Makaranta duniya chapter 27
Makaranta duniya
Chapter27
Asha karatu lafiyaaaaaa
sati biyu murja tayi a kankiya ta dawo hankalinta
tashe, saboda halin rashin Iafiyar da ta iske Hajiya
Aliyaa a ciki. Duk ta rame ta lalalce, tsawon watanni shida da ta yi tana fama da rashin lafiyar, har yanzu hasashe likitoci suke yi, ba su gano takamaiman lalurar ta ba. Ta tabbata akwai matsalar rashi, domin Mansir ne kadai ke kula da ita daga dan albashin da yake samu a matsayin sa na Malamin furamare.
Wani abinda ke kara mata takaici, shi ne rashin samun hadin kan Sulaiman wajen taimaka masu da abinda ‘ya kamata. Kai, ta je ma ta gaishe su, ya kan zamar mata tashin hankali da zarar ta yi magana, zai balbale ta da .masifa, yana goranta mata irin kiyayyar da Hajiya Aliyaar ta nuna masa, saboda haka ba dole bane ta bukaci gaisuwar su, balle abin hannunsaba
Ta kan yi hakuri ta daure, saboda darajar aure, amma ta tabbata Sulaiman ya canza, don da can ba haka yake ba, jikin kowa ya yi sanyi, lokacin da take bada labarin‘ rashin lafiyar kowa ya yi’ mata addu’ar samun sauki. Amma koda wasa Alhaji bai yi marmarin ya je ba, ko ya ce wani ya wakilce shi. ba
Washe gari tana ta kimtsa kayanta a falon Mama. Imam ya yi sallama ya shigo gaishe su, “Sannu Anti!”“lmam an fitO? Ya zauna gefenta bisa kafet ya ce, “Wallahi kuwa, ina kwana ta amsa, “Lafiya lau, ya amarya? Ya‘ce “Kalau Anti, ki na ta shiri ne?
Ta ce, “lnsha-Allahu yau sai gida.” Ya ce, “To Allah ya kai ku lafiya.” Ta amsa da “Amin, Mamanmu.’ Ta shiga wanka. “Yauwa Imam, dama ina so in maka wata magana, ba kuma wata magana bace illa ta _ abinda ya faru tsakanin ka da Jamila ko kuma in ce Baban ta, ka yi hakuri Imam.
Na sani har ga Allah ‘ba’a kyauta maka ba, babu yadda zan yi in gyara wannan al’amari, don Jamila ta fi
jin maganar mahaifinta, saboda haka ka yi hakuri kuma
tabbas ka yi auran huce takaici, duk wanda ya dubi matar ka, dole ya sake kallonta ga shi daidai gwargwado ka sami abin yi; “
Ba kamar yadda-‘suké‘maka’kallon- talauci ya riga ya yi maka‘katutu ba, to Allah’ kenan, ka kara hakuri, sannu’a’ ‘hankali zasu gané kuskuransu, ka gane? A karshé’ “ina”rokonka daka yafema yar
uwanka, ka ji?
Ya gyara’ ‘zama yace, “Na ji jawabin ki. Na’yi, kuma gaskiya da farko na kullaci Yaya Sulaiman’da jamila amma’ daga baya -na sakarwa Allah”al‘amalrin’ sai‘ kuma‘ina “jin ‘shi ya sa ya musanya min da Asma’u, domin ’ban’ taba tunanin zan kalli wata ‘ya mace‘inSOta ba,sai_ gashi lokaci guda Asma‘u ta shiga ‘raina; karki damu’Anti,komai-yawuce lnsha Allahu
Ta ce, ‘Allah ya yi’ maku’albarka’,’ ya. kuma zaunar da ku lafiya‘, ya kade‘dukkan fitina.‘ Ya ce (“Amin Anti.” Yana shiru. Asma’u ta yi Sallama ta’shigo, tasha ado da wani les kalar samaniya, leashin ya amsheta, ga abin wuya‘caSE’
Kamar don ita aka kera‘ shi‘,‘ kamshi kawai take yi,‘nan take ta ‘kwashe’ hankalin lman,- ya zubo mata ido har ta tsugunna gaban‘Murja, ‘ina kwana Anti? Ta amsa ‘cike da fara’a, ta mike za ta’wuce‘dakin mama ina za ki?
“Zan gaida Mamanmune’Ya ce; “wanka’take yi,‘ da‘wo nan ki ‘jira ‘ta’Daga ciki ‘sukaji ‘ta amsa; “Ai na fito.‘ ‘Ta kwasa da sauri Shi ma yabi bayanta
“Matso nan ki manta da shi.” Ta rissina gabanta cike da fara’a ‘lna kwana Mamanmu? “Lafiya lau’Asma’u.” Ta: dafa kafadarta, “Ina fatan babu komai k0? Ta ce, ‘Babu komai Mamanmu.” ‘
Jikinsa duk ya mutu, ya zare_hannayensa daga‘ .aljihu,-ya tsuguna kusa da ita, shi ma ya gaida Mama ta”: amsa ta sanya masu albarka, ka na Asma’u ta tambayeta “Me za ku karya da shi Mamanmu? “Farfesun kan Sa.‘ Inji Imam. Mama ta ba shi amsa “‘Ai kai ne kan San. Asma’u ta tintsire da dariya. Maman na taya ta, ya zungure ta ya tashi yana fadin, “Za ki shigo, ki same ni ne, bari in je wajen Baba na.‘
Ya fice suna masa dariya, ka na ta dubeta “Kin; ga‘kamu kawai-za ki dama wa Babanku,.’sai ki shira ‘ wa Mijinki duk abinda yake so, kya sammana a ciki ko?Ta yi ‘yar dariya, “Ba dai a sammakau ba Mamanmu, bari in je kar rana ta yi.’ “To shi‘ kenan.” Ta wuce Mama; ta bi ta da kallo, har ta fice, ta kada kai farin-ciki fal a
Ran ta.
Bayan an gama‘karyawa. Murja ta kammala; Shiryawa, babu wanda bai yi mata alheri ba. Mudansir? ya kai ta tasha, a mashin din Imam, shi kuwa yana can like da amaryarsa, ba kasafai yake son fita ba, musamman asabar da lahadi. Da yake yau lahadi ce, haka ya wuni more angwancinsa. ‘
. Washe .gari litini duk suka shirya, ya fara ajé ta makaranta yin jarabawa, shi kuma ya wuce wajen aiki kamar yadda ya Saba. Haka suka chaba da jin. dadin su, suna tattalin juna yadda ya kamata.
Asma’u ta gama jarabawar, ta natsu dakin mijinta tana jiran sakamako. Mudansir kuwa kullum kamun kafa yake yi wajenta yana nuna mata da gaske yana rikon Hamdiyya. lta kuma tana, masa yanga, shi ya ‘ ‘ sa duk lokacin da suka kawo ziyara. Mudansir bai da sukuni, idan har yana gida, dan ‘lemon kwalban nan
wajibi ne su sha shi, don tsokana ma sai ta gan su za ta fara zakulezakulen abin kwalama.
Ta ce wai tana sha’awa, don ta kure shi, jikinsa na rawa zai je ya nemo shi, ita kan ta Hamdiyya ta fahimce shi, duk da cewar yarinya ce ‘yar shekara sha uku ajin farko a sakandire, sam ba ta sakin jiki in ta gan shi.
Rannan kawai duk suna tsakar gida, bayan sun‘gaida Mama za su wuce. Maman ta tsokano ta. ‘Ah na ga surukar tawa sai kara kyau take yi. Asma’u ina dai fatan za’a ba autan nawa?
Hamdiyya ta ruga daki sauran suka raka ta da daliya, yayin da Asma’u ke fadin, ‘Mamanmu ai har yanzu bai cika sharuddan ba.‘ Ta ce ‘ ‘Wane Sharadi kuma? Ai kuwa autana ya gama miki komai.’ Ta ce ‘Yaushe, ki na ji shekaran jiya na ce ya kawo min rake, amma ya dawo hannu rabbana.’ Ta yi ‘yar dariya ta ce, ‘Wannan wace irin suruka ce lashe money? Ta wuce suna ta dariya.
Tun daga ranar Hamdiyya ba ta son zuwa gidan, ita a dole kunya take’ji, idan kuwa aka yi sa’a ta zodin, to da nuku-nuku za ta shiga, haka ya sa duka’ bangaren biyu suka dauki zancan da gaske har Malam Sadiq ya kan tsokaneta.
Ya ce ta zo zai aike ta wajen Asma’u yana son ganin yadda take shagWabar karya, tana fadin ‘Kai don Allah ba ,ga Maryam nan ba.’ Yadda yake Yawan tsokanar ta, ya ci ace ta gane, amma saboda yarinta ta kasa ganewa.
Sakamakon jarabawar su ya fito daidai lokacin da (Admission) din Mudansir ya fito. Digirinsa zai je yi a birnin ilimi, a kuma cibiyai’ ilimin watau‘(A.B.U Zaria). Babu ba ta lokaci ita ma Imam ya nemar mata (Poly). ita ma ta zabi fannin (Micro Biology), ta kama karatun ta hankali kwance, domin Imam ya ‘gama kammala
mata dukkan abin bukata. Shi kuwa Mudansir a daran! da zai tafi’ Zariya. Ya kawo ma Asma’u sabuwar jakar makaranta katuwa.
Cike da: littafai da biruka ga maset da. fensira kala‘-kala,- yace ta ba Hamdiyya inji shi. Asma’u ta hangame baki ta ce, *Ah lallai abin da gaske ne.” Haka‘ Imam ya yi ta masa dariya yana tsokanarsa, “Yanzu kaji abinda ake ji k0? Har su ‘Mama ba’a bar su ba wajen tsokanar sa. ‘
Washe ‘gari ya isa Zariya, karatu kawai ya fara don shi ma ya riga‘ya gama komai na abubuwan da’
makaranta ke bukata, duk karshen sati yake zuwa, .kuma duk zuwan da’ zai yi wajibi ne ya kawo ma – Hamdiyya wani abu ya ba Asma’u ta kai mata, ko ta kira.waya Maryam ta zo_ ta amsar ‘mata. Hakika
Mudansir yana tattalin kansa wajan Hamdiyya, duk
da bata San soba, sosai ta ke jin Muda cikin ranta.
‘ K0 alama ba ta mantawa da shi, wani ‘lokaci ma ta kan so ta ga koda gilmawarsa sa, ya sa wani lokacin ta kan damu ta taso kannenta su yo ayari ta zo ta amshi abinda ya kawo mata da kanta. Ai kuwa ranar ta kawo wa Muda aikin zarya. kamar ango buzuzu. lol
‘ shekaru biyu kenan suka shude. Asma”u ‘na kokarin kammala karatu, domin har ta kawo karshen sanin makamin aikin da take yi a babban ,asitibitin (A.B.U) na nan garin Kaduna, a dakin, gwaje- gwaje. Amma shiru babu ‘bayanin kazantar daki, tun Imam na zura ido yana sa rai. ‘
Da zarar- yaji ta ce ba ta jin dadi, harya zo ya daina. ba- wai ya fidda rai bane, kawai fargaba’yake yi idan ya tuna labarin daya samu na tsawon shekarun da iyayensa suka kwashe kafin Allah ya ba su haihuwa ya sa ya bar al’amarinsa wajen Allah, kar damuwarsa ta fito fili, ya goga wa Asma’u ita ma ta sa
abin a ranta. Su kansu su Mama suna wannan fargabar, domin sun kosa su ga jikokinsu tun kafin mai kasancewa ta kasance masu, saboda haka suke ta addu’ar Allah ya nuna masu jikokinsu, ‘idan kuma zai ba su, ya ba su masu albarka.
Kwarai Imam ya bada karfi wajen noma da kiwon sa, domin ya kara inganta gonakin Alhaji wajen noma fiye da abinda ake nomawa a da, musamman gonar da ke Kauran Juli gona mai girman gaske. Rashin kudi ke sawa Alhajin ya ’ noma iya yadda zai iya. A halin yanzu har da raguna imam ya fara ajewa a can Kauran. juli
Inna ce ta ba shi shawarar ya hada da tumakai, bai yi musu ba, nan take ya ba ta kudin ta nemo masa lafiyayyu guda hudu, ita take kula masa da su, na shi kawai ya zo ya aje kudin abincin su.
Al’amarin ya karbi Imam, kafin shekara sun tara masa ‘ya‘ya sun zama garke guda. Shi kan sa Sulaiman . da ya zo ya yanzu kallo kawai ya rinka yi, yana mamaki, ai kuwa sai da lnna ta yi masa gori ta ce.
“Don Allah dubi yadda’yaro karami ya fi ka azanci, shekara da shekaru ka na aiki, amma ba ka kullawa kan ka komai ba, balle ka yi ma wani, sai karya, yau sabuwar mota, gobe sabuwar waya mai tsada. Jibi umarah Nan take ta fusata shi, maimakon ya yi tunanin kuskuran sa, ya gyara, sai ya ce ita ma umarar karya ce?
Ba ibada ake zuwa ba? Ta ce, “Ka yi ibada ‘tun ranar da ka je na farko, ba kuma laifi bane idan ka sake komawa, amma ka duba wanda yake da bukatar zuwa ka biya masa shi ma ya je, ba wai birgewa bane kamar yadda irin ku ‘yan karya suka dauka, me ake. da halinka, ya kamata ka natsu, ka yi tunani mana.
Tun daga ranar da Imam ya sami aiki, zuwa yau , ‘muke jin dadi, dubi wayar hannu na, shi ya siya min,
sam baya jira mu kai masa koken mu, da kansa yake cewa ga shi, kullum cikin albarka yake, dole al’amuransa su yi kyau!. Ba karamin fusata Sulaiman kalamanta suka yi ” ba, shi ya sa- ya shafe shekara bai waiwayo ta ba, wai shi ‘ a dole ya bar ta da Imam ya yi ta mata komai din, dadin ‘ abin kafin‘ Imam ya yi mata shi ya fara, kaIco! Ka ji wani tunani na rashin rabo! Al‘amura kuwa na taci—gaba da yi wa Imam kyau, kamar yadda Inna ta ce. A yau ‘su ka cika, (Form) din karbar bashi wanda Mai-gidan su ya saba bayarwa ga ma’aikatansa duk bayan shekaru biyu. kowa ya kan ‘rubuta iya yadda ‘ albashinsa zai iya biya a shekarun biyu, akwai wadanda‘ ake cire dubu biyar, duk wata, akwai masu dubu goma Naira dubu dari uku Imam ya rubuta cikin (Form) dinsa; ‘ ‘
. Bayan sati biyu Alhaji Sama’iIa Garbati ya sanya hannu, ya bada izinin fitar da kudaden’, a falo Imam ya sami Alhaji ya zauna suna shawara. ‘Baba maganar kudade nan‘ ne, da na gaya maka, to sun’samu, yanzu haka suna cikin (Account) dina.‘ Alhaji ya cé, ‘To” madalla. Allah ya yi masu albarka.‘ Ya ce, ‘Amin.’ Yanzu’ kai shawara‘r me ka yi akan Su?
Ya gyara zama ya ce “Dama tuntuni na ke shawarar na bunkasa wannan kiwon da na _ke yi, tunda AlhamduIiIIah, abin ya karbe ni, kuma ana samun alheri, shi ne na ce zan tambaye ka in ka amince,’cikin gonar ka ta Kauran Juli, ka ban wani yanki in gyara shi, afidda dakuna’koda biyu ne na irinqa kiwon kaji, k0 kuwa ya ka gani? ‘
Dauke‘ da fara’a ya ce, ‘Wannan tunani ya yi kyau Baba na, kaje‘ ka’ dauki masana su shata maka yadda ya kamata. Allah ya sanya wa abin albarka.‘ Shi “ma cike da murna ya amsa, ‘Amin Baba; na’ gode!
Da sauri ya mike ya tarar da Mama na daki, ya shaida mata yadda sukayi da Alhaji. Farin-Ciki ya’rufe
ta, ta daga hannnu sama ta yiwa Allah godiya kafin ta ce ‘Wannan al’amari ya yi kyau -lmamu, ni ma fatana Allah ya taimake ka gudanar da wannan al’amari ya kuma kare ka sharrin masharranta.’
“Amin! Amin!! Mamanmu.” Yana fita daga wajen, dakin sa ya nufa, ya fada bisa kujera a gajiye ya ce, “Ina uwar gidan ne? Ta fito daga uwardaka da sauri ta fesa adon Pakistan, bakin ta har’ kunne take fadin ‘Maraba da Liman.” Hannuu . kujerar ta ‘zauna hannayenta suka wuce bayan wuyansa.
. “Ya ofis? Ya ce ‘Kalau! Yanadubanta, ta sa hannu ta dauke hular kansa ta ce “Da alama ka gaji. mu je ka yi wanka ko ka-ji dadi, gab ake da kiran magariba.” Sosai ya kwanto jikinta, ya ce “Yes Mah.” Ta yi murmushi ta ce, “K0 sai na dauke ka ne? Ya fashe da dariya. “Daukan mana in za ki iya”. “Ka na ganin kamar ba zan iya bane? Ya ce, “Wane ni, ai inda ba kasa nan ake gardamar kokawa.”
Ta. yi wuf! Ta mike, “Tashi ka yi ‘ kallon ikon Allah.” Ya mike yana ta dariya “Bismillah! Ta cukuikuyo shi da gaske take yi, za ta yi masa daukar jarirai, haba yana sakar mata nauyinsa gaba daya suka zube kasa, tana fadin, “Wayyo Allah, na karya hannu.” ‘
‘ Sautin dariyarsa ya karu, “An gaya miki ni na wasa ne? Ke‘ ce dai ake dauka kamarkara, mike kuwa ki gani, duk da gajiyar jiki na cas Zan dauke ki.” Ya jawo hannunta, ta tashi, kafin ayi haka, ya sureta ya yi cikin daki Suna dariya. .
Ya dire ta bisa gado, ta yi tsaye hannayen ta bisa kafadar sa. “Kin san me? Ta ce, “Sai ka fadi ya ce, “Loan din nan ya samu, kuma Baba ya amince da shawarata.” Ta bude ido sosai “Don Allah?
“Wasa nake kenan.’ Ta kada kai “Ah’ha, gani
na ke kamar ba za su samu duka ba.” Ya ce “Ai wannan
ba halin Alhaji Sama’ila bane, shi dai bukatarsa ka tabbatar da ka karbi abinda albashin ka zai iya biya.‘
Ta ce “Uhm! Haka ne, don Baba ya ce da kudin Loan din ya sayi gidansa tun daga lokacin bai sake karba ba. Ya ce wannan karon zai karba, ya ce shi ma harkar wayoyi zai bude.” ,
Ta rungume shi tana fadin “To Allah ya taimake ku Ya sanya, maku albarka.” ‘Amin matar Liman Kamar kar ya rabu da ita, daurewa kawai ya yi ta raka shi bayi, ya yi wanka ya yi shirin‘fita masallaci.
Tamkar yadda Imam ya tsara shirinsa, haka aka; aiwatar da shi a Kauran Juli, wurin ya tsaru ya kuma yayi
kyau, kowa ya gani sai ya yaba, sau uku Alhaji yana zuwa yana ganin yadda aikin ke tafiya, sosai yake farin- ciki da jin dadin wannan azanci na Imam. Haka Mama da Inna Mairo wacce kullum ita ke dafo wa ma’aikatan abinci ta kawo masu da ruwan sha, kaji dubu daya aka . zuba tashi guda. .
Dari biyar masu kwai, dari biyar Gurolas, anan cikin kauyen Inna ta nemo masa natsatstsun matasa su biyar suna kula masa da wajen, duk wata yana biyan su. Kasuwanci ya bunkasa. Imam na ta ci-gaba da tasowa, yanzu abinda ya sa gaba, ya inganta kiwon raguna da tumakinsa, kamar yadda ya yi na kaji, koda yaushe mamaki yake ba mutane.
_ Musamman Jamila da Dadin ta, a hankali yanzu dai ta gama digirinta har ta yi nisa a bautar kasa, yayin da Najeeb da sauran masu hannu da shuni ke ci—gaba da yaudarar ta, ba ita kadai ba harsu Ummi sun hau layi, hudubar Dadinsu kullum su zama masu aji, don su sami mazaje masu azuzuwa. (Ayi dai mu gani)
lol
shekara guda kenan da gama karatun Mudansir da Asma’u, ita Asma’u ma har ta sami
aiki anan dakin gwaje-gwaje na asibitin (A.B.U) na garin Kaduna, watau inda ta yi aikin sanin makamar aiki, tana da kwazo kwarai, kuma shi ya sa suka dauke ta babu jayayya. ,
Allah kenan. Shi kuwa Mudansir bayan ya ga’ma bautar kasa, kai tsaye wajen sana’ar dan-uwansa ya koma ya zama mai ‘sa masa ido akan komai, duk abinda ya zartar ya yi daidai. Imam ba zai ce ah’ah ba. gaba daya suka hada kansu.
Babu mai jin kan su, yanzu abinda ya fi damun Mudansir, shi ne a ba shi dama ya rinka zuwan wajen Hamdiyya tunda shekarunta sun kai hakan, abinda yake ta ma kai kawo kenan wajan Asma’u. Ita kuwa fama take da kanta, ba ta ko sauraronsa. ,
” Da yamma ya dawo daga Kauran Juli kamar yadda ya saba, ‘ya yi sallama dakin yayansa, ta amsa ya shiga ya sameta‘ kwance bisa doguwar kujera. “Anti’wai ke ba za ki daina kwanciya’ba? Ta ce “Ina ruwanka? Ya ce “Oho, shegen karanbani na mana, ina fatan dai yau kin sami biyawa gidan kin isar da sako na?
Ta ce, “Ban je ba, daga asibiti gida kawai na yo.” Cikin damuwa ya ce, “Haba Antina wai ko ba kya so na aure ta ne? Ta ce “Tambaya ka ke, to ka yi min tsaurin ido in ‘Ta kasa karaswa saboda miyau da ya cika mata baki ya ce, “Wannan wace irin kazanta ce? Don Allah je ki zubar, mu yi magana.” Ta ’yi’ shuru ta kyale shi, saboda babu bakin maganar. “Ki tashi mana.” Ta yi tsaki, ta .ta tashi da kyar ta wuce bayi, ta zubar daga nan ta dauko Tom-Tom ta’sawo a bakin, ta fito.’ ‘ “Wai ke me yake damunki ki na tara miyau? Ta watso‘ masa harara ta ce, “Ban Sani ba.” Ta zauna yana fadin ‘“Allah ya’ ba ki hakUri matar Yaya, amma ya
To ba mu labari, hakurin me ka yi? Wai ma in
tambayeka, me ya sa ba za ka gaya ma Yayanka ba ya
“maganarba, ya gayama baban namu kullum fa suna tare wajen aiki.‘ Watau ni ka ‘raina! Ya yi yar dariya ‘Ba haka -; bane Antina, kuma in banda abinki, ai ke da Yayan duk ‘ daya ne, k0 ba haka ba? Ta. ce, ‘Ai ka iya dadin baki, gaskiya Yayanka zan gaya ma wa ya gaya wa Baba.‘ Ya yi mata jinjina yana fadin, ‘Allah ya bar ki .da da yayana Ta watso masa harara tace, ‘Ka ‘bi ni a hankali wallahi, ka ji na gaya ma.’ Ya yi dan murmushi ya ce, ‘An gama matar Yaya, ai biyayya daga yau har aba ni Hamdiyya Ta ce ‘Je ka, na ji.’. To na gode,” ya juya zai Wuce, ya sake dawowa ya ce.
.‘In tambaye ki Anti? Ta cé,”‘Me? “Wai don Allah me ya sa ki ke ta tara miyau ne? Ta dube shi jim, kafin ta ce, “wallahi ka fita ido na Muda? Ya yi ‘yar dariya ya ce ‘Ai ba wani abu bane, shi kansa Yayan na ji yana cewa bai gane miki bane kwanan nan, na ce to, ko……. .’….Ko za mu zama Baba ne? Allah kadai ya sani. nidai ayi min kokari a gaya ma Yayan sakona kar ciwon son Hamdiyya ya kashe ni.’ Ta yi jum, tana kallon
. Yayan na sa da ke tsaye bayansa tun dazu. ‘Kinji Anti? Don Allah.‘ Ya juya da sauri kiris! Ya rage ya gWabza ma Yayan na sa goshi. ‘ .
Ido waje ya shafo kai, ‘Ah Yaya sannu. da zuwa.’
‘ Ya bishi da kallo yana kokarin amsar jakar hannunsa. ’Yanzu na ke ba Anti labari, yau ba karamin ciniki aka yi ba, masu biki ne, masu otel ne, ‘yan sari ne! Yau kam an kwashi kaji da kwayaye! Ya ce “Ko? Baki har kunne
ya ce, “Allah Yayana, ai za ka duba tiranzakshon :dinka ta (Laptop) za ka ga kudaden da aka shigar banki Ya wuce ya zauna yana ‘yar dariya tare da kada kai “Ka yi kokari angon Hamdiyya, ka sa ran ka inuwa, muddin ina numfashi. Insha-Allahu ciwon son ta ba zaui kashe ka ba.” Ya kasa natsuwaw Ba …… Ba…….Ya katse shi, “Ba dai Hamdiyya .bace’jeka ,kawai ka ‘yi barcin ka kar ma kasake kula wannan matar, ina ma take da bakin magana? Abu cike miyau Ya kyalkyale da dariya wata uwar ‘harara suke sha. Dole ta sa shi ma Imam din ya, canja maganar da fadin, “Madam kenan.‘ Ta tashi fuu……tayi cikin daki, yana murmushi ya dubi Muda ya ce,‘ ‘Kama gaban ka; Muda Yace, Yanzu kuwa kar insha muciya.” Ya fice da-sauri yana kara kyakyatawa. ” ‘ . Shi kuwa yana yunkurawa ,dakin ya same ta zaune bisa kujera gaban-Madubi; ta tamke fuska, ya yi dan murmushi, ya nufigun ta ya tsaya bayan ta, .ka na ya dafo kafadunta kadan, ya zuba wa fuskar ta ido ta madubin. “Duba da kan ki, ki gani da kyau.,kyanki ya karu, fatar ki’ ta kara lukuilukui, koda yaushe bakin ki taf Yake da miyau har Mamanmu ta fara magana, Anya ba cikine dakeba
kenan burin da ya rage min a duniya, sai fatan gamawa . da lta lafiya. lye?. ‘ ‘ Ta kara runtse yatsunasa ta ce, ‘Wallahl ni ma sal yau na gwada da na ga ahin kara haukata yake……… Ya duko bayanta sosal ya katseta, “Me sakamakon ya nuna? Ta juya ldanuwan ta cé, ‘liman . ‘ zai zama Baba Gaba daya ya zube gulwa biyu gabanta‘ ya daga hannu sama tsarkl ya kadaita gare ka. ~ – ‘ Ya Ubangljln kowa da komal! Godlya maramisaltuwa na ke a garaka Ya mal badawa mal hanawa, -bukata ta lta ce Ya Allah ka yl wa ablnda ka clkln Asma’u albarka. Allah ka raba mu laflya, ka kuma bata laflya har izuwa lokacin DA zata haihun Da saurl ta runguma shi tana fadin. ‘Amln ‘ ‘ lmamuna Ya jima ya na sarrafa ta yadda yaka so. yana nuna mata farin-clkln da yaka clkl. bai flto ba sal da aka klra magarlba, ya yo alwal ya nufl masallacl, can ma godiya ya rlnka ylwa Allah tare da addu‘ar Allah ya ylwa ablnda ke clkln albarka. ‘ (Wannan addu’a tana da kyau kuma haka aka» a rlnka yl wa yaro tun yana clkl, ba sal an halfo shiba. Fa’ldar tana da yawa kwaral da gaske. Allah ya bamu dacewa, amln). Suna dawowa masallacl. sun Jero shl da Alhajln ‘ yake ce masa, “Sal murna ka ke ta yl Baba na fuskarka ta clka da annurl, koda yake na nan dalilin, domin Muda ya kawo mana labarl dazu mal dadi cewa ta tabbata yanxu na qara tabbatar da zancan Muda gankiya ne, na fadin gasklya? ‘ ‘Fara’ar sa ta karu, ‘Haka ne baba, ni ma na dawo dazu take gaya min da tayo gwaji a can asibltl.” Yayi ‘Alhamdulillahl! Har sau uku “Allah ya yi masu albarka ita da abinda‘ ke clklnta, kuma ya sauketa lafiya.’ Ya ce, “Amln Baba.’ Ya dan’ nuna
‘lna so ka sani, matar ka na bukatar kulawa fiye da wanda take samu’a baya, ka gane? ‘
Ya amsa, “Na gane Baba kuma dama akwai. magana akan Muda na ke so mu yi.’ “Ta me? Ya ce ‘Shifa so yake a ba shi dama .Ya fara zuwa ‘wajen Hamdiyya.’ Ya kada kai ya ce, ‘Ah’ah Baba na, Hamdiyya yarinya ce, ba yanzu ta shiga (ss1) ba?
Ya ce, “Eh ‘Matsalar dai ace , Malam Sadiq ba ya so yarinya na tadi ba tare da ta mallaki hankalinta ba, ni da shi mun sha yin wannan maganar tun kafin a san Muda na son Hamdiyya kuma gaskiya ne, duk da dai ba haramun bane, ko Yayan ku Sulaiman.
Murja na karama ya fara son ta, kuma yana zuwa wajen ta, amma ka san kowa da ra’ayin sa, na san Malam Sadiq ba zai ce ah’ah ba, muddin na yi masa magana. Amma me zai sa shi ba zai hakura ba, ta dan kara cirawa gaba, kamar yadda aka’ yi na ka?.
Ya langwabe wuya ya ce, ‘Ka san so Baba, don Allah a taimaka masa koda sau biyu a sati ya rinka ganin ta.” Ya numfasa daidai kofar shiga falonsa ya ce, “ba komai, lnsha— Allah za mu yi maganar in yazo.” “Mun gode Baba.” lnji Imam.
Ya bude masa kofar ya shiga, shi ma ya bi bayansa,’ kawai ganin Mudansir din suka yi ya fado. “Sannu Baba na! Yayana ya aka‘yl? Ya ce “Na me? Ya ce, “Ah’ah,_ ina nufin kun dawo? Ya ce, “Mun dawo me ya hana ka zuwa masallaci?
Yace, “No, a maSallacin bakin titi na yi sallah, daga nan na siyo ricasg kad.’ Ya ce ‘Ok’, na zaci ,maganar nan ka ke tu’ni akan ta.’ ‘Wace magana kenan Yaya? Ya ‘ce, “Ka ji dan raini wayau ko Baba! Yana dariya ya ai, ‘Wannan kuma tsakanin ku ne, ba dai tadi ya kosa ya fara zuwa ba? Allah ya kawo Baban nasua, zan masa magana‘
Ya saki baki yana kallonsu, “Lah Baba har ka ba ni kunya Wallahl! Oh nI ‘dan nan Muda da zuwa tadi
Yayansa ya kawo masa mangari suka yi cikin gida da
gudu, suka bar Baban su da dariya.
Ba’a jima ba Malam Sadiq ya iso, kamar yadda ya saba, ba su yi nisa da‘ cin abincin ba. Alhaji ya kwashe bukatar Mudansir ya gaya masa, ‘yar dariya ya yi ya ce, ‘Hamdiyya ai taka ce Alhaji a yau ka daura mata aure, babu abinda zan ce “saidai in taya su da addu’a”. Alhaji ya yi farin-ciki kwarai kafin ya ce, “Ba komai baka san wani abu ba, mun kusasamun aboki k0 amarya lnsha-Allahu.’
Malam Sadiq ya tsame hannu ya ce, “Kai don Allah? Take nan ya fede- masa biri har wutsiya. Malam Sadiq ya rasa inda zai sa farin~ciki da ya cika shi. Hamdala yake ta faman. yi tare da addu’a.
A wannan rana kowa ya shigo ya gansu, ya san akwai magana, ba su kadai ba tare da mata da ke cikin gida, tun daga ranar Asma’u ke shan tarairaya ta ko’ina, ta kara zama ‘yar gata, yayin da shi ma Mudansir’ya bare sabuwar soyayya a zuciyar Hamdiyyarsa. Kallon yarinya kawai ake yi mata, amma kalamanta sun wuce da sanin shekarunta, shi ya sa Mudansir ya tsunduma
tsundum! Ya nutse ba a hango shi.
~~~~~~~~~~~~~~ ‘
bayan watanni bakwai. Asma’u ta sauka lafiya
” asibitin da take aiki. Da namiji aka samu kamar . Imam ya yi kaki ya tofar.‘ Girmansa kuwa saida asibiti suka rike ‘shi na awa biyu ana masa gwajegwaje. don tabbatar da lafiyarsa lau. Cikin yardar Allah kalau yake, kowa ya dauke shi, sai ya Ce Masha-Allah. Kwana daya da yini suka yi a asibitin, aka sallamota. Nan ‘ta’ke Alhaji ya sanya masa suna Abubakal Sadiq, wannan suna da Alhaji ya zaba ya ba kowa
mamaki, kamar yadda suke farin-ciki da sunan. Amma
a hakikanin gaskiya shi Imam son kai ya so yi, watau sunan na sa Baban ya so sanyaWa. Koda yaushe gida cike’ yake ‘da ‘yan barka daga ko’ina ‘yan uwa da abokan arziki. ‘
A rana ta biyu Imam na ofis, wayarsa tayi ruri, bai dube ta ba, sai da ya kai aya a rubutun da yake ta sannan ya dauka. Jamila ce ke kiran, ‘ya danna 0k, ya dauka tare da sallama. Ta amsa, sannan ta ce, “Baban Bebi! Ya ce Ya son ran ki? ‘
Ta ce, “Ya kuwa, kamar ‘na kowa yake. To ya Bebin? Yace, ‘Yana nan yana ta ci-gaba da boxsin.” Ta yi dan murmushi “lye! Ya yi. Allah ya raya shi.” “Amin.” Ta ce, “Da yanzu ni ce na haifar maka shi k0?
Kalaman suka soki zuciyarsa, nan take ya dauke wuta ya rasa me zai ce. “Ba ka ce komai? Ya ce “Me ki ke so in ce? Ai wani baya haihuwar dan wani, koda na aure ki, ba za ki haife shi ba. Asma’u ce za ta haife shi.” “Me ka ké nufi? Ya ce, “Duk abinda ki ka fahimta.”
Ta dan nisa tace, “Ka na yawan son kai gwasile ni Yaya Imam, ka na ganin kamar ba na son ka ko? …… Da sauri_ ya amsa, “Me ya kawo wannan maganar? Please ba na son ji, 0k? Ya cire wayar a kunnansa, ya latsa, yana jan tsaki, ya yi kasake yana tunani, “Sakaryar yarinya kawai, ban san ma me ya sa na sake‘ ‘ ba ta lamba ta ba. Yarinya kullum ta kira ni sai ta yi min shirme? lta ba ta san tuntuni na shafe labarinta ta ba? Mts….
Ya sake jan dogon tsaki, ya koma kan aikinsa, yana yi yana sakin tsakin. Yinin nan guda bai daina jin haushi ba, kowa ya kira shi, ya yi masa barka daga Bauchi har da’shi kan sa Sulaiman.
Ranar_ suna raguna biyu firda-firda suka sha Wuka, kaji kuwa dama kullum cikin cin su ake. Wannan
Suna ya yi armashi kwarai da gaske, ko, Muda walima ta’
musamman ya shirya shida jama’arSa a gidan kaji, watau a Kauran Juli, an ci, an sha an bari, masu iya tafiya da shi masun tafi da shi. Murja ma ta zo, saboda tana so ta wuce Kankiya, turmin zani da riguna uku ta kawo
Mama ta karba ta sa albarka, rabon ta da gida, ’tun bikin Imam sai waya kawai. Washe gari ta wuce,
‘ da ta ‘so ta tsaya ta taya‘su sauran aiyukan, amma
babu hali, don ba ta so ta wuce kwana uku kamar
yadda Sulaiman ya ba ta, saboda haka ne ma ta yi
sallama gaba daya, daga can za ta wuce ta Kano. Bayan gida ya natsa. Mai-jego ta ci—gaba da
samun kula ita da Bebinta, koma shalele Abubakar ‘ :Sadiq. Da zarar takwaran na sa ya zo cin abinci, wajibi _- _ne ta kawo masa shi, sai zai koma‘ a maida shi, a
‘hankali ta’yi arba’in ka na ta koma aiki. Hankalinsu
. kwance. Al’amura na ta kara yaduwa cikin farin-ciki.
BAYAN SHEKARU GOMA SHA DAYA!
kan hanyar filin jirgin sama Mando Kaduna anan tafkeken ofishin Alhaji Imam yake, wanda
barorin sa suka cika gari dauke da sunan (Imam Farms Head Office Airport Road Mando Kaduna). Wannan kamfanin ya yi fice wajen noma da kiWo nau’i daban—daban na dabbobingida. _
Ta bangaren noma kuwa, babu abinda ba su nomawa, tun daga akan hatsi zuwa . kayan lambu, musamman timatir da albasa, manyan kamfanonin ‘ sarrafa timatir duk abokan huldar su ne.
Ta bangaren nama kuwa, kusan babu otel din da ba sa kai wa kaji a jihohin arewa har da Abuja. Shekaru biyu da suka wuce.
Tsohon ubangidansa, watau Alhaji Sama’ila Garbati ya shawarce shi da ya dan taba irin harkokinsu na dako, tunda shi ma ana kai masa kayayyaki wurare daban—daban har kudancin kasar nan,. musamman shanu da jar masara kuma anan kamfanin yake daukar hayar motoci. .
‘ Kwarai ya yarda da wannan shawarar, saboda haka ya fara da siyen tireloli biyu, suna masa hidima, a halin yanzu yana da tirelilo shida na shi na kansa, har shi ma ana zuwa a biya kudi, ya tura motocinsa dako. Masha-Allah! Muna iya cewa Imam ya kama kasa kwarai da gaske, idan muka dubi gidajen da ya gina guda biyu a lokaci daya. Manyan benaye hawa daidai irin na zamani a jere suke.
Katanga kadai‘ta raba su, kowanne da get din sa, suna daya daga cikin- gine—gine masu kyau a (Governor: Road). Halas-Malak ya mallaka wa Mudansir daya, suka tare a lokaci daya da iyalansu.
A ranar Mama ta sa aka fasa kofa a tsakanin su, wacce za ta rinka sada su’ da juna, ba sai an fita babban get ba. Shikansa Mudahsir katon (Shopping Mall) gare shi. Yayan na sa ya taimaka masa shagon ya cika da kaya ‘yan waje, shi ma kula masa ake yi da shi, saboda ya saba da zama tare da Yayansa, shi ma Imam baya son kowa kusa da shi, irin dan-uwansa, shi ya sa har
yanzu shi ne Manajansa. ‘ Can bangaren gidansu na gado kuwa, duk wanda ya kalle shi zai yi‘zaton buge shi aka yi aka sake sabo, babu abinda babu na jin dadin rayuwa, masu aiki mata biyu ke kula da abinci da hidimar gidan, ga kuma ‘ mai wanki da guga.
Garejin da aka kwashe kaji, aka maida shi yadda yake da, yanzu wata lafiyayyar Jeep ce a ciki, wacce Alhaji ke shiga idan suna son ziyara, direbansu yana nan dare da rana, yana jiran umarninsu.
Uhm …… ! Duniya mai yayi. Kuma ga ta babbar makaranta wacce take koyawa kowa darasi. Ga kowa ga shi a yau Allah kadai ya san adadin jama’ar da ke cin abinci karkashin Alhaji Imam. ‘
Hatta Inna Mairo ta jima da gano Ka’aba. Ga karamci da kyauta, kuma yana daya daga cikin masu . riga-rigen zuba dukiyarsa wajén daukaka kalmar Allah. Daga ance ina na Allha? Imam baya bata lokaci sai dai in bai sami labari ba.
Yau juma’a masallacin Sultan Bello ya cika makil! Da masoya Manzon rahma (S.A.W). Kamar zai tsage, cikin mintocin da ba su fi sha biyar ba, aka sauko masallaci, can ya keto jama’a cikin fararen kaya tun daga sama har kasa, ya tako a natse zuwa inda ya aje motarsa ya bude ya shige.
Ya tada mota, ya kunna A.C ya ja ya yi gaba, bai fiye yawo da direba ba, idan ba doguwar tafiya zai yi ba, kamar yadda ya saba, duk juma’a idan har yana gari
yake kaiwa Ubangidansa Gaisuwa. Can ya nufa a halin yanzu, yana shiga harabar wajen duk ma’aikata suka taso, ya yi ta musabaha da su.
Murna suke ta yi, don sun san yau ranar samu ce. “Mai-gidan na ciki kuwa? Ya tambayi sakataransa, ya .tabbatar masa yana ciki,” shi ma yanzu ya dawo juma’a, ya wuce ya, tura kofa tare da sallama. Alhaji ya amsa, suka yi musabaha, ka na ya zauna suka gaisa, . “Alhaji Imam ya kasuwa? ; .
‘ Ya amsa, “Mun gode Allah.”‘Ya ce‘, “To madalla, Ah! Ban ga babban Manaja’ ba? Ya yi murmushi ya ce, “Muda? Ai yana can Jidda sun tafi kilik din Baba na ido,- amma gobe za su dawo lnsha—Allahu.” ‘
Ya ce, “Allah ya kai mu, amma idon da sauki k0? Ya amsa “Ah Alhamdulillahi, tuni-a aka yi aikin’, babu matsala, don ma abin ya hade da shekaru ne,” Ya ce, “Gaskiya ne, to Allah ya sa a dace.”
‘Amin ’summa amin.” Sun jimasuna hirarsu ta ‘yan kasuwa, ka na suka yi sallama, ya fito ya bi ma’aikatansa da dubu uku-uku. Gaisuwar juma’a. Daga nan shagon da wayoyin surikinsa ya nufa; watau Malam Sadiq. Anan ya kai la’asar suna hira, tare suka yi ‘ sallama, sannan ya wuce gida.
Yara .bakwai ke harabar gidan kowanne dauke da jaka, suna kokarin shiga wata karamar’ mota Nissan wacce aka rubuta (School Bus) a jikinta gaba daya suka nuti inda yake fakin, kananan cikin su na fadin,‘Abba oyoyo! A cikin su hudu ne na shi, uku kuma na Mudansir. . ‘ .
Yayin da Babban Yaya Sadiq (Khalifa) yake makarantar kwana ta Albani da ke Zariya. Kenan jumlar ‘ya‘yansa biyar ne, sai na shida da ke shirin zuwa nan da‘wata biyar, uku daga cikin su mata ne.’Suwaiba (Husna) Asiya (Yusrah) sai Anisa.
Dan karamin su shi ne magajin Alhaji Abdul. Rasheed. (Babangida) Mudansir kuwa mata ne 2am Kyawawa, akwai Hauwa, A’isha da Khadija,’su ne ayarin da suka yayyame Alhaji Imam, Husna ce kawai ke tSaye tana masu ’dariya. Ya fito da sauri “Kai sai ina haka? Gaba daya suka amsa, “Hadda.” Ya ce, “Wuu! To maza a hanzarta, kar a makara.” Babangida ya ce sai an daga» shi sama.
Haka ya bisu daidai yana dagawa yana fadin, wanda ya fi nauyi, bayan- ya gama ya’ hada su wajen ‘ motarsu, direba ya gaida shi, ya amSa yana saka kananan cikin mota. Husna ta shiga, karshe ya bubbuga kafadarta ya ce; ’ –
” “A kula da su Yaya Husna! Tana murmushi tace?,“To Abba.” Yana tsaye suka bar harabar gidan suna ta daga masa hanhu. Muryoyin su na tashi, babu maijin wani, ya kada kai’yana murmushi, ya juya ya nufi cikin gida.
Uwargida ta taso ta tarbe shi, “Liman! Hannu biyu ta tallafi kuncinsa, “Matar Liman, to ya Bebina? Ta ce, “Kalau yake, ai ina daga sama ina hango ka da ba
taliyar ka.” .
Ya ce, Baba na ya jawo min aikin, ina Hamdiyya gwauruwa? Ta yi ‘yar dariya, “Har da kai? Zan kuwa bata labari, yanzu nan ta koma, ta san ka kusa shigowa.” Ya dan bude ido “K0? Dama ta yi zaman ta, gida shiru‘ ai babu dadi, ga yaran ba sa nan.”
Ta ce, “Kyale Hamdiyyar nan, mu je ka ci abinci.‘ Ya sumbaci kuncinta ya ce, “Mu je matar Liman. Suka jera zuwa tebur, ya~zauna ta rage masa babbar riga da hular sa. ‘
Ta aje gefe ta‘ ‘zuba masa abubuwan da ta tanadar masa, yana ci ,tana taya shi hira, har ya kare, ta kwashe kayansa suka haye Sama. Wanka‘ya fara yi, ya
sanya jallabiya maras hannu ya fito falon saman, ya zauna da jarida yana karantawa.
A nan ta same shi ta zauna gefen sa, “Liman Ya
aje jarida ya dube ta, “Ya aka yi Maman Bebi? Cikin damuwa ta ce, “Wai ya maganar Yaya Sulaiman ne? Ban ji ka yi Wani motSi ba har’yanzu, ga shi gobe in Allah ya yarda Baba zai dawo.’ Ya dube ta .da kyau, ya ce. , ‘ “Ba wai ba na tunanin maganar bane, sai dai ina ganin yanzu ne ya ‘kamata a nuna masa kuskuransa, ai shi kan sa ya san ba shi da idon da zai kalle mu, shi ya sa ya makale a can. Ba don ha’ka ba, me zai’sa ka ,rasa aiki shekara uku babu wanda ya sani? Ciwo ya kama ka, ka yi shiru, ai kin san al’amarin babu gaskiya a ciki, shi yasa a ,koda yaushe ake son bawa ya aikata alheri.‘ ‘ ‘
.Ta numfasa kafin ta ce, “Gaskiya ka fadi, amma umarnin Baba yana da kyau ayi masa biyayya.’ Ya ce, ‘Ke ba don Baban ba, wa ki ke zaton zai kalle shi? K0 Inna ai kin ji abinda ta fadi! Kawai ‘hannun ka baya rubewa ne, ka jefar da shi.”
. Ta ce, “A dai duba limamin Mu Ya dan kada kai, dauke da damuwa ya ce, “Ba nan gizo ke sakar ba asma,u kuma ban ki ta ki ba, ba karamar wahala za’a sha ba, kafin a samu tarbiyar yaran nan ta dawo daidai, ki na ji. ranar da Anti ta yi waya, cewa ta yi Jamila na Lagos.
Me take yi a Lagos? lta ma ba ta sani ba, me zaisa Yaya ya tara ‘ya‘ya har ‘uku ya kasa aurar da su? Kawai ya dorawa kansa rayuwar‘karya, kuma a kanta ya dora yaran, ba sa shakkar kowa, su dai burinsu kudi, ga shi nan ba su ga‘tsuntsu, ba su ga tarko. .
. Aikin ofis din da ake ta ci wa buri, ya ki samuwa, balle mijin auran. .Gagarumin aiki za mu- jajibo wa
kanmu, ina mai tabbatar miki, sai ran kowa ya baci: kafin yaran nan su gyaru” ‘
Ta ce, “ldan har Allah zai taimaka su gyarun, ai an ci riba Yallabai, duk wani shan takaici mai wucewa ne, ku yi hakuri don Allah. Jamila fa shekaru talatin take ~ nema fa Ta daga hannu ta yi masa jinjinar sarakuna. Allah ya taimaki angon na
Dariya ta kwace masa, ya nuno ta ‘yana fadin, “Ke ko? Ta yada kai gefen kafadarsa, “Ko kai fa Ya daga jaridarsa ya ci-gaba da karantawa ,jefi-jefi, suna taba hira, sallamar Hamdiyya suka tsinkaya daga kasa. Asma’u ta tashi ta fito barandar saman, “Ki hawo mana. Yayan bayananne? Sai ga shi tsaye shi ma ya ce da ita “Kar ki damu da ni, hawo abinki! –
Cike da kunya ta hawo ta same su tsaye, “Kadaici ya dame ki ko? Ta sadda kai saboda kunya, “Baiwar Allah,‘shigo abinki.”~’Ya wuce, duk suka biyo bayanta. A falon suka yada zango, “Gaskiya‘ba’a kyauta ba, next time in za’a koma, ni ne zan‘je~ ita ma ta dandana yadda ki.ke ji.” Kanta sunkuye tana ‘yar dariya.
Asma’u ta ba shi ams‘a, “Surukar ka ce dai.’ Ya ce, “Ni kanwa ta ce, ba ruwa na, itace ta ki sakin jikin ta, bari ma ki gani in ba ku wuri.’
Ya aje jarida ya sauka, suna fadin a dawo lafiya. Karamar mota ya dauka, ya nufi Tudun Wada wajen Mama. Can din ma maganar Sulaiman din su ke ta yi, watau suka ci-gaba daga inda suka tsaya da safe.
A hakikanin gaskiya shi baya so suzauna nan gidan tare da su Mama, ya fi so ya sayi Wani gida ya aje su ciki. Abinda ya aje wa ransa kenan, bai gaya ma kowa ba, dori kar a tsaya‘ ana gardama. Amma duk ranar da- ya saya, -zai tura a kwaso su kai tsaye a zube su can. ‘ Washe gari da‘karfe shida. Muda yayo masa waya ya shaida masa za su taso a wannan lokacin.
Lissafin ya nuna karfe sha biyu za su sauka Kaduna daga Kano, domin can za su fara sauka karfe sha biyu da kwata, kira ya shigo wayar Alhaji Imam, ya dauka cikin sauri, “Dan—uwa kun iso ne? Ya ce, ‘ “Mun iso Yayana.’ ‘To gani nan zuwa, ina kan hanya.”
‘To shi kenan.” Cikin minti biyar ya karasa filin jirgi. Suka nufo juna da sauri. Imam ya yi azama ya tarbi Alhaji, ya rungume, .“Baba Ya dan bubbuga kafadarsa cike da fara’a. ‘Baba Dan Baba! Suka dubi juna cike da murna, “An dawo lafiya? Ya jikin?‘ Ya ce, “Lafiya lau, Alhamdulillaihi.’ , –
Ya juya kan Muda, ‘Dogon Manaja! Ya mika masa hannu suka yi musabaha, “Yayana ya aiki? Na ka na nan na jiran ka.’ Ya ce, “Oh ni’ Muda! Amma dai zan huta kwana uku ko Yayana?-Ya ce, “Oho! Ga kwana bakwai ga kwana uku, goma kenan k0? Aiyuka na nan cike ofishin ka.’ Ya dafe goshi ‘ya ce “Oh ni dan nan!
Suka wuce suna masa dariya. Suna ta hirar asibiti da shawarwarin da Likita ya bayar har suka iso gida, cike yake da jikoki, duk suka rufe shi da murna. “Baba mai gilas oyoyo.” Ya tarkato su suka shige ta kofar falonsa. ilahirin kananan duk a jikinsa suka zauna, sai Khadija da ke manne da Baban ta, tana murnar ganinsa. ‘
Mama na zaune gefe tana fadin, “Don Allah kar ku karasa min tsohon miji! Asma’u da Hamdiyya suka gaishe shi. Ya amsa, duk ma’aikatan gidan suka shigo suka yi masa sannu da zuwa. Jibo mai wanki ya shigo da jakar Alhaji, yayin da Hamdiyya ta kawo masa ruwa da fura mai dan sanyi kadan. Ya budejaka ya dauko wa jikokinsa tsaraba kowanne ya danka masa a hannu, Wasu manyan cakulet ne masu kwakwa a ciki. ‘
Sannan ya raba masu wasu tika—tikan zomaye masu aiki da batir, ida
sai su zura da gudun tsiya, kamar zomayen gaske.
“Lallai Baba ka kawo aiki.” lnji Iman, ya ce, ‘Ai ka ga kowa ya kama-gabansa, ma sarara mu yi magana a natse.’ ‘ . Husna ta yatsina fuska ta ce, “Wai kai tsohon nan me ka ke nufi,ne? Ya dube ta cikin tsadadjen gilashin idonsa ya ce_“Au Suwaiba! Ai ni har na‘mance, da ke, wai dama ki na nan? Ta watso masa harara,: “Tafdijan! Lallai yau ba zaman lafiya.” Ta mike ta kama kugu, “Ka me? Duk suka fashe da dariya.
Ya ce “Wai zo nan babbar mata, farar mace: alkyabban mata, ku kauce ga Su’waiba ta nan, ta Abdul- Rasheed, wa ya kai wa za ya fi ki? Ta cunno baki ta nufu shi a hankaii, kowa na mata dariya. Mama ta ce. ‘ .
‘ “Har wata yanga ki ke yi? Ba da ke yake wa. kirari ba, da ni Suwaibar yake.” Mudansir’ya ce, ‘Banda kishi Mamanmu! Tana karasowa, ya sa hannu ya janyo ta, ta ‘zube jikinsa, ya rungumo ta yana dariya “Me aka yi-‘na fushi uwargida?
‘ Ta ce, “Ka na ta raba‘tsarab’a, ni ba ka ba ni‘ba, kashi na yi maka a gado? Ya kamahabarta ya ce “K0 kin yiy sai in wanke Suwaiba, ba wani abu bane, amma kin wani sami wuri kin harde kin ki kula ni, dan ruwan nan da fura duk ke ya kamataki kawo min, to shi kenan ina Fatan kinkawo min farfesun kifin? Ta ce, “Yana nan Madallah SuwaibaTo bari ki ga ta kitsarabar Yamatso da jaka ya bude, ya fiddo wasu warwarayen zinari guda biyu,’ya bude gidan ya dauko su, ya kamo hannunta‘, Kawo’ki gani da kai‘na ‘zan samiki.” .Bakinta har kunne,»ya zira mata su
‘Kai lallai mater-can da gaske, haka kowa ke ‘ fadi,” Mama Ce, “Yarinya kin ci’sadakin ki.” Ta ce, “Oho ai dai, na yi tsada ko Anti?,Suka kyalkyale da dariya “Husna Allah ya shirye ki
Ta sake duban Alhaji “Ka ji Baba mai gilas,‘ na gode. Allah ya bar mu tare.” Ya _ce, “Amin ‘yar matana ga kuma cakulet din nan akwali ki debi iya shanki.” Ta ce, “Ba ji.” Ta dunbuza ta yi waje tana tambayar sa, “A miko farfesun ne? Ya ce, “Zuwa anjima dai uwar gida.”
Ta fice tana fadin “Allah ya kai mu, ldan kuma na lallaba na cinye,‘ ka lashe! Ya dabe su ya ce, “Kun ji ‘yar ku k0? Saura suka yi dariya. Mama ta ba shi amsa, “Ah to ba wariyar launifafata ka ke’ nunawa ba? Ai gara . ta yi maka.’ Ya jawo fura yana motsawa ,“Kishl dai ki ke yi, na siyo’ mata warwaraye.’
Su Asma’u suka five, suna dariya, don su bar shi ya sha fufar sosai, ya kurba ya ce, “Anji min motsin aboki na Malam-Sadiq? Imam ya amsa, ‘Lafiya lau yake Baba, ya ce, jallabiyoyinsa na nan da rawanl, ka san Malamai sai da rawani.” Ya yi ‘yar dariya ya ce, “Gaskiya ne.’ .
_ ‘Ludayi uku ya sha na furar, ya aje ludayi ya dubi Imam, “Kai! Ban gane ba Ina maganar da muka yi kafin mu tafi? Imam ya matso kusa da shi ya zaUna ya ce, “Tana nan mana Baba.” Ya ce, “Kamar yaya? Na yi zaton zan dawo in same su an fara kai shi asibiti. Me ya faru? Ya ce, “Babu abinda ya faru Baba, kawai .dai …….
. Ya katse shi, haba Imam me ya sa ka ke so ka yi .wasa da zancan rashin lafiya? Ciwon koda ai ba wasa bane, rai bace ya ce, ba haka bane, Baba, amma ya .kamata a nuna wa Yaya Sulaiman kuskuransa …….
Kamar yaya? Oho Yanzu na gane -inda ka fuskanta Imam, ko ka ki, ko ka so Sulaiman jinin ku ne, idan ba ka taimake shi ba, wa zai taimaka shi?- To wai ma me ya yi. maka? Don ya hana ka auran Jamila? Da sauri ya amsa, “:Ko’ kadan Baba, hasalima tuntuni na amince wa raina Allah bai rubUta‘min Jamila za ta zama mata ta ba.” –
“To don me zan kullace shi‘akan wannan? “Abu laifukan Yaya Sulaiman zun sha gaban wadanda muka yi wayau mu ka sani, wadanda ba mu sanin ba ma. Inna ta sanar da mu kaf din su, babu abinda ta rufe, tun zamansa’kauye da yadda aka yi ka kwato shi, ko ba su hudu ka rike ba? Da shi da yayyen Anti uku, biyu sun mutu dayan kuwa yana nan da ransa, amma bai taba waiwayar ka ba, saboda wani dalilin na su, wanda Allah kadai ya san shi…. ‘
“Ya isa haka’lmam, abinda na ke soka gane, mai shirin aikata alheri baya tone—tone, kuma ita Mairo bai kamata ta zaunar da ku tana gaya ma ku abinda ba ku sani ba, sam ba ta kyautamin ba Ya gyara zama ya ce, “Baba, _shin Yaya Sulaiman ya aikata laifukan nan ko bai aikata ba? Ya ce “Ya aikata Imam.”
Ya ce “Tunda ya aikata, dole a nuna masa kuskuransa Baba, ai ana tauna tsakuwa ne dan a ba aya tsoro. .Ya kamata Yaya ya gane duk abinda da yake aikatawa muna sane, babu abinda bai maka ba, na cin kashi muka dauke kai.
Me zai sa yanzu daga an ce yana cikin wani hali,
mu tashi jiki na rawa, mu kai masa dauki? Kenan bai mana komai ba, kuma ba zai taba gane kuskuransa ba. Baba, ina da shiri na musamman akan Yaya sai dai ba yanzu bane, ina bukatar dan lokaci kankani.” , Alhaji ya numfasa, ya sassauta murya “Imam, ina so ka dubi abinda na ke maka nuni, ciwon koda aka ce yake damun dan-uwanka, yana bukatar taimakon gaggawa. Don Allah kar maganganun lnnar ku ya sa ka rinka kauda kai ga sakamakon alheri, ga wanda ya aikata maka sharri, banjin akwai abinda zai share wannan kyakkyawan aiki daga zuciyaraka. Saboda koyi ne ga Manzon Allah (S.A.W) ka fa yi tunani.”
Ya kara matso shi ya ce, “Wallahi Baba ina da niyyar taimakonsa, bari dai in gaya maka gaskiya, gidan
da za‘ su zauna shi na bada cigiya zan siya masa.” Ya ce‘, “Ah! Ba ga daki cikin gidan nan ba?
– Ya ce, “Babu daki Baba, ko ka mance ne? Wanda muka tashi cikinsa masu yi wa Mamanmu hidima ke cikinsa? Wannan ciki dayan kuwa ba‘ shi ne
aka fidda kofarsa waje ba. Su Jibo ke kwana ciki? To ina . ‘
dakin yake?
Mama ta cafe sai “Su Salamen su dawo waje na, ba matsala.” Ya kada kai “Ba fa zai yiwu-ba, don Allah ku yi hakuri da shawarata, na-tabbata ba za’a jima ba za’a Samu Insha~Allahu.” ‘Kwarai da gaske.” In ji Muda. Alhaji ya ce.
“Kai jama’a Baba na ya aka’yi ka koyi muSu? To shi kenan, amma don Allah ka kira Murja ta ba ka (Account Number) ka tura masu wani abu ko abinci su siya, shekara ‘uku babu aiki, ai ba lafiya bane.”
Ya ce, “Insha—Allahu za’a tura masu.” Ya dan kada kai ya ce, “Allah na gode maka da kasa ina da rai wannan abu ya faru.” “Me ya sa ka ce haka Baba? Ya ce, “Gani na yi da raina ma ku‘ na so ku yi wasa da zumunci da ace na mutu wannan abu ya faru, ai sai abinda Allah ya yi, ina zaton ba za ku kalli dan-uwanku ba.”
Gaba daya’ murmushi suka yi, “Baba kenan.” Imam ya ci-gaba “Ayi hakuri Baban mu,» burin mu kullum mu faranta maku.” Ya ce, “Allah ya yi maku albarka.” Suka amsa, “Amin._” Nan suka yi ta hira har azahar ta yi suka yi sallah, aka ci abincin rana, sannan suka wuce ofis tare da Muda. Matayensu kuwa sai gab da la’asar suka wuce, yara suka tafi lslamiyya.
Kwana goma kenan bayan yin waccan maganar, kullum Alhaji korafi yake yi, sai dai in ba su je gidan ba, koda Inna Mairo ta zo duba shi ma, haka ta sha fada a Wajensa.
Saboda labarin da ta ba su Imam ne, abinda ba su sani ba game da rayuwar Sulaiman. Sam Inna ba ta yi nadamar gaya masu ba, hasalima cewa ta yi da za ta sami dama da har jakar magori sai ta yayata, sai kowa ya ji mugun butulcin Sulaiman.
Maganar ta daure ma Alhaji kai, ta kuma sanya shi cikin wasi-wasi, wane irin fushi Inna Mairo ke yi da Sulaiman? Allah kadai’ya sani. Yau dai Allah ya kawo karshen korafin Alhaji, domin dai an sami gida kuma an yi sa’a nan kusa ne, tsakanin su babu nisa, gidan na
marayu ne, aka sa a kasuwa. Alhaji Imam ya biya lakadan.
Gidan karamin filat ne mai dakunan’kwana biyu da falo a tsakiya, sai kicin da bayi ga dan karami sito. Farfajiyarsa madaidaiciya ce’, za ta dauki mota guda daya, bai bata lokaci ba ya sa aka gyara duk abinda ya lalace a gidan. Sannan aka sake sabon get saboda wancan karami ne kwarai, kuma yatsufa.
Abu na’gaba da ya yi, shi ne tura motar kaya daga cikin motocinsa tare da motar Alhaji wacce za ta kwaso su. Alhaji ya so zuwa, yaran suka hana shi, saboda yanayin jikinsa. Lambar Murja kawai aka ba Sabo direba da sun isa BauChi, zai kira ta, yayin’ da su ma can suna cikin shiri.
A yammacin da motocin suka isa,.bayan sun ci abinci sun yi sallah, kaya kawai aka loda, kaf sauran abubuwan da suka rage masu, ana sallar magariba direban ya damko hanya. Don su sun saba tafiyar dare. Washe gari. Murja ta yi sallama da makwabta aka sa Sulaiman a mota suka damko hanya, duk wanda ka kalla cikin su. kasan baya cikinsukuni.
Damuwa biyu ke cunkushe cikin zukatansu. talauci‘ya yi masu katutu, ‘ga shi kuma yau za su koma wajen wadanda suke wa kallon su ba komai bane a da. Murja kadai ke’ tunanin ciwon mijin ta da ya ki ci”, ya ki
cinyewa sai wawusar kudi yake yi, kamar wutar daji, kusan ciwon shi ne silar rushewar komai na su.
Muna iya cewa laifin Sulaiman ne da ya yi. ya
kuma hana kowa ya yi masa fallasa, don kar a gane – halin da yake ciki ko kuma ya rasa na yi ne? Dan an ce alheri ga’don barci, to shi bai yi ba balle ya samu wajen rabawa. Allah shi kyauta
Motar kaya ta fara isowa tsakar dare, shi ya sa da sassafe Mamasuka je da ‘yan aiki maza suka sauke kaya, mata na shirya su, inda suke zaton ya dace na dakin barci, suka zube su nan, na kicin suka zuba can haka na bayi da na sito, koda ma falon Imam ya sa Sabon kafet da labulaye, wuri ya yi tsaf Don ma kayan sun tsufa, amma da yake masu tsada ne sai suka yi kyau da suka hade da sabon fenti.
Masu aikin Asma’u da Hamdiyya su suka yi abinci kala uku da abubuwan sha masu sanyi a manyan kuloli’na alfarma. Direba ya kwaso ya kawo gidan, a motar makaranta.’Mama ta yi farin—ciki da ganin irin
‘ kokarin da surukanta suka yi. ‘
, Ba‘a jima da kawo abincinba, motar da ta dauko su ta sawo kai harabar gidan Mama da ‘yan aikinta suka fito suka tarbe su. Daga Murja har yaran sun yi firgai-firgai kamar ba su ba. Shi kuwa Sulaiman duk wanda ya kalle shi, dole ya ji hawaye na neman sauka, saboda yadda ya rame gaba daya kamar me kanjamau! ,
Murja na ganin Mama ta fara kuka, suka rungume juna kowa na hawaye, ganin haka ya sa ma yaran suka hau kuka. Bayan sun natsa a’ falo. Mama ta tura direba ya je ya dauko Alhaji, sannan ta kira kowa a Waya ta shaida masu ‘yan Bauchi sun iso, k0 damasu Asma’u a Shirye suke, nan da nan suka dauki mota.
Asma‘u ta‘ ja. su Imam da Muda kuwa daga ofi suka
wuce tare, a can suka iske Alhaji ya ta sa Sulaiman sai tsiyayar hawaye suke yi. ‘
Su kan su jikin su ya yi mugun‘sanyi, su kuwa su Jamila maka—makan motocin da ake ta shigowa da su sune suka gigita ta su. Tambayar da suke wa junan su ita ce, shi kuwa wannan gidan da aka sauke su na wanene? Suna nan sun baza kunne su ji.
Imam da Muda suna zaune gaban Sulaiman, sun zura masa ido. Alhaji ke fadin -“Kun dai ga dan uwanku k0? Kun ga ‘yadda Allah ya maida shi? Ka yi kuskure Sulaiman don me za ka zauna da ciwo ya so cinyeka haka? Sannan ka rasa aikin ka sama da shekara uku ‘ ka kasa gaya min? Ke kuma Murja ki biye masa, sai ka ce- ba ku da kowa? Ta goge kwalla ta ce, “Hmm…
. Wallahi Baba babu yadda ban yi da shi ba, amm ya nuna min bai yarda ba, kai har ta kai ya ce idan na fadi a bakin aUre na. Baba ko ka san har yanzu Umma na kwance? Amma’ rabona da ita sama da shekara uku kenan?
Babu yadda zan ~yi, tun ina masa magana kafin ciwon nan ya ci karfinsa, ‘har ya zo ya kwanta, kudin maganinsa da alluurai masu tsadar gaske duksu sukacinye duk abinda ke hannunmu har da motarsa ‘shi dama ba tattali gareshi Ba ga shi baya jin shawara, uwar’bari tasa na kira waya komai ‘ta fanjama-fanjam Duk kun san komai, ba sai na fadi
ba, in dai halin Baban Jamila ne ….. ‘
‘ Sallamar Inna ta katse jawabin da ‘Murja take yi. duk suka juya gare ta, “Sannu da zuwa Inna.” Nan take idanuwanta suka cika da hawaye, ba don ganin danta ba, sai don ganin gatan da aka yi ma’sa, ta zauna suna gaisawa, tana tsiyayar hawaye “Ki daina kuka Inna.” Inji Imam. Alhaji ya ba shi amsa, “Dole ta yi kuka Imam, ai
duk wanda ya ‘dubi Sulaiman, dole ya yi masa kukan
tausayi belle mahaifiyarsa.’ Ta share hawaye ta dube shi, ‘Ko kadan ni ba shi na ke wa kuka ba, don ban ga abin tausayi a jikin sa ba, ai rayuwa ce, yadda ka dauke ta, haka lta ma za ta bi da kai.
lta kuma duniya azuzuwa barkatai gare ta na karatu, idan ka ki, ta koya maka gaskiya, to za ta koya maka karya, wacce karshenta yake zama dana-sani. Wallahi abu daya ya sanya ni hawaye, farincikin yadda Allah ya nuna ishararsa a kanka, ba ka ji kunya ba…….
…..Alhaji ya katse ta, ‘Ya isa haka Mairo, ai komai ba dabarar mu bace, kuma ni na sha gaya miki ban yi wa Sulaiman komai ba, don ya rama min …… Ta karbe.
“Haba Alhaji ai Sulaiman ba shi da abinda zai rama maka. koda ace duk abinda ya samu kai yake’ zazzagewa. Ba ma haka ba, ko ba ka yi masa komai ba a rayuwa, matsayinka ya kai ace ya dauki nauyinka, yanzu shi me ya yiwa ‘yan-uwansa da ya cancanci wannan gatan? Ashe dai alheri dadi gare shi, ko don ka sami lada wajen Allah.’ ‘
Kowa ya yi tsit! Saboda maganar Inna gaskiya ce; bakin-ciki ya lullube Sulaiman, kamar sa za’a zaunar gaban yara ana masa tijara. saboda suna da kudi, shi baya da shi yanzu? Gaskiya ne watau duk abubuwan da ya yi a baya, an manta saboda ya tsiyace, kuma
lalura ta same shi.
Ya jinjina kai hawaye suka’ gangaro masa, ‘Babu komai.‘ Haka ya fada cikin ransa. ganin ya fara hawaye, ya sa Imam ya ce, ‘Duk wannan maganar ta qare Inna. Yaya Suleiman na mu ne, duk abinda ya taba shi, tabbas mu ya taba, saboda haka yanzu maganar lafiyarsa ita za mu fuskanta. zai huta yau. . ,
Gabe Allah-ya tashe‘mu lafiyar za mu m (A.B.U.T. Shika), na yi magana da wani Likita mutumin kwarai da gaske, yasan aiki
shi zai tsaya sai inda karfinsa ya kare. Ina fatan kowa zai kwantar da hankalinsa, mu bar wa Allah al’amarinsa.
Magana ta gaba da na ke so in yi itace akan yaran nan, ya zama wajibi ko waccen su ta fidda mijin aure, don ba za mu yarda da zaman su haka ba, suna ‘ya‘ya mata babu aure, sai yawon bin ofisoshi, waida sunan neman aiki, to ya zo karshe, gaskiya ba za mu yarda da wannan ba.‘
Duk wuri ya dauka, ‘Gaskiya ne.’ Sulaiman kuwa zuru ya yi wa Imam yana mamaki, watau yanzu shi ne mai bada umarni? ‘Gaskiya ne.‘ Shi’ma ya fadi ba tare da ya san kalmar ta fito ba. Inna tace, ‘Au yanzu ka gane gaskiya ne? Ai kadan ma ka gani ……
“Haba Mairo ki daina yi masa baki mana.‘ lnjl Mama. Alhaji ya ce, ‘Kyaleta ta yi ta yi, al sai mu ba ta wuri, tunda tana nuna mana ita ta haife shl.’ ‘ ldanuwanta taf! Da kwalla ta mike tana fadin.
‘Yi hakuri Yaya.‘ Waje ta fita ta nemi wuri ta zauna ta ci—gaba da sharar kwalla. Alhaji ya dube su, magana ta kare saura abubuwan da Imam ya lissafi su za mu sa gaba, muna fatan Allah ya yi mana jagora ya kare mu da lafiya.’ Suka amsa da “Amin
Ya sake fadin “To aje ayi salla, a ci abinci.‘ Har kowa ya tafi yin alwala Sulaiman bai ce uffan ba. Murja ta yi masa alwala, yayin‘da Mama ta je ta rarraso Inna Mairo, ita ma ta yi alwala ta yi sallah ko damasu Asma’u tuni suka yi ta su tare da su Jamila.
Kasancewar‘ su ba su cikin taron da aka yi wa Sulaiman, suna daki tare da su Jamila suna hirar ciwon Dadin su. Su Asma’u ne suka wadata kowa da abinci, shi dama sulaiman ba iya ci yake ba. ‘Yar Maltina ya kan sha, ita ma wani lokacin ba ta zama, da zarar ya
sha, ya kan yi kamar zai mutu, sai ya amayo ta.
Bayan duk sun koma gida, masu tafiya ofis s’un tafi. Inna ma can ta tafi gidan yayanta, saura Sulaiman Kadai da iyalansa. Murja ke ci—gaba da gyaran wuri, yayin dasu Jamila suka fita zagaya gida, su ne har waje suka gano yadda yake ta wajen sosai, a kicin suka iske Murja tana kara gyara shi.
‘Umma wai gidan nan kyauta aka ba mu shi ko aro ne? Jamila ta tambaya, ta dubeta a fusace ta ce, “Ban sani ba, sai ki ziki shake ni, in gaya miki! Ganin haka ya sa su Ummi suka juya da sauri suka kama kan su. Jamila ta yatsina fuska ta ce, ‘Ah Umma daga tambaya, uhm ……. Ta wani wuce Murja, ta yi tsaye sororo, kafin ta ce, “Shashasha maras kunya, mts …… Ta ja dogon’ tsaki, ta ci—gaba da aikin ta.
Wajen Dadin su suka rankaya, kowacce ta nemi waje ta zauna. ‘Dadi ka yi barci ne? Ya bude ido a hankall, ya dube su ya dan kada kai “Sannu.’ Ya ce ‘Yauwa.’ Jamila ta zarce da tambaya “Wai Dadi gidan na kyauta aka ba mu ko aro ne?
A hankali yake magan “ina zan sani Jamila, ki na ganin sun zaunar da ni kamar karamin yaro, kowa na fadan abinda ya ga dama akai na, me na yi masu? Don na talauce, ciwo ya‘ kama ni ina neman taimako, shi ne za’a tara yara su ci zarafina, to wai ma menene na ware mana gida, na zama abin kyama k0?
Babu komai, duk Murja ta jawo min, sai da na ce ba na bukatar taimakon kowa, ta kyale ni, ai mutuwa daya ce, amma saboda taurin kai irin na ta, ba ta ji gargadin da na yi mate ba, kawai ji na yi Baba ya kira ni, yana fada.” ‘
Jamila ta ce “Ah’ah Dadi, nan kuma fa ba ka kyauta ba, idan lokacin mutuwar ka bai yi ba ka san irin wahalar da za ka sha ne? Mu kan mu ka san yadda
muke fadi tashin neman kudin magani da alluran da
ake maka, ka ba kallo na tafi Lagos na dawo ban samo komai ba, saboda wanda na je wajen sa,’baya nan. Gaskiya Umma ta yi daidai, don mu ma mun gaji ‘da wahala, idan ba ma mu ka ‘yi ba, ba mu samun abincin kirki, amma yanzu fa? Za’ mu ci, za mu sha Ga Wurin kwana mai kyau, sannan za’a kula da lafiyar ka, wata kila ma a aje mana-Mai gadi da direba, ‘to me ya rage? Ummita tace mudai Allah’ya ba ka lafiya, a kara maka da’. jari; Shi ’kenan‘ duniya sabuwa.” Jamila ta mika mata hannu suka tafa. ‘ – ‘ Yaja dan tsaki ya ce,’ “Lallai ba ku da hankali yaran nan.;..’… ..’.‘.’Da hankalinmu raS Dadi “ni na san gidan nan ma kyauta aka ba mu, kuma gara da ba’a kai mu can gidan ba, don takura za mu yi Wallahi, ba za mu sake ba, ka ji na rantse Dadi.‘ lnji Jamila ya ce, “Na gaji” ‘ da maganar don Allah ku koma dakin ku, wata kila in yi barci.’ Duk suka mike zasu fice kenan. ‘ ‘ : Murja ta shigo, ba ta saurare’ su ba, har suka bar dakin, ta zauna ‘ka na ta numfasa ta ce, “Sannu Baban Jamila.’ Ya‘ Ce, ‘Ke ma sannu.’ Ta ce “Da wasa ka’fadi- ko kuwa wani abu ya faru? ‘
‘ ’ Ya ce “Hankalin‘ki ya kwanta mun dawo Kaduna, ké’kin ji dadi, kowa ya .fadi abinda ya ga dama a kaina, kyale su kawai na yi, don Imam ba sa’ar yina- bane, don ya .yi kudi zai. ‘zauna‘yana bada umarni‘, kamar shi ne ubanmu.‘_
‘ Ta zura. masa ido tana kada’kai, takaici‘ kamar ta’ saka kUka, “kai Baban ’Jamila, ka na da wuyar sha’ani, kai dai kullum gaskiya ce ba kaso, ba don haka ba, me aka fada na batanci?
Menene illar maganar da yace dole yara su fidda miji su yi aure? Ka fi so mu yi ta kallonsu yara dUk sU tsofe“ a gida, ba’a banbance ni dAsu
da su Ya kamata ka yi tunani, tun farko kaika rushe tarbiyyar yaran nan.” ‘
Ya ce ‘Kin gama‘, to don Allah ki koma ki ci gaba da aikin ki, na san dole ki raina ni, tunda ba ni da kudi yanzu kuma ciwo ya tauye ni, bani da wani amfani a gare ki.’ Ta yi dan murmushin ta’kaici, ta kada kai, ‘Allah ya ba ka hakuri, akwai abinda ka ke bukata? Ya ce ‘Babu.’ Duk suka yi shiru, kowannan su yana tunanin
wata guda cur sintirin asibiti kawai ake yi,
gWaje-gwaje har birnin Kano, duk da cewar
likitocin sun san matsalar sa, amma sai da suka yi na su binciken na daban. Binciken kuma ya yi amfani. .
Domin gwaji ya nuna dayar kodar tana barazanar kamuwa da cutar. Hankalin kowa ya tashi musamman Alhaji Abdul-Rasheed, shi ya ‘sa nan take ya ce tunda ana dashe, to a cire ta sa daya a sanya wa Sulaiman‘ din
‘Yayansa ‘kuwa suka ce atafau babu mai taba masu tsoho, a illata masu shi, amma kudi ko nawa ne Imam ya ce zai kashe ayi ta yi masa alluran, duk kwana- goma dubu goma sha biyar, tunda dai Likita ya ce muddin’ana alluran babu fashi akwai yuwuwar zai sami sauki.
Hmmmmmmmmm lol. lbr dai Nata gangarawa
I luv y’ll
Naku har kullun