KUNDIN KADDARATA CHAPTER 32 BY HUGUMA

Cikin abinda duka bai wuce awanni biyu ba isar su asibitin da shiga dakin ganin likitan,umartar ta yayi da tahau wani dan gado wanda kusa da shi na’urar daukar hoton ciki ne.

“Allahu akhbar” shine abinda likitan ke fadi yana jinjina kai tare da girmama iko na ubangiji,yaro ne kwance cikin mahaifarta ga motsi nan yana yi ga bugun zuciyarsa da komai,dukkansu ba wanda idonsa bai gani ba daga sumayya har mama,mamaki fal zukatansu tare da girmama lamarin buwayi gagara misali,sai da ya kammala komai har EDD sai da ya duba mata sannan yace ta sauko ya koma kan tebur dinsa ya soma rubuce rubuce.

Magunguna ya rubuta mata wadanda zasu qara mata lafiya sannan ya bata wasu gwaje gwaje da ya kamata ace a wannam stage din da cikin ke da watanni hudu da sati uku tayi su
“Likita lafiyarsa qalau”furucin ya subuce ya fita daga bakinta jikinta a sanyaye,murmushi yayi yana dubanta
” lafiya qalau komai yake,babu wata damuwa tattare da shi”sai da ya bata amsar sannan kunya ta kamata ta sadda kai qasa,batasan cewa tana bala’in qaunar abinda ke cikin nata ba sai yanzu,wani qwarin gwiwa karsashi da soyayya take ji cikin ruhinta,banu shakka wannan karon tanajin zata iya yaqi kan cikinta a shirye take.

Basu bar asibitin ba sai da suka kammala duk wani gwaji suka siyi magungunan suka nufi gida.

Har yanzun maman ta kasa cewa komai kamar yada sumayya ta kasa magana,sam basuyi zato ba,basu tsammaci akwai sauran ciki jikin sumayyan ba,ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA ko ana muzuru ana shaho sai yayi kenan. Hakanan sumayyan ke jin zuciyarta fes da ita,bini bini ta saki murmushi tare da shafa cikin nata,maman na ankare da ita,tausayinta ya dinga ratsata,haqiqa babu dan halak din da zai guji haihuwa,babu wata halitta da bazato ganin jininta ba,dole dan adam ya koka idan ya rasa baya wato ‘ya’ya,abu ne mai ciwo da cin zukata,Allah kuma maji roqo da addu’ar bayinsa ne,a yau gashi duk yadda akaso rabata da rabon da Allah ta bata amma hakan bai yiwu ba,ya riga ya QADDARA yana cikin QADDARARTA haihuwarsa da dadi ba dadi,saboda hikimarsa sai ya bawa yaron kulawa ta musamman,ya boyeshi daga kallon idanuwa,ta yadda ko mahaifiyarsa bata san da zamansa ba sai yanzu da buwayin sarki yaso ta sanin.

Tun daga sanda suka koma gida daga asibitin maman ta fara bata kulawa ta musamman,ta hanata yin komai komai qanqantaraa,duk da babu wani ciwo ko laulayi da sumayyan keji,lafiya qalau take jin jikinta. Malam na dawowa maman ta sanar masa,sosai shima ya jinjina lamarin yana qara girmama isa da buwaya ta ubangiji,to ita kanta sumayyan ma alokacin ba’a zaci zata kai ba bare d’an dake cikinta
“Yanzu ya zama dole a sanarwa uban yaron saboda yasan da zaman cikin” inji mama.
“Wannan ya zama dole ai,zan sanya abubakar yayimin kiransa ko zuwa gobe ne” cewar malam.

****      ****    ****

Kansa na duqe amma gumi tsatstsafo masa yake har ta kafar farcensa,babu shakka baya ga girman tsohon da yake gani da kuma farin sani da yayi masa kan wane shi da tashin farko zai qaryata batun da a yanzun yake gaya masa.
“Amma ga wadan nan ka duba hoton cikin ne da aka yi mata a jiya,idan ma duka basu gamsar ba kana iya zuwa gobe sai kuje da ita da su halima wani asibitin a sake gwada maka har da watannin cikin” malam ya fadi yana zube takaddun scanning da komai da komai a gabansa,jikinsa na rawa ya dauka ya soma dubawa,tsaf daya lissafa watannin cikin zuwa yanzu dai dai suke,sau taji wani abu na zaga shi,madaukakin farinciki ya wadatu a zuciyarsa
“Na gode maka ya Allah da baka bata damar salwantar min da ciki ba” ya fada cikin zuciyarsa idanunsa a lumshe,duk da zuwa yanzu yana mamakin me yasa ta aikata masa haka?,zuciyarsa kuma na kokwanton ita din ce da kanta?,wani sashi na zuciyarsa kan gaya masa ita dince mana,tunda kaga shaidu na magungunan cikin dakinta,kuma a baya likita ya tabbatar da ta sha din.

Sallamarta ita ta katse dogon nazarin da yake,sanye take da dogon hijabi har qasa mai hannu wanda idan zata shigo wajen malam din haka take sanyashi,din yanzu baki daya irin wannan shigar tafi mata armashi,duk da dama yana daya daga cikin dressing dinta tun a da,sam bata ma san da zuwansa ba,tazo ne karbar rubutun da malam din yace mata zata dinga sha daga tsakanin magariba zuwa isha’i,gefe ta samu kusa da malam din ta zauna har ya zuwa yanzu bata luta da mukhtar din ba dake satan kallonta,abu biyu yake ji dangane da ita,haushin yunqurin zub da masa ciki da kuma qaunar jininsa da take dauke da shi.

“Ka duba su da kyau gasunan” inji malam,wanda maganar da yayi ce ta ja hankalin sumayyan ta lura da mukhtar din,da sauri ta dauke kanta bayan sun hada idanu,qasa qasa tace
“Ina yini” kamar wadda aka tilasta ta fada,tasan dole ne ma ta gaidashi saboda malam dake gun
“Lafiya qalau,ya jiki naki”
“Alhamdulilla” ta fada da qyar tana jan tsaki cikin zuciyarta tare da fadin
“Me ya shafeshi da jiki na ji da nake mai laifi”
“Malam rubutun nazo karba” ta fada a hanzarce don so take ta bar falon ba zata juri zama cikinsa ba
“duba gefan akwatincan ki dauko min farar gorar can” ya fada yana nuna mata,ta miqe ta isa gun yayin da idanun mukhtar din ke kanta,baki daya yanayinta ya nuna mace mai ciki ce,cikin ma da ya soma qwari.

Cikin wata silver mai dauke da rubutun yasin da ayatul kursiyyu ya fara zuba rubutun ya bata ta shanye sannan ya dura mata wani cikin jarka ya miqa mata,a hanzarce ta karba ta fice a dakin.

Kasa tsaiwa tayi a falonsu sai data dire zuwa dakinta ta ajjiye rubutun gefe ta zauna saman gado dafe da kanta,kuka ne ya kubce mata wanda ba zata iya fadar dalilin sa ba,sosai ta koka sai data ji sanyi cikin ranta sannan ta rarrashi kanta.

Cikin kunya da nuyin da ada bai jisu ba sai yanzu suke saukar masa ya dubi malam bayan sun gama tattauna abinda zasu tattauna din
“Malam ina son jin abinda ake da buqata wanda zatabyi amfani da shi” kai malam din ya gyada yana nazarinsa,duk ya fara qarewa kamar wani kudin guzuri,addu’a yake masa cikin zuciyarsa Allah ya yae masa abinda ke damunsa
“Babu wani abu da muke sa buqata,yadda sumayya take diyata kaima d’a na nae,tunda ko babu komai alaqa ta sake qulluwa darajar abinda take dauke dashi” nauyinsa ya sake kamakashi,ya sadda kai qasa
“Na sani malam,amma ka fini sanin haqqina ne yanzu in ci da ita har ta haife abinda take dauke da shi,don Allah a fadamin na sauke haqqin da ya rataye a wuya na” dan shiru malam din yayi sai daga bisani ta numfasa
“Shikenan,kaje ka kawo duk abinda kasan zaka iya”
Kanshi a qasa ya masa godiya sosai,karamcinsa na sake daureshi,yadda malam din ke mu’amalantarsa kamar ba wanda ya sakar masa diya ba,sakin ma kuma mai kankat.

Cikin mota jikinsa yayi sanyi baki daya,da qyar yake iya tuqi,a yau ji yake ina ma bai saki sumayya ba duk har yanzun akwai haushi da zargin yunqurin zubar masa da ciki da tayi,mai yasa baiyi haquri ba ko ya dauki mataki wanda bai zama na rabuwa ba,a lokacin baisan me ya sanya yaji rabuwa da ita ne kawai maslaha a rayuwarsa ba tunda har bata da buqatar hada zuriya da shi
“Ke kika jawo sumayya,me yasa?,me yasa kika aikata abinda ya zama silar datse alaqarmu?” Haka ya dinga fada yana tafe yana tambayar kansa.

Tamkar wanda qwai ya fashewa a ciki haka ya faka motar sannan ya rufeta ya nufi cikin gidan,sosai yayi mamakin ganin qofar falon a bude sabanin dazun da take a kulle,sai yayi zaton ko ‘yan uwan zainab sunzo kwasar kaya bayan fitarsa a gidan saboda har yau sunqi kwashe kayanta
“Sannu da zuwa my mukhtar” yaji muryar zainab na ambata,da sauri ya maida idomsa inda yake jiyo muryat,zainab din ce ta qure ado sanye sa wata matsiyaciyar doguwar riga wadda ta bayyana suffarta baki daya,fari take masa tana sake takowa kusa da shi,da sauri ya daka mata tsawa
“Ke wacce iriyar maca ce,wato da na hanaki bina kasuwa shine kika sauya salon biyoni gida,to ina gargadinki wallahi ki gaggauta ficewa daga gidan nan don gamuwarmu ba zata yi kyau ba,don na tsani kowacce mace tunda sumayya ta ha’ince ni taso cutata ba don Allah ya riga ya rubuta mai taka doron qasa bane” maganar sa ta qarshe ita ta girgizata,idan har tayi dogon nazari da tsinkaye yana son ce mata cikin sumayya yana nan zata haifeshi nan gaba?yana nufin ita ta tashi banu riba?,ita tayi biyu babu ko daya?,bata samu sukunin tambayarsa ba ya daka mata wata tsawa wadda ta dawo da ita hayyacinta ta soma dubansa tana kada kai
“Wallahi bazanyi biyu babu ba mukhtar,kana nufin taci riba?” Sam tunaninsa bai kai ga fassara maganarta ba,burinsa guda kawai ta fice masa a gida a yanzun kadaici yake da buqata,ganin zata bata masa lokaci ya sanyashi fincikar hannunta ya watsa ta waje,sannan ya dawo ya yibi mayafinta da jakarta ya wurga mata har kan fuskarta ya kulle gidan. Dawowa yayi ya zube saman kujera yana maida numfashi zuciyarsa na ci gaba da tuhumar sumayya,ta zamo silar yankewar duk wani jin dadi nasa,wayarsa ce ta soma takura masa da ruri ya dagata ya duban sunan mai kiran,yaya yahanasu ce,baya da buqatar qarin matsala akan wadda yake ciki,saboda haka ya kashe wayar baki daya ya ajjiye
“Wallahi ban tafi kenan ba zan dawo,na dinga bibiyar rayuwarka kenan saboda ni da kai kadai zan rayu” ya jiyi zainab na aiko masa da maganar daga inda take,tsaki ya ja don ya fara daukarta a matsayin mai matsalar qwaqwalwa

****    ****    ****    ****

Siyayyar dukkan wani abun buqatuwa ga sumayyan shine abu na farko da ya soma yi a safiyar washegerin ranar,kai hatta da man goge baki bai rage ba cikin siyayyarsa,sannan ya dora kudi dubu goma akai.

Sanda kayan suka iso gidan tashi tayi ta bar wajen ma baki daya ta koma daki,yadda bata da buqatarsu haka bata da buqatar ganinsu,kuka ne sosai ya kubce mata,har yanzu mamakin mukhtar take da har ya iya amincewa da ta aikata mummunan laifi irin wannan,ba wannan take buqata ba,baki daya mukhtar ya gaka rushe duk wani tanadi na raino da suka ciwa yaran da zasu haifa buri,itakam mai yayi saura,ba gwara ya qyaleta ba baki daya tasan cewa ta rasashi har abada?,dukkan wata kulawa a yanzun da zai nuna babu wani zaqi da zata mata ballantana ta burgeta.

Tun daga lokacin ya zamto duka qarshen wata zai mata siyayyar dukkan wani abu,tun daga na ci zuwa na buqata,duk da malam na hana wasu abubuwan amma sam bai yarda ba,yana jin haqqi ne a kansa kuma nauyi ne da ya rataya wuyansa ya kula da ita saboda yaronshi da take dauke da shi.

Kusan duk zuwansa yakan tsaya ne daga sori,su gaisa da mama da sauran yaran ya bada saqon ya juya,baki daya gashi nan dai a tafe ne,amma sam babu wani abu dake faranta masa illa idan ya tuna ya kusa daukan ‘yarsa ko dansa.

Ta bangaren yaya yahansu kuwa sanda taji labarin sakin,sosai na zainab ya faranta mata,sai a lokacin ta dinga tuna abinda zainab din ra dinga yi musu,ta tabbatar har su ta hada ta asirce shi ya sanya suka gaza tabuka komai,jikinta kuma yayi sanyi da sakin sumayya,ita kanta ta dunga tunanin anya abinda mukhtar ya gaya mata ya faru ba tuggun zainab din bane?,tilas ta bar batun tunda abinda ake gudu ya riga da ya faru,amma lokacin da ya sake dawo mata da batun cikin na nan wani farinciki taji ya mamayeta,tana da muradin zuwa taga sumayyan amman kunya ta hanata,tana ganin kowa yasan gallazawar sa ta yiwa sumayya,da wanne ido ‘yan uwanta zasu dubeta?,sai a yanzun take sake tausayin dan uwan nata ganin yadda ya sauya kamar ba muntarinsu ba.

****      ******    *****

Hakanan yau ya tashi da muradin ganin cikinsa,amma ya kasa tantance cikin yake son gani ko sumayyar duk da zuciyarsa tafi afuwa ga cikin yake son gani,don rabonsa da ganinta tun randa malam ya gaya masa zancan cikin na nan a falonsa.

Saura kusan kwanaki bakwai lokacin da yake mata siyayyar ya cika,amma duk da haka da yammacin ranar ya shiga store din da ya saba siyayyar,shugaban gurin na ganinsa ya san me dame yake buqata,shi ya sanya aka hada masa komai sannan akayi total ya biya ya karba ya fice.

Qarfe biyar a qofar gidan tayi masa,yana sanye da wani yadi mai qarancin kauri ruwan bula mai haske wanda aka yiwa aiki da ruwan bula mai turuwa,duk da sauyawar yanayinsa da rama amma hakan bai hanashi kyau ba,sam rayuwar gidan bata masa dadi saboda a yanzun shikewa kansa komai,hakan ya sanya ya nemi wani saurayi wanda ke zuwa ya masa share share.

Halima ce ta soma ganinsa,ta yiwa mamansu magana aka bashi izini ya shiga,duk da yaran yanzun basa sakewa da shi kamar da,hakan baya masa dadi sam don baiga abinda su ya shiga tsakaninsu ba.

Cikin girmamawa ya gaida maman ta tambayeshi su yahanasun ya amsa mata duk lafiya qalau shi kuma ya tambayi masu jiki(wato sumayya),ba wata hira dama tun da can ke shiga tsakaninsu ba daya wuce gaisuwar,hakan ne ya sanyashi ya miqe bayan an gama shigo da kayan ya musu sallama ya fice.

Sai ya kasa tafiya ya tsaya a soron,yana da muradin ganin cikinsa gashi ko gilmawarta bai gani ba bare yaji muryarta,hakan babu wanda ya masa zancanta,jingina yayi da bangon soron hannunsa harde a qirjinsa yana tunanin ta yadda zai ganta din,cikin ikon Allah sai ga zainab ta fito tana sanya hijabinta zata shagon kusa da gidansu ta karbo klien zata wanke kwanukan da suka kammala abincin dare da su
“Yauwa zainab,don Allah taimaka min ki fito min da yayarki mu gaisa” ya fada yana gyara tsaiwarsa,mamaki ya cikata,kamar tace wani abun kuma sai ta fasa ta juya ta koma ciki.

A dakin sumayyan ta tarad da maman tsaye kanta tana mata fadan rashin fitowa su gaisa da mukhtar,tundanko banza dai ai uban d’anta ne,abinda ya faru kuma babu wanda ya ruga ya gogeshi cikin KUNDIN QADARARTA,hawaye ta soma gogewa abinda maman bata so kenan
“Amma mama meye amfanin fitar tawa mu gaisa,tunda dai lafiya qalau nake”
“Na san da wannan,ko banza ai ko baya ta taki zai so ya tabbatar da lafiyar abinda ke cikinki ko” maman ta fadi
“Shikenan kiyi haquri mama zan dinga gasheshi” tausayinta ya kamata,tana shirin yin magana zainab din ta shigo ta fada mata abinda mukhtar din ya buqata
“Kin gani ai,sai kije ku gaisa” ta fada ta juya tana ficewa,hajibinta ta janyi dake rataye jikin sif ta zura sannan tayo waje.

Tunda ta fito ya zuba mata ido yake kallonta,sosai wannan karon cikin ya fito fiye da waccan karon,hatta tafiyarta ta soma sauyawa,kanta ma qasa din bata son hada ido da shi har ta qaraso,daga can gefe guda ta tsaya sannan tace
“Ina yini” ba tare data daga kai ta dubeshi ba
“Lafiya lau,ya jikin naki”
“Alhamdulillah” ta fada cikin sanyi,sai shiru ya biyo baya kowa da abinda ke saqawa cikin zuciyarsa,tsaiwar ta fara mata tsauri har ya lura da haka,sai ya waiwaya ya gangaro mata wani dutse da suke tokare qofa da shi ya furta
“Ga guri zauna” bata musa ba ta zauna din don tana da buqatar hakan
“Me yasa sumayya?,why?,kinga ayanzun kin zama silar da zamu raini yaronmu a mabanbanta gurare abinda ko a mafarki ban taba hasashen faruwarsa ba”ya furta wani daci na zagaya harshensa,idanuwansa na sauya launi,da sauri ta daga kai ta watsa masa fararen idanuwanta,take wani bacin rai ya soma bijiro mata,wato har yanzun zarginta yake kenan?,dama abinda yake son gaya mata kenan da har ya fiddo ta tana zaman zamanta tana lallaba rayuwarta.

Qin tankawa tayi sai ma yunqurin miqewa da ta soma yi saboda bata ga alfanun ci gaba da tsaiwa a gabansa ba,ganin tana niyyar wucewa ba tare da ya gaya mata abinda zaya fadi ba yace
” idan nayi lissafi dai dai cikin ya kusa shiga wata na tara,zuwa yanzu ya kamata ace anyi siyayya,ki rubuta duk abinda kike da buqata jibi zan dawo na karba in sha Allah”
“Ka kawo duk abinda kake ganin zaka iya” ta fada tana mai shigewa gidan ba tare da ko ta waiwayoshi ba zuciyarta na suya,idanunta na zafi.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE