KUNDIN KADDARATA CHAPTER 47 BY HUGUMA


abu na biyu da nake so makaranta su gane shine,haqiqa Allah baya barin wani don wani yaji dadi,ko kuwa don kuna tsaka da farinciki sai Allah ya kasa dauke bawansa alhali ajalinsa yazo?,na tabbata ni ke ko kai an taba dauke mana masoyanmu,uwa,uba, ‘ya’ya,qawaye maqwafta ko dangi,wala allah muna tsaka da jin dadin rayuwarmu bamu zatan musu mutuwa ba,ba kuma tare da sunyi sallama da mu ba,amma Allah ya daukesu saboda lokacinsu yayi kamar yadda Allah madaukaki ke fada a alqur’ani_
(iza ja’a ajluhum la yasta’akiruna sa’atan wala yastaqdimun/idan lokacinsu yazo ba’a jinkirta musu sa’a daya kuma ba’a gaggauto da ita ma’ana su tafi alhalin suna da sauran minti daya cikin duniya)
(kullu nafsin za’iqatul maut)
(kullu man alaiha faan)
duk abinda ke kanta(qasa)qararre ne
mutuwa dole ce idan tazo sai an tafi,babu wanda zai dawwama cikin duniya ko shekara miliyan nawa zaiyi sai ya tafi,cikin dadi ko wuyar da kake ciki babu ruwan ubangiji,na tabbata babu wanda ba’a taba yiwa mutuwa ba,babu wanda bai taba rashin wani nasa ba,fatanmu Allah yasa mu cika da kyau da imani

A rude ta fada ofishin likitan tana kiransa,likita ne mai kirki,ya gane ko wacece saboda haka ya miqe kawai ya biyota,zata fada dakin ya dakatar da ita yace ta jira a waje
“Sumayya,jikin muntarin ne?” Kawu wanda idar da sallarsu kenan daga masallaci suka yo cikin asibitin suka tambayeta
“Kai kawai ta iya daga musu hawaye na bin kuncinta,don bata jin zata iya cewa komai,jiri ta fara ji yana neman kayar da ita saboda tashin hankali da mintinan da suka kwashe a tsaye,sabida haka sai ta daddafa ta zauna kan kujerar sake barandar dakin.

      Likitoci biyu ne suka zo suka sake shigewa dakin suna nan zaune,awa guda ta kusa shudewa dai dai lokacin da mama halima da zainab suka iso,yayin da malam ya fara biyawa ta police station ko an samu labarin abdallah,jikin mama ta jingina kawai ta kwantar da kanta a kafadarta ba um ba um-um,sannu maman ke mata tana tambayar jikin mukhtar din,kawu ne ya amsa mata da cewa da sauqi don baki dayansu hankalinsu bai jikinsu.

       Budewar qofar dakin ne ya ja hankalinsu,likita na farko ya wuce baice musu komai ba,na biyu ma haka,na ukun ne ya tako gabansu a hankali sannan ya dubesu
” dukkan mai rai mamaci ne wannan alqawarin Allah ne babu mai zama cikin duniya sai ya tafi,ina mai baku haquri,Allah ya yiwa mara lafiyanku cikawa,sai kuyi masa addu’a”,kuka ne da salati ya gauraye wajen,wani dogon numfashi sumayya ta ja,cikin daga murya wadda bata san ta yita ba ta furta
“INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN,ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATI WA AKHLIFNI KHAIRAN MINHA” tun daga haka bafa dada ba bata rage ba,don ba sosai take ganewa ba,bin kowa kawai take da idanuwa.

     Isowar yaya yahanasu shi ya sake ruda gurin,zubewa tayi a qasa tana kuka kamar ranta zai fita,daga bisani ta sume a nan,sai da aka bata taimakon gaggawa sannan ta dawo hayyacinta,zuwa lokacin an kammala settling na tafiya da gawar mukhtar,motar asibiti suka basu a kaishi ciki(ambulance)itakam sumayya ido kawai take bin kowa da shi,sai ajiyar zuciya da take ta faman saki har suka isa gidansu na aure,gidan da suka tanada domin sabunta rayuwar aurensu,gidan da suka ciwa burin sake gina kyakkyawar alaqa da danganta har gaban ABADAN,ashe wannan mafarki nasu bazai cika ba,ashe wannan buri nasu yankakke ne,ashe sunyi zaman qarshe da mukhtar kenan a daren jiya?,abinda ya dinga bijiro mata kenan,kallon mutane take suna kuka,sai ta dinga jin dama itace su,dama itama zatayi kuka,domin kuka ya fiye mata sau dubu akan bala’i da sukar da take ji a qirjinta.

        Cikin uwar dakanta aka wuce da ita aka zaunar da ita,har lokacin babu um ba um um sai ido kawai,a falo aka kwantar da mukhtar,aka bawa makusantansa dama suka wanke shi aka maaa suttura sannan aka buqaci ‘yan uwansa suje suyi masa sallama,take gidan ya sake rudewa da koke koke,hakanne yasa anty salma tace a bar kowa ya gama shiga sannan sumayya ta shiha daga baya,da qyar aka fidda su yaya yahanash,kuka take tana ya yafe mata,itakam ta yafe masa dan bai taba saba mata ba,tsakaninsu biyayya ce irinta d’a da uwarsa tunda ta fara riqonsa har ta aurar da shi.

      A hankali take takowa cikin falon da taimakon hajiyan abdur rahman wadda ta riqeta,gaban gawar mukhtar ta durqusa wadda ke lullube cikin likkafani aka sake rufeta da wani mayafin,kanta ta duqar zuciyarta na suya tana jin zafin yana ratsa dukkan sassan ilahirin jikinta,tana daga kai suka hada idanu da malam,da idanu ya mata nuni ta masa addu’a,hakan ya qwarara zuciyarta,a hankali ta soma fadin
“Allah ya jiqanka ya mukhtar ya gafarta maka,ya Allah ka tsareshi daga azabar qabari da fitinarsa,ya Allah gashinan yana mai buqatuwa izuwa rahamarka,kai mawadaci ne daga barin azabtar da shi,idan ya kasance mai kyautatawa ya Allah ka qara masa kan kyawawan ayyukansa,idan ya kasance mai sabo ya Allah kayi masa afuwa,ya ubangiji ga mukhtar nan,bawanka ne Allah ka gafarta masa kayi masa rahama,ka yalwata masa makwancinsa,ka wankeshi daga laifuffukansa da ruwa da qanqara kamar yadda ake tsaftace farin tufafi daga dauda,ka sauya masa gida wanda yafi gidansa,da iyali wadanda suka fi nasa,da mata wadda tafi tasa…….”sai ta sake yin qasa da kai,karo na farko da hawaye ya samu gurbi cikin idanuwanta,babu wanda bata burgeshi ba a gun da irin jarumtarta,kamar yadda babu wanda tausayinta bai ratsa shi ba,alfaharin haifar diya irin sumayyan ta kama malam,Numfashinta ne ya yanke,duhu ya fara mamaye idanuwanta,kunnenta ya daina jin komai,daga nan ta daina gane komai sai daukarta akayi aka fita da ita,kamar yadda aka dauki gawar mukhtar zuwa gidansa na gaskiya,gidan dake jiran kowanne bawa.

       Bata sake sanin inda kanta yake ba sai gab da sallar la’asar,har ana shawarar kaita asibiti idan aka kammala sallar la’asar din bata farfado ba,da kalmar shahada ta farka,daga bisani kuka ta sake qwace maga,qanqame anty salma tayi tana rusa kuka mai tsuma zuciya,wanda hakan ya sake sanya wadanda ke dakin fashewa da kuka,babu wanda bai tausaya mata ba,ba shakka mutuwar miji babban al’amari ne gun diya mace,mijin ma irin mukhtar,shiru kam yaqi ywuwa a gurinta,har sai da malam ya shigo da kansa ciki wanda basu jima sa dawowa daga wajen ‘yan sanda ba,hankalinsu a tashe yake don babu labarin abdallah,baiso wannan labari ya kai kunnen sumayya,so yake kafin komai ya lafa a ga abdallahn a duk inda yake,ya jima da ita a daki kafin ya fito,tayi shiru amma har hanzu hawaye basu bar bin kuncinta ba,haka nan bata fasa ambatar innalillahi ba cikin zuciyarta.

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE