MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 5 BY RABI’ATU ADAM SHITU
MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 5 BY RABI’ATU ADAM SHITU
hana shi samun soyayyarta, don ya dauki mummuman mataki akansa ba.
An shirya Birtheday din ta yadda yakamata an yi taro wadda ya hada manyan kawayenta da kuma manyan abokanen makarantar ta. Ya yi bajintar da ya saba yi na danka mata mukkulin mota, sai dai a taro ta furta ba ta so bata kaunar motarsa. Saboda haka kusan kowa da bacin rai ya baro wajen
• saboda Abas, duk wani namiji da ya zo in ba wani na jiki ba ne to sai ya yi masa tambayoyin kwakkwafi don ya gano waye shi a wajen Yasmin, abin da ya ba ta haushi ke nan ya danka mata kyautar mukkulin mota ta dawo masa da kayansa a gaban jama’a.
‘Taro ya ta shi kowa na jin cewar rashin yinsa yafi amfani kawayen da suka zo da samarin su, am batawa samarinsu rai, iyayen da suka zo, an yi abin ‘da bai dace ba a gabansu.
Saboda haka kowa ya ta fi gida cikin bacin rai Hajiya sailuba kan yar ta ta yi tana masifa.
“Wace irin yarinyar ce ke mai taurin kai, wane irin abu ne haka
Alhaji Sunusi ya katse ta da cewa “Zaki fara ko, ni ban taba ganin mace irin ki ba da ba ta da mu da farin ciki yar ta ba sai na wani, a kan me, wai me ki ka rasa ne kike bukatar dole sai kin sa ‘yar auren da ba za ta yi farin ciki ba, saboda abin duniya”Baba Ko gawa ta bana fatan ace Abas ya taba na tsani shi bana kaunarsa.
“Yata a kullum da kodayaushe ina miki alkawari
akan ba zan miki auren dole ba, ba zan taba yadda ki yi tarayya da abin da ba kya so ba
Da kuka ta shiga cikin dakin ta a lokaci da suka isa cikin gidan su. Sannan ta rufe dakinta dan uwanta Zaid ya je domin rarrashinta ta ce ya tafi bata da bukatar kowa.
Karfe biyu na dare bacci ya kauracewa idanuwanta,
Zuciyarta ta kasa yin sanyi, ita da kanta ta gaji da halin da take ciki so take yi ta yi bacci domin ta samu hutun bugun zuciyarta.
Ba ta san lokacin da ta dauki wayar ta ba ta rasa me za ta yi sai kawai ta dauki Lambar Umar ta yi Kokarin dannakiransa sai kuma ta ga yanzu dare ya yi, don haka sai ta zabi ta yi masa message.
Yaje fitsari, ya dawo domin kwanciva adai-dai
lokacin da mahaifinsa yaketambayar waye nan ya ba shi amsa da cewar ni ne. Sai ya ga shigowar sako wayarsa, tunaninsa alert ne na wasu kudi da yake bi, don haka ya yi saurin budewa yana dubawa ya ga kamar idanuwansa ne yakemasa gizo ya ga sunanta
Yasmin da sauri ya duba.
“Na yi birtheday di na yau baka zo ba”
Ya yi murmushi ya gyara kwanciya ya fara rubutawa. Tun da ta tura sakon ta ke tunanin ya amsa mata a wannan lokaci sai da ta sare sannan ta ji wayar ta ta yi kara da sauri ta wawuri wayar Allah ya rayaki, ya kuma yafe miki Kurakuren ki na baya, ya kuma haska miki goben ki, ya yi miki albarka duniya da lahira, kin manta ba ki ba ni katin gayyata ba”,
Ba ta san lokacin da taji wani irin abu ya taba
zuciyarta, ta so ta tura masa katin gayyata Khadija ce ta hanata.
Ta nutsu ta fara rubuta masa saboda gudun kada mahaukacin nan ya yi masa wani abu kamar yadda ya yi wa wasu a wajen taron duk da basu da alaka da ita.
Tun daganin sakon ta a wannan daren ya samu wani kwarin guwiwa akan cewar abin da yake ji dangane da Yasmin shi take ji dangane da shi, tuni bacci ya Kauracewa idanuwansa.
Sako ya sake shigowa wayarsa. “Ka yi hakuri na yi maka laift, ka yafe min, na kuma gode kwarai da addu’ar ka, zan iya cewa babu wadda ya yi min addu’ar da na ji dadin ta kamar kai.
Ya yi murmushi yana jinjina maganarta ta karshe, da zai rabu da ita ka da ta ga ya zake da yawa, sai kuma ya kasa gamsuwa da shirun nasa abin da yafi ya tura mata da ko sai da safe ne ya fara rubutu.
“Ki kwana lafiya, na ji dadi da na fi kowa samun
lambar yabo a wajen ki.
Wayar na hannunta ta dauka ta ga abin da ya rubuta ta yi saurin tura masa “Ka na da kirki a tsawon daren nan baka ki amsa min sako na ba, sannan ka yi min furucin da ya wanke min bacin ran da nake ciki”. ..
Ya Kara gyara, zama lokacin da ya ga sakon ya tura mata.
“Damuwa kuma, me zai hada ki da damuwa ke kuwa, ke da a kayi taro domin ki”.
Ta gama karantawa har ta yi rubutu mai tsawo akan matsalar da ta samu sai kuma ta share saboda kawai bai dace ace har ta fara gaya masa halin da take ciki ba. Ba ta san lokacin da ta rubuta Ko zamu iya haduwa gobe”
Ya jima yana kallon rubutun wani irin farin ciki ya cika shi bai san lokacin da ya rubuta
“In kina bukata me zai hana?”
Adress din wajen wani guri da ta sanar da shi bayan. Washe gari da safe ya nemi kayansa masu kyau, ya sanya ya fito daga cikin dakinsa yana saka takalminsa yana jiyo muryar kanwarsa Yusra daga cikin daki ta cewa da Maman su “Ki yi sauri ki sallameni ga yaya can ya zai fita”.
“Ke wai wacce irin yarinya ce, da bata da
kawaici, ke kullum a baki ba ki da tunanin ki tausaya musu duk irin kokarin da suke yi a kan ki?”Zainab na da matsala yasa ni, to amma ya zasuyi, mace ce dole a biya mata bukatar ta, wata irin yarinya ce mai son yin abin da yafi karfin ta, bata daga wa komai kafa matukar taji tana bukatar sa sai ta saka rigima a yi mata.
Ba ta saurari mahaifiyar ta ta fito da gudu yana
Kokarin kaiwa waje, “Yaya”Ya dakata yana dubanta har ta karaso in da yake
“Yusra ya ya dai ba mun yi sallama ba”
Ta riga shi fita waje “Ka fito raka ka zan yi ya
Kara yiwa mahaifiyarsa sallama sannan ya fice tana masa Allah ya ba da sa’a
“Yaya, na gaya maka tun rannan na ji ka shiru,
ga shi lokaci yana kusantowa saura sati uku”
Ya tsaya yana tunani “Tuna min na manta?” “Yanzu yaya ka fara mantawa da bukata ta?”
Ta yi narai-narai kamar za ta yi kuka “Mene ne na damuwa ki tuna min kawai na ce dake, me kike so?”Yaya batun ankor Jamila da za a yi bikinta kowa ya Ya siya, ba dubu bakwai ki ka ce ba har din ki?”Eh yaya?”Ya zaro kudin yana kirgawa ya mika mata, ta yi tsalle
tana murna. “Yusra ba na son ki da tsallake umarnin Umma ki kula da kan ki abin da duk suke yi miki fada a kai gaskiya ne, ka da ki na biyewa kawaye da sauran bukatun da ba su zama dole ba”Ita dai murnarta kawai take yi bata ma jin abin da yake fada mata da haka suka rabu ta wuce kasuwa. Ya wuce shagonsa ya saka ran Al’amin zai zo ya same shi shiru yana zaune.Bayan ya idar da sallar azahar wayar sa ta yi Kara ya dauka Ita ce kamar yadda yasaka sunan ta Yasmin ya daga yana murmushi Ranki ya dade”
“Tare da naka, dafatan dai ba a manta da haduwar mu ta yau ba?”
Ya yi murmushi “Ba zan manta ba, sai dai ina tunanina ina ne zamu hadu?”
“Eh, to, ban san a inda kake ba ka da na jaka da nisa”Ka da ki damu ko ma ina ne ki gaya min zan zo,’Ba damuwa”.Ina jin ki”.
Ta yi murmushi “Akwai wani Sabon Chicken
Republique dake kan Wuse, kafin ka Karasa junction, in ba damuwa mu hadu a nan misalin karfe hudu da rabi”
“In sha Allahu ba matsala zaki same ni mai cika
alkawari”.
“Nagode da amsar gayyata”
“Nagode da wannan gayyatar” Duka sun biyun sun samu kansu cikin matsuwa a lokaci sannan akwai tari wani irin farin ciki mai dauke da fargaba wadda kowa zuciyarsa bugawa take yi yana tunanin abin da ya dace.
Da wannan zulumi aka samu cikar lokaci Umar bai yi kasa a gwiwa ba ya dauki abin hawa har bakin wajen da suka yi zasu hadu da Yasmin.
Ta na zaune tana wasa da yatsun hannunta ta samu table mai daukar mutum biyu nesa kadan da mütane ta yi shiru ta na wasa da yatsun hannun.Samari da yan matan da suke zirga zirga zuwa wajen
kowa kallon ta yake yi. Wani mutum da ya shigo sanye da farin boyel sai faman kyalkyali yake yi ya nufo wajen yana murmushi.
“Salamu alaiki?”
Ta dago ta dube shi “Wa Alaikumissalam” ta ba shi amsa, ya nemi waje ya zauna.
Daga ido ta yi ta dube shi “Lafiya malam?”
Ya yi murmushi “Lafiya na zo ne…
“Ba wajen zaman ka ba ne, akwai mai wajen”
Ya tsaya yana dube dube, wayar ta da ya gani da kuma mukullin motar da suke yashe akan table da kuma yanayinta yasan cewar lallai ba Karamar yariya bace, don haka bai musa mata ba ya mike.Yana ta shi Umar ya shigo ciki yana dube dube da murmushi ta daga masa hannu shi ma hannu ya daga mata alamar ya gano ta.
Ya samu kujera ya zauna “Haduwa ta biyu”.
Ya fada yana murmushi ta mayar masa da murmushi ta ce
“Haka rayuwa take farawa ga kowa, an hadu kuma za a rabu, barka da zuwa, dafatan ban katse maka ayyukan ka ba?’
Ya yi murmushi “Zan yi wannan furucin saboda ni ne na gayyace ki ba ke ba”.
Ta zuba masa ido “Haka ne, to ta ya ya?”
Ya yi murmushi “Ta haduwar farko, da ban tsayar da mai mota ba da ba a fara ta nan ba?”
Tsarin kalamansa sun burge ta yi shiru ta kuma ji fargaban abin da za ta sanar da shi.
Ya katse ta cewa “Bakin ki na son magana”
Hmmm