MAI TAFIYA CHAPTER 3

MAI TAFIYA CHAPTER 3

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Burirrika kamar mayaka su ke a fagen daga wasu sukan kai labari, wasu duk yanda aka so ba za su taba kai labari ba.+

Kano, Nigeria

Ranar Asabar aka kaddamar da sababbin ‘yan kungiya. Hindatu, Lubabatu da Rokaiyatou. Aka kafa musu dokokin kungiya kuma duk suka yi mubaya’a.8

Shugaba Hajiya Kububuwa wace irin ingarmar mace ce mai jarabar tsawo kamar daren wahala. Fuskarta baka ce kirin mai dauke da kalangu a kuncinta. Yanayin girman jikinta kadai ya isa ya yiwa dan adam kwarjini ya sa ma sa tsoro, ga ta da zafi kamar barkono. Sai dai mace ce mai haba haba a inda ta san za ta samu Naira.18

Hajiya na da wasu irin “connections” a kasar Najeriya da ketare wanda idan ka ji sai ka sha mamaki. Mace mai tarin jama’a da dukiya. Duk wani wanda ya ci ya tada kai da Nera kuma shedan ya ma sa fitsari a ka ya san da Hajiya kububuwa kuma ta san da zamansa. Babu irin deal din da bata yi, ita ce safaran mata kano to jiddah, ita ce safarar mata da maza kasar italy su je su yo karuwanci su dawo ma ta da kudi tsababa. Ita ce safarar miyagun kwayoyi daga kasashen Afrika zuwa na ketare, habbaka madigo, luwadi. A halin da ake ciki ta kafa wata kungiya ta jajircewa da yakar gwamnati akan auren jinsi daya.13
Babu wani hali na Allah ya tsine da Hajiya ba ta da hannu dumu dumu a ciki amma da yake su ke da kasar kuma tana da daurin gindi daga sama ko yatsa ba ka isa ka nuna ma ta ba. Sai ma al’amarin na ta ya ke dada bunkasa domin wadanda ya kamata su hana su ne maneman ta ko maneman yaranta.

Hajiya kubuwa ta cigaba da kallon sababbin ‘yan kungiyarta ta ce

” Ban tambaye ku labaran ku ba labaranku ba abun saurare ba ne don na san ba zai wuce na bakin ciki da takaicin duniya ba. Sanin labarin mutum ba shi da wani tasiri a rayuwar da zai yi gaba, ku dauka yau kawai aka haife ku, aka yaye ku , ku ka girma ku kayi hankali a ranar ku ka kuma zabi rayuwar da ta dace da ku. Rayuwar duniya zabi ce, sai ka so za ka sha wahala sai ka so zaka sha wuya. Da a ce na san dabarun duniya tun daga haihuwa to da tun farko na zana kaddarata da hannuna (astagfirulla) na tsallake wahalhalun banza a hannun wadanda ba su isa ba!2

Ban taba ba wa kowa labarina ba, Da me za a anfanu da labarina, ba ni da sha’awar asan ko ni wacece. Ni kungiyata ba ta da takura bani kuma da katanga a aikata son rai. Wacce ta ga zata nemi maza ta nema, mai neman mace ‘yaruwarta ta nema. Kowa ku ka gani a nan da bazata yake rawa.1

Kowa ya iya takunsa ni kuma zan rike ma sa ka maciji yayi wasa da jelar. Ban kuma ce ku ragawa da namiji ba, bariki sa kai ce duk inda ku ka samu faraga ku wawusa. Wanda aka ba ku da wanda ba a ba ku ba duk naku ne!Ni Kububuwa dan kungiyata ba shi da haramiya!1

Wannan tafiya ce mai tsawo, mai cike da tarin nasarori da idan ku ka bi a hankali za ku ci moriya. Mu gagara gasa ne muna da hanyoyi dubu da daya na sarkafe da namiji. Muna yin kowani taro asabar din karshen wata. Haka kowani ciniki mace tayi muna da kamasho a ciki”1

Da haka taro ya tashi , aka dauki sababbin ‘yan kungiya aka kai su gidan shugabar kungiya zuwa wani bangare da ta ware wa ire irinsu. Gidan Hajiya duniya ne fadar girma da fadinsa da kayan alatun da ke cikinsa ma bata baki ne. Hajiya tana da bangaren sabbin ‘yan kungiya da zasu iya zama kafin su ci gashin kan su, duk wacce ta girmama za ta iya barin gidan ta kama na ta. Aka zaunar da su a falo Hajiya ta ce zata turo ‘yar Modu ta karasa musu sauran bayani.

Da suka shiga falon mata uku ne a zaune jummai, Sima da Naima kowacce tana harkar gabanta. Hindatu , Lubabatu da Rokaiyatou suna daga zaune aka kawo musu abinci na alfarma suka ci suka yi kat! Ac na buso su. Wani irin farinciki ya ratsa zuciyar Luba ta ayyana dama tun dawowarta da ga Saudiyya ta hadu da Sadiya Indiyar Daji, ai da bata wahala ba! Dama akwai irin wannan rayuwar bata sani ba? Hajiya Kubuwa ta gama birgeta dama ita ce ta samu daula irin haka, ai da abun ba magana.23

STORY CONTINUES BELOW
Kamar daga sama suka ji wata murya ita ba ta mace ba ba ta namiji ba an ce

” Yauwa ina bakin suke? Sako makoko daga Hajiya Kububuwa ta ce a shiga ayi wanka wacce ba zata iya ba in taimaka in cuccude ta a fidda dattin annakiya. Dattin talauci ai ba karamar dauda ba ce, shi ya baro mu daga kauyikan mu ya kawo birni domin mu ci miya da wasali”15

Baki ne daga can sama suka zo zasu zaba su darje..ehe ..ba a bori da sanyin jiki” kawai ya kama hannun Luba zai tayar da ita daga zaune tayi sauri ta fizge hannunta tana yiwa wanda aka kira da ‘yar Modu kallon mamaki.

Ta ga namiji dan siriri fuskar nan ta sha bilicin yana da tsayi daidai misali. Ya sha kaftani amma sai ya dauki wani zani ya yafila da kallabi. Ta gama ganowa dai dan daudu ne. Yadda ta masa ya bashi haushi ya rike haba ya ce

” Haba ‘yanmata ‘yar Moduwaye ce fa mace yaruwarki, daga tabi? Ai a sa a baka ba tauna ba ce kuma tauna ba za ta taba zamo hadiya ba. Kin ji ko?…ehe!” Ya gatsina baki ya karya kugu.2
Yanayin kwarkwasar sa da maganarsa ya bawa Rokaiyatou dariya ta kuwa dunga kyalkyatawa ya juyo gareta har da kashe ma ta ido ya ce

” Sukari..lallai yanmata ba ki yi farin banza ba, dalli kamar an haska tocila. Wannan irin murmushi haka haskensa kamar wata dan daren goma sha hudu. Ita waccan kawar ta ki ta zata na taba ta ne da wani dalili to ki gaya ma ta ni a wajena yadda ta san naman alade a wajen dan musulmi haka na dauketa. Billahillazi haramiya ta ce, to kin ji yadda aka yi. Ahayyeee!”22

Luba ta daga kai ta galla ma sa harara da alama ba za suyi shiri ba shi kuwa ya ce

” Aa dakata ‘yanmata ai ban san kuna yi ba sai na ga idonki ya fado kasa yana birgima. Kar ki bari dai kwabarki tayi ruwa don duk hangenki da sama ba za ki yi tsallen alkafira ki hau ba, ni ce dai tsanin..kar ma ki ji da wai, na bar ki da wannan”1

Jummai ita ce mai waya da wani maneminta a waya, Sima tana yiwa Naima kitso na karin gashin doki ta ce

” Kai haba ‘yar Modu wai kai ba za ka iya musu ko dan introduction ba ne a matsayinsu na sababbin zuwa”

“Ke Naima mai dattin hula da kika bari a gida kika fito yawan ta zubar shi ne kai ba ni ba, ka da ki sake ki kara sani a jinsin da ba nawa ba” cewarsa6

Ta ce tana kama haba

” Ahh..daga shawara ‘yar Modu…wulakanci”2

Ya ce

” Ba ki ga komai ba Alhaji Nafsin kira goma ya min duk don in nemo masa ke din in miki kafar baya na hada shi da wata sabuwar yankan raken ba wani sabon abu ba ne a gurina” Ta mika ma sa hannu suka tafa.

Ya juyo ga su Hindatu wacce tunda aka fara abun ta ke binsa da ido ya ce su biyo shi dakin suka bi shi a baya. Ya shiga bude wajen aje kayan sawa yana zaro su yana cewa

” To a tuttube a tuttube”29

Ya juyo ya gan su kowacce a tsaye bata tube ba ya ce2

“Yau ni ‘yar Modu na ga abinda ya isheni. Yo ina ruwana da tsarin halittar jikinku tunda duk abunda kuka mallaka ba bako na ba ne? Ni a duniya ba ni da abun kunya dayarku ta gwada shiga bayi yanzu na bi ta da soso da sabulu na cuccudeta kamar sabuwar jinjira wai menene a ido idan ban da ruwa?”9

Haka dai suka yi wanka suka canja da kaya na alfarma. Duk cikinsu ba wacce ta taba saka irin kayan ko makamancinsa. Kowacce da kalar irin tata kwalliyar kayan ma mabanbanta kaloli ne. Shi da kan sa ya musu kwalliyar fuska ya kashe musu dauri. Ya gyaro gashin Rokaiyatou ya tazo shi har gadan bayanta. Sai ta ji ta kamar wata zinariya. Suka ji kan su yayi gingirin zukatansu sun yi fes. Kowacce tana ji kanta ita wata ce.

Yar Modu ya karewa halittar jikin Hindatu kallo ya ce

” Dankari! Wani kaya sai amale, wata babbar motar ai dole sai da babban direba. Wanda ya bar ki kika fito bariki ba karamin asara ya tapka ba. Mijin na ki barzahu ya sheka ko kuwa ma sauta ga wawa ce? Kai..Alqur’an daga gani ma sauta ga sakaran ce”6

STORY CONTINUES BELOW
Sai suka yi dariya gabadaya. Daga gani sun soma sabawa da harkar kawali ‘yar Modu. Ya musu jagora zuwa babban falin Hajiya na kasa in da take mitin da wasu ciyamomi. Kafin su shiga ya ce

” wai me ma sunayenku ne? Suka fado ma sa ya kama baki ya ce

” Ya na ji kuna jero min su kamar sharuddan tuba? To daga yau kun koma Hindu, Luba da Rukky.14
Daga ranar suka kulla wani kawance kawancen da sukai amanna ba zai taba tarwatsewa ba, wata amintaka ta ban mamaki! To sai dai me? Su ba masanan gaibu ba ne don da su masanan gaibu ne da sun roki Allah kar ya halicci wannan rana da ta za ta zame mu su mafari..mafarin gafalalliyar rayuwa mai cike da da na sani!3

*****************************

“Shekarata hudu cur ina dadiro da Isyaku direban babbar mota a tapa, wani gari ne nan kusa da Habuja” cewar Ziza ” kwarankwatsa dubu ina ganin maza masu kishi ban taba ganin ya Isyaku ba. Zalamamme, mahandami ban isa ya ganni da manemi ba sai a nemi a bawa hanmata iska.2

Fitowa ta yawon duniya kenen na hadu da shi ban waye ba ina farkon shigowata bariki tsumma gaba tsumma baya. Kar ki ce wani abu ne ya fito da ni da ya wuce auren dole.1

Saurayina Audullahi tun na kuruciya muka yi alkawarin aure, toshi toshi kuwa na sa a karkashin gadon innata ba kya iya kirgawa ba. Ya kawo kudin na gani ina so, kudin gaisuwar uwa da uba da kayan sa rana har yake saura wata daya kacal aurenmu! Kwatsam ba sai ga wani Alhajin birni ba ya fito wai aure na yake so. Su Innata ba su duba tsawon shekaru da shakuwar da muka yi da Audullahi ba suka mayar da auren na wa kan Alhaji Akilu.1

Irin halin da muka shiga ni da masoyina ba zai kwatantu ba. Abu ya ki ci ya ki cinyewa na gane idan na sake na zauna abunda zai hana a aura min Alhaji Akilu mutuwa. Daga ranar na tattara nawa ya nawa ban kare a ko’ina ba sai a garin Tapa. Dirata kenen Isyaku ya sauke lodi ya ce da wa Allah ya gama shi ba da ni ba.2

Ban san kan dawar garin ba ni dai fatana na yi nesa da gida nayi nesa da auren dole sai ga shi na fado bariki tsundum! Isyaku ya zame min karfen kafa, qarma qarma.

Kar ki ce wata tsiyar yake tsinanamin, o’o o’o kudin hayar dakin da nake ne fa yake biya sai abinci da yake siyo min a wajen Tina, sai ‘yan sitturu da yake min idan an tashi ajo ajo, ko biki ko suna sai kuma kudin gudummuwa. Daga nan kar ki rage kar ki dada amma yadda kika san shi ya sai wa ubana ragon suna ya biya ‘yan fida idan gorinsa ya motsa.4

Ta numfasa su kuma suka cigaba da zuba ma ta ido suna mata kallon talabijin

” Me akai akai dadiro? Dadiro ma da irinsu isyaku hoti ho. Sai ya zuba wata 6 cas! Bai ziyarci mai dakinsa ba, kwatsam rannan sai ba gata ba ta dira a dakinmu irin dirar nan ta mayaka.5

Ashe duk kurin da isyaku ya kan yi duk ashe hotiho ne? Ashe hular ce kawai, a gida shi ke rike da muciyar. Ta tasa keyar shi ta tafi da shi ashe ashe ko kwayar shinkafa bai bar ma ta ba mu kuwa anan ba ma karin safe sai da ti da bredi har a soyo mana kwai a wajen Ilu mai shayi. Ai kuwa dana samu ya dawo sai da na rike shi wata takwas cas! Bai leka ko soron gidansa ba, anan na gwada ma ta sharrin tsohuwar karuwa”3

Suka kwashe da dariya. Su hindu suka kura ma ta ido suna saurare kamar labaran karfe tara. Ziza ta ce2

” Yanzun kuwa na daina wannan wahalar. Ai bari na gaya muku yanzu zamani ya canja ba a wani yayin ki kama gida a mararrraba, ko a gadar tamburawa ko a ibedi. Wannan na karamar karuwa ne me neman cikon canjin da za ta sa nama a miya ko ta dinke farfakken zani. Lo kilas karuwa kenen. Ke kuwa hai kilas abun yanzu duk ai gyara ne . Ya za a yi manemi ya zo wurinki ya gan ki a dan tsukakken dakin da bai ci albarkacin zanin gado ba ki ce zai biya ki da kyau.1

Ai Yanzu matan da suka isa gidaje suke kamawa a manyan birane irinsu kano, kaduna , Abuja da legas. Gida na alfarma ga kayan alatu , ga situru na nunawa sa’a kin ga tun daga nan kin san meneminki ba zai wuce wani babban dan siyasa ba, ko gwamna ko dan majalisa ko babban manajan banki ko wani kasurgumin attajiri! Iya kalarki iya kalar sallamarki ‘yanmata.

STORY CONTINUES BELOW
Ni yanzu da kudi billahillazi bazan yi dadiro ba. Ka kankameni ka takureni akan ‘yan aninan da basu wuce na sha karan sigari ba. Yanzu ne zan yi waje rot da kai. Bazan dorawa kaina kwamfiyushan ba.Ai yanda kawai za ki fi gane lissafinki shi ne yau customer ya zo ya cake kudinsa gobe wani ya zo.17

Luba ce ta ce to yanzu yaya za muyi mu fara fasowa gari? Kin ga dai daga zuwan mu wannan satin Hajiya ce ta hada mu da mutanenta ba ma mu fara fita yawo ba balle mu fara samo namu samarin.

Ziza ta murmusa ta ce

“Waye ya gaya miki ana zama haka sakaka? Duk karuwar da ta zauna ai sai dai ta zaunau. Ai idan kina da kyau kina karawa ne da wanka. Ku tashi mu tafi gidan malami na shi fa oya oya ne aikinsa kamar yankan wuka. Ai inda muka fi matansu na gida kenen , idan a tafe suke mu acan muka kwana!6

Haka suka rankaya su ka shiga motar ziza, wata camry ce golden sai daukan ido take. Ziza farar mace ce ‘yar mitsil kamar kashin tsoro dauke da tsugunna- ka- ci doya daidai a fuskarta. Babu wanda ya san asalin sunanta ballantana daga inda ta fito. Ta fi shekara goma tana yawon duniya tana watangaririya har ta samu ta fado kungiyar Hajiya Kububuwa. Daga nan likkafar ta ta mike Ziza ba ta da tsoro ko na miskala zarratin. Wasu sukan yi gulmar wai ziza na bin kowane jinsi a neme nemanta amma har yanzu babu wanda ya adar da hakan.2

Tana da wani tamfatsetsen gida a unguwar Garki da ke Abuja da wani tsohon maneminta ya mallaka ma ta, ya kuma dandasheta da sabuwar camry din da take hawa yanzu, duk da wannan bai hana an rabu baram baram ba. Haka suka rabu bai iya kwace ko asi ba , ‘yan shaida suka ce wai ziza ta shigar da sunayensa wajen ‘yan tsubbu sun rufe bakinsa ruf!1
Ko ma dai ya batun yake ziza ba ta fasa harkokinta ba da wadakarta da naira. Yanzu ma taron Hajiya Kububuwa ne ya shigo da ita garin kano ta hadu da sababbin zuwa take karanto musu karatun karuwanci.2

” Ban da so don Allah” cewar ziza a daidai lokacin da ta fara murza motarta akan titi ” babu wanda ya aike ki domin ko kin yi babu lada. Son karuwa ba ya wuce ta so abun hannun mutum ranar da ta raba shi da su sai kowa ya raba hanya. Abun duniya shi ake yi wa ranar kuwa da ya kare ai kowa watsewa zai yi. Kar ki sake ki ji tausayin namiji dan bariki shi ma ran da kika ci leda ( aids) tsakaninsa da ke kilometer dubu ce! Ba yace lalacewa yake so ayi ba? ai ke kina da gangar da za ki bugawa shedan kan sa kida kin ga kuwa idan kika bugawa mutum dole sai ya taka!1

Daga nan suka iso gidan malamin. Ba wani boyayyen gida ba ne mai surkuki kamar yadda suka zata , gida ne na ginin zamani bulo da bulo. Suka shiga suka tarar da layi wajen mutum 7 suka zauna har aka zo kan su. Suka shiga sai su Hindatu suka yi mamakin ganin shi.

A tsammaninsu tsoho zasu gani tukuf zaune da kasa a gabansa amma sai suka sha mamaki. Saurayi ne mai jini a jika zaune a wani wadataccen falo. Ya sha farar shadda har da hula zanna bukar zaune a kan kujera mai cin mutum uku. Kafarsa a harde take ya rike wani dan littafi a hannunsa, fuskarsa kadaran kadahan. Suka gaishe shi a al’adance ya amsa ba yabo ba fallasa. Ziza ta ce

” Allah gafarta malam ga ni fa yau na dawo da wasu sabbin ‘yan kungiya. So nake a duba musu a ga ya tafiyar take? Ya za ta kaya (auzubillah) kamar dai yanda aka saba Allah gafarta malam. Sai kuma a yi musu shiri na makaman yaki”

Malam ya ce babu damuwa, ya tambayi sunayensu suka fada ma sa. Ya cewa kowaccensu ta zabi namba daga 1-20. Kowacce ta zaba. Sai Malam ya fara bude littafi.

Suka zuba ma sa ido kowacce da na ta tunanin har malam ya gama. Ya dago ya kalle su kamar koyaushe fuskarsa ba ta nuna alamun farin ciki ko bakin ciki ya ce

” Tafiyar guda daya ce, duk ta inda ku ka bi, ko ta yaya ku ka bi waje daya za ku isa, waje daya zaku kare. Akwai haske, akwai duhu akwai rasa rai!”5

Daga nan bai kara cewa komai ba, sai kowa yake kallon kowa. Luba tayi caraf ta ce4
” Allah gafarta Malam wanne ne farko?”

Ya ce
” Haske”

Sai tayi murmushi ta ce, komai yayi daidai.1

Ziza ce ta karbi zancen da cewa
” To Allah gafarta malam sai kuma makaman yaki”

Ya dauko wani kwalli guda uku ya mika musu ya ce

” Wannan shi ne ” idonka idona”

Daga nan bai kara cewa komai ba. Ziza ta yi musu alamar su tashi, suka tashi bayan ta ajiye masa wani kulli. Suka tafi ba tare da kowa ya cewa danuwansa kanzil ba.

Har suka zo kwanciya ranar Rukky ta kasa cire maganar malamin nan a ranta3

” Akwai haske, akwai duhu, akwai rasa rai!”4

To wani ran za a rasa?????????

Sabo da maza jari ne!5

Kaduna, Nigeria

Bayan shekara biyar

Alhaji Balala-Cinye-du ya duba tsadadden agogonsa na hannu ya ga karfe 10 cif cif na safe, ya ja dan karamin tsaki ganin cewar ya makara. “Bidding” garesu na motoci kuma karfe goma ne daidai ga shi har goman ta masa a daki. Ya dauki hularsa mai taken minista baka ya dora akan Farar shaddarsa mai babbar riga. kallo daya za ka yi wa shaddar kyaunta ya fallasa tsadarta. Sai ya saka takalma rufaffu sau ciki.8

Ya tsaya yana kallon kan sa a gaban mudubin dogon yaro kamar wata ‘yar budurwa mai tashen budurci. Baki ne mai matsakaicin tsawo gwani na saka fiskar gizago musamman idan mutum ba dankwali ya daura akansa ba.4

Dan kasuwa mai samu fiye da daidai misali amma iyalansa ba su wadatu daga hakan ba. Ya gama shirinsa tsaf ya rufa da fesa turare da yake mutum ne mai son gayu na birgewa. Shekarunsa ba zasu wuce 45 ba amma idan ka gan shi ba za ka ce ya kai 40 ba.

Ya dauki “brief case” da ke dauke da farare bugun Abuja ya rike ta kyam sannan ya kulle kofar sashinsa ya jefa mukulli a aljihu. Ya tako taf taf kamar wani ingarman doki ya shigo sashen iyalinsa cikin takama da izza.

Kallo daya zaka yiwa matar ka zata ‘yar aikin gidan ce idan ka karewa yanayinta kallo. Wata kodaddiyar cheras ne a jikinta da ta sha wanki da takalmanta silifas dan madina tana aikace aikace a tsakar gidan. Gida ne yalwatacce ginin zamani sai dai kana zuwa za ka gane babu kulawa.1

Duk irin tarin dukiyarsa matarsa Lantana rura gawayi take don tayi girki. Ya karaso gurinta da niyyar ya bata kudin cefanen ranar kawai sai wani almajiri mai zakin murya ya katse shi

Maula ta sidi maula ta balarabe, maula

Muna bara a bamu domin annabi, maula

Kowa ya bamu ya baiwa annabi,

maula

Alhaji Balala ya daka wata mahaukaciyar tsawa ya ce

” wani dan iskan yaro ne anan? Don iyayenka kar ka kara zuwa mun gida tunda bana ubanka ba ne!Shi ma uban naka ai ya san da yunwar ya turo ka almajiranci. Wai tukunna ma Lantana ba na ce a dunga garkame gate din nan ba saboda shigowar sakarkarun yaranan?”5

Ya cigaba da sababi Lantana kuma ta cigaba da kujiba kujibar aikinta ba ta ko bi ta kan sa ba. Sai ma tana hura gawayinta ta soma rera wata waka

Wayyo wayyo habiba yardamalmala

Dan Allah zo gareni yardamalmala2

Alhaji ya kule. Ya lura da take taken Lantana kwanan nan sai ya ce

“Wai Lantana ba magana nake miki ba kika mayar da ni mahaukaci. Tukunna ma bana hana wake waken nan na wasan hausa ba?”7

Cikin halin ko in kula ta ce

” O’o ni ba kayan kallo ba ina zan kalli wasan hausa? A bakin yara na ke ji idan sun je makwabta kallo sun jiyo”

Wani haushi ya turnuke shi ya ce

” Au don lalacewar tarbiyya har yaran nawa kike bari su shiga makota kallon wasan hausa? Kina da hankali kuwa Lantana?”3

Ta watso ma sa wani kallo wanda bata taba yi ba har sai da Alhaji ya ji ba dadi. Kan sa ya daure? Wai me ke faruwa ne? Wa ke zuga Lantana? Abinda yake gudu fa yana neman ya faru dalilin kenen da duk aure aurensa bai taba auro ‘yar jami’a ba.

Me akai akai ‘yar jami’a fitsararrun yaran mata da kan su ya gama wayewa da ‘yanci, yaya za ayi su lankwasu? Komai kana yi tana jin daidai take da kai. Ya fi ganewa mai karancin wayewa komai aka gaya ma ta ko bata so ta yi.7

Amma mamakin Alhaji bai kai kololuwa ba sai da ta mayar ma sa da

” Yaya za a yi in yi hankali kadangarun barikinka su ma suyi hankali? Ai abun sai yayi mana yawa”3

STORY CONTINUES BELOW

Da a ce Alhaji mai sabon dukan mace ne babu abunda zai hana yau ya yiwa Lantana lilis. To amma ba wai dukan ne bai taba yi ba, muhallin dukan ne babu. Duk cikin aure aurensa shida Lantana ta cikon bakwai babu wacce ta taba zama sama da shekara biyu saboda jarabar maqonsa da neman mata. Duk cikin matan ba wacce bata haihu ba kuma haka lantana ta hada da na ta guda biyar ta killace.

To ma a ajiye wannan a gefe ba Shin ba shekarar bara ba ne da ya fallawa lantana mari mahaifiyarsa Iya ta ce idan ya kara zata tsine ma sa? Ta fara da jero gore gore na halaccin da lta lantanar ta ma sa wanda matan da ya aura har shida suka gaza. Da ya tuna irin cin mutuncin da mahaifiyarsa ta masa akan lantana sai ya ji duk ba dadi.

Ba ya hada Iya da komai, ta je ta ci albarkacin Iya. Kuma da gaske idan lantana ta tafi ‘yayan nan sama da goma ina zai je ya ajiye su? Amma zai yi maganinta a cikin ruwan sanyi da shi take zancen.2

Ya share ta ya zura hannu a cikin aljihun rigarsa na hagu yana lalube kamar zai dauko abun kirki ya zaro wata cikwikwiyayyiyar N200. Dama haka yake yi kudinsa ma su dan daraja a aljihun cikin wandonsa yake adanawa. Kafin ya bata N200 ne wani dan yaro ba zai gaza shekara 5 ba ya fito da kofin koko a hannu ya zo wajen uwar ya ce

” Ummanmu ban koshi ba”

Ta dauki wani fulas a gefenta daga gani rabonta ne ta juye ma sa. Sai a lokacin ya lura da uban ya gaishe shi. Alhajin ya ce

” Sadiq ya baka je makaranta ba?

Yaron ya ce

” Baba ai tun jiya dayawa dayawa aka kore mu wai bamu biya kudin makaranta ba”

Alhaji ga dago ya kalli lantana fuskarta kamar hadarin da ya hadu ya ki saukar da ruwa ya ce

” yanzu lantana don rashin mutunci a kori yara daga makaranta kwana da kwanaki ki kasa gayamin?”2

Ta daga hannu tana cewa

” Dakata dakata Alhaji idan dai don dora ruwan talgen tuwon nan ne da ka ajiyeni sai in sauke in wuce inda na fi wayo! Kai ba ka san cewa lokaci biyan kudin makarantar yara yayi ba? Bar mun su a haka, ai a gida suke kwana”2

Alhaji ya san shagube take ma sa da shi take. Idan banda jiya kwana uku kenen bai kwana a gida ba bai kuma bar kudin cefane ba. Ba dai Lantana Iya zata je ta gayawa ba?

Ya dake ya ce

” Idan jikinki yana miki ciwo zan lallasa ki. To idan na zauna a gidan talgen tuwon zan juya miki? To..to..to shikenen ma!sai ki bani aron zaninki in tafi kofar gida in ke toye toye kin ga nayi daudun da kyau kenen!!”8

Da kyar yake fitar da numfashi saboda bacin rai na son zuciya ya cigaba

” Ana zuga ki ko? Kin kwana kin hantse da fitsara da rashin mutumci. Idan kin fasa ba kya kaunar gyatumarki!! Iya ta daure miki gindi ko? Zamu gani ni da ita wake aurenki!”

Kawai sai ya mayar da N200 sa aljihu ba zai bayar ba. Rashin kunyar tayi ta kudinta. Ita ma ranta a harzuke da alamun rashin tsoro ta ce

” Mu je zuwa! Kai ne dai zaka iya lallabowa da daddare ni kuma na iya rufa maka asiri a lokacin da kadangarun barikinka sukai maka bankada! Bi za til rasulillahi sai Allah ya saka min. Mai kuntaccen tazuge kawai!”16

Alhaji ya lura lantana so take ta dora masa jakar hatsi kaji suyi ta caccaka sai ya fice kawai cikin tsananin bacin rai. Yana jiyo fashewarta da kuka ya buga tsaki yana jin takaicin halin mata. Mace..mace ba tayi ba mace akwai rashin godiyar Allah. Idan ka bata taku daya to wallahi sai ta hau goma sha daya. Balle idan ta gan ta ita kadai..inaa…ai kyaun mace ka yi ma ta kishiya daga nan zata hankalta. Ya na ga dai aure zai kara.6

Amma ba anan take ba shi ba shi da ra’ayin tara mata saboda daukar nauyi. Yanzu mace kana aurota ba ka huce gajiyar hidimar aure ba sai tace ciki. Ka ci da ita ka ci da danta. Ga abun kamar gasa su yi ta haihuwa kamar ‘ya’yan zomaye. Yau abinci gobe rashin lafiya kana ta fitar da kudi.7

STORY CONTINUES BELOW

Ya kuma buga uban tsaki auren nan ba ma shawara ba ce a yanzu sai dai zai san matakan da zai bi yayi maganin lantana.

Ya isa kan dalleliyar motarsa kirar marsandi ta yayi, ya hau ya cilla kan titi. Ya san ya gama makara abunda yake gudu kenen. Ya tsani a rayuwarsa wani ya riga shi isa inda samu yake. Ya fi so ya mallaki komai shi kadai, shi yasa ma ake masa lakani da “cinye-du”.

” Mai kuntaccen tazuge kawai”9

Har ga hau kan titin Govenor road maganar lantana bata gogu daga ransa ba. To ma wai ina ruwan lantana da sabgarsa ta mata? Har zata sa ma sa ido ita ta ga zata iya wahal da kan ta. Saboda ya rage bacin rai sai ya tuno da faifan sidin dan kwairo da ya siya a danja jiya. Sai ya kunna ya na bin wakarsa ta sarkin muri takaicin Lantana yana ficewa daga ransa. Ya fara gyada kai in da yake cewa

Alhaji musa dan kwairo, ga babbar riga ya baka

Ga kufta kuma ga alkyabba, ga rawani kuma ga jar hulla

Har da agogo da takalmansu

Mu biyu sai ya bamu wan tauzan

Yaran dan kwairo goma sha uku

Kowa riga da tu hadred nera

An kayi total an ka hada

Kudin kwairo dana yara

Ya zama faif tauzan da sis hadred nera4

A lokacin ne danja ta tsayar da su sai kuma a bayansa wata karamar mota kirar starlet ta kwararo a guje ba ta lura da tsayawar danja ba ta dokawa Alhaji mota. Alhaji ya fito jiki sa yana rawa kamar mazari saboda tsananin bacin rai. Mutane ‘yan ganin kwaf suka fara dafifi a gaban motar sa su ji yanda aka yi. Sai kunfar baki yake yana zage zage. Sai cewa yake

” Yau zan ga uban da ya tsaya maka a garin nan in ji ko da shi aka taru aka hadu aka shinfida kasar kaduna.”

Wani abu da ya fi bawa Alhajin haushi shi ne duk wannan hargitsa ballin da babatu da ake yi mazaunin motar wacce ke rufe ruf da tint bai ko motsa ba balle yayi alamun fitowa.

Ya kara duban agogon hannunsa sha daya saura abinda ya sa wani mululu ya zo masa makogwaro ya tokare. Ya yanke shawarar ya je wajen motar ya bude ya fizgo mutumin ya sharara ma sa marin gobe- ba -zaka-kara-ba.

Abu daya ne tal ya tsayar da shi bude hancin motar da aka yi hade da bayyanar wata zukekiyar mace mai haske kamar watan sallah. Ba wai yanayin Kyawunta ne kadai ya dada shi da kasa ba, aa ya ga kyawawan mata fiye da adadin shekarunsa a doran kasa. Sai dai me? Yanayin shigarta ne ya rikita shi har ya ji ya nemi kululun nan na makogwaronsa ya rasa.11

Lallai ya yarda wani kaya sai amale. Da ta fito ma tsayawa tayi cak tana kallon dandazon mutanen kamar ‘yan taron sinima daidai.

Wata riga ce marar hannu a jikinta da ta wuce cibiyarta da dakika daya sai wani dogon wando “jegens” mai lafewa a jikin mutum kamar tare aka halicce su. Gashin kan ta an yi kari dana doki an kitse ya sauka har yana tabo kugunta. Ta dauki wani bakin gilashi da yake nuna iya adadin rashin mutuncin da zata iya dokawa ta kwama a fuska. Nan take Alhaji Balala ya raya a ransa cewa wannan safiyar litinin din ta sa ce.5

Babu kunya balle jin nauyin idanuwa kusan hamsin da suka mamaye ta ta tako kamar tana tausayin kasa ta karaso inda yake ta ce

” Yallabai barka da war haka”

Alhaji ya hadiye yawu mukut! Ya saki wani murmushi da yake yiwa masu dankwali in dai ba matansa ba ne ya ce4

” Barka da war haka dai masu gari”

Tayi far da ido ta ce

” Sai wannan tsautsayi ya afku, an yi shi kan kuskure Alhaji sai dai ayi hakuri…je suis desole yallabai”6

Anan Alhaji ya gani abu biyu, faransa ce kuma rabonsa ce don haka sai ya karo mizanin fara’arsa ya ce4

” yanmata wannan ai ba matsala ba ce, asali ma ni ya kamata na baki hakuri ta dalilina har fitilar motarki ta fice ni kuwa kwarzane ne kawai. Bari ma ki gani yanzu zan kira bakanike na ya wuce da motar ta ki. Wannan ai ba abun damuwa ba ne”

STORY CONTINUES BELOW

Ya jawo wayar zai danna kira sai a fusace ya dubi mutanen nan da suke musu kallon kwaf ya ce

” Kai jama’a menene haka wai? Kun zo kun min dafifi a kai..to..to..ko marhaba sinima ce ni..zancen banza zancen wofi”1

Haka aka watse ana masa dariya wai reshe ya juye da mujiya har wani shakiyyi ya ce

” Alhaji mayar da wukar, ji da dankwalin!”

Bai kula ba ya danna waya ya kira bakanike ba a wani jima ba ya karaso. Ya ce ta bada motar ta kwaso tarkacenta duka bakaniken ya wuce da motar.

Ta dubi Alhaji cikin farin ciki ta ce

” Godiya nake yallabai vous remercie dama haka mutanen kaduna ke da karamci?”

Alhaji ya fashe da dariya ganin ta fadi gasassa ya dauki akwatinta yace6

” Mu tafi ko? Zan kai ki duk inda kike da muradi”

Ta murmusa ta ce

” nous pauvons aller”

( za mu iya tafiya)

Alhaji ya jinginar da batun bidding suka shiga mota. Wannan karin ya kashe wakar dan kwairo ya kunna Radio kaduna sannan ya dube ta a tsanake ya ce

“Har yanzu ban san sunan gimbiyar ba”

” Mahfuza” tace da shi

Ya ce

“Lallai sunan ya dace da ke. Me ya shigo da ke garin gwamnan namu?”

Ta ce

” wallahi daga Abuja nake na zo wani aiki ne zan je masauki”

Ya tambayi masaukin ta gaya ma sa Haraba hotel. Bai yi wata wata ba ya zarce.

Alhaji ya cake naira dubu arbain kudin kwana biyu kamar yadda tace za ta yi suka hau sama hawa na biyu daki mai namba 24. Ya kira”room servive” ya ce ta fadi duk abunda take son ci, ta fada aka kawo. Suka ci suka yi nak!9

A ranar yini suka yi suna sheke ayarsu ba tare da Alhaji ya tuna iyalen da ya bari a gida ba cefane ba. Da daddare Alhaji bai fita ba sai daya kulleta ta baya ya tafi da mukullin. Ya san halin irinsu sarai yanzu sai ta tafi abinta ta bar shi bayan bai gama barje kudinsa ba.3

Ya je yayi ‘yan harkokinsa daga karshe ya tsaya a wajen me nama ya siyo gasasshen nama da robobin lemo hade da kayan bukatu kala kala. Bai wuce koina ba sai haraba hotel. Yau ma bazai kwana a gida ba, ya gayawa kan sa hakan.

Ya sa mukulli ha bude kofa ya tarar da ita a inda ya barta yashe a kan gado tana kallon tv. Banbancin kawai yanzu ta sheka wanka ta yi ado da wasu kaya masu daukar hankali. Nan Alhaji ya dada rikicewa shi dai yarinyar nan ta shiga ransa baya jin zai iya barinta ta tafi a kwana biyun nan. Wayo zai yi ma ta ya lallaba ta yi masa sati har ya fanshe kudinsa.

Dama sun yi waya da bakanikensa da ya bawa motarsa gyara ya ce wannan motar ai tana bukatar gyara sosai don komanta ya kwarkwance. To sai yayi amfani da hakan ya ce wai zai canja mata motar ma idan ta kara masa kwanaki.

Sai da ta kara kwanaki biyu ta yini sannan ta dubi Alhaji a cikin fari da ido ta ce

” Alhaji wai yaya ne? Ka san fa aiki na zo amma ka kafa ka tsare. Sai dai ka kulle ni a daki ka fita ka je ka dawo dan aikin da na zo yi ma na gagara lekawa”

Ya kwashe da dariya rayuwa na gara masa yanda yake so. Ya ce

” To wa zai gan ki ya bar ki haka kawai kamar wani sakarai? Ni da nake ta son ki min sati ma!”

Ta kalle shi kasa kasa a ranta tana rayawa wani irin tsohon kwar tu kwar ne wannan? Amma a shagwabe sai ta ce

” A’a ni dai gaskiya Alhaji abunda da fa ya kawo ni kenen ba a yi haka ba”

Ya taso matsowa inda take ya rungumota ya ce

STORY CONTINUES BELOW

” haba haba gimbiyata kwantar da hankalinki. Ni da kai na gobe zan dauke ki na kai ki kiyi alamuranki. Amma fa da sharadin sai kin min sati.”

Ya jawo brief case din sa ya kirgo ‘yan dubu dubu guda hamsin ya danka ma ta a hannunta ya ce

” Kin ga idan mun fita sai ki tsaya kiyi shopping ko?

A haka dai har ya lallabata ta amince.

Da safe ya shirya zai fita ya yi wasu harkoki sannan ya dan leka gidansa. Tana magagin bacci ya ma ta sallama da cewar zai dawo su fita. Ya kulle dakin ya tafi da dan mukullin.

A gurguje ya je gidan nasa ya bada N200 kudin cefane. Lantana ta yi ma sa korafin yaro ya tashi da ciwon ido da kyar ya kara N100 wai a sayi ampikilos a kemis a balle a barbada masa a idon. Bai tsaya jin wani dogon bayani ba ya fice.19

Ya wuce wani wajen sayar da motoci da suka saba harka tare ya duba wata ‘yar madaidaiciyar “thankyou daddy” ya taya. Watakila ya rike yarinyar nan wata 6 in ya so ya dalle ta da wannan mota. Tunaninsa kenen.

Daga nan ya wuce Haraba hotel in da ya fi wayo. Ya shiga daidai reception kamar daga sama ya ji wata zazzakar murya ta ce

” Ranka shi dade Alhaji Balala, dama ashe rai kan ga rai?”

Ya waiwayo a hankali yana mamakin cafkar sunansa da aka yi. A zaune a kujerar reception din ya ga wata bakar yarinya sanye da atamfa ruwan dorawa. Tayi dinkin riga da siket sun matseta tsam! Hakannan wuyan rigar ya sauko yana bayyana rabin kirjinta. Tana karkada kafa tana taunar cingam kas kas. Ta hadu ba karya

Har ga Allah bai gane ta ba bai kuma taba ganinta ba amma kuma ai da kunya kyakkyawar budurwa ta ambaci sunanka ka gwasale ta. Ya karaso har inda take da gaske so yake ya gano ta. Tayi galala da baki ta ce

” Alhaji kar dai ka ce da ni baka gane ni ba”

Ya ce

” Mutum har zai iya manta kyakkyawar fuska kamar ta ki?”

Ta tsare shi da idanuwa da alamun nuna jin zafi ta ce

” wallahi Alhaji baka gane ni ba. Amma nayi mamaki. Ai shikenen ni dana damu da ka ai ga shi ai na rike fuskarka”

Ta mike da alamun da ke nuna tafiya za tayi. Ya jawo ta ya zaunar cikin kaskantar da kai ya ce

” Haba ranki shi dade fushin ba wuya ne? Kin san ni mutum ne mai harkalla shi yasa wasu abubuwan suke subuce min”

Nan dai yayi ta lallashinta yana kwantar da kai don har ga Allah yarinyar ta mugun tafiya da imaninsa. Cikin yauki da rangwada ta ce1

“Ai ka san farida ko? ‘Yar mutan jimeta. Ko ita ma ka manta ta?

Kwarai ya san farida. Wata tsohuwar yarinyarsa ce da yayi yayinta kamar hauka ta kara cewa ” to ni kawar ta ce mun hadu da kai ba sau daya ba kuma na rike fuskarka tunda na damu. Yanzu haka sunana ma sai na gaya maka kai kuwa farat daya na fadi naka. Alhaji ya kwantar da kai yana dariya dariya yana cewa

” afuwan..afuwan da girman kujerarki. Idan an tuna min ai ba alifi ba ne”

Ta dago hannunta ta mika masa ta ce

” A nawa?”

Babu tantama ya zira hannunsa a aljihu ya zaro naira dubu goma cas ya dora ma ta. Ta ce2

” To ka ci gari, sunana Tani”

Nan suka kacame da hira kamar sun saba. Daga baya sai ta mike ta yi wata irin doguwar mika Alhaji ya kura ma ta ido kamar tsohin maye ta ce1

” Zama guri daya tsautsayi in ji kifi bari ka ga in shiga daga ciki dawowa ta kenen na rashe a nan.”

Alhaji ga mike cikin azarbabi ba wai ya manta da yarinyar nan mahfuza ba ne da ya bari a daki to amma idan wannan ta subuce ma sa fa? Shi dama can haka halinsa yake hadamamme ne anan ya samu sunansa cinye-du. Don haka sai ya kalleta ya ce5

STORY CONTINUES BELOW

” Haba tauraruwa ka da ki ce mini ba kya bukatar rakiya”

” Ban ce da kai ba”

Ta ba shi amsa. Daga nan suka qarke a hawa na uku daki mai namba 38.

Lokacin da Alhaji ya samu ya kubuta daga tarkon Tani karfe biyu daidai na rana. Bai so ba amma ba yadda ya iya ne ga shi ya bar mahfuza a daki ya san har ta gaji da jira. Sai ya damkawa Tani damin kudi a hannunta kafin su rabu da cewar zai je ya dawo. A ransa yana mamakin irin wayonsa yanda yayi dubarar darje yanmata har biyu a lokaci daya.2

Nan da nan sai ya wuce daki mai lamba 24 yana taraddadin yanda zasu

Kare da mahfuza don ya san yayi laifi. Kafin ya karasa wani sabis ya taho da keken tura abinci suka ci karo har ya barar da kwanuka. Wata miya ta tsallarwa Alhaji akan tsadadden takalminsa. Ya dunga banka masifa kamar zai tayar da otal din. Wai ba su waye da aikinsu ba. Sabis din yayi ta ba shi hakuri har ya goge masa Alhaji bai daina bala’i ba. Ya buga tsaki ya wuce.1

Ya sa mukulli ya bude dakin mahfuza bai gan ta a kan gadon ba, bai kawo komai ba don ya ji karan ruwa a bandaki. So yake ta fito ya samu ya dan dauraye jikinsa.

Ya cire hularsa ya kishingida akan gadon yana jiran ta fito. Tunaninsa yana ta shawagi akan irin zaryar da zai yi a dakunan biyu yau ranar ta sa ce.2

Shiru shiru bata fito ba har ya gaji ya kwankwasa, ya kara kwankwasawa ya ji shiru. Sai ya tura sai dai me? Wayam!

Gabansa ya yanke ya fadi. Ah ko ga gaji da jiransa ne ta tafi wajen aikin da ya kawo ta? Amma sai ya tuna cewa ya kulle kofar ya tafi da mukullin. To ta ina ta fita? Sai a lokacin ya kula ba jakarta. Yayi sauri ya bude wardrobe nan ma ba akwatinta.

Tsoro tsoro ya fara shigarsa da tunanin ko aljana ya dauko? Ya fita daga dakin da sauri ya tafi reception yana tambayar ko matar da ke daki mai namba 24 tayi “checking out”. Suka ba shi amsa da a’a domin ma ai mukullin dakin yana hannunsu. Kan sa ya kara daurewa.

Sai ya kasa gasgatawa ya koma dakin yana bankade bankaden neman ta kamar allura. Ya gaji don kan sa, ya hada gumi sharkaf ya baro dakin. Tunaninsa ko garin kwashe kwashensa ya dauko aljana gwara yayi sauri ya bar hotel din. Daga nan wucewa zai yi wajen Malam yunusa yayi ma sa rubutun kariya ya sha.2

Ya zira hannu aljihunsa don ya lalubo mukullin motarsa kafin ya karasa inda ya ajiyeta sai mukulli yace daukeni inda ka ajiye. Nan ya shiga waswasi watakila garin bankade bankadensa ya yar a dakin don haka sai ya koma kamar zai tashi sama.1

Nana ma yayi iya dubansa bai gani ba. Sai a lokacin ya tuno ashe fa ya je sheke aya dakin yarinyar nan Tani, ta yiwu anan ya yar. Kamar mahaukaci haka ya bazama daki mai namba 38.3

Ya kwankwasa ba da wani jimawa ba aka bude amma sai yayi ido biyu da “room service”. A hanzarce ya tambaya ina wacce ke dakin. Sabis ya ce

” Ai ba ta fi minti talatin da checking out ba, shi ne ma na karbi mukulli nake gyara dakin”5

Kan Alhaji Balala ya shiga dimuwa. Shin ba yanzu yanzu ya rabu da yarinyar ba ne? Me yasa daga Tani har Mahfuza ya neme su ya rasa?8

Ya kawar da wannan a ransa shi ta mukullin motarsa yake ma. Ya samu ya bar hotel din nan don ya ji komai ya gundire shi.

Yayi wa sabis din takaitaccen bayani suka shiga suka duba dan mukullin amma babu ko alamunsa. Alhaji ya gaji iya gajiya wani sashe na ransa yana raya ma sa watakila ya yar da mukullin a daidai inda ya paka motar.

Ya sauka ya tafi inda ya paka motar sai dai me? Babu mota ko sama ko kasa kamar an yi ruwa an dauke.1

Wata irin rikicewa ta ziyarci kwakwalwar Alhaji, har sai da ya zagaye wajen paka motoci sau uku kamar mahaukaci babu alamun mota. Danqari!17

STORY CONTINUES BELOW

Wanann alamari ya daure ma sa kai wai mota a cikin randa. Wani irin duhu yake gani yana neman kayar da shi, akwai wani rikitaccen alamarin da ya kasa warwarewa.

A lokacin ya danna waya ba don yana cikin cikakken hankalinsa ba ya kira Alhaji Shitu amininsa tun na rai da rai. Halayyar neme neme ta Alhaji Balala ya sa aminin sa ya ja baya da shi duk da dai suna tare. Bai tsaya dogon bayani ba ya ce su hadu a Haraba Hotel.

Ya karasa reception ya tada ballin a kira masa manaja do yau sai an fito ma sa da motarsa. Kafin Alhaji shitu ya karaso rigima ta kacame a hotel, Alhaji yana ta kumfar baki har ya kira yan sanda biyu. Alhaji shitu ya iso aka mayar da yanda aka yi.

Manaja ya rufe ido yace su ba su san da batan mota ba kuma ba zasu biya ba saboda a wajen pakin sun rubuta

” vehicles are parked at owners risk”

Cewa duk wanda fa ya aje motar to hakkin motar a kan sa yake. Rigima ta tsaurara har Alhaji Shitu ya samu ya janye Alhaji Balala da cewar yansanda zasu cigaba da bincike. Ya fice da shi a motarsa yana sharfa gumi.2

Yau wata irin rana ce birkitacciya marar dadin tunawa. Alhaji Shitu ya bude hancin robar ruwa ya mika ma sa ya kwankwada kana ya ce masa

” wai tun farko ma me motarka ta ke yi a otal? Tabbas akwai abunda kake boyemin”

Babu wata kwana kwana Alhaji Balala ya zayyane masa tun daga farko har karshe. Alhaji Shitu ya ci birki ya faka a gefen titi saboda tsanananin mamaki. Ya daki sitiyarinsa ya ce

“Ka gani ko? Ka gani ko Balala na sha gaya maka irin tayuwar nan ba rayuwa ba ce. Babu inda zata ajiyeka sai a tashar asara. Na gaya maka na gaya maka ka kasa ganewa. You were played! Wannan alamarin duk shiri ne..gadar zare ce aka shirya maka bayan an yi watanni da karantarka. Hasbunallahu wa niimal wakeel!

” kamar ya shiri?” Ya tambaya1

Alhaji Shitu ya nisa kan ya ce

” Saurareni da kyau. Wadannan mata guda biyu sun san ka ba tun yau ba sun karance ka sun kuma gano halayyarka ta cinye du. Don haka sai suka sa ka a matsayin target.

Da farko wannan motar da aka zo aka buga maka sai da aka tabbatar bata da mamora tsohon gwangwani ce. Ba tsautsayi ba ne da sane tayi ta san in dai ka gan ta sai ka dauke ta. Daga nan wasan ya fara.

Tani ita ma ta san ka, bakinsu daya da ta farko. Ta yi abunda tayi ne don ta janye hankalinka ita mahfuza ta gudu. Ita tani ita ta dauke maka mukullin mota Allah ya sa ma mukullin motar kadai ta dauke. Kafin daga dakin Tani mai lamba 38 zuwa dakin mahfuza mai lamba 24 Tani za ta gudu ta zure maka mota. Shi yasa a shirin nasu kuka ci karo da sabis don ya kara bata maka lokaci kafin ka isa dakin mahfuza.

Da ka shiga ta bar famfo a kunne don ka zata tana bandaki wannan ma duk wata dubara ce ta kara siyan lokaci. Amma asali shi ne ta dade da fita daga dakin. Tani zai iya zama ita ta fice da motar ko kuma mahfuza ta dade da jiranta a waje ta bata mukullin motar ko kuma su duka biyun. Wannan safa da marwar da kayi ta neman dan mukulli da mahfuza ya isa a gudu da kowacce irin mota.1

Alhaji Balala ya nisa a cikin daurewar kai ya ce

” To ya aka yi mahfuza ta fito daga dakin bayan kullum sai na kulle ta kafin na fito?”

Alhaji shitu yayi murmushi kafin ya ce

“Wai shin Balala ka manta da bariki ne shin ba kai ne a cikinta ba? Ka manta cewar komai in dai da kudi kare magana ne. Za ka sa a yi maka shi ko menene sabida cin amana ba komai ba ne in dai da kudi. Ai wannan hotel din da ka gani tabbas akwai wata mas’ala.

La’alla yanmatan biyu bakinsu daya da manaja sun siye shi. Ko kuma suna da wasu ma’aikatan hotel din da suka siye. Za ta yiwu mai aiki a reception da kuma sabis sabis. Dukkaninsu za su iya samu access zuwa ga spare key na kowani daki. Ai ina ga abu mai sauki ne wanda aka hada baki da shi musamman room sabis ya dauki mukulli ya je ya bude ta ba tare da kowa yayi la’akari ba. Idan dai har zasu ba shi cin hanci. Ina fatan ka fahince ni?”

STORY CONTINUES BELOW

Ya fahinta din sai dai ya gaza gasgatawa har za ayi mishi wayo irin haka cikin fusata ya ce

” To in dai kuwa haka ne yanmatan nan sai na nemo su na kai su kotu. Sai na nunawa yarinya ni Alhaji Balala kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha. Har otal din ma sai na sa an rufe shi, na tona musu asiri!”2

Huci yake yi, yana tsananin cikin tashin hankali. Motarsa ta yayi akalla ta kusa miliyan 3.

Alhaji Shitu yayi murmushin takaici.

Ya ce

“Calm down abokina. Duk abunda za kayi ina so kayi tunani kafin ka aikata kar balli ya tashi da kai. Su wadannan yanmata ina za ka gan su? Ina tabbatar maka ba yan gari ba ne. Yanzu haka ma sunayen da suka gaya maka duk na karya ne.

Wata hujja gareka akan otal bayan kai ka kawo kan ka? Sai uwa uba ta ina zaka fara shariar nan? Labari ya ba za duniya ka dauki matan banza sun damfare ka abu ya je har kunnen iya, matarka , ‘yayanka, masoyanka da makiyanka. Ta ina aka hau ta ina za a sauko?4

Wani irin gumi Alhaji Balala ke sharewa kamar ba gobe. Ambatar Iya a lamarin ya sa ya ji zuciyarsa kanar za ta fashe. Idan Iya ta ji sai ta yi ma sa tsinuwa ta har abada! Da a ce shi mai saurin kuka ne babu abinda zai hana shi zubda hawaye.5

Sai a lokacin ya tuna da wani abu. Wannan tsohuwar motar tata a gurin bakanike. Wata kila ya rage asara. Ya kira shi, bakaniken ya ce

” Alhaji wata mota fa? Motar da ka aiko tun safe aka karba har ma aka bada kudin gyaran in ji ka….”9

Alhajin ya katse wayar ba tare da ya ji karshen wannan kayan takaici ba. Ya bude baki kenen zai labartawa Alhaji Shitu yanda aka yi. Sai ya ji wayoyinsa biyu suna fitar da qara rraki barkatai na shigowar sakonni.2

Cikin sauri ya bude ya gamu da rikicewa da ta ninka ta dazu sau goma sha tara. Bankuna uku yake amfani da UTA , Charity da UD. Kowanne a ciki yana aika masa alert na zarar makudan kudade.7

Cikin azama ya zaro wallet din shi in da atm cards din sa suke, wayam!2

Cikin kaduwa ya dubi Alhaji Shitu wanda ya riga ya hano abunda ake ciki ya ce

” kudina suke kwashemin! Na shiga uku!…kudi na Shitu!13

Shi ma Alhaji Shitu cikin rudewa yake cewa

” kira Manaja yi sauri. Aikin hackers ne…yi maza maza”

Ya rude ya ma rasa wanne zai fara kira har ya samu ya danna kiran na UD. Bai ma san inda hankalinsa yake ba kawai ji yayi yana cewa

” Stop the transaction!! Stop the transaction!4

Alhaji Shitu ya dafe kai, ya san lamarin sai du’a’i. Alamarin sai gyaran Allah!

*********************************

Wani irin gudu take fyallawa a motar kamar zata tashi sama duhu ne yake fara mamaye garin. Can ta gangara daga bakin titi ta sauka wata hanya da babu kwalta. Tayi tafiya ba da yawa ba har ta isa wani yasasahen kango. Unguwar babu mutane sosai sai babura da keke napep da ke wucewa tsilli tsilli. Kamar dai wata hanya ce ta “short cut”

Wayarta ta danna ta kira ta wani mai suna Osi, ya daga ta ce

” gani na iso” ta katse

Ba ayi cikakken minti biyu ba ya bayyana dan tsamurmuri da shi sanye da singileti da dogon wando jins. Hannunsa yana dauke da tabar wiwi yana zuka kamar zai tashi huhunsa daga aiki.

Ya fara tafa hannayensa yana zagaye motar cikin farin ciki ya ce

” Beb komai yayi na yaba da kokarinki” ya kwashe da wata mahaukaciyar dariya.

Ta katse shi da cewar

” Dakata Osi ba wannan ya kawo ni ba. Sallame ni in tafi akan hanya nake”

Ya wani kai mata cafka yana cewa

” haba beb wai ke kan maganar kudi ba kya sassauci? Ni da ke ai mun zama daya”

Ta ce

” Na ji na ji Osi, sallame ni”

Yayi wani matsiyacin murmushi ya daga waya ya kira wani ya ce

” fito da jakar nan”

Wani dan saurayi da bai wuce ahekara 20 baya fito da wata yar jaka irinta ‘yan makaranta ya mika ma ta. Ta zuge jakar sannan ga kirga kudin da ido rafa ce ta dubu daidai har guda goma sha biyu. Ta dago a fusace ta ce

” miliyan daya da dubu dari biyu? A wannan dankareriyar motar da kuma kudin account na Alhaji. Ita motar a karan kan ta ta yi miliyan 3. Ka ji tsoron Allah Osi!”

” Ka ji ‘yar banten uba! Dalla malama kar ki mana e ya ne. Ke tsoron Allah ne yasa kika sato motar? Wannan kudi dana baki a dunqule fa ni ke da risk ke kin ware abinki. Yanzu yanzu zan dauki motar a kara canja ma ta plate number a kuma yi mata feshi. Suk dare sai na bar garin nan. Kika san tsautsayin da zai iya ritsawa da ni? Ke ai ta fado miki gasassa ne kawai!”1

Wani bakin ciki ya tsaya ma ta a makogoro shi yasa ta tsani aiki da Osi saboda son kan sa amma ba komai. Saboda tuwon gobe ake wanke tukunya. Ta karba tayi gaba kadan ta tare me napep. Ba ta fi minti 2 da tafiya ba Osi ya dauki waya ya kira, aka dauka. Ya ce

” Bi ta ka sumar da ita ka karbo min kudina”7

Aka amsa da

” Ok”

Suna karya kwana da mai napep ta sauka ta fyalla a guje bayan wata himilin bola ta kwanta ruf da ciki. A gaba idonta wani ya zo ya wuce a guje ya taddo mai napep, ya leka nemanta bai gan ta ba. Ya kai masa naushi yana tambayarsa ina take ya gaya masa ta sauka a baya. Ya bazama nemanta yana haska tocila domin duhu ya sauka. Daga baya ya koma hanyar da ya fito yana nema.

Ai tana ganin ya juya ta fyalla cikin tsurkukin bolar nan da gudu kamar ranta zai fita. Ba ta nisa ba sai da tazo bakin titi. Kamar a tare wata bakar mota kirar toyota ta ci wawan birki a gabanta. Ta bude ta shiga, matukiyar motar ta take totur ta danna a guje kamar tashin duniya. Mai tukin ta ce

” Damn it! You stink!”

Bata kula ta ba ta dauko waya ta danna nambar Osi yana dagawa ta kundumo masa ashariya ta ce

” haduwarmu ba za tayi kyau ba!”

Yayi wata bahaguwar dariya ya ce

” kin sha wannan karin, amma ki tsumaye ni”

Ta kashe wayar bayan ta danna masa wani zagin.

DIreban motar ba ta daina sharara gudu ba har ta iso fly over, ta dauke kan motar zuwa titin Zariya. Sai da ta dan yi tafiya mai nisa sannan Hindu ta juyo ta kalli Rukky ta ce2

” Sukari, yaya an dace?”

Ita ma ta kalle ta tana jinjina ma ta kai ta ce

” An dace, sosai ma an dace”Dare daya Allah kan yi bature.5

Abuja, Nigeria

Harabar cikin club din na Luoisiana babu haske idan ka cire jajaye da korayen fitilu masu kawowa da daukewa wanda aka fi sani da “disco light”. Kowa harkar gabansa yake yi.

Masu rawa nayi, masu shan taba ko wiwi , masu kwankwadar giya kowa na aikatawa daidai da halayyarsa.

Wasu kuma da suka daukin hakan karancin cinyewa suna zaune a VIP a wasu kalar kujeru masu hade da tebura, suna hirarrakin da ya shafesu tare da shan abunda yayi daidai da raayinsu.

A wata ‘yar kusurwa kadan da babu mutane wata mace ce a zaune ita kadai. Kallo daya za kayi ma ta ka san wayayyiya ce a bariki. Ta sa wata riga mai kama da ta bebin roba iya gwiwa, gashin izgar dokinta ya ziro har kafadunta.2

Ba ta cewa kowa kanzil ba wadanda suka tanka fa ma sun gaji sun tafi. Ba ta da wani aiki sai zukar taba don har ta kusa tashi da kwali daya a a tsawon zamanta.

Ta kuma jan tsaki a karo na ashirin ba daya, a rayuwarta ta tsani jira sai dai a jira ta shi ya ta ta kagu. Ta jefar da kwanson tabar da ta shanye ta janyo wani karan ta kyasta,zuka daya tayi ta ji an janye daga hannunta.2

Cikin tsanannin mamakin son ganin wanda ya isa ta dago kai tayi ido biyu da wani rusheshen mutum mai uban tumbi. Ya saka wani burgujejen wando tiri kwata da wata katuwar riga, ya dora hular inyamurai a ka.

Ya zuki tabar ya fesar ma ta a fuska kana ya ce

” Baby girl sunana tobacco kin ga kuma ban miki adalci ba a ce ina raye na bar ki ke kadai kina tayar da hadari a gizagizai”

Ta dan nisa ta jingina da kujerar da take zaune ta zuba masa ido. Yana murza hannayensa ya ce

” Gaskiya ana sanyi a garin nan anya ma kina jin sanyin nan kuwa?”2

Bata kula ba sai ma tace da shi

” yaya aka yi ka gane ni?”

Yayi wani guntun murmushi ya ce

” kina sanye da fuskar ‘yan wasan karta”

Ta yamutsa fuska don bata gane ba ya ce

” poker face”

Ta gyada kai, ta gaji so take a wuce gurin. Shi kuma sai taga ya daga hannu ya yafito sabis na club din ya fada masa irin kalar giyar da yake so ya kawo masa aka kawo. Ta ga an rubuta blue crystal ba ta taba ganin irinta ba, ta basar wannan ba damuwarta ba ce.

Ya zuba a tambulan ya kwankwada sau daya, watakila wannan ne maganin sanyin da yake bukata. Maganar shi ce ta katse ma ta tunani da ta ji ya ce a tsaurare

“Ina sakona?”

Tayi masa kallon tsaf, sannan ta zuge jakarta ta zaro wani nadi a takarda a farar takarda. Ba ta mika ma sa ba sai ta ajiye akan tebur. Ya sa hannu a aljihu ya jawo wata siririyar ambulan ruwan kasa ya ajiye a daidai saitin da ta aje sakon nasa.

Ta sa hannu zata dauki ambulan din ya kai hannu ga danne ya ce

” not so fast..baby girl..not so fast”

A tare suka janye hannu. Sai ya dauki wannan farar takarda ya bude ya kai hancinsa kamar mai shakar hodar iblis. Ya dandana da bakinsa ya jinjina kai ya ce

” komai yayi kyau”

Ya zira a aljihu ya mike. Ya dauki kwalbar giyarsa da bai karasa ba yayi gaba abunsa ba tare da ya waiwayeta ba.

Ta dauki ambulan din. Kaurinta ya sa ta san ba kudi ne dan kadan ba. Ta jefa a jaka. Bai fi minti biyar da fita ba ta janyo waya kirar samsung ta danna wata namba, a ringin na uku aka dauka. Ta ce

STORY CONTINUES BELOW

” ya taho”

Ta  goge kiran hade da kashe wayar gabadaya ta jefa ta a wani kwandon shara. Sa’annan ta cigaba da kada kafafuwanta.

Fitar tobacco ke da wuya ya shiga motarsa ya dauki wata barauniyar hanya da sai wanda yayi wa Abuja sani bana wasa ba. Bai tsaya a koina ba don ya san tsayuwar bata kamace shi ba kuma hanyar akwai karancin checkpoint.

Yayi hanyar fita daf da Nyanya aka tsayar da shi a wani checkpoint da ya ji bai aminta da shi ba. Dan gajeren dansandan mai lubu lubun kumatu ya haske tobacco da tocila ya ce

“Oga daga ina?”

Tobacco ya kara mazewa kokari yake kar giyar da ya sha ta dauke shi ya tapka kuskuren da zai jawo ma sa asarar nairori. Ya ce

” daga cikin gari”

Dansandan ya cigaba da dallare masa idanu ya ce

” At this time of the night? Its already past 2am”

Tobacco zai bada hakuri ba don ya so ba sai don uzurin da ke gabansa. Dan sanda ya dallaro kwalbar giyar da tobacco ya taho da ita.

” kana tuki da daddare sannan kana drinking. Ba ka san cewa wannan biyun manyan offense ba ne? Za kayi bayani a station”

Nan tobacco ya dago bakin zaren bai tabbatar da hakan ba sai daya dauki gudar dubu daya ha mannawa dansandan a hannu ya ki karba. Sai ma ya kara da cewar

” you are under arrest for late driving, drinking while driving and bribery!yanzu zamu wuce da kai station”

Tobacco ya gane shune ta masa wannan karamar yar iskar, za kuwa ta gane bata da wayo. Kafin dansanda ya kira abokin aikinsa su shigo motarsa su tafi tare yayi wuf ya dauki wayarsa ya danna speed dial 1. Ringing daya tak tayi aka daga a daya bangaren. Ya ce

” Get her!”

Bayan fitar tobacco ne tayi odar giya katamar kwalba daya bata tashi daga gurin ba sai da ta kwankwade. Ta fara jin ga kamar a sararin samaniya take. Ta dauki jakarta ta fara tafiya kamar mai tatata zuwa hanyar fita.

Wani ya zo ya cakume ta yace

” hey make i carry u go home?”

Ta wancakalar da shi tana ji yana aiko ma ta da zagi har da “ashawo”. Wani tsaki ta ja da ta tuna sai ta tsaya taren mai tasi. Wata zuciyar ta ce mata ta tsayar da lift kawai wanda uwarsa ta laance ma sa kawai ya dauketa.

Tana fitowa kamar jiranta ake wata mota baka kirin mai tinted glass ta sha gabanta, wani shirgege mai kyalle a fuska ya damke ta. Za tayi ihu ya toshe bakinta ya watsa ta cikin motar kamar kayan wanki. Suka figa kamar zasu tashi sama.

*******************************

” Hello….baby girl”

Wata kakkaurar murya marar murmushin imani ta ce da ita. Hakan ya fara sawa ta dawo cikin hankalinta saboda ta kwana bata san inda kanta yake ba.

Ta bude fuskarta a hankali har sukai tangararau suka sauka akan faskaceciyar fuskar tobacco. Ya sakar mata wani murmushi wanda kana gani ka san ka kade har hanjinka. Fuskarta ta nuna mamaki cikinta ya bada kululu ya ce

” kin yi mamakin gani na ko? Bayan an hada baki da ke an min cunen yansanda ko? Alhalin na fitar muku da hakkinku ba tare da ragin ko kwandala ba!

Ya nuna kan sa da danyatsa rai a bace ya ce

” Ni tobacco na fi karfin kowane dansanda don a tafin hannuna suke. Ko awa daya ban yi ba na fito saboda mu ne garin nan. Ko da yake ba zama nayi anan don in karanto miki labaran kasa ba”

Ya shako mata wuya kamar ba zai bar ta da rai ba ya xe

” who do you work for?

Ba ta taba jin kamshin mutuwa ba irin na ranar. Ya wancakalar da ita ya sa kafa ya shure ta. Ya dunga kwallo da ita har sai da ta sume.

STORY CONTINUES BELOW

” wannan daga gani za tayi taurin kai”  ya ce da wani shirgege kamarsa ” watsa mata ruwan sanyibta farfado”

Watsa mata ruwan sanyin da aka yi yasa ta dawo daga duniyar cankacakare, ita bata rayu ba ita bata mutu ba. Bata taba shan duka irin na yau ba. Lallai ta yarda bariki alalar gero don kuwa yau ta kwabe ma ta.1

A cikin wannan taraddadin ta dubi tobacco a marairaice ta ce

” Na tuba, na bi Allah na bi ka. Ka rufa min asiri’

A fusace ya ce

”   Ba ki bi ubanki ba kika fito yawon duniya sai ni za ki bi!! Zancen banza kawai..stupid..idiot fuck you!

A daga ta sama cancakat ya ce

” Ina miki tambayar karshe, wa ya turo ki wa kike yiwa aiki?”

Bata ba shi amsa ba. Kawai sai ya sake ta ta fadi rikica.

Ya ce a kai ta wani daki. Mai tsaron dakin ya dube ta yace oga ya baki awanni ki bayyana wanda kike yiwa aiki..if not..yau za ai bako a lahira!

Ta karewa jangin dakin kallo ta ji fuskarta ta ma ta nauyi wanda ta san ba zai wuce dukan shan gishirin da tobacco ya mata ba. Daga nan a karo na farko na rayuwarta ta fara jin fargaba. Fargaban barin duniya ba tare da ta tsinana wani abu kwakkwara ba.1

Daga baya ta samu arzikin wani abinci a wani yasasshen kwano ta ci don kar yunwa tayi ajalinta. Tobacco ya shigo wannan karin ma sanye da burgujejen wando da riga sai ya dora hula mai malafa. Ta gane hakan dai kamar shigarsa kenen. Ya tsugunna a gabanta ya dafa kafadunta ya ce

” Baby girl..are you ready to talk?”

Hawaye ne suka fara zuba mata kamar ruwan fanfo. Wani takaicinta ya kama shi. Shi za a nuna wa taurin kai? Ya fito da pistol ya dana mata a makogoro. Kawai sai ta saki fitsari saboda tsoro.

” you have 2 hours ki bayyana kan ki da wadanda suka turo ki. Idan ba haka ba sai na sa bindigar nan na tarwatsa miki kwakwalwa. Su inna da baba da suka tsine miki sun huta nemanki! Tick..tock..” ya fita abunsa2

Wani tunani ya zo mata. Da alama fa anan za a kasheta a yar da mushenta. Ta yi ta tsinewa son kudinta da ya kawo ta halaka. Ta yanke hukuncin fada za tayi kawai. Wata zuciyar ta ce ma ta ko kin fada ko baki fada ba kashe ki zai yi.

Awa biyu ta kusa cika wani tsamurmuri ya shigo yana mata nuni da lokaci ya kusa. Ta ce

” ka ce da shi ya zo zan yi magana”

Ya shigo rai a bace ya ce

” ina saurarenki”

Zata tsaya kame kame ya tsinka mata mari. Zai kara ma ta kenen suka ji wani kara kamar tashin bomb. Saboda tsananin firgita bata son lokacin da ta fyalla a guje ba ta fada wani bayan drum. Wani ya shigo a firgice ya ce

“Oga we are raided..an zagaye mu”  

Ba su bi ta kan ta ba suka fita a guje. Bata jiyo komai sai karan bindigogi. Can bayan kamar minti talatin sai ta ji dif! Kamar daga sama ta ji aka doko kofar inda take ta ji an fara tafi taf taf. Wata murya ta ce

” fito matsoraciya Luba, kin ci kudinki”33

Ya fara kwantsama dariya hahaha. Ta fito tayi ido biyu da “Roller” anan ta tuna abunda ya faru wata daya daya wuce.

*****************************

Wani maneminta ne a kano da ya fara koya mata shan tabar wiwi ana ce masa Rabs. Dan yaro ne marar mafadi kamarta watarana suna aikin shaye shayensu yace ma ta.

” wani oga na ne ya ce na nema masa yarinya ta ajiyewa a gaban mota ba wacce ta fadomin a rai sai ke.”

Ta daga kai ta kalle shi idonta luhu luhu ta ce

STORY CONTINUES BELOW

” Ni? Kai ko kishina ba ka yi?

Ya yamutsa fuska yace

” Ke dalla malama ana maganar samun kudi wa ke ta kishi? Uwata ta ce ke?”

Ta share shi ta san ya fara tafiya kan ba daya ba. Ya karasa da

” bari in rabu da ke idan kin ji jakar ta miki sakwa sakwa kya neme ni”

Ba a wani dade ba ta neme shi kuwa ya dauketa ya kaita Abuja ya hada ta da Roller. Wani daniskan dan cinikin kwaya ne da ya kasa kamuwa. Ya shiga kashewa Luba kudi har ta ji ina ma tun farko a Abuja take. Dama haka ‘yan Abuja suke holewa?

A wajen yawon shakatawarsu ne rananan ya ce ma ta

” Ni kuwa akwai wani aiki dana ke so ki min”

Ta ce “ina saurarenka”

” Ina da wani abojin hamayya da a ke kira tobacco. Ko da yake gaskiya da aminina ne neman kudi ya sa muka yi baram baram. Harkar tamu dai duk ta kwaya ce.

A hankali tobacco ya zame ya fara production a karan kan sa. Yana fitar da wasu kwayoyin da shi ya hada da kuma syrup na shi na kan sa, ba karamar riba yake ci ba. Ya siye jami’an tsaro ya siye gwamnati.

Abinda har yanzu kowa bai sani ba shi ne ina ne tobacco ya gina empire din sa, plant din sa inda yake production yake kuma boye makudan kudade da yake tarawa. Don ba banki yake kaiwa ba gudun kar a kama shi.”

Luba ta katse shi ta ce

” Ni ban gane ba. Ta ina labarin nan ya shafeni?”

Yayi gajeran murmushi ya ce

” ina ga dai baki cika wata tara a cikin gyatumarki ba ko? Na ga kina da garaje”2

” Barin ciki na tayi” tace da shi a kufule ” ka ga karewar garaje kenen”5

Ya cigaba ba tare da ya tanka ta ba

” A halin da ake ciki yanzu Tobacco yana kan production din wani syrup na maye wanda in har aka sake ya shigo kasuwa to kashina ya bushe. Don mahaukacin kudin da tobacco zai yi zai iya sawa a kama ni a manta da labarina.

Abu daya kacal yake bukata. Wata hoda ce da ake kiranta DZT ba zan gaya miki ainihin sunanta ba saboda tsaro.

DZT ba a shigowa da ita saboda an sanya matakan tsaro masu tsanani. Idan har zai samu hodar nan ko da 5g ce to zai iya producing wannan syrup din iya adadin da tashi daya zai zama biloniya. Maganar da nake miki yanzu ni ina da DZT”

Ta kalle shi baki a washe ta ce

” To ai matsala ta kare sai kayi amfani da shi ka hada maganin kayi mahaukacin kudi”

Ya girgiza kai a hankali ya ce

” Luba DZT kawai gareni bani da formular din wannan syrup ban san da me da me ake hada shi ba. Kin ga DZT ba shi da amfani kenen.” Ta ce

” To kai da can menene dubararka”

Ya ce

” Ke ce zaki kaiwa tobacco DZT”

Ta kware da lemon da take sha ta ce “ni? Kai menene ribarka idan ka dauka ka ba shi? Ina ce abokin hamayyarka ne”

Ya ce

” An zo gurin. Ai shigo shigo ba zurfi za muyi ma sa. Mu kira shi mu ce muna da DzT tunda nema yake ruwa a jallo. A tsadance sai ki dauka ki kai ma sa. Daga nan sai muyi ma sa cunen yansanda. Na san ba zai fi awa ba zai fito kuma daga nan zai sa a kama ki. Mu kuma duk abunda ku ke muna da ido.

Idan ya sa aka daukeki ba shi da inda zai kai ki sai hideout din sa. Zai bi duk wata hanya don ki fada ma sa wanda ya turo ki. Kiyi kokari kar kiyi breaking. Mu kuma dama mun tura dan leken asiri, shi zai fada mana hanyar da kuka bi wacce za mu bi ku. Zamu gano hideout din. Sai mu mamaye shi.

Mu sace duk wasu takardu. Da formular da kudade. Ke kuma mu fito da ke. Wato dai za ki zame mana “bait ne”. Irin tsutsar nan da ake sawa a jikin qugiya a kama kifi..hahahaha”2

” kafin nan su kuma sun saka kaina gabas sun yanka sun zuba jinina a kokuna sun shanye. Kai kuma sai ka zo ka ceceni ko? ” Ta fada tana kalonsa a sakarce

Ya ce

” komai akan timing za a yi. Ke dai kar ki sake kiyi breaking.”

Ta dauki jakarta tana mai cewa

” waziri aku na saurari magana jarinka tun daga na daya har na uku. Lokacin tafiyata yayi” ta fara tafiya tana barin harabar gurin. Ya ce

” Ko da magana jarin tawa tana dauke da zunzurutun kudi har Naira miliyan 2?”

Ta juyo ta dawo ta zauna a kujera ta ce

” Ina jin ka Roller, kamar kana bani labari”2

Ya ce

” ki yi fata Allah ya rufa miki asiri irin rufin da yayi wa dogo mai gyada”

” Sama ‘ya’ya kasa ‘ya’ya ” ta ce da shi

********************************

Ta dawo daga tunaninta bayan ta yi ido biyu da Roller da yake tafa mata. Ta ce

” Duk ba wannan ba ina ladan aikina zan ware? Tun kafin ‘yansanda su zo su karasa ni”

Ya kyalkyace da dariya ya ce

” Ba ki fi ni sauri ba. Kudinki ai a akawun din ki suka kwana saboda raahin tabbas din rayuwarki. Kin ga gyatumi ya samu abun juyawa ko da kin sheka barzaku”1

Ta angaje shi ta wuce. Ya cillo mata mukullin mota da damin dari biyu ta cafe. Ya ce a tsaurare

” Ki bar gari. Kar ki ce ban gaya miki ba. Idan komai ya lafa zan zo in karbi motata.” Ya duba agogon hannunsa ya ce

” karfe 6 na hamma yanzu..Run don zaki dade baki ganni ba”

Cikin sauri suka nufi motar ta mata key ta leko ta taga ta ce

” Ina tobacco din?”

Yace

” Kanin uwarki ne?!! Yayi ta kan sa keme kiyi ta kan ki”4

Da haka ta bi su a baya suka fitar da ita kan titi. Sai yanzu ta amince babu wanda zai gano hideout din tobacco saboda tsananin kasurgumin dajin da ya je ya boye.

Ta hau kan titi ta dauki hanyar titin da zai kai ta  kaduna tana fyalla gudu. Lallai ta yarda dare daya Allah kan yi bature. Yau ga ta da zunzurutun kudi har naira miliyan 2 cas! Lallai su Hindu da Rukky za su sha labarai. Ta san cikin daya biyu ko ta riga su isa ko su riga ta. Ta san ma zasu riga ta.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE