MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 4 BY RABI’ATU ADAM SHITU
MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 4 BY RABI’ATU ADAM SHITU
shi, saboda haka take ta,son ta Kammala kafin safiya.Ta samu kwarin gwiwar yin aikin yadda yakamata, sai dai abin da kamar wuya bata saba shiga unguwannin talakawa ba, ba ta san ire iren abubuwan da ya dace da gidajen ba, dole ta na bukatar taimakawar wani, duk da mahaifinta yasanar da ita cewa, ana bukatar gidaje, masu dakuna uku, sai a fitar da bandakuna biyu, sannan kuma za a fitar da wajen adana mota, da wajen shan iska, da kicin. Ta taba yi masa zanen manyan gidaje guda shida,
kuma ya yi amfani da su ya yi sambarka, sai dai kuma wannan karon dole tana bukatar taimako. In da ta samu akasi ta saka bandakuna duk a cikin dakin, kuma tana tantama a hakan.
Dole ta samu wani wadda yake rayuwa a cikin irin gidajen nan ta yi masa tambaya, duk kawayen ta manya ne babu wadda zai fahimce ta, sai dai kuma akwai wani wadda take tunani zai taimaka mata.
Da sauri ta dauki wayarta ta kira shi, sama tai kira uku bai daga ba. Ta ajiye wayar ta ji ba dadi da aikin zai tsaya ma a iyanan, akwai bukatar ta je ta tashi Daddy domin ya Kara yi mata bayani tunda shi kwararre ne.
Har ta mike sai kuma ta ga katin da umar ya ba ta. Da sauri ta dauka ta karanta aderss dinsa, tabbas zai iya taimaka mata to amma nakira shi a wannan lokacin. Ba ta da wani zabi illa ta kira shi.
Kai matsalar kake nan, ka na mayar da kan ka baya,don ka hadu da yar masu kudi sai ka yi tunanin ba za ta so ka ba, saboda kai ba ka da shi, ka daina wannan tunani, duk wacce kake so a rayuwa ka sanar da ita, Hausawa na cewa kin ta yi ake barin araha, ka da ka yi kasa agwiwa muddin ta ci gaba da zuwa rayuwarka, to ka sanar da ita, za ka sha mamaki”.
Umar ya jinjina kai “Ta tafi Al’amin abin da zai sa takira ni sai dai gyaran….. Wayar sa ta yi Kara a lokaci guda, ba tare da wani
damuwa ba, kafin ya dauko ya fara cewa “Dare ya fara yi Baba zai rufe gida bari na je”
Yana kallon number ya ce “Ba shi ba ne, Hello ya amsa Da fatan ban tashe ka daga bacci ba”.
•Ya dan yi shiru yana nazarin muryar tabbas in ya canka Yasmin ce. “Banyi bacci kamar zan iya cankar mai magana?” Ta yi dariya “Idan har kuwa ka canka, akwai lauje cikin nadi ina jin ka muryar wace ce?” Ya yi murmushi ya ce “Kamar Yasmin, wacce na gyara computer da zu”
“Kai! Ya a ka’ yi ka yi saving din murya ta”
Ya yi dariya yana tabo Al’amin yana yage baki.
– “Dagaske na canka dai-dai”
“Tabbas nice, amma na yi matukar mamaki, ya aka yi haka ta faru?”A’a hakan ta faru saboda duk macen da na ke waya da ita na san muryarta, wannan kuma bakuwa ce, na zargi cewar ko wani abu ya faru da computer ki ne ki ka nemi”Shi ma ya fadi hakanne kawai don kada ta ga zakewarsa. “Ka tabbata da abin da ka fada”Of cource”Ni ce again, I need your help?”.: Ya gyara zama,Ina jin ki”Ka na wata area ne?”Tsoro ya kama shi, ka da wani abu suka rasa a gidansu suke zarginsa.Akwai wani abu ne?’No akwai wani aiki da mahaifina ya saka ni na zana masa Kananun gidaje so wallahi na gaza fahimtar yadda tsarin yake, kayi hakuri ban san yadda zan ce maka ba, kawai dai ina bukatar sani cewa duka ana barin toilet guda daya a farfajiya waje, ko kuwa za a iya barinsu a ciki duka’Dariya ya yi domin ya fara fahimtar ta ya ce Yasmin, na fahimce ki wato ke me zane gidaje ce” Ta yi dariya yaanayin da ya fadi sunanta sai ta ji a yau ne kadai aka fadi sunan dai-dai yadda ake so, ya fito.Eh kuma su ne sabgar mahaifina, yakan sa ni a cikin ayyukansa sau tari, to amma manya yakeba ni, wannan ya ba ni ne don jarrabawa. To kuma ina so na ci jarrabawarsa, domin ina son na zama busy na taimaka masa”.
“Na fahimceki, to bari na wassafa miki gidaje kananu yadda suke kamawa, tun dake mai zane ce kin san yadda zaki yi, yakamata ace, duk gida yana da toilet a tsakar gida, ko wani wajen da ba sai an shiga cikin falo ko daki ba, kowanne irin gida ne kuwa in dai Karami ne wadda bai wuce piloti ko rabi ba, haka ma kwater. Ta yi murmushi “Ban san irin godiyar da zan yi makaba, na gode Umar”
Yadda ta fadi sunan nasa yaji sautin tamkar fitar”busar sarewa yana kayataccen murmushi.
“In ba damuwa ka ajiye number ta muna gaisawa lokaci lokaci, na ga alamar za ka taimake ni da yawa a rayuwata”Na ma riga nayi ranki ya dade”Ta yi murmushi suka yi sallama da juna. Ta ajiye wayar tana murmushi ta dan samu dan lokaci ta na kokarin gano abin da yake cikin ranta, amma ta gaza. Ta samu bacci mai dadi yau.
Shi kuwa a daren da yake kokarin tafiya gida sai da ya kusa Kara awa daya yana bawa Al’ameen labari game da yanayin Yasmin. Sannan ya tafi gida ya samu bacci mai dadi mai cike da mafarkin ta. Kamar kullum da kodayaushe Yasmin ta na da office
da mahaifinta yabude mata ta kan je ta yi wasu ayyukanta domin ta ce bata bukatar ta yi aiki a kamfanin su wato WOLD DECORATED AND AND BUILDING wato WDB COMPANY wanda yake kan babban Titi Abuja zuwa Lagos.
Ta zabi ta zauna ta yi ayyukan ta ita da kawayenta saboda ta san muddin za ta zauna a kamfani tofa Abas ya samu abin da yake so domin zai matsawa rayuwarta, ya hanata rawar gaban hantse, wannan dalili yasa mahaifinta ya kera mata dan káramin Karamin guri wadda za ta nemi na kanta da kanta ta'” sanya masa suna YASMIN HOUSE BULD.Ma’aikatan ta uku, kawar ta Khadija, sai wata da suka samu tana taimaka musu Rafi’ at. Ta kan fita karfe tara na safe ta dawo karfe biyar na yamma a duk ranakun ban da juma’ a da lahadi.
Kamar kullum ta iso office din ta, cike da fara’a
domin yau an wayi gari Asabar, jiya juma’a ba ta zuwa aiki, ta faka motar ta ta rufe ta shiga ciki Rafi’at ta na mata sannu da zuwa ta amshi jakarta da sauran takaddun ta.
“Khadija ba ta karaso ba?”
“Ba ta karaso ba Hajiya”
Ta duba agogon dake daure a hannunta, kafin tara ma ba ta yi ba, lallai ta zo da wuri, ta na kokarin zama ta hango Khadija na adana motar ta. Ba tà san me yasa ta sakin murmushi ba, ta shiga cikin office din ta. Ta zauna Khadija ta shigo da sallama cikin office din, suka hada ido Khadija ta sakar mata murmushi “Lafiyana ganki cikin farin ciki haka akwai labari ke nan”
Ta daga idanuwa ta na dubanta “Farin ciki kuma, ni dama akwai damuwa a tare da ni ne?”
Khadija ta ce, “Ba ki da wata damuwa, amma ki sani ni ba bakuwar ki ba ce, totally kin sauya yau kallon farko na fuskanci hakan,
“Na yi wani aiki fa ba tare da sanin ki ba”.
Khadika ta dube ta “Kamar ya ya?”
“Daddy ya ban wasu ayyuka na yi su a gida, ban kuma tuntube ki ba”.
“Ke kar ki raina min hankali shine sabon abu, da
kuma zai zama kamar kin min ba dai-dai ba speak wani abu ya faru ne, Oh na manta, ki na farin cikin gobe birthday din ki za a sauya miki mota”.Nan ta ke fuskar Yasmin ta sauya. Ita ma Khadija dagangan ta tabo mata nan domin yanzu ne za ta same ta a nutse har su yi maganar da yasa ta yi zuwan wuri yau, kuma ta sauya sosai haka lokaci guda” Ranta ya sosu sosai, ta hade fuska “Bana son haka
kin sa ni Khadija”Eh ni ma na sa ni, amma kina ta min wasa da hankali akwai labari a bakin ki kin tsaya kina min kame kame?”
Ta yi wata dariya ta ce “Ke din ce sai da jan rai,
saboda son jin gulmar ki ya yi yawa, ba kya iya hakuri”Eh na ji, mene ne a gaya min”.
Tayi shiru tana murmushi ta na kallo Khadija “Kin san me?’Khadija ta kada kai cikin gajiyada jan ran Yasmin. Yasmin ta Kara kyalkyale dariya domin ta gama kai Khadija in da take so zuwa.
“Khadi am doubteful, my hert really shock”.
Khadija ta tattaro hankalinta waje guda don ta ga mutuniyar ta dawo nutsuwa kuma tana so ta sauya daga haske zuwa baki.
“Ban fahimce ki ba, Yasmin ki tafi kai tsaye ki gaya min”.Khadi, yau daya zuciyata na bugawa, sannan tana cikin tsoro, sannan ta shiga cikin zurfaffen tunani, na rasa dalili kai tsaye”Khadija ta dube ta ta fahimce ta sarai. “Ba ni labarin bayan barin ki nan kin je kitso mai ya faru”.Yasmin ta yi murmushi ta kwashe duk abin da ya faru ta sanar da ita.
“You are in love yarinya, Allah yasa ki fada hannu na gari, kuma wadda zai kaunace ki dagaske”Dagaske soyayya ce?”
Ta dala matá duka a cinyarta, “Ba ni da lokacinki ina da ayyuka da yawa”Zan iya Kara kiransa?”Ta fada ta fanni zolaya. “Na daure yasa mu sake,babu ruwanaki bi dai a hankali da mahaukacin ki.”Ta lumshe ido tabi Khadija dakallo a lokacin da take fita tabbas dole ta boye duk wani dan adam da yake ranta domin kullum abin da Abas ke bin diddigi ke nan ya gane wane ne ya
Hmmmm