KUNDIN KADDARATA CHAPTER 39 BY HUGUMA

Qarfe tara na safiya tayi wankanta,ta shirya cikin atamfa dinkin riga da zani,ba wani kwalliya tayi ba amma tayi kyau,dakin ta sake karkadewa ta goge sannan ta koma bakin gadonta ta sake kwanciya,idanunta ta lumshe tana saqa da warwara,kewar abdallah take ji sosai cikin zuciyarta har qwalla na shirin kawo mata,tunani ne fal zuciyarta tana wassafa yaya rayuwa zata kuma kaya mata cikin wannan gidan.

   Hayaniya ta dinga jiyowa cikin falon da surutai,ta bude idanunta ta kalli agogon dakin,goma tayi har da mintina arba'in da biyu,saita bude sif dinta ta ciro hijabi ta zura kana ta sanya silifas dinta ta murda qofar dakin ta fito.


     Duk uban hayaniyar da take ji yara hudu ne cikin falon,yarinyar farko wadda ita ta sake hautsina yanayin falon ma hakimce kan kujera kamar wata babbar mace duk da du du du ba zata wuce shakara sha uku ba,kallo take a tashar mbc three ta qure volume kamar ita da mutum dari suke kallon,sai yarinya ta biyu wadda batafi shekara uku ba dake zaune qasanta kan carfet taci uban indomie ta hadeta da ruwan shayi tana wasa da ita,daga can wajen step na dining kuwa wasu yaran ne su biyu,daya shekarunta goma daya takwas suna karyawa,su biyun kadai sun dame gurin kamar qanwar tasu dai,ta sake wurga idanunta,wata yarinya ce data tasamma zama matashiya wadda ta kusa shekara goma sha hudu takure a saqon kujeru,kallo daya zaka mata kasan daban take kamar yadda kamanninsu ya bambanta da sauran yaran dake falon,don dukkansu kamarsu daya ita kadaice kamarta daban kamar yadda ta fisu kyau baki dayansu.


   Dukkansu sun ga fitowarta saidai babu wanda ya kulata,ta dubi qofar dakin karima wanda ke garqame ta sake dauke kai

“Ina kwana anty”
Taji an ambata daga bayanta,saita waiwaya,yarinyar dake zaune ce saqon kujera ta gaidata tana murmushi,maida mata murmushin itama tayi tana mamakin zarnin dake tasowa daga jikinta
“Lafiya qalau,an tashi lafiya?,me sunanki?”
“Nuwaira”
“Sunan mai dadi” sai tayi murmushi tana cewa
“Na gode anty”.
“Ko zaki rakani wajen kakarku?”
“Wa?,hajiya”
“Eh”
“Muje in rakaki anty” ta fada tana wucewa gaba sumayya na rufa mata baya.

  "Wallahi bari umma ta fito sai na gaya mata duk abinda kika yi,bata ja mana kunne ba?" Yarinyar daje saman kujera ita ta ambaci hakan tana jijjiga kai,cak yarinyar ta tsaya kamar an ambata mata mala'ikan mutuwa,idanunta na tara qwalla tace

“Kiyi haquri don Allah kada ki gaya mata”
“Wallahi sai na fada saidai ta kasheki” ta fada tana buga hannu alamun babu fashi,wani abu ya tsayawa sumayya a wuya,takaici da mamaki suka cikata,sai ta janye nuwaira tana fadin
“Muje babu abinda zai faru dake kinji kada ki damu” jikinta babu qwari ta bi sumayyan suka fice.

   Kafin su qarasa gun hajiyan sumayya ta dubeta

“Me yasa kinsan kina fitsarin kwance da kika tashi baki sauya kayanki ba nuwaira?,kinsan fa ba’a son mace da qazanta” sai yarinyar ta fara qwalla ta soma sharewa tana cewa
“Wallahi anty tunda bana fitsarin kwance,saddiqa keyi sai a hadamu kwanciya gado daya,idan tayi duk sai ya jiqani,idan ta tashi ita sai nuratu ta sauya mata kaya,ni kuma ba zan canza ba har sai umma ta gama bacci tayi wanka ta fito sannan zata nunan wadanda zan sauya din,koda asuba bana samu nayi sallah sai rana ta fito” ta fada da alamu abun na ci mata tuwo a qwarya,shiru sumayya tayi tausayin yarinyar na kamata,wannan wanne irin zalunci ne,tun kallon farko da ta yiwa yarinyar ya nuna tana jin jiki a gidan,amma tana tunanin kamar ita ce yarinyar nan daya da karima jiya ta gaya mata uwarta daban,don ta tabbatar sai ta tambayeta
“Ina mamarki to?”
“Mama na tayi aure a wani gidan,tun kafin a yayeni aka karboni aka bawa hajiya ni,to da abbanmu ya sake aure ya auro umma sai umman ta karbeni nake gunta”take tsanar karima ta darsu a zuciyar sumayya,lallai ba shakka bayan shirkar tsafi ma harda azabtar da yarinyar da bata ji ba bata gani ba,wai me mutane suka dauki duniya ne?,kowacce mace son kanta ya mata yawa?,burinta ta mallaki miji ta rabashi da kowa nasa?,ta rabashi da ‘yan uwansa da tazo ta samesu tare,’yan uwa da suka zamar masa bango marufar asiri tun yana zanin tsumma har kawo yau,ta rabashi da duk wani alkhairi uwa uba ta rabashi da mahaliccinsa,ta sakashi a musibar da ranar gobe qiyama bazai iya tsallaketa ba,ta rabashi da hankalinsa bare ya kula da addininsa,wanda ya cancanci a bashi haqqinsa ta hana ya basu yanzu duka wannan qauna ce?,sai tace sonshi take shi yasa ta aikata haka,wannan ko babban maqiyinka ba shakka iya cutarwar da zai maka kenan,da irin wannan tunani suka isa bangaren hajiyan.

   A duqe suka sameta tana share falon nata dake malale da carfet,kallo daya sumayya tayi mata ta fuskanci shekarunta basukai ace tayi tsufar da tayi a yanzu ba,da sallama suka shiga ta dago tana amsa musu riqe da qugunta wanda bisa dukkan alamu ciwo yake mata,nuwaira ce ta gaisheta ta amsa babu yabo ba fallasa yayin da sumayya ta qarasa tana amsar tsintsiyar hannunta tana gaidata,amsawa tayi tana dubanta yayin da sumayya ke qarasa mata sharar har ta kammala sannanbta dawo inda hajiyar ke zaune tana yiwa nuwaira masifar sai zuba zarni take taje bandakinta ta wanke jikinta,mamaki ya cika sumayyar,to ko batasan meke wakana bane cikin gidan?,batasan ba laifin nuwairan bane karima ce ta cancanci fada idan da duka ma ayi mata?,tashi yarinyar tayi ya shige bandakin hajiyar sannan hajiyar ta maido kallonta ga sumayyan

“Ban gane fuskar ba wace ce ne?” Murmushi kawai tayi ta dan sad da kai
“Oho,ko amaryar lukman ce” kai sumayyan ta gyada.

    Shiru ne ya biyo baya,hajiyan na dan satar kallon sumayyan,sai taji ta dan sake da yarinyar duk da ba hira suke ba zaman kurame ne,a haka har nuwaira ta fito daga bandakin sanye da jiqaqqun kayanta wadanda ta wanke bayan ta dauraye jikinta ta maida su a haka

“Wani nuwaira nikam bakuyu abin kari bane yau,gashi har sha daya na shirin gotawa yau ba’a kawo kin komai ba,ko luba mai aikin bata zo bane?”cike da madaukakin mamaki sumayya ke sauraron zancan
“Tazo hajiya,bansan ba’a kawo miki ba,don ko nima yau ban karya ba,naga dai su nuratu na karyawa ni ma ba’a bani nawa ba”ta fadi babu alamun damuwa tattare da ita bisa dukkan alamu ta riga da ta saba da hakan,yamutsa fuska hajiyan tayi
“gaskiya na fara jin yunwa wlh,wannan abu Allah kayi mana maganinsa”
“Amma hajiya ai naga kina da sauran kayan abincinki da kika ce bazaki iya ci gaba da girki ba ai abba bai debe su ba ko?”
“To idan banda abinki ina fama da lalura ina zan iya,sharar ma don bazan iya zama cikin qazanta bane nake daburtawa nake yinta” ta fada ta muskutawa da alamu yunwa na sakadarta,tausayinta duka sai ya kama sumayya ta dubeta
“To hajiya idan ba damuwa sai na shiga na girka miki ai ko?”haba ta riqe
” a’a,har kya fara shiga madafi ta sanadina?,ki barshi babu komai idan da sabo ai mun saba da irin wannan gashin,ke dai kawai Allah yayi mana magani”murmushi tayi kawai ta miqe tana tambayar nuwaira inda kitchen din yake.

   Sallamar karima a gadarance ita ta maida hankalinsu bakin qofar,ita ke gaba gogan na binta a baya riqe da wani dan qaramin flask wanda bako shakka abun karin hajiyan ne a ciki,idanunsa na kan sumayya yana faman sakar mata murmushi ,wani takaici da haushinsa suka qumeta saita dauke kai tana jin kamar taje ta shaqeshi,haka nan kawai taji jarumin namiji yana burgeta,sai ta tuna sanda zainab ta fara murza kambunta lokacin tana gidan mukhtar,tabbas ko a lokacin mukhtar din kan tauna tsakuwa wani lokaci.


  Hajiyan da za'a yiwa sannu a gaisheta ita ke faman yiwa kariman sannu tare da gaisheta,lukman ya koma gefan hajiyan yana gaidata cikin dari dari suke gaisawar kamar suruki da suruka duk don kada su batawa karima rai,baki sumayya ta saki tana kallon abun mamaki bayan hajiya ta bude flask din da aka kawo mata,wani gantalallen soyayyen dankali ne da rabin wainar qwai babu ko tea amma hajiyan sai godiya da sannu take mata

“Saidai yau kici haka hajiya don kafin na fito jikokin naki sun shanye shayin”
“Ai babu komai,idan baka yiwa jikanka ba wa zaka yiwa” ta fada fara’a kamar gonar auduga.

   Kallon sumayya karima tayi bayan sumayyan ta gaida lukman wanda ke faman binta da kallo kamar tsohon maye

“Ke baki iya gaida mutane ba” ta fada fuska a tsuke kamar wata uwarta,waigawa sumayyan tayi ta watsa mata kallo
“Su waye mutanen?” Ta tambayeta bayan ta tsareta da ido,sai kawai taji sumayyan ta mata kwarjini da irin kallon da take mata,janye idonta tayi ta dubi hajiya
“Hajiya kina gani dai a gabanki ko?” Ta fada cikin zafin rai,lukman yayi saurin karbewa
“Bana son rashin zaman lafiya fa sumayya a gida na kinji ko?” Kallon da wa kazo ta watsa masa sannan ta dauke kai,hajiya cikin rawar jiki tace
“Ke yarinya,farincikinmu shine farincikin karima,saboda haka dole ki mata biyayya ki kiyaye” girman hajiyan take gani,saboda haka ta dan rusuna
“Insha Allahu hajiya kiyi haquri” ta fadi da sauri tana shigewa kitchen din hajiyan don bata son ma ta sake kallon fuskar lukman bare ta karima.

   Tana kitchen tana hada girkin duk da wasu kayan buqatun babu,mamaki da tunani fal ranta,a haka taji sallamar hajiyan,ta juya tana amsa mata,qarasowa hajiyan tayi ta kama hannun sumayya kamar zata saki kuka

“Kiyi haquri sumayya da abinda nayi miki dazu,yarinyar nan idan ta umarcemu da abu daga ni har lukman bama iya musa mata,amma nasan alhakin yaran jama’a ne yake bibiyata,haka kawai naji kin kwanta min sumayya zan gaya miki wace ni me na aikata ga rayuwata da rayuwar yarona”
Kafin sumayyan tace wani abu tuni hajiya ta fara bata labarin dukka aure auren da lukman yayi wanda ita ce sila,da fari haushin hajiyan ta dinga ji,amma daga bisani sai tausayinta ita da lukman ya baibayeta baki daya,tabbas abu na farko data fuskanta ya janyo wannan matsalar sakaci da rashin riqe ubangiji hannu bibbiyu,har qwalla sai data yiwa hajiya da lukman din saboda aikin kariman ya shallake hankali.

  Cikin sanyin jiki ta riqe hannun hajiyan ganin tana zubda qwalla

“Kiyi haquri hajiya ki fawwalawa Allah lamarinki,ba shakka inna idan ma alhakin ne ba mamaki,Allah na sonki shi yasa zai hukunta ki tun a duniya,din hukuncin lahira da shi gwara na duniya sau babu adadi,in sha Allahu ni zanyi iya bakin qoqarina wajen ganin na daidaita lamarin iya abinda Allah ya huwace min,ina so daga yau kisa a ranki ba zaki qara jin tsoron karima ba,ba zaki sake bin umarninta ba sai abinda ya dace shi zakiyi,a duk sanda kika ganta idan kika ji faduwar gaba ko tsoro ki karanta ALLAHUMMAKH FINIHIM BIMA SHI’ITA matakin farko kenan,sannan daga yau kada ki sake cin duk abinda ya fito daga hannunta,ki umarci lukman ya kawo miki kayan abincinki a zuwan zaki ci gaba da girki,ni kuma in sha Allahi zanci gaba da dafa miki” kai take gyadawa cike da gamsuwa tana jin tamkar damuwarta na gab da yayewa
“Sannan lukman danki ne hajiya,bakin uwa kaifi gareshi,ki dage da yi masa addu’a,Allah ya yaye masa bala’in da ya fada ta sanadin abinda ke kika aikata shi,bashi kadai ba,har ke dinma saikin dage da addu’a wa kanki na neman tsari”
Kai ta sake jinjinawa
“Har na manta rabon da na sashi a addu’a ta,na gode da tunatar da ni da kikayi,na gode sosai”
“Sannan hajiya,kinsan rayuwar da nuwaira take cikin gida kuwa?” Ta tabo inda yafi mata qaiqayi
“Na sani sumayya na sani,saidai bani da ikon magana bani da ikon gyarawa” ta fada cikin jimami,don har ga Allah duk cikin jikokinta tafi qaubarta,din ta fita daban a cikinsu,nutsuwarta da komai da komai,shiru sumayyan tayi sannan tace
“Babu komai,zanyi iya bakin qoqarina itama akanta kafin Allah ya kawo qarshen lamarin”
“Na gode sumayya na gode,haqiqa kin zamo HASKE cikin gidan d’ana cikin kwana daya tal,ina miki fatan alheri sannan kuma ina miki fatan samun nasara,Allah ya albarkaci rayuwarki da alkhairi masu tarin yawa,ya tsareki” amin sumayya ta dinga cewa tana jin dadin addu’ar har cikin ranta,ko da can ita din mai son wani na gaba da ita ne ya albarkaceta,kusan tare suka gama aikin ta kammalewa hajiyan cikin kula yadda tasan zai ishesu ita da nuwaira,tace zata turo mata ita taci na rana dana dare,don ta lura bata samu albarakacin cin na safe ba,sai na hajiyan da suka yayyafita.

 Nan tayi zamanta gun hajiya,ita kanta hajiyan sai ta dinga jin dadi cikin ranta,nuwaira ma ta dinga sato jiki tana leqowa har sanda sumayyan ta koma bangarensu.

*****    ******     ******


Cikin kwanaki hudu rak sumayya ta gama dukkan wani shiri nata na tunkarar wakeken qalubalen data fuskanci yana danqare a gidan,ita kanta mamakin kanta take yadda zuciyarta ta taurare baki daya har take ganin zata qalubalanci karima wadda baki daya ta rusa rayuwar gidan ta dora ta kan turbar da take so,sam sam yaranta irin yaran nan marasa tarbiyya ko qanqani,su zagi babba duk girmansa ba komai bane a gunsu,sam sam sumayya bata shiga shirginsu ko sakar muau fuska tunda ta fuskanci inda tarbiyyarsu tasa gaba,hakan ya sanya suka fara shakkarta,sai kuma mai biwa babbar da ta soma son kula sumayya,sau tari takan qwanqwasa qofarta idan ta bude mata tace ta shigo kuma sai taqi,sai ta fuskanci shakkar mamarta take,hakan ya sanya ita sumayyan ta fara qoqarin janyota a jiki,ga shegen gulma munafunci da iya kawo labari,hatta da mahaifinsu suna iya dauko gulmarsa su kawo mata ita kuma ta tuhumeshi kan haka,sumayyan na sha'awar hatta da tarbiyyar yaran ta saisaita musu ita,don ta kula sam daga makarantar boko babu kuma wata makaranta ta biyu da yaran ke zuwa wadda ake kira da makarantar addini ko islamiyya,baki daya idan ka dauke sumayya banu mai rayuwa kan ra'ayinsa sai abinda ta shinfida,tun abun na bawa sumayya haushi har ya koma bata tausayi,ita sam ma baki daya bata ta angon ko kadan,wanda zuwa yanzu hatta lokacin fita da dawowarsa gida karima ta sauya masa duk don kada su hadu da sumayyan,ta saka an qara narka masa aikin mantau akan sumayya wadda ko gefen silifas dinta lukman din ma baije ba,sau tari takan tambayi kanta me yasa ta auri lukman sai ta rasa dalili,amsa daya ke zuwa kanta

“Qila don kizo ki ceci rayuwar ‘yar gidan ne” ita kanta tafi gamsuwa da wannan ce sahihiyar amsar

******     *******   *******


 Cikin satittika qalilan shaquwa ta fara shiga tsakaninta da hajiya,kusan koda yaushe can take wuni,ta yima haijan aikace aikace sannan suyi girkinsu abinsu,sannu a hankali sauyi ya fara samuwa tattare da hajiyan,sumayya ta zaburar da ita ta kuma koya mata addu'o'i sosai,rana ta farko da suka fara fuskantar zuwan sauyi shine randa kariman ta shigo da abincinta wanda aka saba sanwa hajiyan don bazance bata ba,duk da hajiyan ta jima bata ci amma sumayya tace ta dinga karba kada ta gaya mata idan yaso saita dinga bayarwa,tunda ta shigo ta lura hajiyan sam bata rawar qafa yadda ta saba idan ta shigo gunta,abu na biyu tana jiran taga hajiyan ta gaidata yadda ta saba sai taga tayi fuska,ta maida hankalinta gun sumayya dake shafa mata man zafi a gwiwarta data riqe mata take mata ciwo,wanda abaya bata da wannan gatan saidai taci ciwonta ta warke don dolenta.


  Kanta yayi masifar daurewa,abu na farko da yazo kanta aikin hajiyan ya fara sako sako don dama kwana biyu tafi maida kai a kan lukman din

“Ga abinci nan” kariman ta fada a wulaqance,juyowa hajiyan tayi tana duban flask din ranta cike da takaicin yadda ma ta dinga karbar wannan abincin
“Wai ni?,ai da kinyi gaba da abinki don na jima banci abincinku ba,’yata na girkamin kullum” ta fada tana duban sumayya,take tsoro ya shigi karima,ashe tayi sake har haka?,ashe fa diyar malamai wannan karon lukman ya kwaso mata,lallai ba shakka shi yasa taga bata taba tambayar abincinta ba a gidan duk yadda ta sha alwashi akan yi mata kaca kaca duk sanda ta tambayi a bata abinci.

  Hankalinta tashe ta fito daga bangaren ciken da tsoron lallai idan ta gama da hajiya babu shakka lukman zata dawowa,kacibus sukayi da nuwaira wadda ke dawowa daga gidan kitso da sumayya ta turata tayi saboda ba zata iya mata ba jiya ta yanke da wuqa a hannunta,baki ta saka tana duban nuwairan yadda ta canza cikin sati biyu kacal da kariman tayi bata nan,ta tilasta lukman ya biya musu umra ita da shi don har sai da yaci bashin wajen dubu dari biyar sannan ya cika musu,su kuma yaranta da zata tafi ta tattarasu ta maida su gidan iyayenta ta bar nuwaira ko oho,don dama ta saba yi mata irin hakan,tsoro ya kama nuwairan sai ta rabe gefe sannan ta tattakura ta sheqa da gudu sai bangaren hajiya,don kayan dake jikinta na waccar sallar ne shekara uku da dinka su,bata barinta ta sanya su sai wani abun ya tashi duk da cewa suna da lodin kaya harda wanda bata taba sawa ba ma sababbi,ta riga ta saba kayanta koda yaushe haka suke tamkar tsummokara,a haka ma sai an bata umarnin wadansa zata saka,bayan 'yan uwanta kullum cikin saka mai kyau suke.


  Bata bi ta kan nuwaira ba don ba ita ce yanzu a gabanta,bangarenta ta wuce hankalinta a matuqar tashe,tabbas lallai babu shakka idan batayi wani abu ba ta lura duniyar rayuwarta gab take da girgiza koma rugujewa baki daya,dole ne gidan ya koma yadda yake,dole kowa ya koma yadda take so ciki kuwa harda sumayyan

*

 Tunda ya karbeshi kusan shi ua zame masa uwa da uba baki daya,yana matuqar debe masa kewa,yana sanyashi nishadi,wata qauna ta yaron nasa yake ji cikin jikinsa da jininsa,sau tari ya kanyi mamakin kansa yadda yake zama yayita kallon abdallan kamar babu gobe,babu yadda yaya yahansu batayi ba akan ya bata shi amma ya qiya,ya bata haquri don bazai iya bata shi din ba.


  Da safe tare suke shiryawa ya bashi abinci su fita kasuwa tare da shi,zuwa azahar zai bar kasuwa ya dan fita da shi su zaga gari su dawo da la'asar,qarfe shida subar kasuwa su dawo gida,har gado ya siya na yara ya sanya masa can cikin shagon,nan ma idan sun dawo sunyi wanka sannan suci takeaway din da ya tsaya hanya yayo musu,daga nan ya zube masa kayan wasansa yana tayashi yana kallon t.v har yaron yayi bacci,wani lokaci yakan bata lokaci saman abun sallah yana wa yaron nasa addu'a tare da yiwa kansa,wanda hakan ya sake samarwa da ruhinsa nutsuwa,shikewa Abdallahn komai,dai dai da rana guda mukhtar bai taba jin ya qosa koya gajiya ba,kai kanka idan ka kalli yaron ba zakayi zaton bai tare da mahaifiyarsa ba,kusan kullum sabon kayan mukhtar zai sanya masa,ado yake masa sosai,hakanan idan shadda zaya sanya ko yadi anko suke abinsu,duk wanda ya gansu a hanya zasu burgeshi,wata qauna ta musamman ce tsakanin d'a da ubansa,wani lokaci idan ya soma rigiman mamansa sai ya kaishi gunsu halima ya wuni don bai iya barinsa ya kwana,da dare yazo ya dauki abinsa su wuce.


   Sau daya yaya yahansu ta taba tuntubarsa da batun bazayayi aure bane,murmushi kawai yayi mata yace tabar batun don ko sha'awar sa bayayi,tilas ta ja bakinta ta tsuke,domin har yau tana tuhumar kanta da cewa ita ce sila,zuwa yanzu itama ta fara gani,don kuwa yaron da jamila ke ao kamar ta mutu shima yayarsa ta hana auren sam tace bata yarda ba,ga fatima nan ma a gabanta babu wani bayani,fiddausi kuwa uwar miji ta sakota gaba,yau tana gidanta gobe tana gidan yaya yahanasun



 *_KOMAI NISAN JIFA_*



    Tunda dukka ayyukanta suka kammalu wajen malaminta data bawa hadin kai wanda har ta kaita da kwanciya da shi,ki a jikinta babu abinda taji tunda har ya mata alqawarin tabbas tamkar ta samu kukhtar ta gama koda kuwa zata sanar masa ita ta shirya duk abinda ya faru a baya da sumayya,babu abinda zai iya aikatawa ba zaiga aibunta ba face sabuwar soyayya da zata sake ballewa a tsakaninsu.


   Ranar lahadi ta shirya zuwa har gida saboda ta tabbatar a ranar bai fita kasuwa,dinki na musamman tayi sabo,baya ga sabon kitso da gidan kwalliya da taje duka aka sauya halittar Allah,saboda tana rayawa matuqar ciniki ya fada tofa ba lallai bane ma ta dawo gidansu ba saidai a biyota da kayanta,tunda har yau a matsayin saki daya yayi mata  haka ta sanarwa mamanta,wanda koda sakin ukun tace an mata ta kuma ce zata koma babu abinda uwar ta isa tayi don ba a bakin komai take a gunta ba.


    Qarfe sha goma na safe ta kammala komai,a nan cikin shagon masu kwalliya wadda ta sanya fitowa tunda safen tayi mata ta sauya kaya,double ta biya kudin makeup din hakan ya sanya ta yiwa jakarta qarqaf,bata da damuwa tunda tana saka ran kome wanda zata fanshe dukkan abinda ta kashe gun mukhtar,ba shakka sai ta rama wahalar da ya bata ba zata sassauta masa ba.


   Qarfe goma sha daya saura mintuna goma ta sauka qofar gidan mukhtar din,wani farinciki ya lullubeta ta soma shaqar iskar komawa cikin gidan,cikin sa'a tana tura qofar gidan ta taddata a bude,a hankali take takawa saboda cogen dake qafarta har ta sada kanta da falon gidan,a hankali take qarewa falon kallo yadda ya sake maidashi ya gyarashi bayan barinsu gidan,sai abun ya sake burgeta,ko ina tsaf kamar akwai mace a ciki kasancewar yana da mai share share da goge goge,cikin kallon da takeyi ne idanuwanta ya saukan kan abdallah dake zaune tsakiyar falon,sanye yake da jallabiya fara tas ta yara wadda ta masa kyau kamar dan larabawa,wasansa yake da kayan wasa turmus a gabansa nau'i daban daban.


   Idanuwa ta zuba masa kamar yadda shima ya zuba mata idanuwa yana kallonta tamkar ya santa,karkata kai take tana gano kamannin mutum biyu tattare da shi,sumayya sumayya mukhtar mukhtar,ci gaba tayi da kallon nasa tana son tantance dan waye?,miqewa yaron yayi yana ci gaba da kallonta sai kuma ya saki kuka tare da juyawa a guje ya shige bangaren baban nasa wanda ke ciki.

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE