MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 16 BY RABI’ATU ADAM SHITU

laifinsa ne shi ma tamkar tilastawa abin ya zo masa, in haka ne akwai wata a kasa, lallai akwai abin dake binne a kasa, ta ya zai gane? Ta ya ya zai dawo da Yasmin hannunsa.

Ya jinjina kai ya samu karfin gwiwa domin ya

tabbatarwa kan sa babu wanda ya isa ya hana shi.

Ta ina zai fara. Ya zama dole ya shiga jikin mahaifin

Yasmin domin a gare shi zai samu sanin komai. To ya zai yi?”

Yasmin na zuwa wajen aikin ta tunda taga mai shara da goge goge har kawo ma’aikatan da kawarta Khadia sai da suka zuba mata idanu suna kallon abin mamaki.

Da fara’a cikin sakin jiki dagaisawa gami da haba-

haba. Ganin haka yasa Khadija ta share ta, sai da ta na satar kallonta saboda ta na so ba sai ta tambaye ta mene ne ya sakata farin ciki ba ta fi so ta sanar da ita da kan ta, saboda haka ta na zaune a bakin aiki Ita kuma Yasmin na zaune a gabanta fara’ a ta ke yi.

“Wai babu wadda zai kula nine?”

Ta fada a dai-dai lokacin da Khadija ta gama gajiya

wai ta na so ta yi mata magana.

Khadija ta numfasa ta ce “Sai mun ji dalili wannan

farin ciki na yaushe rabo kafin mu kula ki, ka da mu je mu ta ya ki murna ba mu sa ni ba duk kin yi cinikinmu

Wata dariya da Yasmin ta yi wacce rabon da ta yi

dariya irin ta har sun manta. Khadija ta ta so ta zo kusa da ita

“Wayar min da kai kawata, na fara shiga damuwa, me ya faranta miki rai”

Wani dan dundu Yasmin ta dumama wa Khadija ta ce

“Mun hadu yau? Na ba shi abincin safe da kai na, sannan mun yi magana da shi a yau mun samu kusan awa daya muna hira da shi”

Khadija ta zuba mata ido ta na so ta tambaye ta waye

sai da hankalinta ya kawo mata cewar babu fa wadda Yasmin za ta yi wa wannan abin har yasa ta farin ciki da walwala ta zo ta na ba da labari kamar Umar. Don haka ta ce “Umar, garin ya ya a ina?”

Wata dariya Yasmin ta Kara yi. Kai duk wadda yasan

Yasmin a kwanaki baya ya zo yasa me ta yau yasan cewar akwai wani kulli da a ka yi aka daure ta da shi a yau ya kwance, saboda yadda ta ke Yasmin haka ta koma.

“Umar Khadi, Umar Khadi ki yi min addu’a Ina son

Umar ya dawo yana aiki a karkashin kamfanin su Daddy.

Jikin Khadija ya yi sanyi lokaci guda da ta tuna da

aure akan kawarta ta take wannan abin don haka sai ta yi saurin ankarar da ita in ma ta manta ne to ta tuna.

“Yasmin kun rabu da Abas ne?”.

Lokaci guda Yasmin ta bata rai ta samu nutsuwa ta

dawo tamkar jiya. Daga nan ba ta Kara cewa da kowa komai ba”

* *

COMPANY

Munir yana ta yawo yana leka office office daga

karshe ya dawo ya shiga office din Abas. Ya tsaya a gaban sa

“Yallabai ban gan ta ba fa?”

“Ka tambayi Linda”

“Eh na tambaye ta ta ce tabbas ta ganta ta shiga office din Guy din can Umar?”

Abbas ya mike tsaye “Umar, to me ta je yi. Yai shiru

yana dogon tunani, daga bisani ya dubi Munir.

“Ban san me ta je yi ba, amma dai ina kyautata zaton

hakuri ta je ba shi, don jiya mun samu sabani a Kofar office din Alhaji Sunusi. To shi wannan guy din me yakenufi, ne ka ga

Munir maganar nan yau ta tabbata, ina so a kawar min da shi,

“Ka da ka damu oga, gobe ba zai zo office din sa ba”.

“Ba kashe shi za ku yi ba, ku ladaftar da shi, saboda

na ga alamun bai fahimci Abbas ba, amma muddin ya Kara wani kuskure nan gaba, to ku gama da shi, yanzu bari nakira mata ta na ji me ta je yi office din sa”

Ya kira lambarta amma ba ta daga ba, ransa ya baci

domin yasan cewar ba za ta taba daga wa ba. “Ka je ku shirya aiyukan ku”

Tun da Munir ya fita ya bar kamfanin ya koma bakin

Aikinsa cikin motarsa ya dakata ya kirawo yaransa ya yi musu umarni a kan su tsaya a cikin shiri zai sanar da su position din da ya da ce. Yana zaune ya tattaro wasu file sai ga Zulaihat nan

«Yauwa wajen ki zan je, yaushe suka ba da umarni zuwa filiyen ne?”

«Sun bayar da izini a je a gani, saboda aikin za a fara

shi ne wata mai kamawa, ka ga kwanaki shida suka rage.

«Ki kirawo ma’aikatan ki, ki sanar da su, su zama

cikin shiri, ka da a sanar da su ba a ka’ida ba”

“Na sanar da Ingeneer tun da na lura aikin na sauri

ne?’

“Ya yi kyau, gwanda muna nuna musu namu

kwarewar”.

Ta yi murmushi ta na kallon sa ya dube ta dariya

yakeyi amma kuma sai ya dan daure fuska “Me ya faru?”

Ta Kara dariya “Just na gan ka ne cikini walwala

kamar ba kai ba”

Yasa ka hannuwansa a aljihu “Ba wani abu”.

Ta dan yi shiru ta na so yi masa magana “Uhmm

Umar ina da maganganu da yawa da na ke so mu tattauna da kai, amma sau tari ba ka ba ni damar hakan dagaske ina so mu yi magana

«Zulaihat ke nan, wacce dama ce ban ba ki ba, kawai

“kin san halina aiki kawai”

“Yanzu za ka iya saurare na?’

“Ina jin ki?”

Ta tsura masa idanu har sai da ya daure fuska domin

ba ya son kallo “Kin ga ma na tuna ba inna dawo”.

Ya kwashe takaddu ya fice daga office din. Zulaihat

ta ji wani mugun haushi ya kamata. Ta na sane da cewar akwai wani Goyayyen sirri da Umar yake binne da shi a cikin zuciyarsa, to amma ya zama dole ta turi wanna sirrin ta dasa kaunarta a wajen domin a ranta ta na ji bayan Umar ba za ta iya son kowa ba.

Saboda haka ita ma fita ta yi da saka cewa duk zame

zamensa za ta sanar da shi abin da yake zuciyarta.

kai tsaye offishin Abbas ya nufa yana zaune

yana waya, amma yana ganin Umar sai ya ajiye waya domin a lokacin yana magana da Munir ne akan ya tsaurara ka da ya gajiya har ya tabbatar da ya cika aikinsa. “Assalamu alaikum, barka da aiki, malam Abbas” Ya a jiye masa takaddun da suke hannunsa “Ina bukatar sa hannun ka”

Abbas ya kwashe takaddu ya bi su da kallo ya dauki

biro ya fara saka hannun sai da ya gama sannan ya mika masa.

Umar ya juya ya ce “A tashi lafiya”

Sai Abbas ya cika da mamakinsa yana ganin kamar

ya sauya akidarsa ne don ya tora ta da shi. Amma kuma a yanayin da ya ga Umar ba mutum ba ne mai saukin kai da zai sauka kai tsaye. “Na ji an ce mata ta ta zo ta kuma shiga office din ka, ko zan iya sanin mene ne kuka tattauna”

Ya dakatar da Umar da yake kokarin murda kofar zai

fice ya dakata “Matar ka kace, dan haka ita ya dace ka yi wa wannan tambayar ba ni ba”

Abbas ya yi murmushi gami da mike wa domin

zarginsa ya tabbata Umar ba zaiyi laushi farat daya ba.Haka ne, ka zo da shawara, amma ka kula da kanka, ina sanar da kai domin ni ba kanwar lasa bane?”Matsala ta aiwatar wa ban fiya yawan surutu ba.

Idan ka kalle ni ka san cewar namiji ne ni cikakke ka aiwatar shi ne zai tabbatar min da kai din namiji ne, na barka lafiya Abbas ya jima yana jinjina kai yana ayyana mugun

abu a kan Abas. Wayarsa ya auko ya kira Munir.

“Guy din nan ba zai yi laushi ba sai kun tabbatar da

kun ja masa kunne, ka da ka yi wasa da aikin nan, yaran dukkaninsu su zama boyayyen fuska bayan aiwatarwa dan na fuskaci da akwai zarra a tare da shi.

Ya ajiye waya lokaci guda ya Kara neman number

Yasmin ya kira again ba ta dauka ba. Ransa ya baci kai tsaye office din Alhaji Sunusi ya nufa.

Haka kawai Umar ya samu karfin gwiwa da jin wani

nishadi na musamman wadda ya jima bai samu irinsa ba.

Bayan karfe biyar ta yi ya bar kamfani yana so ya

hadu da Yasmin amma ya daure gidan su ya nufa. Yana tafe yaran Munir na biye da shi a mota ya jima da mahaifiyarsa suna hira a nan ne take sanar da shi cancantar sa da ya yi aure domin lokacin sa ya yi. “Mama ba a yi wa Yaya Khalil aure ba sai ni”

Ta yi murmushi “Ka na dagaskiya to amma ka sani

shi fa yayanka, bai kaika cancanta ba, saboda ka fi shi karfi, sannan ka na cudanya da mutane da ya dace ace a yanzu kai, kazama kamar su ma’ana ka na da iyali. Kai ne jagoran gidan nan kai ne komai na mu, saboda haka kai ne aure ya kama ba Yayanka ba

«Mama wallahi wayo kike so ki yi min, ni fa ba zan

Yi aure ba sai yaya ya yi, duk wata dama da na ke da ita yaya yana da ita saboda haka ya fito da wacce yakeso ki ga yadda al’ amarin zai kasance .

Umar ya fake da haka ne saboda yasan halin yayan na

shi bai fiya sakewa da mata ba, asalima ba a hirar mace a wajensa in har za a danganta shi da mace yanzun nan zai bar wajen saboda haka sun jima suna kai ruwa rana da shi har sun hakura don haka shi ma ya fake da sai ya yi sannan zai yi domin abu ne mai wuya ta Zulaihat”

“Akwai wata yarinya ta zo nan jiya da yamma, sunan

Ta katse masa tunanin sa “Zulaihat, wajen wa ta zo?’

“A’a ya za ka yi wannan maganar abokiyar aikin ka

ka nuna ba ka san ta ba, bayan ko lokacin da mukaje hatsarin da ka yi mun ga yadda take kai komo a kan ka” Ya sauke ajiyar zuciya “Mama me ta ce mu ku”.

“Kai zamu tuhuma me yasa ba ka son mutumta

wadanda suka mutumta ka?”

“Da na yi me Mama?”

“Ya ci ace ka kawo ta gidan nan mun gaisa da ita,

amma sai da kan ta ta zo, a matsayinta na abokiyar aikin ka, kuma fa yarinyar kirki”

“Umm, waye ya kawo ta gidan nan”. Shi fa yana

zargin ‘yan gidan nan na su da hada masa wani abu ta bayan kasa, yadda suke da alaka da sanin zuwansa ga kuma wannan, anya ma ba su ne suka saka Alhaji ya dawo da shi Abuja ba, ko ba su bane amma dai akwai sanin su a cikin lamarin ga kuma maganar Zulaihat.

“Ka yi shiru, da ma na san akwai wata a kasa”

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE