KASAR WAJE CHAPTER 4 BY MARYAM DATTI

KASAR WAJE CHAPTER 4 BY MARYAM DATTI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Bayan Yusuf ya gama aikin yamma na pool sauri ya ke yau ya dawo gida yaga hayfa gashi gobe bufday d’insa na 27yrs gashi gobe hayfa zata fara aiki zaiyi kokari suyi celebrating ko yaya ne+

********

Tunda ya tashi da asuba bayan yayi sallah yana tsaye kanta yana tunanin abinda zai had’a musu na karyawa kafin yasir ya iso ta fito d’aki ya juya yana kallonta

Tana sanye da doguwar rigar Sheraton dark pink ta matseta kmar da fatar jikinta aka auna d’inki tayi d’auri ta d’an bar gaban kanta gashin a kwance sosai tayi kyaw na fitina ga k’irjinta a cike dam hayfa akwai baiwar k’irji

Wani irin yawu Yusuf ya had’iye, ita yunwa ya fito da ita!

Fitowa yayi daga kantar yazo har gabanta ya d’ago fuskarta ya fara mata wani zazzafan kiss

Itama batasan ya akayi ba ta fara tayashi hannunsa ya rik’o nata ya had’a yana ci gaba da kissing d’inta na fitina kai sai gashi ya mannata da k’irjinsa sosai hannunsa na k’ugunta

sunyi nisa suka ji Yasir na k’ok’arin bud’e k’ofa da d’an sauri hayfa ta janye jikinta ya shiga d’aki

Zama tayi gefen gado ta rik’e kanta tana tanbayar kanta “mai yasa ta fara biyewa wannan talakan da ba zama tayi da shi ba”?

d’an ajiyar zuciya tayi tace in kuma bana sakar masa jiki bazan samu damar sanin kasarnan ba bare har na samu na tafi a lokacin dole ya bani takarda na nema kamal mu shirya na fara karatuna da wannan tunanin taji nutsuwa a zuciyarta tana zaune taji yasir na cewa to ka yiwa ogan café visarta ya k’are?

Yusuf yace eh kasan ana d’an d’aga k’afa wai bayan wata kafin hukuma ta shigo ciki kuma IA zan nema wani aiki gobe bayan pool wanda kaga in na had’a da café da pool da shi zan samu na ansar mata visar ko yaya ne

Yasir ya ce gaskiya tayi dace sosai da samunka a matsayin miji inama da Hamdiyya ce ta samu miji kamar ka

D’an murmushi Yusuf yayi yace meyasa kace haka?

Ita kanta hayfa ta nutsu tana saurarsu

Yasir yace ka duba yadda auren nn yazo maka babu shiri amma duk da haka baka tab’a danasanin auren ba sannan dukda nauyi da matsaloli da kake dashi kullum burinka sauke nauyin matarka da bata hakkinta kana burgeni sosai ba don nasan yadda wannan gimbiyar ya saye zuciyarka ba da na baka hamdiyya nasan ko bana raye ba zata tab’a kukan auren miji kamar ka ba!

Ajiyar zuciya hayfa tayi

Shima Yusuf ajiyar zuciya yayi yace “nagode”

Yasir yace yau wai me za muyi ya kamata muyi celebrating ko yaya ne

Yusuf yace eh ina tunani IA

Yasir yace ni zanyi komai sabida dama ban bada gudunmawar bikinku ba, wai ita madam da zata fara aiki yau ya za kuyi?.

Yusuf yace ay ita nata kamar tym d’in Gizela ne 4:pm zata fara ta tashi sai lokacin tashinmu d’aya

Yasir yace gaskiya ka fiya son yarinyarnan yanzu aikin nn da zai sosai kudin zai taimaka maka amma ka bar mata Allah yasa tana sonka kamar yadda kake sonta

Ajiyar zuciya Yusuf yayi yace munyi latti muje

Fita suka yi duka!

Yayinda hayfa ke zaune duk jikinta ya mutu jin hirarsu

STORY CONTINUES BELOW

Toh shi yaushe ya santa ya ke sonta haka?

Batada ansa ta mik’e ta duk jiki ba k’wari ta fito ta hada tea da bread ta zauna tana karyawa tanata tunanin hirar yasir da Yusuf. A Nigeria ammah ta sayar da waya 310k kash aka biyata a kasuwar makarfi plaza ta wuce taje ta tsaya conditions road kabala ta saya kujeru 150k ta biya ta saya generator 45k tayi d’an cefanen gida domin mijinta gyaran computer yake a kasuwar royal wataran ya dawo da kudi wataran babu dama ita ke rabin hidimarta shiasa duk burinsu kada hayfa ta shiga irin rayuwarsu

Bayan ta dawo gida tayi wanka tana falo yara suka dawo laraba ta cire musu kaya suka yi wanka suka ci abinci gaz ma ya k’are ta bawa laraba kudi taje refiling

Tana falon masu kawo kujeru suka iso kujerun sunyi kyaw sosai tana kallonsu tana k’arawa auren hayfa da yusuf albarka tana cewa tunma auren baije ko’ina ba kujerun masu L ne da 1sitter aka jera falon yayi kyaw bayan tafiyarsu ta fara tunani duk wata in hayfa Tana turo mata kud’i da ita da iyayenta da y’ar uwarta sun kusa fita wahala har abada

d’an murmushi tayi a ranta tana tunani wannan na d’aya daga cikin dalilinta na k’in kamal sabida yadda mutane zasu saka musu ido a gane daga jikinsa suke samu su da iyayensu amma Yusuf kuwa basu da matsala ba d’an Kaduna ba ne gashi babansa ya rasu shi yake jan ragamar arzikinsa ga shi ance danginsu ma can da nisa har sokoto

Sosai amma ke k’ara godewa Allah da samun Yusuf a matsayin wanda zasu cika burinsu da shi

Wayarta ta d’auka ta yiwa hayfa msg mai cike da nasiha da rarrashi akan ta rik’e Yusuf shine cikar burinsu da fitarsu kunya a idanun duniya.

Hayfa na d’aki a kwance ta gama gyaran gida tanata tunanin aikin da zata fara wannan aiki kuma sai asar ba safiya ba wane irin office ne wannan

d’an tsaki tayi tace ko da yake komai na turai daban da na Africa tana cikin tunanin su Yusuf suka shigo gidan

Yasir ya d’an kishingid’a falo inda Yusuf ya wuce d’aki direct

Ganin tana kwance yayi sallama muryarsa kamar ba ta namiji ba

Ansawa tayi a hankali saidai bata tashi daga kwancen ba

Tura k’ofar d’akin yayi ya kulle ya jingina bayansa da k’ofar yace “ki shirya muje kada muyi latti”!

a hankali ta mik’e yana kallonta doguwar riga ce jikinta kamar ko yaushe ya d’ameta ta shiga bayi ta wanke fuskarta dama tayi wanka ta d’an gyara fuskar ta d’ora abaya mai bud’ad’en gaba ta saka flat lopas tayi kyaw sosai

Kallonta Yusuf ke yi cike da so zata shafa humra taji muryarsa “ah ah kada ki saka”

d’an sakin baki tayi tana kallonsa ya rik’o hannunta ya jawo ta jikinsa yana mata wani irin kallo da nan da nan yasa gab’ob’inta suka fara sanyi

Yusuf ganin abinda yayi ya d’anyi yayi d’an tasirin sata saduda yayi murmushi yace “mu je” yana rik’e da hannunta itama ta kasa cire hannun suka fito falo

Yasir ganinsu ya saki murmushi yace d’an uwa ku ganku kuwa?

Hayfa ta sunkwi da kai sannan ta kasa cire hannunta daga na Yusuf

Yasir yace wallahi sabida junanku Allah ya halicceku kunyi masifar had’uwa

Ya kalli hayfa gimbiya barka da saninki da mu kayi

Kasa magana tayi gashi sai tanaji kamar tsoron Yusuf ta keji domin tanason cire hannunta ta kasa yi

Yusuf yace ka cika zolaya mu zamu wuce….

Yasir yace no muje tare kaga sai muyi celebrating ranarka a can

Yasir ya kalli hayfa yace “wai mai kika shiryawa mijinki na 27 d’in nan ne?

STORY CONTINUES BELOW

d’an sunkwi da kai tayi Yusuf ya d’an kalleta shima

Jin shiru yasir yace Ku muje to yasa takalmi suka fito suka nufi café

Koda suka isa Yusuf na rik’e da hannun hayfa har gun manaja ya gabatar da ita ga manaja

Baturen yana ta mamaki sosai na jin yadda hayfa ke turanci kamar bakar baturiya

Shi kansa Yusuf shagala yayi yana kallonta tana k’ara burgeshi suka gama magana

Mamaki ne ya cika hayfa tana jira a bata office sai manaja ya bata t.shirt ta juya tana kallon Yusuf jin ana maganar ko wani 15mnts a goge tebur kuma ta kasance mai fara’a sabida customers domin baturen tashin farko ya lura da jiji da kai da fad’in rai na hayfa

Bayan sun gama baturen yayi musu sallama yace suje Yusuf yasan komai zai nuna mata

Yusuf ganin hayfa na tsaye ya rik’o hannunta zuwa d’akin da ma’aikata ke canza kaya ya rufo ya d’ago fuskarta yana kallonta tuni har ta fara hawaye “itace za ta zama y’ar goge-goge ta saki wani irin jaririn kuka wai wannan wane irin k’addara ne

Janyota Yusuf yayi har k’irjinsa ya kwantar ya sunkuyar da kansa zuwa kunnenta kamar mai mata rad’a yace “ki daina yawan k’orafi akan tsarin Ubangiji in ba haka ba zai yi fushi da ke”

Kuka ta k’ara saki ya d’agota ya fara kissing d’inta sosai kafin ya sake ta ya d’ago hab’arta yace “yace albashinki ko wani sati a naira 110k kina ganin in ma yanzu bakida buk’ata kina turawa ana tara miki wata rana ba zaiyi miki anfani ba”?

Cikin mamaki ta d’ago tana kallonsa da alamar da gaske?

Girgiza kai yayi yace haka ne albashinki ko wani sati a naira idan kinada hidimar biki ko suna da kike so kiyi ihsani a  Nigeria kika yi hak’uri da wannan aikin kawai zaki iya fita kunyar komai in ya taso a danginki kafin Allah ya samawa rayuwarmu mafita mafi alkairi

Hayfa na sauraransa tana lissafi a wata naira 440k tab lallai da wannan ma zata fara fitar da y’an uwanta daga kunya

Sosai Yusuf ya lallashi hayfa sannan ganin gown d’in da ke jikinta hannunsa ya kai gwiwar hannunta ya cire mata abayar sama ya saka mata t.shirt d’in aiki a kai sannan yace ta bud’e d’an kwalin abayar ta yi lullub’i

Haka kuwa tayi ya mata peck a kumatu ya rik’o hannunta suka fito zuwa d’akin kayan aikin café da kansa ya d’auko mata kayan detergents da ake winkin teburan da su

Koda suka fito tuni wacce tayi aiki rana ta wuce Yusuf ya fara goge-gogen

hayfa na kallonsa yana aikin yasir na ta tsokanarsa ya share shi yana d’an mutmushi yayi kusan tebur biyar kafin ya juya ya kalli hayfa da yanayin so yace “zaki gwada”?

d’an girgiza kai tayi ta mik’a hannu ta ansa

Peck Yusuf ya mata a gaban yasir ta fara aikin kana gani kasan sam bata saba aiki ba

Yusuf ya koma suka zauna shi da yasir tebur 12 a falon cafen da k’yar hayfa ta gama mutane tuni har sun fara shigowa ta gama Yusuf ya raka ta taje ta fara ansar buk’atar customers tana kaiwa a saka a bata ta tazo ta ajiye ta d’an saki jiki kawai fuskar ce sai a hankali tun farko bata saba fara’ar ba

Haka take ta aiki magrib yayi Yusuf da yasir su kaje sallah can bayan café suka dawo shima Yusuf ya fara aiki

Hayfa da ta ga babu Yusuf ta d’an fara kalle-kalle taji wata na ce mata tebur na 6 da na goma da d’an hanzari hayfa taje ta kwashe kayan ta nufi kiching da su

Saidai sosai ta bushe ganin Yusuf na wanke-wanke shine jikinsa ya bashi a na kallonsa ya d’an juyo

Bata iya cire idanunta daga mamakin ganinsa yana wanke-wanke ba d’an mutmushi ya k’arasa gabanta ya ansa kayan yace “ki rik’a kulawa in ana yawan nemanki za’aga bakisan darajar aikinki ba”!

STORY CONTINUES BELOW

juyawa tayi a hankali jiyowa ma da tayi anata “khadija”….

Tana fitowa taga falon cafén a cike nan ta fara bi ko ina tana ansar buk’atarsu

9:23 pm suka tashi aiki su duka suka kamo hanya saidai yasir yace suyi gaba yana zuwa

A hanya suna tafiya hayfa na satar kallon Yusuf wani iri take ji ya fara bata tausayi saidai da shima ya juyo take juya fuskarta da sauri haka har suka k’araso gida

Wanka hayfa ta wuce tayi ta fito ta zauna gefen gado tayi tagumi tana tunanin yadda rayuwarta ke sanjawa kamar a mafarki

Ta dad’e tana tunanin duk ranar da zata shigo turai sai don karatu da hutawa da holewa

Ajiyar zuciya tayi “yanzu Allah kad’ai yasan halin da mominmu ke ciki”…

Tana zaune tanata tunani Yusuf ya shiga shima yayi wanka ya fito ya saka wata shirt fara da dogon farin wando yayi kyaw dukda kayan ba wai na gayu ba ne

Yana zaune falo yana tunanin ina yasir ya tsaya ga lokacin aikinsa yayi zaiyi latti

Yaji motsin bud’e k’ofa yasir da ledoji biyu ya ajiye kanta yace “na kira wani colleague d’ina ya kamamin aiki sai 12:am zanje yau za muyi  celebrating bufday d’inka

Yusuf mamaki duk y cika shi, “yasir yace ina gimbiya”?

Yusuf ya mik’e ya shiga d’akin tana zaune inda ya ganta tun d’azu

d’an gyaran murya yayi yace ki zo falo

Kallonsa tayi tace “Na gaji sosai”…

Ajiyar zuciya yayi yace kada ki damu ba aiki za kiyi ba…

“Toh” tace ya fito ta saka doguwar rigar less ja ta d’aura d’ankwalin ba tayi make up ba ta fito falon ta gaida yasir

Mik’ewa Yusuf yayi ya rik’o hannunta ya zaunar da ita kusa da shi yana kallonta..

Murmushi yasir yayi yaje kanta ya ciro cake d’in a jakar ledar ya juye musu chips da kaza ya fito musu da coffee na take away da ya ke ledar duka ya kawo yaja d’an k’aramin center tebur d’in gefen falon ya d’ora

Hayfa ke kallon cake d’in na bufday an d’ora 27 a kai ta juya tana kallon Yusuf wato yau yake cika 27yrs amma tsawonsa da kwarjininsa kamar ya kai 30 d’an sunkwi da Kai tayi

Yasir yace madam ki bud’e mana da addu’a nasan ke malama ce

d’an ajiyar zuciya tayi kafin ta fara addu’a duk suka tsaya suna kallonta inda ta jero addu’oi sosai kafin suka shafa

Yasir yace to muna binki gimbiya yunwa mu ke ji..

D’an kallon Yusuf tayi kafin ta mik’e a hankali taje kanta da d’ebo plates ta dawo duk ta zuba musu chips da kazan ta mik’awa kowa kafin duk ta mik’a musu coffee saidai ita ta kasa cin na ta

Yusuf bai damu ba domin kamun kan hayfa na burgeshi sosai

Bayan sun gama ci ta d’auko k’ananun plates ta yanka musu cake still banda ita

yasir ma yasan ganinsa yasa ta kasa cin komai so yana ta sauri yayi yayi ya wuce aiki

Yusuf ne ya yanka cake d’insa na farko ya rik’e hab’arta yana kallonta hayfa da ta gane manufar Yusuf ga yasir kunya a dole ta bud’e baki a hankali ya saka mata yasir d’an duniya da sauri ya rik’a watsa musu pic sunyi kyaw sosai yayi musu tafi hayfa ta sunkwi da kai

d’an kallon agogo yayi 11:28 pm ya kalli yusuf yace bari na wuce sai da safe

Yusuf yace “OK” take care yayiwa hayfa ma sallama ya wuce

Yana fita hayfa ta mik’e Yusuf ya rik’o hannunta yace “baki ci abinci ba”!

Ya dawo da ita ya zaunar ya fara bata da kansa tun tana k’i har ta amince ta cinye domin sosai ta gaji ga yunwa ta sha coffee zai bata cake tace ta k’oshi sai da safe

Kwashe kayan tayi ta saka sauran cake a fridge ta wuce d’aki

Shima shiru yana zaune falon bai kwanta ba haka itama tunda ta shiga ta kasa kwanciya duk tunani ya isheta za taso tasan waye Yusuf ko kuma waye ta aura koda kuwa bata sonsa…

********

Haka rayuwarsu taci gaba Yusuf na iya k’ok’arinsa na sauke nauyinsa na miji sai hayfa da tuburan ta fara gane rayuwa domin jibi za ta karb’a albashinta na h’ud’u inda ta fad’awa Yusuf tanaso ya turawa mominta kud’in tana tara mata

Haka kuwa akayi Yusuf bai ko damu ba ganin hayfa bata bar ko dala d’aya a hannunta ba suka had’a kud’in tas Yusuf ya turawa ammah.

Ammah na gida yau suna hutun break taji msg ya shigo ta mik’e ta bud’e ganin w/Union Canada kud’i har 410k naira wani irin tsalle ta daka tana mutsuka idanu suna waya kusan ko yaushe da hayfa ko jiya sunyi waya ba tace zata yi aike yau ba ganin sai ma jibi wata zai k’are

Sosai ammah ke shiwa hayfa da Yusuf albarka nan ba b’ata lokaci ta maida kud’in accnt d’inta ta yiwa grp d’insu trnsffr na 250k yadda zata k’ara samun sauk’in albashinta tayi maza ta gama da bashin domin na banki mai sauk’i ne tunda akwai takardun gidansu

Nan ta fara murna dama ga azumi ya kusa za tayiwa iyayensu cefane sannan ta yiwa Adda suwaiba itama tayi nata kafin wani watan

Murmushi ta k’ara yi lallai in hayfa tana yiwa mijinta biyayya sai ta canza gida taje ta Kama haya a Jabi road kafin hayfa ta saya musu gida

A Toronto sosai hayfa ta dena wasa da aiki ganin Yusuf ya bar mata harda wanke-wankensa albashinta a naira ya kai 700k a wata inda shi Yusuf ya samu aiki a club d’in su yasir suna tafiya tare su dawo su wuce pool saidai yana neman wani aikin shi baya son hayaniyar club d’in

Abin gwanin tausayi da sha’awa domin har yanzu hayfa na da burinta na zama mai kud’i ta cikawa y’an uwanta burinsu su duka ta saya musu gida da mota saidai a ganinta da aikin café hakan zaiyi wahala ganin har yanzu ma basu gama basusukansu ba dukda wata nn daya kama duka albashinta 700k zata turawa mominta gashi tanada burin ta maida yaran ammah zamani inda itama tayi karatu gashi tanaso ta fara university ga ga ga buri dai birjik gasu

A Nigeria Alhaji shamsu Ciwon sugar ya sashi gaba sosai suna ta shirin tafiya India saidai sunyi waya da Yusuf tuni ya bashi hak’iru cewa zaiyi hidimar sabon residents permi da gdan zama ga k’anninsa sun fara karatu kasu ya musu hidima don haka sai nan da wata biyu zaici gaba da aike

Sosai alhaji shamsu ke tunani yana tausayawa Yusuf yaron yanada k’ok’ari rayuwa bata zo masa da sauk’i ba da jibi shi zai wuce India ya kira Yusuf suyi sallama

Yusuf na kwance falo ya dawo pool yasir yaje embassy hayfa ta fito cikin shirinta na zuwa café ta fito har yanzu babu abinda ya k’ara shiga tsakaninta da mijinta tun bayan gwajin farko saidai suna d’an mu’amalar sama-sama dukda sosai hayfa ta fara sauka daga iya shegen jiji da kaid’an tsayuwa tayi gefen kujerar da yake ta ce “zan wuce”+

Jin shiru ta d’an juya tana kallonsa taga idanunsa a runtse kamar dai bacci ya keyi

d’an k’ara maimaitawa tayi “zan wuce”…

“Toh” yace cikin wata irin murya da ita kanta bata san sanda ta juya sosai tana kallonsa ba sai yanzu ta lura kamar bayada lafiya

d’an k’arawa tayi gabansa tace “baka da lafiya”?

cikin muryarsa mai gard’i kamar ba namiji ba yace “no bacci ke damuna”

“OK” tace ta juya zata fita taji muryarsa “pls ki rik’a kula da kanki”…

“Toh” tace cikin sanyi murya ta wuce cike da tunani

A taxi tunani take sosai ta rasa inda aurensu ya ke dosa ta sani bata sonsa amma ta fara jin alhakinsa na rashin bashi hakkinsa duk kuwa da har yanzu tanada burin rabuwa da shi ta samu shiga jami’a ta gama ta koma Nigeria a lokacin koda anji bata da aure babu wanda yasan yaushe auren ya mutu…

Bayan fitarta Yusuf ya kira Ahmad suka yi fira da shi da qassim sosai akan karutunsu da rayuwarsu a Kaduna.

Koda hayfa ta isa aiki yau tana shiga tsabar hamkalinta baya jikinta ganin ta kusa lati tayi karo da wani bature da ke shirin fita cafen

Tanata bashi hak’uri shi kuma ya shagala kallonta tun daga sama har k’asa

Sai da ta gama bashi hak’uri ta wuce ya dawo hayyacinsa ya juya tuni har ta fara aikinta zai k’arasa shiga ciki yaji wayarsa na k’ara ya d’aga

OK” ganinan zuwa yanzu kuma da albishir mai dad’i da nasara ya tsinke wayar ya bar cafen cike da farin ciki…

Haka hayfa ta gama aiki ta wuce gida su Yusuf da yasir na ta shirin wucewa café ta gaishesu ta wuce d’aki

Yusuf ne ya bita ya shiga tana k’ok’arin cire rigar jikinta ya tsaya bayanta ya zuge mata zip d’in rigar ta fad’i k’asa ya fara shafa mata bayan

Wani mugun numfashi ta ja ta runtse idanunta bata motsa ba yaci gaba har ya d’ora hannayensa kan hips d’inta yana shafawa

Janyota yayi jikinsa yana jan numfashi yana shafa k’irjinta ya kama nipples d’in ta cikin brasia yana wasa da shi

Sun d’an fara nisa Yasir ya fita Yusuf yaji motsin fitarsa ya juyo hayfa yana kallonta idanunsa duk sun canza ita kanta ta d’an rud’e

Had’a kansa yayi da na ta hancinsu na gugan juna yana kallon idanunta yace “Ina sonki” ya mata peck a kumatu ya fito ya yasa takalmi suka wuce

Tunda ya fita hayfa ta zauna gefen gadon ta fara hawaye mai yasa haka yake faruwa da ita? Saidai kamar a mafarki zuciyarta ta tunano mata maganar Yusuf “in kina yawan k’orafi akan tsarin ubangiji zaiyi fushi da ke”…

Shiru tayi tana tanbayar kanta shin waye “Yusuf Suleiman”?

Mai ya kawo shi Canada? 

********

Paolo Santiago Dasilva and Nawfal Fareed Fation Canada..

Armando Martinez ya kalli Bunil Farhan yace

Yarinyar in ka ganta tayi ne kawai ita ce new face d’in da muke nema tun last year

Bunil yace amma kace bak’a k’arama ce baka ganin ba zata iya biya mana buk’atarmu na yanzu ba saidai ko mu d’auketa sabida gaba?

STORY CONTINUES BELOW

Armando yace ina ina fad’a maka yarinyar she’s perfect ne kawai in muka gayyaci Naomi kambel na 2wks za tayi mata tranning d’in yarinyar yaso sai mu kira conffenrance mu d’aga show d’in mu zuwa 4wks masu zuwa…

Bunil yace amma baka gani hakan zai jawo mana surutan b’atanci ga gidajen jaridu da France Italy su daina had’a

show da mu?

Armando yace na tabbata bayan Naomi ta mana coaching yarinyar mun fidda ita a matsayin new face d’inmu na Summer duniyar d’inkunan duniya zasu san lallai munada dalilin d’aga show

Bunil yace OK! Toh amma kayi magana da yarinyar ne?

Armando yace zanyi jiyan ka kirani…

Bunil yace Ok toh ka tabbata a café d’in take aiki?

Armando yace da idona fa na ganta da kayan aiki tana aiki

Bunil yace OK sai kaje ku gama magana a yau kaga bamuda sauran lokaci dayawa sabida har Qatar sun biya nasu d’azu accountant Ya ke fad’amin

Armando yace nan da 1hr zan wuce sabida naga aikin yamma ta keyi ….

Bunil yace OK ni zan wuce Milan gobe da safe sai muyi magana

Armando yace OK safe journey..

Tana d’aki tana saka wani pencil jeans d’inta tasa suck sabida Yusuf ya k’aro mata rigunan sanyi biyu sun zama shida amma wannan masu tsawo ne zuwa gwiwa ta gama shiryawa tasa t.shirt d’inta ta d’ora rigar sanyi a kai in ta isa café ta cire

Ta fito d’aki kenan Yusuf zai shiga, Tsayuwa su kayi duka sai Yusuf da ke k’are mata kallo daga sama har k’asa

d’an sunkwi da kai tayi

Cikin muryarsa mai d’an kashewa hayfa jiki yace ” ki cire wannan wandon bana so”!

d’agowa tayi tana kallonsa da alamar bata gane ba

Shima kallonta yayi yace “eh bana so ki cire gara ma sicket”

Hayfa ta kalli jikinta da wandon ta d’an sake d’agowa ta kalli Yusuf tana mamaki nan fa turai ne to ko Nageria tana sawa ta d’ora jijabi a kai

K’arasawa yayi gabanta ya d’aga hab’arta yana kallonta yace “aikin kansa inda inada halin baki komai bazan barki kiyi ba sabida Inada tsananin kishi akan duk abinda yake mallakina”

d’an shiru tayi bata san mai yasa ba yanzun tana jin nauyinsa bata son yin jayayya da shi

Gaban wardrobe ta koma ta cire wandon yana tsaye ta d’auki wani bak’in bud’ad’en sicket ta saka ta yane kanta ta juyo

d’an rik’o kanta yayi ya mata peck a goshi ya rik’o hannunta yace muje in raka ki na dawo

Suna café Armando yana shiga ai kuwa ya tsaya kallon yadda hayfa tayi wani masifar kyaw tayi kamar wata world Model…

ganin yadda Armando ke kallon hayfa ran Yusuf ya d’an b’aci domin yana shirin wucewa ne ma gida hayfa tana kantar su na cafe tana rubutu

d’an juyawa Yusuf yayi yaga ita bata ma san mai yake faruwa ba ya wuce ya fita yana hararar Armando

Bayan tafiyar Yusuf Armando ya zauna ya kira wata colleague d’in hayfa ya bada order abinda yake so ta wuce

Saidai da aka had’a masa capocino da black cookies ordersa aka bawa hayfa

Ajiyewa tayi zata juya taji yace “sorry pls 2mnts khadija”!

Hayfa cike da mamaki ta juyo tana kallonsa

d’an murmushi yayi yace Last wk naji sunanki tun ranar na ke son magana da ke

Jin bata ce k’ala ba yace pls ko zaki iya zama minti biyar?

STORY CONTINUES BELOW

Hayfa fuskarnan babu walwala tace “ina aiki”

Yace babu damuwa oganku abokina ne na fad’a masa zanyi magana da ke

K’ara b’ata fuska tayi tace “maganar me”?

d’an murmushi yayi sosai yarinyar ke da komai na ainihin model jiji da kai kamar Naomi kambel da Gizela bunchel

K’ara murmushi yayi yace karki damu pls ki bani aron minti biyar zanyi k’ok’ari na fad’a miki komai a mintuna biyar d’in

a dole hayfa ta zauna saidai still babu walwala a fuskarta

Armando ya kalleta yace fad’a mata sunansa da komai yace ni Agent ne na su models ina yawo k’asashe har Africa neman matasa irinki masu kyawun halitta a yanzu haka muna gab da fitar da sabon collection d’inmu na kayan sanyi to na nan k’asar bamu samu sabon fuska ba tunda na ganki nasan ke ce fuskar da muka dad’e muna nema, Idan kika amince aiki da mu za kiyi kud’i kiyi yawon duniya

Shiru yayi kafin yaci gaba contrack d’inmu na aikin nan zamu biya ki $5000 kuma aikin 2dys ne saidai akwai tranning da coaching da za’a miki na 2wks kafin aikin ya mik’a mata kati yace gashi kije kiyi tunani pls gobe war haka ki bani ansa

Shiru hayfa kamar ta bushe a zaune sam ta kasa magana tunaninta nawa ne $5000 a naira?

d’an murmushi yayi yace kada ki damu ki bari in kika koma gida kiyi tunani a nutse

da haka ta dawo hayyacinta ganin ta kasa ansar katin ya ajiye mata gabanta ya mik’e ko order sa bai ci ba

Mutane tuni suka fara cika cafen inda Clara tace “khadija”

a hankali ta mik’e ta d’auka katin ta saka a aljuhun sicket d’inta taje ta fara ansar orders zuciyarta cike da tunani kala-kala

Bayan Yusuf ya isa gida yayi wanka yayi magrib yana ishaa yasir ya dawo suka yi girki saidai Yusuf ya kasa ci yana tuna baturen da ke ta kallon hayfa baisan mai yasa ba amma tunda ya kalli baturen zuciyarsa ta kasa samun nutsuwa

Yasir ne ya dawo da shi tunaninsa “wai tunanin mai kake yi haka”?

Ajiyar zuciya Yusuf yayi yace no bacci na ke ji ne..

Yasir yace bari ni na wuce sai ka k’araso nasan dole sai an jira dawowar madam kamar kullum

Ajiyar zuciya Yusuf yayi yace “OK” sai na k’araso

Bayan tafiyar yasir ko 10mnts baiyi ba hayfa ta shigo saidai ganin Yusuf zaune hannunsa rik’e da kansa ya sa ta tsayiwa kad’an

d’agowa yayi yana kallonta itama haka

Mintuna 2 ta cire idanunta ta fara k’arasawa za ta shiga d’aki taji muryarsa “zo”

d’an jimm tayi kafin ta k’arasa d’an nesa da shi ta tsaya

mik’ewa yayi yace “ya aiki”?..

Kallonsa tayi sosai a karon farko taji sosai ya bata tausayi saidai bata bari ya gane ba tace

Alhamdulillah…

Yace kije ki canza kizo mu ci abinci kafin na wuce…

“Toh” tace ta d’an matsa ta wuce ya bi ta da kallo a yanzu jiji da kanta ya fara burgeshi domin har yanzu ko yasir ba ta sakarwa fuska…

Yana zaune kusan mintuna goma sha biyar ta fito sanye da doguwar riga saidai idanunta duk a tsume kana ganinta kasan a gajiye ta ke dama tana yin sallah a café

Mik’ewa yayi ya rik’o hannunta ya zaunar da ita kusa da shi ya d’auko mata spoon ya saka mata a gabanta

d’an kallonta yayi yace “bisimillah”!

Cikin nutsiwa ta d’auki spoon d’in suka fara cin abincin saidai su duka basu wani ci dayawa ba ya kalleta da alamar bata ci komai ba cikin shagwaba a karon farko da ta masa tace “bana jin yunwa dama”!

STORY CONTINUES BELOW

Bai ce k’ala ba ya ajiye spoon d’insa shima yace “pls ki had’amin coffee”

“Toh” tace ta mik’e ta shiga kanta

Bayan ya gama sha yasa takalminsa ya mik’e ya rik’ota ya manna da k’irjinsa yana kallonta sosai ya ke jin sha’awarta saidai ya daure ya mata peck a goshi yace “ki kula da kanki sai da safe”!

Hayfa ta tsinci kanta itama da kallonsa kamar ba ta son ya tafin

Mintuna kusan uku ya wuce….

Tun bayan fitar Yusuf ta zauna dinning sosai ta fad’a tunanin aikin da mutumin nan ya mata magana, Tanbayarta ma shine nawa ne $5000 dollars

A gefe tana tunani in ta ansa aikin ya za tayi da café domin gaskiya zan ansa tace a zuciyarta tunawa da y’an uwanta da iyayenta da ta keyi ya kamata tabbas su wanke gidansu da junansu daga talauci tanada burin  tallafawa y’an uwanta su inganta rayuwar yaransu kamar yadda itama y’an uwanta suka inganta mata nata duk kuwa da burinsu bai cika ba a kanta

Ajiyar zuciya tayi a gefe zuwa yanzu ta fahimci Yusuf mutum ne mai zuciya da dogaro da kansa da jajircewa akan kansa dukda bata sonsa bashida dalilin da zata zauna da shi domin burukanta ba zasu cika ba, amma sosai yanzu tanajin shakkarsa da tausayinsa dukda bata san komai ba a kansa

Ajiyar zuciya ta k’ara yi dole zan ansa aikin indai zanyi kud’i na rabu da wannan wahalan na wadata y’an uwana sannan na fara skull gobe zanyi magana da shi sosai naji yadda tsarin zai kasance kafin na yanke hukunci da wannan tunanin taji nutsuwa ta mik’e a kujerar ta d’an runtse idanunta sosai take jin gajiya aikin café kullum ta dawo gida sai taji ciwon jiki.

4:11am yasir ya kalli Yusuf yace wai yanzu visar 3mths ka ansar muku?

Yusuf yace “eh kasan k’annina sun fara skull dukda sunyiwa kansu hidima sosai na biya musu accommodation da registrations fees sai su da innarmu suka k’arasa sauran hidiman

Yasir yace gaskiya kanada k’ok’ari ga danginka ga kanka ga matarka “wai ni tasan duk wannan hidimar kuwa”?

Yusuf yace to hidimarta ne ko nawa da zata sani?

Yasir yace ay maybe zata iya yafe maka wasu hakkokinta na kanka…

Yusuf yayi d’an tsaki yace pls ka daina magana haka a karon k’arshe

Nine mijinta dole na sauke mata hakkokinta na kaina koda itace shugabar k’asa

Yasir yace ai shikenan, ni zan jira Tiffon kasan yace na kama masa yaje gida budurwarsa tazo sai ya iso zan k’araso in yayi latti mu had’u pool

Yusuf yace “OK” yasir yace yawwa ya d’ayan aikin da kaje rannan wannan supermarket?

Yusuf yace sunce sai nayi wani course 3mths kafin su d’aukeni, shine na duba course d’in online sunce akwai na yamma inaso da nayiwa Alhaji aike wannan watan abinda ya saura sai na fara course d’in

Yasir yace gaskiya kayi ko in kanaso na ara maka kud’in ba yawa nima don watan nan bazan yiwa Aunty da mama aike ba

Yusuf yace no haba ka barshi zan biya nx wk d’in IA na fara

Yasir yace shikenan su kayi sallama Yusuf ya nufo gida duk a gajiye ga bacci

Koda ya iso hayfa na ta baccinta na gajiya a falo a hankali ya k’arasa kujerar ya tsuguna wajen fuskarta yana kallonta yana shafa fuskarta a hankali

d’an bud’e idanunta tayi ta ganshi ya sakar mata d’an murmushi kad’an yana kallonta

Fara shafa k’irjinta yayi yana kallonta rigar jikinta a matse k’irjinta har wuya saidai gajiyar da ke jikinta ya saka ta runtse idanu

Yusuf ganin haka ya zame hannunsa a hankali ya janyota k’asa ya d’ora k’irjinsa ya rugumeta a samansa kwance k’asan carpet.

Hayfa bacci da gajiya suna jikinta don haka baccinta taci gaba da yi jikinsa hankali kwance

Shima baccin yake son yi duk da beyi niyar yi ba sabida ya ga asuba ta yi ga tunani ya dameshi shi bayason aikin club d’in nan sosai yake fatan ya samu yayi course na zab’arwa customers kayan buk’atunsu ya fara aiki a supermarket d’in da yaje neman aiki ga alhaji yayi tafiya India babu lafiya ga shi ba damar chart yau ya saya k’aramar waya zai bawa hayfa na sa

yana ta tunanin aka kira sallah yana son d’aga ta saidai ta bashi tausayi yanayin da yake jin numfashin gajiya da take fitarwa a baccin

A hankali ya fara shafa mata bayanta cikin salon d’aga mata sha’awa har a hankali ta bud’e idanunta ta ganta saman Yusuf a kwance da sauri ta bud’e idanu ta d’aga tana kallonsa

Baice k’ala ba ta mik’e a kunyace ta shiga d’aki da sauri shima mik’ewa yayi ya bita zaiyi wanka yayi alwala yayi ya fito tana zaune ya fito ya tayar da sallah

6:38am ya kira yasir yasir yace bazai dawo ba su had’u pool

Baayan ya gama waya da yasir ya cire sim d’insa ya fito da pack d’in wani sim da wata k’aramar waya ya maida sim d’insa ciki wancan sabon sim ya saka a wayarsa ya mik’e ya shiga d’akin.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE