Makaranta duniya chapter 26

Makaranta duniyA

           Chapter26

‘Kana ta jira ko Imam? Yi hakuri don Allah.’ A firgice ya daidaita ‘sahunsa, kunya ta rufe shi, ya shafo nan, ya goga can. ‘Ah…. Ai babu komai.’ Ita kanta kunya ce ta kamata, can jikin bango ta koma ta rabe, ya tada mashin yana fadin.
‘Ashe ki na nan, kudin ku na wajen Hamdiyya, sai mun dawo k0? Ta ce, “Allah ya tsare.’ Ya amsa yana hawan mashin, “Amin-Amin.’ Shi ma Imam ya hau, sannan ya waigo ya dube ta suka hada ido da hannunsa, yake mata alamar ta sauke ‘nikabinta, murmushi take yi tana make kafada.
Malam Sadiq ya ja suka tafi. Imam bai daina waige ba, tana daga masa hannu, shi kuma yana jaddada mata ta sauke nikabi, sai da ta ga za su sha kwana, sannan ta sauke, ka na taga yayi mata bye-bye shi ma, ta kada kai tana murmushi ta ce, “Allah Sarki lmamu na, kamar kar ka tafi.’ Ta koma cikin gida, ta dauko jaka ta hado kannanenta suka wuce makaranta.
sssssssss
ga shi Allah ya hada shi da ubangida mai yawan
alheri, ba’a, hada sati biyu ‘su wuce ba tare da Alhaji ya yi masu rabon kudi ba, kuma masu tsoka, shi ya sa Imam bai dogara da albashin sa kadai ba, shi wannan ma kacokan wani lokacin yake mika wa Mama ya. ce tayi duk abinda ya dace. Tabbas hankalinsu kwance yake.
Karatun Mudansir na tafiya daidai, duk wasu littafan da yake bukata da suka gagare shi siya a can baya, yanzu duk Yayansa ya siya masa, kamar wasa Imam ya yi sha’aWar ya yi kiwo har ya sa ayi masa keji.
Mama ta ce ga garejin mota babu komai ciki? Ya gyara kawai ya zuba kiwon sa. Nan da nan‘ya nemo masana kiwo suka ba shi shawarwari a sanya kofar (Net), watau raga, saboda a rinka bude masu kofa suna shan iska
Sannu a hankali abubuwa na kara budewa Imam.
‘ shan iska da rana, kuma dole a fasa tagogi guda biyu
saboda dare in ya yi an rufe kofar za su sha iska ta taga‘
Cikin kwana daya aka gyara wuri, aka fasa taga’ ta inda ya dace, aka sanya rodi dan kariya ka na aka buga.  manyan fitilu masu haske.
Sannan aka malalo diddigar katako saboda kashin su ya yi saukin sharewa, komai‘ na amfanin Wajen’cin su da shan su duk Imam ya siyo. Daga bisani aka kawo kajin turawa ‘yan sati hudu guda dari  Alhaj da Mama su kaita murna tamkar su aka kawo  ma kiwon.
Koda yaushe hankalinsu na kan kajin suna kula ” da su. k0 dama shi Alhaji‘ abinda ya karanta kenan ,, watau noma da kiwo. Amma duk da haka Imam ya _’ nemo Likitan .dabbobi yana kula da magungunan su da rigakafi. Cikin ikon Allah guda biyu kacal Suka yi wabi, casa’in da takwas suka zama dirka-dirka suna takawa da kyar, nan da nan ya bada cigiyar masu siye. Kudi  Naira na gugar Naira ribar dubu casa’in da biyar ya samu.
Bayan ya sake zuba wasu guda darin, sannan ya‘ zuba masu kwai guda hamsin a siton cikin gida. Mama; , ta kwashe kayan abincin ta mayar dakin da su ‘ Sulaiman suka tashi kafin bikinsa. Kiwon Imam ya yi tambari daga k0 ina ake zuwa siyan kwai da kajin.
Bikin saura wata guda, ya siyo sabon mashin roba-roba. Kowa na ta taya shi murna, ana ta sa masa albarka. Mudansir kuwa wuni ya yi shawagi akan mashin din, saboda murna.’ Bayan sallar Issha ya kaiwa gimbiyar, ita ma ta sa albarka, ta dafa mashin din cike  da fara’a. “Ba shakka lallai ango ba ya jin gari, soyayya dole
Ya tuntsire da dariya “Me ki ke nufi? Ta ce ‘Me ‘ kuwa? Ba sunan mashin din kenan ba? ‘Soyayya dole? Ta Ce, “Uhm… Ya ce, “To da wa? Ta yarfar da hannuta
ce. “Oho! Wata kila Kuma da Antina k0? Ya maka mata harara,‘ ya ja dogon tsaki.
“Da alama kina so ki haukata ni.” Ya wuce ya shige dakin da suke zama, ta biyo shi tana dariya “Akan me  xaka haukace? Bai zauna ba ya ce, “ldan ki ka ci- ‘gaba da ambato min wannan sunan!
Ta hade hamnayenta~ a wuri daya, ta ce “Sorry ‘ Sir! Soyayya dole ai sai ango da. amaryarsa masu yi.” Ya dan~ lumshe ido ya bude‘, ya yi murmushi ‘ya zauna. “Yana daya daga cikin abinda ya sa na’ ke kara son ki.’ ‘ Ta yi dan tagumi ta ‘ce “Me kenan? Ya ce, “K0 na yi ‘fushi, kin san kalaman da zaki sanyaya min zuciya, ina fatan kin tanade su da yawa su zama tsaraba ta ranar tarewa’.”
‘ Ta kauda kai tana murmushi, ya‘ girgiza kai cike da bege ya ce, “Kin san me? Zan kira Jamila in gaya mata na sayi mashin.” Ta dube shi ido cikin ido ta ce ‘ ‘ “‘Gaskiya ban yarda ba
“Saboda me? Ta kara tsuke fuska ta ce, “Ni dai . na ce ban yarda ba, ban yarda ta ji muryar ka ba.” Ya tintsire da dariya ya ce. “0h, ashe da ‘gangan ki ke ‘ tsokanata, to na gane ba za ki sake gwara kainar ba, yanzu gaya min. da meda me ki ka‘shirya na biki?
‘Ta ce “Ni Wallahi na ma rasa na yi, abubuwan fa sun jagule min, sati daya ya rage da nayi (Exams).” Ya ce “Taf Haka ne fa, to kin ga kar ki yi ‘wata wahala, ki bari sai ‘ bayan biki mu shirya walima lafiyayya. Ai dama ‘ka’idar walimar aure _kenan, sai amarya ,ta‘ tare, sunna ta tabbata, sannan ake gabatar da walima.” ‘
Ta yi shiru ba ta kalle shi ba, don ta gane nufin. ‘ Sai sunna ta tabbata, “Kin yi Shiru, ko ba ki yarda bane? Kai sunkuyé ta amsa “Ni na isa, ai sauki ka nema min. Allah ya kai mu lafiya.’ Ya ce “Amin.” Ya duka ya leko fuskar ta, ta dan’ dube. shi, ya yamutsa fuska ya ce
“Menene? “Da aka yi me? “Ki na ta sunkuyar da kai kunyar me ki ke ji? ‘
Nan take ta dake ta wayance, “Kunya kuma,me aka yi na kunya? Ya yi mata zuru, yana murmush‘. “Matar Liman kenan, akwai wayau, banda abin ki amarya, ai dole ta tare idan an daura, meye sabo da zai zama abin kunya? Ta watso masa harara, shikuwa dariya yaké yana tsokanarta.
Sauran sati biyu biki. Inna Mairo da ‘ya‘yanta suka zo, Akai kaya. Mutum hudu ma sun sami zuwa daga unguwar Shanu, akwatunan Imam Set na yayi, ne kaya makare har Sai da aka zuba takalma da jaka cikin (Ghana Most Go). ‘
Da yamma suka hadu da matan makwabta suka kai kayan. Can masun iske mu_tane ‘yan tarbar kaya,- aka gabatar da komai cikin murna da annashuwa.su masun dawo da alheri mai yawa na tukuici, abubuwan motsa baki. . ‘
A ranar ce Mai-gidan Imam ya kira shi ofishinsa, ya damka masa ta sa gudunmawar Naira dubu hamsin, haka Imam ya saki baki yana mamaki, saboda baiyi – zaton zai sami hakan ba. Ya yi ta godiya kamar ba zai daina ba. ‘
Can bangaren su Malam Sadiq ya komasuka kebe,~ ya nuna masa kudi, ya sa albarka, sannan ya gaya masa shi ma dubu hamsin din ya ba shi yanzu, cike da farin—ciki ya dawo gida ya nuna wa su Alhaji. Kai wannan bawan Allah Mutum ne, sam abin sa bai tsole masa ido ba. .
‘ Nan ya bar kudin wajen Alhaji, ya ce idan Malam Sadiq’ya yanke sadakin, sai a biya da Su. Malam Sadiq na zuwa da daddare. Alhaji ya yi masa maganar sadaki. take ya ce sadaki dubu talatin ne, kuma shi da kan sa zai biya. Alhaji ya rasa me zai ce.
Wannan kyauta da kari, babu mai yinta sai Allah, don haka ya fara yiwa Allah godiya kana, kafin ya kwarara ta ga Malam Sadiq, daga nan ya fito ya shaida wa Mama da Inna Mairo, duk suka sawo lullubi suka shigo falon, suka yi wa Malam Sadiq godiya.
Shirye-shirye suka ci—gaba babu kama hannun yaro, dinkuna kala goma ya yi na angwanci, ya yi wa Mudansir kala biyar, haka Mama da Alhaji kowannan su da kala biyar-biyar ya tashi, gaba daya gidan an gyara shi, an zuba masa fenti. Dakin tsaf!
Gwanin sha’awa, tun ranar laraba Inna Mairo da su Raliya suka dawo aikin biki. Abin ka da mai kiwo, duk inda ka bi tashin kamshin suyar kaji ke tashi, yayin da ‘yan danki ke ta aikin gyara dakin amarya, tun daga ranar ake ta burosh da su. ‘
Ranar juma’a da’daddare Sulaiman da iyalinsa kaf Suka iso ko kafin su shiga cikin gidan alamu sun tabbatar wa Sulaiman bikin zai‘ yi armashi, ba kamar yadda yake zato ba, shi ya sa ma bai gaiyaci kowa daga ‘ Bauchi ba, daga cikin abokansa‘, ko alama Imam bai yi zaton Jamila za.ta zo ba, wai sai ya ji har da ita.
Gida ‘ya hargitse da baki ana ta gaishe gaishe. . Kan sa tsaye ‘ya fado falon ya sha wagambari, daukar ido kawai take yi, kamshin turare na yi masa rakiya. Su Maryam (Ummi) suka taso suna masa kirari.
“Ango! Ango!! Bakinsa har kunne ya ce, “Mutanen Bauchi, to ya ku ’ke? “Kalau Wallahi! Ya ce “Kun zo shan biki kenan? Suka yi shewa, “Ah lallai wannan ango ba .ka da dama.‘ ‘ ” ‘
Ya matsa suka gaisa da Murja, ta yi masa fatan alheri, ya juya kan Jamila data ci tagumi tana kallonsa. Ya matsa, ya ture’hannunta ya ce, .“Mutuwa ‘aka yi? Ta tabe baki ta ce.
“Ina kallon ikon Allah ne, wai. za ka yi’aure? Ban ‘ yarda ba fa har yanzu. Mamaki na ke yi.‘ Ya saki baki
yana ‘yar dariya “Meye abin mamaki? Shi aure ai habo ne, zuwa kawai yake yi ko Inna? Ta ce ‘Sosai kuwa Baba na, da lokacinsa ya yi zai kwararo‘ da zarar Mutum ya yi wasa da shi, sai ya wuce ya barshi nan, yana cizon yatsa.‘
Jamila ta watso mata harara, “Ki daina habaici Inna, na san da ni ki ke yi, to menene idan na ce ba zan yi auran ba? Inna ta ce “Sai me kuwa, maras kunya, ki yi ta zama mana, ina ruwan Mairo.” imam ya karba Ah’ah ya isa Inna, kin gane bari inje mu gaisa da Yaya.‘
Ya tashi ya fice. Jamila na binsa da kallo, ita kanta tana jin Imam cikin zuciyarta, sai dai kwadayin abin duniya ya riga ya rufe mata ido, nan da nan Mama ta sa aka baibaye su da abinci, soyyayun kaji filet guda, . ga lému kala-kala. Shi kuwa Imam yana falon Alhaji.
Sulaiman na kallon ikon Allah, falon Alhaji tsaf  An. sake masa malalén kafet sabuwa, “Duk yadda akayi yaron nan sata yake masu a kamfanin, amma bai isa ya yi wannan facakar ba, yaushe ya fara aikin? Sulaiman ke ta sambatu, yana jan farar shinkafa miyar kaji, ba’a jima ba. Malam Sadiq ya iso suka gaisa da Suleiman.
Alhaji ya ce, “Ka gane shi kuwa? Ya ce “Ba Sulaiman bane mutanan Bauchi? Alhaji ya yi murmushi ya ce, ‘Shi ne.’ Ya sake mika masa hannu “An iso lafiya, ya aiki? “Lafiya lau Alhaji.’ Ya dube shi,Ai Kai ka gane shi? Ya‘ kada kai, ‘Ah’ah.’ Ya ce, “Haba dai da shi-fa muka je Bauchi neman aure, abin bai yiwu ba.’ Kunya ta rufe shi, take nan ya rasa natsuwarsa “Au …… Haba? Wallahi ban gane shi ba.’
Alhaji ya ce, ‘Da alama, ai shi ne surukin na Imam.” Ya wani yake baki, “Allah. Sarki… To Allah ya sanya albarka.‘ Duk suka ce amin har da angon.
sannan ya tashi ya fice cikin gida, ya dauko wa ‘su Alhaji
abincin su. Sulaiman dai duk a tsarge yake, ta ‘yan boko kawai yake yi, yana nuna abin kamar baiji kunya ba.
Washe gari ya ga kaji cike da gareji, ga wasu a sito, wai ma an yanka wasu kenan kuma aka ce masa duk na Imam ne, tun daga nan ya tsinke da al’amarin, har .yana lissafin akalla kajin da ke gareji kawai za su kai na dubu dari biyu, koda akan dubu daya da dari biyar aka siyar da su, balle ma ya tabbata sun fi haka, don manya ne ba’ na wasa ba. Har sha dayan rana bai tantance bayanin zuciyarsa ba.
‘Yan daurin aure suka fara taruwa kafin wani
lokaci kofar gidan ya cika fal Da jama’a. Ango
ya fito cikin manyan kaya farin yadi mai tsada, tamkar wata daran sha biyar. Jamila kanta‘ sai da ta ji gaban ta ya fadi har ta raya a ranta dama ace angon tane’. Yana tafe Muda na take masa baya, suka yi waje, ga abokan aikinsa nan  yana fitowa motar ubangidanSa na isowa Alhaji Sama’ila Garbati.
Bayan an gama gaishe—gaishe, motoci suka kwashe su zuwa Hayin  Rigasa, babban gidan su Malama Sadiq, inda aka daura auran akan sadaki dabu talatin. Kai bakin ango baya rufuwa, farin—cikin sa baya misaltuwa. ‘
Daga, ganin sa kadai za ka tabba‘tar da hakan. Shagali ya ci-gaba, musamman can bangaren amarya. Jamila kuwa zugun take, ita kanta ba ta san abinda ya hana ta sakewa ba, alhalin babu wanda- ya takura’mata’.
Bayan sallar Issha, aka kawo amarya dakinta, tunda aka ran’ga’da gudar farko, jikin Jamila ya karasa macewa,’fara’a take yi ko yake ne? Oho! Ga‘ ta nan dai. Ita kuwa Asma’u tuni ta shige dakinta da .kafar dama. tare da addu’a; “A’U ZU BI KALIMATUT—TAMMAT, WA MIN SHARRIL—MA HALAK! ‘ —
’ Tana zama gefen gadon ta, ta sake gocewa da kuka, kawayen ta suka ci~gaba da rarrashinta yayin da Hamdiyya da Amina ke ta kyakkyata dariya. Hamdiyya har da wakarta. “Ke ki ka ce ki na so, da ba ki ce ki na so ba, da ba’a ba ki shi ba! Wata lnnarsu ta maketa ta ce, ‘Ai saura ke, ‘yar kusun uwa, kya ji yadda akeji Nan suka kwana tareda ita.
Shi kuwa Imam sai dai, don an ce barci barawo, da sai muce- bai runtsa ba, saboda dokin amaryarsa. Washe gari biki ya ci-gaba, yayin da Su Jamila suke shirin komawa,’amma ban da Murja, don tana so ta wuce Kankiya ta dUbo mahaifiyarta.
Karfe goma sun gama shiri. Imam ke tambayar Jamila “Kin .kuwa shiga wajen amaryar tawa? Ta ce, “Na shiga mana.” Ya ce “Ban yarda ba, idan kuma har kin san ba kya kishi, to ki taso mu shiga tare.” “Ya aka yi ya san ban shiga ba? Ta tambayi kanta. Ya kamata in shiga, kar in bada kaina, “Taso mana kar Yaya ya ce ku fito.” ‘
Ta taso suka yi sallama dakin, babu kowa, sai amarya, duk wadanda suka kwana sun gudu gida sun bar ta, da kyar ta amsa, tana daga kuryar daki Jamila ta kare wa falon kallo, babu shakka iyayen Asma’u Sun yi kokari, kayan dakinta setin Italy na karfe, wanda ake ya yi lokacin, ga kayan kallon ta ga firij ga kuma (Show Glass) cike da kiristals, suka wuce cikin dakin. can ma ya yi kyau, ba kadan ba, “Har wani yanga ki ke yi…
…Sallamar ma ba za’a amsa mana ba? lnji Jamila. Shi kuwa kai tsaye gefen gadon ya zauna kusa da ita,_ yana fadin.“Ah’ah, kar ki takura mata, ke fa Yayarta ce ko amarya? Yana’ tamabaya’ yana dora hannun’sa’ bayan wuyanta, ta noke’ kai kanta ta rufe ta, ba ta ce komai ba, “Ba ki magana, to ga Jamila na kawo miki.”
Da sauri ta daga ido ta dube ta, suka kalli juna. Asma’u ta ce, “Ina kwana? Ta ce, “Lafiya, ya amarci.’ Imam ya amshe “Ai ba mu fara ba k0? Kamar zai cinye mata fuska. Jamila ta zura masu ido, “Wannan yarinya akwai kyau, kumasun dace Wallahi.”
Nan da nan ta rinka ji tamkar ta ce wa Dadin ta aure za ta yi. Ya sa Najeeb ya turo, sai dai abin tambayar shi ne anya zai yi dokin ta kamar haka, ‘bayan ta riga ta bada kan ta gare shi? Taf! Zance ya lalace!
Ganin yadda Imam ké -ta kara like wa amaryarsa, ya sa ta ce, “Bari inje in gama shiri.’ Asma’u ta ce, “Allah ya kiyaye hanya.’ Ta jaya da sauri‘ ta wuce. Imam na fadin “Sai na fito.” Bata amsa ba, ta yi gaba abin ta, ya bi’amaryarsa da _kallo kafin ya ce, “Saboda Allah kin kyauta kenan? .
Ta dago ido ta dube shi, “Da na’ yi mé? Ya ce, “Kin san babu kowa a dakin nan, maimakon ki latso ni a waya , ki ce inzo sai ki barni can ina hamma?.Ta yi dan murmushi ta kwantar da ido, “Don Allah ka tashi kar a – shigo a same ka.”
Ya dago fuskarta ya ce, “Kalle ni don Allah, kika ce me? Ki na ganin akwai mai kora ta anan? To k0 su waye su zo, gyaran murya kawai zan yi, ki ga yadda za su. rinka rige—rigen fita, suna karo da bango.” Dariya ta kubce mata, ta sadda kai tana yi.
Shi ma’yana taya ta, yana ci‘gaba da fadin “Ke ma‘kya yi dariya matar Liman, wa ya gaya miki ana korar Liman daga masallaci,inhar bai taka shari’a ba, bai’ yi ‘ komai ba? . ‘ . ‘ Ta kasa kallon sa, sai murzar yatsu take yi, ya zura mata ido, a hankali ya dora na ‘sa hannun, ya runtse yatsun ya aje numfashi a natse. Kunya ta kara rufe ta, ta runtse ido tana neman mafita yayin da kirjinta ya hau bugawa.
A dushe ta ji muryarsa ya kira ta Asma’u ta . dago ido da kyar ta dube shi kadan, ta sake maida kanta kasa. Ya sa yatsu biyu ya dago habar ta, “Dube ni Mana, please! ldanuwan nan tar-tar! Take kallonsa, sun jimasuna kallonjuna.
Shi kansa ya rasa me zai ce? Saboda tsaban kyan idanuWanta, gaba daya jikinsa ya mutu, bai san. lokacin da fuskarsa ke ta tafiya ba. Kiris! Ya rage ya. hade fuskokinsu. Mama ta kwala masa kira.
Gaba daya sukai firgita ya mike zumbur! Dan ji yayi kamar a gaban su Mama ke tsaye, ya fita da sauri yana amsawa, yana waigen ta. Ganin tana masa dariya, ‘ ya sa shi ma ya hau_ yi, yana nuna ta “Ai zan dawo.”Ta‘ ci-gaba da yi masa dariya tana kada kai, tana tsaye ‘ tsakar gida. Ya fito. “Maman mu kira ki ke yi?
Ta bishi da kallo “Au, ba shakka watau ,har ka shige dakin abin ka.” Ya fara dariya yana shafar kai,’; “Ah’ah Jamila na raka wajenta.” Ta ce, “Wace Jamilar  ban da wacce ke falona? Ya yamutsa fuska ya ce, “Fitowa ta yi ta bar ni Allah, to ma wai menene in na‘ ; shiga Mamanmu? ‘
‘ Ta ce “Ban sani ba, ka ga ni tambayar ka zan. yi ga kwayaye nan a kwaso a ‘dibar wa yaran nan ne su yi tsaraba? Ya ce “Wadanne yara? Ta ce ‘Yan Bauchi da za . ‘ su koma yanzu.” Ya ce, “Kai Maman mu shi ne sai kin tambaye ni, ki dibar masu mana, kiret nawa aka samu? ‘ ,
Ta‘ ce, “Takwas.” Ya ce “A raba a ba ‘kowa ‘ Mamanmu.” ‘Ta ce, “To shi kenan. Allah ya saka da ‘ ‘alheri.’ Ya ce  Amin.” Ya juya zai koma. Muda ya fado ‘ cikin gidan ya ce, “Yauwa Yaya, Baba na kira.” Ya ce,’ ‘ Wayyo! Mu je.” “Me aka yi Yaya? “Me kuwa.’ Na ji ka ce ‘ wayyo  Mu je na ce, ni ban son sharrinka.”
Ya sha gabansa, “Ah’ah Yaya na gafa da dakin. amarya,xaka ni kuma na kira ka ohk shi ya Sa kace wayyo?  Ya kawo masa mangari, ya tasa qeyarsa
yana masa dariya,_shi ma dariya yake yi, har ya isa wajen kiran Alhaji.
To karshen tika-Tika—Tik! Duk ta wayyo ta kare, tunda an watse, an bar masa amaryar sa, karfe tara ya nado tsarabar amarya ya nufi dakin, daga tagar dakin su yake ta jin gyaran murya, ya zura ma wajen ido. Muda ya hango tsaye yana masa dariya,-kada kai‘ ya yi yana dan murmushi, ya wuce dakin amaryarsa-har .uwar dakin ya shiga, yana sallama. Kamshi na masa marhabin mai sanyaya zuciya.
Tana zaune tsakiyar gado’, ta rufe jikinta ruf! Da ‘katon mayafi fari sol .Ya zuba mata ido yana murmushi, ko bai bude fuskarta ba, ya san amaryarsa ta yi kyau,
jin kadan ya aje leda gefe ya matsa gare ta. _ Shi ma ya hau shimfidar tare da fadin,
“Assalamu-alaiki ya ke wannan kyakkyawa.’ Murya ~ kasa-kasa ta amsa, “Wa’alaikassalam, ya kai wannan Liman mai albarka.”
Ya sauke numfashi ya matsa, daf da kunnanenta ya ce, .“A ban izini in ga fuskar amaryata, idanuwana sun zaku da son ganin ta.” Ta ce “Allah ya halasta maka, ka na iya budewa.” Ya sa hannu a natse ya bude ‘mayafin, ,sai ga nikabinta daure a fuskarta, ya saki baki‘dauke da ‘mamaki kafin yace“Taf Lallai ke kin cika matar Liman, shi kuma ya za’a yi da shi?
. Ta kara sadda kai tana ‘yar dariya, ‘Nakwance shi kenan? Ta ce “Na’am.” Ya nisa cike da fara‘a ya ce, ‘“Da alama fuskar nan mai tsada ce, ya kamata na bada sadakinta ta daban.”.‘ta kada’kai ta ce “Wanda ka bada tun farko Ya wadatar, bani bukatar ‘wani .na musamman, ka kwance kawai.“
Ya ce “Allah ya yi ma wannan amarya albarka.“ Ta amsa, yayin da angonta fara’arsata kam, yasa hannu yakwance nikabin, fuskarta ta bayyana. saidai ba ta dube Shi ba, ya sake sa yatsunsa ya dago habar
ta. Ya juyo ta gare shi, gaban sa ya tsitstsinke ya fadi, ya lumshe ido a hankali ya ce.
‘Subhanallah! ya bude a natse ya bi ta da kallo, kin yi kyau matar Liman.’ Tana murmushi ta ce, ‘Harna kai ka? Ya ce, ‘Ni kuma ina na ga kyan da zan kwatanta shi da na ki? Ta ce, ‘Ai watan da ke haske ba shi da kansa yake fada ba, masu kallon sa suke gane hakan, harsu. yabe shi, kar‘ ka manta ka cika dukkan sharuddan “imam Yusuf!
Wayyo dadi kashe shi. Ya runtse ido tamau Yana fadin. “Allah na gode maka da ka musanya min Asma’u ta zama mata a gare ni.’ Ya bude ido. suka bijuna da kallo, “Kin san me, babu ba ta lokaci dole mu harzanta
yin sallah, don mika godiya ga Allah da ya nuna mana wannan’ rana. sannan mu roke shi kariya daga dukkan sharri, k0 ba haka ba? ‘ –
Tace, ‘Haka ne, to taso.’ Ya sauka da sauri ya miko hannayensa biyu, ta kama ya sauko da ita suna musayar murmushi. Bayan sun kammala ya dube ta suna zaune bisa sallaya ya ce ‘Na san yau farin-ciki bai bar ki kin ci abinci ba, yunwa na nan na nukurkusarki, shi ya sa na yo miki wani dan guzuri.‘
‘ Ta sadda kai tana fadin ‘Ni a koshe na ke Mama da kanta ta kawo min abinci.’ Ya jawo ledar ya ce, ‘To ‘yar gidan Mama, sauranki na dan Maman k0? Yauwa matso sosai ki gani.‘ Ya kara matso da ita kusa da shi, sannan ya fiddo kunshin kaji ya baje, ga kwalayen madarar kwali masu sanyi,
. Ya baro cinya ya mika mata, ‘Ahah! Bude bakin
in sanya miki.‘ Ta rufe fuska tana ‘yar dariya ya ce ‘Kar ‘
ki min haka don Allah, so nake in ciyar da ke da kaina. Yi Bisimillah ki karba, wannan shi ne farin-ciki na farko da za ki fara sanya ni’ ‘
Da kyar ta bude fuskar, ta ce ‘Gaskiya ka rage. ya yi girma.”Ya aje ya yago kadan” ya ce. ‘To na rage-
karbi.” Ta bude baki ya sanya mata ya ce, ‘Yauwa, to saura nima a bani in ji yadda ake ji.’ Ta dake ta yago tsoka ta mika masa, ya runtse ido yana fadin ‘Uuhmm ……
Har ya cinye tana‘kallon sa, tana ‘yar dariya ya sake diba ya ba ta, a hankali ta saki jiki suna ta ciyar da juna. Jim kadan ya ce ‘In tambaye ki, za ki ba ni amsa? Ta ce. – ‘
“Allah ya sa na sani.’ Ya ce ‘Wankan tsarki za ki koya min.” Nan da”nan- ta kauda kai, “Kin ga babu maganar kunya anan, ai daga ni sai ke, ni lmamun ki, kuma angonki mai shirin sanin duk kan sirrinki, to menene don kin koya min wankan tsarki? Ta yi shiru. . Asma’u ta dube shi, ‘Koya min.”
Ta daure ta fara magana, “Abin bukata shi ne ruwa mai tsafta kuma wadatacce, ba kuma ina nufin cikin bokiti ba, bayan an yi tsarki, tare da niyya cikin zuciya, sai alwala ta biyo baya, amma ba za’a wanke kafafuwa ba a wannan lokacin, ruwan za’a diba a kwarara shi cikin kai, sannan a cuccuda har ko’ina ya wa‘datu da ruwa. Fatar kai da kowanne silin gashi.
Daga nan a wanke barin dama’zuwa guiwa, shi ma yana bukatar cudawa, don tabbatar da ruWa.ya isa ko’ina, hakan za’ayi ta bangaren hagu, sannan a gauraye ilahirin jiki da ruwa a wanke tas! Daga nan sai a dan matsa kadan daga wurin, ka na a wanke kafar dama,‘a koma ta hagu a wanke.
Shi kenan wanka ya kammala, kuma duk iri daya ne wankan tsarki, illa iyaka niyya ce ta bambanta su. Haka kuma alwalar da aka yi, za’a iya yin sallah da ita, muddin abubuwan da suke karya alwala ba su samu. ba, kafin _a gama Wankan.” Ya yi mata zuruu, ta sa aya, ka na ya ce “Sadakallahul-
Azeem! Ba shakka na sami Malama ta a gida, to Allah
‘ya yafe mana kurakuranmu.” Ta ce, “Amin.” Ya mika mata madara ya ce, “Jika makoshi ki ji sanyi.“
Ta kurba, ta suke fuska, ya yi ta ba ta tana sha, yana mata tambayoyi, tana ba shi amsa. Sai, da ta ce ta koshi. Tare suka yi hamdala, suka ci-gaba da hira har abubuwan da suka ci suka fada masu, suka zauna daidai, saboda a ka’idar kiwon_ lafiya, ba’a son ana gama cin abu a kwanta barci.
Kiran farko na sallar asuba a kunnan sa aka yi, domin ba barci yake yi ba, saboda tsabar farin-cikin irin kalar matar‘da Allah ya mallaka masa, tambayar kansa yake’ yi ‘anya kuwa ‘akwai wanda ya kai shi sa’a’? Ya lalubi fitila maras haske ya kunna, ka na ya dube ta tana ta barci, numfashin ta yana fita a natse.
. Kyakkyawar fuskarta‘na ta kara annuri, ya yi ta kallon ta baya ko kiftawa, sai da idanunsa suka kawo kwalla, sannan ya dawo hankalinsa, ya duka a’natse ya sumbaci goshinta. Ya kara gyara zaman dogon gashin kanta ya numfasa, ya ce a ransa “Kin kusan haukata ni  Da kyar’ya iya daUrewa ya bar shimfidar ya shiga bayi, ya yi wanka ya fito da alwalar Sa, a shimfidar sallaya ya yi nafilfili har alfijir ya keto, ya fito suka nufi masallaci su uku
Yadda ya bar ta, haka ya dawo ya same ta, ya
tsaya gaban gadon rungume da hannayénsa yana kallonta, “Wai lallai amarya ta gaji.” Ya zauna gefen ta
ya tallafo kuncinta biyu “ ke matar Liman.” Ta ‘ .
bude ido a hankali, ta bi shi da kallo har idon ta ya washe gaba daya,‘ kafin ya ce, “Ya kamata kiyi sallah, na san gajiya ce ta hana ki tashi k0?
Ta runtse ido tana kokarin tashi, amma ta kasa sai mutsu-mustu take yi “Ya dai? Hawaye ya gani yana gangara bisa kuncinta “Asma’u menene na ce? Ta ce, “Na kasa tashi.” ido waje ya ce, “Me yasa?.” Murya na rawa ta ce, “Ni ma ban sani ba.”
Ya ce, ‘An shiga uku Ya yaye bargo ya ciccibo ta, yana fadin “Sannu-Sannu asma.” Kai tsaye ya wuce da ita bayi, ya tara mata ruwan zafi, ya saka ta ciki, “Gasa jikin ki, za ki ji karfi.” Ta ce, “To, ka koma daki.” Ya yi dan murmushi, yaba ta wuri. ‘ ‘
Tsawon minti ashirin ta’fito da‘ kan ta, ya zuba mata ido ya sauke numfashi, kafar ta mike “Alhamdu— lilrlahi, ,gaba na sai faduwa yake, kar matar Liman ta zama gurguwa dare ,daya kawai Ta. banko masa harara’, ya matso ta yana‘ dariya “” Ta wuce shi ta yi shirin sallah, tana idarwa wa tasa’ kai bisa sallaya, wani dum ta ji cikin kanta ya dauki ciwo, ya sauko ya same ta “Ya za ki kwanta nan? Ta ce, “Jiri‘, kaina ciwo?’ Ya ce, “To ko har abin ya samu ne?
Ta kudundune fuska da hijabi, ta kyale shi, ya cicibo kanta ya dora bisa jikinsa, ya marairaice “Sannu ko, na san Liman ya yi laifi, amma ba laifin sa bane, matar Liman din’ ce ta hadu da yawa, shi ya sa Liman ya kasa barinta. Allah yayi maki albarka asmee, kin birge ni, ba’zan taba mantawa da wannan dare ba.”
Ta ce, “Don Allah ka daina fadi.” Ya ce “Dole in fadi, hasalima yanzu na fara son ki, ashe wancan na baya duk shirme ne, dubeni nan ki gani.” Ya juyo da fuskarta gare shi.
“Babu komai cikin zuciyata, sai tsabar son ki asmeena. Gaya min yadda ki ke ji game da ni? Ta ce “Daidai’da yadda _ka ke ji.” Ya ce “Ni fa kamar zan mutu na ke ji.” Ta ce, “Ni na ma mutun  dawowa nayi, don ba zan ‘iya barin ka ba.” Ya rasa me zai ce, kawai jawo ta ya yi ya rungume, bakinsa na fadin “I love you I love you    I love you
asmau

       Wohoho ana zuba soyayyah anan kut

www.Facebook.com/abdullahi.Ismail.salanke

Www.littafanhausane.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE