KUNDIN KADDARATA CHAPTER 42 BY HUGUMA

     Gefansa ta zauna cikin rashin jin dadi,tana jin kamar ta raba yaran da mamansu ne,ta dubi lukman
“Ya kamata zuwa gobe kaje ka dawo da mamarsu islam,kada a ja abun yayi nisa don Allah,yaran na buqatar mamarsu” kai ya kada baison gaya mata wani abu da zai daga mata hankali,a yanzun da karima ta dan tura ta bar gidan sai yake jin kamar an zare masa wata qaya data tsaya masa a maqoshi
“To naji” kawai ya fada.

     Kwana biyu tana masa mitar yaje ya dawo da karima arana ta uku yace kada ta sake masa maganar baiso,idan lokacin dawowa yayi zata dawo,ai ta saba ba yau farau ba,hakan ya sanya ta tsuke bakinta,hankalinta ya dan kwanta ganin yaran basu tada hankali sosai kan rashin dawowar mamansu ba.

       Cikin kwanakin da suka biyo bayan tafiyar karima baki daya gidan yayi dadi,kada ma lukman hajiya da nuwaira suji labari,da fari sumayya ta fara fuskantar matsala daga yaran saboda qarancin tarbiyya da suke da ita,amma sai ta jure tayi amfani da hikima irin tata,a hankali ta fara janye qananan,nuratu basma da syyada,islam ce kawai ta taqi biyuya,ta soma kwaso halin uwarta tsaf,hakan yasa ta tattarata ta watsar gefe,zasu hadu suci abinci tare,suyi karatu,ta basu labarai na annabawa da sahabbai,suna bala’in so ta basu tarihi,har rigima suke idan tace ta gaji,sosai ta shiga jikin yaran suka soma shaquwa da ita,ta koya musu abubuwa da dama wadanda ya kamata ace sun iya amma basu iya ba,kamar alwala,sallah,sallama idan zasu shiga guri,addu’ar sanya kanya,addu’ar bacci da tashi daga bacci,addu’ar shiga bandaki data fitowa,addu’ar fita daga gida da ta shigowa da yin bismillah da hamdala kafin da bayan gama cin abinci,su kansu yaran dadi sukeji,nuwaira tafi kowa murna takance
“Anty dama tuntuni kema ‘yar gidan nan ce,ai da tuni nayi saukar qur’ani ko?” Dariya takanyi tace
“To ai yanzun ba gashi na zo ba?,kuma zakiyi ne in sha Allah”,tarbiyya take basu sosai mai wuyar bari ko mantawa,tana musu ne bilhaqqi fisabilillahi,don har ga Allah tana son yaran,ko ba komai babansu da kakarsu na gwada mata qauna.

      A hankali sai itama islam din ta fara biyuwa,ta shige cikinsu,idan kaga sumayya da yaran zakayi zaton qannenta ne,dama gata gwanar son yara,abun ya yiwa hajiya dadi,wani lokaci har takan tsinci kanta da addu’ar kada Allah yasa karima dawo,don ita kanta yanzu anan bangaren take wuni sai dare zata kwashi jikokinta suje su kwana tare da ita a can,a yanzu sumayya ta koya musu qaunarta da ganin girmanta,ta bangaren lukman kansa yana mamakin yadda hankalinsa yake a kwance,sau tari ma sai ya mance da wata karima,kwanciyar hankali da nutsuwa ya samu sosai irin wadda bai taba samun irinta ba tunda ya fara aure,ba shakka sumayya ta dabance,zai kuma yi fatan kasancewa da ita har qarshen rayuwarsa,hatta da mai gadi da mai aikin gidan sunga sauyi,sun kuma ga banbanci,suma sun samu ‘yanci.

       Kwanci tashi har aka kusa shafe wata biyu ba motsin karima,sam sun mance ma basa maganarta,banda yaran da wani lokaci zasu dan tada zancanta shikenan an wuce gun,ta maida qaunar dake tsakaninsu baki daya saboda haka nuwaira ta samu matsayinta na babba a gidan,a yanzu takan iya tsawatarwa dukkaninsu sabanin daa da bata isa ba,basma ma na iya dungurinta ta wuce,da tace musu abu babu kyau zasu daina saboda ta gaya musu wanda keyin abinda babu kyau Allah zai sashi a wuta,ta wassafa musu yadda wuta take dai dai da tunaninsu yadda zasu gane haka ma aljanna,don haka da tace abu da kyau tofa zasu shiga yi saboda sun san aljanna sun san wuta.

       Da kanta ta nemi lukman kan ya sanya yaran islamiyya,saboda duk wanu ilimi da zai basu matuqar babu karatun addini aikin banza ne,ya yarje mata kan ta nema musu ya amince,da kanta ta duba islamiyar dake qarshen layinsu,ta gamsu da yanayin karatunsu saboda haka ta yankar musu foam,cikin kwanakin da basu wuce uku ba aka gama musu komai har dinkin unifoarm suka fara zuwa,su kansu yaran murna suke da fara zuwa makarantar,idan suka dawo tare suke bitar dukka karatuttukansu,wani dadi hajiya da lukman din ke ji,sai yanzu suka gane tabbas ashe da rayuwa suke cikin duhu sai da Allah ya kawo musu SUMAYYA HASKE.

    KUNDIN QADDARARTA

      Ya sake bude mata shafi ne daga lokacin da karima ta cika wata biyu da rabi da barin gidan,sauyin data fara gani daga lukman din,kusan tun bayan tafiyar karima sumayya ta dorashi kan ibada saboda gunewa faruwar wani abu,cikin sati gaba daya ta fuskanci ya zama mai son jiki da wata muguwar kasala,da qyar yake iya sallolinsa na farilla balle akai ga na nafila,idan qur’ani suka dauko zasuyi tilawa yadda suka saba sai ya soma gyangyadi daga nan sai bacci,idan sallar asuba ce kullum sai ya makara sai tayi da gaske,duk wani abu na ibada ya zama very lazy akansa,tun abun na bata mamaki har ya soma bata tsoro,hakan ya sanya ta samu hajiya da maganan,sam bata kowa komai ba tace sumayyan taci gaba da haquri da kuma qoqarin ci gaba da dorashi a hanya har ya daina,kuma itama zata yi masa fada
     A hankali sai abun ya soma cin tura,hatta idan yana bacci bai da aiki sai kiran sunan karima,idan ya tashi kuwa washegari haka zai yini babu wannan walwalar sam.haka kawai yake jin rayuwarsa da zuciyarsa cikin takura da qunci,ji yake kamar yana cikin wata kurkuru,burinsa kawai yaga karima cikin gidan,saidai duk da haka bai taba furtawa sumayya ba.

      Bayan sati d’aya

         Bayan sallar isha’i ne dukkansu suna zaune a falom gidan banda hajiya dake bangarenta saboda yau da wuri ta kwanta,sumayya da nuratu da nuwaira na zaune tana koya musu aikin gida(assigment)da aka basu a makaranta,basma na saman kujera tana bacci tun sanda suka gama cin abincin dare,sai islam dake kwashe kwanukan da suka ci abinci da su tana shigarwa kitchen.

       Lukman ne ya fito falon a gaggauce wanda tunda ya dawo daga kasuwa yana cikin daki bai fito ba sai yanzu,hannunsa riqe da dan mukulli,daya hannun nasa kuma riqe da hularsa,kana ganinsa kamar wanda aka jefo ko aka tunkudo,daga kai sumayya tayi tana dubansa sanda ya giftasu zai fice ganin bai cewa kowa komai ba
“Abban nuwaira” waiwayowa yayi yana dubanta tare da amsawa
“Ina zaka fita haka tara na dare?” Ta fada a marairaice
“Sorry airphort zani,yanzu zamu dawo” ya fadi yana ficewa da sauri jin wayarsa na ringing,kanta ta maida suka ci gaba da assigment din da yaran,hakanan taji gabanta na yawaita faduwa,hasbunallahu wa ni’imal wakil ta dinga maimaitawa,suna gamawa ta tattara yaran duka suka tafi dakinsu,sai da kowa ya sanya kayam baccinsa ya karanta addu’ar kwanciya bacci suka kwanta sannan ta rufo musu dakin ta koma nata dakin,alwala tayu tayi shafa’i da wutirinta sannan ta zauna ta karanta suratul mulk,har ta gama abinda take bata ji shigowarsa ba,saboda haka ta sanya hijabinta ta nufi bangaren hajiya.

      A kashingide ta sameta riqe da carbi,ganin sumayyan ya sanyata zama tana murmushi
“Yanzu kuwa nake zancanki a zuciyata” itama murmushin take tana cewa
“Hajiya baki bacci ba?”
“Kin ganni nan wlh banyi ba,gabana ne yake ta faduwa sai na tuna dazu banyi waraddallahu ba,sai nake yinta yanzu (waraddallahul lazina kafaru bi gaizihim lam yanaluu khairaa,wa khafallahul mu’umininal qital,wa kanallahu qawiyyan aziza,ana karanta ta ne qafa dari bayan sallar asaba kariya daga dukkan kaidin wani maqiyi dake nufarka da shi in sha Allah)”
“Ai gwara hajiya” ta fada tana tunanin faduwar gaban da itama take ji tayi dai dai data hajiya kenan
“Ina lukman din kuma?”
“Ya dan fita ne hajiya yara kuma sun kwanta saboda makaranta goben”
“Sannunki kedai sumayya,Allah yayi albarka” “amin hajiya”ta fada tana murmushi kanta a qasa,shiru ne ya biyo baya kafin su soma taba hira kadan kadan,ganin har sha daya na dare tayi ya sanyata yiwa hajiyan sallama ta koma sashenta.

      Tana zaune har sha daya da rabi sannan taji muryar lukman,a hankali ta tashi ta leqa,shine a gaba janye da akwati daya hannun jaka,sai KARIMA dake biye da shi a baya,da sauri ta saki labulen ta koma da baya tana kiran sunayen Allah,sannu a hankali nutsuwa ta saukar mata,sai ta daura alwala ta kwanta,don jikinta na bata lukman ba zaya nemeta a yau ba.

      Ilai kuwa bata sake jin motsinsa ko na karima ba har bacci yayi awon gaba da ita.

       *    *****

      Washegari yadda suka saba haka tayi bata fasa ba,ita ta tashi yaran baki daya sukayi sallar asuba,sannan ta dafa ruwa mai zafi islam ta fara yi sannan nuwaira ta dinga yiwa qananan tana tura su islam na shiryasu ita kuma tayi daga qarshe,sumayya kuma na kitchen tana hada breakfast da wanda zasu tafi da shi makaranta,abinda dukka a da basu saba yi ba amma a yanzu ya zame musu jiki.

       Sun shirya tsaf suna karyawa ya zagaya ta buga dakin karima don taga idan sun tashi ta tura yaran su gaida mamansu kan su wuce,saidai har ta gama bugunta ko tari bata ji anyi ba,abinda bata sani ba lukman na jin bugun,ya kuma san sumayyarsa ce,kamar ya zura a guje ya bude saidai ina sam bai isa ba,saboda bai samu umarni ba,tunda ta dawo a jiyan qasan zuciyarsa ke a cunkushe cike da baqinciki bacin rai da tsananin tsoronta,amma a fili tsantsar farinciki ne da tsananin biyayya bayyane a fuskar tasa,abinda zai baka mamaki tunda ta dawo bai taba kwatanta tambayarta inda ta tafi da aurensa a kanta ba kuma ba tare da izininsa ba har na tsawon wata biyu ba,a lokacin ma yana bandaki yana wanke mata tana son shiga wanka saidai ya hada qura a tsawon wata biyu da bata nan tunda ba wani ke shiga ba gun nata na a rufe ne.

       Dawowa tayi inda suke kowa ya kammala mai adaidaitan dake kaisu ma ya iso ta dubesu
” mamanku fa ta dawo jiya da daddare”ta tsammaci zata ga tsantsar farinciki a fuskokinsu,sai taga babu yabo ba fallasa,babu wani zumudi ko doki,nuwaira kuwa tsoro da fargaba ne ma ya mamayeta,a haka ta rakasu suka fice sannan ta dawo ta gyara falo zuwa kitchen ta barwa mai aikinsu wanke wanke idan ta iso tayi wanka ta leqa bangaren hajiya,sai ta sameta tana bacci,saboda haka ta mata ‘yan gyare gyarenta ta fito ta barta ta dawo falo ta zauna tana jira sha daya da rabi tayi ta karya,sai ta kunna t.v tana kallon arewa 24 don ta debe mata kewa,zuwa yanzu sum shaqu sosai da yaran,idan basa tare duk sai taji babu dadi kasancewarta mai son yara.

       Tana jiyo qarar bude qofar karima amma bata maida hankalinta kai ba har sai da taji cikin taqama tana fadin
“Ina yara na” cikin ladabi kamar bawa da uban gidansa taji lukman na cewa
“Eh sun tafi makaranta ai sumayya ta turasu” cikin harzuqa tace
“Eh wato suma an shige musu za’a shanyesu a rabani da su kenan?” Sai ta saki wani shu’umin murmushi tana kada kai
“Mu zuba mu gani,muje ka rakani naga hajiya nata salon ita kuma” ta fada tana yin gaba,jiki na rawa yana tafe yana waiwayen sumayya yabi bayanta,kai ta jinjina bayan fitarsu
“Innalillahi wa ‘inna ilaihi raji’un” ta fada tana kada kai ganin hannun agogo nason komawa baya game da lamarin lukman din.

   Zuwanta gun hajiyan ta taddata fiye da yadda ma ta barta,don fada hajiyan ma ta mata kan dalilin tafiyarta wani gu bayan tana da aure,sosai hajiyan keji qarfin zuciyarta sam babu wani dar da taji balle taji tsoron karimar,sai lokacin ta yadda lallai idan kayi sakaci da addu'a babu abinda ba zaya iya faruwa da bawa ba duk da cewa akwai QADDARA amma babu abinda ke sauya qaddarar irin ADDU'A.


 Ko da rana da yaran suka dawo sun gaidata,baki ta saki tana kallon yadda suka sauya baki daya,tana kallon yadda suke girmama nuwaira da islam,lallai sumayya ta sauya mata yara,ya akayi bata sanya an musu farraqu ba ita da au ta barsu suka shaqu haka,tana gani suka sauya kayansu zuwa na islamiya bayan sunci abinci,suna sanya hijabansu sumayya na tsakiyarsu tana hada musu litattafan islamiyar su kariman ta banko qofar dakin tana huci,tsayawa tayi tana dubansu fuska a tsuke,sumayya data kalleta saita maida kai taci gaba da abinda take

“Laaa,mama bakiyi sallama ba fa,kuma babu kyau shiga gu ba sallama” nuratu ta fada,mamaki ya kama kariman sai ta waiwaya tana kallonta amma sai ta wayance da cewa
“Ku cire kayan nan,babu wata makaranta da zaku sake zuwa daga dawowarku daga boko ko hutawa bakuyi ba” islam ce ta maqe wuya tana cewa
“Mama ki barmu muje,idan mun dawo ma huta din,idan kana fashi fa ana wuceka a karatun” ido ta kuma zarowa mamki na sake kasheta,lallai sumayya tayi amfani da irin surkullensu ta rabata da yaranta,tsawa ta daka musu tana cewa
“Don ubanki da ni kike jayayya,ku cire kayanku nace babu inda zaku” sumayya ce ta bar abinda take ta tako zuwa inda take tana cewa
“Haba maman nuratu,meye na zagi har haka?,ina cewa ke zaki fi kowa farincikin zuwan yaranki makaranta,ba girmanki bane” sai ta waiwaya ga yaran da sukayi carko carko suna kallon karimar
“Maza ku wuce ku tafi mamarku ta haqura” da sauri suka fice kuwa daya bayan daya,sai da suka kammala ficewa tas sannan karima ta kalli sumayya
“Yaro man kaza,ke da su baki daya baku da bambanci a gurina,lokaci na baki shi nake jira” tana gama fada ta fita
“Allah ya fiki,Allah ya isar min da ke akan dukkan wani nufinki,alkhairin ubangiji nake nemawa rayuwata” ta fada tana gyara dakin yaran da suka bata tare da killace kayan makarantarsu gu guda kafin su dawo su wanke

  Baki daya sai aka koma 'yar gidan jiya kan halayen mukhtar,yayin da bangare guda sauyawar yaranta da hajiya ke ciwa kariman tuwo a qwarya,saidai ta kammala dukkan wani shirinta na maida hannun agogo baya ranar kawai take jira,wanda hakan ya sanya ta sanyawa kowa ido,wannan kuma ya bada damar da shaquwa mai qarfi taci gaba da gudana tsakanin sumayya yaran da hajiyar.

*

 Qarfe daya na rana ne wanda saika dauka qarfe takwas ne na safe saboda yanayin sanyin da ake zabgawa a garin,tuni ta kammala abincin rana ita da mai aikin gidan qwaya daya saboda biyu na rana yaran zasu dawo ta baiwa kowa haqqinsa,kasancewar tunda karima ta dawo gidan bata ko dubi kitchen ba.


  Tayi sallar azahar dinta sai ta qudundune kan gado kafin yaran su dawo,bude qofar dakin nata da akayi shi ya sanyata daga kai ta kalli qofar,karima ce cikin kwalliya da daurin ture kaga tsiya,jambaki kamar zai digo daga bakinta,itace a gaba lukman na biye da ita janye da trolly,sallama kariman tayi wadda ta bawa sumayya mamaki,qarasowa tayi bakin gadon tana duban sumayya

“Mijinki ko mijina?….oho koma meye,shi na rako ya miki sallama zaiyi tafiya,wadda itace zata kasance sallama ta qarshe tsakaninku” ta qarashe tana dariya dariya,ta waiwaya ta dubi lukman dake tsaye,fuskarnan tamkar zai sanya kuka ,amma tana dubansa sai ya saki murmushi
“Bari na baku guri ko don kuyi sallama sosai” sai ta juya ta fice.

  Sakin akwatin yayi ya qaraso inda take ya zauna gefanta,sai ta tashi daga kwanciyar ta zauna sosai tana kallon fuskarsa gabanta na faduwa

“Kiyi haquri sumayya,kiyi haquri don Allah,ba laifina bane sumayya,haka nan nake jin bazan iya ci gaba da ke ba,haka kawai nake jin idan naci gaba da zama da ke akwai cutarwa,sumayya ki yafemin akwai QADDARAR dake bibiyar rayuwata,ina sonki har cikin zuciyata amma bazan iya zama da ke ba….”
“Ya isa lukman,ka fadi abinda kake son fada,ka fadi a wuce gurin” ta fada cikin rawar murya,bai kai ga cewa komai ba karima ta sake shigowa dakin,cikin daga murya tace
“Wai me kakeyi ne hakan har yanzu,kasan dai jirgi baya jira saidai a jirashi ko?” Ta fada tana tsareshi da ido,cikin sanyi jiki ya sanya hannunsa a aljuhunsa ya fiddo takarda a ninke ya miqa mata,hannu kawai ta sanya ta karba,koda baiyi mata bayani ba tasan takardar meye,saboda haka bata da buqatar budeta,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki haka ya miqe yaja akwatinsa yana waiwayenta har ya fice karima ta rufa masa baya.

  Cikin dogon tunanin da batasan tsawon lokacin data dauka cikinsa ba taji islam na girgiza kafadarta

“Momy,tun dazu muke sallama shiru baki amsa mana ba” sai ta daga kai ta kallesu,dukkansu suna tsaye gabanta suna kallonta cirko cirko,alamun damuwa duka sun bayyana kan fuskokinsu,tausayinsu sai ya lullubeta duk da a yanzu tafi jin tausayin kanta,don nasu mai sauqi ne,qwalla ta cika mata idanu amma sai tayi ta maza ta hadiyeta,ta qaqalo murmushi tana cewa
“Wa’alaikumus salam warahmatullahi wabarkatuhu,banjin sallamar taku bane,muje maza a shirya yau kun dawo a makare ko?” Ta fadi tana saukowa daga kan gadon,biyo bayanta sukayi kowa na bata labarin yau na makaranta,tana shiryasu tana biye musu,yayin da qarqashin zuciyarta ke a cunkushe,tausayinsu naci gaba da lullubeta musamman nuwaira,duk da tana da yaqinin insha Allah ba zata tozarta kamar baya ba tunda a yanzu an samu kan ‘yan uwanta da kakarta,sosai tayi jarumtar danne damuwarta,saidai duk da haka nuwaira sai da taso dagota,don ta saci kallonta sai daya taga tana dauke qwalla,duk sai yarinyar ta tsargu taqi sakin jiki,duk inda sumayyan tayi tana biye da ita da idanu,har suka gama dabdalarsu bataji motsi ko giftawar karima ba,da haka ta shiryasu suka fice,ko sanda zasu fita din sai data juyo ta sake kallonta ita kuma ta rakata da murmushi.

   Sai data fara hada kayanta sannan taji kuka ya qwace mata,bakin gado ta koma tayi kuka san ranta sannan ta hada duk abinda zata buqata cikin akwati ta zira hijabinta ta janyo akwatin nata bayan ta saka takalmanta.


 Sallama tayi bangaren hajiyan ta amsa mata tana murmushi tana tsokanarta

“Yau sanyi ya boyeki ko sumayya” ganin yanayin fuskar sumayyan ya katse fara’ar hajiyan,gefan hajiyan ta zauna kanta na a qasa
“A’ah lafiya kuwa sumayya?” Cikin rawar murya tace
“Zuwa nayi muyi sallama hajiya zan tafi” cikin tashin hankali tace
“Sallama,tafiya zuwa ina?” Kasa bata amsa tayi saita miqa mata takardar dake nade a hannunta,da sauri hajiyan ta karba tana dubawa,salati ta saki.”yaushe hakan ya faru?,me yasa ban gaya min ba dazu yamin sallama zai je ghana,sumayya….”sai ta rasa abinda zata fada
“Haka lukman zaimin?,to wallahi nima bani zama a gidansa,yaci gaba da zama da karima ita kadai” Cewar hajiyan,sai kuma ta saki kuka,da sauri sumayya ta goge nata hawayen ta kama hannun hajiyan tana girgiza kai
“A’ah hajiya don Allah ki daina masa kuka,zaki sake jefashi cikin wani bala’in bayan bai fita daga wanda yake ciki ba,hajiya,lukman danki ne ke kika haife abinki,ke kika san zafinsa,idan bakiyi yaqi a kansa kin saita rayuwarsa ba duk duniya wazai miki wannan aikin,hajiya ke zaki zauna kici gaba da aikin da na fara”wajen mintuna ashirin ta kashe tana yiwa hajiyam bayani tare da jan hankalinta sannan ta fara samun nutsuwa
” naji sumayya,nan zaki zauna gurina,tilas na nemo lukman duk inda ya tafi,dole ya dawo da ke,akwai sauran igiya daya tsakaninku”kai ta kada tace
“A’ah hajiya,kada ki tilas ta shi wanda hakan zai iya haifar da wani abun daban,babu abin buqata a yanzu fiye da dawowarsa kan hanya,Allah ne mafi sani kan dalilin faruwar hakan,na yadda cewa wannan ma na cikin QADDARAR rayuwa ta,koda yaushe Allah nake miqawa zabi kan rayuwata ya zaba min abinda yake gani shine dai dai ba abinda ni nake ganin shine dai dai ba,na gode masa ma da ya bani ikon fiddaku ke da su islam daga halin da na riskeku,abun da nake so hajiya kimin alqawari shine,ba zaki sake zubda masa qwalla ba,ba zaki saki addu’o’inki ba,ba zaki bar su islam su koma irin rayuwarsu ta baya ba,sannan ba zaki gaji da nemawa lukman kubuta da tsiraba,wannan yaqin naki ne,duk na dora miki hajiya zan kuma tayaki da addu’a”
“Insha Allahu sumayya in sha Allahu,Allah ubangiji ya albarkaci rayuwarki,kuma in sha Allahu ina mai tabbatar miki da yardar Allah zaki sake dawowa gidan nan,duk inda lukman yake zan nemeshi zan nemeshi ya dawo da ke” ta fada zuciyarta a raunane,cikin irin wannan yanayi mai ban tausayi sukayi sallama.

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE