KAUNA CE PART 1 BY MAMAN NOOR
Wata matashiyar budurwa na hango a titi rike da gana most go tana yawu da alamu bakuwa ce a garin minna da ka kalleta kasan tana tare da yunwa da gajiya
Yawu take tana zagaye Mobil
Gajiya tayi domin bata San inda zata ba
Zama tayi gefen titi tayi tagumi tana tunanin halin da ta sinci kanta
Wani mutumi ne ya lura da ita tun lokacin da take yawo
Karasawa yayi inda take
yace”baiwar Allah lafiya?”kallonshi tayi tace”lafiya lau”
Yace”kai ba lafiya tun d’azun na lura kina ta zageye wurin nan in akwai matsala ki sanar dani in taimaka miki,
Ajiyar zuciya ta sauke tace”bawan Allah ni bakuwa ce a gari nan bani da kowa a garin nan
Kallonta yayi da mamaki yace”toh meya kawo ki?”
Tace”kaddara”a takaice
Yace”amma be kamata a ce mace kamar ki,kin bar gida ba me yayi zafi haka?”
Tace”akwai abubuwa a rayuwa da fad’a su bata da fahida ni yariya ce da ake zaluntar”
Kallonta yayi yace”toh muje ga shagona can nasan kina jin yunwa”
Tace”toh nagode”tare da mikewa ta bi bayanshi
Shagon sayar da takalma mata ne,kujera ya bata ta zauna ya kira a kawo mata abinci
A take away wata budurwa ta kawo musu,ya karb’a ya mika mata
Yace’ki ci in kin koshi sai muyi magana”
Tace”toh”cin shinkafa da miyar ta farayi kamar Wanda bata tab’a ganin abinci ba
Shidai Salisu kallonta yake
Bayan ta gama yace”yanzu ki fada min ke wacece”
Ledar pure water ta cire a baki tace”labari ne mai tsawo,bana jin zan iya fada maka”
A ranshi yace”kenan ta shigo yawon bariki ne”a fili yace”toh ba damuwa amma a ina zaki kwana?”
Kallonshi tayi hawaye na bin kuncin ta
Tace”
Kallonshi tayi tace”ko a bakin gada na samu zan kwana”
Murmushi jin dadi yayi yace”a’ah kina mace me zai kai ki kwanciya bakin gada?karki damu zan taimaka miki in kaiki gidana “ya kare magana da tsare ta da ido
Sungunawa tayi har kasa tace”nagode Allah ya kara budi nagode sosai”
Yace”babu komai,amma ya sunan ki?”
Tace”sunana Rauda“
Yace”suna mai dadi “murmushi tayi tace” nagode”
Shiko kare mata kallo yake yi yana aiyana inda daren yau zai kasance
Da misalin karfe 6:pm aka fara kulle shaguna
Kallonta yayi yace”d’auki jakar ki muje”
D’auka gana most go tayi ta bishi bayan ya kulle shagon shi
Bayan mashin dinshi ta hau a hanya ya tsaya ya tsiye masu take away a wani restaurant
Wani karamin gida ya kaita babu mai gadi a gate ya paka ta sauka
Shima sauka yayi ya Ciro makulli a aljihu ya bude gate din
Kallonta yayi yace”muje ciki ko?”
Binshi tayi suka Shiga sai kalle-kalle takeyi domin alamu sun nuna shi kadai ne a gidan
D’akin ya bude suka shiga,a falo ta tsaya
Yace”ki zauna mana”
Tace”ina matan ka?”
Murmushi yayi yace”ni bani da aure”
Zatayi magana ya katseta da cewa”ki zauna zamuyi magana anjima amma yanzu kina bukatar hutu”
A takure ta zauna shi kuma ya shige ciki bedroom din ba a jima ba ya fito tsanye da jallabiya da alwala
Tace”zanyi sallah”
Yace”ki Shiga ciki akwai bayi”
Tace”toh”
Yace”ni zan tafi masalaci”
Tace”toh sai ka dawo”yana fita ta mike tana karewa d’akin kallo
Shiga d’aki tayi tana kallo save contain ne me d’auke da d’aki d’aya falo sai kicin
Shiga bayin tayi ta d’auro alwala ta fito falo ta bude zip din gana most go dinta ta Ciro hijabi
Dadduma ta gani a saman kushin ta d’auka ta shimfide sanan ta tada sallah
Sanda ta tabbatar ta rama sallah da ake binta sanan tayi addo’oi ta shafa
Tashi tayi ta shimfide dadduma ta maidashi saman kujeran zama tayi a kasa tayi tagumi tana hawaye
A haka salisu ya dawo ya sameta
Cikin damuwa yace”ya haka kuma Rauda miye na kuka?”
Share hawayen tayi tace”babu komai”
Yace”meyasa baki kunna tvn ba kuma ga abinci baki ci ba”
Tace”yanzu zan ci”
Yace”maza cinye shi tas karki kwana da yunwa”
D’aukan take away din tayi ta bude fried rice ne da kaza,ci ta farayi tana kallon tv da ya kunna
Bayan awa biyu lokacin goma tayi
Yace”Rauda tashi kije ciki ki kwanta”
Tace”ah’ah kai ka tafi ni nan ta isheni”
Ya gane tsoro take ji dan haka yace”kije ni zan kwana a kujera”
Tace”nan yafi min”
Yace”toh ba damuwa tunda kin fi son nan din toh sai da safe”
Tace”Allah ya tashe mu”
Shigewa yayi tana ganin haka ta Ciro zani a jakarta ta kwanta a 3seater ta rufe jikinta
Sai dai bacci ya ki d’aukanta sai juye-juye takeyi
Bayan awa d’aya wani bacci mai nauyi ya kwasheta
Cikin dare misalin 2″ 03
DOWNLOAD COMPLETE BELOW ⬇️