KUNDIN KADDARATA CHAPTER 8 BY HUGUMA

Cikin mintuna qalilan ta kammala jallope din taliyar ta rarraba cikin coolers,mukhtar din ta fara kaiwa,tana niyyar juyawa ta fita yace da ita
“Wannan cooler din fa na waye?” Ta dubi cooler din sannan ta dubeshi
“Na fa’ixa ne a ciki”
“Ajjiye a nan” ya fada yana gwada mata inda zata ajjiye din da idonsa,bata kawo komai cikin ranta ba ta ajjiye din ta nufi dakinta.

            Can ta taddasu sun baje suna kallo,duk da cewa kallo daya zaka yiwa yahanasun kasan tabbas har yau ranta a bace yake,ta dire cooler din tana cewa
“Ga abincinku yaya” wani banzan kallo ta watsa mata
“Eh zamu ci ai kuma zamu ambaci sunan Allah,in sha Allahu babu abinda zai samemu,makira,idan ma shiga kika tsakaninmu da fa’iza har take wannan tashan rashin kunyan to ni zanyi maganinku ke da iyan baki daya” kai ta kada ba tare da tace komai ba ta shige uwar dakinta,ta tube kayanta ta sauya na bacci,sai tayi zamanta gefan gado ta janyo RIYADUL JANNAH littafin addu’o’inta da malam ya bata wanda bata rabi da shi ta soma duba wasu shafuka.

          Sumayyan na fita ya dauki cooler din baki daya ya fita da ita waje,wasu almajirai da rabonsu ya rantse ya samu qofar gida zazzaune ya basu,take suka karba suka rabe a tsakaninsu suna zabga godiya banza ta faadi garesu.

             Yana kammala rufe gidan sukayi karo da fa’iza wadda ta dawo daga dakin sumayya ta bankade labulenta ko kallo su ya yahanasu basu isheta ba ta qwallawa sumayya tambayar ina abincinta,tana daga cikin dakin ta gaya mata yana gun yaya mukhtar.

          Dubansa tayi”ina abinci na?”banza ya bawa ajiyarta yayi wucewarsa,sai ta bishi da kallo,bata haqura ba tabi bayansa tana sake tambayarsa,wani wawan birki yaci wanda sai da ya sanyata ja da baya
“Baki daku ba kenan ko?,tare muka hada muka siyo abincin?,ko kinzo da bayi ne daga gidanku?,uban wani ne ya hanaki dafawa kici,ki fice min daga nan tun kafin na hasala na sake kikkifa miki mari” tana qunquni ta juya ta fice ranta qunci fal,ga uwar yunwar dake sakadarta,abinka da mutum mai shegen ci ta riga da ta saba.

            A tsakar gida taci karo da jamila na wanke hannunta,da gayya ta bangajeta tayi taga taga ta fadi,sai ta miqe kuwa ta lailayawa fa’izar ashar abinka da itama tana ji da tata rashin kunyar,ai kuwa fa’izan tayo kanta zata huce bisa kan nata,dai dai sanda yaya yahanasu ta qaraso tayi hanzarin riqeta ta gabza mata mari dama tana ciki da ita ne,tana waiwayowa kuwa ta cakumi wuyan yaya yahanasun take jamila ta shigarwa uwarta nan fada ya kaure tsakanin su ukun.

           Sumayya ce ta fara fitowa,cikin tashin hankali taje dubansu idanunta a waje,dambe da yaya yahanasu?,tab,lallai fa’iza ta kai,dakin mukhtar ta nufa da hanzari tana mamakin me ya hanashi fitowa,ga mamakinta yana tsaye bakin window yana kallonsu,saidai idanun nan sun kada sunyi jazur,a hankali ya juyo ya zuba mata su,itama sai jikinta yayi sanyi,tausayinta ya kamashi,babu shakka wata jarrabawa ce ta fado rayuwarsu,idanunta suka cika taf da qwalla ta tausayin mijin nata,sai kawai ya saki labulen ya taka a hankali ya fita tsakar gidan,wata gigitacciyar tsawa ya sakarwa fa’iza dake tsakiyarsu tana cin na jaki wadda tsawar sai data sanya hanjin sumayya hadewa ya cure guri guda,ta runtse idanunta tana jin ruguginta na ratsa kunnanta.

         Nuni kawai ya yiwa fa’iza da hanyar dakinta yana mata wani irin kallo mai cike da tsana,ba musu ta wuce jikinta na rawa,ya juya ya dubi yaya yahanasu sai kawai ya kamata yayi dakin sumayya da ita.

          Bakin rijiya ta zauna,sai ta kasa daurewa idanunta ya shiga fidda qwalla,wannan wacce iriyar masifa ce lokaci guda,duk wani farinciki da zaman lafiya na gidansu yayi qaura lokaci daya?,tana share hawayen idanunta tana tausayin mukhtar dinta.

           Tana zaune a nan mukhtar din ya fito ya shige dakin fa’iza,a nan ne ta jiyo tashin muryarsa saidai nan din ma bata ji duka abinda yake fadi ba,daga bisani ne ya fito,ta miqe tsaye ta isa gabansa tana kallonsa,tabbas taso ace yau ranar girkinta ne,ta lallashi mukhtar din,saidai sam bata da wannan damar,karyar da kai tayi murya a tausashe tace
“Kayi haquri don Allah yaya mukhtat,komai na duniya mai wucewa ne,jarrabawa ce daga Allah” murmushin qarfin hali ya saki ya shafi gefan fuskarta
“Babu komai my sumy,kije ki kwanta,kuma ban lamunce ki sanya abun cikin ranki ba,ki kwanta kiyi bacci sosai” ya sanya bakinsa yayi kissing  goshinta,sai ya bata kunya har ta dan murmusa,yana tsaye har ta wuce dakinta sannan ya juya nashi.

           Ko da ta isa dakin tuni ta taras da su sun rarrashe kan gadonta,sai yaya yahanasu dake zaune gefan gadon tana huci,abinda take da buqata ta dauka zata fice taji sakin qwafar da yaya yahanasu tayi,ranar kan doguwar kujerar falo ta kwana,saidai tayi qoqari kamar yadda mukhtar ya buqace ta tayi bacci ta qoqarta tayi na ‘yan awowi.


        Cikin kwanakin gaba daya mukhtar ya fita harkar fa’izan duk da cewa daman can ba shiga yake yi ba,saidai duk wani abu da yake haqqinta ne kansa yana sauke mata bakin gwargwado.

           Zaman yaya yahanasu a gidan ya dauki sabon salo,wani irin zama ake a gidan,sosai yaya yahanasun kejin haushin fa’izan gami da ganin baikenta tun farko data daure gindin dan uwanta ya zama miji gareta,sai dai kuma duk da wannan bai hanata jin haushin sumayya ba,gani taje tamkar itace ta shiga tsakaninsu.

          Duk kwanan duniya gari na wayewa da zarar mukhtar din ya sanya qafa ya fice itama fa’izan ke ficewa,ba zata dawo ba sai yaba gab da dawowa koda kuwa ranakun girkinta ne,sai a sannan zata tsiri girkin dare shima tsoron hukuncin mukhtar din ya hau kanta take,ba qaramin horata yayi ba lokacin da ya amshi maqullin locker din abincinsa daga hannunta ba,da rana kuwa saidai kowa tashi ta fishsheshi,shiga su jamila suke kitchen kansu tsaye su girka duk abinda suka ga dama,su din ma ba baya bane wajen iya barnar abinci da ta’adi,sam ko sau daya sumayyan bata taba daga kai ta dubesu ba bare ta gwadawa mukhtar abinda sukeyi cikin gidan,dakinta kam tuni ta sallama musu shi,ta dauke kai baki daya da shi saboda yadda suke abinda suka ga dama cikinsa,wani abun da gayya da gadara suke mata,koda bata tankasu ba sukan bude baki suce “kayan dakin da kudin dan uwansu aka sauya su” sau tari dariya abun yake bata,ta kuma godewa Allah da ya sanya iyayenta masu rufin asiri da zuciyar yiwa iyalinsu ne,suma sun san da haka,babu shakka da Allah kadai ne yasan halin da zata tsinci kanta ciki,hatta da kayan sawarta sai suka fara dauka dai dai da dai dai suna sanyawa idan zasu fita wata unguwa ko biki,ranar da mukhtar ya soma gani ransa ya baci matuqa,bai iya jurewa ba sai da ya kirasu ya musu jan kunne.

            Ganin haka ya sanya mukhtar yace ta debe duk wani abu nata mai amfani ta dawo da shi dakinsa,ya bude ma’ajiyarsa ya adana mata ciki.

            Fa’iza kuwa tsakaninsu da yaya yahanasun da yaran ma baki daya sai harare harare da baqar magana,wanda yawanci ma sunfi yi da jamilan ko sayyada,bata san me mukhtar ya gaya musu ba amma da alama shi ya kawo wannan dan qaramin sauyin da aka samu.

          Cikin wata d’aya kacal mukhtar ya kammala musu gyaran suka tattara suka koma nasu gidan,ko a ranar da zasu tafi din ma sai da ka kusa kwata ta ranar da suka zo din,da zagi suka rabu,ba qaramin qona ran yaya yahanasun abun yayi ba ganin mukhtar din ya gaza daukar kowanne irin mataki,abinda bata sani ba shine ya fita jin takaicin abinda ke faruwar,saidai ya riga da ya tsarama ransa sai sun gama d’aukar darasin rayuwa tukunna.


           Qarfe takwas na dare ya iso gida tun bayan fitar da yayi da safe sakamakon aiki da suke a shagon sa na kasuwa,sosai yake a gajiye tiqis,saidai yasan cewa abu mafi muhimmanci shine ya adana gajiyarsa,matuqar fa’iza ke da girki babu wani abu da yake iya tsinta ko ya dorar a wunin ranar baki daya,qarin gajiyarsa machine dinsa yau da ya masa tsiya ya baroshi gun bakinike ya tari adaidaita ya iso gida.

         Babu wutar nepa a unguwar tasu hakan shi ya sabba ba duhun da gidan yayi,sai hasken fitila daga dakin sumayya dakin fa’iza da kuma kitchen din gidan.

           Bashi da sha’awar yin tozali da fa’izar ko kadan,saboda haka ya bude dakinsa ya shige da zummar zuwa ya rage kayan jikinsa ya koma bayi ya tanadi ruwan wanka,hular kansa ya cire ya jefata saman gadonsa,ya balle maballan rigarsa ya zareta ya ajjiye sannan ya nufi window dinsa ya yaye labulen don ya bawa iska damar shigowa.

            Kamar wanda aka kira idanunsa suka sauka kan kitchen,fa’iza ya hango,da farko yayi niyyar dauke kansa,saidai wani abu da ya hango shi ya ja hankalinsa,idanu ya zuba sosai don yana son ya tabbatar da abinda idanunsa ke gane masa,baiso yayi hukunci bisa kuskure zato ko tsammani.

Sakin labulen yayi sannan a hankali ya fita izuwa kitchen din cikin takun sanda,bakin window ya isa sannan ya lafe daga jikin bangon yana kallon komai tar kamar yadda idanunsa suka soma nuna masa daga cikin dakinsa,yana tsaye harta sheqe da dariya sannan tace…………..

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE