MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 22 BY RABI’ATU ADAM SHITU

“Umar mahaifina na Kaunata, dan Allah kada mu yi abin da za a raba ni da shi, na san shi bai da mu da tashi rayuwar ba, burinsa ya ga ina farin ciki, don haka ka yi taka tsantsan”

“Ina son ki Yasmin, duk abin da zai zamo farin cikin ki shine abin da nake so, ba zan so kaina ba har sai na so abin da kike so Yäsmin”

Ta yi murmushim lokaci guda kuma ta daure fuska

“Ni dai ka nisanta kan ka da wannan matar”.

Ya zura mata ido ita ma ta zura masa ido cikin

shagwaba kamar za ta yi kuka tace “Ba wasa nakeyi ba Umar ka rabu da ita

“Me yasa kike so na yi ta maimaita miki magana

ne Yasmin, kina ganin zan iya barin ki ne na so ta. Ki sani cewa ke ce kadai tawa, da ba dan ke ba da yanzu ina da iyali, ba zan iya rayuwa ba sai dake?”

“To amma ya zan yi da zuciyata, idan na tuna ta

, zuciyata suya take yi, idan na ganta kuma bugawa zuciya ta take yi ka da na mutu Umar ban yi rayuwa da kai ba’- “Ba zaki mutu ba, ki saka juriya a ranki, babu wani abu a raina dangane da Zulaihat, asalima ba ma jituwa da ita kwatakwata. kuma asali ya samo ne ganin yadda take “‘shisshige min”Ka jiko”.

Hira sosai suka sha har sai da magriba ta kawo kai

sannan ta tafi don zuwa ta dawo ta kwana tare da shi bayan kowa ya watse.

Sati guda ya yi aka sallame shi kuma ya samu

kwari sosai abin ka da Asibitin kudi, a gidan su ya fara zama ganin cewar zai takura ya nemi Al’amin da su koma gidan sa tare. Duka duka jinyar kwana biyar ya Kara yi ya koma bakin aikinsa, duk da cewar sai a hankali, a wannan kwanaki biyar din ya yi bincike ya gano cewar Balarabe

Sa’ad na da alaka tsakanin sa da Abbas, mahaifin Abbas, Alhaji Mashiro, akwai jitawa numbobin wayoyinsu a wadancan lokutan. Sai dai babu layin na Balarabe Sa’ad ya jima a kwance yana nazari

Saboda haka dole akwai bukatar a samo

Abbas don ya duba number mai suna Balarabe,

Barazanar da Abbas ya yiwa ‘Yasmin ta gidan sa shine zai tabbatar mata da cewar ba shi da kiris, domin ya fito da makaman da zai iya tsare manafinta da su, wannan dalili yasa ta hakura ta koma gidansa tun bayan kwana uku da faruwar hadarin, sai dai bai san kowanne motsinta ba.

Duk safiya Yasmin ke shirya wa Umar abin da zai karya, su zauna a cikin gidan sa su yini suna hira, abin yana Kara dugunzuma wa Zulaihat rai matuka da gaske. A ranar da Umar ya koma Office dinsa

abubuwa suka ci gaba. Sai dai abubuwa sun toshe masa domin ya lura da saka masa ido da Munir babban yaron Abbas ya yi har ta kai cewa yana bibiyarsa duk in da ya fita, ya lura da haka ne saboda ganin motar sa bibiyarsa. Ya zama dole ya kaucewa wanna bibiyar tasa domin zai iya gano shirin su, in sun gano kuma zai iya nisanta su daga nasarar da suke bukata Dan haka ya yi wa Muhsin abokinsa kwararre ne wajen satar page ya nemi da ya duba waya

ma’aikatan JIS na tsawon shekaru goma fitar masa da sunan wani wadda ake Kira bayan ya yi haka ya yi kokari ya samar masa da

 da faruwar hakan Muhsin da yake kwana

ya yi akan aiki yasa mu nasara yin kutse na cikin dacument din campany ya yi duk mai yiwuwa ya samu sunan Balarabe Sa’ad wadda shi ne kadai mai sunan, sannan kuma baya cikin sabon jadawalin ma’aikatan su a yanzu”Lokacin da ya hattama wannan aiki shi kuma Umar da- Alhaji Sunusi suka je unguwar don yin binciken Umar, sun yi sa’a sun samu cikakken da tabbatarwa ya zauna a unguwar sannan ya bar unguwar a tsakanin lokacin da aka samu akasi

na afkawar wannan qaddarar. Sun bukaci sanin in da ya koma babu wadda ya sanar dasu, amma sun yi zargin wani abu daga cikin mutanen da suke

tambaya dan haka Umar ya fuskanci mutum da ya gane cewar akwai sanayya sosai a tsakanin su da Balarabe don haka ya ja shi gefe guda.

*Na san ka san in da yake, kana jin shakkar ka gaya

mana, in da yake, ba hukuma ba ne mu, sannan muna neman sanin wani abu ne da ya shigar da bawan Allah can da kake gani cikin tsaka mai wuya babu wadda zai cire mana wannan shakku illa shi, idan har ya fito ya sanar da mu, to na tabbata zan ninka masa abin da aka ba shi ya gindayo a takanin mugayen mutanen da suke saka mu cikin tararrabi”.

Da jin haka sai mutumin ya yi gyaran murya “Mai gida,

ko nawa za ka ba shi ba zai zo ba, amma ni idan ka ba.ni zan gaya maka in da yake”.

Dabarar da Umar ya yi tayi don haka sai ya yi murmushi Yace yadda da kai?” Mutumin ya yi dariya yace Ba dan uwana bane, daman ina cikin bukatuwar kudi a matsayinsa na abokina yadda ya rufa masa asiri, ga duk wadanda suko taho nemansa, shekara daya daya wuco na bukaci ya ba ni

so bayan kun tafi nakira shi na gaya masa cewar ya bani kudi ko na tona masa asiri, to jin ka fadi kudin da zaka ba shi yasa na ji cewar bari ni ku ba ni na fadi in da yake tun kafin ku kubuce min”.

Umar ya yi murmushi “Biyo ni mu je”.

Suka koma wajen Alhaji Sunusi duk abin da ya faru

Umar ya kwashe ya sanar da su. Take Umar ya ce “Nawa ne kudin hayar taka?”

“Ina biyan dubu dari uku da hamsin” .

“Idan mu kabaka dubu dari biyar ya yi”.

Dariya mutumin ya yi yace Sun ishe ni, ba kuma abin da zance da kusai godiya”.

“Ba ni account din ka”

Ta ke ya bayar Umar ya zuba masa kudin. Daga nan ya basu cikakken address da kuma lokacin da ya dace su je zasu same shi.

Alhaji Sunusi ya yi farin ciki matuka da Kokarin da

Umar ya yi. Suna tafe cikin mota Umar ya dubi Alhaji Sunusi ya ce “Ba bukatar mu saka ‘yansanda a cikin lamarin nan, ya zama dole mu ma mu yi aiki da ‘yan zarra marasa kunya, saboda su yi aikin da ya dace domin su dauko mana shi, sannan su matsa shi har sai ya yi magana”.

Alhaji Sunusi ya jinjina kai ya ce “Ka yi tunani mai fadi, to amma su waye zasu iya yi mana aikin nan?”

“Akwai ma’aikatan da na bukace su da su zo daga kano yarane matasa masu budadden ido, babbancin su da sauran tsageru su suna neman kudi, sannan suna da suffar ban tsoro, duk abin da mu katsara musu zasu yi”.

“Sai ka bi a hankali saboda gudun kuskuren abin da zai sa kai ma ka shiga matsala”.

“In sha Allahu babu matsala zamu yi komai cikin kulawa”.

Lokacin da ya suka rabu da Alhaji Sunusi kai tsaye gida ya tafi, don ya kwana biyu bai leka gidansu ba, saboda yana gudun zancen Zulaihat da mahaifiyarsa ke yi masa, yau kuma

ya shirya tsaf dan fahimtar da su iya alakar da Zulaihat babu wani abu wai shi so.

A lokacin da ya shigo gidan, Baba na nan, Yaya Khalil ne baya cikin gidan kawai, don haka ya gaida Baba da

Mama, suka nutso suna hira.

“Da gaske ne mijin yarinyar nan Yasmin ne ya yi maka haka?”

Umar ya yi shiru yasan ba wanda zai gaya musu haka sai Zulaihat, tun da kaf ita ce ta san mu’amalarsa da Abbas, shi ma yadda Yasmin ta tabbatar da shi din ba ne. Suka yi ido biyu da mahaifinsa su biyu suka dauke kai daga duban juna hakan ya tabbatar masa da cewar mahaifin nasa yana so ya fuskanci wani abu a tsakaninsa da Yasmin da kuma mijinta dan haka ya gyara murya ya dubi mahaifiyarsa yace

“Mama wai me yasa ku ke shakka ta ne, me yasa yanzu kuka dauke amincin da ku ka yi min ne, shin ba ku yadda da ni ba ne, shin ba gidan nan ba ne gidan aminci, mama kice bakya yadda da cece kucen mutane, me yasa yanzu ki ka fi aminta da wasu mutane akan dan ki”.

“Zulaihat kake nufi, tana da kirki yarinyar nan mutuniyar arziki ce mai kaunarka da gaskiya, na yadda da kai a lokacin da zuciyarka bata gaya maka karya a game da yarinyar can, ta ci amanar ka, yanzu kuma ka zama wani tana so ta kashe auren ta tazo ta rayu da kai, wannan shine ko ban hana ba Allah ba zai bari ba

Dariya Umar ya yi ya ce “Mama Yasmin da kike fada ba ta ci amanata ba, ba kuma ta yaudare ni ba, domin ni kuwa akwai boyayyen wani abu abu, wadda ba kusa ni ba, za kuma kusan shi tan ba da jima wa ba, amma abin da nake so dake Mama

babu wani abu a tsakani da Yasmin face

Hmmmm

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE