KUNDIN KADDARATA CHAPTER 40 BY HUGUMA
Mukhtar dake falo zaune saman abun sallah yayi saurin sallame raka’arsa ta qarshe wadda dama zaman tahiya yake,qarasowa abdallah yayi yana kebe baki ya fada jikin mukhtar,tambayarsa yake menene kamar wani babba,babu baki sai gwalanto da yake masa wanda bai gane mai yake cewa,miqewa yayi da sauri sabe da shi a kafadarsa sabida tunawar da yayi dazu da ya fita siyo ma abdallan alawa ya manta ya bar qofar gidan a bude.
Tana zaune qafa daya kan daya tana kadasu hankalinta kwance,tana jin ba ma sai taje nemansa ba da kanshi zai fito,qamshin turarensa da ta ji shi ya maida hankalinta zuwa qofarsa,shi dinne dauke da abdallah sanye da jallabiya sak irin ta abdallan,har ga Allah bai lura da ita ba sai da yaji an ambaci
“Ranka ya dade” cak ya tsaya sannan ya waiwayo ya dubeta,idanunta ya dan juya don tabbatar da cewar ita din ce?,ita ce don kuwa zuwa yanzu gabansa take takowa,dab da shi ta qaraso tamkar zata shige jikinsa,cikin narke murya ta soma magana
“Haba my mukhtar,ka riga da kasan irin kamun da soyayyarka tawa zuciyata,ta yaya kake tunanin nisanta kanka da ni bayan kasan cewa ina mutuwar sonka,a yau ina so ka maidani dakina ba sai gobe ba domin shine burina kaji” ta qarashe maganar ta sigar bada umarni.
Wani bala'i ke cinsa,ya tabbata cewa idan har baiwa zainab akuyanci ba ba zata taba barin rayuwarsa ba,yarinyar da kullum kwanan duniya ya zauna tunani yake tare da tambayar yaya akayi ya aureta ma wai?,mene ya ja hankalinsa,ko da yaushe yakan godewa Allah da bai QADDARA rabon zuria a tsakaninsu ba.
Cikin tsantsar bacin rai ya soma nuna ta da yatsa kamar zai tsone mata idanuwa
“Cikin halittun dabbobi ke wacce iriya ce a cikinsu?,bakiji gargadin da na miki ba kenan?,tunda nake ban taba ganin ballagazar mace irinki ba,sha sha sha kawai wawiya,to wallahi zan miki gargadi na qarshe,duk sanda kika sake shiga rayuwata sai na miki abinda ko hanyar da nake bi aka ce kibi ba zaki biba,bace min da gani banza qazama kawai” ya fada kamar zai hankadata.
Tsantsar tashin hankali da baqinciki suka taso suka tokareta,amma data tuna yadda bokanta ya jaddada mata kyawun aikin da yayi mata sai taga bari ta sake gwada sa'arta
“Wai mukhtar me na maka da zafi haka,nina shiryawa sumayya dukkan wata gadar zare kuma a idanunka sumayya ce ta aikata laifin,to amma na lura tsanar da ka yimin baka yi mata koda rabinta ba” sosai maganar ta daki kunnensa gangar jiki da zuciyarsa duka lokaci daya,wani abu yaji yana zagaya kansa,wani irin sanyi jikinsa yayi ya zubawa zainab ido har baisan sanda yace
“Kika shirya mata gadar zare kamar yaya?” Wani fari tayi da idanuwa tana ci gaba da kallonsa,a tunaninta sanyin da jikinsa yayi aikinsu ya fara shiga jikinsa ne,sai ta kama hannunsa babu musu ya bita zungui zungui,don baya gane komai a yanzu,abinda ke yawo kansa kawai shine irin abubuwan da suka dinga faruwa tsakaninsa da sumayya a lokacin,sai da ta kaishi gefan kujera ta zaunar sannan ta zauna gefansa.
A hankali ta dinga warware masa zare da abawa tamkar wadda ake umarta,ko da yake umarni ne na rabbil izzati da yaso ya fidda bayinsa daga wani mummunan sharri,ta qare da cewa
“Dukkan wannan saboda tsananin qaunarka da kishinka da nakeyi ne ya janyo na aikata hakan,kuma babu abinda bazan iya aikatawa duk don saboda kai saboda na mallakeka ni kadai,a shirye nake na sadaukar da dukkan abinda na mallaka” ta fadi tana karya wuya tare da sakin murmushin alamun samun nasara a tunaninta.
Gaba daya daina zagayawa jini yayi a jikinsa,kansa ya masa nauyi,cak qwaqwalwarsa ta tsaya da aiki,wani duba yakewa zainab din mai cike da tsantsar tsana,daki daki musgunawa da zargi da kallon tsana da ya dinga yiwa sumayya ya dinga dawo masa kamar bitar karatu,yanzu duk baki daya ba bisa laifinta bane ashe?,ashe ita din bata aikata komai ba kamar yadda tasha sanar masa?,bai taba jin ya tsani wata halitta a duniya ba kamar yadda yake jin tsanar zainab na yawo cikin jininsa da ruhinsa ba,sai da wuta ta dauke masa na wasu mintuna kafin ya fara tunaninsa ya fara dawowa kan hanya.
Yana jin yau idan bai ci uban zainab a duniya ba yayi asarar rayuwarsa,baisan wanne ne hukunci na qarshe da ya cancanci yayi mata ba,miqewa yayi da hanzari ta ruqo hannunsa
“Ina zaka?” Wani kallo ya juya ya watsa mata wanda ya sata sanqamewa,fargaba ta lullubeta tana fatan ba abinda take tunani bane ke shirin aukuwa
“Gidan uwarki da ubanki zani,zauna ki jirani” ya fada a tsawace yana tsige hannunsa daga nata,wani malolon takaici ya cika zuciyarta,kada dai ace mukhtar din na cikin saitinsa tayi wannan barin zancen?,yana nufin aikinta baiyi tasiri a kansa ba?,waishin wani irin mutum ne mukhtar din?,yana nufin dukka kashe kudi bata lokaci da sadaukar da jikinta da tayi ya tashi a banza?,to wallahi wannan karo kam bai isa ba,bai isa ya sanyata ci gaba da yin asara ba,kota hanyar tsiya kota arziqi,tsaye ta miqe a zafafe tana dubansa
“Kai mukhtar,na gaji,na gaji da asarar lokacina da kudina a kanka,me yasa bakasan darajar soyayya ba?”
Dauketa yayi da wani zazzafan mari wanda ya haddasa mata ganin wulgawar wasu taurari tare da zubewa warwas a qasa,lokaci guda jini yayi kwance gefan qwayar idanuwanta,kafin ta kai ga dawowa hayyacinta tuni ya garqame qofar falon sannan ya wuce ciki cikin matsanancin sauri,bedroom dinsa ya shiga ya kwantar da abdallah da bacci ya daukeshi kan fadar mukhtar din sannan ya fito ya rufe qofar dakin baccin ya rufe ta falo baki daya don bai fatan yaji ko yaga abinda yake shirin aikatawa,wani irin suya qirjinsa yake a fuskarsa yana jin wani hucin zafi na fita kamar wanda aka cilla cikin rumbun gasa biredi.
Nan saman kujerar ya sameta zaune tana shafawa tare da jajjabin kuncin da ya mareta wanda lafiyayyun yatsunsa suka fito rada rada tamkar an zana su,bata lura da fitowarsa ba sai da flower vase din dake kan t.v stand ta fado ta fashe saman tiles sanadiyyar finciko wayoyin dake jikin kayan kallon ta ankarar da ita,nufota ya soma yi wanda hakan yayi matuqar firgitata,gaba daya kamanninsa sun sauya mata,ganinsa take kamar wani mayunwacin zaki yaga abun farauta
“Me kake shirin yi mukhtar,kada dai kace dukana zakayi”
“Idan akwai abinda yafi duka yau zaki dan dana shi,inaso gangar jikinki ta fara dandana azaba kafin na kai ga ruhinki,yau zakiyi dana sanin raba masoya,daga yau ko a shirin film aka ce ki fito a matsayin jarumar dake raba masoya ba zakiyi marmari ba”
“Amma dai kasan…….” Sai maganar ta katse sakamakon ihun da ta tsala saboda kyakkyawan masauki da wayar ta samu a gadon bayanta,duka kota ina ya dinga kai mata,baki daya ya fice hayyacinsa kamar yadda itama ta fara dan dana kudarta,duk duka daya da zai kaimata sai ya tuno baqar azabar da sumayyan ta sha a wancan lokaci,tun zuwan zainab din gidan har ya zuwa ranar data kwanta gadon asibiti,ranar data zamto rana ta qarshe a tarihin zamantakewar rayuwar aurensu.
Duk inda ta nufa da nufin samun mafaka ko maboya sai ya bita,tuni takalman qafarta sukayi nasu guri daban,haka dankwali da mayafinta,ganin abun nasa na gaske ne babu alamun sassauci yasa ta fara bashi haquri,saidai sam baya fahimtar me take fada,sai bada haqurin ya zamo tamkar tana qunduma masa zagi ne a gurinsa.
Tun zainab na iya ihu da neman agaji har muryarta ta dakushe,tuni fuskarta ta cabe baki daya,kwalliya tayi nata guri,baka iya tantance ina kwalliyar tata bare fuskarta,babu inda bai fasa ba ajikinta har wani sashe na kayan jikinta ya yage saboda tsantsar dameta da kayan sukayi,jagaf ta jiqa kayanta da gun da ta dinga malelekuwa da fitsari,wurgar da bulalar yayi gefe kamar yadda zainab ke yashe gefe daya tana fidda qwalla hadi da numfashi,sai yau ta yarda da maganar hausawa na cewa kuka ma rahama ne,gashi a yanzun bata da qwarin ma fidda sautin kukan,azaba take ji na shigarta takowacce kafa ta jikinta,dukan da tunda tazo duniya ba'a taba yi mata kwatankwacinsa ba duk da kasancewarta yarinya gagararriya tun a wancan lokacin,yana haki numfashinsa na fita da qarfi saboda tsananin bacin rai,ji yake kamar ya shaqeta ta mutu ya daina kallonta,duk duba daya da zaiwa fuskarta tsanarta ke ninkuwa cikin ruhinsa,ba shakka wannan duka babu abinda ya rage cikin zuciyarsa na daga bala'in da yake ji,qafarta daya ya kama ya bude qofar falon ya dinga janta tamkar kayan wanki,bai direta ko ina ba sai bakin qofar gidan,ya koma ya kwaso tarkacen takalmi jaka da mayafinta ya watsa mata,yana tsaye a kanta ya nunata da yatsa
“Ba qarshen hukuncinki kenan ba,ki jirayi abinda zai biyo baya” ya fada yana juyawa cikin gida.
Wani irin jiri ya dinga kwasarsa,da qyar ya kai kansa cikin dakin baccinsa inda abdallah ke baccinsa lakadan baisan meke faruwa ba,gefansa ya zauna ya zuba masa idanu yana kallonsa cike da tausayinsa tausayin kansa da kuma tausayim sumayya baki daya,tambayar kansa yake ta yaya ya yarda sumayya zata iya aikata haka ma wai?,sumayyarsa ce fa?,rainonsa ce,tarbiyyarsa ce,yaya akai har ya gaza bincike tashin farko ya yarda ya dora zarginsa kan halittar da bai taba samunta da cutar da wani qwaro ba ballanta na mutum dan adam mutum din ma shi mukhtar,mukhtar dinta,wannw iri kaidi ne mata suke da shi haka?,wanne irin halakakken kishi ne wannan?,yunqurin kisan kai fa kenan a taqaice,ta yaya zai ga sumayya?,ta ina zai fara neman yafiyarta?,da wanne ido ko fuska zai kalleta?,shi kansa baisan amsar dukkan wadan nan tambayoyi ba,haqiqa ya cutar da ita,ya cutar da zuciyarta,babu shakka shi yasa tun daga ranar da ya saketa bai sake samun sukuni nutsuwa ko farinciki cikin zuciyarsa ba,ya sani haqqinta ne Allah bazai taba barinsa ya huta ba bayan ya cutar da ruhin dake masa qauna ta domin Allah,sai kawai ya dafe kansa da hannu bibbiyu wanda yakejin kamar zai tsage,kuka ya saki mai tsuma zuciya hawaye na bin fuskarsa,fata yake ya samu sauqin azabar da zuciyarsa ke masa,fata yake ya samu salama qirjinsa ya bar suya,baisan wanne hukunci ya dace ya sake yiwa zainab ba,ba shakka wannan hukunci yana ji har cikin zucuyarsa bai gamsar da shi ba yayi kadan.