MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 18 BY RABI’ATU ADAM SHITU

“Mun Kulla alaka da Mama da kuma Yusra tun kana

kwance a Asibiti, idan na yi wa Yusra waya ta zo ta kai ni zata ki ne”Ya fuskanci ta in da matsala take yanzu ya daina

zargin Alhaji ita ce muguwar. “Okay na yi mamaki ne shi yasa nakira ki

Wata harara kawai yake amsa daga wajen Yasmin

domin ya saki ransa yana yi mata magana. Ya kalli Yasmin ta murguda masa baki.

“Yasmin nagode da kulawar”

“Ba na bukata”

Tana fadin hakan ta mike daga in da take tsaye ta fice

daga office din.

Ya ji dadin fitar data yi don haka ya dubi ZUlaihat

“Ko zakigaya min dalilin da yasa ki ka je?”

“Ni ma ka gaya min dalilin da yasa kake tare da

wannan yarinyar alhalin ka san matar makiyinka ce”

Ransa ya 6aci “Ban kira ki nan don ki zo ki na

tuhumata ba”

“Ni ma ban zo nan wajen dan ka tuhume ni akan abin

da na yi wadda ya dace ace na yi shi ba dear”

**’A wane ne dalili kike kira na haka?”

Ta yi ajiyar zuciya “Umar me yasa kake min magana

a tsaye ne, ban cancinci kyautata maka ba ke nan, me yasa ba ka gaya min kana bukatar kayan abinci ba sai wannan ce za ta kawo maka

Ransa ya Kara baci ‘Zulaihar ki je ma hadu an jima”.

Tun da yayi furucin bai sake ko kallonta ba, dan haka

ta mike kai tsaye office din Alhaji Sunusi ta nufa. Yana hada kayan break dinsa cikin nishadi, Zulaihat na fita Yasmin.Ya yi dariya “Uhmm ashe ba mu iska ki ka yi”

“Eh ba ku iska na yi, amma ka san raina yana baci

idan ana samun irin haka ko?”

Dariya ya yi, “Me ya faru?”

Cikin wani salon jin haushi da haukan kishi irin na

Yasmin take kwatanta maganar Zulahat “Ban da raini da wulakanci a gabana take gaya maka dear, kuma tana wani kallonka, kai kuma sai cika kake kana batsewa. Ni ba na son ta”.

Yayi murmushi “Yasmin dama kinada  kishi”Ban sani ba”

Ya kara murmushi “Kin manta matsayin ki ne

Yasmin, matar wani ce ke fa”

Ta zabga masa harara “Shi ne kake so ka zama mijin

wata”

Ya gyara zama “Ki nutsu mana Yasmin, ka da ace

kin manta cewar ni daya ne dake mu ke da sanin auren ki.

“Me kake nufi kana nufin na ci gaba da kallonta ta na

gaya maka dear ni ba zan lamunta ba, ko ma mene ne zai faru ya faru ai ba ni da aure kuma ni kai nake so mun riga mun fahimci juna na daga abin da ya wuce, ina da iko na ce ba na son ka kula kowa, domin nice ubangiji ya bawa amanarka, idan kuma ka shirya ci min amana ne zamu ga ni”

Dariya Umar ya yi “Yasmin sabodake, ba zan iya

kula wata ‘ya mace ba, sabodake na fitar da ran zan yi aure, sabodake na samu kaina cikin rashin walwala, me zai sa ki na tunani zan iya juya baya a gare ki, bayan dalilin ki ne a yau na ke iya farin ciki, duk kuwa da dimbin alkairan da ya same ni a rayuwa”

Ta shiga damuwa har hawaye na neman kwacewa

daga idanuwanta. Ya mike da sauri yana rarrashita “Ba na ce laifin ki ba ne, na gaya miki ne saboda ki fahimci muhimmancin da kike da shi a gare ni Yasmin. Ta yaya zan rayu da farin ciki alhalin ba na tare dake”.

Umar na san ina son kai na, kuma ba zai daina son

kaina ba akan ka, dan Allah Umar ko da ba mu samu damar yin aure ba, na roke ka da mu rayu a haka, muna tare ba kuma mu bawa kowa kofa ya shigo rayuwar mu ba. Na iya jure rashin ganinka na tsawon lokaci, amma ba zan iya jure ganinka da kowa ba, zan iya mutuwa dan Allah na maka alkawarin dauwama da kai a cikin rayuwa ta, har mu samu damar da zamu mallaki junan mu”

“Wannan alkawarin ne?”

Ta yi saurin jinjina kai tana kallon sa tana so ta ga ya

yadda”. “Ko da kina tare da Abbas ba zan iya auren wata ba, saboda duk wacce zan aura zan cutar da ita, na jima da yi miki wannan alkawarin Yasmin”

Wani farin ciki ya lullube ta.

Zulaihat da ta jima ta ga Yasmin ba ta fito ba, tana

tsoron shiga office din dan ka da ta gane wa idanuwanta abin da zai tada mata da hankali. Gabanta ke faduwa dif-dif tana nan tsave ta ji ana tahowa ta bayanta. Abbas ne tare da mukarrasabansa.

Wata dabara ta fado mata tana ganin ya shiga ta bi shi office din sa “Jira nakike dama?”

Da abin da ya tare ta ke nan “Ko daya, ina da da

muhimmiyar magana da kai?”

“Ba ni da lokacin ki in har akan waccan partner din ki

Ne?”In kuma akan matarka ne fa?”

Ya dago daga duken da ya yi “Me kika ce?”

“Me ka ji na ce”Ina jin ki me ya faru wani abu ya faru ne?”Ta samu guri ta zauna “Akwai abin da yake faruwa a kamfanin nan, sai ka saka ido sosai?”

“Dangane da Tsakanin ta da Umar”.

Ya harzuka ya ta so mata “Me ki ka ga ni me kike

shirin fada min gaya min”.

“Ka taba tuntubar rayuwar Umar, ko ka tada tuntubar

rayuwar soyayyar matarka a can baya, yakamata ka bincike komai, amma ina so maganar nan ta tsaya a tsakanin mu, zan taimaka maka”

Ya ci gaba da dubanta “Idan har kin yi haka ne don

wata manufa kuma fa”.

“Ba ni da wata manufa akan ka”

Ya tsura ta da idanuwansa “Karya kike”.

Ya fada gami da fara kewayen office din “Na san

zaki yi mamakin idan kin ji na ambaci kisa, to na sha kashewa, saboda haka partner din ki ya kai makura, don haka zan kashe shi, da ace na san akwai wata alaka tsakaninsa da matata to babu shakka da bai kwana ba, amma duk da haka ba zan yi garaje ba zan yi bincike domin na fahimci mene ne alakar su”.

“Kisan kai wannan ra’ayi ne, kowa ya ga dama zai

iya aikata wa, amma ka sa ni, jarumtarka dukiyarka, shi kuma Umar Jarumtarsa hikimarsa, ba kamar sauran mutane yake ba, ka bi a sannu in ba haka ba zakayi danasani”

Ya daki table din gabansa idanuwansa sun yi jawur

ya ce “Mu zuba mu gani’

Bai tsayasauraranta ba ya fice daga office din daf da

fitowar sa ya ga Yasmin ta fito daga office din Umar tana ta faman murmusawa da kwandon abinci a hannunta.

Ya Karaso wa in da take yana taku dai-dai na ya

kamata. Ta na waigo wa daga tura wa Umar kofa ta yi ido biyu da shi.

Ya Kare mata kallo tana tsaye ita ma kallon sa take

duk da cewar ta samu firgici amma sai ta daure. “Mene nehaka ka saka min ido?”

“Waye shi?”Wa din?”

Ta tambaye shi alamar bata fahimci in da yasa gaba

***Shi wadda ki ka fito daga wajensa kina dariyar da na jima ban ganta a fuskar ki ba tun da ki ka kasance tare da ni”.

“Ba ni da lokacin batawa don na yi maka bayanin

wasu mutane da suke da muhimmanci a wajena”.

“Me yasa?”

“Saboda kowa a duniya ya fika muhimmanci a

wajena, ba ka da wani muhimmanci”

Ransa ya sosu ya jinjina kai “Ya yi kyau, to amma ki

sani rayuwar duniya iyawa ce, kuma bahaushe yace iya ruwa fidda kai, zaki fara girbar abin da kike shukuwa”

“Me za ka yi”.

“Mutanen da suke da muhimmanci zan raba ki da su,

ko kina ganin ba zan aikata bane, zan kashe dukkan mutanen duniya domin nayi rayuwa dake Yasmin Ya jinina kai ya bar ta a tsaye yadda ta ga

idanuwansa sun kada sun yi, jawur ta san da cewar zai iya aikatawa.

Waya ya zaro ya kira Munir. “Wannan Guy din ka yi

maza ka nemo min bayanan sa, su waye iyayensa mene ne alakarsa da mata ta tsawon shekaru uku baya, bana son binciken ya wuce yau”.

– Ya kashe wayarsa ya fita daga kamfanin baki daya.

Ofishin mahaifinta ta nufa ta zaiyane masa komai

Alhaji Sunusi ya yi dogowar ajiyar zuciya gami da gyaran murya

“Zai iya Yasmin, bai kamata ace kin dawo da abin da ya wuce ba, kin san Abas mijin ki ne kuma Umar haramun din ki ne, me yasa zaki zabi tarayya da shi, duk da cewa na san irin zaman da kike da Abas ba sai kin fadi komai ba Yasmin, amma ki sa ni akwai igiyar aure a tsakanin ku, ko da ace ke kina ganin babu wani abu da ya shiga tsakanin ki na aure. Umar Haramun din ki ne, Allah zai iya kama ki da wannan hakkin”

“Daddy ka yadda da ni, ba zan yi wani abu da

ubangiji bai umarce ni da yi ba, ban aikata da zunubi ba don na je wajen Umar Daddy”

_Ya kura mata ido “Me kike nufi ke ba matar Abas

bace”Ni ba matar sa bace Daddy, ban yadda da zan aure shi ba, sai da muka yi yarjejenyar zai sake ni bayan mun yi aure, ya kuma sake ni, saki daya ina da takaddar sakin a dakina in ka je gida ka shiga ga duba cikin karamar akwatina lambar budewa hudu, shida, biyar, tara, daya, daya.

Ya tsura mata idanu “Ta ya haka ta faru?”

“Daddy ba zan bari ka cutu adalili na ba, sannan ba

zan iya ruguza rayuwa ta da Abbas ba, na san Abbas zai iya zama da ni akowane irin condition ne, dalili ke nan na nemi saki ko kuma rasa rayuwata gabadaya, shi kuma ya amince min dalili yana gani akwai ranar da zan dawo na amincewa soyayyarsa”

Daddy ya yi shiru ya jinjina abin “Amma baki taba

sanar da ni ba ‘ya ta, ko ya ya zan rayu da farin ciki kin sani”

“Daddy na san ka yadda da ni, amma ina so ka Kara

ba ni yadda Daddy ba zan yi wani abu da Allah zai kama ni ba,

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE