MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 15 BY RABI’ATU ADAM SHITU

Wadannan kalamai sun saka yasamu sukuni to amma

mene ne matsalar?

Lallai babban abu ne wadda yakeda girman gaske, to.

mene ne. Ya mike ya fara fita daga wajen sai da ya bude motarsa sannan ya ce a ransa to inma yasan dalili maganin me zai yi

* *

Da misalin Karfe takwas na safiya ya yi niyar fita

wajen aiki, saboda haka bayan ya shirya ya so ya je gidan su

•domin ya karya a can, amma saboda was muhimman abubuwa da ya kwana da su, yasa ya fito.

Ya shiga motar sa masu gadin wajen suka bude masa

get ya fito daga layin dai-dai fitarsa bakin titi yana tsaye yana jiran motoci su ga ma shigewa sai ya hau titi sosai ya kama hanya.

Irin sammakon da ya yi na safiya irin sa ne Yasmin ta

yi domin zaman breakfast ma gagararta ya yi saboda tsanar da ta yiwa Abas, ba ta so ko kallonsa ta kara yi.

Ta na tafe ta hango shi ta gilashin motar sa a ya yin

da yakekokarin -fita saboda haka sai ta rage gudu alamar ya yi gaba, bai fahimci komai ba ya wuce har da yi mata fitala na godiya. Daga nan ta ci gaba da bin bayansa, bai tsaya ko ina ba sai kamfani.

Ya adana motarsa ya fito ya shiga ciki, ita ma hakan

ta yi ta biyo shi har cikin office dinsa.

Yana kunna AC da wasu fitilu ya ji an bude kofar,

bai dubi wadda yake bude kofar ba saboda yasan sakariyarsa ce za ta yi masa tambaya idan da akwai abin da yake so. Shi kuwa yana tare da yunwa.

“Alina, ina ne zan samu abinci kuwa”.

Ya’ yi furucin yana jiran ya ji ta amsa masa ya ji shiru

hakan yasa ya dago kai sai dagabansa ya fadi a lokacin da ya yi ido biyù da Yasmin tsaye.

Kallo yake yi mata mai cike da mamaki, guri yasamu

-ya zauna sannan ya katse ta daga kallon da ya ga ta na yi masa.

” “Barka dai, lafiya kuwa?” Ta dawo cikin nutsuwar ta. “Lafiya Kalau, ka yi

hakuri na shigo ba tare da neman izini ba”

Ya jinjina kai “Babu komai, amma me ya kawo ki

man?”

“Shi yasa na ce kayi hakuri.”

Ya yi shiru yana jiran abin da za ta ci gaba da cewa

“Ka yi min afuwa ina zuwa”.

Haka ta fada ba ‘tare da ya ce komai ba ta fita. Sama

da minti talatin yana zaune ya kasa katabus domin gabadaya ganin Yasmin na neman ya sukurkuta masa lissafin sa.

Me hakan yakenufi me ya za ta zo, shin ta zo ta ba shi

hakuri ne kamar yadda mahaifin ta ya yi a jiya. Ita ai bai kamata ta zo ba bai kamata ta yi magana da ni ba tana matsayin matar wani, yakamata ya takawa al,amarin birki..

Kofa ta bude wani ya shigo da wani tray a hannunsa,

a bisa tray din kuma wasu plait ne wadda aka nade su da leda yana shigo wa ya ji wani kamshi ya karade wajen, a hannunsa kuma flask din shayi ne.

Yana ajiye wa ta na shigowa cikin office din ta yi wa

ma’ aikacin kamfanin na su godiya ya fita.

Umar ya bi kayan alatun da kallo “Mene ne haka

Yasmin?”

Ta kalli abubuwan kamar yadda yake bin su da kallo

“Ka fito ba ka karya ba, na taba yi maka wannan alkawarin ba zan taba barin kaka fito ba ka karya ba, ka tuna?”

«Yasmin me ke damun ki ne, ka da ki manta da

matsayin ki”.

Ta jinjina kai “Ka ci na baka mintuna ashirin ina

office din daddy zan dawo na same ka”.

Ya kasa yi mata magana har ta fice daga cikin office

din. Dole ya so abin da Yasmin ta sanya alfarmarta a ciki, dole ya so abin da ta zadar masa.

Tea ne da soyayyen dankali sai wani bread mai

matukar laushi da dadi, shi kansa tea din na musamman ne dankalin yasha soyayyen shimfidadden kwai. Ya ci sosai har bai iya barin komai a ciki ba. Ya shiga

toilet ya wanke hannunsa ya kuma kimtsa ya dawo ya dauki ruwan roba a firij dinsa ya sha, yana kokarin zama ta turo kofar.

¿Ya amsa mata sallama sannan ya zauna “Nagode”

Yasanar da ita ta na kallon saman plait din “Me yasa

haka?”

•Ta fada. Ya zaro ido “Me ya faru?’

“Tun yaushe rabon ka da abinci?”

Ya lumshe idon sa “Yasmin kin ce da dalilin da ya

kawo ki, ki sanar da ni ba ni da hurumin zama irin haka a tsakanin mu”

Ta cika idanuwanta da kallonsa har sai da ya ce “Me

yasa kike kallona Yasmin ki koma cikin hankalin ki”

Sannan ne ta nutsu ta samu guri ta zauna. “Me yasa

ka guje ni Umar?’

Tambayar ya ji kamar rainin hankali, to amma jin

bayanan mahaifinta a jiya yasa shi fahimtar dagaske take.

“Ya kike so na yi?”

“Amma dai in da ka tsaya za ka ji komai, ka san ba

zan rabu da kai akan gayya ba” .

“Yasmin koma nene ne ya riga da ya wuce”

*Ke nan za ka iya barina a halin da na ke ciki, ba za

ka taimake ni ko ya ya ace ina ganin haske ba, Umar idanuwana duhu su ke gane, tun daga ranar da ka bar ni na daina ganin haske, zuciyata kusa take da wuta wannan zafin kullum cin zuciya ta yakeyi, Umar ba haka na shiryawa rayuwa ba”

Ya dubi tsakar idanuwanta ya ga yadda take zubar da

hawaye.

“Yasmin matar wani ce ke, wadannankalaman

harumin ne mu yi su a tsakanin mu”

Ta zuba masa ido “Za ka yadda da dukkan abin da

zan gaya maka”

“Na taba kin yadda dake?”

Umar babu abin da Allah zai yi mana don mun

kadaice muna hira da kai, babu abin da ubangiji zai yi mana don mun ci gaba da son junan mu..”

“Yasmin” Bai san lokacin da ya mike daga zaman da yake yi ba «Haba Yasmin ina miki kallon mai hankali yaushe

dabi un ki suka zama haka, me yasa zaki kaunace sabawa Allah madadin ki yi masa bauta cikakkiya, ke ce rayuwa ta, amma ba zan sabawa ubangiji na ba saboda na more rayuwar duniya ba, ki ta shi ki tafi dan ta ni na yafe kuma ba zan Kara daukar fishi a kan ki ba, ki ta shi

Tun da ya fara maganar murmushi take yi har sai da

ya Kara cewa ta fita sannan kalmar ta subuce mata “Ban yi aure ba’Me?”

Ya fada da karfi. Ta kara murmushi sannan ta ce in

ka shirya yadda da ni ka bude kunnuwanka na fada maka sirrin da babu wadda ya sani a duniya daga ni sai Abas”Yasmin me kike shirin cewa ne, kina cikin hankalinKi

“Ba na cikin hankalina tun ranar da na rasa ka. Ba zan

taba iya cin amanar ka ba Umar. An daura aure na da Abas bisa sharadin zai rubuta min takadar saki daya bayan kowa ya watse.

Ban taba kwana a dakin Abas ba, Abas wane irin

mutane mai matukar Kaunata tun ina Karamar yarinya, na yadda zan aure shine bisa sharadin üku, zai sake ni, bayan aure amma da sharadin babu wadda zai sa ni, sannan zamu rayu a gida daya amma ba a daki daya ba. A cewar Abas zai rayu da ni a kowane hali matukar zan iya jure zama da rike sirrin muna da aure, sannan ba zan yadda na auri kowa ba.

Na yadda da haka ne saboda in rike alkawarin dake

tsakanin mu, ban tada fadawa kowa wannan ba, kai ne na ke so na gaya maka”

“Yasmin wannan wace irin tatsuniya kike ba ni”.

Haka”

“Ka ce ka yadda da ni, iyaka gaskiya ta na gaya

“Ta ya zan amince dake”

“In har ka yadda da son da na ke yi ma ka, to ka

yadda da ni, in ba ka yadda da son da na ke ma ka ba, ka da ka yadda da ni” “Amma Yasmin duk ta ya haka ta faru ta ya ya shi ya

amince ya zauna dake ba tare da wani abu na aure ya shiga tsakanin ku ba”

“A hankali za ka fahimci wane ne Abas a kai na,

Abas mutum ne mai son girma mai kokarin ganin ya zama jin kowa baya son gazawa, yana ga ni idan har ya gaza samu na to ya samu tawaye ne a rayuwarsa, bai taba sa son wani abu a rayuwarsa ya gaza ba, ya yadda ya nuna duniya ni yasame ni, ko da ace gasa namansa na ke a gida na ke ci. Abas yana so na mati kululuwar so sai dai bai so ni kamar yadda ya dace a so mutum* ba, shi kansa yake so son farin cikin sa kawai yakeso, bai da mu da kowa ya yi farin ciki ba, ya damu da biyan bukatar sa bai damu da kowa ta sa bukatar ta biya ba”

Shi dai Umar bai san Yasmin da karya ba, sannan bai

tsammanin za ta shirya wannan abu domin ya ci gaba da son ta, ta na yin haka ne kawai don ya daina ganin laifinta”

“Yasmin na san ki na gaya min duk wannan ne domin

ki cire damuwar da take raina, Yasmin ba ni da wani mugun kulli a raina dangane dake, na yadda da dukkan abin da Dady ya ce, ka da ki sako wani abu don na huce tuni na huce ba komai”

-Ta yi shiru ta na wasa da yatsun hannunta. “ban yi

tsammanin haka daga gare ka ba, yadda da so da kauna ce tsantsa a tsakanin mu, ta ya ka kasa ba ni yadda waye zai yadda da ni ke nan a duniya”

Hawaye ya fara biyo kuncinta. Gabansa ya fadi

“Yasmin shi ke nan, to amma duk me yasa hakan ta kasance?”.

“Ka da ka tambaye ni, domin dalili ne mai karfi idan

na gaya maka domin na tonawa mahaifina asiri ne, ka yi hakuri mu zauna a haka ka da ka tambaye ni, Allah zai kawo warwara da kaina zan kawo karshen komai”

Ya tsura mata ido tsantsar gaskiya yakekallo a tare da ita. Zan wuce, gobe ma zan dawo in ka min izini”

Bai iya hanata ba lumshe idanuwansa kawai ya yi, har

ta fita ya kasa motsawa wata sabuwar soyayyar ta ce ta Kara shiga ransa, mene ne wannan abin da ta kasa gaya masa, ya yadda da ita ne domin ya fahimci yanayin Alhaji Sunusi kuma ya ce duk

Hmmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE