MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 3 BY RABI’ATU ADAM SHITU
MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 3 BY RABI’ATU ADAM SHITU
Zaid dake gefe ya dubi Dady “Amma Daddy idan ta yiwa Abbas haka ba a yi masa adalci ba, dukkan gidan nan sun manta da ranar BIrtheday dinta amma shi yana rike duk wani abin, da, ako bukata ya siya hatta hall din da za a yi taron ya tanadar, ina tabbatar maka da cewar zai sauya mata mota a ranar kamar yadda ya saba, don me yasa za ka ce haka”
Alhaji Sunusi ya yi shiru yana jinjina lamarin. Ya*
dubi yarsa “Kina son shi?””Dady bana ko san ganinsa”To me yasa idan ya baki abu kike amsa”.
“Daddy akwai abin da ka rage mu da shi ne?”
Ya girgiza kai yana dubanta “Bai taba ba ni abu na amsa sai da tilastawarsa da Mom”.
Ya shaki iska cikin bacin rai “Kada ki yarda zalamar ki tayi tunanin zaki yi amfani da yarana domin biyan bukatar kan ki, ba zan lamunci wannnan ba”Yadda take hararar Yasmin din ya taba ransa Zaid ya kawar da daddy abin dake kokarin fadi.
“Daddy Abbas na son yaya so ba na wasa ba, ka da ku yi masa haka Daddy”Rufe min baki, da wane hankalin za ka iya fahimtar
abin da ya dace da wadda bai dace ba, ka da ka kara shigo min magana ina magana”
Ran Zaid ya yi matukar baci ya mike da sauri ya bar wajen ya nufi dakinsa.Yasmin ta mike da sauri ta bi bayansa, shi kansa
Daddy sai da ya ji bai kyauta ba da ya fadi hakan amma hakanna ya cije bai bi bayansa ba, domin yana gamin soyayyar da ake nunawa Zaid ita take sawa yakeyi abin da yake so a cikin gidan.
“Abin kunya ne abin da kake shirin yi a gare ni,
butulci ne in har za a dubi Abbas a hana shi auren Yasmin, da wane irin ido zamu dubi Alhaji Hashim ka sanar da shi cewar “yar ka bata son dansa da aure don haka ba za a ba shi ba?”
* Kallon ta kawai yakeyi amma shi yanzu hankalinsa ya tafi akan dansa ya fita daga cin abinci ransa a bace zai iya ya tafi akan all ba tare daya iya sha ba, saboda kawai abin da ya yi masa yanzu. “Ka ba ni amsa”
Ta Kara katse shi bai saurare ta ba shima ya mike ya bar dinning amma ba dakin Zaid din ya nufa ba kai tsaye waje ya fita domin ya samu sukuni.
Zaman cin abincin su ya tarwatse ba tare da an yi
abin da ya dace ba Yasmin ta same shi a daki yana zubar da hawaye hankalinta ya yi mugun tashin tana son dan uwanta tana kaunarsa su kadai ne a duniya, basu da yawan dangi basu da kowa a. rayuwarsu. Ta zo kusa da shi ta zauna.
“Zaid”Ta ambaci sunansa ya juya mata baya ta kamo hannunsa ya fizge “Kana fishi da ni ne Zaid:,Ba tare da ta ji amsar sa ba ta ci gaba da cewa “iyakar mu ke nan a wajen mahaifan mu, ba mu da kowa ba mu san kowa ba sai junan mu. Idan za ka iya fishi da ni, watarana za ka iya rabuwa da ni gaba daya a rayuwarkake nan”.
Ya mike daga zaunen da yake yana hawaye ya ce
“Yaya kina jin abin da daddy yake fadi akaina, ni ke nan ban isa na shiga maganar ku ba, ko ban isa na hango alkairin ki na goyi bayansa ba”
“Zaid Mun haifi iyayen mu ne?’
Ya yi shiru ya kada kai “Mun fi su sanin abin da ya
dace da mu”Ya Kara kada kai “Daddy shine Babba, da Mommy da ni da kai dukka a karkashin ikon Daddy muke”To Amma yaya idan kin amince kina son Yaya Abbas Daddy ma zai amince?”
“Mene ne damuwar ka da wadda nake so da wadda bana so Zaid? Ko kana so ka rasa murmushi na farin cikina da dukkan rayuwata ne?”Kin fi kowa sanin na fi kowa son walwalar ki
Yasmin”To ka daina danganta ni da abin da bana so, na tsani Abbas bana son shi Zaid, Dady ya dakatar da kai ne daga shiga sabgar maganar da bata shafe ka ba ne, domin bakasan mene ne so ba, a Kokarin son ganina tare da Abbas hakan shi zai haifar da ‘mummunar alakar da za ta zo ta zama an yi rabuwa uwar watse, ba laifi ba ne don ka gaya wa mutum gaskiya akan ra’ayinka, amma laifi ne ka boyewa mutum ra’ayinka akan karya.”
Ya fara fahimtar ta, “Kuma ka ga Daddy na fama da kai akan yawo da kuma shaye shaye, wadda na tabbata har yanzu baka daina ba, shi ke nan Zaid da alama bakin cikin ka shi ne zai kashe mu duka a rasa family kamar ba a yi mu ba “
Ya gyara zama “Yaya ya zan yi, ko na daina sai na dawo na rasa yadda zan yi Yaya?”
“Da yadda za ka yi Zaid, ka Kauracewa abokan da suke baka, ka daina zuwa in da suke, ka zauna a gida tare da mu, muddin ka bar gida, ka na yawaita dauko wani abun da zai faranta ranka akan waccan abin Zaid ina tsoro ace dan uwa na ya haukace?”Ta fada ta kama zubar da hawaye. Shi ma kuka ya fara yi ya ci gaba da cewa “Ba zan Kara ba yayana yi miki alkawari zan bi dukkan shawarar da ki ka ba ni”
“Idan har ka yi hakan ka faranta min raina, zan
kasance cikin farin ciki”.Wannan rayuwar gidan
Alhaji Sunisi ke nan mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa domnin kyautatawa iyalinsa.
水米
Katafaren gida ne mai dauke da duk wani abu da ake bukata a ciki gidan abin da ya kama Lambu, filin motsa jiki, wajen shan iska, da dakunan barkatai na zaman mazauna gidan, idan ka na cikin gida ka dauka wata ma’ aikata ce daban. Dukka a cikin gidan mutum uku ne suke rayuwa a matsayin dangi sai masu yi musu hidima rututu.
Gidan Alhaji Hashim ke nan babban attajiri da yayi fice a Nigeria da.Ghana da Nijar da saukan Kasashen da suka yi makota ka da juna. Dan kasuwa ne, kuma mai hannu da cikin gwamnati ne kace kace, ba don komai ba sai taimakawa da daukar bataliyar ma’aikata da suke Karkashin kamfaninsa Na kere Kiren gidaje da kamfanoni da kuma manyan hotels babu wani mahaluki da ya wuceshi ko kamo shi a wannan da ira. Dan sa daya Abas suna matukar kaunar sa, sun mugun sangarta shi sangarcin da ya kai a yanzu ma ba sa iya control din dabi’ unsa. Babu wani abu da yake so a rayuwarsa da basu ba shi yanzun ma cikin fushi ya shigo cikin gidan a cikin tsadaddiyar motarsa. Ya faka a daidai a partement din daki
Amadu dake tsaye a wajen motar Daddy ya bazamo da sauri ya bude masa motar.
Ya fito ransa*a matuka bace ya shiga cikin gidan
Amadu ya dauke motar zuwa inda ya dace,
A lokacin da ya isa kai tsaye Bangaren cin abinci ya yi saboda ya riga da yasan time ne na dinner. Shi su ke jira yana zuwa ya same su a zazzaune suna saurarensa. Murmushi Hajiya Zulihat ta fara yi a lokacin da ta saka shi cikin idon ta mahaifinsa ya lura da yanayinsa tun lokacin da ya zauna.
Bai yiwa kowa magana ba haka ba fara’a ya dauki cokali ya kasa saka abincin abakinsa. Mahaifinsa ya nisa ya ce.Akwai matsala ne my son?” Ya dube mahaifin nasa yana mai cije labe ba tare daya ce komai ba ya yi yunkurin barin wajen. Mahaifinsa ya yi saurin dakatar da shi, “gaya min damuwar ka, ka sanar da ni bukatar, kai da na ne, ban ga dalilin da wani abu zai bata ranka, in har kuwa akwai wani abu da zan bari ya bata maka rai to ban ga amfanin fadi tashi na ba, Abas, kai ne magajina, kai ne kadai dan da na haifa kuma nake matukar kauna a rayuwata. Babu wani da face kai sai da mahaifiyar ka ta haifi ‘ya’ ya har guda hudu suna mutuwa, kai ne daya ka rayu, dukiya bata iya siyan da, kai ne kyautarmu mafi soyuwa a ran mu, ka sanar da ni damuwar ka” Abas ya dakatà ya dawo ya zauna, yana duban Mahaifinsa, cikin kakkausar murya ya dubi mahaifinsa “Sau nawa, sau nawa nake sanar da kai cewar ina son Yasmin, sau nawa nake sanar da kai ina kaunarta, sau nawa ina gaya maka ita ce rayuwata, sau nawa Dad, ko sai ka rasa ni a rayuwata za ka fara danasani”
Alhaji Hashim ya yi dif kamar an dauke lantarki jinin jikinsa. Zan yi magana. Ya raunana murya “My son…. ‘ “Dad idan ka san ba za ka iya ba kada ka Kalubalance ni a ranar da ka waye gari bana tare da kai, zan iya komai akan ta”
Hajiya Zulaihat ta fara “Kwantar da hankalinka dana, wace ce Yasmin, takamar da suke yi na abin da suke mallaka mu ne, mu ne gatan su, saboda haka babu wani abu da zai hana ka aure Yasmin. Ya dubi Zulaihat “Nagode Mom”
Ya ta shi ya bar wajen ko ba komai ta Kara masa
Karfin gwaiwa. Har mahaifin ya yi yunkuri tada shi mahaifiyarsa ta dakatar da shi. Sai da ya shiga sashinsa sannan ta fara.
“Ya zama lallai ka daina tunanin kin amincewar
mahaifinta, ya zama lallai dan mu ya samu abin da yake so”Ta na fadin hakan ta bar wajen cikin tsananin fushi.
Suka bar shi yana jinjina girman al’amari da kuma ta yadda zai biyo masa babu wani mutum da yake shigo masa a cikn ransa tamkar Alhaji Sunusi, yasan halinsa farin sani idan har dansa na bukatar abu in har mai kyau ne zai jagorance shi wajen samar masa da shi, in mara kyau ne kuma cikin hikima da dabara zai zai cire musu shi arai, kudi ba abin da Sunisi ya rasa bane, saboda
-haka amsar Yasmin a hannunsu babban abu ne mai girma, yadda kuma ya fahimici yarinyar ta tsani Abas mummunar tsana.
**
Yasmin na zaune wani abu ya tsaya mata a rai, amma. kuma ta rasa mene ne, kwakwalwarta ta cunkushe ta rasa tsayar da ita daga wannan sabon yanayi da ta tsinci kanta a ciki. Tabbas ta san ba batun Abas ba ne domin Abas ba ya fiye damunta, illa. dai kawai takura ce zai yi abin ya gama. Bata so mahaifinta kuma kullum alkawarinsa ba zai taba yi mata dole ba.
Lokaci guda ta tuno da yanayin yadda yake dariya a lokacin da yake zaune yana.amsa mata magana bayan ta yi. Ba ta san lokacin da ita ma murmushin ya suduce mata ba. Waye wannan daga ina yake. Ko ma dai mene ne yana da kirki.
Lokaci guda sai ta ji wannan abin da ya cunkushe
mata zuciya ya warware lokaci guda. Har ta ji karfin dauko computer domin ta fara zane gidaje kamar yadda ta dauki aikin Zanen gidaje goma a a layi daya. Wata kwangila ce da mahaifinta
Hmmm