MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 8 BY RABI’ATU ADAM SHITU

“Abas Stop bana son ina fada ka na fada kana ganin

na ci amanar kamfanin nan ne ko me Ina Baban ka?”

“Ya yi tafiya zuwa Germany ba ka da masaniya,

kowane lokaci hukumar EFCC NA iya zuwa muddin suka zo kai ne a ciki”

Ya juya da niyar barin office din “Abbas ka zo mu

zauna mu san abin yi mana ka tafi ka bar ni, cikin wannan mummumanan al’amarin wadda mahaifin ka ya umarce na yarje musu”

Abas ya dawo “Mahaifina”Alhaji Sunusi ya mike tsaye a zafafe “Shine mana,na taba yin wani abu a bayan sa in ba shi ya umarce ni ba ka kira shi ku yi magana?”

Abbas ya yi murmushi “Shine kuma babu tambarin

Kamfanin mu, ta ya haka za ta faru

Alhaii Sunusi wannan al’amari ba na haka ba ne, dora wa wani laifi idan abin ya girma kai zai shafa. Ni nan ka san zan iya maganin wannan al’ amarin cikin kankanin lokaci in har a shirye kake da mu zauna akan maganar ni ma a shirye nake”.

Alhaji. Sunisi ya tabbatar da maganar da Abas din yayi haka take domin yaro ne mai hatsarin gaske don haka yasamu nutsuwa*”Ina jin ka Abas ya kake so a yi ta ina za a fara”Abas ya jinjina kai yana murmushi ya ce “Abu daya ne za ka yi zan shiga rigimar nan na yi maganinta cikin kankanin lokaci, ko nawa ne zan kashe domin a kashe ta wannan abu ba wani abu ba ne face zama sirikinka kamar yadda ka sa ni”.

Alhaji Sunusi ya mike cikin zafin rai “Wannan ma

shirme ne”Yana kallonsa cikin bacin rai amma shi Abas

murmushi yake hakan yasa Alhaji Sunusi ya ce “Kai ka hado min wannan tuggun ke nan ko?”

Murmushi Abas ya Kara yi “Ni kuma a ina a wane

lokaci, na san lokacin da ka kulla abin ka, sam ban sani ba, yadda ka tsara ni ne zan warware idan kana da bukata ka ba ni auren Yasmin. In kuwa ba haka ba babu ruwana a ciki sai dai na yi kallo.

Dafa shi da Yasmin ta yi shi ne ya dawo masa da

tunanin da ya tafi ganin yadda ya ganta a rikice ya fara tunanin kwantar da hankalinta “Ki kwantar da hankalin ki ya ta babu wani abu babu abin da,zai faru. Ba ki ji dai-dai ba ne”

“Ni ba zan boye miki ba ‘yata muddin ba ki yadda

kin auri Abas ba to mahaifinki zai rayu a cikin kurkukusai ki yankewa kan ki shawara mahaifin ki ko Umar?”Mahaifiyarta ta fada cikin nuna bacin rai da takaici

Yasmin ta juya ta dubi mahaifin nata da yake ta faman dakawa matarsa Sailuba tsawa akan ka da ta amayar da abin da take fada amma sai da ta fada. Ta kuma fita daga cikin dakin cikin bacin rai.

“Dad dagaske ne?”Ya zauna da ita “Kwantar da hankalin ki ‘ya ta…Dad ka gaya min dagaske ne abin da Mommy ta fada”

Ya yi shiru jikinsa a sanyaye “Dagaske ne ‘ya ta,

amma dukkan abin da ya faru shirya shi a ka yi na sani, an shirya min gadar zare ne na afka cikin rashin sani da yadda da su, amma ka da ki sare da kaunar da kike yiwa Umar na amince Umar ne mai son ki dagaskiya ni rayuwata fansace ga rayuwarki na amince da kaddarar da ta afko min”

Ta girgiza kai “Dad ka da ka ce haka, Farin ciki ba

rasa rayuwa ba ne, amma rayuwar rashin “yanci da tozarta shi ne a waye gari a ciki ka tafi prison akan wani abu cin amana, gwanda ace na rayuwa a gidan Abas ko wane irin rayuwa ce na amince zan yi”

“A’a ‘ya ta. Ba zan yafewa kaina ba idan har ki ka

amince da hakan”

“Daddy ba zan iya bari ka tafi gidan yari ba, na

amince ka sanar da shi na amince zan aure shi”.

“Yasmin”ya fada zuciyarsa na kuna”.

A gogo ta duba Karfe takwas da rabi na dare don haka

ta bar gidan ta bar mahaifinta a tsaye yana kukan zuci,

Babu in da ta nufa sai bayan gidansu wato katafaren gidan Hamishim ta kunna kai ciki cikin tsananin 6acin rai sashin Abas ta nufa. Tun kafin ta isa aka yi masa waya aka sanar da shi cewar ga Yasmin nan ‘zuwa. A lokacin yana tare da Kaninta Zaid yasamar masa ‘yan mata suna badala a dai-dai lokacin. Don haka ya gyara ya fito falonsa ya kuma saka mukulli ya rufe Zaid da yan matan da ya kawo don su debewa yaron kewa.

Ta shigo cikin falon dai-dai lokacin da ya ya fito ke

nan. “Yasmin barka da zuwa”

“Ba wannan ne ya kawo ni ba, na zone domin na

gargade ka, na kuma yi maka mugun albishir Abas bana son ka, Abas bana son ka, Abas bana son ka, kaji da bakina na gaya maka to ka da ka zargi wani ga dukkan kaddararka, domin zan aure ka ne kawai domin daukar fansar abin da ka shirya wa mahaifina, zan zauna a tare da kai saboda kawai ni ‘yar mutumci ce kuma ina son mutumcin gidan mu ya ci gaba da amsa sunansa.

Amma ka da ka taba zaton ka auri macen farin ciki, domin ba za ka taba samun farin ciki daga gare ni ba, wanan shine gargadi na a gare ka.

A lokacin da take maganar murmushi yakeyi kawai

yana kallon ta bai bude baki don magana ba sai lokacin da za ta fita.

“Ko dake ce bala’ in duniya Yasmin na amince da na

rayu dake, zan zauna dake koda wuta ce take fita a jikin ki, sannan zan rayu dake na faranta rayuwarki koda a kullum kina min barazanar toshe numfashina. Abas nine mai son abin da yake so mai tsanar abin da ya tsana, tun daga yarintar ki nake son ki Yasmin soyayyarki gyambo ce a cikin zuciyata ba zan taba barin ki abin gori a rayuwa ta wani ya zo ya raba ni dake wannan abin kunya ne”.

Ba ta tsayasaurarensa ba ta fice daga cikin gidan

domin wadannan kalaman sakarcin ta saba jinsu daga gare shi”.

Ta tafi ta barshi a tsaye maimakon ya ji zafin

maganganunta sai suke Kawata shi wani farin ciki ya shiga cikin ransa har wani dunkule hannu yake yana jinjinawa fasaharsa da hikimarsa, babu mai ja da ni, babu wadda ya isa ya hana ni muradina a duniya, duk abin da nake so sai na same shi.

Ta koma gida dakinta ta shiga ta dinga rusa kukan

takaici da bakin ciki ta ya za ta fahimtar da Umar ya ya zai fahimce ta, ba za ta rasa mahaifinta ba saboda rayuwar jin dadin ta,, gwanda ta rayu da takaicin zuciya da ace mahaifinta ya wulakanta a duniya. Ta amince da dukkan kallon da Umar zai yi mata komai zai ce da ita ta amince ta yadda.

A ranar kwana ta yi bata rintse ido ba ga kiran wayar

Umar nan kusan kashi uku” amma ta kasa dagawa domin ba ta gama shirya abin da za ta sanar da shi ba gwanda su yi ido hudu da juna.

Ta na mikewa ta rubuta masa sakon haduwa a in da

suka saba haduwa misalin karfe goma na safiya.

Umar na zaune da abokinsa Al’ amin a kofar gidan su.

Al’amin ya dubi Umar ya ce “Wai kai ya haka ne

Umar da ya luluka cikin tunani ya dago ya dubi

Al’amin ya dan yi murmushi ya ce, kana yasake hannuwansa da ya rataye a kirjinsa ya dafa kafadar Al’ amin kawai. Al’amin ya gaza gane matsalar ya cce “Baka da lafiya ne?”

Murmushi Umar yasake yi ya dubi Al’ amin “Me ka

ga ni?”

“Mun zauna tun dazu ina ta maka hira ka yi min shiru

wani abu ya shiga tsakanin ku da Yasmin ne?”

Umar_ ya yi ajiyar zuciya gami da jinjina kai

“Al’amarin ya wuce haka abokina, tun jiya ina kiran Yasmin bata ko daga min waya ba, tabbas wani abu ya faru jikina ya gaya min akwai matsala, yanzu haka wallahi wani irin zafi na ke ji a cikin zuciyata Al’amin tun da na tashi nake son na Kara kiranta amma fargaba nake saboda ban san abin da ya nisanta tsakanin mu ni da ita ba

Al’amin ya yi ajiyar zuciya gami da jinjina al’ amari

yasan halin abokinsa yasan irin son da yake yiwa Yasmin tun yana yiwa soyayyarsu kallon ba zai yiwuwa ba yar mai kúdi kamar ta ta aure shi har ya gamsu da kansa sabodaganin irin zazzafan soyayyar da take yiwa abokin nasa don haka Al’ amin ya ce.

“Haba abokina, a da ka san ina daga cikin mutum na

farko da na kasa gasgata soyayyarka da Yasmin, saboda fifikon dake tsakanin ku, amma zuwa yanzu na gama yanke kaunar akan irin soyayyar da kuke yiwa junan ku Yasmin ta na yi maka so ne zalla so mai tsananin kuwa, haka kai ma, don haka ka daina tada hankalinka akan’ ta, babu abin da zai hanata ta aure ka, domin banga abin da za ta yaudara, a wajen ka ba, son ka take yi da cikakkiyar zuciyarta, ko da rabuwa za ku yi da ita sai ta fika shan wahala, saboda ita ya

mace ce, don haka ka da ka saka ranka cewar za ta iya rabuwa da kai.

Dai-dai wannan lokacin sako ya shigo wayar Umar

da sauri ya daga wayar ya ga ita ce, ya karanta sakon, al’ amin ya ce “Ita ce-ko?”

Cikin sanyin jiki Umar ya amsa masa ita ce wai mu

hadu an jima misalin karfe goma, Al’ amin akwai matsala jiya ta sanar da ni zamu gana da mahaifinta yau, ina kyautata zaton akwai matsala”

Al amin ya girgiza kai yana murmushi “Babu komai

abokina ka je ka shirya yanzu tara da kusan kivata”

Ya dubi wayar “Yanzu Al’amin idan ace Yasmin

cewa za ta yi aurena da ita ba zai yiwu ba, yakenan, kana ganin zan yi wata rayuwar farin ciki a gaba?”

“Babu abin da zai raba ka da masoyiyarka abokina ka

ta shi ka je”.

Ya dubi Al’amin ya yi murmushi

“Nagode bisa

karfafamin gwiwa abokina”

Suka yi sallama ya bar wajen domin zuwa ya shirya

ya tafi in da zasu hadu da Yasmin.

Karfe goma ta gota a lokacin da ya iso wajen babu

kowa sai kadawa ganyayyakin bishiya motar ta ya hango a wajen ya gangaro wajen motar bai ga kowa ba, ya Kara sa ciki yana dube dube nan ba bai ganta ba. Can ya hangota tsaye a jingine da bishiya tana kallon can jakarta rataye a kafadarta yanayin da ya ganta a ciki ya fádar mata dagaba, don haka cikin sanyin jiki da faduwar gaba ya karasa in da take tsaye. Kafin ya iso ta share kwallar da take zuba a cikin idanuwanta. Ta jure ta juyo tana masa murmushi.

Hannuwanta a harde da na juna kallo daya ya yi mata

ya ji wata mummunar faduwar gaba domin ya gano tsantsan

tashin hankali a cikin kwayar idanuwanta.

“Yasmin lafiyar ki kuwa, me yake faruwa ba ki da

lafiya ne?”

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE