KUNDIN KADDARATA CHAPTER 29 BY HUGUMA

Yau babu tantama abinda ke mata kaikawo a zuciya ya tabbata,mukhtar ya daina sonta ya daina mararin ganinta,wannan wacce iriyar rayuwa ce?,haka mata keji duk sanda suka samu juya baya daga wajen mazajensu ba tare da haqqinsu ba?,me yakai wannan zunubi shiga tsakanin ma’aurata?,shiga tsakanin masoya?,masoyan da suka gina zuciyoyinsu da qaunar juna,tsaftatacciyar qauna ta fisabilillahi. Wani mugun amai mai zafi taji yana taso mata,da qyar ta samu ta isa bandaki,ta dinga kakarin aman tamkar hanjin cikinta zai fito,saidai banda wahala da yunquri babu abinda abinda ya fita din saboda babu komai cikin cikin nata,don a yanzu ba kowanne lokaci take yarda da abincin zainab ba. Haka ta gama wahalarta sai yawu kawai data fitar ta sakarwa kanta shower tana wanka tana kuka har ta kammala sannan ta dawo cikin dakin iska na dibarta ta zabi doguwar riga ta sanya ta koma saman gadonta tayi dai dai,jinta take wani iri daban,zazzabi taji na son rufeta,haka ta yunqura ta sha paracetamol ta dawo ta kuma kwanciya,tunani ta shiga mai zurfi lokaci lokaci tana dauke hawayen dake bin kuncinta.

Kamar daga sama ta dinga jiyo sallamar zainab qanwarta,daurewa tayi ta miqe ta dawo bakin qofar dakinta don ta sanar mata tana ciki kada zainab tayi qaryar bata nan,sai data tabbata zainab din taji sannan ta koma bakin gadonta ta zauna har ta shigo. Kallo daya ta yiwa sumayyan tace
“Lafiya kike kuwa anty” qoqarin qaqalo murmushi tayi sannan ta dan ja tsaki
“Qalau nake,yau ne kinga na tashi bana jin dadin jikina da bakina gaba daya”
“Yaya kamar fa kuka naga kinyi” sai ta basar ta hanyar fadin
“Barni kawai,nida mukhtar ne ya matsan sai da nasha magani,ni kuma kinsan bana son qwayoyi” sai zainab din ta gamsu da maganarta ta zauna tana fadin
“Kamar kuwa mamanmu ta sani kinga tace sai na tsaya tayi dambu mutuminki na kawo miki”,ba jira kuwa ta sanya hannu ta janyo flask din ta bude ta soma ci. Sosai taji dadinsa cikin bakinta,sai data ci fiye da rabi sannan ta ajjiye.

Bata sake fitowa daga dakin ba ranar,kusan yini sukayi ita da zainab tana mata ‘yan gyare gyare cikin dakin,koda ta yunqura don sama mata abinci sai tace azumi ma takeyi,a nan take gaya mata mama tace taje ta yiwa anty dije sallama zasu koma abuja ita da mai gidanta,gwamnatin tarayya ta qara masa matsayi,duk sai jikinta yayi sanyi,bata son rabuwa da anty dijen,idan ta tafi bata da gun wanda zata je su shawarta matsalarta kenan,anty dije zata tafi ta barta a sanda alamu ke nuna matsalolinta qara qarfi suke. Sai taji zuciyarta na neman raurawa amma sai ta aro dakiya da juriya ta yafa wa kanta gudun kada zainab din ta fahimci wani abu.

Sai yamma lis zainab ta tafi ko banza ta debe mata kewa sosai kuwa,a ranar ta sanar da mukhtar tana so taje wajen anty dijen washegari,saboda jibi zasu tafi,Allah ya dorata a kansa ranar tambotsan nasa da sauqi,don a dakinsa ma ta kwana duk da zaman kurame sukeyi.

****      ****      ****

Tun goma na safe ta kammala shirinta tsaf cikin shadd ja wadda aka yiwa adon stone work baqi,ita kanta sai data tsaya ta kalli kanta,duk damuwar da take ciki amma sai taga ramarta bata fito kamar baya ba,mamakin yadda ta qara haske da cika takeyi,haka ta yafa baqin mayafi a kanta ta saqala baqar jaka ta fito.

A harabar gidan sukayi clashing da su kasancewar harabar ba mai girma bace,tilas idan zata wuce din su ganta,yana zaune cikin mota zainab na tsaye riqe da murfim mota,kudade ta yanka masa zai bata shine ta biyoshi amsa,tana karba ta juya tayi ciki abinta,zuwa lokacin sumayyan ma har takai ga ficewa daga gidan.

A hankali yake bin bayanta,sosai ya rage gudun motar yana tafiya a hankali don baison ya wuceta,tafiya take cikin nutsuwa,idan ka kalleta sai ka rantse da Allah bata taba aure ba,sosai shaddar ta haska jar fatarta,ga komai nata yayi mata cif a jikinta duk da da shigarta babu inda ta bayyana tsiraici,a haka har suka kai bakin titi,yana so yace ta shigo ya kaita amma kamar an masa shamaki da ita haka yakeji,haka ya karya kan motarsa ya wuceta ya hau kwalta sosai. Itakam sai a lokacin ne ma ta lura da shi,da idanu ta rakashi sannan daga bisani ta dauke kanta tana hadiye wani abu mai d’aci.

Sosai ta lula tunani tsaye a bakin titin wanda hakan ya sanya ta kasa ankara da horn din da yake ta zabga mata,murmushi tayi ta qaraso gaban motar bayan ya sauke glass din
“Wa nake gani kamar abdur rahman cikin mota?”ta fada tana duban motar samfurin *vibe* fara qal da ita,sosai motar ta mata kyau
Murmushi yayi yana fadin
“Eh mana,ya son ranki?” Cikin dariya tace
“Fes wallahi”
“Ina zuwa haka da safe?”
“Zani gidan anty dije ne zamuyi sallama suna shirin bar mana kano su gudu abuja”
“Shigo ciki ma qarasa maganar ai hanya ta ce indai gidan da take har yanzu shine” ya fada yana bude mata mazaunin gaba
“Rufan asiri nan ai na qanwata ne,nan ma ya isa” ta fada tana shiga baya
“Yayarki dai,kina nufin nidin ban girme miki da wajen shekara uku ko hudu ba?”
“Jimin mutum da shegen son girma,shekara hudu kakar wata shekara arba’in,kai uku ne ma”
“Ko second daya ne dai na fiki ko?” Ya fada yana dariya,don sun saba da wannan caftar indai shi da sumayyan ne,itama dariya ta saki sannan suka shiga gaisawa a mutunce,ta tambayeshi mutanan gidan da kawunsa wanda qani ne ga mahaifin mukhtar.

“Kinsan tun ranar nan naso kawowa yaya mukhtar mota ta ya gani da kuma takardar zanen filin da zamu fara gina islamic clinic to ban samu dama ba”
“Da kyau masha Allah abdhr rahman,Allah ya sanya alkhairi ya kade fitina,kace yanzu sai bude asibiti”
“In sha Allah duk da aikin ginin ba qaramin abu bane,har kwantarwa nake sa ran zamu dinga yi,zamuyi amfani da likitancin musulunci da kuma na’urorin bature”
“Kace mun kusa fara kiranka alhaji abdur rahman”
“Da ba alhajin bane?,mijinki zaki cewa haka,gashi har yau ya kasa zuwa ko ina,ya zama sai a hankali wallahi” sai ta danyi shiru tana sauke boyayyar ajiyar zuciya don ha taba mata inda yake mata qaiqayi
“Ina fata kina ci gaba da addh’o’inki ko?”
“Babu abinda na fasa abdur rahman,sauqin ne sai a hankali”
“Haka ne,kada ki gaji,kinsan ita cuta farad daya take shiga sauqi kuma samuwarsa sai a hankali,Allah ya yaye ma dukkan musulmi baki daya”
“Amin abdur rahman,na gode” haka suka ci gaba da hira jifa jifa yana kwasarta da tsokana,har qofar gidan anty dije ya sauketa sanna ya mata kyautar dubu uku,da fari taqi karba sai da ya bata rai sannan ta amsa tayi godiya tare da bashi saaon gaisuwa gun qanwarsa bahijja da mamarsu.

Anty dije taji dadin ganinta sosai,nan suka wuni suna hira,ta tayata hada ragowar kayayyakin da bata kammala hada kansu ba,tuni yaranta sunyi gaba don su qarasa kammale gidan kafin isowar maman tasu. Suna hada kayan tana mata nasiha mai ratsa jiki,idanun sumayyan ya hada qwalla har ta kai ga gangarowa,ta share qwallar tana fadin
“Yanzu shikenan anty?,gurin wa zan dinga zuwa” sosai ta bata tausayi,yarinyar da dududu bata wuce shekara sha tara ba amma ta hadu da kaidin kishiyoyi kala kala,sai ta saki abinda take ta koma gefanta ta zauna
“Kina da Allah sumayya,baya ga haka akwai waya hannunki,duk abinda ya shige miki duhu ki kirani ki tambayeni,koda babu kudi a ciki kimin plashing zan kiraki da yardar Allah,ki ninka haqurinki kawai,domin duk wata mace da kika ga ta zama wata gidan mijinta ki tambayeta wanne irin haquri ta hadiya kafin ta kai ga cimma wannan matakin”
“To anty na gode”
“Babu godiya,ke diyata ce kamar su yasmin kike a gurina…..amma sumayya yanayin jikinki kamar ya sauya?,ko baki kula ba?” Ta fada tana kallonta
“Me kika gani anty?”
“Bakya jin wani sauyi a jikinki?”
“Babu abinda nake ji” ta fada tana kallon anty,shiru ta danyi sannan tace
“Shikenan…..koyaya kika ji wani abu kada ki zauna,kije asibiti”duk da bata fahimci abinda take nufi ba amma ta amsa mata da to.

Ana gab da sallar magariba ta koma gida,a gajiye ta koma,bandaki kawai ta fara shiga tayi wanka ya daura alwala,sai da ta kammala sallahr magariban sannan ta fita,cikin kitchen taji motsinta sai ta tura qofar ta shiga,tana tsaye tana hada food flask na abincin mukhtar,qarasawa tayi kusa da ita ta mata sallama,kai kawai ta daga ta dubeta ta maida kai taci gaba da abinda take ba tare data amsa ba,ita din ma bata damu data amsa ba kai tsaye ta jeho mata tambayar da ta fito da ita
“ina abincina zainab,banga flask dina ba”
Dagowa tayi sosai ta sake kallonta,sai ta saka wata dariya data sanya dole sumayyan ta tsaya tana kallonta cike da alamar tambaya,sai da ta tsagaita don kanta sannan tace
“Ince ko baki samu labarin baki da abinci a gidan nan ba” jin maganar tayi banbarakwai,ba kuma ta fahimci inda ta sa gaba ba,saboda haka taci gaba da kallonta,dauke kai tayi daga bisani sai ta nufi dan qaramin store din dake kitchen din da niyyar fiddo da ko indomie ce ta tafasa,sai ta tarad da store din a garqame da kwado,waiwayowa tayi ta sake duban zainab din
“Naga alamun baki fahimta ba,amma bari nayi miki bayani dalla dalla,mukhtar ya soke baki abincinsa,walau ni na dafa ko ke kika dafa kin fahimta ai yanzu ko?” Sosai maganar ta daketa,sai ta kasa furta komai baya ga wani abu da ya tokare maqoshinta,bata fahimci me hakan ke nufi,tilas ta jira dawowarsa tunda shi ya ajiyeta ba zainab ba,wannan maganar ba tata bace. Wuce zainab din tayi ta nufi sashenta ta dauki tukunya ta tari ruwa ta dora kan gas tare da jefa lipton,tilas ta sanya wani abu a cikinta ba don haka ba abinda take ji cikin zuciyarta bata jin wani abu mai suna abinci zai iya wucewa ta maqogoronta.

Hannayenta ta harde saman qirjinta tana jiran ruwan ya tafasa,tamkar zata fadi haka take ji,ga yunwa ga bacin rai,tana kammalawa ta juye a cup ta nufi daki,bata ko bi ta kan qananun habaicin da zainab keta jefawa cikin waqe,don yanzu bata ita take ba ta kanta take. Tea ta hada da kayan shayinta wanda dama a dakin suke.

Ko rabi bata sha ba ta soma yunqurin dawo da shi,sai data amayar da shi tas sannan ta dawo ta zube qasan carfet din dakin cikinta naci gaba da juyawa,rasa abinda ke mata dadi tayi,fashewa tayi da kuka tana kiran sunan Allah.

Kwananta biyu kwance cikin dakin babu abinda take iya hasalawa,daga kwanciya sai bacci,ga wani shegen zazzabi da yaqi sauka daga jikinta,duk lokacin da ta yunqura ta yiwa kanta duren shayi tofa qarshensa ya dawo baki daya,abinci kuwa ko kadan bata da sha’awar cin komai,hakan ya sanya ta haqura ta zubawa sarautar Allah ido,banda ruwa babu abinda take kurba,roqon Allah take ya sassauta mata ko ya jefo mata wanda zaya taimaketa,hatta da wayarta bata san inda ta cillata ba,a haka ta shafe kwana hudu cur bata ga kowa ba rana gurzar ciwnta ita daya,duk da cewa taci ranar girkinta har ta fita amma bata ga idon mukhtar ba,to idan da sabo dama ta riga data saba da hakan,data ga irin hakan tasan an karbi kwananta ne an qarawa zainab.

****     *****     *****

Cikon kwana na biyar din cikin ikon Allah ta ji sauqi sauqin jikinta,tana jin qwari qwari a jikinta,har ta iya shiga da yammaci gab da magariba bandaki tayi wanka,tana fitowa ta soma laluben wayarta,can cikin jakar da ta dawo daga gidan anty dije ta ganta,a nan taci karo da dubu ukun da abdur rahman ya bata,sai taji dadin kudin don bata da ko siai a hannunta,to ina ma taga mai batan tunda ita ba sana’a take ba,caji ta sanya a socket din dake daura da madubinta,ta dawo bakin gadonta ta zauna ta soma shafa mai,daga inda take zaunen tana iya hango kanta sosai cikin madubi,ta rame sosai tayi wani fayau da ita,sai uban fari da ta qara kamar wadda ta hadiyi qwayar qara hasken fata.

Tura qofar dakin nata da akayi shi ya maidota cikin hayyacinta,ta dubi bakin qofar,mukhtar ke shigowa,sanye da yadi tissue na maza orange wanda ya ciza,yayi kyau sosai amma sai taga kamar ya rame,duj da bata sani ba ko idanunta ne,don idan ba makuwa tayi ba rabonta da shi yau kwanaki shida cif. Kanta ta dauke don bata ga dalilin ci gaba da kallonsa ba,ta soma lalubar mayafinta ta lullube jikinta saboda guntun towel ne kawai daure a qirjinta.

Shikam kallonta yake ci gaba da yi yana son lalubar sonta cikim zuciyarsa amma ya rasa duk da dumbin qaunar da yake jin tana zanga zanga cikin zuciyarsa wadda ya azata a bigiren tausayi,uban haushinta da yake ji yau babu shi kamar yadda bai jin soyayyarta cikin zuciyar tasa. Bata sake bi ta kansa ba har ta gama shafa manta,ta bude drower dinta ta fidda kayan da zata sanyasai a lokacin ta kuma dubansa
“Ka fita don Allah zan sanya kaya” ta fada idanunta tsakar nashi
“Me ya sameki haka sumayya naga kin rame?,ko duk shegen kishin da kika sanyawa ranki ne kamar yadda zainab ta fada?”ya fadi ba tare da yayi duba ga qorafinta na farko ba
“Kan bala’i” ta fada cikin zuciyarta,wani baqinciki na takore mata qirji,wannan rainin hankalin da me yayi kama?,ita yake tambaya ma meke damunta?
“Ba wannan ne a gabana ba,ka ficen a daki” ta fada ranta na suya,sai ya fara takowa inda take,wani shauqinta na fusgarsa,son kasancewa kawai yake da ita,yayi kewarta kwanakin bakwai din nan da bai ziyarceta ba
“Bari na qaraso ki gayamin nawa muka hada muka gina gidan da har dakin ya zama naki”. Qarasowarsa ke da wuya qamshin turarensa ya daki hancinta,wani tashin hankali ya ziyarceta,take ta saki kayan hannunta ta buqaci bandaki,nan ta fara kelaya aman da yayi sanadiyyar ficewar ruwan tea din data samu yau ya zauna mata.

” lafiya sumayya?,meke damunki?,me ya sameki?”haka ya dinga fadi yana riqe da ita,dukkan alamun tashin hankali sun bayyana a fuskarsa wanda hakan yayi matuqar daurewa sumayya kai,mukhtar din tamkar wani bugun jinnu haka ya koma,idan yaso ya dinga gasa mata aya a hannu shi da matarsa,amma wani lokaci sai ya dinga yunqurin juyewa ya koma mata yaya mukhtar dinta sak wanda ta sani a can baya.

Ganin qamshin turaren ke sake dugunzuma tunaninta ya sanya ta buqaceshi da ya matsa ya barta bata so,haka ya koma baya ya zuba mata ido har ta kammala ta gyara wajen ta dawo bakin gadon ta zauna tana maida numfashi
“Kishirya na kaiki asibiti,ni bansan baki da lafiya ba” duk da yadda take fidda numfashi dai dai amma hakan bai hanata maida masa magana ba
“Bani buqata,me magani zaya yimin?,shin wai damuwa kayi ma da wata sumayya?,na tabbata bakaqi na mutu ba,tunda har zaka iya hanawa a bani abincin gidanka ina a matsayin matar ka” ta qarashe maganar tana sakin kuka don sosai batun ke ci mata qoqon zuciya,ba wai don ta damu da abincin ba,a’ah,ta dauka tafi qarfin komai a gidan mukhtar din,ta dauka ita din mai iya dauka ce ta bayar ma kyauta,sai gashi ita ake hanawa abinci
“Wallahi ni bansan lokacin da akayi hakan ba,waye ya gaya miki ni na hana?”maganarsa ta ratsa kunnenta,sai ta daga ido tana dubansa tana daga kwancen,gani take kawai raina mata wayau zai yi,aljanu gareshi ko farfadiya ce ta kamashi lokacin da ya bawa zainab din umarni?,baqinciki ne ya hanata magana,ganin tayi shiru ba tare da tace komai ba sai kukan ta data ci gaba da yi yasa yace
” duka mubar wannan maganar muje asibitin a dubaki tukun,zanje nayi sallah ma dawo”ya fada yana ficewa.

Da fari taso taqi yarda,amma jin tsaiwa na niyyar gagararta sanda zata bada faralin sallar magariba yasa ra taushi zuciyarta ta amince,ita kanta zata so taji meke damunta bawai tayita zama da ciwo ba,tunda tunda take bata taba jin irin hakan ba.

Ba jimawa da idar da sallar sai gashi ya dawo,zuwa lokacin da qyar ta samu ta gama tata sallar aman ya sake tsinke mata,jikinta yayi laushi tubus sai numfashi da take maidawa,yaso taimaka mata wajen fita amma tace bata buqata,haka ta dinga bin bango har suka isa cikin motar.

Wani private hospital dake cikin unguwar tasu ya kaita,bayan taga likita ya bata takardar gwaji taje lab,minti goma ta karbi sakamakon ta koma dakin ganin likitan ta kai masa
“Alhamdulillah,sai ka godewa Allah,madam na dauke da juna biyu”baki dayansu wuta ce ta dauke musu kada ma sumayya taji labari,sai ta fara girgiza kai hawaye na sauko mata,magana take son yi amma bakinta ya gaza furta komai
” likita don Allah ka daina mana irin wannan wasan sai ka dauki haqqinmu”ta fusgi kalaman da qyar,sau ya dago kai ya dubeta
“Bama yiwa patient wasa cikin abinda ya shafi lalurar da ta kawo su,ki baki yarda bane hajiya,ai muna da na’urar daukan hoto bismillah ga gado can hau in nuna miki” kasa tashi tayi baki daya,ga rashin qwarin jiki ga luguden da maganar tayi mata,mukhtar dake son tabbatar da gaskiyar labarin shi ya taimaka mata har suka isa bakin gadon.

Cikin qwarewa ya shiga nuna masu dan qaramin tayin dake cikinta wanda duka baifi wata biyu da rabi ba,basu iya ganewa amma sun lura da wani dan digo wanda shike alamta yaronsu kenan,wata doguwar ajiyar zuciya ya saki tare da lumshe ido yana jinsa cikin wata sabuwar duniyar,yayin da sumayyan ta fashe da kuka,jikinta baki daya rawa yake,ashe tana daga cikin mata masu haihuwa?,ashe akwai rabon zata ga yaron kanta?,ashe ita ma din watan watarana zata zama uwa?,zata yi raino ta kuma bada tarbiyya?,lallai ubangiji babu wanda ya kaishi iyawa cikin mulki da kyauta,babu ko shakka ubangiji baya bacci,baya mantawa da duk wanda ya ambaceshi ya kuma nemi agajinsa.

Barinsu likitan yayi suka gama murnarsu,don ya fahimci dukkansu ba’a cikin hayyacinsu suke ba sannan ya sanarwa mukhtar din jikin sumayyan ba qwari,zasu riqeta su sanya mata drip(ruwa)har zuwa safiya ko zata ji karsashi,sannan ya rubuta magungunan da zatayi amfani da su wadanda zasu taimaka mata ita da abinda ke cikinta,sannan ya jadda masa alfanun cina abinci mai kyau da gina jiki da qara kuzari a gareta,karba yayi saida ya tabbatar an gama komai an sanya mata drip din sannan ya fita siyo magungunan.

Ya jima zaune cikin mota ya kasa tayar da ita,ina zaikai wannan kayan farincikin?,da wa ya kamata ya raba wannan farincikin kada ya masa yawa ya masa illa?,da sauri ya zaro wayarsa daga aljihu ya soma daddanna wasu lambobi kyakkyawan murmushi kwance a kan fuskarsa,jinsa yake cikin wata duniya mai dauke dimbin farincikin da ya jima bai jishi ba,jinsa yau yake wani na daban.

****      *****     ****

Ji take idan ga zauna gu d’aya tamkar wani mummunan abu zai faru ne tare da ita,tana jin qwaqwalwarta ko zuciyarta daya daga ciki zai iya tarwatsewa,tunda take bata taba cin karo da mummunan labari da ya firgita duniyarta ba irin wannan labarin,idanunta basu taba mummunan gani ba irin na wadan nan kwanakin,sumayya kishiyarta da ciki?,ita kuwa tana me?,wanne shirme take?,wanne baccin asarar tayi har mukhtar ya yiwa sumayya ciki duk da uban takatsantsan din da take?,duk da raba tsakaninsu da tayi ya daina sha’awarta?,tabbas idan har ta bari sumayyan ta rigata haihuwa cikin gidan ta dibga babbar asara,hakazalika bata ci sunanta,gidan da take da buri a cikinsa,gidan da take so shi da mamallakin gidan duka su zama qarqashin ikonta shine wata zata riga ta fara ajjiye iri?,tun yanzu ta fara ganin manya manyan sauye sauye ina ga ta haihu?,tun yanzun mukhtar ya ruguza dukkan wani plan data yi cikin gidan,wani kukawa yake bawa sumayyan wanda hakan ke nuni da qiris ya rage sun koma su dinke kamar daa koma sufi daa dinkewa,abinda idan har ya faru ba zata taba gafartawa kanta ba,lallai ko zatayi yawo tsirara sai ta tabbatar ta kawar da duk wata barazana dake shirin tunkaro ta.

Kamar mahaukaciya haka ta suri wayarta ta soma laluben lambar wayar aminiyarta qawarta,wadda bata aiwatar da komai sai da shawarat,zama tayi dabas gefan gadonta jin wayar ta shiga,cikin qananun sakanni mamallakiyar lambar ta daga,ko ta kan gaisuwar da take jefo mata bata bi ba ta soma zayyano mata abinda ke gudana cikin gidan.

Tsawon minti talatin ta dauka kan layin wayar suna qulla saqa a mugun zare,sosai taji dadi da shawarar data baga,shi yasa bata da kamarta,shawara ce mai sauqi wadda babu zuwa gun boka ko malami,hakanan babu barnar kudi,amma fa buqata zata biya,don dama babbar matsalarta yanzun duka jarinta ya karye warwas,saboda ribar da uwar kudin duka sun tafi gun ‘yan tsubbu,bata kwana arba’in bata je an mata service ba,tun tana tsoron hadisin data taba tsintar wasu yaran ‘yan makarantar islamiya na karantawa na cewa duk wanda yaje gun boka ko dan duba,to sallarsa ta kwana arba’in Allah bazai karbeta har tazo ta dake tama manta da hadisin baki daya bare ta tunoshi ya zame mata birki. (daya daga cikin abinda Allah ke jarabtar masu biye biyen malamai kenan,basu taba tara abun hannunsu,kullum suna kan hanyar rabawa matsubbata da ‘yan duba,ko kishiya gareki mai irin wannan biye biyen ki lura da kyau,duk abinda miji zai baku sai ki nemi nata ki rasa,kullum cikin babu da bani bani take,ba zaki taba ganin burbushin abun ba ko a dakinta ko a jikinta ko a jikin yaranta,Allah ka kiyashemu ka tsare mana imaninmu).

Tana kammala wayar ta saki murmushi ita daya take magana da kanta
“Kissa ai tafi magani,ba shakka quruciyarki ta yimin rana,zan amfana da ita sosai” ta fada tana ficewa a dakin inda kai tsaye ta nufi dakin sumayya.

Tana kwance saman carfet din dakin nata tayi matashin kai da pillow,duk da ba yadda mukhtar baiyi ta dora kan nata saman cinyansa ba amma ta qiya,yana zaune dirshan gabanta da faranti a tsakiyarsu wanda ke dauke da kankana da tuffa da gwanda,ayaba yake bare mata yana miqa mata tana daga kashingide take amsa tana ci,dubansa take kawai cike da mamaki,yana son dawo mata mukhtar dinta,”Allah yasa ba yaudara bace,ya Allah kasa kada ya juyan baya”haka ta dinga fada cikin ranta tana binsa da kallo wanda shi sam bai ma kula ba,hannu ta sanya ta shafi cikinta wansa daga can qasa ta fara jin dan tudu kadan,lumshe idonta tayi tana jin qauna cakude da farinciki na ratsata,duk kwanan duniya takan shafa cikin sau babu adadi,wani lokaci takan tsaya gaban madubi ta dage rigarta tayita kallon fatar cikinta tana mamaki yau ita ke dauke da juna biyu,idanu ya zuba mata shima yana kallonta farinciki na bibiyar duk wara gaba ta jikinsa,a haka ta bude idanunta karaf cikin nashi,sai kunya taso kamata,murmushi yayi sannan yace
“Bakiyi laifi ba sumayya ki qaunaceshi yadda ya kamata,wallahi Allah a duniya ban taba jin son wani abu a rayuwata ba kamar yadda nakejin son cikin dake jikinki ba,zan iya rasa komai sabida shi,zan iya rabuwa da komai saboda shi,don Allah ki kularmin da kanki da abinda ke cikinki komai runtsi” ko bai fadi ba tasan zancan daga zuciyarsa kai tsaye yake fitowa,ita kanta bata san irin son da takewa cikin ba,kai ta sunkuyar tana murmushi tare da furta
“In sha Allah ya mukhtar”.

Dukkan wannan maganganun cikin kunnen zainab suka yisu wadda ta sawo kai don shigowa dakin
” ka nunawa kucciya baka”ta fada sannan ta shigo dakin da sallama tana sake sai saita nutsuwarta,gaban sumayya ya fadi har sai data runtse ido cikin zuciyarta tana fadin
“Allahummakh finihim bima shi’ita(Allah ka isar min da su da abinda kaso)(addu’a ce mai kyau ga wanda yaji tsoron zaluncin wasu mutane)” murmushi taje jifarsu da shi wanda shi kansa mukhtar din sai da yayi mamaki
“Ashe kana gun uwar gidanmu my mukhtar” ta fada tana zama kusa da shi,amsa mata yayi sannan ta dora
“Gwara ai ka kular mana da ita sosai musamman da take dauke da cikar muradinmu,Allah mun gode maka daka nuna mana wannan lokaci” ta fada tana maida hankalinta ga sumayya,hannunta tasa ta riqe nata hannun,ji take kamar ta kama garwashin wuta amma sai ta dake
“Sannu sumayya ya jikin naki?” Da qyar ta bude labbanta tace
“Da sauqi”
“Allah ya inganta ya qara miki lafiya kinji,na godewa Allah da zaki samarwa mukhtar sanyin idaniya,naji dadi qwarai dama ke ya cancanta ki fara samun wannan matsayin,don Allah duk abinda kike da buqata ki sanarmin kada kice zaki yiwa kanki wani abu,kada ki duba duka wasu abubuwa da suka faru a baya,sharrin shaidan ne da kuma zuciya wadda bata da qashi,in sha Allah ba zasu sake faruwa ba,sai yanzu na fahimci kyakkyawar zuciya da kuma haqurin da kike da shi,don Allah mu hada kai mu zauna lafiya kinji?” Duk da bata gama gamsuwa ba amma taji dadin maganganun zainab din,ko babu komai wake son tashin hankali?,ai babu abinda yafi zaman lafiya dadi
“Ba komai maman nafi’u,Allah ya sake hada kanmu”
“Ba amin ba,don wallahi da kai na ya hadu da na kishiya gwara na qare rayuwata kan nawa na ciwo” ta fada a zuciyarta,amma afili sai ta saki murmushi tana fadin amin.

Sake matsowa tayi ta karbi bare ayabar daga hannun mukhtar din,ita ta dinga barewa sumayyan tana miqa mata,tanayi can qasan zuciyarta na mata suya,amma fuskarta kuwa murmushi da kulawa ne kwance a cikinsu.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE