KASAR WAJE CHAPTER 7 BY MARYAM DATTI

KASAR WAJE CHAPTER 7 BY MARYAM DATTI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Bayan fitarsa hayfa tayi shiru domin itama yanzu yanayinta ya fara sata zargi domin yanzu take tuna bataga al’adarta ba na wannan watan saidai da sauri ta kawar da tunanin domin tunawa da tayi daga bayan nan da sun gama sex take shan ruwan d’umi da gishiri sabida kiyaye ciki bataso ta d’orawa Yusuf wahala bayan wanda suke ciki gara sai sun samu gidansu inma za tayi cikin ba suna gida d’aya da yasir ba+

da wannan tunanin ta tashi taci gaba da aiki…

Koda su Yusuf suka dawo café yasir ya wuce motsa jiki kafin magrib inda Yusuf ya d’an kwanta kafin hayfa ta dawo

Tana hanya ma taxi wari taji yana mata a dole ta toshe hancinta har ta iso gida
Tana shigowa ta ganshi yana bacci ta kulle k’ofar zata wuce d’aki ya rik’o hannunta ya dawo da ita jikinsa

Bud’e idanunsa da ke kashe mata dukkan gab’ob’i yayi yana kallonta
d’an ajiyar zuciya tayi tace “barka da gida” !

Murmushi yayi ya janyota jikinsa ya kwantar yana shafa bayanta ajiyar zuciya ta fara saukewa a hankali

Jin jikinta da d’an zafi a hankali kamar mai rad’a yace “mai yake damunki”?

Mugun bugawa k’irjinta yayi ta d’anyi shiru kafin tace “mura”!

Yace kinsha wani abu?

Tace “eh” ba tason yin komai sai bayan tasan damuwarta

d’ago ta yayi yace “gashi ni da yunwarki na dawo”…

d’an shafa fuskarsa itama tayi ta maida kanta k’irjinsa tace “ina shirye a duk lokacin da kake so”!

d’an ajiyar zuciya yayi yace no ki huta jikinki ya sauka, kinci abinci?

Ah ah tace bana jin yunwa..

Yace no dole kici abinci kinji? Anjuma bayan munyi sallah
“Toh” tace tana kwance still jikinsa zuciyarya cike da sak’e-sak’e
Suna kwance haka hayfa a samansa har aka kira magrib ya d’agota yayi mata peck yace muje muyi alwala
Bayan sun idar da magrib ma k’ara kwantar da ita yayi jikinsa shiru su duka saidai zuciyoyinsu ke aiki

Shi Yusuf zuwa yanzu sauran kusan 6M kud’in alhaji amma dikda haka ya fara matsuwa yaga hayfa da ciki
A b’angaren hayfa wani irin mutuwar son Yusuf ta kamu dashi takan kashe lokaci tana tunaninsa duk kuwa da cewa a yanzu sukan ma kwana gado d’aya ko falo in ya dawo aiki club duk kuwa da tana pretending bata nuna masa hakan sam shima bai damu ba ganin zuwa yanzu tana k’ok’ari wajen bashi hakkinsa na mijinta

Shafa cikinta yayi yace “Allah yasa ina dab da samun wani alkairi daga nan
d’an shiru tayi saidai itama zuwa yanzu yadda take jinsa tana ji kamar ta shigar da kanta jikinsa ko ta cire zuciyarta ta bashi amma gaskiya bata yadda su haihu a irin wannan yanayin ba

Jin shiru ba tace komai ba ya d’agota ya juyo ta suna facing juna tana son sunkwi da kai yace “pls luk at me”.!

d’an d’agowa tayi tana kallon idanunsa da taga wasu abubuwa na fitowa daga ciki suna shiga nata yace ” pls kada kiyi bak’in ciki in muka samu k’aruwa sabida yanayin rayuwarmu bazai hana mu rik’e abinda Allah zai bamu ba kinji”?

STORY CONTINUES BELOW
Ita mamaki ne ma ya kamata kamar yasan mai take tunani… Taji muryarsa zuciyata tana tare da ke a kowa ni dak’ik’a da kike kusa dani koda baki yi magana ba tana sanar dani abinda ke zuciyarki

Ajiyar zuciya tayi tai shiru. …

d’an d’ago fuskarta yayi yace “har yanzu kina bak’in cikin aurena ko”?

da sauri ta girgiza kai har k’wallah ya zo mata. . .

d’an ajiyar zuciya shima yayi yace pls kada ki k’ara domin ni in za’a bani zab’i da ke ko a mallakamin duniyar nan da abinda ke cikinta ke zan d’auka
Matse k’wallah tayi ya k’ara rik’o hab’arta yace pls zuciyarki kawai na ke so tafimin duk wani abu da zan mallaka a duniya
Sosai hayfa ke hawaye tana kallonsa
Shima kallonta yake yayi shiru kamar mai tuna wani abu saidai yana fata ne Allah ya bashi abinda zai wadata dashi
ganin kamar shima zaiyi k’wallan ta bud’e bakinta da k’yar tace “nima ina sonka”…!

Kallonta yake kamar bai gasgata maganarta ba saidai yaga alamar gaskiyar a idanunta d’an rik’o hannunta yayi yana kallo kafin daga bisani yayi kissing hannun ya rungume ta..

Tunda da Yusuf ya wuce pool itama tayi shiri dukda ba dad’in jikinta take ji ba har yanzu. A haka ta lallab’a ta shirya tana falo tana saka takalmi driver ya iso ta fita suka wuce..

A kamfanin Raudha da liliana ke ta hira inda Liliana ke tanvayar Raudha ina Zakir ya kwana da kawo mata information d’in Yusuf?

Raudha tayi murmushi tace ya kawomin iya abinda zan iya mora domin kuwa har gidan gayen ya sani saidai yace basu cika zama sunma fimu wahala domin 80%100 na rayuwarsu aiki suke

d’an dariya Liliana tayi tace ay dole suyi aiki dama gadin club ba isar rayuwarsu zaiyi ba nima wancan guy d’in yamin fa saidai shima d’an wulak’anci ne domin ranar da muka fara ganinsu na saka masa katina amma bai tab’a kirana ba
Tsaki Raudha tayi tace ay da ganinsu za suyi taurin kai amma ni a haka zanyi duk yadda zanyi sai munyi soyayya dashi k’ila ma harda aure

Liliana tace wato shiasa kika ce mu daina zuwa club d’in?

Raudha tace eh mana, sabida mu musulmai laifi ne zuwa club a addininmu

Mugun dariya liliana ta saki ta kalli raudha tace “yanzu ke dama akwai abinda kike aikatawa na nuna ke musulma ce? Kodai sabida yanzu kinga musulmi kina so?

harararta raudha tayi tace “eh” yanzu dole na fara abubuwan mu na musulmai sabida naja hankalinsa
Suna cikin hirar Hayfa ta shigo d’an taayuwa tayi suka gaisa da su dukda raudha na bak’in cikin ganin hayfa kamar ta mutu amma da ke ta iya duniyanci sai tana basarwa sabida so ta keyi ta nutsu ta rusa hayfa ta bayan gida ba tare da kowa yasan tanada hannu ba domin tasha alwashin ita zata samu bangon “GALA” na Milan
Koda hayfa ta wuce taje d’akin canza kaya zuwa na motsa jiki tana fitowa suka had’u da Armando yace “yawwa muje Dr na jiranki”

Binsa tayi a baya suka wuce can da d’an tafiya suka isa office d’in Dr na kamfanin

Armando yayi masa bayanin yayiwa hayfa check up
Dr yace sai ta fara fad’a mana abinda ke damunta tukuna
Armando ya kalli hayfa
da k’yar ta kalli Dr tace amai tayi sau biyu sai yawan tashin zuciya da nauyin jiki da d’aurewar mara

Kallon Armando Dr yayi domin ko bai yiwa hayfa test ba ya gane abinda ke damunta saidai duk da haka ya cewa Armando bari mu fara gwada jininta ya d’iba ya kira nurse ya bata

STORY CONTINUES BELOW
Tunda Dr ya d’iba jininta k’irjinta ke bugawa tana jin mugun tsoro na shigarta Armando na kula da ita shima ya fara shan jinin jikinsa ciki ne da hayfa

Suna gun Dr wata nurse da ta kawo masa result d’in da ya bata ta kawo masa result ya duba “positive”
Ya kalli Armando ya mik’a masa result d’in
Armando ya gama dubawa ya gani ciki ne da hayfa don haka ya kalli Dr yace muna dawowa yanzu ya kalli hayfa yace muje

Jiki babu k’wari ta mik’e suka fita shi Dr ma dariya hayfa ta bashi yadda take kamar wadda tayi wani babban zunubi dake su wannan ba sabon abu bane a gunsu

Haka hayfa da Armando suka wuce su Raudha da ke ta Motsa jiki abinsu saidai yanayin da su raudha suka ga hayfa ya sasu zargin wani abu gashi daga b’angaren clinic d’in kamfanin suka fito hakan yasa liliana tace “anya ba ciki bane da Khadija”!

Raudha tace mai yasa kika ce haka?

Liliana tace duk kwanan nan batada wani k’wari gashi rannan coffee ma shanshanawa ta rik’ayi k’arshe ta kasa sha kinsan nima haka lokacin da nayi ciki da Nadal kamar ita cikin ya rik’amin ko coffee d’in kamfanin nan bana so

Raudha tayi ajiyar zuciya tace munafuka amma kullum tana yi kamar wata virgin ko taro a ke maza na mata magana tana sharesu wai ita nutsatsiya to yanzu uban waye ya mata ciki ko a drink tasha

Dariya liliana tayi tace kika sani ko mugun son sairayin nata take shiasa bata kula wasu ko for fun Kamar yadda aka sammu models maza kamar kayan sawan mu suke

Tsaki raudha tayi tace I hate her yarinyar munafuka ce duk yadda za kayi da ita baka sanin cikinta amma bazan hak’ura ba saina bincikota
Liliana tace nima tana bani mamaki sam bata amincewa kowa tsabar bak’ar zuciya ga jiji da kan tsiya kamar tafi kowa

Tsaki raudha tayi tace bari nazo ki jirani…

Liliana tace ina zaki?

Tace sai na dawo zaki ji.
a office d’in Armando ya kalli hayfa yace kin gane? Babu ruwanmu da wanda kike kwanciya ko ince saduwa munsan dama kunada samarinku da kuke saduwa dasu amma in kin manta na tuna miki a cikin contract da kika yi signing yana rubuce ko aure za kiyi zaki sanar da mu sannan babu bare ciki dukda musan a lot suna ma fara son samun baby kafin auren amma dole sai in ka gama da mu… Raudha ta manna kunnenta da jikinta jikin k’ofar… Yaci gaba sannan yaushe kika fara aiki? Yanzu fa tauraronki ke shirin fitowa sosai ina tabbatar miki in kika maida hankali a 2yrs d’in nan zan sama miki contracts da zakiyi kud’in da jikokinki in kika tafiyar da kud’in da kyaw to baza suyi kukan talauci ba

Hawaye hayfa ke tayi sosai..
Yace wlh in Bunill yaji ma zaice laifina ne dukda munsha samun irin Case d’in nan da yara anan amma ke daban ce a gurina ina d’aukarki kamar k’anwata ta jini shiasa bazan bari ki b’ata wayinki ba 5mths ina aikin fito da ke idanun duniya sai da muka kusa cinma burinmu zaki b’ata komai
Ganin tanata kuka ya d’anyi shiru kafin yaci gaba “kinji yace cikin jst 3wks baiyi k’wari ba so bazai bamu wahala ba wajen fitarwa kinga saura 5dys aikinku ga sauran duk sun gama kintsawa ke kinata laulayi

Yanzu za muje allura ne kawai zaiyi miki cikin ya zube kamar wasa shikenan sai in kika gama wankin jinin ya baki protection na yadda ko kuna saduwa da saurayin ki babu maganar ciki

Sosai hayfa ta fashe masa da kuka har tana sheshek’a
Raudha tayi ajiyar zuciya lallaima yarinyar munafuka ce cire cikin ne take ma kuka kamar ita za’a zarewa rai
Tsaki tayi lallai da alama tana son wanda ya mata cikin sosai, saidai raudha addu’a ma take Allah yasa kada cikin ya fita ta juya ta koma gun su liliana tana tsaki

STORY CONTINUES BELOW
Liliana tace yaya?

Raudha tace munafukar nan gaskiyarki ciki ne da ita sannan ance za’a cire tanata kuka

Liliana tace k’ila tanason cikin.. Raudha tace ko kuma tanason mai cikin ba shegiya ashe tanada zuciyar son wani ma da irin shegen fad’in ranta

Liliana tace to yanzu ya za suyi da cikin?

Tsaki raudha tayi tace ay dole zata hak’ura in aikin za tayi kema kinsan k’aidar aikinmu

Liliana tace har ta bani tausayi bcs nasan mai take ji nima ina son cikin nadal dole na hak’ura gashi yanzu na rasa biyu ba nadal babu ciki…. Raudha tace amma ay kinada kud’i da ko wani namiji zai so budurwarsa na dashi
d’an shiru tayi kafin tace haka ne amma karki manta dayawan maza na kallonmu a matsayin mata marasa sanin darajar kansu sabida aikinmu

Tsaki raudha tayi tace ke ni ko ajikina tunda inada kud’i da kyawu da k’uruciya dole wata rana zan samu namijin da zai aure ni yana alfahri ya auri kamata
Liliana tace haka ne…

Raudha tace ni fatana ma Allah yasa kada cikin ya fita Armando tunda ya samu yarinyarnan yake fifitata a kanmu bayan da mu kamfaninsu ya k’ara shahara
Liliana tace ki rabu dashi munafuki ki duba ayyukan da ya samo mata a watannin nan ni nama rasa mai yarinyar keyi da kud’inta har yanzu ko mota bata hawa kuma naji Fabiola tace wai da iyayenta take zama har yanzu. Tsaki raudha tayi tace shiasa take wannan munafuncin kamun kan inda sunsan nutsatsiya ce uban wa yace su barta yin aikin models
Haka dai suna gulmarsu suna exercise…

A office d’in armando sosai hayfa ke kuka domin tabbas a ganinta batada zab’i daya wuce a zubar da cikin duba da yanayin samun Yusuf da rayuwarsu dama zai barta ta tallafa ne to ta sani bazai tab’a yadda ba domin yawancin abubuwan gidan ma yanzu inta saya da albashinta na café rok’on yasir take tace yace shi ya saya, ga $20000 tun na interview d’inta har yanzu suna ajiye bata kashe ba gudun kada Yusuf ya fahimci facakarta da kud’i ya fara zarginta

d’an saukar da murya Armando yayi yace “khadija”…!
Kinada kyaw da k’uriciya da rayuwa sosai a gabanki don haka kada ki wani damu nan gaba zaki k’ara samun yara sosai har ki gaji yanzu ki gina rayiwarki shine farko domin ko haihuwar yaro kika yi bakida k’arfin biya masa buk’atunsa yaron zai dawo yana tsanarki yana jin kunya da bak’in cikin kasancewarki mahaifiyarsa
Da kalamai da lallashi har hayfa ta hak’ura a cire ciki nan suka koma office d’in Dr gashi duk lokaci ya tafi ko exercise ba ta yi ba
Armando yacewa Dr kamar yadda aka saba ma’ana a cire cikin ya fita yace yana zuwa bayan an gama
Tunda ya fita hayfa ke kuka tana tuna kalaman Yusuf “pls kada kiyi bak’in ciki idan Allah ya bamu rabo”

Kuka ta k’ara saki sosai ta k’ara tuna kalmarsa lokacin da yake shafa mata ciki ” Allah yasa ina dab da samun alkairi daga nan gurin”…!

Sosai take kuka kamar ranta zai fita shi Dr ma mamaki take bashi sai kace wace za a cirewa rai nan wasu model d’in da kansu suke kawo kansu a cire musu
d’an rarrashinta yayi shima kafin ta d’an tsagaita kukan ya bata green riga yace tasa ya juya bayansa ta mik’e jiki ba k’wari ta cire kayan jikinta ta saka rigar ta koma gadon ya juyo yace ta kwanta
a hankali ta kwanta yayinda idanunta har lokacin hawaye suke zubdawa
Kallonta yayi yace ki saki jikinki sabida kar allurar ta baki wahala dayawa
ritse idanunta ma tayi idanunta na ci gaba da zubda hawaye sai jin allura tayi taja wani irin numfashi mai d’an nauyi kafin nan da nan ma bacci ya jata
A pool Yusuf bayan ya gama aiki yana pool d’in yara gun yasir yaji kansa ya d’an sara masa ya rintse idanunsa tare da rik’e gaban kansa saidai wani mugun fad’uwa yaji k’irjinsa nayi a yayinda zuciyarsa ke masa wani irin zafi
Kallonsa yasir yayi yace “lafiya”..?

d’an daurewa yayi yace kaina…

Yasir yace muje ka d’an kwanta ni bari naje na samo maka magani suka muk’e can d’an d’akin kayan aikinsu ne Yusuf ya shiga ya kwanta kan wata tsohuwar kujera dake d’akin yasir shi kuma ya fita pharmacy ganin har kamannin Yusuf d’in ya d’an canza
Hayfa da wani mugun murd’awar ciki ya saka ta farkawa daga d’an baccin da ya kwasheta a gigice ta fara kuka tana tab’a mararta Dr ma baya office d’in
Kuka ta k’ara saki domin jikinta har rawa ya keyi tana danna mararta kusan 20mnts saiga wata nurse ta shigo ta k’arasa gadon da sauri saidai tuni hayfa ta suma nurse d’in ta tab’ata bata damu da suman ba domin da alama hayfa bata tab’a cire ciki ba allurar ya mata k’arfi

Ruwa ta d’auko ta wanke mata fuska ta farfad’o saidai ko minti biyu ba tayi ba ta saki k’ara da su raudha duk suka d’unguma clinic saidai suna k’ofar suka ji nurse na cewa “sannu yanzu zaki huta ya fita sannu kinji”? don baki tab’a yi bane shiasa ya baki wahala haka nx tym ba zaki wahala haka ba

Hawaye kawai ke bin idanun hayfa sai jinta tayi a jik’e inda nurse ta fara bata agaji su raudha suka wuce suna dariya+

sai kusan 1:23pm hayfa ta d’an samu kanta tuni an nurse ta mata wanka da ruwan d’umi sosai ta gyarata tasa maida mata kayanta domin babu maganar exercise aka bata magunguna Armando yace ta huta 3dys a gida zai kira café ma ya fad’a sannan zaiyi arrangements a d’aga aikinsu zuwa nx wk da haka driver ya dawo da hayfa gida….

Bayan ta kulle gidan ta wuce d’aki ta kwanta ta tura ledar magani karkashin gado. Ta kwanta saidai hawaye ta fara sosai tana tunanin wai yaushe ta shigar da kanta wannan duniyar aikin? Mai yasa ta fara?

Saidai tsit tayi tuna aikin ke rufawa y’an uwanta da iyayenta asiri a yanzu saidai sosai hankalinta ke tashi in ta tuna Yusuf da aurensa a kanta take wannan aikin

Sosai tayi kuka kafin bacci ya kwasheta sabida allurai da magunguna da tasha tun a asibitin.

Yusuf da sam ko daya jarraba yin d’an bacci ya kasa zuciyarsa ke masa wani iri ga kansa yanzu yayi sauk’i saidai haka kawai yana jin babu dad’i a zuciyarsa

Yana kwancen yasir ya dawo ya bashi drug da sandwich ya d’anci yasha panadol inda yasir yace ka koma gida kawai ka kwanta a can ni zanma aikin yamman in ma ba zaka iya zuwa club ba kayi zamanka zanma aikin ko nasa tiffon ya karb’a maka dama ina binsa bashin lst wk tym da budurwarsa tazo ya kwana gida

Yusuf ya mik’e da k’yar ya kalli yasir yace “kai d’an uwa ne na gaskiya Nagode”…!

Yasir yace babu komai ya rako Yusuf har ya shiga taxi suka yi sallama…

Tun bayan tafiyar hayfa raudha da liliana ke dariya liliana tace “gaskiya da alama kadhija bata dad’e da sanin namiji ba shegiya k’ila shiasa duk take jin tafi kowa” suka fashe da dariya

Raudha tace ke k’ila kuma saurayin ma ya mata alk’awarin aure ne shiasa take sonsa take k’in kula wasu, kuma kinsan mu musulmai iyayenmu da kinyi 12yrs kullum maganarsu da ke aure

Liliana tace da kenan ko?

Raudha tace ke har yanzu wasu haka suke ko mu a India matsalar da ake fama da ita kenan wasu iyayen su hana yaransu cika burinsu ko zama wani abu a rayuwa su turasu aure

Liliana tace haka…

Raudha tace amma kinsan wani abu da nima na gane da khadija?

Liliana tace ah ah

Raudha tace da alama ta fito inda akwai tarbiya domin ina zargin wannan aikin da wuya in iyayenta sun sani kuma indai nayi bincike na gano basu sani ba ni zan fallasa ta

Liliana tace nima tuni na fara zargin haka in ba haka ba ko kud’inta ba taci sannan kullum muka yi aiki bata zama dinner take guduwa in anyi magana tace ta gaji ne ko aikinta daban ne da wanda muke oho

Raudha tayi mutmushi ki barni da ita zan gano wacece ita sannan in fitar da ita daga duniyarmu

Liliana ta daki kafad’ar raudha tace na yadda da ke, yauwa yau ba zamu club ba?

Raudha tace zamu amma da shiga mai kyaw sabida zanje gina gimnati na ne

Liliana tace shiga mai kyaw kamar yaya?

Raudha tace ni zan saka abaya ta Dubai da d’an kwali ke kuma gown har gwiwa koda baki musulma ya kamata su fara tsammanin munada tarbiya kawai rannan akasi aka samu muka je club a yanayin tsiraici

STORY CONTINUES BELOW

Liliana tace gaskiya da gaske wannan gayen ya tafi da ke, mutmushi raudha tayi suka ci gaba da hirarsu…

Koda Yusuf ya isa gida ya wuce d’aki da nufin wanka kafin ya kwanta yayi sallah dama pool saidai ganin hayfa kwance itama da alamar rashin lafiya da d’an sauri ya k’arasa gurinta yana dafa kanta yaji da d’an d’umi

jin motsinsa ya saka hayfa d’an bud’e idanu kad’an saidai ganinsa ya sata bud’e idanu da kyaw sanin lokacin dawowarsa baiyi ba

Hannunta ya rik’o yace cikin sanyin murya baki da lafiya?

d’an k’wallah ne ya zo mata ganin haka Yusuf da sauri ya d’agota yana kallonta yace “sorry ko wani abu ya faru a Nigeria”..?

Still ba tace k’ala ba sai fashewa da tayi da kuka ya rungumeta yana lallashi k’ara rungume shi tayi da kyaw tana kuka sosai ya k’yaleta tayi mai isarta kafin ya d’an d’agora yace “pls kiyi hak’uri haka ko rasuwa a kayi kiyi wa mamacin addu’a karki jawowa kanki ciwo kinji..?

d’an girgiza kai tayi saidai sosai tausayinsa da sonsa taji sun k’ara addabarta ta k’ara sakin kukan ta rungume shi shima haka yana k’ara lallashi yana shafa mata baya itama sai lokacin taji jikinsa da mugun zafi ta d’an d’ago tana kallonsa

yace kaina ya dameni da ciwo shiasa na dawo bazan iya aikin ba haka kawai naji zuciyata bata yimin dad’i sai yanzu da nazo na ganki a wannan halin ya tabbatarmin dama kina buk’ata na shiasa

Ci gaba yayi pls ki dainamin asarar hawayen nan kinji? Ko so kike kaina yaqi daina ciwo zuciyata ta kumbur?

da sauri ta girgiza kai alamar ah ah

Yace toh pls ya isa haka ya goge mata hawayen ya maidata k’irjinsa tana ajiyar zuciya. Kusan mintuna ashirin suna zaune haka kafin daga bisani hayfa da kanta ta d’ago tace “na had’o maka coffee”?

d’an murmushi yayi yace “ah ah saidai zuwa yamma yanzu inaso nayi wanka ne”….!

toh tace ya mik’e itama haka saidai jiri yaso d’ibarta da sauri Yusuf ya tare ta yace “ki zauna ki huta kuka kika yi dayawa ko?

Shiru tayi ta sunkwi da kai…..

Ajiyar zuciya yayi baya son takurata in har batajin fad’a masa damuwarta don haka yace “ki zauna bari nayi wanka nayi alwala muyi asar…”

cikin sanyayyiyar murya tace “ni ina hutu…”

OK” yace ya wuce bayin yayi wanka yayi alwala ya fito tana zaune ya fito da tawul d’aure tanata kallonsa jikinsa ya basa ya d’ago yana kallonta tayi maza ta kau da kai yayi murmushi ya fito falo gun akwatinsa ya saka dogon wandon Nike mai nauyi da safa ya saka suwaita ya dawo d’akin ya tada sallah

Koda ya idar da sallah ya gama addu’a ya shafa hayfa na zaune gadon kanta na k’asa

a hankali ya mik’e ya hau gadon ya zauna ya janyota jikinsa ya kwantar yana shafa mata gashi yace “ki bani labarin mana…”!

d’an shiru tayi…

shima bai k’ara magana ba…

A hankali tace kaima ka bani na ka…

Murmushi yayi yace ” wai ke mai wayo ko”…?

d’an dariya tayi tace “ah ah”

Yace duk chart d’in da mu keyi har mu kayi aure baki tab’a tanbayana ba why sai yau?

hayfa bata fahimta ba ganin baifi sau 4 suka yi wpp ba suka shiga maganar aure

Junta shiru yace shikenan mu rufe wannan chapter d’in naga bakyaso ko…

Still shiru bata ce komai ba, ita kunya take ji ta fad’a masa itama y’ar talakawa ce duk jiji da kan da take yi da tak’ama

d’an shafa fuskarta yayi yace yau a karon farko inaso mu kira gidanku tare mu gaishesu kin amince?

STORY CONTINUES BELOW

“Eh” tace tare da d’an mik’ewa tana dube-dube shine ya hango jakarta kan wani akwatinta gefen wardrobe ya mik’e ya d’auko mata ya bata

Ansa tayi a hankali tace “Nagode”..!

bud’e jakar tayi ta d’auki wayarta ta kunna data ta shiga wpp saidai Ammah bata onlyn don haka ta fita wpp ta jefa direct Call

Ammah na falo tana aiki a system ba taje aiki ba laraba na shirya musu launch a dinning yara na skull  wayarta ya fara ringing da sauri ta duba ganin hayfa ce

Sallama hayfa tayi ammah ta ansa, hayfa tace mominmu ki hau wpp yanzu

Ammah tace toh y’an matana lafiya dai ko…?

Hayfa tace lafiya zai gasheki ne.. Ammah ta gane da sauri ta kashe wayar ta kunna data a wayarta Samsung Galaxy s5

Kallon Yusuf hayfa tayi shima yana kallonta tace ” ko zamu je bayan gida”?

Yace mai yasa?

Ita hayfa tana tsoro ne kada ammah ta gane wani abu sabida gidansu ya cika k’arami, saidai ta cewa Yusuf yawanci in muna video call a nan da gida sai yayi ta tsinkewa

Yusuf yace OK suka mik’e ita bama ta da k’wari sosai haka ya rik’e hannunta suka fita can wajen ciyayin bayan gidansu inda suka zauna babu ma alamar akwai mutane a gurin

Hayfa ta kalli Yusuf tace “Na kira yanzu”..?

Eh yace yana shafa fuskarta…

Shafa hannunsa tayi itama suka d’an kalli juna na minti biyu kafin hayfa ta cire idanunta ta jefa layin ammah

da d’an hanzari ammah ta ansa call d’in hayfa ta k’ara gaisheta tace “y’an matana kuna waje ne”?

Hayfa tace eh mominmu ina su khairat?

Ammah tace suna school yanzu driver zaije d’aukosu

OK” tace kafin ammah tace kin tsareni da surutu ki bashi mu gaisa mana

d’an shagwab’a tayi kafin ta juya ta mik’awa Yusuf wayar

Yusuf mugun ajiyar zuciya yayi ganin falon da ammah ke ciki a ransa yace lallai masu kud’i ne sosai tab

Ammah ce ta dawo dashi tunaninsa tace, surikina yaya kuke?

Cikin girmamawa yace lafiya Mama ya gida da yaran?

Tace lafiya kowa ya aiki?

Yace lafiya hayfa ta dawo kusa dashi kad’an duk suna kallon ammah tace “mominmu ki turomin number Surayya Adda suwaiba tace wai ita batasan number ba

Ammah tace toh zan turo miki hayfa tace bari nazo ta mik’e pad d’inta taji ya jik’e

Ammah ta kalli Yusuf tace “kaci gaba da hak’uri da ita kaji kasan yara sai a hankali sai hak’uri ka rik’a nuna mata abinda ya kamata da wanda bai kamata ba har ta gane komai Allah ya k’ara muku zaman lafiya da fahimtar juna..

Amin Yusuf yace Insha Allah mama a gaida mutanen gida

Ammah tace toh tana shirin kashewa yara suka shigo falon inda suka ansa wayar sunata masa shirme sun dad’e kafin basu ma kashe ba khairat na ta yawo tana masa magana da shirme har kiching ta shiga gun laraba tana ce masa abinci zanci kaima za kaci?

Murmushi yayi yace kici da nawa.. Tace to ka jira nagama fa kada ka tafi

mutmushi Yusuf yayi yace toh tana cin abincin tana kallonsa ta d’aga masa hannu tana gun laraba tazo tace ke ko uniform ba zaki cire ba ko?

Kallon Yusuf tayi tace ka ganta ko? Kace mata ta barni nagama cin abinci

Yace toh kawai duk ya gaji bacci yake ma ji

Haka ta gama tana haurawa sama tana bashi labarin sunyi fad’a da k’awarta a skull yayi dariya har ya gaji yace mai ya had’aku?

Tace tazo da bufday cake d’in Daddynta ta hanani bayan raina ya biya

K’ara fashewa Yusuf yayi sosai da dariya gaskiya dole hayfa tayi jiji da kai ganin falon saman inda khairat ta zauna tana ta zuba masa surutu tace za ka kalla “Miraculous Lady” na saka maka”?

Yace No sai gobe zan…. Hayfa ta dawo ta zauna gefensa ganin da khairat na ta shitme tace “je maza kiyi shirin islamiyya tym na tafiya”.. Ta kashe wayar

Yusuf cike da murnushi yace ta burgeni sosai zamu rik’a kiranta kinji”?

Hayfa itama d’an murmushi tayi tace “toh” suka ci gaba da zamansu a gurin iskar sanyin na kad’asu har aka kira magrib suka shigo gida.

Bayan magrib hayfa ta daure ta dafa masu rice da miyar naman gongoni da coffee sabida Dr yace a wannan kwanakin ta kiyaye shan abu mai sanyi

a falo suka ci su duka ba wani dayawa suka ci ba sai suka sha coffee ta kwashe kayan

Bayan ta dawo Yusuf ya kalleta yace “mai yasa baki je aiki ba”?

Mugun bugawa k’irjinta yayi kafin ta dake tace “nima banajin dad’i shine na ansa hutu na 3dys”!

Kallonta yayi da kyaw sai yanzu ya lura da yadda idanunta suka yi kwarmi kamar tayi jinya

shiru yayi kafin yace OK kawai

d’an mik’ewa tayi kamar zata bayi ta d’auki magungunanta ta shiga bayi tasha ta fito ta maidasu k’ark’ashin gadon ta fito falo…

Haka dai ranar suka kasance tare har bacci inda suka d’auko katifar suka kawo falo suka kwanta manne da juna kamar yadda ainihin ma”aurata ke bacci” …

Da safe bayan sun karya Yusuf ya wuce pool a can yasir ke bashi labarin su raudha sunje nemansa, tsaki yayi kawai ya wuce d’akin canza kaya

Yasir yace ka ganta kuwa jiya a ainihin musulmarta tazo da alama ka fara tasiri a rayuwarta domin ba Karamin tashi hankalinta yayi ba da nace mata bakada lafiya ba zaka zo aiki ba

Yusuf yace ka share maganar y’an iskan nan kai bakasan inada mata ba? Kai koma banida mai zanyi da wannan kangararriyar mai yad’a jikinta da kamanninta a duniya

Yasir yace ka bita a hankali ku rabu lafiya na lura yarinyar batada limit ga shi bata ji da gani

Yusuf yayi tsaki yace “OK” to ni zanyi maganinta ya fito ya wuce ya fara aikinsa

Haka hayfa ta share kwanakinta Yusuf na jinyarta ba tare da yasan jinyar zubar masa da ciki yake ba har ta warware ta koma duka ayyukanta biyu..

Aiki tuk’uru hayfa domin d’an 3dys da tayi a gida tayi d’an k’iba sabida tsantsar soyayya da Yusuf ke nuna mata

Don haka Armando yace exercise babu hutawa sai jikinta ya koma yadda kamar da..

Haka take aiki tana ta café nan da nan kuwa ta fara zubewa aikin kuma mai yaji ne Armando yace zasu ja kud’i sosai

Gobe ne show ko ince “fashion parade d’in da suke aiki akai na kamfanin wani Antonio davincci.²⁰

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE