MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 14 BY RABI’ATU ADAM SHITU

mahaifina zai ga cewar na kasa mantawa da shi zai taso da abin da ya wuce in dai ya ga ina cikin damuwa

“Me zai ta so da shi?”

Yasmin ta daga ido ta dubi Khadija, ashe tana

kokarin fasa sirrin mahaifinta ne ba ta sani ba yakamata ta nutsu kawai jakarta ta dauka ta tafi gida domin ta samu komai ya wuce dakinta na cikin gidan su ta shiga ta kwanta don ta hutawa ranta kwakwalwarta juyawa take ta kasa samun nutsuwa.

Office Umar

Yana zaune a office dinsa yana juya katin Alhaji

Sunusi yana jinjina kai kai tsaye tunani ya fado masa shekara uku da suka wuce da su watanni.

Suna zaune a in da suka saba zama, ya Kura mata

idanu ita ma shi take kallo daga karshe ta ce “Me ye kake kallo na haka?”

Yasmin dan Allah ka da ki bar ni, ina son na rayu

dake, ko da za a hana ki rayuwa da ni dan Allah ka da ki bawa kowa dama, ni kuma na yi miki alkawarin zan zame miki dan halak a duniyakena ke so”

“Umar ina son ka ne soyayyar da ba ni na kirkire ta

ba, ba na jin zan samu sukunin rayuwa idan har ba zan rayu da kai ba, ka daina tunani wani fifiko na arziki dake tsakanin mu, ni ban taba yi wa kaina wani kallon wata ba, abin da na sani kawai duk abin da zuciyata ke so shi ne farin cikinta, Umar ina girmama farin cikin mutane, ina jin dadi idan ina tare da kai, kai zan ce kada ka bar ni”

Ya yi murmushi ya ce “Kece farko a rayuwata da na

taba furtawa so, ina son ki Yasmin ina yawan maimaita miki wadannan kalamai ne saboda kawai ina shakkar ka da ki rabu da mi, idan na auna cewar zaki iya rayuwa ba da ni ba, ina jin wata katuwar guduma na kaiwa zuciyata duka”.

“Duk ranar da ba ma tare da juna, to wannan ranar ka

tabbatar da kiran Ubangijin mu ne, amma matukar zamu rayu a duniya to tare ne zamu rayu ni da kai Umar, ba wadda zai raba mu”

Nan take idanuwansa suka yi jawur, hankalinsa ya yi

matukar tashi lokaci guda. Ya a jiye kowane aikin hatta belt din jikinsa sai da ya ji ya shaki shi maballin rigarsa ya jí tamkar ya shake shi yasassauta shi zuciyarsa ta kumbura.

Ya Kara gudun AC din office din duk bai samu

sassauci ba, ba bata lokaci ya je ya ba da report din cewar bai da lafiya zai je yasamu hutu.

Ya bar kamfanin zuwa masaukinsa ya so ya je gida to

amma yasan idan ya je a cikin wannan halin to ba zai samu nutsuwa ba.

Yana komawa gidan Kur’ani ya dauka ya fara kafarantawa

• sai da yasamu ya yi iyaka abin da zaiyi sannan ya kwanta domin ko zai samu bacci.

Cikin ikon Allah yasamu baccin har bai so la’asar ta yi ba domin kiran sallar wayarsa ne ya ta she shi.

Bayan ya idar da sallah ya jima yana zaune jingine da jikin kujera “Waye mijinta, wa ta aura?.

Yakamata yasan wadannan abubuwa tun kafin ya bar

garin Kano, wai shin ma kuwa ya yiwa Yasmin Adalci

•Na danka amanar kaina a wajenka Umar, ka shiga

lamarina a duk lokacin da ka ga zan yi wani abu bai dai-dai ba”

Wannan maganar ta fado masa cikin rai kai tsaye. Bai

san lokacin da ya mike tsaye ba. Wayarsa ya dauka ya zaro katin mahaifin Yasmin Alhaji Sunusi ya kira shi

“Assalamu alaikum Alhaji na kira ka ne domin ina

son ji daga gare ka, me kake son sanar da ni”.

A dai-dai lokacin da yasmin na tare da Alhaji Sunusi

a katon sitroom dinsa, ta na kwance shi kuma yana gaya mata yadda ayyukanta suka yi kyau domin ya nuna yi mata maganar

Umar ta nuna ba ta da damuwa akan hakan.

“Eh haka ne, to amma yanzu ina gida, á ina zamu

hadu da kai?”

“Alhaji duk yadda ka ce haka za a yi?”

“Kana ina kai yanzu?”

“Ina gidan da aka sauke mu”

“Okay nan gaban mu”

“Haka ne Alhaji, “To bari zan zo na same ka”.

Suka kashe waya ta dubi mahaifinta “Daddy Umar Ya dan sauke ajiyar zuciya “Eh shine, Yasmin

yakamata mu sanar da shi komai da ya faru domin ka da ya dinga yi miki kallon kamar kin ci amanarsa”.

“A’a Daddy, ka da ka sanar da shi wannan sirrin mu

ne Daddy”

“Ina Kaunar sa Yasmin, ina ji cewar da na yi babban

dace ace na samu suruki kamar sa, hankali, girmamawa, saukin kai, jajurcewa, wadannan kadai na hange su a gare shi a yau kawai, ki yi hakuri”

“Daddy in ka gaya masa maganar da ta wuce za ta

Kara ta shi, domin tabbas Umar yasan dalilin aure na da Abas zai yi kokari ya ce sai ya kawo karshen sa, jajurtacce ne kamar yadda ka fada, sannan yana da zafin kai ba komai yakesaka shi saduda ba, in har ba ya je karshen gaskiya ba. Komai zai dawo danye ne da zarar yasa ni”

“Shi ke nan *ya ta zan yi magana da shi ta yadda zai

fuskance ki”

“Nagode Daddy”.

Ba ta ji ma da komawa gida ba Abbas ya shigo cikin

gidan kai tsaye ya tambayi ta na ina ‘yan aikin gidan suka sanar da shi cewar tana dakin ta, da hanzari ya nufi cikin dakin. Ta kasance kamar mara lafiya ta nade akan gado tana ta sake sake.

Ya turo kofa. Tsaye ta mike kamar wacce aka tsikara “Me ka shigo min cikin daki?”

Ya yi taku kadan zuwa in da take yana murmushi

“Dan na shigo dakin mata ta sai an tambaye ni dalili?’

“Ka da ka Kara kirana matarka domin ni ba matar ka

ba ce, ban amince da auren ka sai bisa sharadi, sharadin da kuma bai isa ya halasta min kai a matsayin miji ba in ka manta na tunasheka”

Ransa ya baci zuciyarsa ta yi bakikkirin ya dube ta

“Yasmin sai yaushe ne zaki saduda, sai yaushe zaki so ni, sai yaushe ne zaki gane babu wadda ya fi ni son ki a duniya”.

Wata dariya ta yi ta bacin rai “Da Allah malam ka

fita, sannan ka da ka Kara yi min magana makamanciyar hakan”

“Yasmin ina son ki?” Ta jinjina kai “Ban ga laifin ka ba tun da na lura ba

ka da sanin mene ne so, waye yasanar da kai a na so a bangare daya, shi so bangare biyu ne su ke hafar da shi, muddin, bangare daya ya yi so in har ba mahaukaci ba, to zai ji daga wadda ya amayarwa da so shin yana yi ko baya yi, idan yana yi sai su tattali soyayyarsu ta kai Kululuwa, idan kuma ba ta yi sai ya rissina ya kaunace ta da abin da take so, wannan shi ne so, kai ba so kake ba son kai kake, ka raba ni da masoyina, ka raba mahaifina da farin ciki Abas, ka farka Abas ka fahimce ni ba na son ka ba zan taba son ka ba, ka da ka yaudari kanka da zuciyarka cewar akwai dalili da zai sa na so ka, zan dauwama a haka muddin ba ka rabu da ni ba”

Wata shu’umar dariya ya yi, “Na yarda Yasmin na yadda ki rayu da ni, ki rayu kina cikin iko na ko da ba zan taba kusantar ki ba, wannan shi ne ainihin so ina matukar kaunar ki rayuwata ba za ta gudana ba muddin ina tare dake”.

Ranta ya baci sosai “Ba zan dauwama da kai ba

domin ba ka isa ka cutar min rayuwa ba, ina da wadda na ke so, ina burin zaman aure ni da shi.

Wata tsawa ya daka mata “Ki min, shiru ki min shiru,

ka da ki sa ka na yi rashin ki na har abada, kuma duk daren dadewa sai na gano wane ne wannan wadda kike ikirarin, idan ba ya numfashi a wannan lokaci soyayyarki za ta dawo gare ni”

Fice wa ta yi ta ba shi guri domin ya daga mata

:hankali jin kalamansa a kashe wadda take so. Ya biyo bayan ta da sauri “Yasmin yasmin kina sawa ina yi miki ihu ki dinga sanin kalaman da zaki dinga yi min.

Ba ta kula shi ba da ta tabbatar ya fita daga dakin sai

ta dawo ta rufe cikin dakin nata ta koma ta kwanta ta ci gaba da kuka domin hakan shi yake samarwa kanta nutsuwa na rashin abin kaunarta a tare da ita.

Ta ya za ta hadu da Umar lallai ta na so su hadu, to

amma zai saurare ta, zai fahimce ta? In ya fahimce ta saura me?

Wannan tunanin ne ya tsaya mata a rai.

Bayan Umar ya dawo daga cikin unguwar su, saboda

kiran da Alhaji Sunusi ya yi masa na haduwa a wani babban wajen cin abinci a hanyar shiga layinsu wato Maina Joint Restuaranta, saboda haka ya bar gida bayan sun dan jima suna hira wajejen karfe tara na dare suka samu, zama a teburi. Lemoka da wasu nau’ikan abu aka kawo mu su marasa ganye.

«Nine mahaifin Yasmin, nine wadda yakamata ka ga

laifi akan abin da ya faru, na san cewar kana yi wa Yasmin kallon ta cutar da kai, ta yaudare ka..

A’a. Ba hak.

Umar ni ma sai da na biyo ta in da kake kafin na

kawo wannan shekarun, sannan ni makaranci ne, kuma ma’ abocin son kallace kallace, wannan dalilin yasa na ke da nazari da kuma kyakkyawar fahimta akan iyalina, na yi wa ‘ya ta alkawarin ba zan tauye ta ba, na kuma ci burin hakan, to amma shi lamari idan Allah fa ya ce ga shirinsa babu wadda ya isa ya gyara ko ya kwace daga yadda ya tsaro.

Ba laifinta ba ne, laifi na ne, ni ma kuma kaddara ce

ba yin kaina ba ne, haka Allah ya kaga mana. Ina so ka cire tsana da Kimarta sannan ka cire cewar mun cutar da kai, tun shekaru uku baya hankalina ya gaza kwancewa, ina so na hadu da kai amma abu ya ci tura, sai a yanzu da Allah ya hada mu. Umar ina so ka fadi ko nawa kake so ni zan kyautar da su a gare ka”

• Umar ya jinjina al’ amari yana kallon Alhaji Sunusi yana dauko biro da kuma katin shaidar bankin ya cire takadda ya miko masa.

“Na gode da ka cire min wata Kaya a zuciyata, na

gode da ka ba ni amsar da na jima ina tambayar kai na, ba sai ka ba ni komai ba, ban so Yasmin don wani abu nata ba, haka kuma ba zan rabu da ita domin wani tagomashi ba. Ina mata fatan alkairi”

Alhaji Sunusi ya jinjina kai gami da cewa “Na gode,

sannan ka taya mu jaje domin mun rasa nagartaccen mutum a cikin family mu irin ka, na barka lafiya”.

Daga fadin hakan Alhaji Sunusi ya mike ya bar cikin

wajen ya bar Umar yana zaune zuciyarsa ta rasa me take ciki farin ciki ne ko bakin ciki, farin ciki jin cewar ba sigar yaudara Yasmin ta rabu da shi ba, to amma me yasa? Ya sha tambayar kansa cewar me yasa Yasmin ta yi masa haka yau yasamu amsar sa, ba a son ranta ba ne

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE