kanta tana kuka ya k’arasa ya d’auka wayar ya kara a kunnensa yayiwa ammah sallama ya d’auka hayfa kukan shagwab’a take
Ammah taci gaba ba kuka za kiyi ba saukar da kanki za kiyi mu sauke nauyin da ke kanmu ko mai zeyi miki ki jure indai buk’atunmu zasu biya shikenan shima dole zai sakko duk girman kansa haka masu kud’i suke karkiga da kina budurwa suna binki kamar karnuka duk kud’insu suna saukar miki da kai duk don su samu ki auresu ne ko waye da kin shiga ciki dole sai kinyi hakuri da siyasa kafin buk’atunmu su biya kuma ko yaya ki fara aike daga k’arshen watan nan
Yusuf bushewa yayi da wayar hannunsa sai lokacin hayfa ta farga da sauri ta mik’e ta anshi wayar ta kashe taci gaba da kukanta
Ammah ko kallon wayar tayi hala katin hayfa ne ya k’are murmushi ta d’anyi da tsaki tace hayfa dai sai na k’ara da lallashi in ba haka ba haka zata zauna tana yiwa miji girman kai mu da muke da nauyi a kanmu.
Sosai Yusuf ke kallon hayfa da alamar tanvayoyi sa kusan 5mnts ya fito falo ya zauna cike da tunani kala-kala yana son sanin manufar aurensa da hayfa saidai zai bi ta nasa dabarun domin ya gano komai hakan ya k’ara tabbatar masa kada ya sakarwa hayfa kansa!
Haka kwanaki suka shud’e Yusuf da hayfa babu abinda ke had’asu saidai ya fara maganinta sosai domin ya dena girki da ita tun tana aikin cin bread da cornflakes har ta d’an fara gwada girkin saidai in ya dawo gida ya samu tayi shirmenta shima ya ci abinda ya saura dole sannan iyakarsa shara da mopping falo a dole ta fara gyaran d’aki da wankin kayanta
*********
Rayuwa na tafiya lokaci na wucewa yau kwanan hayfa 27 inda sosai ta fara fahimtar rayuwa sannan Yusuf yakan shiga har d’akinta ya tsaya kanta ya kira mata ammah ya bata suyi waya saidai kullum kansa na k’ara d’aurewa idan yaga suna waya tana kuka saidai yayi d’an murmushi suka gama ya ansa wayarsa ya fito d’akin
A Nigeria kamal ya nema hayfa har ya gaji kamfanin da ya saya mata waya sun bashi number ta saidai baya shiga inda layin Yusuf kuma Yusuf yayi blocking d’insa ya sashi a black list kamal kamar zai haukace kullum yana tunanin mafita.
Hayfa na kwance duk tunanin duniya ya isheta ta rasa ta ina zata b’ullowa matsalolinta gashi ta kasa fad’awa mominsu gaskiya ba tason d’aga mata hankali da wuri to amma ina zata rik’a samun kud’i ko 100k da momin tace ta rik’a turowa ko wani 2wks sabida wai kada Yusuf ya d’ago su da wuri suna kwashe masa kud’i
Hawaye ta share ta tabbata wannan mugun shima baida 100k a sati bare har ya ajiye ta d’iba!
wai ta yaya wannan auren nasu ya fara a ina mominmu ta samoshi? har ya yaudareta ya mata k’arya, innalillahi take ta maimaitawa ta saki wani jaririn kuka Yusuf ya shigo gidan yana falo yana jinta yayi tsaki shi yanzu ya ma fara sabawa da shrgen kukan tsiyarta tunda har cikin dare sa’in zaiji tana yi don iskanci
Tsaki yayi ya bud’e fridge ya d’auka abin sha ya koma yana sha bacci yake son yi kadan kafin ya fita café.
Yau kud’in gidan yake k’arewa inda Yusuf ya fad’awa yasir zasu dawo gidansa da yamma IA sosai yasir yayi murna bayan pool Yusuf ya bar pool 4:11pm ya dawo gida sabida sai 6:pm zai fita café sabida da k’afa yake zuwa café
STORY CONTINUES BELOW

Tana bayi tana matse kayanta da ta kwashe a washing machine zata je shanyawa taji motsinsa a bayanta
d’an d’agowa tayi fuskarsa shima babu walwala yace “da kyaw kamar kinsan yau zamu bar gidan nan gara da kika yi wankin”
d’an b’ata fuska tayi yace zan wuce aiki anjuma kika gama kiyi gugan ki tas ki had’a kaya anjuma zamu tashi nan yau kud’inmu ya k’are
Kallonsa take kamar sakarya bata iya tanbayarsa komai ba
d’an murmushi yayi yace kada kuma na dawo aiki baki gama ba ya fito falo.
Mik’ewa yayi abinsa ya fara d’an bacci yasa alarm da 6:pm zai tashi
Tunda ya fita hayfa taji d’an nishad’i da murna dama wato kama nan yayi haya don kawai ya gwadata ta gode Allah da ta jure da bata yi saurin fad’awa mominsu ba sosai ta shiga murna ta fita taje ta shanya kayanta
Ta dawo ta fara had’a kayanta komai da komai, 6:08 Yusuf ya tashi ya shiga yayi wanka hayfa na waje tana kwaso kayanta na wanki yayi magrib ya fito ya wuce café.
A café Yusuf na aiki yaji wata abokiyar aikinsu zata koma kasarsu Argentina nan da 2wks nan Yusuf yace mata pls ta yiwa ogansu magana zai had’a aikin harda nata kada a d’auki wani
Cikin fara’a tace “toh” domin tunda Yusuf ya fara aiki suke shiri.
A gida tuni hayfa ta gama shirya komai na ta taci abinci ta saka wata tsinanniyar doguwar rigar vlisco sosai ya fidda komai na jikinta ta kawo bak’ar abaya ta d’ora kai ta yane kanta dama tun bayan kitson da ta shigo Canada dashi ya tsufa kalaba take yiwa kanta duk kwana hud’u ta wanke ta sake wani babu laifi sosai tayi kyaw ta fito a maryarta dukda tayi rama ta zauna falo tana jiransa.
9:34 Yusuf ya gama aiki a café yana fitowa kiran Yasir ya shigo ya d’aga
Wai ko dai ka fasa dawowar ne yau?
Yusuf yayi murmushi yace yau nayi lattin aiki ne a café yanzu na fito ina komawa zamu kamo hanya
Yasir yace kaga saura mintuna na wuce aiki idan kuka yi latti ka d’aga wani flourvase a gaban gidan ka d’auka key
Yusuf yace “OK” su kayi sallama ya k’araso gida hayfa na shan coffee a tsaye a gaban kanta
Tsayuwa yayi yana kallonta wani irin mugun sonta ne yaji yana fisgarta gashi tayi wani kyaw na fitina
d’an k’arasawa yayi gabanta ganinsa ta ajiye cup d’in tana kallonsa itama kafin ta cire idanunta
Hannunsa ya d’aga a hankali yana shafa fuskarta
Hayfa da ke cikin farin cikin yau zata koma palace ta kasa hanashi
Shi kuwa yaci gaba d’an janyota yayi ta fad’o k’irjinsa ya d’ago fiskarta ya fara kissing d’inta cikin wani irin yanayi da yasa gab’ob’inta suka k’ara mutuwa sosai
Kusan 5mnts yana kissing d’inta ya fara shafarta abayar saman ya cire mata bakinsa na kan nata
Wani mugun numfashi yaja bayan cire mata abayar hannunsa ya sauka kan hips d’inta
Shafawa yake yana wani irin numfashi
Hayfa kanta yanayin da yake mata ta fara sakankancewa dukda tana ji bata sonsa ammah yau dole ta sakar masa kanta tunda ya d’auko hanyar cika musu burinsu
A hankali ya zame bakinsa yana d’an kallonta ya rik’o hannunta suka koma d’akin ya zaunar da ita gado ya zaga bayanta ya zuge mata zip d’in rigar ya saukar da rigar ya fara kissing d’in bayanta da bakinsa ya b’alle mata bra d’inta ya juyo ta wani fitinannen wasa yake mata da k’irjin hayfa kanta sosai ta sakankance
Abu dai yayi nisa kowannensu ya fara manta inda yake
A hankali Yusuf ya kwantar da ita gadon ya bita yana kissing sosai ya sakko saidai nan komai ya tsaya da ya fara cirewa hayfa lyt pink inda yaga al’adarta ya fara zuwa inda ita kanta bata sani ba domin tama yi magrib
Kusan 3mnts yana kallon gurin kafin ya maida mata pant d’inta cike da takaici ya kama kansa
Itama dama da ya fara cire mata pant d’in ta tsorata tuna last tym da tayi saidai tunawa da tayi yau shima zai maidata matsayinta na gimbiya matar mai kud’i yasa ta sakar masa jikin jin shiru ga kunya yasa ta kasa d’agowa
a hankali ya mik’e daga d’an gadon yace “ki shirya muje dare na yi” ya d’auki rigarsa da dogon wandon ya fito falo”!
Bayan fitarsa ta mik’e da k’yar ta maida bra d’inta da rigarta ta gyara jikinta sai sun isa tayi wanka ta canza
Tana fitowa taga har ya rigada ya fitar mata komai waje shima ya fita da nasa tabi bayansa tana tsaye ya kwaso musu y’an sauran kayan abincinsu a wata babbar Leda ya kulle gidan ya cike wasu takardu ya ninke yasa key da takardun a envelope ya ajiye k’ofar d’akin ya kira musu taxi biyu suka yi kamar ranar da ta iso Toronto suka nufi gidan Yasir!