MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 10 BY RABI’ATU ADAM SHITU

MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 10 BY RABI’ATU ADAM SHITU

mutane ana raha da shi ba, in baka san shi za ka ce mutum ne „mara fara’ a sai idan ka jibance shi ne za ka gane cewar rayuwarsa ce a haka, daga Karshe ka fahimci damuwa ce fal a cikin zuciyarsa.

Kamar kodayaushe idan Umar yana bakin aiki da

yaransa, bai iya zama ya ce komai sai an yi ba, duk abin da ya gagare su shi yake kokarin ganin ya dai-daita shi.

Can Kululuwar sama ake kokarin saka wasuna’ urorin

CCTV an saka su sau kusan biyar amma basu dai-daita yadda ake so ba, don haka yau yasanya kayan aiki don hawa ya daidaita su.

Duk da yaran na kokarin sanar da shi cewar ya bar su

su yi aikinsu ya nuna babu damuwa, wannan abin da yake yi yana sawa suna jin Kaunarsa a cikin ransu yasanya kayan aiki ya fara hawa saman domin inganta aikinsu. Bai damu da saka belt ko wani abu haka ya hawan saman ya fara gyarawa, sai da yasaita su wajen sakkowa Rafarsa ta zame ya fado yayo kasa. Ya fado kasa ko motsi bai iya ba cikin tashin hankali aka yi Asibiti da shi.

Da yake aiki ne na gwabnati take abin ya dauka ko ina zancen ake yi har gidajen talabijin da jaridu an wayi gari ana labarin faduwar Engeneer Umar Abubakar Muhammad

**

“A katafaren gidan Alhaji Hashim zaune Alhaj!

Hashim ne da matarsa Zulaihat da kuma dan sa Abas. Suna zaune akan kujeru domin hutun ranar Lahadi kamar yadda suka saba.

Tsakanin Abas da mahaifinsa sun dan dukufa cikin

•hirar ayyukan dake gabansu ya yin da Hajiya Zulaihat take sauraren labarin gidan talabijin.

Fitowar Yasmin daga muhallinta yasa suka dawo da

hankalinsu kanta. Ta yiwa musu sallama suka amsá, da jakarta ta yi shirin fita.

“Zan shiga gidan mu”

Abas ya dago ya dube ta yana murmushi “Ki jira muje tare mana saurin me kike yi?”

“Ban..” ta dakata da abin da take niyar fada ganin

iyayensa a wajen. “A’a zai fi kyau ka yi zaman tun da kana da uziri ni ma uziri zai kai ni an jima zan dawo

Ba ta sake bi ta kansa ko sauraren abin da zai ce ba ta

nufi hanyar waje.

Cikin muryar talabijin din ta ji cewar “Kwararren

Engeneer Umar Khalil, yasamu hatsari fadowa daga saman bene, a Kokarinsa na sakkowa, wannan abu ya faru ne a yammacin jiya a garin kano, a lokacin da ake kammala aikin hada na’urar CCTB na sabonta Airport din Aminu kano da ake kan yi.

Matashin bai samu raumika ba, sai dai yana cikin mawuyacin halin rai ko rayuwa a rahoton da mu kasamu daga likitoci ke nan.

Ba ta san lokacin da jakar da take kafadarta ta zabe ta

fadi kasa ba, kiris ya rage ta rusa ihu ga hoton Umar din a na nunawa a lokacin da yake Kokarin hawa saman da yadda ya kammala gyaran.

Abas ya zuba mata ido yana mamakin yadda

hankalinta ya ta shi lokaci guda. Mahaifinsa Hashim ne ya ji yana waya akan batun Umar din don haka ya kasa tantance shi din waye ga shi mahaifinsa ma yasan yaron ita kuma matarsa a ina ta san shi. Ya ta so ya dauki jakarta ya mika mata.

“Me ya faru ne?”

Da sauri ta girgiza kai ba ta ce da shi komai ba ta fice

daga cikin gidan ta nufi na su gidan. Dakinta ta shiga ta dinga rusar kuka domin ta na ganin ita ce ta jawowa Umar komai yasame shi.

Kokarin da take yi ta je gidansu Umar wadda yau

rabon ta da gidan kusan shekaru uku tun da mahaifiyar Umar ta gargade ta ta ji gargadinta kuma ta saka wa ranta daukar matakin da zai nisanta ta da duk abin da zai sa ta ji labarin sa. Amma yau ga shi ta samu labarin da ta gaza samun sukúni babu yadda ta iya gidansu Umar din ta nufa.

A lokacin da ta isa gidan a rufe ta same shi babu

kowa a kofar gidan. Ta jima a tsaye ta ma rasa abin da ya dace da ta yi, lambar Yusra ta tuna har yanzu tana da lambarta a wayarta don haka sai ta kira lambar kai tsaye.

Wayan ta shiga a dai-dai lokacin da Yusra na bakin

gadon Asibiti da yayan ke kwance. Ta dubi lambar ta ga sunan ta ras a wayar ita kanta ta manta da lambar na cikin wayarta. Ta dubi Mama da sauran yan uwanta ta dubi Yayanta ta kara wayar a kunnenta.

“Hello wake magana?”

“Ni ce Yasmin Yusra ya jikin Umar, yaya Umar yake

na zo gidan ku yanzu na ga kofar a rufe”.

“Ga shi nan lafiyarsa kalau muna Asibiti ne yanzu

haka”

“Ki gaya min gaskiya Yusra yana ina”. ..

“Yaya ya farfado ga shi nan yana kallona ma*

Cikin yanayin ciwo ya ce “Da wa kike magana Anti

Yahanasu ce?”

Ya tambayi Yusra wadda har sai da Yasmin taji

sautin muryarsa a lokacin da yake tambaya”.

“Yusra ka da ki ce nice dan Allah Yusra, sannan ina

neman wata alfarma a wajen ki, ko wane hali yake ki sanar da ni kin ji kanwata”.

“Ba matsala zan kira insha Allahu”.

Ta a jiye wayar lokaci guda. Mama ta dube ta “Wace

ce?”

“A..Am Safiya ce, wai ta zo gidan ba ma nan shi ne ta

tambaya aka sanar da ita mun taho kano”.

Kallo daya ya yi waYusra ya fuskanci karya take yi

domin yasan halinta. Sai dai bai damu da ya matsa mata ba, watakila ma saurayinta ne ya kira ta take yin karya da Safiya”

Mama ta ce Anti Yahanasu ta so ta biyo mu tana

cikin damuwa sosai, in ka samu dama ka yi mata waya da kanka za ta ji dadi”

Ya yi murmushi “Ina waya ta, yanzun ma na samu

sauqi sallama na ke bukata, Ai Allah ya tsare ba karaya ba-ba buguwa.

“To me suka ce maka?”

Khalil ya tambaya yana rike da hannunsa. Saboda

sanin abin da suka sanar da shi din zai sa su shiga damuwa da kuma tuna faruwar abun da ya wuce a baya yasa yace “Ba wata damuwa duk gwaje gwajensu sun ce suma ne kawai saboda kidima Khalil bai yadda da shiba don haka ya share zance

bai sake tada masa da maganar ba sai da Baba da Mama suka fita sannan ya ce “Na san ko me suka sanar da kai, sun ce damuwa ce da kai wacce har ta jawo jininka ya yi kasa, Umar ka saurara ka ji, lokaci ya yi da za ka gina rayuwarka kamar yadda ta manta da kai ta gina tata rayuwar, na sani cewar har yanzu kunar rabuwarka da Yasmin yana sukar zuciyarka, wannan dalili yasa ka tako ka zo gida har yanzu ya gagare ka, damuwa irin wannan na da wuyar sha’ ani amma daurewa za ka yi kamar yadda ita ma ta fita daga taka rayuwa ka fita a tata

Umar bai iya cewa komai ba sai hawaye da suka

dinga biyo masa zuciya “Yaya ka bar wannan maganar dan Allah ka da ka Kara yi min wannan maganar”.

Har zai yi magana Likita ya shigo yana murmushi

“Abokina ya dai, lafiya ta samu

‘Dukkansu suka kai dubansa ga Likitan suka gaisa da

Khalil sannan ya dubi Khalil ya ce “Ko za ka ba mu wasu ‘yan kalilan lokuta

Khalil ya ta shi jikinsa a sanyaye yana tausayawa dan

uwansa tabbas ya so Yasmin soyayyar lokaci guda, kaf gidansu. sai da suka tabbatar da cewar Umar yasauya

-“Tabbas sai ka rage tunani Umar saboda kwata-kwata abin da gwaje gwajenmu ya nuna mana zuciyarka na iya shiga hatsari saboda haka ka yi kokari ka koyawa kan ka zama da farin ciki, duk in da ka san ranka zai baci ka yi kokarin barin wajen, ka ji yaro kamar ka bai dace ace ka rayu cikin wannan yanayin ba”.

Umar ya ce “Likita me zai faru idan na kasa danne

damuwa ta?”

Likita ya dube shi “Kai

‘ma ka san mene ne,

rayuwarka na cikin hadari zuciyarka za ta iya bugawa ka yi mutuwar farad daya?”

Umar ya yi murmushi “Na riga na mutu Likita, ba ni

da wata dauriya da zan iya jure irin abin da yake sukar zuciyata, ba zan iya ba, sannan dan Allah ka da ka kara yiwa kowa bayani dangane da abin da yake damuna”.Ko me yasa?’

“Dan Allah” Ya dakatar da Likitan Likitan ya jinjina kai. Ai kuwa

bai ji ba sai da ya kira iyayensa da dan uwansa ya Kara kafa musu sharuda daga Karshe kafin sallama sai da yasanar da mai gidansu akan matsalalolin da suke damunsa da kuma kula da magungunan da ya bayar sannan ya ja kunne wajan kawar masa da duk wani abu da zai bata ransa.

Shi kansa mai gidan nasa sai da ya yi zama da

yayansa Khalil domin ya ji rayuwar Umar ta baya, domin tun da suka fara harkokinsu shi dai bai taba ganin Umar yana dariya ba, bai kuma taba tsintar Umar cikin abokai ana raha da dariya da shi ba, alhalin ya fuskanci yaron kirki ne mai amana da son kyautatawa.

Babu abin da Khalil ya boye masa, saboda haka

bayan an sallami Umar daga asibiti yasamu sauqi sosai Alhaji Nasir ya kira shi don su yi zama da sun jima suna tattaunawa a kai.

A babban falon gidan Alhaji Nasir su ke zaune bisa

mamakin Umar sai ya ga ba shi kadai ne aka gayyata ba kusan mutum biyar abokan aikinsa na kamfani.

Zaliha, Rufa’i Hajiya Binta Sa’id da kuma Ibrahim

manager.

Zulaiha wata kyakkyawar budurwa ce wacce ta

tattara hankalinta da Kulafucinta akan Umar tun a lokacin da aiki ya hada na wani kamfani wadda aikin kusan shi ne aikinsa na uku a tare da su. Ta yi supervising din aiki dan haka a ganin alaka mai karfi ta faru wacce ta samu raunin soyayyarsa a ranta, sai dai ta gaza gaya masa saboda halinsa na nuna ko in kula da kuma kaucewa a duk lokacin da ta shirya ta sanar da shi.

Ita ta fara yi masa murmushi da ya shigo cikin falon

ta kuma Kara yi masa sannu da jiki bayan ya gaida kowa yasamu waje ya zauna Alhaji Nasir ya fara,

“Babu abin da zan ce da kusai godiya musamman ga

ci gaban kamfanin mu, kun jajurce kun mayar da hankali kazalika kun rike amana wacce ita ce ta kai mu ga cin nasara. Hannuun mu ba zai rabe ba zamu ci gaba da kafa resa a fadin kasar nan da wajenta, domin bukatar mu mu ha66aka mu kuma samarwa da sauran engineers ayyukan yi, babbar reshen mu a jahar kano, na

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE