KUNDIN KADDARATA CHAPTER 36 BY HUGUMA

Har ta idar sallahr isha’i babu abdallah ba mukhtar,sai ta rushe sa kika ganin qarfe takwas na neman gotawa,komawa tayi ta jingina da jikin katifa tana maida numfashi tare da sakin ajiyar zuciya.

Kamar daga sama taji muryar mukhtar din kamar daga can soro suna magana da yaya abubakar,sai ta miqe zumbur ta zauna tana saurare har zuwa sanda abubakar din ya daga labulen qofar dakinta ya leqo
“Kije ki karbi abdallah,wai yau ni zaiwa rashin m yaga babansa yaqi yarda na karboshi” ya qarashe zancan yana sakin labulen,tana ji yana ma mama qorafi tana musu dariya,zumbur ta miqe kamar mai jira,dama tun hijabin da tayi sallah shine a jikinta bata cireshi ba.

A soron ta tadda su tsaye yana rungume da abdallan,tana zuwa ta miqa hannu alamar ya bata shi,banza yayi kamar bai gane me take nufi ba,ya dubeta fuskar nan a dinke tsaf
“Duk randa kika sake gigin fitowa gun bazawarinki da yaro na,idan har na tafi da shi ya tafi kenan har abada” ya qare maganan sannan ya miqa mata shi wanda tuni bacci ya fara dibansa,hannu tasa cikin azaba ta karbeshi,cikin hanzarin ta shige gida kamar wanda zaice mata dawo da shi,binsu yayi da kallo har suka shige,ya jima tsaye cikin soron ba tare da ya iya tafiya na a haka abubakar ya cimmasa sannan sukayi sallama ya tagi,har yanzu bai cimma burinsa na ganin wanda ke zuwa gun sumayyan ba,amma babu shakka ba zai guahe ba har sai ya gano waye.

Dare ya fara miqawa amma tana kwance idanunta biyu,abdallah na jikinta yana ta barcinsa,a haka halima ta daga labulen dakin ta shigo
“Yaya sumayya wani ne keta kira tun dazu yana cewa sumayya yake nema,nace masa ba ita bace amma yace ita ta bashi number din ”
“Wani?” Ta tambaya cikin mamaki,don har ga Allah ta mance shaf da luqman.
“Eh,yace dazu da yamma” sai a lakacin ta tuna da shi,don baki daya abdur rahman ya hargitsa tunaninta,maganar sa ta mata girma,ga mukhtar shima da yaso hautsina ta,kafin tace komai wayar ta sake ruri,haliman ta kalleta
“Yaya gashi,shi ya sake kira” tsaki ta dan ja tana ganin baiken kanta tun farko da bata bashi lambar bogi ba,kanta ta maida kan filo sannan tace
“Kice da shi nayi bacci”
“Amma yaya…..” Haliman taso yin qorafi saboda ba sabonsu bane yin qarya
“Don Allah ki fita ki bani guri ki gaya masa yadda nace din ko kisan me zaki gaya masa” ganin sumayyan ta harzuqa har haka wanda basu saba ganin hakan tattare da ita ba ya sanya ta juya ya fice ba tare data amsa wayar dake ta faman kururuwa ba.

*****     ******    *******

Cikin kwanakin da suka biyo baya gaba daya haka take wuni sukuku,ga maganar abdur rahman dake mata amsa kuwwa a kai,gefe guda kuma ga luqman daya matsanta da kiran waya ba dare ba rana,duk da ko daya bata taba amsa wayarsa ba amma hakan bai sanya ta gajiya ba.

Gani take baki daya abdur rahman ta shigo da maganar ne don ya dagula lissafinta,domin shi kansa yasan yana magana ne kan abinda bashi yiwuwa,ta yaya zata aure shi bayan ta auri dan uwansa?,ta yaya zata yadda ta sake maida kanta cikin ahalin da bata da farinjini ko sau daya a gunsu?,ahalin da tasha wahala tasha jinyar zuciyarta duk a kansu,ahalin da basu ganin alkhairi tattare da ita?,duk a ture ta wannan ma yaushe zata aure musu abdur rahman?,matashin saurayin da ko auren fari baiyi ba?,sam bata jin zata iya wannan abu koda a mafarki ne ballanta na kuma a gaske.

Ranar da ta fara amsa wayarsa suna zaune ne baki dayasu a falon maman suna cin tuwon dare wayar haliman ta sake tsuwwa karo na wajen uku kenan,mama ce da ringing din wayar ya soma damu ta dubi halima
“Wai halima idan ba zaki daga wayar nan ba ki kashe ta mana haba”
“Mama bani ake kira ba yaya ake kira,yau kusan kwana hudu kenan wlh taqi ta daga ko sau daya” sai maman ta juya tana suban aumayya wadda ta cika tayi fam sabida halima ta gayawa maman
“Ke sumayya wake kiranki” cikin murya mai kama da shagwaba wanda sau tari idan ranta na bace bata aon magana haka yanayin muryarta ke komawa tace
“Wani ne nima mama ban sanshi ba”hade rai maman tayi sannan tace
“Ha’aa,baki sanshi ba kamar yaya?,ina cewa ke kika bashi lambar ko?” Dan jim tayi sannan ta gyada kai
“To maza bana son shashanci karbi ki amsa kirab,na gane take takenki sarai,kuma kinfi kowa sani malam ya fara maganar baiga kina magana da wani ba,kinsan halinshi sarai tun da can baya ma shi ba mai barin yara su girme a gabanshi bane,su kansu su halima rashin tsayayye ye ne ya sanya har suke gida iwar haka” gabanta ya fadi fargaba ta lullubeta,wani irin aure kuma?,duka duka mutuwar auren nata da bai wuce shekara biyu ba?,tilas ta karbi wayar ta miqe ta shige daki.

Sun dan dauki lokaci kan wayar yana qoqarin shigar da kansa a gunta,ba yabo ba fallasa ta amsa masa duk wata magana da yayi mata,da qyar ya shawo kanta ta bashi lambarta,yayi murna da godiya sosai tare da alqawarin zai kirata gobe,tabe baki tayi tana bin wayar da kallo bayan sun gama wayar,sai ta miqe nan saman katifa tayi kwanciyarta taqi komawa falon don koda ma mama ta sake baro wata maganar.

*****    ******     ******

Kullum ta Allah baya fashin kiranta,koda kuwa bata dauka ba zai mata tex,qoqarin kafa kanshi yake sosai da gaske,duk da gaya masa ita din fa ba budurwa bace har da yaronta,yace babu komai shi hakan ma yake so,a haka har sati dayan da abdur rahman ya diba mata ya cika,satin guda cif bai sake nemanta ko takowa gidan ba har cikar wa’adin kwanakin.

Tun safe take addu’ar kada Allah ya dawo da shi,a haka har lokacin tafiya makaranta yayi ta shirya ta tafi tare da abdallah wanda yau ya tubure sai ya bita.

Yau sai kusan biyar suka taso,tun daga qofar gidan ta hangi motarsa,a hankali ta dinga takawa jikinta a sanyaye har ta isa gab da motar,qofar mazaunin direba a bude take alamun mamallakin motar yana ciki,tuni abdallah ya gane motar waye,ya zame daga jikinta yayi wajen motar yana kiran abba,hankalin abdur rahman yayo wajen ya waiwayo yana murmushi sannan ya fito ya dage shi sama ya cafe suna dariya,sanye yake da yadi irin na maza blue black,hula da takalminsa sau ciki duka baqi,yayi kyau sosai. Ya sauke idanunshi a kanta yana kallonta
“Yau kam kin dade,kinsan tun nawa nake nan ina jiranki?” Kai ta girgiza ba tare da tace komai ba,yatsun hannunsa ya daga guda hudu ya nuna mata,sannan ya dora da fadin
“Shine yau kika dauke abokin hirar ko?” Kai ta sake kadawa sannan tace
“Shine ya nace yau sai ya biji,nima bana son tafiya da shi”
“Mukam muna maraba da shi ko yaushe,shiga ki kintsa kafin naje can qasan layinku na dawo na baki minti talatin”
“Amma dai da ka shigo ciki ko?”
“Amma dai kinsan gunki nazo ko?”ya bata amsa da salon yadda tayi tata maganar,ta lura jan magana yake ji saboda haka ta sanya kanta gida tana fadin
“A dawo lafiya”.

Salla kawai tayi wadda lokacinta ya kubce mata,ko abincin ta kasa ci tanaa zaune tana nazarin hanyar da zata bi abdur rahman ya janye zancansa salin alin ba tare da an kai ruwa rana ba,don gaskiya bata jin zata iya maida kanta cikin familyn su mukhtar,an gudu ba’a tsira ba kenan,ko kuma tsugune bata qare ba?,cikin haka zainab ta shigo dakin ta gaya mata taje ya abdur rahman na waje ta karbi abdallah.

Kamar wancan karon wannan ma haka ya tilasta mata shiga motar tasa,shuru ya ratsa motar na wasu daqiqu ba wanda ya sake cewa uffan bayan abdur rahman ya gama jaddada bayanansa a gareta
“Da farko abinda zan fara cewa shine na gode na gode matuqa,na yaba da qaunata da kace kana yi,har ka nuna sha’awar zamantowa abokiyar rayuwarka duk da ban cancanci wannan darajar ba,amma abdur rahman kayi haquri,bazan iya aurenka ba,saboda wasu dalilai wadanda ni da kai duka mun sansu wasunsu kuma ni da ubangiji na ne kawai muka sansu” kai yake jinjinawa yana dubanta sannan yace
“Ban gamsu da baya nanki ba ko kadan,babu wani abu da zai sanya ni janyewa daga batun neman aurenki sumayya,ina sonki babu wanda zai hanani”so take ya fahinceta bilhaqqi don su bar maganar sun wuce gun,sai ta sake fuskantar sosai wani abu na taba zuciyarta na daga abubuwa da suka faru da ita a baya
” ta yaya abdur rahman kake so na sake komawa cikin danginku,bayan kaima kana daya daga cikin mutanan da zasu shaidi irin rayuwar da nayi a cikinsu,ya kake so ka sake maidani rayuwar baqincikin da nayi bankwana da ita?,ko kuwa zaka sauya dangi ne saboda zaka aureni ni sumayya ‘yar gwal,ko ka manta waje mijina na baya,ka manta alaqar da take tsakanin ku,don Allah abdur rahman muci gaba da mutunci mu ajjiye zancan soyayya a gefe”ta qarashe maganar tsohon mikin dake zuciyarta na taso mata,sai ta sanyo qafafunta waje ta fito daga motar,da sauri shima ya fito ya zagayo inda take tsayen,kafin yace mata komai suka ji tsaiwar mota,waiwayawa sukayi dukkansu don ganin waye.

Mukhtar ne,tun yana cikin motar tasa yake qarewa motar kallo,babu shakka wannan motar yake tawan gani a qofar gidan su sumayyan,kenan yau zai ga waye mamallakinta zaiga wake zuwa gunta,amma idan idanuwansa na nuna masa dai dai kamar abdur rahman yake gani tsaye tare da sumayya,to meye yake haka a gidan?,meyw hadinsu?,shine mai motar da yake gani kullum na ficewa daga layin?,don samun amsaoshin tambayoyinsa sai ya balle murfin ya fito bayan ya kashe motar ya nufosu idanuwansa a kansu zuciyarsa na azalzala tare da ayyana masa wani abu wanda baya fatan kasancewaraa.

Sallamarsa ita ta katse abdur rahman daga kallon sumayya da tuni idanunta suka cika da qwalla,sannan suka katse shi dag fadar abinda yake shirin fada,dukkansu waiwaya suka yi suka dubeshi,fuskar abdur rahman din dauke da murmushi ya miqawa mukhtar hannu yana fadin
“Ah,ya mukhtar kai ne?” Baiqi miqa masa nasa hannun ba suka yi musabaha yana fadi tare da tsareshi da wani irin kallo
“Eh,ya kawu da sauren mutanen gidan”
“Duka lafiya alhamdulillahi” ya fada yana sakin hannun mukhtar din sannan ya juya ga sumayya
“Ki nazari a nutse,kada ki ruda kanki,kada ki cuci kanki ki cuceni,gobe in sha Allah zan dawo” ya fada yana juyawa zuwa wajen motarsa,dukkansu ita da mukhtar din suka yi masa rakiyar idanuwa,saidai kowa da abinda ke kai kawo cikin zuciyarsa,ya bude motar ya shiga bayan ya bawa abdallah ‘yar madaidaiciyar baqar leda cike da biscuite da choculet ya saukeshi ya tada motar ya wuce.

 

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE