KUNDIN KADDARATA CHAPTER 44 BY HUGUMA
Duk yadda ta kai ga tunanin duniyar gidanta zata sameta yadda takeso ba haka abun yazo mata ba,komai na neman lalace mata bayan ta tabbatar da cewa tayi nasarar tuge sumayya daga gidan,gaba daya yaranta yadda ta sansu a yanzu ba haka suke ba,baki dayansu kansu a hade yake,qarami na girmama babba,haka babba na tausayin qarami,nuwaira na cikinsu tamkar cikinsu daya da ita,ita ke jagorancin ragamar sauran a matsayinta na babba,duk yadda taso ga sake raba kansu abun yaci tura,duka ne a yanzu basa tsoron dukanta,da tayi abu zasu ce mama babu kyau fa abu kaza,ko daya daga cikin tarbiyyar da sumayya ta dorasu babu wadda suka watsar,a yanzu haka sunfi qaunar zama wajen hajiya akan wurinta,saboda babu abinda ke shiga tsakaninsu sai duka hantara da tsawa saboda basa mata yadda takeso,babu mai bin umarninta cikinsu matuqar ba kan dai dai bane hatta da qaramarsu basma,bata fuskanci sumayya ta gama da rayuwar gidanta ba sai da yaran suka dinga gudunta,idan ranar makaranta ne ba zata sanyasu a idanunta ba sai dare,don idan suka dawo daga boko don kada ta hanasu zuwa uslamiyya gun hajiya suke togewa su shirya su wuce abinsu,ranakun qarshen mako kuwa gun hajiyar suke wuni,idan ka gansu a bangarensu to wani abu suka zo yi suyi su sake komawa.
Lukman kuwa mallakar data yi masa sai ra soma damunta,ba irinta take buqata daga gunsa ba,ya zama kamar irin dolayen nan,komai tace sai yace to,ya zama kamar qaramin yaro,hatta wanka da cin abinci sai tace yayi,sai ya zame mata qarin nauyi cikim rayuwarta,bashi da wani tunani ko kadan,ko wuta tace ya sanya hannunsa ba musu zai tsumbula,abinda ta fuskanta har yau sumayya na maqale cikin zuciyarsa,sau tari zai zauna ya yita kallon qofar dakinta babu qaqqautawa har sai tazo ta koreshi,hakanan ko sunan sumayya yaji an kira koda a hanya ne sai yayi firgigit kamar wanda aka tasa daga bacci,idan kuwa su nuwaira na zaune suna hirarta sai ya zauna daga gefansu yana saurararsu yana tambayarsu kan wasu abubuwa ko sanya musu baki,a kan hirarta da suke zama suyi sai da karima ta tara su ta musu dukan tsiya,ta kulle nuwaira kuma a daki sai da hajiya ta shigo taci mata mutunci ta bude ta tace kada kuma ta sake dukar mata jikoki itace abar a daka ai basu ba,nan ta saki baki ta dinga caccabawa hajiyan magana,bata bu ta kanta ba ta kada kan jikokinta suka fice.
Wannan shine halin da karima ke ciki.
Kansa na sunkuye a qasa yana mai jin nauyi da kunyar abinda zai fito daga bakinsa,saidau tilas ya furta din saboda yana mai cike da fata da burin inganta rayuwa ne ta mutum uku,shi abdallahnsa da sumayyarsa,kasa magana yayi har sai da malam ya maimaita fadin ina jinka,yayin da ya abubakar ya gyara zamansa,kawu sulaiman wanda yake qani ga malam ma yazo kawowa malam ziyara suyi hira kamar yadda suka saba kasancewar su biyu suka rage raye a duniya ya tadda zuwan mukhtar din
“Malam,ina mai jin kunyar neman wannan alfarma daga gunku,nasan cewa na muku laifin da dukkan iyaye zasu ji babu dadi a cikin ransu,saidai malam wannan alfarma da zan nema ina fatan zata shafe dukkan wani abu mara kyau da ya faru a baya,sannan zata inganta rayuwar mu baki daya” dan shiru yayi sannan daga bisani ya dora
“Malam,don Allah don annabi ina son ka bani auren sumayya karo na biyu” shiru dakin ya dauka kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarsa,tsawon wani lokaci babu wanda yayi magana,jinjina kai malam yake kafin ya motsa
“Mukhtar,babu shakka kai mutum ne na qwarai,wanda shine babban abinda yaja hankalina karon farko na baka auren sumayya,na sani na shaida cewa dukkan wani abu da ya faru tsakaninku sharri ne da makirci wanda babu wanda bazai iya fadawa cikinsa ba,abu na biyu kuma sakaci da addu’a,na ukunsu rashin game hankali guri guda tare da yin dogon nazari da bincike kan lamura,ammm….mukhtar”
Sai ya dago yana mai amsawa zuciyarsa na gudu daya bayan daya,duk da cewa yana da cikakken fata na cewa zai cimma nasara
“A qa’ida ta addinin musulunci bazawara ita ke da ikon zabawa kanta miji,saidai idan har anga tana neman jefa kanta wajen wanda bai cancanta ba bayan ga wanda ya cancanta a gefe,kada ka manta sumayya bazawara ce ita ke sa ikon zabawa kanta miji duk da nasan cewa ko a yanzu nayi mata zaben miji ba zata musanta min ba,to amma dai zan bata damarta,mukhtar,bazan hanaka neman sumayya ba,amma kadai zan amince ne idan ta yarda da aurenka”.
Shiru yayi kafin daga bisani yace
” malam,na gode da wannan alfarmar da ka yimin,amma ina mai neman alfarma ta gaba”
“Uhmmm,ina jinka”
“Malam,don girman Allah ina neman alfarma a gunka da ka karbi sadakin sumayya daga gurina,nayi maka alqawari tsakanina da ubangiji na matuqar sumayya taqi aminta da ni zan karbi sadakina zan haqura,na maka wannan alqawarin” shiru ne ya sake biyowa baya,kowa da abinda yake nazarta qasan ransa,malam na gudun shiga haqqin sumayya,yayin da ya abbakar ke tunanin tabbas dama ce wannan,don shi kadai yake iya fahimtar yaren sumayya,saidai ya hango alamun rashin amincewa qarara a fuskar malam,yayin da mukhtar ke duqe yana mai cike da fatan samun nasara,ya abbakar ne yayi saurin yankan hanzarin malam din
“Malam,ina ga ka bawa mukhtar wannan damar,domin ni na shaida cewa sumayya na son mukhtar,hakanan na tabbata ba za’ayi nadamar karbar sadakin nan ba in sha Allahu gyara ne zai tabbata a tsakaninsu” kusan abinda kawu sulaiman ke ayyanawa cikin ransa kenan,don ko shi yana tausayin sumayya da abdallah,saboda haka ya ari bakin malam ya ci masa albasa
“Kaje muntari,an baka wannan damar,kaje ka kawo sadakin amma tare da manyanka zaka dawo”. Jinsa yayi kamar ba a duniya yake ba,godiya ma rasa wacce iriya zaiyi,ya tabbata yana jin karsashin samun nasara da shawo kan sumayyansa.
Kasancewar juma’a ce ta zamo washegarin ranar,qarfe hudu bayan sallar la’asar mukhtar ya iso gidan shida kawunsa wato mahaifin abdur rahman da kuma baffansa wanda yake wa ne ga innarsu da qanin innar yasu su hudu kenan,kawu sulaiman da babban dansa sai yaya abubakar su suka sake karbar sadakin sumayya karo na biyu,wanda ita wadda ma ake batun sam batasan ana yi ba,don a lokacin ta tafi kitso,ta dawo dai ta tadda mutane cikin sitting room din malam,saidai batasan ko su waye ba tunda bata shiga ciki ba cikin gida ta zarce,bayan malam din ya sallami kowa ya shigo cikin gida ya tadda mama ya buqaci ganinta sannan ya sanar mata tare sa gaya mata baya son ta sanrwa kowa har sai sun hada kansu da kansu,to ita din macace,kuna tasan burin kowacce mace ta zauna da uban ‘ya’yanga,hakanan kowa ya san nagarta da kyawun halayen mukhtar tun kafin wannan qaddarar ta afkowa rayuwarsu.
ZAINAB
Tunda ta farka daga suman da tayi take qaraji tana kuka,sai data tada hankalim duk marasa lafiyan dake dakin,babu yadda zinatu batayi kan ta lallabata ba amma taqi yin shiru,duk yadda take jin dadin halin da taga zainab din a ciki amma ji take kamar ta zura da gudu,dadi take ji sosai da wannan labarin na samuwar cutar qanjamau jikin zainab din,ganin yadda zainab din ke firgita musu marasa lafiya ya sanya suka canza mata daki.
Kusan kwana tayi a haka kafin daga baya ta fara sassauta qugin da takeyi saboda ta fara jin sassaucin radadin da take ji a zuciyarta.
Tana jingine a bango har zinatu ta gama bata shayin,saidai har a lokacin bata ce komai ba sai faman jinjina kai da take,kanta ta daga ta kalli zinatu da jajayen idanuwanta kamar na maza murya a kausashe tace
” kin gayawa wani a gidan mu abinda ke faruwa ne”kai ta kada tana ajjiye kofin hannunta
“A’ah,babu wanda na gayawa”
“To bana buqatar kowa ya sani”
“To” kawai zinatun ta fada tana dariyar mugunta cikin zuciyarta.
“Cutar qanjamau zinatu” tayi furucin tana kallon zinatu tamkar mai neman tabbaci kan wata magana,cikin fuskar tausayin qarya tace
“Don Allah ki bar daga hankalinki zainab,mutum nawa ne masu irin cuwin ke rayuwarsu hankali kwance”
“Dalla can malama daqiqiya kawai,bani da dama kenan ta komawa mukhtar ko kin manta?” Shiru zinatu tayi zagin da tayi mata yana mata ciwo amma ba zata iya maidawa ba
“Zinatu,hakan fa yana nufin mutuwata gab take da ni kenan”
Kallonta kawai zinatun tayi ba tare da tace komai ba,kamar zararriya sai ta miqe tsaye tana girgiza kai
“Inaaa,wallahi bazai yiwu ba,wallahil azim bazan mutu ni kadai ba,kai ka zama silar kasancewata cikin wannan hali,kaine sila,kai ka jawo min” ta fada tana zarya cikin dakin,mayafinta ta figa ta yafa tana fadin
“Ki nemo kudinsu ki biyasu ki sameni a gida zamu warware” tayi maganar tana ficewa daga asibitin.