MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 21 BY RABI’ATU ADAM SHITU
bana Baya wacce yadda ce a tsakanin ku da ita da zata hada ku,
“A kan yarinyar da ta yaudare ka kake Kokarin
kara zuwa Mama ta yi bayanin cike da fushi ganin yadda take furucin yasa ya rinse idanuwansa ya yi shiru suka Kari maganganunsu, Allah Allah yake likita ya zo duba shi yace su ba shi waje ya kira Yasmin ta gaya masa wani abu ko zai samu dan sauki a zuciyarsa. Ita kuma Zulaihat murna a wajenta kamar ta zuba ruwa a kasa tasha an ce za ta auri Umar sannan an yi masa tsakani da Yasmin.
Baba da Khalil da Bashir suka tafi, mahaifiyarsa da
Zulaihat da Yusra suka rage, su ma cikin ikon Allah likita ya basu hakurin ganin majinyaci.
Tana kwance a dakinta tana daddadan mafarki Umar yazo cikin dakin da take ya kwanta a kusa da ita, ya tallafo kanta ya yi mata kiss, ta bude idanuwanta tana masa murmushi, “Kullum in ina kallonka, la66anka nake jin kwadayin naga na subbata shin da gaske ne yau ka zama nawa”
Dariya ya yi mata gami da Kara dago kanta zai sumbace ta ta ji ana dokan kofa da karfi.
Firgigit ta mike daga kwancen da take, “Yasmin ki zo
ki bude. Muryar mutumin da ta tsana, wadda kuma ta ci alwashin sai dai ita ko shi yau, dan haka da Karfin gwiwa ta isa ta bude Kofar.
Mahailiyar tana bayan shi ya tsura mata ido, wata
ajiyar zuciya ya yi. “Me zai sa ki rufe kan ki a daki mata ta…fita mana daga gidan mu”
Ka da ka kuskura ka Kara kira na da matar ka, ka fitar
“Yasmin lafiyar ki kuwa?”
Ya tambaye ta “Ko za ka ce ban san abin da ka aikata
ba ne to ka sani idan ka sake ka Kara saka hannun ka akan Umar,
Ya ci gaba da kallon “Na gan ki cikin damuwa shin
wani abu ya faru ne?”Daddy Abbas ya yi kokarin kashe Umar?”Ya zaro ido cikin mamaki “Garin yaya?”
Duk abin da ya far ta kwashe ta sanar da shi “Bari na
je na gan shi, Subhanallahi wannan yaron ba shi da hankali”.
“Na baro gidansa Daddy ba zan koma ba”.
Ya zura mata ido kana ya jinina kai “Kin yi daidai
Yasmin bari ina zuwa zan je wajen Umar ba ni address”
Kai tsaye Daddy ya nufi Asibiti Yasmin ta ki ta saki
jiki da mahaifiyarta domin tana wa mahaifiyarta kallon koma mene ne ita take bawa Abbas fuskar duk irin abin da ya yi mata don haka bata son taji suna maganar sa da ita ko sun fara katse ta take yi.
Alhaji Sunusi ya yi sallama cikin dakin jinyar, ya same
Umar a kwance shi kadai a cikin dakin, bayan gaisuwa da jaje suka yi dan shiru,
Akwai abin da make so mu yi magana da kai a kai
Umar, to sai dai ganin halin da kake ciki zan jinkirta har ka sami sallama”
Umar ya gyara kwanciya “Ka gaya min koma mene ne
duk daya ne.”
Yadda ya ga alhaji Sunusi ya nutsu ya fahimci maganar bata wuce ta sarke sun da Abbas ya yi ba.
Alhaji Sunusi ya jinjina kai “Yasmin bata so na gaya
maka ba, amma yau ya zama dole na gaya maka, ban bayar da auren Yasmin ga Abbas ba sai dan wani dalili dalilin shine, Abbas da mahaifinsa sun shirya min wata gadar zare wacce na riga na tsallaka a cikin rashin sani, na amshi kwangila tsakanin mu da kamfanin JIS, haramtaccen aiki ne wadda a ciki an yi harkallar kashe mutane, sannan suka fitar da hannunsu a ciki suka ba ni na saka hannu a cewar nizan mallaki aikin wadda kuma a tsari na je ne akan kamfanin mu, da dukkan takaddu, to amma da yake sun yi wa abin tsari, sai suka sanya takaddun bogi ba na kamfanin ba, ni kuma ban duba ba, na rattaba hannu, a lokacin sun yi amfani da wannan damar ne, ko auren Yasmin ko kuma su nuna cewar ba kamfanin su bane
-ya amshi kwangilar a matsayin sulhu nine na amshi kwangilar saboda rajin kaina, ka ga gwamnati za ta yi bincike akan kamfani na
*wadda suka Kirkirar min wadda ba shi da rigester da Kasa, sannan kuma a Karkashin zasu gano badakalar da aka rufe a ciki.
Za a kamani da laifi biyu, na tabbatar zan fita a
binciken kisan kan mutum biyu da a ka yi amma ba zan fita daga boyayyen kamfanin ba, wadda shi ma tara ce wacce ban mallaki adadin abin da zan iya biyan su ba, ke nan za a daure ne a bisa hakan. Ka ji wannan shine abin da ya faru, na kuma so na amshi laifina amma’ Yasmin ta ji batun ta hana ni cewar ta hakura za ta auri Abbas”.
Umar ya yi shiru abin ya tada masa zuciya lallai ya
jinjina wa Alhaji Sunusi ya cancanci zama uba, sannan Yasmin
‘yace wacce ya dace ace an yi alfahari da ita
“Alhaji wannan shine daurin da Abbas ya yi?”
“Shi ne wannan, kuma daga yau za ka taimake ni domin mu kwance shi, ina aiki ta bayan fage, zan iya cewa na kai ga cimma wasu abubuwa wadanda suke abinne, mutum dayanake
nema wadda har yanzu ban same shi ba ban kuma san in da zan same shi ba”
“Waye shi “Balarabe Sa’ ad shi ne wadda aka hada baki da shi aka tura ni a cikin ramin, lallai ina son ganin Balarabe, domin ganinsa tamkar warwarewar komai ne”.Kana da lambar wayar sane?”Ina da ita, amma ba ta shiga?”Ka tura min lambarsa da tsohowar ma’aikatar sa ka koma ka huta ina zaune a daki zan gano maka komai ka da ka damu kan ka, in sha Allahu komai zaizo Karshe”
Mama da Zulaihat suka shigo bayan sun gaisa ne
Zulaihat take gabatar da su ga juna, amma bata ce abokin aiki ba ta sanar wa Mama cewa mahaifin Yasmin ne, don haka ba ta ba shi fuska yadda yakamata ba. Ya fita ya bar su Zulaihat ki sauke Mama a gida”.Mama ta kalle shi “Me yasa?”
“Yakamata ku je gida haka Mama idan bakya gida kin
san yadda abubuwa suke rincabe miki, Ina Yusra?”
“Ba ni da wani abu da zan yi a gida masu gidan duk nan zasu taho an jima
“To amma Likita yagaya min cewar an dan dame su a
“basu lokaci”.
“Korar mukake so ka yi”.
Ya yi murmushi “Kullum burina in gan ki kusa da ni,
nan din ne bana so ai ta zuwa ana kada ku waje, suna da aiki da zasu yi min yanzu’
“To ba sai ta kai mu ba, zamu tafi da kan mu, da
yamma zan kawo maka komai?”
Ran Zulaihat ya gama baci domin ta fuskanci Yasmin
ce take son zuwa, babu yadda za ta yi dole ta bi Mama ta rage mata hanya don ta Kara fitar mata da Yasmin daga cikin ranta
Har sun je kofa sannan ya kira sunan Zulaihat. Ta dawo in da yake kwance “Zulaihat, na fuskance ki, amma ki bari yin hakan ba abu bane mai kyau”.
«Mai na..Babu kyau, ke ‘ya mace ce, ina kuma daraja ki, ke ma.ki daraja kan ki
Jikinta ya yi sanyi kalau ta fita jin ya yi shiru bai kara
cewa da ita komai ba. Tana fita ya kira Yasmin ya sanar da ita tazo Tuni dama ta sa ma’aikatan gidan su sun shirya mata
kayan abinci wadda mara, lafiya kebukata musamman rauni, musamman ta yiwa DR Kamal waya ta sanar da shi. Ko cikakken awa guda ba a yi ba an kammala komai ta Kara so Asibitin ta shigo cikin dakin jinyar yana kwance. Tun da yaga an shigo da flasks jikinsa ya basa Yasmin ce take tafe. Ta shigo ta zauna kusa da shi kallon ciwon da yake rufe take yi. “Ya kake ji, Umar, amma ya rage zafi Kai ya jinjina mata yana jin zugin yana cijewa “Sannun ki da kokari Yasmin, wannan wai duk ni kadai ta ina zan iya cin
wannan Ta harare shi gami da dauke hirar “Na ga matar nan tazo”
“Wacce mata kike magana?”
“Wannan da kuka zo kamfani tare?’
Saboda wulakanci irin na Yasmin ko ince kishi sunan
Zulaihat din ma ba za ta fada ba.
“Umar ba na son ganinta Umar idan kana so zuciyata ta huta dan Allah ka ce ta daina zuwa in da kake, ka rabu da ita ta tafi nata waje, tun da tare ta gan mu”
Ya yi murmushi “Ki kwantar da hankalin ki, lokacin da
zata rabu da ni dole ya kusa”.
Ta gyara zama “Wani abu ya faru?”
Ya jinjina kai “Daddy ya zo nan ya kuma gaya min
komai sannan ya sanar da ni cewar lallai na taimaka masa mu cire kullin da aka yi masa, wani abin nasara ma a cikin kaso dari ya cinye arba’in kuma abin da ya rage lallai yana da bukata ta, domin aiki ne na kutse a intent, wannan fannin mu ne kuma zan yi iya bakin Kokarina wajen ganin na samar mana da zama a inuwa daya ni dake”.
Tun da ya fara maganar ta shiga tashin hankali,
tsoro yakamata ya fuskanci haka “Yasmin babu abin da zai faru da Daddy, na yi miki alkawari Daddy zai yi free ki samu nutsuwa kuma ki ban aminci”.
Hmmm