KASAR WAJE CHAPTER 9 BY MARYAM DATTI

KASAR WAJE CHAPTER 9 BY MARYAM DATTI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Itama tunani ta d’anyi ta kalleshi cikin shagwab’a da nuna bata san akwai wani a gurin ba bayan su tace “pls ka ci wani abu ko kad’an ne”+

k’in d’agowa yayi ya kalleta Yasir kuwa ganin kallon da hayfa ke yiwa Yusuf yasa da sauri ya fara cin nasa ita kuma taqi tashi tana kallon Yusuf
Yasir ya gama ya d’auka take away da ta musu yace “madam mun gode” ya kalli Yusuf yace ni zan wuce sai ka k’araso…

Yusuf ma mik’ewa yayi duk da hayfa ta kusa rinjayarsa amma ya dake dole ya hukuntata kafin ya sakko….

Yana mik’ewa tuni Yasir yayi waje abinsa shima Yusuf yana k’ok’arin binsa itama ta mik’e ta rungumoshi ta baya tare da kwantar da kanta a bayansa
Sosai yake jinta amma ya dake yace “aikin nan da shi na dogara ko so kike a koreni”?

d’agashi tayi jiki babu k’wari bai ko juyo ba ya wuce abinsa…

Bayan fitarsa ta fara gyaran wurin tare da tunanin mai zata shirya masa kafin ya dawo su shirya tana cikin tunanin tana aikin cikin gida wayarta ta fara ringing ta shiga d’aki ta d’auka ganin Armando ne ta ansa

Queen yaya kike? Yaya gajiya? Yaya jikinki?

d’an murmushi tayi tace “lafiya”…

dariya yayi yace “yaya mijinki”..?

d’an shiru tayi kafin tace “yana lafiya”..!

Yace yawwa albashinki duka biyu sai aikin da za kiyi na tallan wannan balaraben na Bahrain munyi dashi kudinki $100000 sannan na aikin da kika yi jiya $150000 na tura duka $250000 a accnt d’inku na Nageria sannan kiyi k’ok’ari ki d’an d’auki hutu a café dama nayi masa magana yace babu damuwa sabida aikin larabawa akwai wahala kinga hijabai ne zaki masa tallah amma kuma yace zaayi shotting ne na video kina yawo kad’an a gari da hijaban to munyi zamu je har Ontario da Cubec can arewacin Canada da d’an nisa da nan Toronto don haka kiyi k’ok’ari ki bar café ki huta iyakarki kamfani exercise kinji?

d’an ajiyar zuciya tayi tace “toh”

Yace sannan shima hubby d’inki kada kuyi wasa dayawa a kwanakin nan hakan zai janyo miki yawan kasala da nauyin jiki kin gane wannan qa’idar aikin nan kenan in kanada aiki a k’asa baka wasa dayawa kin gane ay

Ajiyar zuciya ta k’ara yi tace “toh” yace ki kula da kanki sanann akwai gift da bunil ya Baku ku duka agogone kamfanin swatch suka mana discounts saidai duk da haka yanada tsada dayawa bansan ko zaki iya anfani dashi ba yanzu ko kuma zaki ajiye kuma mixed ne ma’ana maza da mata

OK tace Nagode yace “kizo kamfani anjuma kiyi signing d’in contract d’in Bahrain sai ki dawo da sauri sabida ni gobe zanyi tafiya Milan kinsan muma har mun fara shirin Gala

ajiyar zuciya tayi tace “pls kasa driver ya kawomin nayi signing bana son fita yau”..!

Dariya yayi yace da kyaw hubby na gida kenan babu fita ko…?

d’an dariya tayi tace ah ah baya nan bana jin fita ne yau

Ajiyar zuciya Armando yayi yana tunani sosai hayfa ke burgeshi yadda sam aikin models bai sanya ta canza ba dukda yawan kud’ad’e da shahararrun mutane da ta fara had’uwa da su amma har yanzu wannan jan ajin da ya ganta da shi tun ranar da ya fara had’uwa da ita yana nan amma yanzu ya qara gane hakan na da nasaba da yadda take girmama aurenta, ajiyar zuciya yayi yana qara mamaki y’ar k’aramar yarinya amma tasan mutuncin kanta da na mijinta… Hayfa ce ta dawo dashi tunaninsa
STORY CONTINUES BELOW
Tace “ina jiransa yanzu zai zo?

Armando yace muna gama wayar nan zaizo karki damu sai munyi magana ki kula da kanki suka yi sllama
Suna gama wayar ta taci gaba da aikin tayi wanke-wanke da mopping d’inta da goge-gogen gida ta yi turaren wuta ta wanke kayansu ita da Yusuf hatta boxers d’insa duka ta wanke ta kwashe a washing machine taje ta shanya waje ta dawo tana shirin d’an kwanciya ganin 10:38am tana ma tunani zata d’auka mai yi musu hidimar komai na gida tana biya ta yi ta tafi kafin su Yusuf su dawo, lokacin taji nucking ta mik’e tasa hijabi ta fita

Gaisawa suka yi da driven wanda Armando yayiwa gargad’in kada ya tab’a nunawa kowa yasan gidansu hayfa domin yasan halin y’an matan models da halin fitina musamman ga Raudha
Mik’awa hayfa takardun yayi ta bud’e tayi signing duka ta mik’a masa zata wuce ya mik’o mata y’ar jaka kamar ta bufday gift ta ansa ta masa godiya suka yi sallama ya wuce ta shiga gida

D’aki ta wuce direct ta zauna gefen gado ta yage ledar ta bud’e d’an akwatin
d’an bugawa qirjinta yayi ganin agogo ubansu na kamfanin swatch gashi a jikin kwalin kudinsa har $15000 kuma gaskiya zai fi kyaw da maza tace a ranta dama-dama tace

d’an ajiyar zuciya tayi da tayi wani tunani amma ta yaya hakan zai yuwu nan dabara ta fad’o mata ta mik’e ta bud’e wardrobe ta d’auko wani kit d’inta na kayan sark’ok’inta ta saka agogon a ciki ta dawo ta fara tunani da shiri kala-kala inda tayiwa Yasir msg kamar haka

Salaam.
Pls za a iya biyan wani ya ansar mana aiki na yau?

Yasir da Yusuf sun gama aikin safe suna gurin zamansu suna hira msg d’in hayfa ya shigo

d’an mutsuke idanu Yasir yayi ya qara karantawa shi Yusuf ma yana yiwa Aliy msg ne kan gobe zaije café su had’u suyi chart

Yasir yayi ajiyar zuciya tabbas tiffun mayen kud’i zai ansa kud’i yayi aiki

Don haka ya fara yiwa tiffun msg ya fad’a masa dama yana neman kud’i zai sayawa budurwarsa flyt  ticket na zuwa beach da sauri yayiwa Yasir reply da “eh”….

Yasir yayi murmushi dama ya sani, sannan yayiwa hayfa msg da “eh an samu”!
tace “OK” Nagode!

gyaran gidan ta qara yi sosai ta kwaso kayansu ta goge ta jerawa Yusuf na sa a akwatin sa ta bud’e akwatinta na kayan bacci ta duba kaf ba taga abinda zaiyi daidai da buk’atarta ba ta maida ta shiga internet.

Kamfanin Victoria secret lingerie ta shiga ta zab’i y’an ubansu guda uku latest na collection d’in da zasu saki bayan Summer inda ya kama $11000 ko damuwa ba tayi da tsadarsu ba domin kowa sosai ta ke son burge mijinta, saidai bata da account da sauri ta fita ta jefa layin Armando

Yana office yana ma shirin wucewa airport kiran hayfa ya shigo ta gaisheshi yace “yaya dai queen”?

Ta masa bayani tace sai cash na ke da…

d’an dariya yayi yace ba kinqi ko da sunan kamfani na bud’e miki accnt ba da yanzu duk sati kudinki na nunkuwa idan kina ajiya
Shiru tayi…

Yace babu damuwa yanzu ay akwai albashinki na gun bunill na kud’in kashewa $5000 ko wani wata dama bana baki ne ganin bakya cika buk’ata sai ina tara miki yanzu haka kinada kusan $30000 bari na biya miki zasu kawo miki

Godiya ta masa sosai ta tura masa information na web syd da kayan da ta saya, su kayi sallama ta fara tunanin mai kuma zata dafa wa Yusuf

da sauri tayi murna tunawa da tayi akwai su yaji daddawa kub’ewa busassa kuka karkashi zogale duk da aka mata akwati guda da zata zo Canada bata tab’a bud’ewa ba sabida tsabar tashi da hankalinta yayi da ta iso taga rayiwar ba yadda su kayi tsammani ba
STORY CONTINUES BELOW
Mik’ewa tayi taje falo gun akwatunanta da ke falon ta fara bud’ewa har ta samu wanda ke cike da zallan kayan abincin gargajiya na Nigeria da Ammah ta loda mata bata manta sawa hayfa komai ba na abincin har su tsakin pate da garin d’anwake
cikin farin ciki ta d’auko babban ledar kub’ewa da na daddawa saura sai zuwa jibi za tayi gyara ta sama musu guri a kiching d’insu

Shinkafa ta d’iba ta jik’a ta kalli agogo 12:57 ta koma d’aki tayi alwala tayi sallah. Tana idarwa ta fito kenan aka buga k’ofa ta saka hijabi ta fita

Ganin ma’aikacin kamfanin Victoria secret ta san saqonta ne gaisawa suka yi ya mik’a mata ta ansa ya nuna mata inda za tayi signing tayi ya wuce

Bayan tafiyar ta shigo ta bud’e kayanta saidai wani sansanyar ajiyar zuciya tayi ganin kayan sunma fi kyaw a zahiri ta saka cikin wardrobe ta sake bud’e akwatin cosmetics d’inta na aure ta d’auko zafafan parfume masu dad’i ta saka su suma a gurin kayanta sabida d’akin babu mirror

Bayan tayi asar ne ta fito ta wanke shinkafar ta sake zuba ruwa ta d’ora kafin sunada nama a dukda baida yawa sosai ta wanke ta dora ta markad’a tattasai da tarugu da albasa ta zuba kan naman ta zuba man ja ta saka maggi da gishiri ta rufe takan ga yadda laraba ke girki tun tana gida kawai yi ne ba tayi

Shinkafar tayi ta tuqa tuwonta yayi kyaw ta lelaya shi a bull ganin babu leda ta jerashi a wani mazubi kafin ta ajiye miyan har ya fara k’anshi

Wayarta ta d’auka ta duba 5:11pm duk yadda akayi suna hanya domin yau da gobe Yusuf ba yada zuwa tranning

Suna train Yasir ya kalli Yusuf yace “tiffun yace yau yana jin nishad’i kayi zamanka zai karb’ar maka aiki”

Yusuf yace hm kyawta ko dai in biyashi?

Yasir yace kai yanzu ka b’aci da lissafi kadai zai karb’ar maka babu wani maganar biya

Yusuf yaji dad’i saidai ranshi na b’ace da hayfa don haka sai yana jin gara ma ya tafi aiki abinsa

Koda suka iso gida tun suna bud’e qofar falon qanshi ya fara dukan hancinsu na turaren wuta a hankali Yusuf ya bud’e suka shiga saidai duk tsayiwa suka yi ganin yadda ta jera komai harda ruwan wanke hannu

Shi Yasir mamakinsa ma shine mai zasu ci haka har da ruwan wanke hannu saidai duk suka k’arasa shiga suka zauna kuma yunwar suke ji sabida taliyar dama ba dayawa ta dafa musu ba

Yasir ne ya fara bud’e qaramin bull d’in inda ya wani had’iyi yawu ganin miyar kub’ewa Allah ya jarrabeshi da son kub’ewa ya sake bud’e babban yaga tuwon shinkafa kama kansa yayi yana ajiyar zuciya ya kalli Yusuf yace “Allah yayi maka albarka da ka auro mana y’ar albarka”…!

Yusuf shi dariya ma Yasir ya bashi inda nan da nan Yasir ya d’auka plate ya fara lodi sosai kamar wanda ya kwana da yunwa

Shi Yusuf ma ya kasa ci dukda kuwa sosai shima abincin ya burgeshi rabonshi kusan 2yrs
Hayfa na d’aki tana chart da Salma
Bayan Yasir yayi nak ya wanke hannu ya kalli Yusuf yace tab ni wai har yanzu baka ci ba? Ko jira kake sai anzo an baka a baki..?

Shi Yusuf dariya ma Yasir ke bashi yadda duk ya rikice yaci tuwo sai kace wanda yaci raqumi

Yasir yace munyi magana d’azu Walid bari na shiga gunsa daga can zan wuce club sai gobe pls ka cewa madam ta ajiyemin sauran zan karya dashi gobe
Yusuf yace “OK” to ka bari muyi sallah mu je tare
Yasir yace OK

Ya shiga d’akin yayi alwala ya fito ko inda take bai kalla ba kanta na kan waya itama ta kame sai zuwa anjuma za tayi attakin d’insa ta kawo k’arshen wannan fushin

STORY CONTINUES BELOW
Yana fitowa shima Yasir ya tsaya kanta zinc yayi alwala suka fara magrib bayan sun idar tare suka fita

Bayan fitarsu ta fito falon saidai sosai ranta yayi sanyi ganin plate d’aya ne kawai aka ci abinci wato Yusuf bai ci ba

Sun dad’e can suka yi ishaa sai kusan 9:34 Yasir d walid kowa zai wuce aiki

Suka yi sallama Yusuf ya dawo gida ya d’an mik’e abinsa a kujerar har yanzu baya jin saukowa daga fushi da hayfa dukda yana jin yaji dad’in yadda ta kyawtatawa Yasir domin sa

a hankali ta fito falon ta tsaya kansa
Wani fitinannen qanshi ne ya daki hancinsa a hankali ya bud’e idanunsa da ke lumshe

Saidai wani irin d’an numfashi yaja ganin hayfa da wata doguwar rigar atamfa ja ta matse ta sosai tayi d’aurin d’ankwali tayi simple makeup tayi wani sihirtaccen kyaw

Sosai ta tsuma shi saidai ya daure ya kame yama cire idanunsa daga kanta

a hankali ta zauna ta d’an fara magana

“Kasan mai yake sa ni kuka”?

Bai mata magana ba ko tak

Tace ina ganine ne kamar bana fita hakkinka yadda ya kamata yadda Allah ya d’oramin

a d’an bud’e idanu yayi yana kallonta saidai yaga idanunta da k’wallah still baiyi magana ba

Taci gaba “a duk sadda na tuna wata qila bana sauke hakkina na mata hawaye kad’ai ke sanyani naji sanyi, amma inda na san shima hakan zai qara zama nauyin ka da na kasa saukewa da bazan yi ba”..

Sosai yake kallonta yanzu yana son gane gaskiyar abinda ta ke fad’a..

Pls 4give IA zan daina….

Ajiyar zuciya yayi cikin muryarsa da ke susutata yace ” is OK”

a hankali tace “na saka maka abinci”?

Kallonta yayi duk tayi kamar wadda aka yiwa rasuwa
Girgiza kai yayi..

da d’an hanzari ta d’auka plate ta saka masa ya sauko k’asa da kanta ta fara bashi

Sosai shima yaci domin shima yana son tuwo sosai ya kalleta “tace ni naci tun dazu “..

Baiyi magana ba ta kwashe kayan ta dawo ta zauna  kallonsa tayi har yanzu bai saki ba sosai a hankali ta mik’e yana zaune kan kujerar taje ta dad’e kusan 40mnts kafin ta fito da katifa tayi musu shimfid’a yana kallonta
Bayan ta gama tana kallonsa ta koma d’aki tayi wanka kusan 30mnts tanata shafe-shafen turarurka humra kusan kala goma ga na turawa shi a falo ma d’an bacci ya fara saman kujerar
Ta gama ta d’auko d’aya daga cikin shed’anun kayan da ta saya mai white tas lingerie mai hannu brasia iya rabin cinya babu ko pant yanada siririn pant d’insa tasa dama ta kama gashinta tsakiyar ka ta dunqule, d’an tsayuwa tayi tana tunani anya zata iya fita masa haka?

Saidai ta bawa kanta ansa da ay mijina ne babu wani abu da bai sani ba jikina kuma a irin wannan lokacin babu wata kunya tsakaninmu

d’an murmushi tayi ta bawa kanta k’warin gwiwa ta nufo falon tun kan ta qaraso fitinnanun qanshin suka saka Yusuf farkawa a hankali ya bud’e idanunsa

Wani irin yawu ya had’iye ganin hayfa tsaye a gabansa da wani riga da kamar da yadin gidan sauro a ka d’inkashi sabida shara-shararsa

Qarasa bud’e idanunsa yayi da kyaw yana kallonta sosai ya qara jan wani gauron numfashi

Itama tana tsaye ta sakar masa d’an murmushi ganin tarkonta ya Kama tak’i motsa daga inda take
Kusan 10mnts Yusuf na kallonta kamar tv kafin a hankali ya mik’e ya qaraso gabanta yana kallon cikin idanunta da wani irin zafaffen so da sha’awa a inda ta sunkwi da kanta wani irin fitinannen yanayi ta keji a duk sanda fatarta ta had’u da ta sa ga wani santsi da zuciyarta ke yi idan tana kallon cikin idanunsa wani zazzafan harbawa qirjita ke yi idan tana jin nunfashinsa kusa da na ta gaba d’aya loosing control ta keyi tayi

Hannunsa yasa a hankali yana shafa fuskarta ta qara limshe idanu tayi tare da sakin d’an siririn ajiyar zuciya da ya qara susuta Yusuf ya kamo bakinta ya fara sha itama ta fara tayashi nan da nan suka d’au zafi suka maqalqale juna
Yusuf ya d’an d’ago yana kallonta idanunsa duk sun qara tsumewa tsabar fitina
da rigar ya dirarwa qirjinta domin ji yayi shima baya son cire mata rigar tsabar kyaw da rigar ta mata
A hakan dai da rigar ake ta abubuwa inda sai cakud’ata yake tana tayashi wanda hakan ke qara kusancin ma’aurata domin ba namiji ba ne kad’ai zai zauna yana miki hidima kamar bawanki abu ne na mu gudu tare mu tsira tare wannan shine abinda hayfa ta fara fahimta a aurensu da Yusuf.

Sosai suka luntsuma anata harka Yusuf kamar ya mutu yadda hayfa ke susutashi domin ko tasha madara ne fresh da zuma sosai bayan da su Yusuf suka fita d’azu wanda ammah ta fad’a mata ta riqa yawan shan madara da zuma
Wani irin sakar masa kanta tayi ya kwashi gara har yana mata kuka wiwi dukda ita kanta ba qaramin zautata yayi ba gashi tayi laushida haka dai har komai ya gama wakana inda suka rungume juna sosai ita ma gimbiya hayfa hawaye take mai d’umi Yusuf na jin d’igarsu a kafad’arsa na wani irin duniyar nishad’i da farin ciki da Yusuf ya kai ta, wani wutar sonsa ne taji yana ruruwa mata a zuciya ta qara kwantar da kanta kafad’arsa tana ci gaba da sakin hawaye

shima qara matse ta yayi jikinsa kamar kada su tab’a rabuwa ikon Allah hayfa an daina jiji da kai an maqalewa talaka..lol

Sai kusan 1:08am suka samu nutsuwar d’an sakin junansu kad’an kowa na maida numfashi a hankali suka kwanta

Shafa kanta da ke qanshi Yusuf yayi a hankali ya mata peck tsakiyar kan, yayinda ita kuma ta riqo hannunsa da ke cikin na ta ta d’an juya bayan hannun ta manna masa kiss cikin yanayin tausasa leb’enta a kan fatar hannunsa

Yusuf har lumshe idanu yayi shi kansa ji ya ke ya fi ko wani namiji sa’a a duniya

Babu wani magana da suka yi bacci yayi gaba da su a yanayin da suke kwancen cinyar hayfa d’aya zuwa k’afarta na jikin Yusuf sannan ta sama ma jikinta na kan qirjinsa shi kuma ya qara rungumeta….

Asuba ta gari Yusuf ne ya iya farkawa hayfa kuwa sosai tayi tsami bata gane Yusuf ya wujijjigata ba sai yanzun da taji y’an yatsunta ma sun mata tsami ta kasa d’aga su ko ranar farkonsu ba taji tsamin jiki irin yau ba

Yusuf ganin haka ya d’aga ta a hankali ya mata peck ya nufi bayi yayi na sa wanka sannan ya had’a mata ruwa mai d’umi ya zuba mata dettol ya zo ya d’auke ta kamar baby ya wuce da ita ya zaunar cikin ruwan d’an qara tayi ya mata peck a goshi yana “sorry baby” ki d’an zauna ruwan ya shiga jikinki ina zuwa kinji?

girgiza masa kai tayi cikin shagwab’a ya qara manna mata peck ya fito zai yi sallah

Bayan ya idar da sallah da hanzari ya koma bayin d’an gyangyad’i ma take cikin ruwan ya qarasa da kansa ya mata wanka ya saki ruwan ya qara hada mata wani ya sake wanketa sannan ya sake had’a mata wani yace “ki daure kiyi na tsarki kinji”?

Girgiza kai tayi ya fito wadrobe ya d’auko mata rigar sanyi da bud’ad’en sicket da hula da suck ya d’auko mata lotion ya ajiye kan gado ya juya zai koma bayin ya ganta tana fitowa d’aure da tawul duk ta qara laushi da d’an tausayawa ya qarasa ya riqota ya  cire mata tawul ya saka mata hijabi tayi sallah tana idarwa ya fara shafa mata lotion sai shagwab’a take masa yana aikin lallashi kamar yau ne ya fara saninta a mace

Har dai da kansa ya shiryata tsaf kafin yaje ya had’o mata coffee ya dumama mata tuwo yace itama taci da kansa ya ke bata ta kuwa ji dad’in tuwon kamar ba ita ta dafa ba

Suna zaune yana bata coffee Yasir ya qonqonsa k’ofa Yusuf ya mata peck a goshi yace “bari na zo”

“Toh” kawai tace tace cikin d’an yanayin shagwab’a tana fatan kada ya tafi aiki ya barta

Yana bud’e k’ofar Yasir ya fara masa iskanci ya shigo Yusuf yace kaci abinci ina zuwa ni

Yasir ya d’an saki dariya yace ay babu komai nasan kai yanzu ko yaushe in kana gida to kana cikin hidima ne ya qara sakin dariya

Yusuf ya wuce kawai sai sun fita waje zai rama yace a ransa. tana zaune ko bayan fitarsa qin cin tuwon tayi sai da ya dawo ya ci gaba da bata da kansa

A falo ma Yasir sosai ya ke Lodi na tuwon kamar bai ci jiya ba.. Lol

Bayan ta gama ci da k’yar ma taci da rarrashi da kalaman soyayya da Yusuf ke mata a kunne tukuna

STORY CONTINUES BELOW

Kwashe kayan yayi ya kawo falo Yasir na ganinsa ya d’an saki dariya a hankali shima baya so hayfa ta jiyo su yace cikin tsokana ” sannu da aiki miji”

Shareshi Yusuf yayi ya ajiye kwanukan zai koma ciki Yasir yace “zaka aiki ne ko yau ma zaman aikin gida za kayi”.?

Yusuf ya kalleshi yace “lokacinka ne yanzu nawa na hanya”. .. Ka jirani inzo mu wuce ya shige

Dariya Yasir ya qara saki

A d’aki “Yusuf ya kalli hayfa yace pls drewdrop ki min afuwa dole na je aiki kinji”?

d’an tabe fuska tayi tace “ni uhm uhm”

dariya ma taso bashi ya dake kada ya tsokano finita yace pls promise ko wani 30mnts zan kira ki pls kinji…?

kallonsa tayi tana son qaqalo kukan shagwab’a ya janyota jikinsa ya rungume yana rad’a mata “bana son kina kuka saidai na lura sosai yanayin kuka ke qara miki kyaw” ya saki d’an dariya

Ture shi tayi tana alamar kuka ya qara janyota jikinsa yace sorry drewdrop pls 4give me ya kama bakinta yayi kissing mai sanyaya zuciya na 3mnts kafin ya miqe ya fito a dole baya son qara jan lokaci

Yana fitowa takalmi kawai yasa suka kama hanya Yasir na tanvayarsa hayfa yace “ina ruwanka ne da matata”..?

Yasir yace Allah dole zanyi aure kwanan nn wulak’ancinka ya isheni har yaushe…?

Yusuf yace inka shirya yi pls ka fad’amin na baka layla yana d’an dariya…

Yasir yace da gaske?

Yusuf ya fashe da dariya yace eh mana don nasan ba kudine da mu ba gara muna tallafawa junanmu sai na baka ita kyawta sadaki kawai zaka biya

Yasir shi da gaske ya dage yace “shekararta ma nawa”?

Yusuf yace da sauranta nasan kai baka son yara kamar matata ko?

Yasir yace pls ka bar maganar kawai ka fad’amin shekararta nawa?

Yusuf cike da mamaki ganin Yasir ya d’auka da gaske alhalin shi wasa yake “d’an kallon Yasir yayi yace tana shirin gama secondary yanzu ta cika 17yrs”

Yasir yace saura 5mths ayi waec ko?

Yusuf bai bashi ansa ba yana kallonsa kawai….

Yasir yace ka bani number mamanku sai na fara kiranta tun yanzu wlh na amince indai za ka bani ita

Yusuf cike da mamaki yace “yanzu kaima sai ka shiga rikici kamar yadda nayi”?

Yasir yayi tsaki yace “eh zan shiga wlh nima tuni na fara buqatar aure ay kaima da ka shiga baka mutu ba haka matar ba ga kunan Allah yana rufa muku asiri ba

Ajiyar zuciya Yusuf yayi yace toh in ba ta sonka fa?

Yasir yace zan koya mata wuyarta muyi auren…!

Ajiyar zuciya Yusuf yayi har ya fara dana sanin furicinsa saidai yasir ya masa hallaci kuma baya da aibu quriciya ke saka shi wasu y’an shirme tym to tym

Kallon Yasir yayi yace shikenan zan baka number in bata amince ba babu yadda zanyi…!

Yasir da yasan kansa da mata yace “promise in na kasa shawo kanta zan hak’ura”

da haka suka iso pool kowa yayi b’angarensa domin sun kusa makara.

A Nageria ana cikin tashin hankali sosai iyalan Alhaji shamsu da Allah ya yiwa rasuwa cikin daren jiya da safen nan za ayi janazar sa..

Aliy sosai hankalinsa shima ya ke tashe sanin halin iyalan Alhajin da sam basu shiri tsakaninsu ga son abin duniya yanzu za su fara rigima a kan abinda ya bari

STORY CONTINUES BELOW

Sosai ya fad’a tunani yana zaune gurin makokin kafin a fito a wuce da Alhajin gidansa na gaskiya

Tunani Aliy ke yi ya za su qare da Yusuf ya tabbata dole iyalan Alhaji shamsu su riqe gidansu Yusuf koda kuwa sunga yarjejeniyar da ke tsakanin Alhajin da Yusuf za suce babu ruwansu ko kud’insu ko gidansu Yusuf

d’an miqewa yayi ya je nesa da mutane ya saya credit ta banki sannan ya jefa layin Yusuf

Hayfa da tun bayan tafiyarsu Yusuf d’an bacci ne ya kwasheta ta jiyo ringing d’in wayar Yusuf wanda hakan na nuna mantawa yayi da wayar

d’an bud’e idanunta tayi a hankali tana neman inda ta ke jin qarar wayar

Ganin kamar a kan gadon ne ta mik’e a hankali ta fara nema dukda bacci da ke idanunta sosai

Har kiran ya tsinke ta a ka sake jefawa tana nema can ta ganshi saidai ko kafin ta ansa kiran ya qara tsinkewa

Aliy d’an tsaki yayi kafin ya fara yiwa Yusuf dogon text domin ba tym zasu wuce maqabarta

Sosai ya yi masa text da nuna tsananin tashin hankalinsa a kan mafitar da zasu nema kafin iyalan Alhaji shamsu su tijara mahaifiyar Yusuf da qaninsa inda Aliy ke fad’a masa da kaga msg d’ina ka je café muyi magana sosai.

Yana gama text d’in ana fitowa da gawar Alhaji shamsu za a sallace

Jin shigowar text hayfa ta kalli wayar kamar ta maida ta ajiye saidai haka kawai ta ji curiosity na sanin wa zaiwa mijinta txt da sassafe haka

A hankali ta bud’e wayar ta fara karanta msg d’in

Tana karantawa tana hawaye mai yasa Yusuf ba ya fad’a mata komai ga me da rayiwarsa…?

Mai ya kawo bashi tsakaninsa da wanda aka ce ya rasun…?

mai ya had’a bashin da gidansu Yusuf har iyalan mamacin zasu k’wace gidansu mamansa da qanninsa su wulaqanta..?

ba wannan ba ne damuwarta a yanzu haka tace a ranta damuwarta shine yadda za ta warware wannan matsalar ba tare da ko shi kansa Yusuf ya san komai ba

Goge msg d’in tayi da miss call ta kwashe number Aliy a wayarta jefa kira

Suna maqabarta ana binne alhaji shamsu

Jin bai d’aga ba tayi msg “da ka zama free ka nemi wannan layin”!

Suna aiki a pool ya fara laluba aljihunsa babu waya d’an tsaki yayi tunawa da yayi ya manta wayar inda ya bawa Hayfa abinci gashi ya mata alqawarin kiranta ko wani 30mnts

A dole ya nufi b’angaren yasir ya karb’a wayarsa ya kira ta

Tana zaune shiru ta had’a kai da gwiwa tunani ta ke, babu wani Abu da Ubangiji ya ke tsarashi face yanada hikimarsa

Idan ya qaddara aurenta da Yusuf lallai sabida akwai wata manufarsa akan hakan idan tayi la’akari da rayuwarsu kusan iri d’aya shima Yusuf a yadda ta fara fahimta nauyin gidansu na kansa ne

d’an hawaye ta saki taji wayarta na ringing kamar kada ta d’aga saidai tayi tunanin Aliy ne ta d’aga jin muryarsa wani irin sanyi taji tare da tausayin Kansu duka

A hankali ta ansa sallamar..

“Yace kina bacci ko”?

“Eh” tace..

Yace ya jikinki..?

d’an ajiyar zuciya tayi tace “da sauqi”..

Yace bari na barki kinga na manta wayana a gida amma zan sake kiranki anjuma kinji?

d’an shiru tayi…

Yace pls baby kiyi hak’uri da rayuwarmu ki rik’a yiwa mijinki addu’a kinji.. ?

STORY CONTINUES BELOW

Hawaye ta saki sosai wai da duk nauyin da ke kansa kullum yana duba ta

Jinta shiru yace “kina ji na”?

Eh tace bacci ke damuna…

Yace “OK” kiyi sosai ki huta IA zan dawo da wuri..

“Toh” tace

Yace “love u”..!

Tace “me too”..!

Suka yi sallama ta kashe wayar tana hawaye sosai za ta miqe kiran Aliy ma ya shigo da sauri ta d’aga wayar

Sallama Aliy yayi ko saurarawa baiyi ba ya fara magana” kai hankalina na tashe wlh bansan mai zan cewa innarku ba idan iyalan Alhaji suka je da lauyoyi

Ajiyar zuciya hayfa tayi “ta qara yi masa sallama”

Ajiyar zuciya shima Aliy yayi kafin ya ansa cike da fargabar yayi tab’argaza

Jinsa shiru tace, Pls Ni matarsa ce inada hakkin sanin duk abinda zai sanyashi cikin tashin hankali da

Aliy shiru yayi ya kasa magana domin yasan in Yusuf ya san ya fad’awa hayfa wani abu ga me da abinda ya sani na rayuwarsa sosai za su b’ata

Jin shiru hayfa tace “pls ka taimakamin ka fad’amin wlh na fishi shiga damuwa yanzu da na fara ji kuma bazan iya bacci ba indai baka fad’amin ba

Aliy yace wlh in na fad’a miki alaqata da shi Zata iya tsinkewa ni kuma ina k’aunarsa kamar d’an uwana na jini bana fatan sab’ani ya tab’a had’amu

Ajiyar zuciya tayi tace “na maka alqawarin ba zan tab’a fad’a masa ba har sai in Kaine ka fad’a masa”…

Aliy yayi ajiyar zuciya kafin ya bata labarin Yarjejeniyar Yusuf da Alhaji na kud’in zuwa Canada na ta na Yusuf da kuma hidimar aurenta sosai ta ke hawaye why

saidai Aliy ya qara da cewa a gaskiya sam a wancan lokacin Yusuf bayada tunanin aure saidai ya bani labarin yadda ya kamu da tsananin sonki wanda har ni sai da na hanashi ya qi saurarona

Sosai Hayfa ke hawaye da tanbayar kanta to a ina Mominsu ta had’u da Yusuf har ta had’a su aure…?

Saidai babu mai bata wannan ansar sai momin kuma ba zata iya tanbayarta ba tunda har yau bata fad’a mata ba

Ajiyar zuciya hayfa tayi tace “ka turomin account no yanzu zan turo maka kudin amma nima kayimin alqawari koda zaka fad’a masa rasuwar alhaji kada ka tab’a fad’a masa na biya kada ma ka tab’a nuna masa mun taba koda gaisawa

Aliy cike da mamaki yace “wai kudin duka zaki biya”?

A hankali tace “eh”

Sanann abinda ya saura ka yiwa Inna sayayya na kayan abinci sannan daga yanzu duk halin da suke ciki ko na buqata ka rik’a sanar da ni koda msg kayimin

Aliy shi mamaki yake wai zata biya 6M tashi guda tab sai kuma yace ay dama lokacin bikin yaji ance y’ar masu kud’i ce

Godiya ya fara mata tace “nice zanyi maka godiya domin wannan matsalar wani b’angarene na rayuwata da ban sani ba ka sanar da ni “Nagode”

Nan suka yi sallama

Nan Aliy ya tura mata account no inda ita hayfa suna gama magana ta kira Armando ta fad’a masa tana buqatar 7M na Nageria

Lissafi yayi na kud’inta da ke gunsa yace zan miki ciko kad’an yaso kya cikamin daga baya

Tace akwai wannan cash na interview…

Yace ah ah ki ajiye ay zaki iya buqata wani lokacin

Toh tace ta masa godiya yace ki turo account d’in da zan tura kudin zan wuce yanzu

STORY CONTINUES BELOW

Toh tace ta qara yi masa godiya

Suna gama waya ta tura masa account

Aliy na gun makoki cike da tunanin irin sa’ar da Yusuf yayi na samun mata kamar hayfa yaji shigowar alert ya bud’e sosai ya qara girgiza

D’an fitowa yayi yaje nesa da mutane ya qara kiran hayfa

Sallama tayi yace naga saqon amma kudin 6M ne naga 7M

Tace eh kayi musu gyare-gyare ka saya musu duk wani abu na buqata

Sosai ya qara mata godiya

Tace pls kada ka bari ko inna tasan komai sannan shi ka samu dabara yadda za ka masa bayani

Aliy yace karki damu IA su kayi sallama. Sosai Aliy ke cikin farin-ciki ya sallami y’an uwansa ya bar gun makokin inda ya kira lauyansu da Yusuf

Lauyan ya kira lauyan Alhaji nan aka warware komai Aliy ya biya kudin aka maida musu takardun gidansu Yusuf Aliy wani irin farin ciki yaji ganin takardun hannunsa

Allah ya had’amu da abokai na gari kamar Aliy da Yasir…!

Bayan Aliy ya gama da lauyoyi gidansu Yusuf inda Inna na maqota yayiwa Rafi’a da Layla dabara ya shiga d’akin Yusuf ya maida takardun inda dama Yusuf ya fad’a masa da dad’ewa cewa nan zai maida in ya gama biyan alhaji

Ya adana can k’asan akwatin ya fito suna zaune tsakar gida suna d’an hira da y’an matan domin shi kamar Yusuf suke d’aukarsa har innarsu ta dawo bayan sun gaisa yake fad’a mata Yusuf Ya d’anyi aike shine nace ko su qassim suma sunada wasu y’an buqatu

Tace ay wa’anan yaran tunda suka fara jami’arnan kullum cikin bik’atu suke saidai ay rayuwa ba komai ake so ake samu ba

Aliy yace haka ne inna amma karatu dama buqatu ne dashi bari na kirasu naji

Tace toh ta mik’e ta shiga kiching ita da Layla

Aliy sun dade suna waya shi da Qassim da Ahmad inda buqatunsu sunkai kowa 35k don haka a take ya tura musu 200k yace musu inji Yusuf amma ba sai sunkirashi sun masa godiya ba

Kamar su sume yaran don farin ciki suka masa godiya suka yi sallama

Nan ya yiwa innarsu Yusuf sallama yace yana dawowa

Toh tace tana gyaran itacen ta

Kasuwa ya shiga ya saya mata resho mai gurin wuta biyu ya saya musu TV plasma da kwanon gotv da carfet ya sayawa yaran katifa domin sosai yasan yadda innar ke kwanciya qasa ta basu gado ya saya musu kujeru sai kayan abinci sosai buhun shinkafa biyu da da carton taliya macaroni komai na abinci bai manta ba ya dauki hayar pickup a ka loda masa komai ya isa gidan inda sosai innarsu Yusuf ke cike da mamaki haka Aliy yasa kaita shiga da kaya aka jera yace Inna gobe za a miki pentin gidann

Itadai mamaki ya cika ta sai kallo take yayinda Rafi’a ke ta murna sun zama y’an gayu sai layla itama tayi farincikin ganin sun samu TV

Haka dai aka gama sauke kaya duka Aliy ya sallami masu mota ya dawo ya zauna kusa da Inna

Shiru ba tayi magana ba shi ya fara

Inna Yusuf ya turo ayi muku sayyaya amma bayaso ki ta masa godiya shi yana ganin nauyinsa ne dama yayi shiasa bai sanar da ke ba Inna ki ta masa Addu’a da saka albarka shine abinda yafi buqata

Hawaye Inna ta share tace haka ne Aliyu Allah yayi muku albarka duka

Amin yace sannan ya ce Inna ga sauran kud’in 289k ki riqe hannunki sabida wasu buqatun

Kallon hannunsa tayi tace kai ma ka dauki wani abu ko katin waya ka saka

Murmushi yayi yace haba Inna in ban qara miki ba ay bayyi daidai ba na rage amma zan cire 30k xan sayawa Layla waya mai kyaw sabida Ku riqa magana da shi ta yanar gizo

Inna tace eh hakan ma yayi dama tuni su Qassimu ke mata alqawari

Nan ya cire 35 sabida ya saya mata sim ya mata subc na wata da rigar waya mai kyaw ta y’an mata

Nan suka yi sallama inda ya fad’awa inna gobe suje wuni wani gurin zaizo ayi pentin gidan

Inna tace toh tanata saka masa albarka ya wuce

A Canada hayfa na zaune duk tunani ya isheta lallai dole ta qara maida hankali ta taimakawa danginta da na Yusuf sosai taji tausayin innarsu da y’an uwansa za tayi qoqari ta fara kulawa da su kamar yadda take da danginta

d’an hawaye ta keyi na tausayi da son Yusuf da taji yana k’aruwa mata sosai ya keda mutunci da sanin darajar kansa domin ko a wasa tasan bazai tab’a bari tasan halin da rayuwarsa da gidansu ke ciki ba sannan da yadda ya aureta da bashi

Abin tanbayar anan shine tun yaushe ne ya santa?

Batada ansa saidai a yau sosai darajarsa ta k’aru azuciyarta da idanunta da rayiwarta za tayi aiki tuk’uru domin samar da wadata a zuri’arsa da tata

Tun bayan fitan Aliy Innarsu Yusuf ke yiwa yaranta duka Addu’a da fatan nasara a rayuwa kamar ko yaushe sosai ta ke hawaye tana kallon tulin kaya ko wannan cefanen ay sai suyi shekara bai k’are ba ga tulin kud’i tunani tayi bari ta kira su qassim ta tura musu kud’i suma

K’walawa layla da rafi’a dake daki kira tayi suka fito ta bawa layla wayarta tace layla ta kira su Ahmad

Ahmad suka ansa cike da farinciki suka ce Inna dama yanzu zamu kira ki

Tace karku damu gobe zan bawa Aliyu kudi ya turo muku

Da sauri Ahmad yace Inna ay ya turo mana kud’i d’azu za mufi wata biyu ma bamuda matsalar kudi

Shiru Inna tayi tace to kuci gaba da yiwa yayanku addu’ar bud’i kunji

Duk suka ce IA Inna domin dama speaker suke sakawa inta kirasu ko suka kirata

Haka suka yi hirarrakinsu suka gama kowa cike da farinciki

A Kaduna Ammah da suwaiba kamar su haukace ganin alert na kusan 94M inda su tuni suka daina tanbayar hayfa yadda take samun kudin hannun mijinta

Ba ko b’ata lokaci ammah taje ta qarasa kudin kamfaninsu na jabi rd komai ya zama nasu yanzu ta fara shirin shiga Italy da China da Dubai saro kaya kai ko a kabala sosai ake girmama ammah domin kuwa yanzu BMW2018 take hawa motar ta ta bawa suwaiba domin itama suwaiba ta fara karatu a kasu na Literature a yayinda babnsu ke fama da hawan jini ga yawan mafarki da yake da kakan Hayfa mahaifin mamarta na wasiyar da ya bar masa cewa su nema danginsa da suka b’ace saidai shi baban hayfa a da yayi burus ganin bayada kud’i amma yanzu da yaga rayiwarsu ta canza yanason gano dangin na hayfa domin shine alkairi d’aya dazai mata kafin ya bar duniya

Yayi magana da su ammah suka ce ya manta maganar ay hayfa batada wanda ya fisu a duniya shi kuma ya qudure dole ya cikawa kakanta da mahaifiyarta wannan burin shiasa a yanzu ya yanke hukuncin yin binciken ba tare da sanin su Ammah ba

Yana zaune barandar su Da ke gidan ammah suna BQ ne can baya goggo alje na can bayan gida tana gyara zogale tana shanyawa

Tunani yake kakan hayfa Inzo Haru yace y’an uwansa sun b’ace ne a tashar sokoto to shin daga sokoto zai fara nemansu ko kuma duk garuruwan da suke sokoto, gashi yace duk sauran maza ne y’ar uwarsu mace d’aya ce wacce yace sunanta Yalwatu
Ajiyar zuciya tabbas ba qaramin qalubale bane a gabansa domin abu tsawon shekaru 63 gaskiya akwai matsala sosai saidai dole zai fita ya nemowa hayfa danginta koda zai mutu a hanya

Ammah da suwaiba suka yanke shawarar sakawa kamfaninsu suna HH world ma’ana Hadiza Haladu domin gaskiya sosai Ammah ke yiwa hayfa hallaci domin kuwa komai da sunan hayfa take siya sudai ke cin moriyar abin kawai

Wani makeken kamfanine gaskiya wanda ita kanta ammah sai bayan da suka biya kudin take ta tunanin da taga tsadar gurin ashe babba ne haka na nufin gaskiya sai sun tsula masa kudi sosai kafin ya cika dam yadda y’an gayun Kaduna zasu fara sintiri a gurin

Kudi fa iya kudi kamar almara haka hayfa tayi kudi domin sosai dukiyarta ke tafiya a Nigeria taxi napep acab’a ga gidajen haya biyar abin dai kamar mafarki gaskiya kuma haka Models ke tara kud’i kamar y’an k’wallon k’afa shiasa ma  sai su ya su suke aure a turai

A Canada hayfa aiki tuquru domin anata shirin aiki y’an Bahrain ga contract na magajin mulkin saudiya na yad’a mabufar foundation d’insa a Europe domin tallafa marayu da gajiyayyun africa inda yasa a zab’o masa matasan mata masu tashe da na k’asashe daban-daban inda ba B’ata lokaci wani agent yayiwa Armando magana inda Armando ya tanbaya harda Nageria a manufar foundation d’in agent d’in yace eh nan kuwa ya karb’awa hayfa contract d’in da za a biyata $500000 domin zata wakilci Nageria a k’asashe 8 da zaayi taron

Yusuf ma wannan satin zai fara aikin supermarket har an masa interview inda yaci tsabar farin ciki ya kama musu wani motel shi da hayfa 2dys za suyi su barwa yasir gidansa inda kuma yace albashinsa na 2mths zai kama musu gidansu saidai yanata mamakin maiyasa kwanan nan layin aliy baya shiga yanaso yayiwa alhaji aike gashi shima na Alhajin baya shiga

Yana tafiya yana tunani ya iso wani layi da yaga mutane na ta shiga masallaci dukda lokacin sallah bai yiba d’an tsayuwa yayi ganin wata k’atuwar takarda manne gaban masallacin
A hankali ya qarasa ya fara karantawa ana neman mai gadin masallacin ne aiki daga 10pm to 6am

d’an jim Yusuf yayi kafin yaci gaba da karantawa inda yaga albashi $1000 wata

Zaro idanu yayi ya had’iyi yawu ya fara kalle-kalle kafin ya qarasa ya shiga masallacin

Ganin mutane zaune yawanci duk karatu suke kafin a tayar da magrib

Zama shim a yayi nan yayi magrib yayi ishaa sai bayan an watse yaga wani mutum kamar bature amma musulmi sallama Yusuf ya masa ya ansa

Yace ni sunana Yusuf
Baturen yace ni sunana Hamzad
Yusuf yace naga ana neman mai gadi ne…!

Hamzad yace eh mai gadinmu ya rasu
Yusuf yace Allah ya masa rahama

Hamzad yace amin samari

Yusuf yace inason aikin ne
STORY CONTINUES BELOW
d’an shiru hamzad yayi yana kallon Yusuf ganin matashi da kyaw da quriciya yace zaiyi gadi na masallaci kasancewar yawanci masu gadin da suke samu dattijawa ne

Yusuf yace IA duk dokar da zaku shimfid’amin zanbi amma don Allah ka bani aikin zanyi

Hamzad yayi ajiyar zuciya yace samari bazance maka zamu d’auke ka ba sai bayan committee masallaci sun zauna sun duba takardunka sabida mai masallacin shine ministan ilmi na nan Toronto asalinsa d’an Bagdad ne amma haifaffen nan Toronto don haka kaga yau laraba ka kawo takardunka ranar lahadi litinin zan qaddamar da shi abinda duk commeety ta yanke za kaji IA

Yusuf yayi d’an ajiyar zuciya gwiwarsa tayi sanyi shi da iyakarsa secondary da wuya su d’aukeshi

Nan Hamzad ya bashi katin masallaci da number da address da komai da zai rubuta application na neman aikin…. Ikon Allah wani abu sai turai wai gadi a masallaci sai an rubuta application…!

Suka yi sallama da Yusuf ya fito yana tafiya yana addu’ar Allah ya d’orashi kan Committee masallacin har ya iso gida dama tun pool suka rabu da Yasir wai gidan tiffun zai wuce daga can zasu wuce club

Hayfa na café ya dawo yayi wanka ya duba kanta ta dafa masa jolof d’in shinkafa da kifi da zogale kamar yadda yace mata yana so

d’an murmushi yayi ya d’iba yana niyar zama itama ta shigo
Tsayuwa yayi suna kallon juna
Ajiye abinci yayi a kantar ya qarasa ya janyota ya rungume yana shanshanar kanta itama tana shanshanar qirjinsa da take kwance

d’an d’agowa yayi yana kallonta yace “drewdrop kin rame why”?

d’an tsoro taji kafin ta sunkwi da kanta
D’ago kanta yayi yana kallon yadda idanunta suka qara manya gaskiya ta rame ya qara fad’a a ransa

Rik’o hannunta yayi suka je kujera ya zaunar da ita cinyarsa yana kallonta yace “pls tell me wani abu ke damunki”..?

kasa bashi ansa tayi domin tsabar exercise ne da suke yi na shirin gala ya ramar da ita wanda wai hakan ne ma daidai a gurin iyayen gidanta su Armando da Bunil

K’wallah ne ya ciko mata…

hannunsa yasa a hankali yana goge hawayen yana lashewa yace “pls ina nace banason anamin wannan asarar”?

had’iyewa tayi kamar ba itaba saidai kanta still yana qasa..

A hankali ya fara magana” pls babyna  addu’a za ki rik’a yiwa rayuwarmu nasan kina aiki dayawa duba da yadda café d’inku ya shahara a area d’in nan kullum cike yake koni da nakan gaji kamar zan mutu sabida aikin baya qarewa sai lokacin tashin mutum yayi, amma kiyi hak’uri ki sani babu wani nasara ga rayuwar mutum bayan ya nema halak d’insa da kansa koda munada arziki zaki iyajin sha’awar yin aiki domin nishad’antar da kanki saidai nasan wannan aikin yayi miki yawa kuma na fiki bak’incikin wahalar da kike yi

d’an shiru yayi kafin yace amma IA ba zaki dawwama kina wannan bautar ba bazan tab’a barinki ki wahala ba IA

Hawayen da ta rik’e ne ta saki a hankali ta rungume kansa shi kuma ya runguma cikinta su duka suna ajiyar zuciya

Kusan 5mnts ya d’ago yace “kinci abinci”?

Girgiza kai tayi sabida kullum daga kamfani ake bata abincinta taci bayan magrib a café kan ta dawo gida abincin ya gama sauka tas dukda haka saidai tea dinta zata sha shima a kamfanin ake bata wannan masifa ta rayuwar model
Saukowa tayi ta fara bashi da kanta har ya qoshi ta kwashe kayan ta kai kanta ta had’o masa coffee tana bashi har ya shanye suka zauna kujerar tana kwance jikinsa yana bata labarin jiya ya gama contract d’insa na aikin dare sosai hayfa tayi murna
STORY CONTINUES BELOW
Saidai d’an shiru yayi shi kansa bayan ya tuna masallaci in ya samu basuda wani sauran zaman gida. hayfa ma shiru tayi tunawa da tayi jibi zasu tafi aikin y’an Bahrain a Ontario da Cubec
Kowa ya fad’a tunani sai Yusuf ne ya cakulkule ta yace “kina tare da mijinki tunanin mai kike yi”?

ajiyar zuciya tayi tace “a café ance akwai wani bikin sarauta na larabawa zamu je mu kwana aikin bada café”!

Armando ne yace tace haka
d’an shiru Yusuf yayi shima jibi zai fara supermarket saidai bayason tana wahala dayawa yace “amma wannan zalimci ne su turaku wani guri aiki bayan biyan da suke muku na iya café ne”…

d’an ajiyar zuciya tayi tace sun biyamu wannan d’in daban

Shiru yayi….

d’an juyowa tayi tana shafa fuskarsa ta masa peck a kumatu tace karka damu zan iya aikin IA
ajiyar zuciya yayi yace shikenan

Ita hayfa mamakinta shine tunda ta fara aikin café Yusuf ko sau d’aya bai tab’a tanbayarya mai tayi da kud’inta ba kuma har yanzu yakan siyo mata rigar sanyi ko pads ko chocolate in yayi cefanen gida dukda yanzu kafin yayi sai ya samu anyi in ya tanbaya tace yasir yayi ta mita a qarshe yaje ya sakawa yasir kud’i a drower pool shi kuwa yasir yayita murna ya daina cefane ga kud’i hayfa kan bashi tym to tym tace ya qara kud’in haya kuma kada ya tab’a bari Yusuf ya sani
Jinta shiru ya sunkuyo ya fara kissing d’in wuyanta saidai ma tana period amma bata habashi tab’ata ba domin yanzu taji saukar period d’in.

da safe bayan sun karya ta yi musu samosa ta nad’e suka sha kiss ita da Yusuf ya wuce aiki ta fara shirin zuwa kamfani itama

Haka a pool Yusuf ya bawa yasir labarin masallaci yasir sosai ya tayashi murna da bakincikin still dai babu morar dare kai da gimbiya

duka Yusuf ya kai masa yace kaidai Allah ya shiryeka.

  A kamfani Raudha na ta satar kallon hayfa da ita hankalinta ma na can kan exercise d’inta
Sosai Raudha ke jin kishin hayfa domin da kanta ta fara gano nasarar da ke fuskantar hayfa a duniyar models sabida yawanci wasu sai suyi shekara ko shekaru kafin su fara samun contract na qasashen qetare amma hayfa Armando ya taqarqare sai samo mata ya keyi yanzu anjuma kaji ta samu bangon Gala na Milan
Inaa tace da sauri ni zan samu komai zai faru kuwa
Liliana ce ta dafa ta tace ” wai ko kinsan contrac d’in prince d’in Saudia Khadija ce za tayi representing Nageria?

Raudha tayi tsaki kawai…

Liliana tace bayan ga Monaliza ta kamfanin Baharj kinsan tare mu ka fara aiki da ita amma Armando ya bawa wannan uwar jiji da kan sannan ki duba duk mun girmeta mun fita experience
Raudha dai tsabar takaici bata cewa komai sai tym to tym ta kalli hayfa a b’angarenta
Liliana ma kallonta tayi tace “Ni na rasa Ina Armando ya samo yarinyarnan ya maidata kamar Rachel

Tsaki dai Raudha ta qara yi ta kalli Liliana tace “gobe kinsan suna can Ontario gurin shooting d’in aikinta na Bahrain so mu daga nan Unguwa zaki raka ni”

Liliana tace Unguwa ina?

Murmushi Raudha tayi tace gidan Mutumina yau zan fara kai masa ziyara kinsan Zakir ya bani address
Kallonta Liliana tayi tace bakya tsoron ya wulaqanta mu?

Tsaki Raudha tayi tace komai zaimin na shirya jurewa zuwa lokacin da zan mallaki zuciyarsa
STORY CONTINUES BELOW
Liliana tace tab ay shikenan …. Wane tym za muje?

Raudha tace dare mana kinsan komai yaya lokacin yana nan domin jiya na tura zakir club a kace ya daina aikin club
Liliana tace sister da gaske haka kike bibiyar rayuwar sa? amma na lura fa guy d’in d’an wulaqanci ne sosai

Raudha tace kin manta ni ne idan na so abu?

Liliana ta saki dariya tace haka ne kuma
Raudha tace zan baki kayan da saki saka sabida na fad’a miki so nake mu canza image d’inmu a idanunsa

Liliana tace ay babu damuwa sister haka suka gama exercise d’insu suka bar gym d’in suna hango hayfa da Coach yanata gasa mata azabar aiki

Su su Raudha suna zaune ne gidan Liliana domin yanzu ita ke da contract da su Armando ita Raudha na cash take dukda sun shirya da Armando ya lallab’a bunil zasu sake bata chance su bata contract amma Armando yace sai bayan Gala domin ya qudure hayfa zata samu bangon Gala IA
Bayan ta gama exercise ta shirya ta shiga office d’in Armando yana ta aiki yace “queen ki shigo mana”

Qarasawa tayi a hankali ta gaisheshi yace zaki wuce gida ko?

Eh tace…

Ya jawo drawer ya d’auko wani d’an qaramin kwali nannad’e ya miqa mata

d’an kallon kwallin tayi bata ansa ba

Murmushi yayi yace duk mata na son gift shiasa kikaga duk gidajen d’inkunan duniya mu ke yawan yiwa yaranmu kyawta

d’an ajiyar zuciya tayi kafin ta ansa ta masa godiya yace gobe 2:pm zamu wuce IA amma zaifi kyaw kizo kamfanin tun 10:am haka sabida shiri kinsani kamar ko yaushe

OK tace ta masa sallama ta fito a qafa ma take d’an tafiya ta ga wata kasuwar layi haka ta tsaya kaji nama kifi duk fresh
jakarta ta bud’e taga tanada kud’inta sauran na aikin café taje ta saya kazar da nama da kifi sai vegetables da Irish ta hau taxi sai gida

Tana dawowa ganin har 2:pm ta kusa tayi wanka tasa wata rigarta mai kyaw ja ta material ta tufke gashinta ta shiga kanta girki

Paten Irish da vegetables tayi musu sannan ta musu paper chicken yayi kyaw ta jera musu a carfet tayi musu drink na abarba da fresh milk duk ta shirya musu ta koma Ta kwanta ta kuna data suna wpp call da aminiyarta tana bata labarin tayi saurayi balarabe

Dariya hayfa tayi tace ina duk y’an uwanmu mazan nja
Salma tace to sunqi kawo katin gayyatar ba sai na ansa na wanda ya kawo ba koda waye

Dariya hayfa ta qara yi tace Allah yasa alkairi to

Salma tace nima fa ba aurensa zanyi ba ina zan iya da iskanci y’an masar shan sigari da shisha d bin mata kawai sai 4 fun ne
Hayfa tace Allah ya kawo mana nagari kinji karki damu lokacine
Salma tace haka ne sisto ya hubby d’inki?

Hayfa tayi murmushi tace yana lafiya

Salma tace kinsan sai inta mamaki wai kece Khadija Khalid d’ina kika yi aure…

Hayfa tayi d’an murmushi
Salma tace wlh nima gaskiya kullm ina tunani bikinki yayi sauri kodai nima kin b’oyemin tuntuni kuke tare da shi..?

Hayfa dai murmushi tayi tace wlh iya gaskiya na fad’a miki
Salma tace amma yaushe kika fara sonsa har kuka yi auren..?

STORY CONTINUES BELOW
d’an shiru hayfa tayi kafin ta fara tunani ranar da ta shigo Canada zuwa komai da ya faru tsakaninta da Yusuf daki-daki ta fara sonsa ne cikin lokaci irin kulawa da ita da tarbiyarta da yake kamar qanwarsa ba matarsa ba d’an lumshe idanu tayi tabbas da lokaci ta kamu da sonsa ba tare da ita kanta ta sani ba har sonsa yayi mata zurfi
Qara Lumshe idanu tayi tunowa da tayi da yadda yake mata magana yadda yake tab’ata yadda yake kallonta sosai Yusuf ya tafi da dukkan zuciyarta tabbas ya koyar da ita sonsa ne kamar yadda ake koyar da yara karatu a makaranta cikin rarrashi da juriya uwa uba tausayawa

Salma jin shiru tace “Kk kina nan”?

ajiyar zuciya hayfa tayi tace “ina ji”

Salma tace amma ki fad’amin gaskiya kinsan su Nusaiba Bello da Hanan Turaki suna cewa wai kud’i kika bi babu wani love kinsan kowa yasanki da Kamal
Ajiyar zuciya hayfa tayi tai shiru…

Yusuf da suka shigo jin shiru sai abincinsu yasir ya zauna zai fara cin abinci Yusuf shi ya nufi d’aki sam bata ji motsinsa ba

Salma tace wai kina ji na kuwa?

Hayfa tace kinsan Allah?

Salma tace eh mana sisto

Hayfa tace wlh inason mijina ne da dukkan zuciyata kuma koda shi yafi kowa talauci nan duniya zanci gaba da sonsa haka kuma koda yafi dangote kudi son da nake masa bayada alaqa da kudin har abada
Salma tace na yadda sisto Allah ya barku tare ya baku zaman lafiya
Amin hayfa tace suka koma hirar karatun Salma Yusuf juyawa yayi ya dawo falo zuciyarsa wasai kamar auduga wani irin farin ciki ya ke ji da har yunwar da ya keji yaji ta gushe

Yasir ya gama cin abinci ya kalla yasir yace bari na d’anyi bacci a gurin walid kafin magrib
Yusuf yace OK domin sosai yanzu suka fahimci junansu shi da walid da yasir kuma suke taimakawa junansu sanin Yusuf na da aure dole yana buqatar kad’aici da matarsa hakan yasa walid yace somtym yasir ya rik’a zuwa suna kwana gunsa

Bayan sun gama waya da Salma ta fito sai ganinsa tayi mik’e a kujera yana bacci juyawa tayi za ta koma ciki ya rik’o hannunta ta fad’o jikinsa

Peck ya mata a tsakiyar ka yace kin wuni lafiya?

Girgiza kai tayi alamar “eh”

A hankali tace kaci abinci?

Yace waye zai bani..?

d’an dukan qirjinsa tayi ta tashi ta sauko ta fara zuba masa ta koma kujerar shima ya tashi ya zauna ta fara bashi

Saida ya k’oshi ta kwashe kayan kusan 5:pm lokacin tace masa yau ba aiki sai gobe in za suyi tafiyar gaba d’aya

Zamansu suka yi manne da juna sunata hirarrakinsu inda Yusuf yace mata shima gobe zai fara sabon aikinsa
Haka har magrib yayi sallah ita tana hutu ya idar yace tasa hijabi su d’anje yawo
Koda suka fita taxi taga ya tsaida suka yi tafiya mai d’an nisa amma taqi tanbayrsa har saida suka iso suka sauka

Ganin motel ta kalli Yusuf yace In kika dawo aiki zamu zo nan ki huta na 2dys
d’an kallonsa tayi da wani irin yanayi
Rik’o hannunta yayi ya tsaya gabanta shima yana kallonta yace “bamu tab’a samun kasancewa tare ba tun da muka yi aure ko kuma ya d’an saki dariya yace ko kuma tun da mu ka fara rayuwa a ma’aurata”

d’an ajiyar zuciya tayi tai shiru…

Yace IA nan da wata biyu ma zamu samu gidanmu wannan matar ta kusa da walid zata tashi wata biyu nan gaba tuni nasa Yasir yayi mana buking d’in kuma an bamu kafin ta tashi IA na gama shiri sai mu koma

Hawaye hayfa ta saki ita da keda damar gida kyawta ma amma dole ta hak’ura kuma inma tace masa su kama mai d’an fad’i ba yadda zaiyi ba Armando yace mata da $2000 zasu samu 2bdrms mai d’an fad’i da wadata kuma koda kudin kashewarta na wata zasu iya Kama haya da cefane da biyan su bills amma yaya za tayi

d’ago fuskarta yayi yana kallonta yace “Ina sonki fiye da yadda na ke son kaina nasan bana baki dukka hakkokin da ke kaina pls ki rik’a yimin afuwa”..!

d’an d’agowa tayi tana kallonsa shima kallonta yake kasa magana tayi sai rungumeta yayi sun dad’e kafin suka bar gurin inda suka tsaya kafe ya fito da katin masallaci ya shiga Internet yayi typing komai na information d’insa ya tura a Email d’in masallaci kamar yadda Hamzad yace bayan ya gama suka kamo hanyar gida

Wanka suka yi tare suka saka kayan bacci Yusuf yayi Ishaa suka kwanta manne da junansu suna d’an hira har suka yi bacci.

A Nageria bayan an gama gyaran gidansu Yusuf yayi kyaw har d’akin Yusuf an gyara Innarsu Yusuf ganin suma su Qassim basu nan in rafi’a ta tafi makaranta gidan shiru yake sabida ita layla tana ta shirin zana waec don haka Inna tayi tunani gara ta d’auko qanwar kakarsu Yusuf ita kad’ai ta saura cikin dangin su manya…

Kiran layla da ke d’aki tayi layla tace gani Inna

Inna tace ki kiramin Baffa Yahuza zanyi magana fa shi

Layla ta zauna kusa da innar ta karb’a wayar Inna ta lalubo number ta jefa koda ya ansa suka gaisa ta miqawa Inna

Bayan sun gama gaisawa Inna tace “dama kwanaki kace ciwon qafa ya dami goggo Yalwati ko?

Yahuza yace eh wallahi kwana biyun nan ma ya tashi gashinan munata fama

Tace toh ko zaka shirya ka kawota nan sai muna zuwa malam aminu IA zamu dace
Yahuza yace baki ganin nauyi zai qaru miki?

Tace babu komai ka kawota kawai IA Allah zai dafa mana
Yahuza yace shikenan zan mata shiri IA zuwa jibi sai mu shigo
Inna tace kada ka damu da shiri ka turomin lambar da za a turo kudi sai na turo muku na hanya d’in

²⁵

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE