MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 24 BY RABI’ATU ADAM SHITU
Balarabe har shi ya zama mutum na budu sai Alhaji Sunusi wadda za a kira shi idan an samu nasara kamo shi. Sun yi shigar kotakwana, sunyi shiri na musamman domin daya daga cikinsu da ake kira isyaku, tun magriba ya samu tsugunnawa a cikin unguwar, yana kuma sanar da su duk wani motsi.
A cikin motar kirar SIENNA suna zaune a cikin motar
Umar na gaba shi da direba mutum dayana baya a zaune.
Balarabe mutum ne hatsabibin gaske wadda ya shahara akan rashin gaskiya, yana zaune a unguwar ne, domin badda kama iyalansa kuma na zaune a wata unguwar daban, dan haka wasu lokutan baya zuwa wanna gidan da ya kwana, yana zuwa wajen iyalinsa, in zai zo wannan gida sau tari da karuwarsa yake kwana a nan, in har bai zo da karuwa ba to akwai was mutane da zai hadu da su wadanda suke har kallolinsu tare
Misalin Karfe dayan dare Umar ya dubi agogo “Duk da cewar muna da lasisin da zamu wuce akan tituna idan jami’an tsaro sun tare mu, yakamata mu gane cewar ba zai zo ba, Sama’ila ka-kira wo Isyaku mu tafi
Sama’ila ya kira Isyaku. Isyaku yazo ya same su ya shiga mota har sun tashe ta zasu bar wajen kawai sai suka ga hasked fitilar mota ya haske kofar gidan. Suna ganin haka mutum biyu daga cikin mota wato Sama’ila da Isyaku sukai saurin fita daga motar suka tsaya a inda ya dace ba tare da wani ya ankara da su ba.
Abbas ya yi zama yana jiran kadan ya zaburi motar zuwa in da suke, shi kuma Alhasan ya tsaya a daidai kofar motar yana jiran yaga abin da zai fara.
Har Isyaku da Sama’ila suka je kusa da motar ta shi, baya tare da kowa. ya fito daga motar ya dubi gabas da yamma gudu da arewa babu motsin komai. Sannan ya fara takawa zai je ya bude get din gidansa Kafin ya ankara ya Ji an rungume shi, an shaka masa wani abu a hanci, bai kara sanin in da kansa yake ba sai wajen karfe budun asuba a daddaure a wani dogon gini.
Ko da ya farka babu wadda ya kula shi, har sai da safiya tayi Umar yazo, da Alhaji Sunusi misalin Karfe bakwai na safiya sannan suka fito da shi suka gurfanar da shi a gaban su Alhaji Abbas ya dube shi duba na tsanake sannan ya yi masa murmushi anan take ya bada umarni a cire masa abin da aka rufe masa baki da shi. Aka bude masa “Me na yi muku, mene ne hadina da ku”
“Kwantar da hankalin ka, ba kamar ka muke ba mu, saboda ba mugaye ba ne mu, mun daukoka ne bisa wata bukata tamo, idan ka biya mana bukatarma, shi ke nan zamu sake kaka yi tafiyarka, idan kuma ka gaza warware mana zamu yi ramuwar gayya akan ka”.
Umar ya sanar da shi yana duban sa. Alhaji Sunusi kuma ya ce “Ka gane ni?”Ni ban san ka ba”
“To shi ke nan, baka sanni ba, amma mi na san ka, ka sani na yi signing akan takaddun bogi da kamfanin JIBS wadda Abbas ya saka ka ka aikata min hakan”
“Ni ban san abin da kake magana a kai ba, ba ni bane, ban sanka ba sannan ban san wani Abbas ba”.
“Na gaya muku dama ka da mu dauki doka a hannunma, mu kai shi ga hukuma kawai, tawa mai sauki ce na tabbata ban aikata ba, idan mun je ga hukuma zasu san yadda zasu yi da shi ya fadi gaskiya.
“Wannan furucin nasa yana daga cikin shirin da suka hada baki zasu yi a gabansa, domin sun san cewar ba zai so ya je ga bukuma ba, tunda komai nasa a boye yake yi, hakan ya basu damar fahimtar huluma manemansa take yi.
Alhaji Sunusi ya mike “Kuje ku kai shi, Allah yana tare da mai gaskiya”
Har sun mike zasu tafi da shi ya ce a tsaya. “Me ku ke da bukata?”
Alhaji Sunusi ya dube shi “Mun riga mun sanar da kai, amsa kawai muke bukata, ya a ka yi aka hada wannan al’amarin kuka yaudare ni”
“Ni ba ruwana a ciki, an saka nine kawai akan hakan domin a dora maka laifi daganga
“Ban gane dagangan ba”.
“Duka duka shiri ne karya ne, takaddun da duk wani abu da aka yi amfani da su karya ne, an yi haka ne don a saka tsoro a zuciyarka, ka basu abin da suke bukata, police din da suka zo office dinka suka nema ka har Abbas din ya turo lauyoyansa a lokacin duk na bogi ne, babu kamshi gaskiya a i cika”Karya kake yi?”
“Wallabi wanna ita ce iyaka gaskiya, kudi aka bani masu yawa saboda in boye kaina, aka yada cewar an kama mu, amma da ni da wadda mu kasa ka yi wannan aikin ba ma cikin wata matsala, ka je ka yi binciken Rufa’i Dahiru zai
-warware maka komai, ya bibiyi rayuwarka yana so ya warware maka komai saboda tsoron haduwarsa da Allah to amma kuma sai Abbas ya yi masa barazana da biyansa dukkanin kudadensa sannan kuma zai sa kafar wando daya da shi, tsoron sa da ya ji yasa yaja bakinsa ya yi shiru”
Umar da Alhaji Sunusi suka dubi juna sun gasgata shi suka mike a tare “Abbas ku ci gaba da kula da shi zamu je mu yi binciken mu”.
Abbas ya gama shirinsa tsaf zai fita wajen aiki ya nufo dakin Yasmin. Ya same ta akwance saboda sanin shi ne ko waigowa ba ta yi daga yadda take ba.
“Idan kin mutu kin cutar da ni, domin rayuwata ba tare dake ba, zan rayu ne cikin mugun yanayi, Yasmin ki daure kirayu domin ina so watarana tazo ace muna rayuwa a matsayin mata da miji masu matukar so da kaunar juna’.Ta tashi zumbur daga in da take kwance “Har abada, wallahi azimin har abada, tsantsar tsanar ka ita ce kadai zata ci gaba da rururwa a cikin wannan zuciyar”. Ya kai mari ya- kai gwaro ya dauke wuta da jin kalamanta, babu yadda ya iya dole ya jure jinta tunda ya riga yasan halin da ake ciki. Ya Runshe haushinsa.Rana daya zaki fahimta Yasmin, ni mai kaunarki ne”.Ta juyar da kai da barin kallon sa. “Duk abin da ka Kudundune domin ka same ni ya kusa zuwa karshe Abbas, ni da kai har abada”.Ya dan yi wani murmushin takaici ya fice daga
cikin dakin nata. Kai tsaye motarsa ya nufa. Yana
shiga kiran Munir ya ratsa motarsa “Kamar yadda ka
umarta, babu Balarabe a gidansa, babu shi kuma a
inda mu ka ajiye shi, sannan motarsa na kofar gidan
da alamun akwai wani abu da ya faru”.
Katse wayar ya yi domin neman lambar
makocin Balaraben wadda shi ma takanas aka ajiye
shi domin ya dinga lura da shige ficin balaraben.
“Mas’udu ya ake ciki baka sanar da ni da wuri
ba”Ranka ya dade ba ni da zarafin da zai katse ka
daga bacci dan haka nakira yaron ka na sanar da shi,
motar Balarabe kadai ce sannan ko gidan ba abude
ba, sannan jiya wasu suna maganar cewa akwai wani
da yake ta kai kamo a wajen gidan nasa”
Maganar da ta gaya masa yanzu ta fado masa a
rai akwai muna tabbatuwa a cikin maganarta babu
tsoro kamar a baya da in zata yi masa magana dangane da abin da yake kange a tsakaninsu.
“Tabbas biri ya yi kama da mutum””, take wani tunani ya fado masa, tuntuni yake so ya sarke su daga afkawa cikin wani takunkumin amma yana ganin wannan ba zasu gano karshensa ba, don haka ya yi maza ya kira Munir ya sanar da shi cewar ya shirva masa ‘yan mata guda biyu’ wadanda zasu bada hadin kai, ya basu kudade masu yawa cewar zasu bada hadin kai wajen aikata abin da zai shirya.
Abin da ya so ya yi a farko ya saka kaninta ya yi kisan kai, kisan kan wasa, wadda kuma yaron zai tabbatar dagaske ya aikata kisan, idan ya aikata haka zai ci gaba da rike Yasmin a matsayin matarsa, domin abin zai tsaya a tsakanin su idan har za ta rabu da shi to zai tona musu asiri akama Kanin nata a rufe, yasan idan ya aikata wannan shirin zai ci gaba da zama da Yasmin har Karshen rayuwarsa da ita
Ya yi wani ni’imtaccen murmushi ya fada a sarari “Babu wadda zai raba ni dake, babu shi”.
Kai tsaye ya tuna da Zulaihat, bai bata lokaci ba ya nufi kamfani kai tsaye office dinta ya nufa.
*In kin amince zamu hada hannu dake, kamar yadda kika bukata a baya?”
Wata shu’ umin murmushi ta yi ta kalle shi “Ka makara”.
“Ban makara ba, idan kin san cewar mugun kallin da nayi na rufe nake tare da Yasmio an rugaza shi, Yasmin dab take da ta bar gidana, sannan
Hmmm