MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 9 BY RABI’ATU ADAM SHITU
Ta Kara yi masa murmushi “Me ka ga ni Umar?”
“Ta ya za a yi na gaza gane halin farin ciki ko na
bakin ciki a tare dake, in har zan gaza gane damuwa a kan wannan kyakkyawar fuskar ta ki, to ban cancanci zama masoyi a gare ki ba, ki gaya min damuwar”.
Ta jinjina kai ta Kara jin wata karaya ta shake mata
numfashi da kyar ta iya dabarar nuna masa wajen zama ta ce “Mu zauna?”
Yana juya in da ta nuna masa ta yi sauri share
hawayen da ya gangaro a fuskarta kafin ya Kara dubanta ta share.
Ya girgiza kai “A halin da nake ciki ba zan iya zama
ba, ki dai-daita min numfashina da sanar da ni damuwar ki Yasmin”.
Ta kura masa idanuwa wata irin tausayi da tsantsan
kaunarsa tana sukar ranta. Ta tafi a hankali ta zauna akan dadduma sannan ta ce “Ka zauna”.
Ba yadda ya iya yasamu guri ya zauna kana ya dube
ta “Ina sauraren ki Yasmin, ban taba ganin ki cikin wannan hali ba ki sanar da ni me yake faruwa”.
-Ta yi shiru ganin ya tsura. ta da idanu yasa ta ce “Na
yi kuskure Umar, na boye maka wani abu wadda ban yi dana sanin boye maka shi ba sai yau din nan. Ba komai yasa na boye maka ba sai don saboda rashin muhimmancinsa ba, Umar ka taba tambayata waye yake yawan kirana ba na dauka in muna tare. Ka na dagaskiya bana dauka amma ba dan muna tare ba ne ko ni kadai ce a daki bana dauka Umar”.
ya kasa cewar komai saboda wani suka da zuciyarsa
ke masa gabansa yana faduwa ita kawai yake kallo yadda hawaye suke sakkowa daga cikin idanuwanta.
“Wani ne dan mai gidan mahaifina, yake so na.. tun
ina Karama.. bana son shi bana kaunarsa.. ban taba tunanin akwai lokacin da za a 6ata a kansa ba, tun da na yadda da mahaifina akan akidarsa. Umar ka tuna wata hira da mu kayi da kai a wasu watanni da suka shude farkon fara gabatarwa da junanmu halin da
Zuciyoyinmu ke ciki.
Babu wani dalili da zai sa shi ya yi wata magana
hankalinsa na kanta jira yake yi ya ji karshen abin da za ta furta. “Mun yi magana akan shakuwa da ciwon da yake tare da rabuwa da juna….
Ya katse ta “Shshh Yasmin Kalma daya ta ishe ni, ka da ki dauki tsawon lokaci wajen azabtar da zuciya ta. Dama kin fada bayan an hadu kuma za a rabu. Yau shi ne ranar rabuwar”
“A’a Umar ka fahimce ni”.
“Innalillahi wa Inna ilahir raj’un innalillahi wa inna
ilahir raj’un Allahuma ajirni ya fada yana nanatawa. “Me yasa na yadda dake, me yasa na yadda dake?’
Babu abin da ta iyasai kuka, kuka ta ke yi tamkar zuciyarta za ta fito shi kuwa mikewa ya yi tsaye yana ta nanata
“Me yasa na yadda dake me yasa bata lura da hakan ba sai da ta daina jiyo amon muryarsa ta mike da sauri ta bi bayansa. Babu shi babu dalilinsa ta dauki waya ta kira wayansa ya katse da ta Kara kira na biyu ta ji wayan a kashe.
Ta rike ce ta rasa abin dake mata dadi tafi kusan awa
biyu a wajen kafin ta dauki motar ta ta nufi gida.
Babu abin da ya tsaya masa a rai ko da ya bar wajen
face tunanin abin da zai raba shi dagarin Abuja, wayarsa ya dauka. domin tuntubar wani aiki da wani kamfani ya bukace shi, wanda a kalla a kullum a duk wata zai amshi naira dubu dari biyu da hamsin a matsayin albashinsa ya ki amincewa ne kawai saboda yasan zai samu fiye da haka a nan. Yanzu da rabuwa da Yasmin ya zo masa sai yakeji zai tafi Kano ko da babu kosisin kwabo.
Abokin mahaifinsa ya kira wadda shi ne ya zo masa
da batun kusan wata guda da wucewarsa.
“Kawu ina wuni”
“Lafiya Kalau Umar ya mahaifin naka?”
“Yana nan Kalau, Kawo na kira ka ne dangane da
aikin da ka samar min in har ban makaraba ina da bukatarsa, in ma babu ina da bukatar zuwa nan garin a yau ka sanar da Baba kai ne ka bukaci na zo”
“Umar lafiyarka wani abu ne ya faru” =
Ya tambaye shi dalilin jin alamar kuka yake yi. “Ka taimakamin Kawu bana son Kara koda awa guda
a garin nan ka sanarwa da Baba cewar kai ka bukace ni kuma a , yau ake da son zuwa”
“To ka kwantar da hankalinka Umar ka bi komai a
nutse na ga alamar kamar kana cikin damuwa, dama ban sanar da Kamfanin cewar ba za ka yi aiki da su ba, saboda haka yanzu zan Kara tuntubar su, bana shakkar akan ka domin aikin ku aiki ne mai wahalarsa mukabi komai a sannu, sannan zan yi magana da mahaifinka yanzu”.
Tun daga wannan lokacin Umar ya yi bankwana da
birnin Tarayya Abuja ya zo cikin garin kano domin samun hucewar zuciyarsa.
Ya kashe wayarsa, duk wata hanya da Yasmin za ta
same shi ta gagara karshe bayan kwana biyu ta je gidansu, a lokacin Baba shi na goge gogen a tsakar gidan, ta yi sallama ta shigo duk ta rame ta shiga cikin wani hali. Bayan sun gaisa ta ce
“Mama Ina Umar kwana biyu in na kira shi wayansa
a kashe”.
Mama ta yi shiru gami da tsura mata idanu “Ki gaya
min gaskiya Yasmin mai ya hada ku da Umar?”
Yasmin ta dan yi shiru tana tunani bai gayawa iyayensa ba ke nan. “Yasmin ki gaya min me ya faru a tsakanin
“Mama ya ce da ku wani abu ya faru ne”.
Mama ta yi sak domin dama tuntuni neman dalilin
yanke soyayyar su Umar suke yi da ya yi a lokaci guda “Abin ne abin mamaki, lokaci guda ya zo ya tattara kayansa bai ce ga dalilin komai ba ya tafi, kuma tun da ya tafi in mun kira shi ba ma samunsa sai dai duk lokacin da ya ga dama ya kira mu”
Hankalinta ya yi matukar ta shi “Mama ku yafe ni,
ban san a wane matsayi zan dau kaina ba nice na raba ku da dan ku, na gaza cikawa Umar burinsa, Mama ban san ya zanyi ba dan Allah mama ku yi hakuri”.Ban fahimce ki ba Yasmin wani abu ya faru a
tsakanin ku?” “Mama” ta fada tana kuka. “Kin ji ‘yata kina kara tada min da hankali mene ne ya shiga tsakanin ku da Umar din ki gaya min Yasmin”
“Na gaya masa ba zamu samu ikon yin aure ba, shi ne ya fusata yaqi yasaurare ni ya ta shi ya bar ni, ya kashè wayarsa, don Allah Mama in kin san in da Umar yake ki gaya min ina son na fahimtar da shi komai”
Mama ta yi shiru gami da jinjina al’ amari “Yasmin
dama abin da ya faru ke nan, ya zo ya bar gida acewarsa wai yasauya shawarar zai koma kano da aiki, a she dalilili rashin jituwar ku ne”
“A kano a ina zan same shi ki ban adress Mama ina
bukatar ganin Umar”
“A’a Yasmin in har kin san ba zaki dawowa da Umar
farin cikinsa na cewar za ku yi aure ba, babu dalilin da zai sa ki je in da yake, ki yi hakuri tun da kaddara ta raba ku ki je a hakan ka da ki sake ki kara neman Umar, ya zabi haka ne domin hakan shi ne abin da zai warware masa fushin zuciyarsa, ba na son ki je ku Kara harzuka zuciyoyin juna, amma garin yaya me yasa ki kai .masa haka alhalin na san kuna son junan ku?”Hawaye ya ci gaba da fita daga idanuwan Yasmin
– Mama kaddara a duk in da nake ba zan taba kasancewa cikin farin ciki ba, na roke ki da ki yi min addu’a ina cikin tashin hankali mama wannan zuciyar ta wa jin ta nake kamar tana ci da wuta.
“Ki yi hakuri na fuskance ki Yasmin na yaba da
‘ halayenki na kirki ba Umar ba, mu kan mu mun san cewar mun rabu da sirikar arziki addu’a ta a gare ki ba za ta tada yankewa ba, ki je Allah ya yi miki albarka, sannan iná gargadin ki ko da wasa ka da ki sake neman Umar kin ji
Yasmin ta jinjina kai ta mike ta fita daga cikin gidan
jikinta a sanyaye yanzu shi ke nan ta rabu da Umar. Wani waje ta kalla a harabar gidansu ta tuna wani lokaci da ta zo suka zauna da
“shi a wajen, ta ke sanar da shi ceawr ita fa tana so ko zasu yi aure a gidan ta ke son ta zauna saboda tana kaunar mama. tsarin
.
gidansuna birgeta. Duk lokacin da ta tuna da maganar mahaifiyarsa ta
karshe sai ta ji gabanta ya fadi wato ka da ta sake ta nemi Umar ta
. rasa ta ya ya za ta iya jure rashinsa
Bayan shekaru uku
Ita duniya ba kai ne kake juyata ba, duniya tana
hannun ubangijinka, duk kuma da yadda ya tsara haka ce zata
– tabbata, ko da kana jin radadi idan ya nufe ka da arziki to ta cikin wannan radadin za ka ratsa sannan ka cimma gaci.
Umar ya taho kano cikin tsananin takaici wadda a
lissafinsa ya zo kano ne ba tare da ya lura da hanyar da aka biyo da shi ba, in da zai kure tunaninsa ba zai iya tuna irin motar da ya shigo ya zo kano ba, ba kuma zai iya tantance mace ce ko namiji a kusa da shi ba.
Cikin kankanin lokaci a shekaru uku ya zama
hamshakin sananne kuma jajurtaccen ma’aikacin da ko ina ana damawa da shi a cikin arewacin Nigeria, samun bunkasar kamfanin NLD wato na Nasir Lamiz Darazo. Yasa suka dauke shi a matsayin Daraknta na kamfaninsuna gine gine. A dukkan watan duniya Umar yana samun naira milyan daya albashinsa, alawus kuwa babu tantancewa domin ya danganta da yadda suka gudanar da ayyukansu.
Ya yaye yara kwararru masu sanin makamar aiki
wajen sarrafa na’ura, Gangaren saita camera a wurare daban daban gwabnati ita kanta a duk lokacin da za ta yi aiki ko sabon waje ko gyaran waje a zamanantar da shi to duk dan kwangilar da ya amshi aikin yana daukar Umar domin tsara masa na’ urori,
Alhaii Nasir Lamiz Darazo bai dauki Umar a
matsayin mai taimaka masa kawai ba, ya dauke shi a matsayin da, domin nasarori da suka samu da yaron a kodayaushe yana fadin cewar nasarorinsa na tafe da karfin nasarar Umar ne domin tsare tsaren Umar da fasaharsa kadai yake sawa mutane da dama suke kulla yarjejeniyar aiki da su.
Ta bangaren Umar shi ma ya dauki soyayyar duniya
ya dora wa Alhaji Nasir yana kallonsa tamkar mahaifi. Babban abin dake damun Alhaji Nasir shi ne ya tabbatar akwai wani abu dake damun zuciyar Umar amma shekaru uku da suka wuce ya gagara ya fahimce shi domin bai taba ganin Umar yana zaune da
Hmmm