KUNDIN KADDARATA CHAPTER 2 BY HUGUMA

KUNDIN KADDARATA CHAPTER 2 BY HUGUMA

 

 

Suna cikin hirar mukhatr ya turo qaninta mubarak yayi kiranta ta fito zasu tafi,nan mama ta hada mata su kuka kubaiwa daddawa barkono har da tsakin masara saboda dambu ko dan malele,tana hada mata kayan tana dada kwantar mata da hankali tare da jaddada mata kada ta sake ta tashi hankalin mijinta ko ita kanta,ko tace zata yi wani rashin kyautawa ga daya daga cikin ‘yan uwan mukhtar,haihuwa kuwa lokaci ne,idan Allah yaso ma sai taga sanadiyyar shigowar wata ita ma ta samu nata rabon,ta dora da cewa
“Bare ma duka duka nawa kike sumayya,mu a da can Allah na tuba ba sai kiyi shekara goma da aure baki haihu ba babu wanda ya damu da ke,haka kema baki damu kanki ba,ci da zuci ne kawai yanzu irin na yaran zamani” maganar sai ta bama sumayya dariya da kunya,har ta sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta.

Suna shirin kwanciya bacci lokacin yana zaune gefan gadonsu yana shan ruwan baqin shayi,ita kuma tana taje kanta,ta cikin madubin yake qare mata kallo yadda kullum take sake zama cikakkiyar mace,tamkar ba zata masa magana ba amma abun nata cinta a zuciya,saboda daga shigowarsu gida zuwa shirin kwanciya da sukeyi yanzu yaya yahanasu ta kira shi ya kusa sau biyar,duk da bata kusa amma ta fahimci taqaddamar me suke,maganar lefe ne da yace ba zaya yi ba,ta dan cije lebanta sannan tace
“Ya mukhtar”
“Ya akayi sumy?” Ya fadi yana saurarenta.

Sai data jawo dressing chair gabansa ta zauna sannan ya dubeshi,cikin nutsuwar nan tata hadi da kaifin hankali da zurfin tunani
“Ya mukhtar kayi haquri idan na maka shishshigi,sai nake ganin baka kyauta ba”,cikin rashin fahimta ya tambayeta
” da akayi me fa?”ta danyi jim kamar ba zata yi magana ba sannan tace
“A ganina bai kamata ka dinga sa’insa da yaya yahanasu ba,ko banza ta girmeka,bugu da qari ita ta zame maka tamkar mahaifiyarka ka manta?,ita ta raineka har ka kawo girmanka,ka san cewa dai ba zata taba yin abinda zai cutar da kai ba,a ganina auren nan saboda qaruwarka ne take buqatar kayi,ko babu komai idan fa’iza ta haihu sai an fara cewa danka kafin a ce dan yaya yahanasu ko?” Ta dan sarara da maganar tana hadiye wani abu mai daci wanda bata san meue sanadiyyar tasowarsa ba daga qirjinta.

Ko bata qarasa ba ya fahimci kan me take magana,saboda haka ya bata fuska
“Kinga sumayya,babu ruwanki da wannan maganar ki fita a cikinta,lefe ne nace bazanyi ba suyi mata,ai bani nace ina son auren ba ko?,ina zaman zamana haka kawai ina lallaba rayuwata sai su baro min aikin da bani na saka su ba?”.

Kai take gyadawa idonta cikin nasa wanda tuni ya tara qwalla shirin zubowa kawai take
” na gode ya mukhatar,ina ka taba gani an auri budurwa ba’a yi mata lefe ba?bayan haka kuma ka riga da ka san cewa matuqar bakayi lefe ba to sumayya ce ta hanaka,duk wanda yaga laifina ko ya zageni ya mukhtar kai ka jawomin”sai ta tashi daga saman kujerar ta haye gado ta lulluba har saman kanta kaana ta fashe da kuka.

Har cikin ransa ya dinga jin shigar kukan nata,ya runtse ido yana jin bata can can ci haka ba,da me zata ji cikin abu ukun,sai ya sanya hannayeshi ya dagota baki daya zuwa jikinsa yana goge mata hawayen tare da fadin
“Ya isa sumayya,ya isa,me kike so ayi?,gaya min” sai da taja hanci kadan sannan tace
“Kayi lefe kamar yadda yaya yahanasu ta buqata”
“Shikenan an gama,sunci darajarki” sai ta saki dan qaramin murmushi sannan tace
“Na gode”.

Washegari yana cikin karyawa kafin ya fita wayarsa ta soma ringing,sumayya ta dauko ta miqa masa da yake tana kan t.v stand tana chargy,daga yanayin maganarsa kawai ya tabbatar mata yaya yahanasu ce,kuma zancan jiya ne bai wuce ba,a gimtse ya amsa cewa zaiyi laifen,amma fa sam shi ba kudi zai bada ba,zaiyi iyakacin abinda zai iya ya kawo musu,daga haka ya kashe wayan ma baki daya,tana gefe tana saurarensu kanta sunkuye tana wasa da yatsun hannunta,ya kammala ta masa rakiya kamar yadda ta saba,dawowa yayi da baya ya rungumeta sannan ya sumbaci goshinta
” Allah yayi miki albarka”ya fada yana sakinta
“Amin ya mukhtar” ta fada cikin farinciki,saboda tuni maman ta ta gaya mata albarkar miji na bin mace,hakanan fushinsa ko  yardarsa na tare da ta ubangiji.

Cike da farinciki ta koma cikin gidan saboda albarkar da ya sa mata ta faranta mata,taci gaba da kintsa ragowar ayyukan da suka rage mata,bata jima da kammalawa ba ta zauna tana hutawa wayarta ta dauki qara,da sauri ta daga ganin sunan abbanta na yawo bisa screen din wayar.

Cikin girmamawa ta gaidashi ya amsa mata yana tambayarta gida da kuma mukhtar tace ai yama fita.

“Mamanki ta gaya min mukhtar zai qara aure”
“Eh abba malam”
“To ina fata ba zaki watsa mana qasa a ido ba,ba za kiyi watsi da tarbiyyar da muka baki ba”
“In sha Allahu malam”
“To Allah ubangiji ya albarkaceki ya albarkaci aurenki” daga haka ya dora mata da nasiha cikin hikima da ilimi,cike da fadar Allah da ma’aikinsa,hakan ba qaramin sake kwantar mata da hankali yayi ba,ya qare nasihar tasa da fadin
“Babu wani abu da kike buqata?”
“Eh babu malam” ta fadi hakan saboda babu abinda mukhtar ya gaza da shi,don hatta kudin kashewa yakan qimanta ya bata,ya danganta da yanayin samun da yayi a kasuwa.

“To shikenan,haka ake so,inaga zan duba wajen sati na gaba ko wajejen satin sama,zan aiko abubakar(yayanta ne shine na fari a gidansu,amma baiyi aure ba karatu yake)zaizo. A fidda kayan gadonki da kujerunki a sauya miki wasu” farinciki ya cikata,duk da cewa wadan nan natan ma babu abinda sukayi,don sanda sukayi shekara hudu da aure mukhtar ya fitar da na aurenta na ainihi ya sauya mata su.

“Na gode,na gode qwarai malam Allah ya saka da alkhairi,ya qara lafiya da nisan kwana mai amfani,Allah ya qara budi da rufin asiri”
“Amin ya Allah,amma abinda zaki biyani da shi kawai kici gaba da zaman aure cikin gidanki”
“Da yardar Allah malam” ta amsa masa daga haka sukayi sallama.

Sosai malam yake aon sumayya,don tun tana mitsitsiyarta halayyarta daban take,tana da tarin haquri kawaici da zurfin ciki,shi yasa duk cikin yaransa yafi sonta,duk da cewar dukan yaran nasa maman sumayyan ce ta haifesu,ko a lokacin da suka aura mata mukhtar ma ce mata kawai yayi ga miji yayi mata kuma aure zaiyi mata,bata ce komai ba don ba wayo gareta ba,duk da haka dama kunya gareta,gudu tayi ma ta bar gurin sanda malam din ke gaya mata,ita ce yarinya mace ta farko a gurinsa sai qannenta su hudu.

Mukhtar zamu iya cewa rako wani abokinsa yayi gurin malam din kasancewar malam din yana bada karatu tsakanin sallar magariba da isha’i wa matasa da dattijan unguwa,gani daya ya yiwa sumayya yaji tayi masa kasancewarsa mutum wanda sam baya da sha’awar auren macen da tayi zurfi a karatu,tunda yayi universty shima yaga irin qazamar rayuwar da mafi yawancin ‘yammatan keyi duk da ba duka aka taru aka zama daya ba.

To sara ne yazo kan gaba shima malam ba mai son yaransa suyi bokon bane,saboda haka yana bincike kan mukhtar ya tabbatar da nagartar halayyarsa ya basu auren sumayyan.

Da fari ‘yan uwansa sun so su turje kan mai zai sa ya auri yarinyar da rainonta kawai zaiyi,musamman yaya yahanasu wadda ita ta riqe mukhtar din,saboda bai wuce shekara biyar a duniya ba Allah ya yiwa mahaifiyarsu rasuwa wanda dama tun mukhtar na da watanni a duniya mahaifinsu ya rasu,to amma daga bisani suka haqura kasancewar sun lura mukhtar din bashi da niyyar fasa aurensa.

Da fari sun karbi sumayyan a matsayin ‘ya kuma qanwa,amma daga lokacin da suka lura da gatan da mukhtar ke mata hassada ta soma aiki,duk da ba zaka kirashi mai kudi ba amma mai arziqi ne,iyalansa sunfi qarfin yin kukan rashin wani abu cikin gidansa,shekara uku tayi ta cika shekara sha shida,a lokacin ta zama mace saboda Allah ya mata halitta da jiki mai kyau,sai suka juya akalar hassadarsu kuma zuwa sa mata idon yaushe zata samu ciki?,yaushe zata haihu?,wanda har yau suna bisa wannan bigire basu sauka daga kai ba

Wannan kenan…..

Sati hudu suka sanya lokacin aurensu,sunata budirinsu suna shirye shiryensu ango ko oho,kayan lefe ne yace zaiyi kuma bai fasa yi din ba.

A falonta ta tadda shi yana amsa waya bayan ta gama soya masa wainar fulawa da yace yana sha’awa har tana ta masa dariya qai qwalama ce kawai ta dameshi,mai ya hadashi da abincin mata,ya sauke wayar daga kunnensa yana janyo plate din tare da budewa yana fadin
“Yauwa amaryata kuma uwargida na” qeya ta juya masa tana turo baki
“Um_um,barni a uwar gidan dai,amaren na nan tafe” cikin sigar tsokana ya dan talle mata qeyar data turo masa
“Ka jini da yarinyar nan wai itama ta iya kishi?” Duk da tasan wasa yake sai ta juyo tana dubansa zuciyarta na raunana amma ta dake
“Don me bazanyi kishinka ba ya mukhtar?” Bai so maganar tayi tsayi don bata masa rai maganar take balle ita saboda haka yace
“Haka ne” a taqaice sannan ya hau qirqiro santin waina duk da cewa a zahiri tayi dadin,biye masa tayi tana masa dariya tare da kara masa filo a bayansa.

Sai da yaci kusan rabi sannan tace da shi
“Nikam yaya mukhtar banga kana shiri ba” cikin son samun qarin bayani yace
“Wanne irin shiri?,name?”
“Banga wani sauyi ba agidan nan?”
“Kamar wanne iri fa” ya sake tambayarta
“Gani nayi kace na kwashe shirgin dake cikin dakin shirgin can nan amarya zata zauna,nace maka ka hada mata da naka dakin itama ta samu falle biyu ka qiya,to a barshi a hakan,amma ya kamata ace daga dakin nata zuwa tsakar gida ko shafen farar qasa ka yi masa don ya haska ko,tunda nawa dakin ba’a jima da yi masa fenti mai tsada ba fes yake kamar yau akayi”.

Banza yayi da ita kamar bai ji ba har sai da ta qosa tace masa
” kana jina kuwa ya mukhtar?”
“Ina jinki kuma bazan yi ba,ke wallahil azim kika sake yimin magana makamanciyar haka sai ranki ya baci,idan zata zo ta zauna haka ta zauna,idan ba zata zauna ba ta qara gaba dama ba ni na gayyatota ba,haba,dame kike so naji?”.sai ya miqe a fusace ya fice zuwa dakinsa ya barta da sauran wainarta.

Jikinta ne yayi sanyi,tayi da na sanin yi masa maganar,sai data bashi kusan awa guda sannan ta gyara gurin ta shirya zuwa shigar barci tabi bayansa don ta lallashe shi.

Bata sake masa maganar ba kuwa,sai ranar asabar ranar ‘yan yaranta duka suna gida saboda ba ranar karatu bace,ta aika nana tayi mata kiran wani dan saurayi dake maqotansu,tace ya duba mata don Allah farar qasa kwano nawa zai isa dakin zuwa tsakar gidansu ya gaya mata yadda yake zaton zata isa,cikin kudin da take adanawa ta qirgo ta bashi har da kudin mota,cikin minti talatin ya dawo,tasa ya jiqa mata sannan ya tafi ta masa godiya ta bashi dari tace yasha ruwa.

Yaranta ta kalla wadanda sun kai su takwas,akwai bilkisu,fatima,hauwa’u,khadija,aisha,ummi,asma’u sai nana ta gurinta
” maza kowa yaje gida ya cire kayan jikinsa ya saka marasa kyau zamuyi fenti”cikin zumudi kuwa har suna rige rige suka fice suna murna.

Kafin su dawo itama har ta sauya nata kayan,saiga yaran kuwa,nan suka zage suka dinga shafen farar qasar,abinka da ba aikinsu bane tun safe har bayan la’asar,nan ta musu girki suka ci,idan sun huta su dora.

Cikin haka sai ga maman nana ta shigo,salati ta saka tare da kama habarta ganin sumayya saman tsani,duk sunyi face face da farar qasa
“Ni salma,ai nayi zaton qarya nana take da tace fenti zakuyi ashe da gaske take”,dariya ta qyalqyale da ita tana saukowa daga kan tsanin
” to ya zanyi maman naana,ya mukhtar yaqi yarda yayi fenti,shi yasa na siyo da kaina mukeyi ni da ‘ya’ya na”(da yake ita kadai ta gayawa zancan,saboda yadda take mata tamkar mamanta,tafi shaquwa da ita fiye da sauran iyayen yaran.

kai maman naana ta dafe tana cewa
“Lallai sumayya quruciya na damunki,yanzu kishiya kike yiwa fenti da kudinki da jikinki,Allah ya shiryeku” ta fada tana dariya
“To sauko hakanan na kira muku jamilu(babban danta) ya qarasa muku,tunda kun rantse sai kunyi” murmushi tayi tana kakkabe jikinta tare da fadin
“Ai kuwa mun gode” da kanta maman naanan ta leqa ga nemo jamilun,cikin ‘yan qananun mintina ya qarasa musu inda basu qarasa din ba.

“Magana ba zata yiwu yau ba sumayya na dawo gobe,tunda yau kun zama ‘yan qwadago yinin fenti kukayi” ta fada tana miqa mata ledar data shigo da ita,tana dariya ta amsa tana dubawa,ko bata ce mata komai ba ta fahimci meta kawo mata,magunguna ne masu kyau ingantattu na ‘ya’yan itatuwa data saba bata.

Sanda mukhtar ya dawo yaga aikin da sukayi cak ya tsaya,sai kuma yayi gaba ba tare da yace komai ba,qaunarta ke saka ratshi,uwa uba kuma tausayi don yasan har yau da zallar quruciya tattare da ita,inda yasan zata yi da tun sanda yace ba zaiyi ba da tuni ya hada da yimata hannunka mai sanda don kada ma tace zata yi din.

Kamar yadda abba malam ya alqawarta mata,sati biyu da yin maganarsu kuwa saiga motar kaya,irin kayan da sam sumayya bata zata ba,kaya ne ‘yan italy masu kyau da tsada har kujerun wanda ko a aurenta ba’a yi mata irinsu ba,har da qarin labulaye masu kyau da door mat,mamam naana da maman ummi ne tare da uaran gidanta suka tayata jerawa,saiga dakinta ya fito fes tamkar ma ita ce amaryar,mukhtar baiyi qasa a gwiwa ba yace har gida yiwa abba godiya,hakanan shima ba’a barshi a baya ba,kayan kitchen baki daya ya sauya mata,kasancewar yanzun an maida kitchen din bangare biyu,hannun hagu da hannun dama,kowacce anyi mata kantarta da drowers dinta,hakanan ya sauya maya plasma wadda tafi waccar girma harda qarin home thierther,sai ta dinga mamaki da yace bashi da kudi da bazaiyi lefe da fenti ba,bata ce masa komai ba tunda ta fuskanci dama ce bai gani ba,godiya ta dinga zuba masa sosai kamar yadda yake al’adarta.

Mamanta ita ta sauya mata showglass da kayan cikinta baki daya,farinciki duk ya cika sumayyan,ta fuskanci ita ‘yar gata ce sosai,batasan duk sunyi haka bane don kwantar mata da hankali da sake sa mata nutsuwa,ba qaramin kyau dakinta ya sake yi ba sai ka rantse amarya ce.

Sati guda da kammala gyara gidan ranar wata litinin mukhtar ke gaya mata ran laraba masu kafin amarya zasu zo,sai da taji wata faduwar gaba da bata san ta mece ba
“Allah ya kawo su” ta fada kawai kana tayi shiru tana dubansa yana rubuta lissafin kasuwa cikin wani qaramin excercise book.

Jin shirun yayi yawa ya sanyashi dago kansa ya dubeta,sai yaga littafin take kallo,ya sanya tsinin biron ya dan mintsini cinyarta,sai ga dago tana dubansa fuskarta dauke da murmushi tana sosa gurin
“Yadai ‘yammata?” Kai ta girgiza tana murmushi
“Babu komai…..cewa nayi ai za’a yi musu girki ko,tunda naga ana yi”,rai ya bata,don yasan yanzu zata fara soko masa zantukan da baiso,ya tabbatar sumayya danya ce shakaf,domin da wata macen ce aka yi mata zancan kishiya da tuni yanzu gidan ya dade da zama dan qaramin sansanin yaqi,ya tabbatar ba qaramin dauki ba dadi za’a yi ba,duk da quruciyarta ma ya tabbatar da gudun mawar qarin tarbiyya da ta samo daga gida,tunda ko a gidansu bata taso taga mamanta da kishiya ba,da wata ce wannan kadai ya isheta mafaka.

” ba da kayan abinci na ba,kuma kema ban lamunce kiyi ba,idan kunne yaji…..”sai ta ja bakinta ta tsuke,don bata son yayi fushi da ita irin na baya kan zancan fenti da lefe.

Washe gari ranar talata gefin magariba lokacin dawowarsa,ta gama komai kamar yadda yake al’adarta,gidan nata qamshin turaren tsinke,tana tsakiyar yaranta ta siyo madarar ruwa ta musu iloka ta rarraba musu suna sha,wani yaro dake bayan gidansu yayi sallama dauke da akwati wasu yaran na bayansa.

“Wai gashi inji yaya mukhtar” ya fada kamar yadda yaji matar gidan na gaya masa,sai mamaki ya kamata don bata ji alamar  shigowarsa ko qarar babur dinsa ba,tashi tayi ta bude masa labulen falonta suka shiga da su,akwatunane guda shida masu kyau duka iri daya uku set daya uku set daya.

Suna fita ya shigo yana dauke da baqar leda,duka yaran suka masa sannu da zuwa suna qoqarin tafiya gida,ya bibbisu da alawa kamar yadda al’adaraa take sannan suka bi sumayya da
“Anty sai da safe…..anty sai gobe”
“To Allah ya bamu alheri” ta amsa musu suka fice ta rufe gidan sannan tabi bayan mukhtar da tuni ya shige falon.

Murmushi ta sakar masa kamar yadda ya sakar mata
“Kinyi kyau sumayya ta” kanta ta sunkuyar cikin kunya tana murmushi
“Na gode yaya na,sannu da zuwa” ta fada tana cire masa hular kansa da bai samu cirewa ba
“Ya kasuwar” ta sake fadi tana qoqarin ajjiye masa ruwa mai sanyi
“Kasuwa alhamdulillah……kinga ai my sumy abinci zaki kawomin don yunwa nake ji”,ta dan zaro ido tana dubansa
” da wuri haka yau?,na zaci sai ka dawo daga sallar magariba”,shafa cikinsa yayi yana murmushi
“Salla bazata yiwu cikin nutsuwa ba ina fama da yunwa,taimakeni ki bani sumayya magaribar da sauran lokaci,idan na kammala ko masallacin sun idar mayi jam’in da ke”
“To” ta fada tana miqewa zuwa kitchen.

Bayan ta gabatar masa da komai tuwon semo ne miyar kuka sai qamshin daddawa take duk da babu nama amma tayi dadi qwarai,taasa bismillah sannan ta koma gefansa ta zauna.

Sai da ya kai loma biyu sannan yace
“Ga kayanku nan ki duba kiga” ya fada yana mata nuni da akwatunan dake jere gefe,da to ta amsa masa sannan sannan ta sauka qasa ta janyo akwatunan ta soma dubawa.

Tana dubawa yana zuba mata santin tuwo,yayin da itama ke santin kayan,komai yayi kyau,sai data kammala tas,lokacin har ya gama cin twon ya jngina da kujera yana kallonta tana ta daga kayan tana yabawa,ta rurrufesu yadda ta gansu sannan ta dubeshi.
“Nayi zaton ma har an kai kayan ne naga lokaci ya qurato”

“Um um” ya fada a taqaice

“Sunyi kyau sosai ya mukhtar,Allah ya qara budi,saidai komai naga bibbiyu ka saka kala daya,nufina kayan dake cikin akwatin kayan sawa sune a daya akwatin,under wears da mayafai ma”

“Eh,akwatin uku naki ne uku nata”, idanu ta zaro a firgice tana dubansa
” aini yaya ka manta ka yimin lefe na tun sanda zaka aure ni?”
“Na fiki sani,kayan fadar kishiya na miki”.

Tsoro ne sosai ya kamata,tsoron su yaya yahanasu,ina zata sa kanta idan suka ga wadan nan kayan,komai iri daya ita da amaryarsu,hatta da man lebe iri daya ne?,tabdi lallai ya mukhtar so yake ya janyo mata bayan lallabawa takeyi.

” gaskiya ya mukhtar ba’a haka,itafa amarya ce ya zaka hadamu kayi mana abu iri daya?bayan kayan kitchen da kayimin,ka sauya min kayan kallo,kasan su yaya yahanasu sai sunce wani abu idan ma basu ga laifina ba lo sun zargeni ba”

“Eh,saboda kin fiye min ita,ke din zabi na ce,kuma raino na ce,tun kan kisan ciwon kanki kike zaune da ni,tun ana ciyar da mu bana daukar nauyinki,ita din ban santa ba,bansan halinta ba bansan ko zata iya irin zaman da kika yi da ni ba,sannan idan su yaya yaha da kike zance ai basu suka yimin ba,da kudina nayi balle a ce don me?,kufi na ne kuma iyali na ne,saboda haka bana buqatar ki sake cewa komai”.

Tun asali ita ba mai musu bace da ya mukhtar din ba,girmansa take gani,kallon yaya take masa saboda haka cikin sanyin jiki tsoro da sanyin murya tace
” hidimar ce naga kamar taso tayi yawa,na gode Allah ya saka da alheri,Allah ya jiqan magabata ya basu aljanna madawwamiya”cike da jin dadin yadda ta yiwa mahaifansa addu’a yace
“Amin,Allah yayi miki albarka”
“Amin ya mukhtar na gode sosai”.

Tun qarfe takwas washegari ta kammala komai saboda da wuri mukhtar yace zai fita saboda masu jere,qarfe tara ta sallameshi,har ya fita ya dawo ya dubeta
” idan kinga babu dadi zaman gidan,na baki izini kina iya tafiya duk inda kike so,idan yaso idan sai kimin waya ki gayan inda kike,idan na taso daga kasuwa sai na biyo na daukeki”murmushin yaqe kawai tayi,don hakanan tunda ta tashi yau take jin fargaba da bacin rai
“Babu komai ya mukhtar zan iya zaman ma,me zai hana”
“Kada dai ki takura kanki idan ba hali kiyi ficewarki”
“To,a dawo lafiya”,ya amsa mata da ” Allah yasa”ya saka kai ya fice.

Tayi wanka ta shirya tsaf cikin atamfarta da abbanta ya dinka mata ita kwanaki,dark brown ce da adon mint green ajiki,sosai ta mata kyau dinkin ya zauna mata das a jikinta,falo ta koma ta zauna,jikinta a sanyaye bata san dalili ba,gidan ya mata shiru kasancewar ‘yan hirar tata duka ana makarantar boko sai sha biyu da rabi suke tashi.

Ganin akwai wuta ya sanyata jona kayan kallo,tashar arewa 24 ta kama,cikin sa’a suna maimaicin shirin agent ragab,tana son film din sosai,kusan shi ya dauke mata hankali har sha daya da rabi.

Gamawarsu yayi dai dai da bugun qofa da ta soma ji,ta miqe ta fito tana tambayar waye tare da nufat soron,tun kafin ta kai ga budewa taji cikin kakkausar murya
“Malama ki bude bana son salo kin wani kama qofar gida kin rufe,bayan kinsan akwai wadanda zasu zo,dadin abun saura ‘yan kwanaki naga ta iyayi” da sauri ta qarasa bude qofar domin tuni ta dauki muryar wace,yaya bara’atu ce sai fadima tsaye a bayanta,dai sauran da bata san su waye ba,tasan dai ba zasu wuce dangin amaryar ba tunda ita daga amaryar har ‘yan uwanta babu wanda ta sani,iyaka dai tasan cewa amaryar ‘yar aminiyar yaya yahanasun ce.

Saura kadan yaya bara’atun tayi gaba da ita badan tayi gaggawar matsawa gefe ba ta wuceta saura suka biyo bayanta suka bar mazan da zasu shigo da kayan katakon da kujerun.

Bata qosa ba tabi bayansu zuwa dakin da aka bawa fa’izan wanda tuni yasha fentin farar qasar data siya tayi da kudinta,babu komai a dakin a share yake fes kasancewarta gwanar tsafta ce,tun kafin tace wani abun yaya bara’atun ta galla mata harara yayin da sauran suka mata caa da ido
“Uban me kuma kika biyo mu ki mana?” Ta tambayeta tana huci,qasa tayi da kanta saboda yaya bara’atun ta girme mata nesa ba kusa ba cikin ladabi tace
“Zuwa nayi mu gaisa ne”
“Riqe gaisuwarki bama so”
“Uhmm,wallahi kuwa” fatima tayi caraf ta karbi zancan
“Allah ya baku haquri” ta fada sannan ta juya ta fice kai tsaye falonta ta shige taci gaba da kallonta.

Miqewa tayi zata dauko wayarta dake uwar daki tana ringing ta hangosu suna kici kicin budw kwadon dake rufe da dakin ya mukhtar wanda da kansa yasa ya rufe ya tafi da abinsa,da taga a kulle yake sai ta saka tana fadin
“Lallai,kaddai yaya mukhtar daki daya ya bayar,tabdi lallai,yana nufin ita a falle daya zata zauna waccar tana da ciki da falo….haka ne….mu shirya mata kayan idan muka koma ma sanar da yaya yahan”,bata ce uffan ba don ba mas’alarta bace,ko tata din ce ma basu sako da ita ba.

Ya mukhtar ne ya kira yana tambayarta komai lafiya ko tace eh sannan sukayi sallama ya kashe wayar.

Kafin wani lokaci gidan nasu ya cika da ‘yan jeren,ko ina sai shewa ke tashi da qananun magan ganu,take tsoro ya cika sumayya,ta dinga kiran lambar maman naana kan ta shigo ta tayata zama amma wayar a kashe take,ta dinga leqe ta window dinta taga ko akwai hanyar da zata ratsasu ta fice.

Bata samu sararin gurin ba sai da suka fara daura alwalar sallar azuhur,tayi hanzarin shiga uwar dakanta ta dauko hijabinta tare da padlock  ta sanyawa qofar dakin nata ta fice.

A qofar gida ta tarad da su naana suna tsaye,suna ganinta suka nufota da sauri,ta dubesu tana cewa
” me kuma yau kuke tsaye a qofar gida?”bilkisu ce tace
“Hanamu shiga anty akayi?”
“Waye ya hana ku shiga?”
“Masu jeran amarya”inji nana,take taji ranta ya baci,sam bata son abinda zai taba mata yaran,ba zata juri haka ba sam,bata ce misi komai ba sai
” kuzo muje,qila fitina zaku shiga kuyi musu shi yasa suka hanaku shiga don kada ku bata masu kaya”
“Wallahi anty a’ah” inji aysha
“Shshshshah” sumayya tace da su,sun san me take nufi ko batayi magana ba,bata da son su kawo mata hirar wani dama.

Gidan mamam naana ta shiga,ta taras da ita tana kwashe abinci cikin kula
“Ina zaku haka ke da gayyar yaran naki,ina kika baro baqin naki,ai yanzu nake shirin shiga kinga girki ya tsayar da ni ina so na kammala na turasu islamiya sannan na shigo” murmushin yaqe tayi ta ja kujera ‘yar tsuguno ta zauna daga bakin qofar falon maman nanan,yaran nata suka zazzauna kusa da ita
“Eh wlh,na gaji da zama ni daya nace bari na leqo”
“Banda abinki sumayya aiko baki aiko na shigo miki ba kyayi waya a turo miki halima da zainab ko su tayaki zama”
“Wallahi maman naana bansan haka akeyi ba ai” murmushi tayi tana tausayawa sumayya da quruciyarta
“Ai shikenan,Allah ya bada zaman lafiya,ya kade fitina tsakaninku”
“Amin” sumayyan ta fada cikin faduwar gaba.

Duka yaran ta zubawa abinci suka ci sannan ta tura kowa ya gida saboda ganin lokacin tafiya islamiya yayi,ta shirya su naana ma suka tafi sannan suka daura alwala sukayi sallar azahar ita da sumayyan.

Shinkafa da miya har da salad da kifi abinda ta dafa ta zubo musi cikin plate
“Sauko sumayya maza muci” kai ta girgiza don a cunkushe take jin cikinta babu space din abinci
“Na qoshi maman nana” tausayinta ya kamata amma ta dake tayi murmushi
“Sauko muci akwai abinda nakeson gaya miki” bata da jan doguwar magana saboda haka ta sauko ta sanya hannu suka soma ci.

Cikin hikima maman nanan ke kwatantawa sumayya dabarun zama da kishiya,qissa dabara da wayo kala kala,ta dora da yi mata nuni da haquri,kau da kai kara da alkunya,gaskiya da amana,zama na tsakani da Allah,sai gashi sun tashi da abincin tas,har sai da hannayensu ya fara bushewa da miya saboda sun kasa tashi a gun darussan maman naana sunqi su qare,saiga sumayya na kwasar dariya saboda wani abun idan maman nanan na gaya mata kunya ce ke kamata ko mamaki.

Hararta maman nana tayi dariya itama nason qwace mata itama amma ta dake saboda yadda taga sumayya na dariya wani abu da ta gaya mata
“Au dariya ma nake baki ko?,zaki ci gidanku wallahi idan baki dauke duk abinda nake gaya miki ba” cikin dariyar ta dafe baki
“Yi haquri maman nana,abunne wallahi” ta kuna saka dariya,kada kai maman nana tayi itama dariyar ta qwace mata,ba shakka sumayya danyace har yau,ta miqe ta dauke plate din da suka gama cin abincin ta fice da shi.

Basu ankara ba sukaji ana qwala kiran sallar la’asar,nan suka tashi sukayi,maman nana ta dubeta tace
“Ba zaki koma gida kiyi girki wa mukhtar bane”
“Ina som in koma maman nana amma ina zaton har yau basu tafi ba,bari na kira ya mukhtar din naji mai zai ce”.

Koda ta kirashi cewa yayi tayi zamanta kawai idan ya dawo din ya kirata ta dawo,a nan tayi zamanta suka ci gaba da hirarsu har su nana suka dawo daga islamiya,sai qarfe shida kiran mukhtar ya shigo wayarta,ta yiwa maman nana sallama ta wuce gida.

Kaca-kaca ta tarad da gidan tun daga qofar gidan tamkar bata taba shara ba,kwalaye da ledojin abubuwan da suka jera duja ko ina a gidan,ga kwanukan abinci nan nata har da sabbi da bata taba amfani da su ba,da alama ma girki sukayi saboda kitchen din na bude zasu jerawa amarya nata kayan a ciki,mukhtar na tsaye a tsakar gidan riqe da qugu cikin bacin rai,da alama ransa ya baci da irin abinda sukayi,ga abincin da suka dafa din ma basu iya cinyewa ba sun kuma lalata bare a bawa wani,zai soma sababi ta shige jikinsa ta soma lallabashi,sai da ta sauke masa temper dinsa sannan ya tayata suka fara kintsa gidan fes.

Kafin su kammala anyi kiran sallar magariba,ruwan wanka ta dora musu sannan sukayi alwala sukayi sallah,bayan sun idar ta juye musu ruwan sukayi wankan tare,ta shirya tsaf tayi kwalliya cikin qananun kaya,zata dora musu girki yace ta barshi kawai ya zura jallabiyyarsa ya fita.

Cikin minti a shirin ya dawo da ledoji a hannunsa,ya ajjiye kan kujerar yana cewa
“Dauko faranti ki juye mana wannan,ki hado da cups,hala ma yau duka bakici abinci ba” murmushi tayi sanda take fita daga falon tana cewa
“Naci mana ya mukhtar a gidan maman naana” ,ta dawo dauke da plates din ta juye abinda ke cikin ledar.

Tsire ne da zafinsa sai zuba qamshi yake,sai rabin gasashshiyar kaza,ta bude dayar ledar,lemon roba ne na fanta sai maltina wanda tasan ta mukhtar din ce tunda ita bata dameta ba.

A nutse suke ci suna hirarsu jifa jifa kamar babu wani abu dake damunsu.

Suna tsaka da ci wayar sa ta dauki qara,sumayya ta miqe ta isa inda take chargy ta ciro masa kana tazo ta miqa masa,baquwar lambace,yayi kamar bazai daga ba amma yadda kiran keta nacin shigowa ya sanyashi dagawa ya kara a kunnensa.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE