KUNDIN KADDARATA CHAPTER 23 BY HUGUMA

Bata gayyaci kowa ba baya ga mutanen da suka mata rakiya suka ga gida suka kama gabansu,hakan ga sanya randa za’a kawo amarya ita daya ce qwal,cikin dakinta tayi zamanta saboda falon nasu cike yake da ‘yan kawo amarya,wadanda tun daga motsinsu ta karanci yanayinsu,su din ma dukkan alamau sun nuna babu arziqi,saboda haka tayi musu aji guda ta sanya su.

       Bata fito ba sai da taji motsin ‘yan uwan mukhtar wadanda da su aka dauko amarya,fuska sake ta fito falon tana musu maraba,saidai kowanne wanu irin kallo yake binta da shu,ganin babu dole ya sanya ta juya ta koma dakinta tun kafin su yarfata cikin jama’a,yanzun kam ba da bace da quruciya ke dibarta balle ta nace sai an kula ta ko ta faranta ran wanda bai damu da nata farincikin ba.

            Ganin tara na dare yayi hayaniyar ta sarara da alama sun watse sun bar masu gidan da gidansu,sai ta miqe ta sanya turaran wuta cikin dakinta zuwa corridor dinta a burner din da anty dije ta siya mata guda biyu kyauta,take qamshin ya karade ko ina har zuwa falon nasu,wanka ta shiga ta tsala ado cikin wani marron material wanda aka yiwa ado da golden din zare,sosai ya fidda salsalar farar fatarta wanda jan lallen da tayi ya sake bada gudun mawa,baga wani cika kwalliya ba ta dai yiwa kanta barin turare kama daga humra,body spray body mist zuwa perfume na kaya.ta yane kanta da mayafi golden ba tare data buqaci daura dankwali ba ta kame gefab gadonta tare da janyo wayarta ta soma ‘yan danne danne don ta dauke mata abinda take ji cikin zuciyarta.

          Qarfe goma taji sallamar mukhtar din cikin falonsu,burus tayi tamkar bata jishi ba,wani kishi da matsananciyat faduwar gaba suka ziyarceta,sai ta dakata da abinda takeyi din tayi shiru tana sauraron motsinsa da kuma bugun zuciyarta.

         A hankali ya yaye labulen yayi sallama,ta amsa ba tare da ta dubeshi ba,idanu ya zuba mata,ta masa kyau sosai tamkar yau take amaryarsa,wanu qaunarta ke taso masa ta wani lungu can dake saqon zuciyarsa wanda wani abu da baisan ko meye ba ke qoqarin fatali da abinda yake ji din,ya rasa me yaje ji cikin zuciyarsa a yau din,koda zaka ritsashi da bindiga ha zaya iya gaya maka ainihin me yake ji ba,farinciki koko baqinciki,ya jima cikin wannan yanayin wanda baisan sanda ya shige shi ba,da yayi yunqurin wani tunani kuma sai ya shagala,tunanin ya qwace masa.

        Ganin bata da niyyar cewa komai ya sanyashi qarasowa gefanta ya zauna yana zube ledojin hannunshi a qasa
“My sumy…..yau kan arziqin sannu da zuwan ma ban samu ba” ya fada cikin marairaicewa,a hankali ta dago kai ta kafeshi da idanunta wanda suka sanya yaji wata fargaba da kamashi,yayi kyau cikin shadda butter colour dinkin babbar riga,yasha askin saisaye da gyarab fuska wanda ya sakw fidda shape sin kyakkyawar fuskarsa.

       Tamkar an dorawa zuciyarta dutse haka taji saboda tsabar kishi,yau nukhtar dinta zai sake zama na wata a karo na biyu,me yasa yaya yahanasu taqi barinsu su huta,me yasa ba zata gane irin yadda take son mukhtar dinta ba,laifi ne dan baka haihu ba?,shine lawai dalilin da yasa suke ta rabata da farincikinta  a lokuta mabanbanta,ina ma ace ana siyar da haihuwa yau da ta sayeta koda zata rasa zanin daurawa,koda zata rasa lomar abincin da zata sanyawa bakinta,don dai kawai su barta da mukhtar suyi rayuwar farinciki.

          So take ta bude baki da gaya masa magana ko zata ji sauqin tuquqin da zuciyarta ke maga amma sai ta kasa,girman mukhtar cikin idonta yafi gaban haka,miqewa tayi gudu gudu sauri sauri idonta na saukar da qwalla kan kuncinta,miqewa yayi biyita da sauri cike da muradin cimmata,saidai tuni ta afka toilet dinta ta rufe qofa tare da sakin kuka.

         Bakin toilet din ya tsaya yana naci da magiyar ta fito,sai da suka kusa kwashe minti ashirin a haka,ba zata iya kallonsa ya tafi dakin wata ba hakan ya sanyata cikin muryar kuka tace
“Bana son ganinka yaya mukhtar ka tafi don Allah ka qyaleni”
“Yau nine sumayya baki son gani?…..yau…….” Bai kamamala maganar ba wayarsa dake aljihun gaban rigarsa ya hau ruri,hannunshi ya zira,ganin mai kiran ya sanyashi dagawa
“Dear m,ina ka tsaya ne wai bayan na ji shigowarka”,bazai iya tantance mai yaji ba,so yake ya rufeta da masifa amma sai ya kasa,maimakon haka sai ya bige da cewa
” ina gun yayarki zance ko qanwarki ina lallashi”gabanta ha fadi haushi ta turniqeta,kada fa ace duk abinda ake bata labari kan sumayyar gaskiya ne,amma babu komai saura qiris tayi maganin abun
“Lallashin me kuma dear bayan ba wannan ne karo na farko ba da aka fara mata kishiya,ka taho ko nazo da kaina na tafi da kai”
“Ok gani nan” ya fadi da sauri tare da katse kiran,maida idanunsa yayi ga qofar toilet din,ya tabbatar taji duk abinda suka ce,kamar sumayyan ce ke gabansa ya marairaice
“Shikenan sumayya zan tafi,ga ledarki can cikin daki Allah ya bamu alkhairi” ya fada yana juyawa.

        Zamewa tayi tayi zaman dirshan saman tiles din bandakin sabon kuka na kubce mata wanda ta sanya tafin hannunta ta toshe bakinta don kada su jiyota,duk da cewa ita tace ya tafin bata yi tsammanin tafiyar tasa da gaggawa ba haka.

        Ta jima tana kuka a ciki kafin ta lallashi kanta bayan tayi tilawar wasiyyoyin mahaifiyarta tun daga auren da aka qara mata na fari zuwa wannan da ya kasance na biyu.

        Bata bar bayin ba sai da cikakkiyar alwala,ta koma daki ta sauya kayan bacci,doguwar riga ce har qasa mai taushi da kauri,hijabi ta dora saman riga ta shimfida abun sallaha ta tayar da sallah hawaye na layi kan kumatunta.

         Yana shiga ta miqe ta taroshi cikin karairaya da yauqi,ta amshi ledar hannunsa ta ajjye kana ta rungumeshi,yaqe haqora kawai yake,ko daya bata burgeshi ba,alamu sun nuna babu kunya ko qwaya daya cikin idanunta,ko daya baiji dadin kasancewarta cikin jikinsa ba amma sai ya kasa cewa da ita komai,sai ya dinga dauko daren farkon sumayya da na fa’iza da nata yana hadawa,tuni lissafin ya wargaje don tako ina sun sha banban.

           Biye yake da ita kawai sai ido da yake binta da shi,ita ta hada musu ruwa sukayi wanka sannan ta samo plate ta juye kazar a ciki,kusan ita ta dinga ciyar da shi ta kuma ci da kanta har suka kammala ta janyeshi gado don tuni ta dokanta,kusan ita ta gabatar da komai a maimakonshi,mamaki da haushi ke tuqeshi,gefe guda wani irin takaici wanda idan ya yunqura zaiyi magana sai yaji ya kasa cewa komai,data dubeshi kuma sai yaji komai ya wuce ya bar tasiri cikin ransa.

         Kwana tayi zaune bayan ta gaji da yin sallolin,abinda bata taba zata zata iya ba,yaushe mukhtar ya sake zame mata wani na daban haka,ita kanta tana mamakin yadda ta koyi kishinsa har haka,sai da ta gabatar da sallar asuba taji idanunta sun soma nauyi da zugi,duk yadda taso ta yakice baccin amma bata samu nasara ba,haka yazo ya saceta cikin gaggawa ya kuma mata nauyi wanda hakan ya sanya ta gaza sanin meke wakana cikin gidan har misalin qarfe goma da rabi ma safe wanda ta farka a firgice.

         Bandakin cikin dakinta ta shiga da yake bayan na corridor akwaai cikin daki,wanka tayi bayan ta wanke bakinta ta dawo cikin dakin,jikinta babu qwari ta shirya cikin atamfa doguwar riga wadda ta mata kyau,duk da bata jin qwarin jikinta amma tayi lite make up wadda ta dace da yanayinta,babu dauda ko qura a rea dinta sai dan kakkabe kakkabe kawai da tayi sannan ta fito don samawa kanta abinda zata ci koda ruwan zafi ne,don jinta take iska na yawo da ita tsabar babu komai a cikinta,ledar jiya mukhtar din ya bata ta dauka ta fice da ita.

         Bata kula da su ba sai data shigo cikin falon sosai,mukhyat sanye da yadi mai taushi fari tas wanda ka yiwa aiki da zare ash,sai wandda idanunta suka sake sauka kanta wanda bata tantama itace zainab din.

        Macace wadda kallo daya ta yi mata ta fuskanci ta girmesu ita da fa’iza baki daya,A qalla tayi shekaru ashirin ta takwas wanda hakan ke nuna ta girmi sumayyan da shekara goma tunda sai yanzu taje cikin shekararta ta goma sha tara,baqa ce zainab din amma ba baqi can ba,tana da cika wadda za’a iya kiranta qiba kai tsaye duk da wata mai yawa bace,bata daga cikin sahun kyawawa ko kadan amma zaiyi wuya kai tsaye ka kirata da mummuna saboda yanayin iya gogayya da iya salo,saidai tako ina sumayyan ta mata fintikau,abu daya zata iya nuna mata qwala qwalan idanu da suke zagayayyu suka fi na sumayya girma,sakamakon natan lumsassu ne ba kowanne lokaci kake iya gane girmansu ba,sanye take da material mai santsi wanda aka yiwa dinkin riga da skert,breakfast sukeyi wanda ya qunshi tea da soyayyen qwai da bread,sai kaji wanda ba tantama na jiya ne aka sake gasa su.

         Shi ya soma ganinta lokacin da zainab ke qoqarin bashi naman a baki,sai ya goce wanda hakan ya janyo hankalin zainab din ta ankara da fitowar sumayyan,murmushi ya sakar mata yayin da itama tayi qoqarin maida masa martani
“Kin tashi kenan,na leqaki na taras kina bacci”
“Eh,ban jima ai da tashi ba” ta fada tana takowa gabansu
“Kinyi kyau sumy ta” ya fada yana sake dubanta wanda kalmar ba qaramin dukan qirjin zainab tayi ba,lokaci daya ranta yayi baqi,sumayyan ta yaga mata tako ina,kyau da quruciya,akwai alamun nutsuwa tattare da ita sosai,hakan ta kwana da sanin lamba daya ce ita cikin zuciyar mukhtar din,don ko darensu na jiya ya bata amsa,duk yadda taso rikitashi ban manta sumayyan ba ita yake kira.

      “Na gode ango mijin amarya,da fatan kun tashi lafiya” ta fada wajen kaiwa matuqa gurin boye kishi da damuwarta,sai ta dubi zainab
“Amarya ina kwana ya kwanan baqunta”
“Lafiya ya kike”ta fada tana yatsina tare da qoqarin baiwa mukhtar tea
“Qalau” itama sumayyan ta fada cikin yanayin data amsa mata tare da motsa kafada kana ta nufi kitchen don kaucewa ci gaba da kallon abinda ke faruwa.

        Alamu sun nuna iyaka na cikinsu ne abincin,batasan waye yayi ba,amaryar ko mijin amaryar,koma waye dama bata da buqata,sai ta dora tea kan gas da a yanzu shi mukhtar ya siya mata take amfani da shi,ta bude kazar ta sake mata sabon hadi na spices,ta duba dan madaidaicin ovean dinta ta soma kici kicin hadawa tare da duba hanyoyin da ake hadawar.

       Cikin haka mukhtar din ya shigi kitchen din dauke da kwanukan da suka ci abincin zainab din na biye da shi,bata bi takan sumayyan ba ta nufi side dinta ta dire kayan,mukhtar ya dubu sumayyan
“Me za’a girka mana ne naga ana hada ovean”
“Ai baka da buqatar abinci na malam” ta fada cikin gatse,murmushi yayi yana kallonta,lallai sumayyan ta fara zama babbar mace,tunda har tafara banbance tsakanin aya da tsakuwa.

          Kafin ya furta komai muryar zainab ta ratsa kunnuwansu tana qwala masa kira cikin wani irin salo,tamkar an soketa a qirji amma saita basar,ya juya yana cewa da ita
“Ina zuwa”
“Banda buqatar dawowarka ma” ta fada kishi na cinta tana qoqarin danneshi.

        Har ta kammala babu shi babu alamarsa,ta juye ta koma daki da abincinta zuciyarta na raunana,saboda wannan ne karo na farko data taba ganin sauyi daga gareshi har irin haka.

        ****      *****    ****

     Cikin kwanakin wani amarci ta dinga gani cikin gidan wanda bata tsammata ba,baki daya kamar daukar mukhtar din akayi aka sauya mata shi,hutu ya dauka na fita kasuwa har na kwanaki bakwai,ko yaushe suna daki idan kaga fitowarsa salla ce zaya yi,saita wuni sur bata sanyashi cikin idanunta ba,abun na taba ranta saidai bata yarda ta fiya zurfafa lamarin cikin ranta,runda anty dije ta gaya mata dole zata iya ganin wasu sauye sauye duk son da yake mata,amarya kota buzuz ce sai an mata rawar qafa,to bare baya ga wannan babu wani sauyi da ta gani cikin ma’amalarsu shi da ita.

KUNDIN QADDARA TA

          Kwanaki uku take zaton zaya yiwa zainab din tunda bazawara ce,sai gashi ya shiga cikin kwana na hudu biyar shida har zuwa bakwai.

        Ranar kwana na bakwai din a ranar zaya soma fita kasuwa,tana kwance dakinta bayan sha daya na safe taji sallamarsa,sai ta miqe ta zauna tana amsa masa,fuskarta babu yabo babu fallasa,gefanta ya samu ya zauna yana fadin
“Ranki ya dade kinyi wuyar gani” ido ta daga ta dubeshi,lallai ne wai ita za’a yiwa halin maza,magana yake gaya mata a fakaice koko yaya,duk da hakan sai ta dake ta kuma basar ta kaufa zancan ta hanyar fadin
“Ina kwana”
“Lafiya sumy ta,kinga na qarawa zainab kwana ko,kinga baquwace tace kuma tan tsorom zama ita daya” wani haushi ya taso ya turniqeta,budurwa ce zainab din ko yau ta fara zaman gidan aure,ko ko tsabagen rainin wayo ne,wadan nan kalaman takeson gayawa mukhtar din amma girmansa da take gani yasa ta gaza furtasu ta hadiye kayanta sai ta bige da cewa
“Ko,Allah sarki” daga yanayin da tayi maganar kawai ya tabbatar masa cewa ta inda zancansa ya shiga ta nan ya fice.

         Kafin su sake cewa wani abu zainab din ta daga labulen dakin ta danno tana fadin
“Dear fito mana na rakaka,ina ta jira fa”
“Ai gani nan” ya fada yana fiddo kudin cefane daga aljihunsa,wani banzan kallo da sumayyan batasan ta iyashi ba sai yau ta jefawa zainab sannan ta miqe zata fice ta bar musu dakin,mukhtar yace
“Ina kuma zaki sumayya bamu gama magana ba”
“Baka shirya yin maganar da ni bane” ta fada tana shigewa toilet abinta ta soma daura alwalar sallar walhar da dama ita take shirib tashi tayi.

        Tana jiyosu daga nan zainab din na gaya masa ya qyaleta yazo su tafi,yace a’a taje falo ta jirashi zaya fito yanzu,a bandakin ya cimmata ta gama alwalar tana gyara daurin kallabinta,fuska a hade cikin kakkaurar murya yace mata
“Wai wane irin hali kika koya sumayya wanda ban sanki da shi ba,wannan wannw irin wulaqanci ne ina miki magana kina tafiya gaban zainab salon ki koya mata yadda zata raina ni”, tsayawa tayi tana kallon ikon Allah,lallai a daki mutum a kuma hanashi kuka.

        ” ai tare muka siyi foam din makarantar koyon sabbin halaye ni da kai muka cike,muka kuma fara daukar darasi a ciki”sarai yaso ya fahimceta amma sai ya waske
“Wai duka sumayya don na qarawa zainab kwanaki kike wannan abun,yanzun ban isa da gidana ba kenan?”
“Isa kai,tunda gashi ka nuna salon taka isar” ta fada tana kashe famfo tare da qoqarin rabeshi ta wuce,sai ya janyota jikinsa ya matse gam,yasan kan abarsa take ya fara sauke mata fushinta,yayi nasara kam don itama bata bijire masa ba,don babu qarya tayi kewar mijinta sosai.

        Ita ta fara zame jikinta sannan tace
“Ka gayawa matarka kada ta sake shigo kin daki kanta tsaye,sabida hakan ya sabawa dokar addinin musulunci idan ita din bata sani ba” sai ya lumshe ido ya dafe kai
“Oh sumayya harda mita ma sai da kika koya,to ayi haquri” daga nan sukayi sallama ya ajjiye mata kudin cefane duk da suna da komai.

        Sosai zainab din ta qulu,ta fara lura sumayyan ta shalle zatonta,amma daga yau zata fara dasa bamabamanta cikin gidan,shanye komai tayi ta masa rakiya kamar ta hadeshu,duk yadda ya nuna jin dadinsa a fili amma zuciyarsa ta gaza karbar hakan,a boye ma Allah Allah yake ta koma ya samu ya fice daga gidan.

        Da azahar ta shiga kitchen ta musu girkin rana,tana fitowa ta samu zainab din a falon zaune tana kallo,qafarta daya kan daya tana amsa waya,har sumayyan ta gifata ta taji ance
“Ke!” Da fari tayi zatan cikin wayarta ne sai taji ta sake cewa
“Ke dake nake magana sumayyata” waiwayowa tayi tana tsaye daga inda take
“Wai da ni kike?”
“Akwai wata mai sunan ne bayanke a gidan nan,koma ki dauko min abinci na”.

         Baki ta sake tana kallonta cikin mamaki,ita kuma nata salon kenan,sai ta kada kai kawai tace
” idan kin damu ki shiga da kanki ki dauko”
“Ni kike gayawa wannan maganar,lallai yau zaki gane niba irin sauran kishiyoyinki bane,wallahi yau sai kin gane matsayina gun mukhtar” bata tsaya bi ta kanta ba tayi komawarta daki don tana da abunyi.

        Lambar mukhtar ta soma laluba tana huci,yana tsaka da sallamar custumer yaga kiran nata,sai da yaji wani dumm cikin kansa da yaga sunar,ko kadan baiyi farinciki ba amma sai ya gaza share kiran
“Amarya bakya laifi,ya gidan”
“Gida ba lafiya ba,mukhtar na fuskanci ka auroni ne don matarka ta rainani”
“Ya salam,me ya faru me tayi miki?”
“Bazan hanaka sana’a ba kabari idan ka dawo kaji koma mene ne,amma wallahi idan baka dauki mataki ba bazan ci gaba da zama cikin gidan nan ba” sai yaji wata faduwar gaba da sauri yace
“Haba zainab ki daina fadar wannan maganar mana,mai rabu mu ai sai Allah,bari na kira ita sumayyan naji” da sauri ta katseshi don bata son ya mata fadan tun yanzu lamarin ya wuce ba tare data iza wutar tafi haka ba
“A’ah nidai ban saka ba,nace ka bari kawai ka dawo”
“To shikenan sai na dawo din” ya fadi yana sauke wayar,sam jikinsa bai bashi sumayyan zata aikata wani abu na rashin mutunci ga zaina din ba,amma sai ya samu kansa da yarda da duka magan ganun zainab din.

           Tun shuda saura ta gama fesa kwalliya tare da bade jikinta da turarenta data tanada na musamman wanda ke hargitsa tunani da lissafin mukhtar ya dinga maida su ba dai dai ba.

Cikin izza da isa ta fito daga dakin nata hannunta dauke da jug na kwalba wanda ta cikashi da lemin zobo da cups dinsa,tana tafe tana murmushin tarkon data d’ana ta ratso ta falo don fita harabar gidan,so take mukhtar din ya fara karo da ita kafin kowa saboda abinda ta tsara ya tafi dai dai ba tare da mishkila ba,idanunta ne suka sauka kan sumayya tada tsume cikin tata kwalliyar,wani irin material ne mai santsi kamar yanayin shufom saidai ya fishi kauri da aka matsawa dinkin wata shegiyar gown wadda ta fidda duk wata qira tata,kalar pink(ruwan hoda) ne mai turuwa,tayi amfani da dankunne da siririyar sarqa fashion baqaqe,hakanan abun hannunta zuwa zobe,take farincikin dake ranta ya ja baya ta raina tata kwalliyar data hasko farar fata ta hadu da pink da baqi,kishi ya sake taso mata,ya zama lallai kota halin qaqa tayi rugu rugu da gwamnatin sumayyan cikin zuciyar mukhtar ya zama tata ke wannan tashen,ta yadda zata yaga yarinyar yadda taga dama,yarinyar na neman fin qarfin zatonta,don ba’a rufe awa ba taga yadda ta tashi hankalin gidan da qamshin girkin abincin dare,ranta na suya ta fuce fuuu wanda sumayya bata ma lura da ita ba sai ficewarta ta gani kamar guguwa.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE