KUNDIN KADDARATA CHAPTER 27 BY HUGUMA
Tana bayansa har suka qarasa inda yaya yahanasu taje zaune tana kallon ikon Allah,a mutunce sumayyan tace
“Yaya ina kwana?”
“Lafiya” ta amsa babu yabo ba fallasa,tana son ganin kyawun kyautatawar data mata idan da hali ta mata godiya amma sai ta kasa,dama sumayyan ba domin ita tayi ba,tayi ne domin girman Allah da kuma girman da zumunci ke da shi a wajen ubangiji,hakanan ko ita ba zata so ace yau yaya abbakar ya auri wata da zata rabashi da su ba,ko ita ta haifa ya auri wadda zata rabasu din,kitchen ta wuce ta soma hadawa kanta dan abinda zata iya ci,ko kafin ta kammala ta fito ma falon babu kowa da alama ta tafi,sai ta zauna ta fara kurbar ruwan shayinta.
Kamar daga sama zainab din ta fito tana banbamin masifa kamar zata ci baki mukhtar na biye da ita yana son shan gabanta amma ya gaza cimmata,qerere tayi a kan sumayya wadda ko mutuncin kallonta bata samu ba
“Uban wa ya saki ki tabamin turaren wuta na?” Sosai abun ya bata mamaki,har tana iya bude baki tayi cigiyar kayan data tabbatar ba na Allah bane?,qare matsota tayi tana huci ta kuma maimaita tambayar tata,ganin zainab din na qoqarin kai hannunta jikinta ya sanya sumayyan dubanta
“Kada ki soma,don fankan fankan bata kilishi wallahi kika dakeni bazan dubi girmanki ba tsaf zan rama” idanu ta zaro tana nuna qirjinta
“Ni zaki daka don ubanki,to dokeni din”
“Wai meye haka ne zainab ba tun cikin daki nake miki magana ba?,ke sumayya tashi ki koma dakinki” wani kallo ta watsa masa sannan ta dakata da shan tea dinta
“Kayi haquri amma bata isa ba wlh don yanzu na fito ban kuma kammala uziri na ba,kana iya janye matarka idan na gama na tafi ita ta fito” ta fada tana ci gaba da kurbar shayinta duk da wata iriyar tafasa da zuciyarta ke mata,jinta take dai~dai sa su baki dayansu,banda daraja da girman sa da take gani babu abinda zai hana ta yayyaba masa baqaqen maganganu masu zafi
“Muje nace zan biyaki kudin ko?” Sai ta sauke ajiyar zuciya,dama abinda yafi damunta kenan,don sake samun wani maganin wannan da sauqi
“Allah ya ceceki” ta fada tana huci sannan ta juya tabi mukhtar din,cak shayin ya tsaya mata a wuya,ambaton sunan Allah ta dinga yi don ya kawo mata dauki,tabbas sai yau ta tabbatar mukhtar dinta ba cikin hayyacinsa yake ba,kayan karin da bata gama ci ba kenan.
**** **** *****
Wani nannauyan bacci ne ya dauketa tun bayan kammala sallar asuba,hakan ya sanya bata tashi ba sai wajen sha daya saura na rana saboda zafin rana da ya fara hudo labule.
Da wata mahaukaciyar yunwa ta farka,saboda haka bandaki kawai ta shiga ta wanko bakinta ta shiga kitchen don samarwa kanta abinda zata ci,don bata sa aka ba tasan ba samun abun kari zata yi ba,haka ne yake faruwa duk ranar girkin zainab din,shi kansa mai gidan wani lokaci sai dai ya fita haka.
Sam bata lura da meke faruwa ba sai data shiga cikin kitchen din sosai,nafi’u ne yaron zainab tsaye dare dare kan stool yana sauke dukkan farantanta na tangaran dake jere cikin glass drower dinta yana sakinsu qasa daya bayab daya suna tarwatsewa.
Da sauri ta qarasa ciki tana kiran sunansa cikin tsawa,ko gezau baiyi ba bare ya fasa aikata abinda yakeyi din,hannunshi ta riqe gam kana ta saukeshi daga kan stool din tana dubansa ransa a bace
“Baka da hankali?,ko bakasan me kake yi ba?,ko bakasan abin amfani kake lalatawa ba?”,cikin rashin kunya yace mata
“na sani mana”abun sai ya bata haushi ta kama kunnansa ba tare da ta murde ba tace
” wato tsabar rashin ji ne kenan ko?”
“Sakarmin kunnena ai kema bake kika siya ba,kuma Allah ya isa na da tabamin kunne da kikayi” sosai yaron ya bata haushi da mamaki,ta sanya tafin hannunta ta buge masa baki,wata qara ya saki kamar wanda aka sanya wuqa aka yanke masa maqogaro yana fadin “wayyo bakina wayyo mama ta fasamin baki”.
A hautsine ta fado kitchen din dama tasan hakan na iya faruwa,don ita ta sanyashi,saboda har yau bata huce takaicin asarara maganinta da sumayyan ta jawo mata ba,duk da mukhtar din sai da ya biya ninkin kudinsa,da sauri ta qarasa inda suke tsaye ta ture sumayya tana fadin
“me kika yi masa?,me tayi maka nafs(da yake haka take kiransa)”
“Bakina ta dakarmin mama duba ki gani”hannunsa ta sauke tana duba bakin,babu wani abu da yayi tunda duka duka dukan data masa ba wani mai zafi bane,waiwayawa tayi ta dubi sumayya dake tsaye rungume da hannu tana dubansu
” dukarmin yaro kikayi saboda bakisan ciwon haihuwa ba ko?,to wallahi sai na rama masa”sai kuwa tayo kan sumayyan gadan gadan.
Ko alama bata motsa ba har ta qaraso inda take,ta daga hannu da niyyar zuba mata mari caraf ta kama hannun nata ta yarfar da shi gefe,sannan cikin bacin rai tace mata
“Bansan ke din wace iriyar uwa bace,ban kuma san irin tarbiyyar da kika bama yaronki ba,amma bari na gaya miki,matuqar irin wannan tarbiyyar ita kika bashi to ba shakka kin cuci kanki,abu na gaba duk iya zaluncin da zaki aikata cikin gidan nan kiyi,Allah na sane da ke,amma kada ki soma gigin daukar hannu kice zaki dake ni,don baki haifeni ba,ba kuma kisan ciwo na ba kamar yadda kika ce bansan ciwon haihuwa ba,kuma kema ba Allah kika yiwa fadanci ba ya baki,ganin……..”.ihun da zainab din ta qwalla gami da dora hannu bisa ka ya dakatar da ita daga maganar da takeyi,sai tayi sororo tana dubanta tare da tunanin ko zainab din nada ciwon hauka ne dake tashi lokaci bayan lokaci?.
Sam bata fahimci tarko bane ta dana mata sai data ga shigowar mukhtar cikin kitchen din a rude,ashe tuni taga giftawar inuwarsa ita zainab din,binsa tayi da kallo sanda ya nufi zainab,ta manta kwana nawa rabon da ta sanyashi cikin idanunta,ranar qarshe kawai zata iya tunawa da bata kuma ganinsa ba sai yau,itace randa ya rufeta da fada tamkar zaya daketa,sabida tayi dan wake abincin dare,ita kuma zainab tace sam bazata ci ba ai dan wake ba abinci bane,ya umarceta ta shiga kitchen ta yiwa zainab din shinkafa da miya qarfe goma na dare,umarnin ya yi mata tsauri saboda haka bata ko tanka ba ta wuce dakinta tayi kwanciyarta bayan ta kulle qofarta,don tana da yaqinin zaya iya biyota,ilai kuwa ya biyo sahun nata,yayi bugun duniya taqi ta bude masa,hakan ya sake harzuqa shi,haka ya koma tare da ci mata alwashin sai ya sabar mata,to tun daga ranar rabon data karbi girki ma cikin gidan,saidai idan sun kammala a barshi a kitchen,idan tana da sha’awarci ta diba,idan bata ga dama ba ma ko kallo bai isheta ba.
“Wato ke kin zama ‘yar iska mara mutunci ko?” Ya fada yana nufota cikin huci bayan zainab ta gama tsara masa qarya kan abinda ya faru,hannu tasa ta toshe bakinta saboda yadda taji kanta ya mata dummm,kalmar ta yiwa qwaqwalwarta tsauri haka nan ta yiwa kanta nauyi,ita mukhtar ke kira da ‘yar iska?,kalmar da babu wani mahaluqi da ya taba jifarta da ita?,da sauri ta juya ta fita daga kitchen din cikin sassarfa saboda kukan dake shirin qwace mata ba wai don mukhtar din dake nufota ba.
Yau babu tantama abinda ke mata kaikawo a zuciya ya tabbata,mukhtar ya daina sonta ya daina mararin ganinta,wannan wacce iriyar rayuwa ce?,haka mata keji duk sanda suka samu juya baya daga wajen mazajensu ba tare da haqqinsu ba?,me yakai wannan zunubi shiga tsakanin ma’aurata?,shiga tsakanin masoya?,masoyan da suka gina zuciyoyinsu da qaunar juna,tsaftatacciyar qauna ta fisabilillahi. Wani mugun amai mai zafi taji yana taso mata,da qyar ta samu ta isa bandaki,ta dinga kakarin aman tamkar hanjin cikinta zai fito,saidai banda wahala da yunquri babu abinda abinda ya fita din saboda babu komai cikin cikin nata,don a yanzu ba kowanne lokaci take yarda da abincin zainab ba. Haka ta gama wahalarta sai yawu kawai data fitar ta sakarwa kanta shower tana wanka tana kuka har ta kammala sannan ta dawo cikin dakin iska na dibarta ta zabi doguwar riga ta sanya ta koma saman gadonta tayi dai dai,jinta take wani iri daban,zazzabi taji na son rufeta,haka ta yunqura ta sha paracetamol ta dawo ta kuma kwanciya,tunani ta shiga mai zurfi lokaci lokaci tana dauke hawayen dake bin kuncinta.
Kamar daga sama ta dinga jiyo sallamar zainab qanwarta,daurewa tayi ta miqe ta dawo bakin qofar dakinta don ta sanar mata tana ciki kada zainab tayi qaryar bata nan,sai data tabbata zainab din taji sannan ta koma bakin gadonta ta zauna har ta shigo. Kallo daya ta yiwa sumayyan tace
“Lafiya kike kuwa anty” qoqarin qaqalo murmushi tayi sannan ta dan ja tsaki
“Qalau nake,yau ne kinga na tashi bana jin dadin jikina da bakina gaba daya”
“Yaya kamar fa kuka naga kinyi” sai ta basar ta hanyar fadin
“Barni kawai,nida mukhtar ne ya matsan sai da nasha magani,ni kuma kinsan bana son qwayoyi” sai zainab din ta gamsu da maganarta ta zauna tana fadin
“Kamar kuwa mamanmu ta sani kinga tace sai na tsaya tayi dambu mutuminki na kawo miki”,ba jira kuwa ta sanya hannu ta janyo flask din ta bude ta soma ci. Sosai taji dadinsa cikin bakinta,sai data ci fiye da rabi sannan ta ajjiye.
Bata sake fitowa daga dakin ba ranar,kusan yini sukayi ita da zainab tana mata ‘yan gyare gyare cikin dakin,koda ta yunqura don sama mata abinci sai tace azumi ma takeyi,a nan take gaya mata mama tace taje ta yiwa anty dije sallama zasu koma abuja ita da mai gidanta,gwamnatin tarayya ta qara masa matsayi,duk sai jikinta yayi sanyi,bata son rabuwa da anty dijen,idan ta tafi bata da gun wanda zata je su shawarta matsalarta kenan,anty dije zata tafi ta barta a sanda alamu ke nuna matsalolinta qara qarfi suke. Sai taji zuciyarta na neman raurawa amma sai ta aro dakiya da juriya ta yafa wa kanta gudun kada zainab din ta fahimci wani abu.
Sai yamma lis zainab ta tafi ko banza ta debe mata kewa sosai kuwa,a ranar ta sanar da mukhtar tana so taje wajen anty dijen washegari,saboda jibi zasu tafi,Allah ya dorata a kansa ranar tambotsan nasa da sauqi,don a dakinsa ma ta kwana duk da zaman kurame sukeyi.
**** **** ****
Tun goma na safe ta kammala shirinta tsaf cikin shadd ja wadda aka yiwa adon stone work baqi,ita kanta sai data tsaya ta kalli kanta,duk damuwar da take ciki amma sai taga ramarta bata fito kamar baya ba,mamakin yadda ta qara haske da cika takeyi,haka ta yafa baqin mayafi a kanta ta saqala baqar jaka ta fito.
A harabar gidan sukayi clashing da su kasancewar harabar ba mai girma bace,tilas idan zata wuce din su ganta,yana zaune cikin mota zainab na tsaye riqe da murfim mota,kudade ta yanka masa zai bata shine ta biyoshi amsa,tana karba ta juya tayi ciki abinta,zuwa lokacin sumayyan ma har takai ga ficewa daga gidan.
A hankali yake bin bayanta,sosai ya rage gudun motar yana tafiya a hankali don baison ya wuceta,tafiya take cikin nutsuwa,idan ka kalleta sai ka rantse da Allah bata taba aure ba,sosai shaddar ta haska jar fatarta,ga komai nata yayi mata cif a jikinta duk da da shigarta babu inda ta bayyana tsiraici,a haka har suka kai bakin titi,yana so yace ta shigo ya kaita amma kamar an masa shamaki da ita haka yakeji,haka ya karya kan motarsa ya wuceta ya hau kwalta sosai. Itakam sai a lokacin ne ma ta lura da shi,da idanu ta rakashi sannan daga bisani ta dauke kanta tana hadiye wani abu mai d’aci.
Sosai ta lula tunani tsaye a bakin titin wanda hakan ya sanya ta kasa ankara da horn din da yake ta zabga mata,murmushi tayi ta qaraso gaban motar bayan ya sauke glass din
“Wa nake gani kamar abdur rahman cikin mota?”ta fada tana duban motar samfurin *vibe* fara qal da ita,sosai motar ta mata kyau
Murmushi yayi yana fadin
“Eh mana,ya son ranki?” Cikin dariya tace
“Fes wallahi”
“Ina zuwa haka da safe?”
“Zani gidan anty dije ne zamuyi sallama suna shirin bar mana kano su gudu abuja”
“Shigo ciki ma qarasa maganar ai hanya ta ce indai gidan da take har yanzu shine” ya fada yana bude mata mazaunin gaba
“Rufan asiri nan ai na qanwata ne,nan ma ya isa” ta fada tana shiga baya
“Yayarki dai,kina nufin nidin ban girme miki da wajen shekara uku ko hudu ba?”
“Jimin mutum da shegen son girma,shekara hudu kakar wata shekara arba’in,kai uku ne ma”
“Ko second daya ne dai na fiki ko?” Ya fada yana dariya,don sun saba da wannan caftar indai shi da sumayyan ne,itama dariya ta saki sannan suka shiga gaisawa a mutunce,ta tambayeshi mutanan gidan da kawunsa wanda qani ne ga mahaifin mukhtar.
“Kinsan tun ranar nan naso kawowa yaya mukhtar mota ta ya gani da kuma takardar zanen filin da zamu fara gina islamic clinic to ban samu dama ba”
“Da kyau masha Allah abdhr rahman,Allah ya sanya alkhairi ya kade fitina,kace yanzu sai bude asibiti”
“In sha Allah duk da aikin ginin ba qaramin abu bane,har kwantarwa nake sa ran zamu dinga yi,zamuyi amfani da likitancin musulunci da kuma na’urorin bature”
“Kace mun kusa fara kiranka alhaji abdur rahman”
“Da ba alhajin bane?,mijinki zaki cewa haka,gashi har yau ya kasa zuwa ko ina,ya zama sai a hankali wallahi” sai ta danyi shiru tana sauke boyayyar ajiyar zuciya don ha taba mata inda yake mata qaiqayi
“Ina fata kina ci gaba da addh’o’inki ko?”
“Babu abinda na fasa abdur rahman,sauqin ne sai a hankali”
“Haka ne,kada ki gaji,kinsan ita cuta farad daya take shiga sauqi kuma samuwarsa sai a hankali,Allah ya yaye ma dukkan musulmi baki daya”
“Amin abdur rahman,na gode” haka suka ci gaba da hira jifa jifa yana kwasarta da tsokana,har qofar gidan anty dije ya sauketa sanna ya mata kyautar dubu uku,da fari taqi karba sai da ya bata rai sannan ta amsa tayi godiya tare da bashi saaon gaisuwa gun qanwarsa bahijja da mamarsu.
Anty dije taji dadin ganinta sosai,nan suka wuni suna hira,ta tayata hada ragowar kayayyakin da bata kammala hada kansu ba,tuni yaranta sunyi gaba don su qarasa kammale gidan kafin isowar maman tasu. Suna hada kayan tana mata nasiha mai ratsa jiki,idanun sumayyan ya hada qwalla har ta kai ga gangarowa,ta share qwallar tana fadin
“Yanzu shikenan anty?,gurin wa zan dinga zuwa” sosai ta bata tausayi,yarinyar da dududu bata wuce shekara sha tara ba amma ta hadu da kaidin kishiyoyi kala kala,sai ta saki abinda take ta koma gefanta ta zauna
“Kina da Allah sumayya,baya ga haka akwai waya hannunki,duk abinda ya shige miki duhu ki kirani ki tambayeni,koda babu kudi a ciki kimin plashing zan kiraki da yardar Allah,ki ninka haqurinki kawai,domin duk wata mace da kika ga ta zama wata gidan mijinta ki tambayeta wanne irin haquri ta hadiya kafin ta kai ga cimma wannan matakin”
“To anty na gode”
“Babu godiya,ke diyata ce kamar su yasmin kike a gurina…..amma sumayya yanayin jikinki kamar ya sauya?,ko baki kula ba?” Ta fada tana kallonta
“Me kika gani anty?”
“Bakya jin wani sauyi a jikinki?”
“Babu abinda nake ji” ta fada tana kallon anty,shiru ta danyi sannan tace
“Shikenan…..koyaya kika ji wani abu kada ki zauna,kije asibiti”duk da bata fahimci abinda take nufi ba amma ta amsa mata da to.
Ana gab da sallar magariba ta koma gida,a gajiye ta koma,bandaki kawai ta fara shiga tayi wanka ya daura alwala,sai da ta kammala sallahr magariban sannan ta fita,cikin kitchen taji motsinta sai ta tura qofar ta shiga,tana tsaye tana hada food flask na abincin mukhtar,qarasawa tayi kusa da ita ta mata sallama,kai kawai ta daga ta dubeta ta maida kai taci gaba da abinda take ba tare data amsa ba,ita din ma bata damu data amsa ba kai tsaye ta jeho mata tambayar da ta fito da ita
“ina abincina zainab,banga flask dina ba”
Dagowa tayi sosai ta sake kallonta,sai ta saka wata dariya data sanya dole sumayyan ta tsaya tana kallonta cike da alamar tambaya,sai da ta tsagaita don kanta sannan tace
“Ince ko baki samu labarin baki da abinci a gidan nan ba” jin maganar tayi banbarakwai,ba kuma ta fahimci inda ta sa gaba ba,saboda haka taci gaba da kallonta,dauke kai tayi daga bisani sai ta nufi dan qaramin store din dake kitchen din da niyyar fiddo da ko indomie ce ta tafasa,sai ta tarad da store din a garqame da kwado,waiwayowa tayi ta sake duban zainab din
“Naga alamun baki fahimta ba,amma bari nayi miki bayani dalla dalla,mukhtar ya soke baki abincinsa,walau ni na dafa ko ke kika dafa kin fahimta ai yanzu ko?” Sosai maganar ta daketa,sai ta kasa furta komai baya ga wani abu da ya tokare maqoshinta,bata fahimci me hakan ke nufi,tilas ta jira dawowarsa tunda shi ya ajiyeta ba zainab ba,wannan maganar ba tata bace. Wuce zainab din tayi ta nufi sashenta ta dauki tukunya ta tari ruwa ta dora kan gas tare da jefa lipton,tilas ta sanya wani abu a cikinta ba don haka ba abinda take ji cikin zuciyarta bata jin wani abu mai suna abinci zai iya wucewa ta maqogoronta.
Hannayenta ta harde saman qirjinta tana jiran ruwan ya tafasa,tamkar zata fadi haka take ji,ga yunwa ga bacin rai,tana kammalawa ta juye a cup ta nufi daki,bata ko bi ta kan qananun habaicin da zainab keta jefawa cikin waqe,don yanzu bata ita take ba ta kanta take. Tea ta hada da kayan shayinta wanda dama a dakin suke.
Ko rabi bata sha ba ta soma yunqurin dawo da shi,sai data amayar da shi tas sannan ta dawo ta zube qasan carfet din dakin cikinta naci gaba da juyawa,rasa abinda ke mata dadi tayi,fashewa tayi da kuka tana kiran sunan Allah.