KUNDIN KADDARATA CHAPTER 24 BY HUGUMA

Guguwar dawowarta sumayya da taji ya sanyata daga kai ta bita da ido har ta shige dakinta.

          Cikin mintinan da basu wuce biyu sumayyan ta fara jiyo qauri wanda yake da alama da wani abu aka sanya cikin garwashin wuta,data lura sosai sai ta fuskanci daga bangaren zainab ke fitowa,mai da kanta tayi taci gaba da kallonta,cikin sakanni qaurin ya buwayeta,hakan ya sanya ta koma dakinta ta dauko burner da turaren wuta ta fito falon wanda hakan yayi dai dai da sake ficewar fa’izan zuwa harabar gidan,jikin socket din dake daura da kayan kallon ta jona ta cikata da turaren wuta,mintina qalilan ya danne qaurin ya koma qamshi.

          Tana zaune taji bude get din gidan da qarar motar mukhtar din,wanda hakan ke alamta dawowarsa,sai ta miqe ta koma daki ta sake feshe jikinta da turare sanna ta nufo harabar gidan.

           Turus tayi ganin zainab gefan mukhtar tamkar zata shige jikinsa tana dubansa,hannunsa riqe da cup wanda ta cika masa da zobo wanda tuni ya fara kwankwada,yi tayi kamar ta juya saboda takaici sai kuna taga sam hakan baiyi tsari ba,zai kuma faranta ran zainab har taci karenta babu babbaka tunda ta riga da taga tsaiwarta.

         Fuskarta ta fadada da fara’a,sannu a hankai ta soma takowa gun wanda takalmin qafarta duj da plate ne ya dinga bada sauti,hakan shi ya janye hankalin mukhtar ya zuba mata ido,ta masa kyau sosai,ji yake kamar ya tafi ya sureta ya daga sama yadfa suka saba,yau ta sauya masa sosai sumayyan,da wannan tunanin ta qaraso inda suke ta tsaya gabansa tana jifansa da murmushi,so yake take sumayyata kinyi kyau,so yake ya yaba mata,amma wani dunqulallen abun ya danne zuciyarsa,ya sake duban qwayar idanunta sai yaji wani bacin rai ya kamashi,murmushin da yakeson maida mata sai ya musanyashi da hade fusjarsa tsaf wanda hakan ya baiwa sumayyan mamaki,saidai duk da haka bata karaya ba ta miqa hannu ta amshi jakarsa tana masa sannu da zuwa.

          Bai amsa ba don ji yayi ya gaza amsawar
“Wash” zainab ta fada wanda shi ya sanya su duja suka dubeta,baikai ga tambaya ba ta dora da nata jawabin
“Ka gani ko mukhtar,kaga abinda nake gaya maka ko?,yanzu fisabilillahi duk fadin gurin nan bai isheta ba sai ta takani saboda tsabar raini?” Mamaki fal zuciyar sumayya take dubanta,ya Allahu,nata salon kenan?matar da tazarar dake tsakaninsu ya isa tiqa tiqan mata biyu su tsaya shibe zata ce har ta taka ta?,tamkar dama neman abun fadan yake ya sake tunzura yana ji ana azqlzalar zuciyarsa,juyawa yayi yana jifan sumayyan da wani irin kallo
“Halayyar banzan da kike son koya kenan ko sumayya?,halayyar da ban sanki da ita ba?,to bari kiji ni bazan lamunta ba,bana son tashin hankali kin sani,har sau yaushe zan huta daga dawowata ko iskar gidan ban gama shaqa ba daga shigowarki zaki tada mana fitina?,to ki shiga hankalinki da ni idan ba haka ba zanyi mugun saba miki”, bata data cewa,to me zata fada ma tunda ya riga ya yarda ya hau kai kuma ya zauna?,bata baki ne kawai tsayawa kare kai,saboda haka aladabce tace
” bansan na taka ta ba in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba kayi haquri ya mukhtar”sai da yaja fasali sannan yace
“Shikenan ta wuce”
“Au ni ba zaka ce ma ta ban haquri ba shikenan na gane matsayina wallahi” ta fada a zafafe tana fashewa da kukan kirsa sannan ta kwasa tayi cikin gidan da sauri,don sosai ta shaqa ba haka taso ya kasance ba,so tayi cikin biyu ayi daya,imma yace sumayyan ta durqusa ta bata haquri,ko kuma tayi qoqarin kare kanta ko ta masa turjiya ya jibgi banza a gabanta taci dariya ta more.

         Da idanu sumayyan tabi mukhtar din ganin yadda ya diba shima ya bita cikin wani tashin hankali da yaji ya rikito masa sanda ya fara jiyo sautin kukanta,wanda babu qwalla ko daya sai tsabar ihu da iya manaqisa,kai sumayya ta kada zuciyarta ta karye,lallai babu shakka wani sabon SHAFIN QADDARAR TA NE YA SAKE BUDEWA CIKIN KUNDIN QADDARARTA,sau ta lallashi kanta kawai ta shige ciki da jakar tasa ta ratsa ta cikin falon nasu ta wuce sashen sa.

          A qalla ta dauki kusan minti talatin zaune kafin ya shigo bangaren nasa,fuskarsa kadai zaka duba ta bayyana maka yanayin da yake ciki,kallonta yayi tana zaune gu guda,tausayinta nason masa tasiri amma wani abu mai qarfi na maye gurbin tausayin da jin haushi
“Na kai maka ruwan wankanka” tace da shi,bai amsa mata ba illa rage kayan jikinsa da yayi ya shiga wankan kawai.

         Tana zaunw taga yana shiryawa cikin yadin kaftan ruwan zuma,ya kammala ya zira hularsa tare sa daura agogom hannunsa,muqullin motarsa da taga ya dauka shi ya tabbatar mata da cewa lallai fita zaya yi,da hanzarinta tace.
“Ya mukhtar baka ci abincinka ba fa,kuma naga kana shirin fita”
“Sai na dawo” ya fada yana ficewa ba tare da ko ya waiwayeta ba,sai ta zube agun ta sanya kuka,da sauri ta sanya tafin hannunta ta qunshe kukan saboda fadan da zuciyarta tayi mata na ba kuka zata yi ba,take ta kama ambaton ‘Allahumma la sahla illa ma ja’altahu sahla,wa anta taj’alal hazna iza shi’ita sahla’.

         Tana daga nan amma tana iya jiyo muryar zainab wanda hakan ya tabbatar mata fita zasuyi kenan.

          Kusan awa guda da rabi ta share zaune tana ambaton sunayen Allah,ya zuwa lokacin quncin dake cin ranta ya ragu qwarai,wayarta ta soma ruri,ganin sunan mukhtar ya bata mamaki amma sai ta daga gabanta na faduwa jikinta na gaya mata ko dai ba lafiya ba,a daqile ya amsa sallamarta sannan ha dora
“Ya zuwa yanzu nasan abinda kika girka tun yamma yayi sanyi,ina so ki tashi ki hada min fried rice nan da awa guda ina bisa hanya” bata da hurumin da zata musanta masa tunda iko yake da ita,biyayya a gareshi kuma tilas ne matuqar bai sabawa mahaliccinta ba,tuni ya katse wayar don haka itama ta ajjiye ta nufi kitchen  kai tsaye.

         Komai suna da shi alhamdulillah tunda yanzun kam arziqi ya zaunawa mukhtar din gwargwado,da hanzarinta ta shiga hada komai,cikin abinda yai qasa da awa daya da rabi ta gama tunda ba wata mai yawa bace can,bugu da qari kuna ta horu wajen aiki.

         Dakinta ta wuce ta debo kayan baccinta ta koma sashen mukhtar din,cikin toilet dinsa tayi wanka ta shirya tsaf,wannan duka cikin karatun anty dije ne,falonsa ta koma ta kwanta saman doguwar kujerarsa,a hankali tunani yayi awin gaba da ita tanayi taba sauke ajiyar zuciya.

         Tarayyarsu da mukhtar tun farkon aurensu kawi yanzu,bata taba sanin so ba sai a kansa,da shi ta saba da shi ra qarasa mallakar hankalin kanta,dashi ta qarsa cikasa kammaluwar hankali da rayuwarta,ta yaya zata iya jure wani baqin lamari daga gunsa ta farad daya?,ya zata iya lamuntar juya baya daga gunsa,idan ma har laifi ta masa a yau kam zata kawo qarshen horon da yake mata.

         Tana tsaka da tunanin ta jiyo muryarsu suna shirin turo qofa,hakan ya sanya tayi hanzari foge qwallarta,tare suka ahigo manne da juna,sai ta kauda kanta daga saitinsu din ragewa kanta kaifin kibiyar mashin da ta soketa,ba haka zainab taso ba,wacce iriyar mayyace yarinyar mara zuciya,ita miji bai bata mata rai tayi fushi da shi ne,sai ta zame jikinta daga na mukhtar tana masa sallana hannunta dauke da leda mai dauke da tambarin SS store.

        Wuceta yayi kamar bai ganta ya ya shiga daki fuskarnan kamar ta mayunwacin zaki,tamkar ba shine ya shigo yanzun yana dariya ba,jikinta sai ya mutu murus ta kasa tashi har aka kusan cin minti talatin sannan ta yunqura ta tashi.

        Gefan gado ta sameshi yana waya wanda da alama da zainab din yakeyi,ya ilahi ba yanzu suka rabu ba kuma?,sumayya ta fada a zuciyarta,kafin ta qaraso ciki ya kashe wayar yana qoqarin kwanciya
“Yaya kace na maka fried rice kuma naga kana shirin kwanciya baka ci ba” a banzace yace
“Bani zanci ba,don ni naci abinci gidansu zainab na cika cikina,ita zaki kaimawa ita ke sha’awar ci” shiru tayi ta tsaya cak kamar an kafata,me kenan?,wannan zallar wulaqanci ne,dama saboda cikin zainab din ya tasheta tara saura na dare ta hau sanon girki?
“Ko ba zaki bane ni na taso da kaina na kai mata?” Ya fada yana daga kwancen,tabbas da ta iya rashin kunya yau da zata yiwa mukhtar ko yaya take,saidai kowanne tsuntsu ance kukan gidansu yakeyi, tunda ta taso gidansu dai dai da rana daya bata taba katarin ganin innarta ta yiwa malam musu ba duk girma da wuyar umarnin da ya bata,sai ta kada kai da dauki flask din ta nufi sashen zainab din.

        Har ta rufe qofar falonta amma ta qwanqwasa mata saboda cika umarnin mukhtar din,minti biyu tsakani aka bude,tana sanye da kayan bacci,kallonta tayi daga sama zuwa qasa sannan ta yatsina
“Ya akayi”
“Abincinki” ta bata amsa a qaice
“Mtsweeew,bazan iya ci ba gaskiya” bata jira sauran abinda zai biyo bakinta ba ta juya,taku na shida cikin na bakwai taji tace
“Kawo dai na taimaka miki na dandana kada kiyi wahalar banza” idan kujerun dake gun sun amaa to itama ta tanka,banza ta baiwa ajiyarta taci gaba da takunta,sai ta tsinto muryarta
“A sannu dai yarinya,kishi da zainabu abu babu dadi,hattara wlh da ni,yanzu kika fara gani sai kin fice sa qafafunki” ta fada tana qoqarin maida qofarta
“Ni nafi qarfinki,na kuma fi qarfin ire irenki,irinki dubu ma wallahi saidai suga sumayya su qyale” cike da mamaki tace
“Au haka kikace?,bari Allah ya kaimu gobe zaki amshi sakamakon wannan diban albarkar da kika yimin hannun mukhtar,sai nasa ya dakaki wlh cikin gidan nan” tsaki sumayyan ta ja sannan tace
“Mukhtar ne taqamarki ni kuwa Allah na riqe,da ni dake maga wanda yayi riqo da kakkaurar igiyar da bata tsinkewa” daga haka ta juya ta barta gun sake da baki tare da saqa mugun zare sake tada qaimi a kan sumayyan,babu shakka sai tasa an mata daurin butar malam yadda zata zamo qarqashin ikonta kamar yadda ta soma maida mukhtar.

        Ta jima tsugunne gaban gadon tana zubda hawaye tare da roqon ya yafe mata idan ta masa wani laifine da ya canza shi,yana jinta zuciyarsa na masa suya yana tuhumar kansa na dalilinsa na quntatawa sumayyar,saidai wani sashe mai qarfi na zuciyarsa na gaya masa yayi dai dai,da wannan ya shareta har ta gaji da tsugon nan ta miqe.

         Bata bari tayi asarar daren ba,alwala ta daura,ta kuma duqufa qwarai wajen roqon ubangiji ya kawo mata haske,ya tsaresu ita da mukhtar din,tana yi ta zubda hawaye masu dumi,lallai sai yanzu tasan meye rayuwar aure,ashe a baya duk wasa takeyi?kallon kitse take yiwa rogo?,ya jima cikin bargon yana kallonta,tausayinta na son tasiri cikin zuciyarsa amma hakan ya gagara,a haka bacci yayi awon gaba da shi.

        ****     ****    ****

WATA RAYUWA……….

       Wata bahuguwar rayuwa mai ban mamaki ta soma yi cikin gidan wadda ko cikin nafarkai mafarkinta bai taba biyowa ta irin wannan bigiren ba.

        Zainab ta zama tauraruwa mai wutsiya cikin gidan,a zahiri idan kayi naxari da tsinkaye ba zaka kawo ita ke sarrafa lamuran gidan ba,saidai ga duk wanda ya taba katari da fadawa halin da sumayya ke ciki tashin farko zai fuskanci inda zaman gidan ya sanya gaba.

          Ta bawa asiri amanna,kusan shi ya zame mata jagorar zamowarta mata ga mukhtar din,baya ga haka,macace mai tsananin kissa wadda ta cakuda ta da asirin take matuqar tasiri kan mukhtar din,cikin salo da sanabe zata bashi umarni kai tsaye zaya aiwatar,wanda idan kai dake gefe ka kalla zakayi zaton tsabar iya biyayya ce da iya zama da miji,saidai ina sam ba haka abun yake ba,asiri ke yawo kan qirji da qwaqwalwarsa,dukkan wani lamari da ikon sarrafawa na hannunta,abu GUDA DAYA TAK da yayi mata karen tsaye cikin tafiyar da aikinta shine SUMAYYA,ta kasa maida ita qarqashin mulkin nallakarta,wanda hatta su yaya yahanasu yanzun na qarqashin ikonta,,suna jin zafin yadda take mulkasun amma koda kudi basu isa suyi qorafi ba,saidai a bayan idonta suyita zagi da qorafi iyakarsu kenan.

        Abu guda data fuskanta shine,sumayyan ta lazumci karanta qur’ani,alwala ta zama abokiyarta,qur’ani ya zama abokin hirarta,koda wani abu ya tsorata ta abu na farko dakw fitowa bakinta shine SUBHANALLAH KO BISMILLAH,bata mantawa akwai ranar da aka kawo mata yaronta da ta haifa da bashir wato nafi’u,yaro ne maras ji sosai suka batawa mahaifinsa tarbiyyar yaro tunda yanzun haka yana hannun mama amarya ne mahaifiyat zainab,yana wasa da macijin roba,daidai fitowar sumayya ya wurga mata shi wanda sam bata ma kula da yaron na gurinka ba,sosai ta tsorata amma abinda ya fara fitowa daga bakinta shine BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM,daga haka ta shige zainab din na taya dan nata dariyar yadda ya tsorata sumayyan kallo basu isheta ba.

          Kusan babu wanda yasan halin da take ciki banda anty dije itama don tana ganin ita daya hankalinta bai kai mizanin sarrafa matsalolin irin wadan nan ba ita daya,tana amfani da shawararta kuma ta qaruwa tare da ganin nasarori,duk da ayanzun ta tattara lamarin mukhtar tana biyarshi da addu’a,sau tari wani lokacin ko ganinta ta fuskanci baison yi,abinda tafi daga mata hankali kenan,wasu lokutan kuma sai ka ganshi kamar ba shi ba ya koma mata yaya mukhtar dinta.

          Duk abinda ta gani tana dorashi ne kan mizanin nan da hausawa kance AURE IBADA NE ta yadda kumma tayi imani da hakanne,don sau tari anty dije na maimaita mata kalmar.

muje zuwa babi na gaba

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE