KUNDIN KADDARATA CHAPTER 48

Cikin kwana daya tal amma ji take duniyar ta mata daurin huhun goro,babu abinda qwaqwalwarta keyi sai bitar rayuwarta da mukhtar,idanunta sunqi dakatawa da zubda hawaye dai dai da second d’aya,cikin kwana gudan tal ta rame ta fige ta fita hayyacinta,ba ta cewa uffan sai ido kawai,ko gaisuwa aka yi mata saidai ta amsa da ka,daga jiyan zuwa yau babu abinda ta kai bakinta illa ruwa da take kurba lokaci zuwa lokaci idan an matsa mata,sam abincin bai iya wucewa ta maqogaronta balle ya kai ga uwar hanjinta,a washegarin ranar anty dije ta iso hankali tashe,sai sabon kuka ya balle tsakaninsu,ba qaramin tausayawa sumayya take ba,yarinya qarama amma taga jarabtar rayuwa iri iri,da qyar aka sha kansu.

      Bayan sallar la’asar tana saman abun sallah tana lazumi cikin dakin gadonta,anty salma ya yahanasu antu dije da mama ne zaune a dakin sai ita ta biyar,sai yaran ‘yan uwa dake gefe suna wasa,idanuwanta da hankalinta na kansu
“Abdallah” sunan da ya fado kanta kenan,cak ta tsaya da lazumin tana lissafin ina abdallah yake?,bata ga abdallah ba duk cikin kai komon yata,haka bata ganshi gaban gawar mukhtar ba
“Ina Abdallah” lokaci na farko da tayi magana tun bayan tsawon awanni kusan talatin,dif dakin sukayi don babu mai amsar bata,tuni hawaye ya cika idanuwan anty dije ta sanya mayafinya ta soma sharewa,mama tafi kowa shiga cikin taraddadi,don ba’ayi minti goma ba malam ya kirata yace suna gun ‘yan sanda,sumayyan dai bata yi maganar sa ba ko?tace masa eh
“Ina abdallah yake?” Ta kuma tambaya wannan karon tana dubansu hawaye na bin kuncinta
“Don Allah kuce min wani abu kunyi shiru,ko shima ya mutu ne?,shima yabi sahun mukhtar?,ku daina boyemin ku gaya min don Allah”
“Abdallah na nan a raye bai mutu ba,kiyi haquri kinji sumayya” inji yaya yahanasu ta fada tana share hawaye,murmushi mai dauke da hawaye tayi wanda ya sanyasu yin jagale suna kallonta
“Meye na boyemin idan shima ya mutun,ban isa nayi komai ba saidai nayi haquri,ku fadan don Allah na sashi cikin addu’ata idan har ya mutun” mama ce cikin hawaye ta taso ta iso gabanta ta soma share mata qwallar
“Haka ne sumayya,kiyi haquri kan wanda kika yi,a iya binciken da jami’an tsaro sukayi abdallah bai mutu ba,saidai ya bata an rasashi ba’a san inda yake ba,amma in sha Allahu ana gab da samunsa ‘yan sanda na nan suna bincike kan inda yake” shiru sumayyan tayi tana duban maman,sai ta sake qas da kanta bata sake cewa komai ba sai taci gaba da jan carbinta,ta riga ta sallama abdallah ya riga ya tafi kamar yadda mukhtar ya tafi ya barta,kasa zama anty dije tayi sai ta miqe ta fice tana hawaye,ba’a yi sallar magariba ba wani zazzafan zazzabi ya rufeta.

      Zazzabin shi yaci gaba da jigata ta da wahal da ita tsahon kwanaki biyu har ranar sadakar bakwai,qarin ruwa kam ta shashi har ta godewa Allahi,idan ka ganta baka cewa itace sumayya,ita kadai tasan me take ji a gangar jikinta da zuciyarta,ta riga data sallamawa rayuwa baki daya.

     **  *****

     Zaune take a falon gidan sanye da hijabi da carbi,idarwarta kenan daga sallar walha,gidan ba kowa sai yaya yahanasu wadda ke zuwa kullum ta wuni ta tafi anty dije halima da matar kawun abdur rahman,tun shekaran jiya da akayi sadakar bakwai kowa ya watse aka barta da su.

     Anty salma ce ta fito daga kitchen dauke da cup ta qaraso inda sumayya ke zaune
“Ungo ai kin idar da sallar karbi kisha” kai ta gigirza hawaye fal idanuwanta
“Bazan iya sha ba anty salma,babu dadi,tsayamin yake a wuya”
“Haba sumayya,haba sumayya,ana yabonki sallah kuma ya haka,kowa na yabawa tawakkalin da kikayi,akwai ciwo rashin miji da batan da’a,amma kinsan babu yadda za’ayi rayuwa ta yiwu ba abinci,tunda abun nan ya faru baki sake sanya abu cikinki ba,mu kanmu da muke tare da ke kinsan ba zamu ji dadi ba,daure ki karba kisha don Allah ko kurba uku ce” hawaye na bin kuncinta ta karba ta kafa kai tare da rintse ido kamar wadda zata sha guba,kurba uku tayi masa ta dire kofin tana maida numfashi,dai dai lokacin da aka yi sallama bakin qofar falon amsawa sukayi halima ta duba tace ‘yan sanda ne,anty dije tace eh abban laila ne ya turosu su shigo suke bincike kan batan abdallah da musabbabin hadarin mukhtar,gaban sumayya yayi mummunan faduwa idanuwanta kan qofar falon har suka shigo,suka samu gu suka zauna,tambayoyi suka yiwa sumayyan suna saurarenta har ta gama,daya daga cikinsu wanda da alama shine babbansu ya fiddo wata leda wadda kana iya hango abinda ke ciki ya miqo musu
“Kince gab da lokacin da abin zai faru kunyi waya,munga komai nashi cikin motar saidai bamu ga wayar tasa ba,ko akwai wanda yayi kiran lambarsa tun bayan rasuwar?” Anty yahanasu dake zaune gefe tace
“Gsky a’ah”
“Ok,ko zamu iya samun lambar wayar tasa?”
“Eh” anty dije tace,ita ta karanta masu lambobin yana rubutawa,ya kammala rubutawa sannan ya latsa kiran,cikin second uku kiran ya shiga,tsit dakin yayi kamar babu wani mai numfashi suna sauraren shigan kiran wayar
“Waye me magana” wata murya ta fada daga can bangaren
“Am,mukhtar nake nema don Allah” wata dariya aka saki wadda cika falon kasancewar a hands-free ya sakata
“Ai mukhtar ya dade da wulawa barzahu,idan ma qarin bayani ake nema bari nayi maka,mun kashe mukhtar,hakanan d’ansa yana hannunmu mun daukeshi,zamuyi masa irin tarbiyyar da muka ga dama mu kuma moreshi sannan mu aikashi inda babansa ya tafi,na tabbata wannan ya ishi babbarsa itama tabi sahunsu” qit aka katse kiran,salati suka dauka baki dayansu,basu ankara ba sai ganin sumayya sukayi ta sulale a gurin,tashin hankali sabo,a rude baki dayansu sukayi kanta.

      A hankali ta bude idanuwanta tana fadin
“Allahumma la sahla illa ma ja’altahu sahla,wa anta taj’alik hazna iza shi’ita sahla” idanunta ya sauka cikin falon,wannan karon mutane sun dadu sabanin dazu,malam ya abbakar kawu da mijin anty dije wato umar farouq duka suna cikin falon,sai ta sanya kuka tana kiran sunan Allah,tausayinta ya kama kowa,wannan karon babu wanda ya hanata,don sunsan cewa abun ya mata yawa,dole ta zubda hawaye ko zata samu sauqin radadin dake cikin zuciyarta,a qalla kimanin minti goma tana kukan mai fidda sauti kafin ta koma yin na zuci,sai a sannan ‘yan sandam suka samu damar yin magana,wanda yayi magana dazun wannan karon ma shi ya maganta
“Alhamdulillahi mun gode Allah,ba shakka wannan bincike ya zo mana cikin sauqi,cikin ikon Allah sun sauqaqa mana wahalar bincike”
“Haka nace cikin zuciyata ASP,yanzu me kake ganin za’ayi,don ya kamata cikin gaggawa a nemo yaron kada  su samu nasarar cutar da rayuwarsa” cewar mijin anty dije cikin tsananin takaici da zaquwa
“Hakane alhj farouq,ina ganin zamuyi amfani da hikimar tracing layin har don mu gano indo suke”
“Good,hakan yayi,kamar zuwa yaushe kenan ?”alh farouq ya sake fada
” daga yau zuwa gobe in sha Allahu zamu aiwatar da komai”
“Na gode ASP,na gode qwarai” alhj farouq ya fada yana bawa ASP hannu,sukayi sallama daga nan suka fice.

     Hankalinsa ya maida ga su malam
“Malam,sai mu dage da addu’a,Allah ya bada nasara a gano ko su waye,ba shakka idan aka ganosu ba zamu qyalesu ba,sai mun bi haqqin ran mukhtar da yardar Allah….sumayya saiki qara haquri,Allah ya baki juriya ya baki ladan haqurin da kikeyi”. Godiya sosai su malam ya yiwa farouq gajin yadda yayi uwa yayi makarbiya kan lamarin,bai gari ma sanda abun ya faru amma ya dawo ya karbi ragamar al’amarin,a nan sukayi sallar azahar sannan suka tafi bayan ban baki da suka sake yiwa sumayya.

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE