KUNDIN KADDARATA CHAPTER 35 BY HUGUMA

A makare ya tashi yau wanda hakan ya sabba ba masa yin sallar asubahi cikin gida,tunda ya idar da sallar yake zaune saman daddumar bai tashi ba kamar yadda bai aiwatar da komai ba,tunanin sumayya ne fal zuciyarsa yau ya wayi gari da shi,hakanan yake jin wunin yau ba zai iya qarewa ba ba tare da yaje ya ganta da lafiyar abinda ke cikinta ba,kusan tunda ta shiga watan haihuwarta da ita yaje kwana yake tashi.

Qarar wayarsa ce ta katse masa hanzari,ya juya bangaren da take ya jawota ya duba,baquwar lamba ce,ya latsa sannan ya kara a kunnensa,runtse idanunsa yayi zuciyarsa ta soma quna saboda muryar wadda yaji,bai taba jin ya tsani wani abu tsana mai tsanani ba irin na mamallakiyar muryar,zainab ce take magana cikin maqale murya da wani irin salo nason tafiyar da hankali,tun a daren jiya bokanta wanda take kira da malam ya bata wannan sa’ar ya kuma tabbatar mata bayan sallar asubahi ne zata sameshi,sanda ya daga wayar zuciyarta sai ta cika da farincikin samun nasara,don dama ya sanar mata bayan sallar asubar a gobe bazai koma bacci ba,jin tana ta magana ya mata shiru ya sanya ta fashewa da wani makirin kuka
“Habaa my mukhtar,dama laifin wani kan iya shafar wani?,mene laifina ni a ciki?,duk iya yina nayi don inga abinda ke cikin yarinyar nan ya kubuta,duk tarin hidima dana dinga yi da ita rana daya duk ka mance ka watsar da alkhairi na a gareku ka sakeni,kuma ma tunda an samu cikin na nan ba shikenan ba komai ya wuce sai ka maidani daki na ko?”.
Kamar garwashin wuta haka yaji kalaman nata,cikin harzuqa ya dakatar da ita
” ke wacce iriyar jahila ce wai?,shin kin manta zama ni dake a yanzu ya haramta ne sau nawa zan nana ta miki,ke koda kuwa ma zamanmu ya halatta bazan iya zama da kowacce mace ba a yanzu,tunda sumayya da na raina da kaina ta iya min haka babu wata diya mace da ba zata iya aikata min makamancin haka koma fiye da shi ba,saboda haka gargadina dake na qarshe,kada ki sake gigin kiran layi na ko tarar hanyar da kika san zan bi,idan kuma kinqi ji ba zaki qi gani ba”daga haka ya katse kiran ya ajjiye wayar a fusace.

Daga daya bangaren nata itama ajjiye wayar tayi tana huci sannan ta dubi qawar tata
“Wannan wanne irin mutum ne haka?,duk zama da wuyar da muka sha wajen malam ta tashi kenan a banza,kinji maganganun banzan da yake gaya min?,to wallahi wannan karon babban aikin zan saka a masa koda duniya zata zageni,ko zanyi yawo babu zanin daurawa” kafada ta daga tana fadin
“Au ho sai yanzu kika gane kenan?,tuntuni ai malam din ya gaya miki ki saki naira kiga aikin da ko uwarsa dake kabari ba zai ganta a gabansa ba sai ke” miqewa tayi ta fice daga dakin fuuu tana fadin
“Ai anzo gurin kuma”.

A hasale ya kuma waiwayowa ga wayar tasa jin ta sake tsuwwa a karo na biyu yana zaton ita din ce ta sake kiransa,sai jikinsa yayi sanyi gabansa ya fara faduwa ganin sunan abubakar kan screen din,cikin sanyi da sallama ya amsa wayar,lumshe idanuwa yayi wata rahama na sauka cikin zuciyarsa lokacin da abubakar ke furta masa albishir mafi dadi da ya taba sauraro tsawon rayuwarsa,sumayya ta haihu ta haifa masa yaro,baisan adadin lokacin da ya dauka ba cikin duniyar madaukakin farinciki shidai ya farka yaga har kiran na abubakar ya katse.

Faduwa yayi saman a bin sallar yayi sujudush shukur yana mai tasbihi ga ubangiji,bai wani jinkiri ba ya miqe ya fada makewayi ya shiga wanka,cikin mintina talatin ya fito,kai tsaye gaban sif dinsa ya isa bayan ya tsane jikinsa,ya bude yana kallon kayan,a sanyaye ya sauke hannayensa yana duban kayan kala bakwai da suke sababbi dukkansu,ba zai manta randa ya bada dinkinsu ba,tun cikin sumayya na da wata uku a lokacin tana gidan,musamman ya tanadesu ya dinkasu saboda ya sanyasu tun daga rana ta farko da aka haifa masa yaronsa har ranar suna,baya iya manta lokacin da take dariya tana tsokanarsa da cewa gandoki,sai ya koma bakin gadon ya zauna yana yarfa hannu,yana jin yadda bacin rai ke taso masa yana son danne farincikin da yake ciki,baisan mai yasa har yau zuciyarsa ta kasa daina jin ciwon abinda tayi masa ba duk da cewa an cimma nasarar tsallakewar cikin gashi har yau Allah ya nufa ya iso duniya.

Da qyar ya samu ya hadiye wani dunqulen abu mai daci sannan ya miqe ya shirya cikin wani yadi mai kyau na maza fari sol wanda ya masa kyau sosai,ko abinda zai sawa cikinsa bai nema ba ya fito don dama ba ko yaushe yake samun damar karyawar safe ba,yana shirin tada motarsa ya kira ya yahansu ya shaida mata,hamdala ta dinga yi matiqa da gaske tana jin dadi a zuciyarta,ta kuma shaida masa lalle ya biyo gidan nata kafin ya wuce.

Kafin sha daya na safe tuni gidan ya cika da jama’a ‘yan uwa da abokan arzuqi,kowa barka yake mata tare da tayata farincikin wannan rana da aka jima ana saka ran zuwanta,sam ita bata san me ake ba ma,bacci take sosai ita daya a dakinsu,yaron shima nashi baccin yake,sai da ya farka ya fara kuka alamar yunwa sannan mama ta baro dakinta wanda suke zaune da mutane ta shigo dakin ta tasheta,sai data sake hada mata shayi mai kauri ta sake sha sannan ta dora mata shi saman cinyarta ta fara koya mata yadda zata shayar da shi,runtse tayi sannan ta fara qorafin zafi maman tace
“A haka zaki daure har ki saba”.

Sallamar da kunnuwanta ya jiyo shi ya sanya jikinta saki,sai ta zubawa bakin qofar dakin ido tare da barin qorafin da takeyi,halima ce ta shigo
” mama ga yaya mukhtar”
“To ya shigo mana” ta fada tana gyara mayafin jikinta,qasa sumayya tayi da kanta tana duban yaron dake saman cinyarta yana tsotsar nono a hankali,sallama yayi cikin dakin sannan ya qaraso a nutse hannunsa dauke da qatuwar baqar leda,baki daya idonsa na kan sumayya da yaron wadanda kowannensu yake jin mabanbantan yanayi a kansa cikin zuciyarsa,wata qauna ta musamman yaji ta dirar masa tun kafin yayi tozali da gudan jinin nasa,yayin da tausayi da kuma wata daraja ta sumayya ta daban yaji ta ginu a ransa,a mutunce suka gaisa da maman sannan ta miqe ta fice,shiru ya ratsa dakin bayan ficewar tata,shi yana zaune yana aukin kallonsu ya rasa daga inda zaya fara,yayin da itama taqi motsin kirki dukkan idanunta na kan yaron nata tana dubansa,tana jin yadda yake zuqar mama har cikin ranta,ci gaba yayi da dubansu wani yanayi na ratsashi,sai suka burgeshi sosai,karo na farko da yaji zai iya yafewa sumayyan kome tayi masa,yana ji a yanzu ta cancanci yafiyarsa.

Cikin qwarin gwiwa da karsashi yayi gyaran murya tare da muskutawa yace
“Sannu sumayya”ta dan cije lebe kadan sannan ta amsa can qasa
” yauwa”
“Sannu da qoqari,Allah ya saka miki da alkhairi,na yafe miki sumayyan duk wani abu da kika yimin” da sauri ta daga kai ta dubeshi sannan ta kau da kai
“Bana buqatar yafiyarka tunda ni din ban aikata maka ko wanne laifi ba,hasalima ni nafi cancanta da a nemi yafiya ta” mamaki kalaman nata suka bashi,bai kai ga furta komai ba mama ta sake shigowa hannunta dauke da kofi cike da kunun kanwa yana tururi
“A’ah,baki bashi shi ya ganshi ba,ki cire shi haka idan ya gama ganinsa yaci gaba da sha ko” ta fada tana dire kofin tare da ficewa.

Bata kammala ficewar ba ya taso da kuzarinsa ya qaraso gabanta sanda ta cire maman daga bakinsa tana gyara masa rufa,ya miqo hannunsa ta dora masa shi saman hannun nasa tana fadin
“Ga abdallah nan”sai ya cira kai ya dubeta,tabbas suna ne mai kyau da asali,ko shi din ma sunan yayi masa,baice komai ba ya koma da baya ya zauna inda ya tashin yana kallon yaron,baisan fuskarsa ta wadata da murmushi ba,baisan hawaye na bin fuskarsa ba sai da yaga digarsu kan kuncin yaron wanda hakan ya sanya yaron bude idanunsa yana kallonsa,wata qaunar sumayyan ke son dawowa cikin zuciyarsa,ko babu komai koda ta aikata laifin tayi fama da dakon wannan qaton babyn cikin cikinta tsawon watanni tara ta kuma yi naqudarsa ta haife masa,rana da wani matsayi na daban wanda babu diya macen da ta takashi cikin rayuwarsa,ita din ma dubansu take tana daga zaune,wani wawan rauni keson ziyartar zuciyarta,saidai zargin saurin yanke hukunci na mukhtar da rashin bincike ke naushin zuciyarta,sai ta dauke kai daga dubansu tana jin kuka nason qwace mata tana qoqarin maida shi.

Ya jima zaune yana aikin kallon yaron da yi masa addu’a tamkar zai maidashi ciki,sam kamar ma bashi da niyyar tafiya,har sai da aka sake yin baqi sannan ya miqe ya dora mata shi saman cinyarta,ya sunkuya ya sumbace har tana jin hucin numfashinsa wanda hakan ya sanya ta ja da baya,ya dago yana dubanta bayan ya ajjiye ledar da ya shigo da ita a gefanta ya dora kudi a sama
” ga wadan nan ko zakuyi amfani da su,ban yarda a dorawa kowa wani nauyi wanda yake nawa ne,Allah ya qara muku lafiya”ya fada yana juyawa ya fice daga dakin a sanyaye tamkar bai son tafiyar

**** ***** **** ****

Cikin kwanakin hidima aka dinga yi sosai cikin gidan,duk wani dan uwa na jiki ko aboki babu wanda baizo ya tayasu murna ba,mukhtar kuwa kullum qafarsa na gidan babu ranar da bazaizo ganin fuskar Abdallah ba,sau tari saidai sumayyan tasa a miqa masa shi tana daga cikin gida.

Yaya yahanasu tazo a kunyace saidai ita daya don sauran duk sun kasa zuwa,atamfa ta kawowa sumayya turmi biyu sai dan qaramin akwati na qarshen wanda ta cikoshi da kayan baby,ba wanda ya nuna mata komai suka karba suka mata godiya.

Suna akayi na gani na fadan tamkar tana gidanta,hatta anty dije dake abuja ba’a barta abaya ba sai data halarta ita da yaranta baki daya,duk da cewa suna tsaka da zangon karatu amma sai da suka dauki uzuri suka zo,rago da saa mukhtar ya yanka masa,sosai abdallah yaga gata,yaron yazo da farinjini da goshi mai yawa,qauna da soyayya ko ta ina,kowa gwada masa kalar tasa yake yi.

**** ***** *****

Jego take sosai irin na daa shi mama take mata,sosai take gasata ta kuma cikata da cimaka,irinsu romon nama,tuwon dawa kunun kanwa kunun gyada da sauransu,hakanan babu fashin wankan ganye safe da yamma take yinsa har sai data cika kwanaki arba’in harda doriyar kwana biyar,zuwa lokacin ta murje ta dada kyau,idan ka dubeta ba zaka taba cewa ita ta haife abdallah ba,yayin da abdallahn yayi wani irin wayau da qiba dauka da nishi ajjiyewa da nishi,kullum mukhtar na hanyar gajin yaronsa,sau tari yakan bawa mama da malam tausayi yadda baya ko gajiya,duk sanda zaizo hannunsa dauke da wani abu yace na abdallah ne,har da abinda bazai yi masa amfani a yanzu ba saidai ko nan gaba,itakam sumayyan bata ma yarda su hadu bada yaron take ta shige daki,yakan jima yana yiwa yaron wasa tare da jin qaunarsa da kewar mahaifiyarsa cikin zuciyarsa.

**** ***** ***** ****

Rayuwa ta mata kyau saboda ta samu gata yadda ya kamata,cikin watanni uku abdallah ya soma iya zama,wata na biyar rarrafe ya miqa,sosai yaron yake da shiga zuciya da daukan hankali,saboda tsafta da kukawa da yake samu,ko yaushe zaka ganshi tsaf cikin shiga ta gayu kamar wani saurayi,idan manyan kaya ta sanya masa kai kace babban mutum ne,idan kuma qananun kaya ne sai ka dauka saurayi ne,baya rabo da qamshi shi yasa har maqota aikowa suke daukarsa,zuwa wannan lokaci mukhtar wani lokacin yakan zo ya daukeshi ya jima wajensa wani lokaci har kasuwa yake leqawa da shu,tun tana bata rai mama na mata fadan na zata raba da da uba ba har ta saki ranta ta haqura,wata goma ya qware a tafiya sosai,idan ka ganshi sai ka zaci yayi shekara daya da rabi ne.

 

A lokacin yaya abubakar ya sama mata foam na wata makaranta dake koyar sana’o’i,ta zabi ta koyi yadda ake saqa da humra turaren wuta da na kaya da na tsugu no,hankali kwance take zuwa makarantarta ta dawo don bayan layinsu take,abdallah kuwa bai cika rigima ba sai idan yaso,saboda haka a gida take barinsa taje abinta ta dawo,koda ya sa rigima ma zainab ko halima kan daukeshi su kai mata shi,a lokacin ta sake wani kyau da cika,saika rantse da Allah bata taba aure ba balle har ta haifi yaro.

***** ****** ******

Qarfe hudu da mintuna ta iso gida a gajiye,tana sallama abdallahn ya kubce daga hannun zainab dake shafa masa hoda a wuya da alama wanka aka sake masa,riga ce mara hannu a jikinsa sai wando three quater,yayi kyau sosai,da gudunsa ya taho ya tareta yana mata gwalantu wanda ke nuna alamar fara koyon magana,daga shi sama tayi tana juya shi suna qyalqyala dariya sannan ta direshi tana amsa maganar zainab wadda ke mata qorafin yau abdallah ya bata kaya sunfi uku
“Kunfi kusa ai,bake ke kareshi ba idan za’a masa fada” tayi maganar tana qarasawa bakin fanfo don daura alwala tana sake fadin
“Mama fa?,naji gidan shiru” zainab dake tattara kayan kwalliyar abdallah ta amsa mata
“Eh sun fita ita da ya halima gidan maman shafa’atu ganin salima”
“Kice biki ya kusa kenan”
“Wlh saura ‘yan satittika basu wuce uku ba”
“Allah ya sanya alkhairi” ta fada tana gyara daurin dankwalinta ta shige daki donyin sallah abdallah na biye da ita a baya yana mata surutu.

Tana kammala sallar abdallah na saman jikinta yana faman qiriniya da nuqurqusarta taji sallama kamar ta bahijja,kafin ta yunquro taji ana tambayar tana nan zainab ta amsa da eh,bahijjan ce kuwa,hannu bibbiyu ta karbeta sai da suka fara gaisawa ta sanar mata tare da abdur rahman suke yazo ganin abdallah,idanu ta zaro tana dariya
“Iyeee,kice da tare da larabawan madina kuke kada kai ace har an gama karatun?” Cikin murmushi bahijja tace
“A’h,yadai samu hutu ne yace tunda ya shekara bari yazo yaga gida”
“Da kyau…..zainab zoki dauki carfet ki shimfida masa a zaure(soro)”ta fadi tana murmushi tare da qoqarin miqewa.

Tare suka fito da bahijjan saboda abdallahn na hannunta,ji take kamar kada ta ajjiyeshi yaron ya shiga zuciyarta sosai.

Tun kafin ta qarasa soron wani kalar qamshi na daban ya ziyarci hancinta,zaune yake ya hakimce kan carfet din,yana sanye da shadda ruwan siminti sai qyalli take,kansa saye da baqar hula,baki ta riqe tana murmushi,sosai abdur rahman din ya sauya,ya zama wani babban mutum lokaci daya,kai bakace abdur rahman din dake tayata zama bane sanda tana amarya mai qarancin shekarun da basu gaza goma sha uku ba,ya zama mai cikakkiyar kamala da haiba,fatar nan tayi fresh da ita,duk yadda taso ta zolayeshi da tsokana kamar yadda suka saba sai ta kasa sanda shi yake tsokanarta da iyeeem ba,yarinya ta girma gata da yato ta zama mama,bayan sun gama barkwancinsu kasancewarsa mutum mai yawan son barkwanci sannan ya shiga jajanta mata abinda ya faru tun daga samuwar cikin abdallan zuwa haifeshi,suna tattaunawa yana wasa da abdallahn har bahijja ta gaji ta tashi ta koma ciki wajen zainab ta barsu a nan.

Sosai yaron ya masa ya tafi da shi har ya gaza boyewa sai da ya furta,murmushi kawai tayi suka ci gaba da hirarsu a haka mama ta cimmasu,a mutunce suka gaisa tana mamakin ganinsa da sauyawarsa ta tambayeshi mutanan gidan ya amsa duka lafiya ta dubi sumayya
“Amma ai abdur rahman ba baqo bane da zaki barshi a soro,maza tashi ka dawo tsakar gida” cikin tsokana yace
“Atoh mama na sani ko rowar gidan ake min,ni kuma naga gun hira kuwa har na koma,tunda nayi aboki” hararar wasa sumayyan ta masa tana cewa
“Dadinta ai na maka tayi kace a’a tunda mama bata nan nan zaka zauna” ta fada tana shigewa cikin gidan.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE