KUNDIN KADDARATA CHAPTER 31 BY HUGUMA
Zainab qanwarta ce akan gaba,sai mama da yaya abubakar halima na biye da shi,umma sadiya qanwar babansu na biye da su
“Yaya sannu yanzu muka ga ya mukhtar din ma ai ya fita” ta fada ba tare da sun ankara baki daya da yanayinda take ciki ba,haka ma basu lura da zainab dake tsaye gefe ba tana tsuma tare da kallon fitsarin da ya gama wanke mata qafafu. Kallo daya mamanta ta yi mata ta fuskanci ba dai dai taje ba duk da cewa akwai ciwo tattare da ita.
Da idanu kawai take binsu tana fata ta farka daga mummunan mafarkin da takeyi,sai da maman ta qarasa gefan gadon ta zauna ta soma yi mata sannu sannan sumayya ta tabbatarwa kanta idanuntq biyu,a zahiri komai ke faruwa,wata cukuikuya ta yiwa maman nata tana sauke wata ajiyar zuciya tare da fadin
“Ya sakeni mama,ya rabu da ni bayan bani da wani laifi”,cikin rudani suke kallonta duk suna zaton zafin ciwo ne
“Sumayya zafin ciwo ne duka hakan?” Sai ta fashe da wani kuka mai azabar cin rai tana maimaita fadin
“Walllahi mama ya sakeni,yanzun nan da kuka ganshi ya fita sakina yayi mama” salati suka saka baki daya wanda ya dawo da zainab hayyacinta
“Allah ya isa ‘yarku ta jawo min masifa,ta jawo min zawarci kashi na biyu garin qoqarin zubar da cikinta” ta fada tana wucewa fuuuu ta bar dakin.
Shiru ya ratsa dakin,babu wani abu dake tashi sai shashsheqar kukan sumayya wanda zainab da halima ke tayata saboda tsantsar tausayin ‘yar uwarsy,yayin da zuciyoyin sauran ke quna,zancan zainab kuma ke musu kai kawo
“Mama har saki uku yaya mukhtar ya yimin,mama wallahi ban aikata ba,na fishi son naga na haihu mama ki…….” Sai ta fara jan numfashi da qyar wanda hakan ya sanya su sake rudewa,da sauri yaya abubakar ya nufi reception don kiran nurse ko likita,cin qanqanin lokaci sai gashi tare da likita wanda yake gab da tashi Allah yasa bai fita ba,waje ya fid dasu baki daya sannan ya rufe dakin,take suka rude da koke koke cike da tashin hankali.
Kusan mintina talatin sannan likitan ya fito bayan ya gama dubata ya mata allurar bacci tare da sanya mata wani ruwan,ya sanar musu bata buqatar hayaniya,sannan don Allah su guji tada mata hankali idan baso suke ta hadu da hawan jini ba,don ko a yanzun jini nata ya fara sama,bugu da qari kuma ta zubda jini mai yawa,godiya suka yi masa sannan suka koma dakin kowa ya samu gu ya zauna zugum,dukkansu da abinda suke saqawa zukatansu,daga bisani yaya abubakar ya fice dan yi musu siyesiyen abubuwan da zasu buqata kafin suga yadda hali zaiyi.
Tun a hanya take sumbatu,ko da wasa bata taba zaton ramin da ta haqa zai rufta da ita ba,bata taba ganin masifa irin wannan ba,taga samu taga rashi,gidan da takewa kanta hasashen samun abun duniya yau dare daya an rabata da shi
“Ina!!!,wlh sam bazai yiwu ba,mukhtar ko baka qaunar Allah sai ka ci gaba da zama da ni,babu wanda zan sanarwa ma ka yimin saki uku,wallahi yanzu na fara aurenka” maganar da tayi kenan wadda ta sanya mai adaidaitam juyowa ya dubeta,banda kayan jikinta da basu nuna alamun akwai hauka tattare da ita ba da babu abinda zai hana yace mahaukaciya ce,a qofar gidansu ya sauketa ya juya ya kama gabansa.
Tunda ya bar asibitin gida ya wuce kansa tsaye tamkar wani mahaukacu,kuka yake wiwi da haka ya kashe motarsa qofar gidan ba tare da ya samu qwarin gwiwar tura dan matsakaicin get din ba bare ya iya shiga da ita,dakinsa ya wuce ya fada saman gado yana dafe da kansa,me yasa sumayya zata yi masa haka?,wanne abu ya mata da zata saka masa da wannan?,zata rabashi da gudan jininsa,sata rabashi da burin rayuwarsa,shin ta manta cewa samun d’a shine CUKAR BURINSU shi da ita?,wani kukan ya sake saki kamar qaramin yaro,sai a lokacin ya fara ambaton sunayen Allah daya bayan daya,sannu a hanakali nutsuwa ta fara saukar masa,yabar tumurmusa gadon da yake yayi luf saman gadom cikin yanayin na kwanciyar rub da ciki idanunsa na ci gaba da fidsa qwalla masu zafi.
**** ***** *****
Kwana daya rak amma sunfi kwanaki dubu ciwo da wahala a rayuwarta,baki daya ta sauya kamar ba sumayya ba,tayi wani mugun dashewa wanda ya sanya nurses suka soma tunanin tana buqatar qarin jini ko babu jini jikinta,da likita ya duba sai yaga magungunan qarin jini ma kadai sun isheta sai maida kai gun cin abin mai lafiya.
Ko kallon abincin bata yi bare ta kai ga ci,ko ruwa bata iya kurba a bakinta,ki da yaushe tana kwance idanunta rufe kamar mutum mutumi,sai da malam yazo shi daya ya shiga dakin sukayi magana ta tsawon mintina kusan ashirin shi da ita sannan aka fara samun salama,takan karbi duk abinda aka bata taci koda zata yi amansa,hakan ba um ba um um sai zubda hawaye tamkar qwayar idonta zai tsiyaye,kusan kowa tausaya mata yake tare da girgiza da al’amarin,duk da cewa har yau malam kawai ta iya yiwa bayanin abinda ya faru shi kuma ya sanar da abubakar da umma sadiya,sosai umma sadiyan ta fusata qwarai tace sam ba zasu yarda ba tilas su maka mukhtar a kotu shi da zainab din baki daya,baisan halin sumayyan bane?,yarinyar da kusan shi ya qarasa yi mata tarbiyya,malam ne ya hana yace sam hakan baida amfani,tunda koda sun aikata hakan ba zasu iya maida hannun agogo baya ba,ba zasu iya gyara lamarin ba tunda abinda zai faru ya riga da ya farun,da wannan zancan suka rufe batun suka maida hankali wajen kula da lafiyar sumayyan.
Da wani yammaci sumayyan na zaune jingine da bango,bata jima da yin wanka ba tana sanye da atamfa,mamanta ne da zaina da halima sai khadija da hajara cousing dinta zauneba dakin suna dan taba hirarsu,sallama akayi suka kalli bakin qofar baki daya suna amsawa,haj salamatu ce wato umma mahaifiyar abdur rahman ita da qanwarsa bahijja,duk da quncin da zuciyarta ke ciki saida sumayyan ta washe haqora ta sake gyara zama tana mata sannu da zuwa.
Cikin mutuntawa suka gaisa su halima suka gaidata tare da miqewa suka fice don zuwa karbo canjin ruwan da suka siya cikin shagon asibitin a dazu
“Sannu sumayya ya jiki?,ya kuma mukaji da wannan abu” umma ta fadi fuskarta dauke da alhini da tsantsar tausayi,qasa tayi da kanta hawaye na zirarar mata
“Alhamdulillahi umm” ta fada muryarta a karye
“Ki yi haquri kan haquri sumayya,duk da na sanki dama ke gwanar haqurin ce,haqiqa Allah ba azzalumin sarki bane,ni sam bansan meke faruwa ba,abdur rahman da bahijja dai sunje zasu miki sallama da yake zai sake koma wa jami’atu ummul quraa zai hado masters dinsa,to da suka dawo sai suka ce sun tadda gidan naku a kulle,babu wanda ya kawo komai don har mukhtar din ya kira ya masa sallama baice da shi komai ba,sai jiya da safe saiga mukhtar din yazo gaida kawun nasa,a nan yake gaya masa duk abinda ya faru,wallahi mama ina jin batun na tabbatar sharrin kishiya ne da asiri ke dawainiya da yaron,cikin kwana uku tal da faruwar lamarin kada kiso kiga yadda ya fige ya lalace,babban abun haushin ma duk yadda muka so tunatar da shi wace sumayyan wallahi yaqi fuskanta yaqi gane wacece ita,har yau da haushi da zargin abun a ransa,amma babu komai mai gaskiya yana tare da Allah,kuma in sha Allahu Allah zai miki KYAKKYAWAN SAKAMAKO”.
” babu komai ai umma,kowanne bawa da irin tasa QADDARAR,kuma shi aure rai ne da shi,da zarar zaman ya qare sai kiga ko babu sanadi an rabu”.hawaye ne kawai ke ci gaba da tsiyaya idanun sumayya,tamkar ta zura a guje haka take ji,bata qaunar jin duk wani zance da ya danganci mukhtar din,tunda mukhtar ya yi mata haka a duniya yaqi bata dukkan yarda da amincinsa bayan yasan wace ita to babu wanda bazai iya cin zarafinta ya ha’inceta ya wulaqanta ta ba.
Maganganu masu sanyi umma ta dinga fada mata masu kwantar da rai wadanda suka sauke kaso mai yawa na bacin rai baqinciki da firgicin da take ciki,sosai taji sukuni cikin zuciyarta,sai wajejan la’asar sannan umma ta musu sallama ta tafi bayan ta ajjiyewa sumayyan dubu uku tace tasha lemo.
**** ***** ****
Cikin kwana biyar jikinta yayi sauqi sosai,hakan ya sanya likita ya bata sallama tare da gargadarta ta rage damuwa ta kuma kula da lafiyarta.
Sosai take samun kulawa daga dukkan wani da yake cikin gidan nasu,kowa haba haba yake da ita,dakinta daban wannan karon malam yasa aka ware mata don kada su takura mata,amma duk da hakan wani lokaci cikinsu haliman take kwana,ganin yadda kowa ke son farincikinta ya sanyata warewa,tayi qoqari qwarai wajen fidda damuwa daga ranta duk don saboda su,duk da abadini hakan ba mai yiwuwa bane gareta.
Watanta guda da komawa yayanta abubakar ya siya kata foam na wata makarantar koyon sana’o’in hannu na mata don rage mata kewa da dauke kaso mafi tsoka a cikin lokacinta wanda hakan zai taka rawa matuqa da gaske wajen hanata tunani ko damuwa,kama daga dinkin labulaye,zannuwan gado,suturu kayan sawa,carfet zuwa saqa,hadin su humra,sabulu,man shafawa man kitso da sauransu dukka suna koyawa,sosai take jin dadin makarantar hakanan ta maifa hankalinta sosai tana dauke duk wani abu da aka koya mata,har ya zuwa lokacin ba’a debo kayanta daga gidan mukhtar ba din baki daya ta tsane su ta tsani ganinsu,hakan ya sanya umna halima tace idan an tashi daukosun a wuce da su gun masu saida furniture a siyar kawai.
*ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA*
Kusan a yanzu ya zame mata al’adarta,takan kwashi lokaci mai tsawo kwance cikin nazarin da tunani kafin bacci ya samu nasarar daukarta.
Yauma kamar kullum tana kwance ruf da ciki,duk da cewa dakin babu hasken fitila amma idanunta a bude suke tar,kwanyarta na aikin sarrafa tunane tunanen dake bijiro mata daya bayan daya.
Zumbur ta miqe sakamakon motsin da take ji can qasan mararta,wanda wannan shine karo na barkatai da take jin hakan cikin wannan satin,sau tari takanyi kasaqe tana sauraran motsin har zuwa sanda zai lafa mata,hakan ce ta faru wannan karon,bayan motsin ya lafa sai ta koma ta kwanta rigingine tana mai lumshe idanunta,tana tunanin gobe zata sanarwa mama don tana zaton ba lafiya saboda bata taba jin irin hakan ba.
Qarfe takwas na safe tana tsakar gidan tana shara bayan ta kammala duk wani aiki na gidan qannanta sun wuce islamiyya wadda suke shiga tara zuwa biyat da rabi na yamma,tunda tazo ta koma al’adarta ta da,tun kafin tayi aure ita ke hidimar gidan duk da qarancin shekarunta a lokacin,sai abinda yafi qarfinta ne kawai wanda ba zata iya ba take barma maman nata shi,to hakan ce ta kasance wannan karon,duk da maman na hanata kai bama ita ba har su haliman idan suna nan basa yarda tayi komai,amma takan qiya saboda hakan na matuqar debe mata kewa da sata jin qwarin jikinta.
Tana daga rumfarta zaune amma tana iya hango duk abinda ke faruwa cikin tsakar gidan kasancewar labulen falon a dage yake don ta samu iska ta shiga inda take,da idanu take bin duk wani motsi na sumayyar da kallo,tausayi da qaunar yarinyar tata na ratsata,sai kima wasu sauye sauye da take ci gaba da gani dangane da ita,har sai da ta kammala komai sannan ta shigo falon
“Wash” ta fada wanda hakan ya sanya maman juyawa ta kalleta
“Lafiya dai ko?”
“Lafiya lau,kawai gajiya nake ji da kasala mama” shiru ta danyi sannan ta sake dubanta,tunani ne fal cikin zuciyarta amma bata aminta da abinda zuciyarta ke kawo mata ba don bata jin hakan zai yiwu
“Bakijin komai a jikinki sai kasalar kawai?” Dan shiru tayi sannam tace
“Ummmm,wani lokaci inajin motsi mama har nace zan gaya miki ko zanje asibiti,sai kuma naji motsin ne kawai baya ko ciwo cikin nawa” ta fada cike da quruciya dake nuni da rashin sanin abinda ke faruwa da ita
“Tun wajen yaushe kike jin hakan?” Ta tambayeta tana dubanta da saka ran jin amsa
“Eh wajen kwana goma kenan”
“Lallai kuwa ya kamata mu koma asibiti” maman ta fada tana jinjina kai cikin qarafafawa wanda hakan ya bawa sumayyan tsoro,take hantar cikinta ya kada,kodai wani babban ciwo ke shirin samunta?,gaza yin shiru tayi saboda tsabar tsoro
“Mama!……bani da lafiya ko?” Ta fada kamar zata saki kuka,murmushi ta saki don kwantar mata da hanakali,bugu da qari itama bata da tabbas din abinda take zato kansa
“Lafiya lau kike,dauko min wayata na kira malam in sanar da shi idan yaso sa muje kiga likitan”
“To” ta fada jikinta a sanyaye qirjinta na bugawa duk da maman tace mata lafiyarta lau,dakin gadon maman ta shiga ta fiddo wayar ta dawo ta miqa mata sannan ta samu gefe ta koma ta zauna.