MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 13 BY RABI’ATU ADAM SHITU

Saboda kiyayyar ta hada kanta da Abas a matsayin

mata yasa ba ta iya gaya mata: cewar matar Karamin shugaban, kamfanin ce, shi kansa mahaifinta ya kasa gabatar da hakan saboda yasan idan ya yi tamkar ya soki zuciyar ‘yarsa ne”

Zulaihat ta zauna a ka ci gaba da gabatar mata da

takaddum zanen tana dubawa. “Za a iya kiran ki da talent, gaskiya sun yi kuma kin Kokarta, yanzu zan je da su, wajen Umar ya yi na shi kiyasin, kafin mu kai ga karamin shugaban kamfani, saboda komai ya tafi a dai-dai”

Lokacin da ta ambaci Umar sai ta ji gabanta ya fadi

wane Umar ta fada a cikin ran ta. Sanin cewa ba abin da zai kawo Umar nan ta share.

OFFICE

Umar na zaune a office dinsa ya hada wasu takaddu

ya nufi ofishin karamin shugaban kamfani har ya kama kofar zai bude sakatariyarsa ta sanar da shi yana zuwa.

Zulaihat ta gaya masa cewar za ta je Office din Alhaji

  • Sunusi don haka ya ga da ya tsaya jiran gwanda ya leka su gaisa da shi tun da har yanzu bai ji shigowar shugaban kamfani ba wato Alhaji Hashim. Har ya nufi Kofar zai murda ke nan ya ji muryar Abas a bayansa.
  • *Ka na da nawa, daga zuwa diban takaddu ka dauki lokaci”.

“Kai kuma kana da gaggawa, ka san mene ne sharrin

gaggawa kuwa?”

Abas ya jinjina kai “koma mene ne bai dame ni ba ka je office ka jira ni”

“Ai ni ba na jiran wadanda suke saba ka ‘ida”

Abbas ya dube shi ido cikin ido “Kai me ka dauki

kan ka ne?”

“Dai-dai matsayina, ka fahimta matsayina an sanar da

kai ko na sanar da kai yanzu”.

Ran Abas ya 6aci “Kai ka fara wuce gona da iri,

amma zan rangwanta maka ne saboda kai bako ne kaje ka fara bincike a kaina kafin ka ce za ka fara ja’inja da ni”

Umar ya yi dariya “Ka ji sakarai, waye zai bata lokaci akan bincike akan ka, idan kana mafarki ne ka farka, sannan ka

sani ni ba irin mutanen da zaka tankwara ba ne, ka bi a sannu, domin hakan da kake kokarin yi zai ja maka zubewar mutumci ka dauke ni a matsayin abokin aiki, ba wadda za ka wulakanta ba.”

Yana fadin hakan ya bar wajen Alhaji Sunusi Zulait suka fito tare da Yasmin suka fito, a lokacin da Umar ya nufi sashin office dinsa Yasmin na fitowa ta hango Umar, Umar din ta wadda take so take burin kasancewa tare da shi a fusace ya shiga office ya banko kofa.

Shi kuma Abas ganin Yasmin yasa damuwarsa ta

sauka ya fara kiran sunanta “*Yasmin, yaushe ki ka shigo ban sa ni ba”.

Hankalinta ya tafi akan Umar hankalinta ya yi

matukar tashi, yana mata magana ba ma ta ji abin da yake cewa ba, maimaita sunan kawai take a cikin ranta. Tana cewa ya dawo ya dawo Umar ya dawo, babu wadda ya ji abin da takè furta wa sai mahaifinta don haka sai ya yi saurin daukewa Abas hankali da

cewa

“Me ya hada ku ne na ji kamar kuna hayaniya”.

Abbas ya yi murmushi ya ce “Ka da ka damu sirikina,

Isasshe ne shi yake ganin kamar ya kai ni isa shi yasa nake so na ganar da shi, amma da alama kansa a duhu yake kuma zai yi wuyar fahimta, lallai ka sanarwa da mahaifina ko ya gyara Ko darasina ya gyara shi”

Zulaihat ta zaro ido cikin ji da kai “Kai kar ka so ma, domin in ba ka yi wasa ba za ka fuskanci mummunan faduwa kasa”

“Ke saurara ba na ja’inja da mata, in kuma ke ma mace ce mai kamar maza to ga fili ga mai doki”

“Abbas mai yasa kake da dabi’u na yara kana ne, ba ka ganin bakin mu ne, kumá sun zone domin su taimaka mana ba mu taimaka musu ba”.

Abas ya jinjina kai ya ce “In har kun dauke shi da

muhimmanci to ku yi maza ku ladaftar da shi don in ya fiya shiga sharafina za ku daina ganinsa, don ni bana son raini. Mata ta mu je office mana”

Kallo ta yi masa na tsana kawai ta ce “Dady na tafi”

Ta bar wajen cikin zafin rai-daidai lokacin da za ta

gifta ta office din da ya shiga sai da ta yi kamar ta bude ta shiga amma babu yadda za ta yi domin a ganinta Umar zai gaggaya

mata maganganu ba zai girmama uzirinta ba.

Zulaihat ta ce “Ina gaya maka ka kama kan ka dan ba kai

kadai bane tsagera ka ji ko”.

Ya yi wani murmushi ya dube ta “Sa’ar mata ta ku kayi, ba

na son na yi abin da bai dace ba a gabanta, amma ke karamar

mara kunya da babban duk zaku zo ku ba ni hakuri zaku raina kanku”

Ya bar wajen Alhaji Sunusi ya ce da ita yana zuwa. Office

din Umar ya shiga.

“Barka da aiki Umar”

Umar ya dago ya dube shi “Yawwa Alhaji Barka da

yamma”

Abin da ya bawa Alhaji Sunusi mamaki ya zata zai zo

yasame shi yana huci da fisga sai yasame shi ya bude wani file

yana dubawa.

Alhaji Sunusi ya samu waje ya zauna “Kayi hakuri

dan Allah ka yi hakuri, kuma ina so in baka shawara, kai

daganinka an ga yaron kirki wadda yake da tarbiya, dan Allah ka

da ka daka ta wannan sakaran yaron ka yi abin da yake gabanka

kawai

Umar ya yi murmushi ya ce *Nagode Alhaji, in dai hakuri

ne zan yi iya yadda zan yi, sai dai duk ranar da yake Kokarin taka ni zan nuna masa bai isa ba, watakila shi zuwa Abuja ya yi

lokacin da yasamu dama, ni kuma haifaffen Abuja ne, babu wani

abu da zai nuna min gari na ne nan, kudi da yake takama da su ba

ma su dame ni ba bare ya ci zarafina akansu. Alhaji a rayuwata

babu abin da yake burge ni da ya wuce aikina, abin da yake sa ni

farin ciki shi ne na yi aiki mai kyau a yaba min”

Alhaji Sunusi ya yi murmushi “Na gamsu da bayaninka,

sannan nayi kace kai haifaffen abuja ne, ke nan kano ka koma da aiki yanzu kuma ka dawo”

“Haka yake, iyayena suna nan, yau shekaru uku ke nan

rabona da nan. Na bar nan ne saboda ina so na yi rayuwar sauki,

ba zan bari na dawo nan wani ya shiga rayuwata ba, ku yi kokarin

sai ta shi, ko kuma ku yi kokarin hana zirga zirgar aiki a tsakaninmu” “Na fahimce ka

Alhaji Sunusi ya zuba wa Umar idanu cike da tausayawa har Umar ya dago sau uku ya dube shi sannan ya ce “Akwai wani abu ne?’

Alhaji Sunusi ya dawo daga duniyar tunanin da ya fada tsawon shekaru uku sannan ya ce “A’ah ba komai, ina maka fatan nasara dana”.

Ya ji dadin furucin da na da ya kira shi don haka ya mike cikin girmamawa ya ce “Nagode bisa damuwarka da ni, dama na zo in gaishe ka ne dazu sai kuma Abas ya zo, na gode”.

Zulaihat ta fado cikin office din ta na hayaniya akan Abas.

“Zulait kwantar da hankalinki mu yi abin dake gaban mu, muna da manufa ba hauka ne ke gaban mu ba, kar ki kara tanka masa

Ta samu waje ta zauna anan suka zube zanennukan gidajen da zasu fitar wadda aka dauki kwangilarsu wadda za a fitar. da wata unguwar guda. Tun da ya amshi zanen yake kallo Alhaji Sunisi yake kallonsa, shi kuwa gabadaya yanayinsa ya sauya yanayin rubutun hannu da kuma zanen dukka ya dawo masa da tunanin Yasmin tabbas baya tantama ita ce ta yi wanna zanen a nan ya tuna sunan Sunusi ya kuma tuna da cikakken sunan-• Yasmin sai jikinsa ya yi sanyi ya mike tsaye.

* Zulaihat ki gaya min gaskiya me ki ka sani dangane da Alhaji Nasir da ya yi jagoran hada mu aiki da wannan kamfanin?”

Cikin mamaki ta dube shi “Ban fahimta ba, mena sani wadda ba ka sani ba”

“Zulaihat akwai wani abu, Alhaji Nasir yasan sirrina. Me yasa ya yi min haka me yasa?”

“Kwantar da hankalinka Umar, kwantar da hankalinka

“Kai ne mahaifinta?”

Alhaji Sunusi ya rintse idanuwansa “Kwarai nine, amma a sani na babu wani dalili da yasa aka turoka nan baya ga binciken da alhaji Hashim ya yi ya gano kwarewar aikinka, mun sha fama da Alhaji Nasir akan ya barka ka yi aiki da mu, bai amince ba har sai da ya nemi saka hannun jari da mu”.

Wani irin gwauron numfashi Umar ya ajiye hawaye suka fara zubowa daga idanuwansa “Wannan nata ne?”

Alhaji Sunusi ya amsa da ka tare da cewa “Na ta ne”. “Me yake faruwa ne. Ku fahimtar da ni”.

Alhaji Sunusi ya ta shi zai fita ya ce “Na ji ma ina son

haduwa da kai, ina maraba da kai a duk lokacin da kazo domin yin magana da ni”.

Ya zaro katin sa ya a jiye masa akan table “Duk ranar da kaso in wani abu ka kira ni zan ba ka lokaci da wajen haduwar mu,

kafin nan ina mai baka hakuri”

Bai iya cewa komai ba har Alhaj Sunusi ya fita ya rufo

kofa. Zulaihat ta ce “Ni ban san me yake faruwa ba ka gaya min Kije office Zulaihat”.

“Umar me kake boye…Ki tafi office na ce, bai shafe ki ba” bar shi.

Ya fada da yar tsawa ta mike jikin ta babu kwari ta

Tafi office dinta ta koma ta shiga ciki ta rufo kofa

ta ci kuka ta gaji babu yadda Khadija ba ta yi ba akan ta bude kofa amma taki budewa. Sai da ta ci kukanta ta more sannan ta bude.

“Khadi Umar Umar ya dawo Umar yana Kamfanin su

Daddy yanzu na gan shi suna sa’ insa da Abas”

Cikin mamaki Khadija ta ce “Umar din akan me suke

sa’insa sun san juna dama

“Ban sa ni ba ban san komai ba tambayoyi fal

kwakwalwata ban san me fassara min su ba”

“To ya a ka yi haka ta faru? Kin ce Abas bai san

Umar ba, sannan Umar bai san kowa naki ba, haka zalika.Ina zuwa ina zuwa”

Abin da ya fado ranta shi ne lokacin da Alhaji

‘Hashim ya ga hatsarin da Umar yasamu yanayin tashin hankalinsa

da wayar da ya dauka. Yana magana akan Umar din.

“Na tuna wani abu, Bai san komai ba, ya zo kamfanin

ne aiki ba dan yasan wani abu dake tsakanin mu ba, babu mamaki

ya nemi aiki ne yasamu a bangarensu”.

“Kina ganin Umar zai nemi aiki a cikin garin Abuja?’

“Kin yi tambaya mai kyau, babu wadda zai warware

min wannan sai mahaifina, to amma idan na yi maganarsa da

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE