KUNDIN KADDARATA CHAPTER 30 BY HUGUMA
Kulawa ta musammanzainab ke bawa sumayya wadda zata kwantar da hankalin dukkan wani mai zargi,ta hanata komai,babu abinda sumayyan keyi cikin gidan banda wanke goma ta tsoma biyar,hatta da ruwan wanka ita ke dafa mata ta ajjiye mata a bandaki,girki kowa saidai kawai taci kuma mukhtar ya kwana dakinta,sau tari zainab din kan yafewa sumayya kwananta a zuwan yaje su kwana tare tafi samun kulawa,ta dauke dukka ayyukan gidan bisa wuyanta,ita kadai tasan me take ji cikin zuciyarta,wani lokaci zuciya kan raya mata ta shaqe sumayyan kawai ta mutu ta huta da ganinta da ganin abinda ke cikinta,saidai mardiyya qawarta kan yawaita ja mata kunne da cewa,matuqar ba zatayi haquri ba to kuwa ba zata cimma nasara ba,hakan shike yawaita taka mata burki tana jira har zuwa lokacin da zata kammala qudirinta.
Qwarai mukhtar na jin dadin yadda take kula da sumayyan,yana yaba mata sosai,hankalinsa ya kwanta,duk da cewa har ya zuwa yanzu akwai tasirin ragowar sihirinta a jikinsa,a duniya yanzu babu abinda yake so irin cikin jikin sumayyan,shi yasa hakan da takeyi yake sake saka farinta a idonsa,shi din ma ba’a barshi a baya,hidima da tattali yake mata kan jiki kan qarfi,duk da sai data masa tutsun abinda ya dinga mata a baya,saidai abun mamaki yaje bashi,ya sanar mata sam baisan sadda hakan ta dinga faruwa ba,kallon ya raina mata hankali ta dinga masa,hakan da ya lura da shi ya sanya ya karbi lefin kawai ya kuma bata haquri.
Ita din ma sumayyan ba’a barta a baya ba wajen tattalin kanta da abinda ke cikinta,duk wani abu da tasan zaya kawo tarnaqi ga lafiyar cikinta tana kauce masa,har yau bata bar mamaki ba wai itace yau da ciki bayan shekaru kusan takwas cikin na tara da aurenta,bayan da ta riga ta debe haso?,lallai rabon kwado baya taba hawa saka ko ya hau din ma rabi zaya sauko da shi,babu ranar da zata fito ta fadi bata godewa ubangiji ba.
Mama mahaufiyarta kuwa kullum cikin kiranta a waya take da turowa a duba mata ita,duk sanda zata aiko da abinda zata kawo mata na kayan qwalama na masu ciki,ita kanta yaya yahanasu da taji labarin laqwas jikinta yayi,sai ta rasa me take ciki farinciki ko baqinciki,amma jikinta yayi sanyi ta kuma taya mukhtar din murna,saidai har yau bata je ta ganta ba,tanq gudun wulaqancin da zata taras a gun zainab,don ta yanka musu gargadi kan zuwa gidan duk sadda suka ga dama.
*………KAYAN KWALABA*
_MAFARI_
Zaune yake gefan gadon dakinsa yana sanya maballan rigarsa a shirin sa na fita kasuwa. Ahankali zainab ra bude qofar dakin ta turo ta a hankali kamar wadda qwai ya fashewa a ciki,kujerar madubu ta janyo ta zauna tana fuskantar mukhtar idanunta a kansa,shi ya soma magana
“Lafiya dai ko?,na lura tun jiya jikinki a sanyaye yake,mu da muke cikin farinciki a kwanakin nan”
“Kake cikin farinciki dai,kuma na kusa datse igiyar farincikin”. A zahiri sai ta soma goge qwalla da ta fara sakkowa a idanunta tana kallon mukhtar din
” mukhtar,wannan farincikin da muka samu idan bamuyi wasa ba yana gab da qwacewa daga cikin gidan nan,bansan me yasa take ta qoqarin aikata haka ba,bansan me yake damunta ba”barin sanya takalman da yake qoqarin yi yayi,ya dago ya dubeta idanunsa cike fal da tambaya,har ya gaza boye hakan sai da ya furta
“Kamar yaya fa?,me yake faruwa ne?” Kai ta shiga girgizawa cike kirsa
“A’ah mukhtar,barin maganar nan shi yafi alkhairi,don bansan ya zaka dauketa ba”
“Idan kina tunanin wani abu ne da zai cutar da ni qauna ce ki boyemin kiqi gayan,gaya min zainab” dan shiru tayi a zahiri fuskarta dauke da tashin hankali,yayin da zuciyarta ke cike fal da murna da farinciki tare da fata da addu’ar samu nasara tamkar wata wadda zata aikata abun arziqi,bata kuma magana ba har sai da mukhtar din ya jaddada sake tambayarta,taba goge qwalla tace
“Mukhtar,sumayya ce……sumayya ce naji tana magana da wata baquwa da tayi,bansanta ba,ina tunani ko qawarta ce ko qanwarta ko ‘yar uwarsu,wai wallahi sam batayi farinciki da samuwar wannan ciki ba,ina ita ina haihuwa bayan ko shekara ashirim baga gama rufawa ba,dama ita can kawai nunawa take tana son haihuwa amma wlh sam bata qaunarta,bare wai ta lura ba wani kulawa take samu yanzu daga gareka ba,tunda kwanakin baya ka juya mata baya yanzu haka data haihu qila ka sake komawa halayyarka,yanzu haka maganar da nake maka har ta bata shawarar ta sha maganin da zai barar da cikin kawai ta huta”.
Tamkar guduma zainab ta sanya ta daki qahon zuciyarsa haka yaji,take maganar da yaya yahansu ta ta sha gaya masa shekarun baya suka bijiro mada suka cakudu da wannan sabon batun
” kai idan zaka farka gwara ka farka,matarka fa ba son haihuwa take ba,bata ma sha’awarta,tunda kuke ka taba gani ta sha wani magani don ta haihu ko ta taba maka maganar kuje asibiti a dubaku?,ina kyautata zatan ma ita tasha maganin da zata hana kanta haihuwa,banda haka yarinyar dake da quruciya mai zai hanata haihuwa a irin wannan lokacin?”. Wani fushi da bacin rai mai tsanani ya sauko masa,sai kawai ya miqe,burinsa kawai yaje ya samu sumayya yanzun nan,da sauri ta riqeshi don ba yanzu take da muradin nakiyar ta fashe ba
” a’ah mukhtar ina kuma zaka?”
“Sakeni zainab,sakeni naje na sameta” wani mugun marairaicewa tayi sannan tace
“Shi yasa fa naqi gaya maka tun jiyan,yanzu me zakaje ka yiwa yarinyar mutane kana cikin fushi haka?,idan baka iya kama barawo ba sai shi barawo ya kamaka,zauna muyi magana akwai mafita” babu musu ya koma ya zauna yana maida numfashi
“Mukhtar,kada ka damu,ni mai qaunarka,ina son abinda kake so,idan baka manta ba nike kulawa da sumayya…to kada ka damu,zan sanya ido sosai a kanta,sannan zan hana duk wani abu faruwa har Allah yasa ta haihu lafiya na maka alqawari” hakanan yaji kalamanta sun kwanta masa a rai,sai ya sauke ajiyar zuciya
“Na gode zainab,don Allah na roqeki ki kula da ita,a duniya yanzu babu abinda nakeso sama da cikin nan don Allah” wani shegen kishi ya takore mata,cabdi,a haka zata bari sumayya ta fara haihuwa,ai ba zaya yiwu ba,a fili tace masa
“Na maka alqawari tare ma zamu dinga wuni insha Allahu kada ka damu” jikinsa a sanyaye ya gama shirin zuciyarsa na bugawa,mamaki da haushin sumayya ne fal cikin zuciyarsa,da kamar ya wuce abinsa ba tare da ya mata sallama ba zainab din ce ta tursasashi kan sai ya shiga din,koda ya shiga sumayyan sai taga yanayinsa ya sauya sosai,ba kamar yadda ya saba mata ba,gabanta ne ya dinga faduwa tana fatan ba halayensa na baya bane zasu dawo,don ko kusa bata da buqatar wannan yanayin.
Har ya juya zai fita sai ya sake waiwayowa ya dubeta
“Ki kularmin da cikina,din bazan iya jurewa ko yafiya gareki ba ga duk wani abun qi da zaya samu cikin nan ba” dai ya juya ya fita,kanta ne ya daure sosai,me yake nufi kenan,ta jima tana qoqarin lalubo amsar,daga qarshe abinda qwaqwalwarta ta bata shine tsabar son cikin da mukhtar din keyi ne haka ta barwa ranta taci gaba da sabgoginta.
**** **** ****
Bata gushe ba tana ci gaba da cusawa mukhtar tunani kala kala kan zub da ciki sumayya ke qoqarin yi,amma ta nuna masa tana bala’in takatsantsan akan faruwar hakan,sosai ya shiga damuwa da tashin hankali,mamakin sumayyan yake yi,da ya matsanta kan sai ya mata magana yana son daukar mataki,bazai iya jura ba idan wani abun ya samu cikin sai ta masa alqawarin zata nuna masa da idanunsa zai gani saboda hukunci da hujja yafi.
*KUNDIN QADDARA*
*_BAQAR RANA_*
Tun da safe ta hada mata shayi kamar yadda ta sabarwa kanta,duka yana cikin qudurinta da tsarinta. Ranar kusan da wuri mukhtar ya fita,tana kwancan har ya fita din ko abin kari ma bata masa ba saboda mugun qudirinta data qulla aiwatarwa a yau din nan ko farkawa bata nuna tayi ba,hakan ya sanya data shiga da shayin ta zauna tana jan sumayyan da hira,bata bar dakin ba sai data tabbata ta kammala shan shayin,sannu a hankali ta soma hamma,zainab din ta dubeta fuskarta qunshe da murmushi wanda ke dauke da manufofi uku,manufar cimma nasara da manufar mugunta,sai kuma dadi daya kamata saboda tafuskanci magungunanta zasu soma aiki lokaci guda yadda take so
“Kwanta ki huta qanwata na fuskanci kamar bacci kike ji”
“Wallahi kuwa,duk jikina ya mutu” ta fada tana jan pillow ya yada kai saboda nauyi da taji kanta ya soma yi sakamakon bacci mai nuyi daya lullube idanunta. Leqa fuskarta tayi ta tabbata ta soma baccin sannan ta sake sakin murmushi,a nutse ta nufi drower din gefan gadon sumayyan ta fiddo magungunan da suke soke cikin rigar mamanta,magunguna ne har saches uku dukka na zub da ciki ne,saches daya aka balla guda gudu wanda ita tayi amfani da shi ta zubawa sumayyan cikin ruwan shayin data kammala sha yanzu,sai wata ‘yar qalamar kwalba da wani saches din wanda duka maganin dake bugarwa ne da saka bacci wanda yawanci ‘yan shaye shaye aka sani suna ta’ammali da shi. Dorasu duka tayi kan drower din sannan ta fice.
Kitchen ta shiga ta samo kofi cikin kayan sumayyan ta zuba ruwa ta dawo kusa da magungunan ta ajjuye,ta bude kwabar kayanta ta ciro hijabi ta ajjiye saman kanta sannam ta nufi ma’ajiyar takalmanta ta ciro ta sanya mata daya daga ciki a qafafunta,sai data qare mata kallo ta tabbatar komai ya kammala sannan ta saki dariya ta fice zuwa dakinta.
Tazarar mintina goma ta bada kamar yadda aka ce mata magungunan zasu fara aiki amma maganin baccin zai sa ba zasu tashi aikinsu gadan gadan ba sai bayan minti ashirin,dakin ta sake nufa ta leqata sai ta tarar har yanzu baccin take amma tana motsawa akai a kai,jinjina kai tayi ta sake komawa dakinta.
Kai tsaye ta dauki wayarta ta laluba lambar mukhtar,bugu uku ya daga tare da yin sallama,bata bi ta kan amsawa ba ta soma magana cikin yanayi na matuqar rudewa qwarai da gaske
“Wayyo Allah mukhtar mun shiga uku,mukhtar na kasa riqe amanar da ka bani” cikin wani mugun tashin hankali ya miqe tsaye daga inda yake zaune sannan ya fara tambayarta
“Lafiya zainab yi magana mene ne?”
“Kasan ka barni a daki ina kwance ina bacci,to ina tashi naga lokaci ya ja,sai na tuna sumayya na barta bata ci komai ba,da sauri na shiga kitchen na hada mata abun kari na nufi dakinta,ina shiga naga babu kowa na duba gidan baki daya ban ganta ba,ina falo ina taraddi ina ma shirin kiran wayarka ko kasam zata fita?,kawai sai gata ta dawo dauke da wata baqar leda ita da wannan ‘yar uwar tata,da nayi mata magana ma kallon banza ta yimin tayi tsaki ta wuce daki,sai ma qyaleta sabida nasan masu ciki da fushi,sai daga baya na sake leqata sai na tarar tana shan wani magani,na mata zancan abinci tace ta qoshi bata buqata taci a waje,na qyaleta na dawo ina hidimar gida,bayan wajen minti talatin sai na fara jiyo ihunta tana wayyo cikina wayyo bayana inzo in taimaketa” sai ta fashe da kuka kamar gaske,ya gaji da dogon jawabi kawai jira yake azo gurin
“Ki gayan me ya faru?”
“Jini ma gani daga jikinta mukhtar yana fita wanda ke nuna kamar bari tayi”
“Me!” Ya fada da madaukakin sauti,kafin ta kai ga amsawar ta soma jiyo kumar sumayyan na kiran sunata,dadi ya kamata komai yazo a daidai kenan?,sai ta sake dububurcewa
“Tana kirana mukhtar don Allah kayi sauri kazo mu kaita asibiti kada mu rasa cikin nan” sai ta katse kiran kawai cikin gaggawa ta nufi dakin sumayya.
Murququsu ta cimmata tana yi da malelekuwa daga saman gadon har qasan carfet din dakin,tun daga kan gadon jini ne har qasan dakin,wata azaba ke ratsata ilahirin jikinta,duk da azabar da takeji bai hana hankalinta tashi ba,tasha jin ana cewa zubar jini hadari ne gun mace mai ciki tun daga shigar ciki zuwa haihuwarsa,tsoro fal da fargaba ke zaga zuciyarta,tsoron rasa cikin jikinta,tsorom rasa gudan jininta
“Ki taimaka kin don Allah amarya kada na rasa baby na” ta fada hawaye da gumi na hade mata saboda tsabar azabar radadin da mararta ke mata,ga tarin mamakinta sai taga zainab din ta sheqe da dariya
“Kadan kika gani,ci gaba da karbar gashin ciwon rasa d’a kafin ki rasa mijinki ma baki daya,nice sila ba zan iya taimaka miki da komai ba,burina nake so ya cika” sai ta sake takowa zuwa gabanta ta ranqwafo
“An fada miki akwai ranar da kishiya zata so kishiyarta ne?,an gaya miki ni sauna ce da zan dinga miki bauta?ko an fada miki wawiya ce ni bansan me nake ba?,lallai dukkan wanda ya riga ka kwana tilas ya rigaka tashi,wannan ya isheki ishara game da kaidin kishiya,ke yarinyace,bakisan komai ba sumayya,daga yau zaki shaidi kaidin kishiya” ta fada tana juyawa ta fice ta barta a dakin tare da komawa falo tayi zamanta.
Runtse idanunta tayi wani abu na dawafi kan qwaqwalwarta,babu shakka ayanzun maganganun da zainab ta furta mata sunfi mata ciwo fiye da ciwon dake nuqurqusarta,tana nufin ita ta mata silar abinda ke faruwa yanzun da ita?,me ta aikatama zainab din haka mai muni da zata zama silar rabata da abinda ta jima tana dakon isowarta gareta?,don kawai sun hada miji?,saboda kawai suna qarqashin inuwa daya?WANNAN ITACE KAWAI HUJJAR?dafe mararta tayi tana ci gaba da kallon yadda jini ke kwaranya yanabin qafafunta tare da bin lafiyar carfet dinta.
Tana jin qarar tsaiwar motarsa ta miqe da hanzari ta shige dakin sumayyan,kanta tsaye ta nufi kan drower din ta kwaso magungunan dake ajjiye a kai ta riqe a hannunta tana kallon sumayyan taba murmushi sannan tace
“Yanzu zaki ga babban kaidina don na tabbatar bakisan da zaman wadan nan magungunan ba,baki ta saki tana kallonta tare da jijjuya kai cike da azaba,ko magana ma ta kasa yi,sai da taji takun shigowarsa yana qwala musu kira ta saki kuka tana jujjuyasu tare da matso hawaye tana fadin
“Me yasa kika aikata haka sumayya?,me yasa zaki raba shi da farincikinsa?,abinda ya jima yana nema sumayya shine yau zaki zama silar rabashi da shi,ina ma ni Allah ya bawa sumayya kin cika butulu ta gaske,wayyo Allah yau mun rasa yaronmu”sai ta rushe da kuka,wani duka zantukanta suka yiwa dodon kunneta,sai ta daga kai tana duban baki qofa saboda ganin inuwar mutum,take idanunta suka sauka cikin na mukhtar wanda ke dauke da tsantsar bala’in da bata taba katarin ganinsa cikin idanun nashi ba,tsaf mukhtar yaji duka abinda zainab din ke fada,yi tayi kamar bata ganshi ba taci gaba da cewa
” yanzu har da maganin ‘yan shaye shaye sumayya da tarbiyyarki da komai……
“Kasa ci gaba da daukar batun kunnuwanta sukayi,dummmm taji sunyi mata,a hankali ta soma jin jiri na kwasarta tana daga zaune,cikin ‘yan sakanni wani duhu ya mamaye idanunta ta daina gani ta daina ji.
**** ***** *****
Sannu a hankali ta soma yunqurin bude idanunta har taci nasara ta kammala budesu baki daya,idanunta suja sauka kan ruwan dake rataye yana shiga jikinta sannu a hankali,take abinda ya faru da ita ya dawo mata tar,tayi hanzarin fadin
” la’ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin”bakinta ya furta
“Hmmmm,kamar gaske” muryarsa ta daki dodon kunnuwanta,da sauri ta waiga ta dubi bangaren da sautin ke fitowa,mukhtar ne tsaye hannayensa nannade a qirjinsa,duba daya zaka yi masa ka fuskanci a yamutse yake,har yanzu idanunsa jajur suke tamkar an badesu da barkono,kafin tace wani abu ya tako zuwa gaban gadon da take. Babu shakka da zata iya da tashi zata yi ta arta ana kare saboda yadda kamanninsa suka sauya baki daya kamar wani mayunwacin zaki
“Sumayya,ban taba zaton soyayya zata juye ta koma qiyayya ba sai yau,babu shakka kin cuce ni kin zalunceni,kuma Allah ya isa tsakanina dake,don bazan taba iya yafe miki ba,na zauna da ke tsawon shekaru ina kare martaba da mutuncinki,ina tattalin farincikinki ashe ni nawa kike rusawa,meye aibuna da bakison ki haihu da ni?,me yasa baki gaya min ba tun wuri nayi nesa da rayuwarki?,a yau na tsaneki tsanar da ban taba yiwa wata halitta makamanciyar irinta ba,na gani da idona ba gaya min akayi ba”zuciyarta na mata wata iriyar muguwar suya ta bude baki don kare kanta duk da rashin qwarin gwiwar da take da ita,sai ya watsa mata magungunan da kuma sakamakon gwajin da ka yi mata na dalilin barinta wanda ya nuna maganin zub da ciki ta sha
“Allah ya saka min sumayya na dora buri kanki amma kin zalunceni” abun mamaki kawai saiga hawaye na fita a idonsa,abinda bata taba tsammanin ganin ba agreshi
“Zan bar rayuwarki kije kiyi duk yadda kika ga dama da ita,KIJE NA SAKEKI SAKI UKU don bazan tab iya ci gaba da rayuwa da ke ba” wani tashin hankali ya rikito mata,sai ta ware baki daya idanunta tana son tabbatar da gaskiyar lamarin,ko dai barin da tayi ya shafi awaqwalwarta da jinta?.
“Haba my dear wannan danyan hukunci haka?,ai yayi tsauri” ta fada tana isowa gareshi cike da kisisina
*Dakata da Allah!”ya katseta cikin kakkausar murya,gabanta yayi mugun bugawa saboda ta tuno da sharadin da malam ya gindaya mata nacewa kada ta kuskura tace komai har a qare lamarin,saboda ba qaramin so yakewa cikin ba hakanan har yau duk da daurin da aka yiwa zuciyarsa da sanya masa ganin baqin sumayya har yau sonta na da sauran tasiri cikin zuciyarsa,itadai kawai ta sanya layarta cikin bakinta tayita taunawa,jajayen idanunsa da suka firgitata ya zuba mata
“Tunda sumayya ta iya yimin haka a rayuwa,to babu macen da zan aura ta kasa aikata min haka,saboda haka kema kije na sakeki saki uku!”
“Iyeee!” Ta fada cikin madaukakiyar murya fitsari na kubcr mata take ya fara bin qafarta saboda azabar rudewa,kai ya sanya ya fice daga dakin,wanda kammala fita su mama(babar sumayya) suka sanyo kai da alama dama suna cikin asibitin.