Makaranta duniya chapter 30

Makaranta duniya

           Chapter30

masa shishshigi. Wayarsa ya dauka ya kira Mudansir  ya sanar wa ma’aikata gobe kowa ya dawo aiki.  mudassir ya zura masa ido ya ce “Alki Yaya?
Ya ce ‘Ka daina tambaya Muda, duk abinda na saka yi kawai, umarin ba nawa bane kuma ban ce ka ‘gaya wa kowa hakan ba, ai ka gane? Ya numfasa ya ce. ‘Na gane, Yaya, Allah ya kawo mana mafita.‘ ‘Amin, miliyan hamsin za mu fidda gobe da sassafe za mu je banki, abinda suka bukata kenan?
Ya amsa da ka kafin ya ce, ‘Komai na gaya
maka sirri ne, ka kula sosai saboda guje wa kuskure.’ Ya ce. ‘lnsha-Allahu zan kula Yaya.‘ Ya ce, ‘Allah ya ; taimake mu.” ‘Amin. ka na iya tafiya ka samu ka sanar wa ma’aikata.’ Ya mike ya bar ofishin cike da tausayin Yayan sa. haka shi ma ya raka shi da kallon, tausayl ganln yadda dan—uwansa ya rame a tsaye.
Da sassafe suka shigo da kudaden, shi ya sa har suka gama shlrya su a kwalaye uku. Ma’aikata ba su fara zuwa ba, sannu a hankali ma‘aikata suka hallara kowa cike yake da mamaki dawowar su aiki ba tare da an ga Alhaji ba.
Washe gari ma hada—hada ta ci-gaba a kamfanin kamar yadda aka saba, sai dai shi Imam da Muda suna cikin dardar! Ne, gaba daya jinin su a kumba yake har zuwa karfe uku na yamma. Bugun kirjin su ya kam kamar zai tsage masu kirji, amma har karfe shida babu alamar zuwan bakin su.
Hankalinsu ya kara tashi, har karfe bakwai suna zaman jira, sannan suka bar ofis suka wuce Tudun Wada. Mama na kwance lnna Malro na gefen ta a zaune tana goga mata jikakken tawul, saboda zafin da
jikin ta ya yi, ya dan ragu.
Bayan sun gaisa. Imam ya zuba mata ido, yayin da Muda ya dauko kanta ya dora bisa cinyoyinsa‘ “Mamanmu ya kamata ki yarda akai ki asibiti, jikin nan naki kara narkewa yake yi.”
Ta ce, “Asibiti ba za ~su iya’ yi min komai ba Muda. Ni na san ba ciwo na keyi ba, idanuwa na né suke so su ga’ koda gawar sa ce, na tabbata zan sami sukuni, jiki na ya daina zafi.” ldanuwansu suka tara kwalla.
“Wannan shiru ya yi yawa, zai‘ yi wuya in Babanku yana da rai, dama ba komai suke so ba ransa
‘kawai suke so, to menene na rike mana gawarsa? Su kawo mana mu yi masa sutura hankulan mu su kwanta mana.‘ – Imam ya yi wuf! Ya mike ya yi waje yana share fuska, a zaure suka yi kicibis da Sulaiman. “Me ya faru
ka ke kuka! Ya ce “Ba komai Yaya.” Ya zuba masa ido,
ya ce, “To wai me ya sa har yanzu ba su sake kira ba? Ya ce “Ban sani ba Yaya, ban san dalilin su na yin hakan ba.” Ya ce, “Ko ka na yin wani abu ne a boye? “Kamar
yaya?
ka na yi a boye ne? Da sauri ya amsa, “Me zai sa in yi haka? Bayan sun gargade ni, ga mahaifina a hannunsu, ‘ me zai sa in yi wasa da ‘rayuwar wanda na fi so a rayuwa ta? Yakamata ka yarda da ni Yaya, babu wata kafa da na ba ‘yan Sanda, don shigowa cikin wannan maganar.”
Ya numfasa ya ce, “Shi kenan, ka daina damuwa, komai zai zo karshe da yardar Allah. Ya jikin na Mamanmu? Ya ce “Tana nan a kwance, ita ma ta ki bada hadin kai a kai ta asibiti.” Ya dafa kafadarsa ya ce, “Ciwon ta ba na asibiti bane, da zarar ta ga Baba, za ta tashi, so ka kyale ta.
Ya ce, “Communicating da ‘yan Sanda mana, ko‘
Tunda Likita ya zo ya ba ta ‘yan magunguna, Bari in shiga in duba ta, ka daina kuka ka ji’? Ya ce, “Na ‘  gode Yaya.” Ya kamo hannunsa suka dawo falon na Mama, sai goman dare suka koma gida.  Haka ya kwana ko kafadarsa bai yada ba, balle barci ya shammace shi, haka al’amarin yake wajen ‘Muda. Matayen su ke ta iya kokarin su wajen dan Kwantar masu da hankali, amma yau_ kura ta kai bango. “abin da Mama ke ciki da rashin ganin mutanan nan ‘ sun hadu‘ sun kara dagula masu lissafi, sallolin nafil‘a shi kan sa saida ya fara manta yawan raka’o’in da ya yl. Sannan ya natsu bisa sallaya har aka kira asalatu, ya yi raka’atanin fair, ya sallaci subahi.
– Asma’u ta matso kusa da shi ta kama shi tana fadin “Ka yi wa girman Allah ka dan kwanta ka runtsa, jinin ka zai hau ogana, shi kenan‘ ayi haihuwar guzuma, ka sani fa kai ne jigon komai, kai ne ragama’, idan ka fadi, ya ka ke so mu yi da rayuwar mu?
A hankali ya wuce jikinta ya kwanta, ya sauke numfashi ya ce, “Ba laifi na bane na rasa inda zan sa rai na ne Asma’u  tsoro na ke ji kar mu rasa Maman mu, idan
‘ al’amarin nan ya ci-gaba da tsawo, ban san me zai faru da ita ba? A hankali take shafar kan sa.
“Haba angona, ka dainakawo wannan tunanin, addu’o’in da ake_yi‘, ai Allah na ji kuma na tabbata zai mana agaji, don shi mai jin tausayin bayin sa ne, ka yi hakuri ka yi barci, koda na awa daya ne, za ka ji dadin jlkin ka, ka ji? Ya ce, “Na ji.” A natse. ta yi ta ririta shi har barci ya‘sace shi.
Ai kuwa‘bai farka ba,’sai karfe takwas da Muda ya shigo sasan su, ya hanzarta wanka ya shirya, bai‘ tsaya karyawa ba suka fice. Tudun Wada suka fara isa, suka duba jikin Mama, a can suka iske Malam Sadiq da kansa ya zauna ya tasa_ta tana shan kokon-da ta sa aka
dama mata, abin ya yi masu dan dadi. ‘
Bayan sun gaisa, su ma ya kwantar masu hankali da kalamai masu dadi, kamar yadda ya saba, tun lokacin da abin ya faru, ba su isa ofis ba sai sha daya saura. Zaune yake kawai ba ya aikin komai, shi ya sa duk wata takardar da ta shigo ofishinsa, ba ta fitowa saboda ba aikin yake yiba balle ya duba ta.
Wayarsa ta buga, ya dauka ta jiki na rawa ya » danna ok “Hello! Muryar nan ya ji, “Kai Wallahi ka na
burgeni. Kullum ka na’ kusa da wayar ka,‘ to ina alkawarin mu? Ya ce, ‘Komai yana shirye tun shekaran jiya na kejiran ku.” – . . . .Ya ce “Ka ci-gaba da ajiye mana, wata kila nan da wata daya mu zo mu karba.” Da sauri yace, “Ku yi wa girman Allah kar ku yi min ,haka. Duk sharuddan ku na cika su, ya kamata kuma ku cika min alkawari, idan ba _za ku sami zuwa ba, ni ku gaya min wurin‘da zan ‘kawo maku, please!. ‘ ‘ Ya kyalkyale da dariya‘, Ha-Ha-Ha-Ha! “Alhaji Imam me ka ke ci, na baka na zubane? Ina ruwan ka
da kudin mu da’ka ke so ka kawo mana? Har ka, ke‘
wani rawar murya. 0k, ka shirya wani abu ‘ko? “Haba-Haba me zan shirya? Yakamata ku yarda da ni, dukkan hadin kai na ba ku, ba ni kadai na kosa in ga Baba na‘ ba, har dai mahaifiyata. ‘Tsohuwa ce damuwa ta kai ta kwanciya, rashin lafiya, don girman Allah ku tausaya mata.” . _ ’ . Yace‘“To shi kenan, tunda ka sanya uwa ka gama‘magana, ka san ina ganin girman uwa, wata kila
ma da ita mu ka dauka da farashin ya fi haka, ka na ji ‘ na? Karfe uku ka shirya karbar bakuntar mu, tamkar
yadda ka saba. amsar bakin ka, musamman abokan (Business) din‘ka, in ka yi’shirme, mu aikata shirme akan tsohon ka;.. Ya kashe wayar ba tare da ya tsaya jin me Imam zai ce ba.
Tunda ya yi sallar azahar, baya aikin komai face gallon agogo. Karfe uku daidai wata (Pegeout 409) ta
.shigo harabar kamfanin, bayan ta yi fakin, direban ya fito da sauri ya bude murfin bayan, wani hamshakin alhaji ya fito, kayan jikinsa babbar riga da ‘yar ciki da_ ‘ Wando, tsadaddiyar hular sa ‘ta zauna bisa kan sa kwarai da gaske. Shaddar sai daukar ido take yi. Ta daya bangaren kuma wani dan dogo baki ne ya fito, shi tazarce ya sanya kuma karamar shadda ce wacce kudin ta ba su wuce dubu ‘biyu da dari biyar ba. yana dauke da (Brief ,Case) din Alhajin. Alhajin waya yake yi lokacin da ya fito.
‘ Ba su bar jikin motar ba. Imam ya fito da sauri bakinsa har kunne, ya nufi gun su, suka yi musabaha sannan ya ce, “Kai sannu ku da zuwa.~Bismillah Suka wuce suna tattaunawa, daidai cikin babban falon Imam ke fadin.
“Kai da kan ka Alhaji? Ai da ba ka taso ba, k0 aikowa ka yi, babu abinda zai gagara.” Ya ce, “Ah, haba, ni din ma ina ta son zuwa, saboda tunda ka bude sabon ofis ban ziyarce ka ba, na sa albarka.’ Sakatare da
‘ sauran ma’aikata suka ja gaisuwa, ya amsa cike da
, fara’a.
Imam ya bude ofis yana fadin, “Gaskiya naji
dadin zuwan ka. Bismillah ku shigo.‘ Gaba dayan su
‘ suka shigesu biyun, yayin da shi direba na can zaune cikin mota, ya maida kofa ya rufe, ya nuna masu wuri suka zauna._Ya karéWa ofishin kallo ya’ ce, “Wuri ya yi kyau, kuma ku na hutawa Wallahi, ka daina ganin laifin mu, dan mun zo karbar rabon mu.”
Imam ya nisa, “Ba haka bane, ai shi kudi da rashin sa duk halittar Allah ce kuma jarabawarsa ce, dan Mutum .ya daure ya dauka daidai, to ya cika, jarabawar, sakamkonsa yana wajen Allah
Ya yi ‘yar dariya ya dubi wanda suke tare ya ce “Ya ka ji jawabin nan? Yaro tamkar Babansa, akwai kalamai, shi ya sa ba na so in rabu da Baba Wallahi,. don dai ka matsa ne. To shi kenan mu je maganar’ (Business), saboda babu lokaci, yaya kajin’? An shirya mana kamar yadda mu ka ce? , Ya ce‘ “Kwarai kuWa suna can an zuba a siton’ sanyi,  ku20 a kwaso su kamar yadda ake wa kowane kostoma.” Ya lalUba aljihu’ ya dauko ‘yar karamar bindiga ya kama gefen rigarsa, ya dan goge ta, ka na ya hure bakin ta, ya maidakallonsa kan Imam. Ya bude katuwar muryarSa ya ce “Ka’ tabbata komai ya cika? Ya ce “Kudi cif Suke, ba na haufi, don ba zan yi . wasa da sharuddan ku ba.” “K0? . Ya- amsa da“Kai Ya yi dan “murmushi; “Ka na_ son Baba da yawa, koda yake mai Uba kamar Baba dole ya so shi, amma na sami labari ba‘ shi kadai ka ke so be, har da wata wai Asma’u, wace ce ma? lman ya yi
‘Shiru gabansa ya “fara harbawa. Ya mike yana dan murmushi “0k, kar ka damu, ba sai ka gaya min ko
wace ce ba. Nan gaba zan sani. Mu je a fito mana da ”
kajin k0?
Ya hadiye miyau da kyar, ya mike suka jero, ‘yayin dayake maida bindigarsa cikin’ aljihu. “Gaskiya Baba yana da dadin zama,‘ koda yaushe addu’a yake yi Allah ya shirye mu. Abin yana min ‘dadi, domin babu wanda’ya taba gaya min hakan. Har da mahaifina.”
Ya fada daidai Imam yana bude kofa, duk da
haka‘ bai yi shiru ba. “Koda yaushe na dawo gida a bige, sai ya yi’ta zagi na yana tsine min, a karshe ya kore ‘ni gidansa, ya ce je ka ka gani, ashe alheri zan gani, ga shi ina danne kan miliyan hamsin, ban siya ba balle in siyar, ko‘kuwa? Ya fada yana kalon Imam, bakinsa har kunne ya ce “Gaskiya ne.-” Ya ba shi hannu suka tafa.
Ya kwala wa Mudansir kira-, ya fito da sauri, suka gaisa da baki, sannan Imam ya ce “A’ debo wa Alhaji katon hudu na kaji.” Nan take ya gane sakon, don haka da kansa ya shiga siton ya debo guda biyu, can mota ya same su, aka bude but, ya zuba, suka koma da direba suka kwaso sauran biyun tare cikin raha da annashuwa. Bayan an rufe but, ya sallame su ya koma ofishin sa. Imam ya dube su ya ce, “Da karfe nawa za mu-gan sa? Ya ce ’Kar ka damu, yadda ya” tafi, tohaka zai dawo, ai ka gane‘? Ya fadi cikin fara‘a sosai. Dole shi ma Imam ya wadata ta sa ‘fuskar da murmushi, ya. mika masa hannu suka yi sallama, Suka fada mota, suka bar kamfanin. Shi kuwa Imam kai tsaye ya koma ofishinsa.
Bai jima da shiga ba. Mudansir ya shigo ya same shi yana ta kai kawo a tsakar ofishin .“Yaushe suka ce Baban zai .dawo? Ya numfasa “Ba su fada ba, ammasun ce ta yadda ya tafi, haka zai dawo.” Ya kara matso shi, “Anya ba mu yi kuskureba Yaya? ldan Suka ki bada shi fa ……. ?
Da sauri ya daga masa hannu “Don Allah ka daina ‘fadi, kar ka kara firgita ni, damin tunanin da zuciya ta ke yi kenan. Mts! Allah ka yaye mana masifa, wai ga mai laifita’ gaba na, amma ban da abin yi. Allah ka jarabce mu, kuma mun gode maka, a gare ka mu ke neman taimako’, don da kai mu ka dogara.” Ya sauke numfashi ya nemi kujera ya zauna, shi ma Mudansir ya zauna a hankali a cike da tausayin kan su.
Har daran washe garl suna ta sa ido don. ganin ina Alhaji zai fito, amma shiru ka ke ji. Hankali kowa ya kara tashi, jin- cewa miliyan hamsin ta tafi kamar_kudin banza. ‘ a ” .- Sulaiman ya bude wuta yana” ta fada, wai me ya
sa Imam bai nemi shawarar sa ba, kafin ya’bada kudin, da ba’a ba su duka ba, dole anemi ragi, kuma za su rage_ Imam shiru kawai ya yi, dalilin ya san Alhaji ya fiye masa miliyan hamsin, to menene na bata lokacin sa Wajen neman ragi. Alhalin bai san me neman ragin zai jawo masa ba?
§§§§§§§§§§§§§
karfe goma ta gota duk suna tare   Mama ke magana, “Imam
yakamata ku tashi Ku koma gida, dare ya fara yi_» Ya numfasa ya ce, “Za mu tashi Maman’mu.” Yana rufe baki suka tsinkayi sallama. ‘ ‘
Babu wanda gabansa ‘bai- fadi ba, wannan murya ta yi kama data Alahji‘, ko kuwa kunnuwan su ne? Kafin su gama tababa, ya kara Wata sallamar a kofar falon’ Mama. Haba in ba ka yi, ba ni wuri, zo ku ga rige rigen fita har da Mama da ,ke kwance sharkaf
Kowa rungumara sa yake yi, nan take kuma’suka goce da kukan dadi, suka shiga da shi cikin falon ya zauna. Imam da Mudansir suka sake zubewa gabansa, kowannansu ya yada kai ‘ jikinsa. saboda murna, ya shafa kawunan su ya ce. :
“Allah ya yi ma ku albarka,” Ya dubi Mama da Inna Mairo ya ce, “Sannu’ku, ya mu ka ji da fargaba? Suka amsa, “Mun gode Allah.” .‘ “
Ya jinjina kai ya ce, “Tabbas Allah abin godiya ne, mun gode masamun kara gode masa. Ina son kowannan _ku ya dauki wannan abu a matsayin jarabawan, kar‘ ka yi zaton ka yi asarar dukiyar ka Imam, ka yi fatan Allah ya mayar maka da alheri, idan kuma ra‘bon ka ce. Allah ya tona asirin su.” Kowa’ya amsa da amin. ‘ ~
Imam ya dube shi ya ce, “Ina fatan lafiya lau ka ke Baba? Ya ce “Lafiya ta lau Imam kosau daya Allah- bai ba su lkon taba jiki na ba, duk abinda na ke son ci, shi suke kawo min. Akwai wurin wanka da sabulu mai tsada, sun kawo min jallabiyoyi guda‘hUdU, don canjin
Kaya kumasu suke wanke wanda na cire. Yau tun safe ya gaya min zan tafi gida, amma ba mu fito ba, sai da “na yi sallar magariba. ‘
Suka daure min fuska da kyalle, sannan‘,suka fitO da ni, suka sanya a mote. Mun jima muna tafiya Kamar ranar da suka dauke ni, ka na na ji mun tsaya, suka bude min fuska. Ogan su ya ce mun iso, ya bude – aljihu na ya sanya min dari biyar suka ce in fita‘ motar. Ina futowa, suka’ja a guje suka wuce. ’
Na tako a hankali ina yiwa Allah godiya, duk da cewar ban fahimci lnda suka aje ni ba. Sai da na iso wajen Wani mai gasa nama, na tambaye shi. Ya .gaya min Rigachukun ne. ‘
Shi ya taimaka min na sami shatan a daidaita sahu ya dauko ni a dari bakwai. Bawan Allah nan shi ya cika min kudin da na ce ya bar shi idan mun zo gida zan karba, amma ya ki, ya ce ya taimaka min ne saboda ya. ganni dattijo, kun ji yadda muka yi da su.’
Kowa kada kai yake’yi cike da tausayin Alhaji. Mudansir- ya ce, “Mun gode Allah da ba su yi maka komai ba, mu dama shi ne zullumin mu.” Ya ce, “Hakika mutane ne su masu ban tsoro, domin za su iya alkata duk abinda suka furta.’
Sun sha yi min hargagi da barazanar. harbewa, sai dai su kan naba’a su saurare ni, da zarar‘na fara yi masu nasiha. Na‘ san Allah ne kadai ya tsare ni daga sharrinsu. Ina fatan kowa da kowa suna lafiya? Mama ta ce.
“Lafiya ‘lau. Su Malam Sadiq da Sulaiman ma ba su jima da» komawa gida ba. Kowanne ya bada gudunmawarsa ‘wajen kwantar mana da hankali, shig kuwa Alhaji Sama’ila Garbati rahoto ya kai wa “yan Sanda, sai dai ba su sami hadin kai- ba, saboda tsoron
me zai faru.” ‘
Ya ce “Haka ne, amma bada rahoton ma yana da amfani, koda za’a yi nasarar kamasu wata rana. ‘Yan Sanda za su taimaka wajen bincike, to Allah ya saka wa kowa da alkhari, ya tsare mu baki daya.” Duk suka amsa da amin. –
Imam da kansa.ya kira ‘su Malam Sadiq da Sulaiman ya shaida masu daddadan labari, haka kowa ya kira iyalinsa shi.’ Mudansir haba murna da tsalle tare da yi wa Allah godiya abin ba’a cewa komai, nan da nan Sulaiman da Malam Sadiq suka iso.
Duk’ da cewa ya ce su yi zaman su, sai Allah ya kai mu gobe. Malam Sadiq ya fara lsowa, suka rungume juna, ya yi murna kamar ya zubda ruwa kasa ya sha. Can kuwa Sulaima ya iso a mota tare da lyalansa duka.
Yana zuwa ya rungume shi, ya. fara kwalla yana fadin “Allah ya isa tsakanin mu da su, ba ka ci musu ba, ba ka sha masu ba, ko firgicin da suka jefa mu, ya isa Allah ya hukunta su balle wadannan makudan kudi da suka karbe. Allah ya tona asirinsu.”
Alhaji ya ce “Duk hakuri za mu yi, tunda Allah ya kubuto da ni lafiya, sannan mu roke shi- ya kara tsarewa.” Inna Mairo ta amshe, “Ai abinda Sule ya fada gaskiya ne, muna nan za’ mu ci-gaba da addu’a sai Allah ya tona asirin su, da yardar Allah wadannan kudin ba za suciyu ba.”
Sulaiman ya dube ta ya ce, “Inna ai kudi idan suka shiga hannun wadannan mutanan sai abinda Allah
ya yi, koda za’a kamasu, ba’a ganin komai a tare da .
su.” Ta ce, “MU ko babu kudin; muna addu’a Allah ya tona asirin kowane la’ananne keda hannu a cikin wannan al’amari. Allah ya wulakanta shi, ya ji kunyar duniya da’ lahira.”
Alhaji ya kwabeta “Haba Mairo ya’isa haka, ai ba sai kin fadi ba. Duk wanda ya yi da kyau, tabbas zai
mai kyau, akasin haka kuwa nadama ce za ta biyo baya.” Malam Sadiq ya ce. .
“Hakkun Jikin Sulaiman ya yi‘sanyi, don haka ya‘mike ya ce, “Bari mu koma gida, dare ya yi sosai.’ Alhaji ya ce, “Kowa ma .ya tashi ya koma gida mu saurari Allah ya kai mu gobe. Duk na gode Allah yayi maku albarka.” Suka’ ce amin, suka yi sallama kowa ya kama gabansa cike da farin-ciki. Sai da suka fara aje Malam Sadiq gida, sannan suka wuce, lokaci na neman sha biyun dare.
Washe gari dawowar Alhaji Abdul-Rasheed gida ta yi tambarl Jama’a suka yi ta barkowa yi masu jaje, gida fa ya yi damkan da ‘yan-uwa da abokan arziki. Husna sai faman tsokanar Alhaji take yi kamar ita ma ba ta sha kuka ba, har ta gode Allah ba. Zuwa sha biyun rana Mansur ya iso da matarsa a motar da lmam ya siya masa, saboda zirga-zirgar neman kwastamomi.
‘ Nan suka kwana. Washe gari suka wuce tare da Inna Mairo da saUran ‘Yan- Kauran Juli da suka kwana, sannu a hankali gida’ ya natsa, hankula’suka kwanta, ‘ amma shi Imam bai daina zullumi ba.
Saboda kalaman ogan barayin mutanen akan Asma’u, sai dai ya kara kaimi wajen addu’a da sadaka, don neman tsari ga sharrin wadannan mutane maSu neman nakasa shi. (Allah ka tsare mu ga sharrin masu sharri).
~~~~~~~~~~~~~~~~~~
sati biyu tsakani yayi daidai da rananr da Sulaiman’zai koma kilinik a asibitin Shika, ranar da Jamila ya
shirya tafiyar sa, ya ce Murja ta’ zauna ta huta, da kan sa ya ja mota suka .damki hanyar Zariya. Jamila ta dube shi ta ce, “Duk na kosa kudin nan su shigo hannu na.” Ya ce “Ke mahaukaciya ce? K0 sun shigo facaka za kiyi a gane ki? Ta ce, “Haba Dadi da wayau ~na ‘fa, amma in na – dan tsakura na yi abinda rai na ke so, wa zai fahimce ni, bayan kowa ya san ina da masu ba ni? Ya dan dube ta ya dauke kai, “Na ga alamar ba ki da hankaii, saboda haka gaba daya kudaden cikin‘ (Account) dina za’a zuba su, sai na gama Plan dina, ka na mu fara cin su.”
Ta gyara zama ta ce,” “Ba ni labarin Plan din? Ya ce, ‘Bayan mun amso miliyan talatin din mun adana a banki, za mu ci-gaba da zama fakirai har’zuwa’ watanni biyu. . Daga nan zance wani Aboki na ya kira ni daga‘ Lagos ya ce idan na ji sauki inzo ga aiki ya samar min. Daga nan zan fara karyar na sami kwangila guda biyu, na siyar da guda daya na yi amfani da kudin wajen a_watar da dayar, wa zai tuhume ni, don an ga ina cin kare na babu babbaka? ‘
Ta yi ‘yar dariya, “Dadi na kenan, akwai iya bojet, amma kar ka manta, kamukan biyu za su zama, tunda mu biyu ne, so sai mu ci abin mu babu babbaka.”
Ya kalle ta a kaikaice, ‘Don Allah matsa can, ‘yar
miliyan biyar din ta ki shi ne ki ke ta zalama? Ta sheke ‘ –
da dariya har da shewa, “Allah na tuba. Dadi kenan ai‘ duk abinka sai ka kara min wani abu.” Ya ce “K0 sisi ba 2a ki samu ba, me za ki yi da kudi da miliyan biyar ba za ta ishe ki ba?,Ta ce,_ “Ai ka na zama dan kwangila, ni kuma zan fara‘ katafaren (Business), Dubai; China, Malesia, babu inda ba zan buga ba, da miliyan biyar din? : . ‘ Ta ce, “Za fa ka kara min maganar. gaskiya Ya
ce, “Sai dai ki bari nan da’shekara daya da‘rabi, idan ya sake biyan sadakin matarsa, zan sakar miki kashi saba’in cikin dari. Koma me za ki yi, kije ki ta yi.” Ta dan bata rai tana cunno baki, “Gaskiya Dadi, ni dai ban yarda ba, ko miliyan daya ka kara min.”
, shi kenan ,zan kara miki, an wuce wajen? Ta yi dan murmushi, “An wuce, na gode Dadina.” Maganar su ke ta. yi har suka iso Zariya, kai tsaye asibitin suka wuce’ganin Likita. ’
Sun kai azahar a asibitin. Suna fitowa Al-nasiha suka shiga cin abinci. Bayan’sun kammala. Sulaiman ya dauko waya ya kira wasu lambobi, wadanda ya yi (Saving) da sunan Oga, yana dauka ya ce.
“Ya akayi ne? Ya ce sai “Oga, ga mu a Zariyar, yaushe za mu hadu? Ya ce, ‘Kafe tara na dare, a (Kainuwa Guest inn), cikin GRA.‘ Ya ce,_ “Za mu. tambayi wajenyanzun nan, da zararmun bar gidan abinci nan.”
“Karfe tara‘na ce, k0 kun zo. yanzu ba 2a ku same mu ba.‘ Ya’amsa “Na sani, kawai ina so a. nuna mana shi yanzu ne, kar ya yi mana wahala idan daran ya yi.” Ya ce, Ba’matsala Kowa ya kashe wayar sa. Suna ta’shi cikin GRA suka nufa. Da tambaya suka ’gano (Guest inn) din har suka shiga suka yi bukin daki.
Don sun tabbata dole su kwana. Dakin aka kai su. Sulaiman ya yi sallah, ita kuwa Jamila al’adar ta‘ take yi, ba sallar 2a ta yi ba, shi ya sa tana zuwa ta zube bisa gado ta .hau barci. Shi’ ma Sulaiman din yana, idarwa, ya dauki filo ya jefa bisa doguwar-kujera, ya kwanta. Bai jima ba barci mai nauyi ya kwasheshi.
‘ . Karfe biyar wayarsa ke ta faman ruri, har ta ~katse bai farka ba. Ta sake dauka yi ta kamar za ta ce wayyo Allah, gab‘ take da katsewa, ya farka ya rarumo ta a firgice ya duba. Murja ce ke kiransa, ya danna ok ya. kai ‘wa kunnansa, “Hello.” Ta ce, “Na ji ku shiru ne
‘Baban Jamila? Ya yi dan guntun tsaki, “Wallahi motar
ce ta lalace, tana can wajen masu gyara.’ Ta ce; “Ashsha! To yaya ku ka yi‘yanzu? ,
‘ Yace, “Dole mu ka kama daki a wani (Guest in”) don mu ci abinci mu dan kwanta, mu huta kafin su
gama gyaran.” Ta ‘ce “Allah Sarki, ka ce’ kun wahala
yau? ‘Ke dai bari, tunda na‘yi sallah na kwanta barci ya dauke ni, yanzu wayar ki ta tashe ni. Bari in yi la’asar mu koma wajen masu gyaran.’
Ta ce, ‘To shi kenan. Allah ya tsare.’ Ya ce, ‘Amin.’ Ya kashe wayar ya yi doguwar‘ mika tare da hamma, sannan ya wuce bayi ya yi alwala ya fito. ya yi sallah, duk Jamila na ta sharar barci kamarta mutu.
Har magariba suna nan. Sulaiman ya kira Marja ya shaida mata gyara bai yuwu ba, ga shi kuma dare .ya yi, ba za su ’iya biyo motar haya ba, saboda haka za su kwana, idan an karasa gyaran zuwa gobe za su dawo. Gaba daya ta ji jikin ta ya yi san’yi, a kasale ta yi’ masa fatan dacewa. _
Anan aka kawo masu abincin dare suka ci, wayar Oga ita ya dauka misalin karfe takwas da rabi, ‘Ku na ina? Ya ce, “(Kainuwa Guest inn), daki na sha bakwai.’ Ya ce, “An riga Malam zuwa masallaci kenan! Ku har kun ci uba na’son kudi Sulaiman ya kwashe da dariya, bai ma san Oga ya kashe wayar ba’. . ‘ ‘
Karfe tara suka iso su hudu, suka karbi daki hawa biyu watau (Double), gadaje biyu ke cikin sa, kuma shine daki na ashirin. Bayan sun natsa. Oga da yaransa suka sadado suka shige daki na sha bakwai. Wajen su Sulaiman.
bakin Sulaiman har kunne,.jiki na rawa ya nuna masu kujera, “Ga wuri ku zauna Sannu ku fa Oga.‘ Ya zauna saura,.suka dogare bayansa suka fiddo bindigogi suka rike a hannayensu, ‘oga ya dauki kafa daya ya dora bisa daya. Ya ce, “An gama .kwaranniya a karshe ga mu mun hadu, mece ce shawara? –
Sulaiman ya matso jiki na bari ya ce, “Ban gan ku da jakunkuna ba? Ya ce,“Kai mahaukaci ne? Mu fito da jakunkuna wasu su biyo mu? Ko ba ka san wurin nan babu tsaro bane? ‘
Kowa yana zauna ne karkashin tsaron kansa, shi
yasa koda yaushe na ke zabar wurin don gudanar da
(Business) di na, kudi na mota, ‘kowane kwali .biyu miliyan
‘ ashirin da biyar ke cikinsa, ku biyo, mu biyu, Idan’kun amince, dauka kawai za’a yi a maida but din ku.”
“Kamar yaya? Sulaiman ya tambaya. Oga ya ba shi amsa, “Raba daidai aka yi.” Sulaiman da‘ Jamila suka zuba masu ido. “Ba mu gane ba Ai ba haka mu ka yi da ku ba, miliyan goma mu ka yi da ku kafin a-samu kari daga baya, da na ji yana. ta cika bakin ko nawa zai iya biya ya fanshi mahaifinsa, shi‘ ya sa na ce mu kara farashin daga .miliyan talatin zuwa hamsin, na kara maku goma, ya zama ashirin, me ya sa 2a ku karya mana alkawari? “
Ya ce, “Babu shi cikin aikin mu Alkawari ba shi cikin dokokin aikin mu, kawai abinda muka sani, ‘idan kai ka saba mana, mu yi maganinka.”..jamila ta yi fit Ta mike tsaye ta ce, “Zalunci kenan, ai..’.. ‘
Ya dago mata hannu cikin fushi, dole ta hadiye maganganunta, ya ‘ mika hannu, aka dora masa sigarinsa, ya lika baki, wani cikin su ya kunna masa, ya mike ya matsa kusa da Jamila ya ja hayaki, ya feshe ta da shi, ka na ya ce, “Zalunci ya wuce na ki da na ubanki? Ina laifi ma da na yi raba daidai.”
‘ K0 alamar’tsoro babu a fuskar ta,cikin tsiwa ta ce, “wa za ka bude wa ido? Don an taimaka ma, shi ne za ka nuna mana halin Dan—adam? Ka jawo shi inuwa, sai ya gyagije, kai.ya tura ka ranar, to ba ka isa ba, ka debi iya na ku, ku ba mu na mu, ko duk ta tashi, ba _wai tsoron hakan na ke ji, ba.” . :
Oga ya koma da baya da baya, yana tafa mata, yayin da Sulaiman ya matso ta a gigice yana fadin, “Jamila kin yi hauka ne? Ya za ki bata mana shiri? Ka‘ ga Oga ka yi hakuri, yarinya ce,… Ya daga masa hannu,
“Ba sai ka fada ba, ai na san yarinya ce.” Yana magana Yana matsowa kusa da ita.
Cikin zafin nama ya zaro wata ‘yar ,karamar, bindiga watau‘ fistol, kan ayi haka ya dirka mata a kashin guiwarta, kafin ta yi kasa, ya kara mata a daya kafar, ta yi kara ta zu’be kasa. Sulaiman‘ya dora‘hannu bisa kai ya ce, “Me ya kawo‘ haka? Ya ce “Ba ka gani ne? Ai yarinya ce ko tafiya ba ta fara ba
Zai kara magana ya ce “Shiru! Bai yi shirun ba,  cewa ya yi “Ba ka kyauta min ba Oga Ka saba alkawari, kamar ba mu ‘yi yarjejeniya ba? Ji ka ke tus Bullet ya ba . shi amsa a kashin guiwarsa shi ma, nan ya zube; Oga ya matso ya tsaya kansa yace
“Ban fi ka son kudin ba, amma na yi kokari na raba daidai? Shi ne za ka gaya min ba dadi, haba Malam, ka dan bi doka mana, ai Oga ba tsaran sa’in sarka bane. Umarni yake badawa kawai, ace to.” Ya sake sakar masa a daya guiwar.
Ya tsugunna gabansa ya ce, “Ai ka‘ji abinda na ce ko_tunda kun raina kason ku, mu muna so, kai dan raini wayau k0? Na gama shan Wahalar, ina jefa kaina ‘ cikin hadari da kaina fa na je na amso kudin, ku, ku na can kwance a gida, shi ne har ku ke rainawa, don na raba daidai.‘ ‘ .
Oga ba mahauci bane, kuma ya fi kowa ‘son kudi, uba na cewa ya yi jeka ka gani, ga shi kuma ina ta ‘ ganin alheri, ku ba ku isa ku raina min wayau ba Ya busa hayaki ya tashi ya kira yaransa da hannu suka yi waje, suka bar su azaba, ta hana su koda motsi.
Kai tsaye babban falo suka koma suka bada makulli suka ce suna dawowa. Cikin hanzari suka bar harabar wajen da kudaden; Jamila kuka take tana karawa, “Jini na zai kare Dadi, na shiga uku zan mutu.” Da kyar ya iya ta maza ,ya jawo wayarsa a aljihu ya’ kira lambar hotel din da ke rubuce jikin’kofar‘ dakin.
“Hello! Hellol! Den Allah ku kawo agaji, akwai barayi cikin hotel din nan Sun harbe mu sun kwace mana kudi. Please jinin mu zai kare, a kawo mana taimako, daki na-sha bakwai Tsoro ya kama jami’an hotel, suka danna‘ kararrawar sukuriti.
Nan da nan ‘suka bayyana, duk suka’ dunguma daki na sha bakwai. suna  budewa suka gansu shame- shame jini. na bin kafufuwan su. Taimakon farko suka fara yi masu ta hanyar daure kafafuwan, ka na suka yi’ wa ‘yan Sanda waya.
Su naWa ne suka shigo? Daya daga cikin jama,an tsaro ya tambaya. Sulaiman ya ce ‘Su hudu ne “Su hudu kar dai ace su ne suka dawo mana da makullansu? Ai kuwa ba su yi nisa ba, da police za su 20 yanzu za su iya~kamasu. Amma ba. mu ji karar harbi ba
Sulaiman ke_magana, “Karamar’bindiga suka yi amfani da ita. Kudin mu dubu hamsin dazu na ciro su a banki,, wata kila tim a can suke bin mu.” Gaba daya suka ce, “Babu mamaki, kai Allah ya shirya wadannan mutane azzalumai.” ‘ ‘
‘Yan Sanda suka iso wajen, suka ce ba za su dauke su ba, sai sun ga shugaban hotel din. Ma’aikatan suka ce bayanan yana Lagos. Nan take aka kira shi aka .shaida masa abinda ke faruwa, shi ma rudewa ya yi, sannan ya roki‘Yan Sanda da yin duk abinda ya dace kafin ya dawo. _
Asibiti aka fara wacewa da su can (A.B.U.T.H. Shika); Nan da nan aka turasu dakin gaggawa don’ciro ‘ harsashen. Kowan‘nan su dai kashin guiwa ya yi fata— fata. Kowa ya ga harbin sai ya‘ ce barayin nan mugaye ne, sun san makasa. ‘
Bayan an fito da su. Sulaiman ya bukaci da a kira masa iyalinsa, watau Murja. Daya daga cikin ‘Yan Sanda shi ya kira ta, ya shaida mata halin da mijinta da
‘yarta suke ‘ ciki. “Inna-Lillahi’wa-Inna-llaihir—Raji’un! Abinda take ta faman fadi kenan, har ta kawo kan ta gidan su Mama, misalin karfe sha dayan dare. Can ta baro su Ummi na ta faman kuka. ‘ ‘
Har sun kulle gida, ta yi’ta bugawa su Jibo da ke dakin waje suka fara fitowa, “Lafiya Hajiya? “Ina fa lafiya. Jamila da Babanta, barayi sun-harbe su Suka
dauki salati, yayin da ‘ake bude kofa. Alhaji da Mama ke_
tsaye “Lafiya Murja? Ta kara rushewa da kuka. ‘Barayi
sun harbe Jamila da Babanta Ta yi cikin gida suka biyo‘ ‘
bayanta, suna sallallami. Nan take ta yamutsa gidan
Alhaji ke tambaya, “Ina suke yanzu? , .
Ta ce, “Zariya, ai tun da suka tafi kilinik mota ta lalace masu, ba su dawo ba. Shi_ ne ya ce minza su kwana can, har sun kama daki a wani (Guest Inn), kuma
sai ga waya wai a gaya min barayi ‘sun biyo su hotel din, ‘
duk sun harbe masu kafafuwa. Yanzu haka suna asibiti! , Alhaji neman wuri ya yi ya zauna, domin ganin ” ya yi wurin yana juya’ ma‘sa. “Yanzu menene ‘abin yi’? Inji Mama. Alhaji ya ce, “Bari a gaya wa su Imam, sai a’ bi hanya.” Nan da nan ya kira wayar ‘lmam, barcinsa ya yi nisa, amma dole ya farka, Babureshon din da wayarsa
ke yi gefengado ya cika masa kunni. ’ Yana ganin Baba idanuwansa‘ suka tangare, “Hello! Baba in ce ko lafiya? Ya ce, “Babu Imam. Yayanku na Zariya barayi.sun ‘ harharbe – su, a kafafuwansu shi da Jamila.” Ya yi zumbur ya mike tsaye, “Barayi kuma? Garin yaya? “Allah kadai ya sa’ni, an dai ce suna asibiti. Yanzu menene abin yi? . Ya ce, “Dare ya yi Baba, hatsari ne yanzu mu bi
hanyar Zariya, mu yi hakuri zuwa sallar asuba sai mu ‘
wuce, tunda suna asibiti, ai za’ su sami _kulawar gaggawa.” Alhaji ya ce, “To shi kenan. Allah ya kai mu goben,’ka gaya wa dan-Uwanka don Allah.”
Ya amsa da, to, kai tsaye’ wayar Mudansir ya kira ya shaida masa .abinda ke faruwa. Tsananin
mamaki ya hana kowannansu komawa barci. Haka can .
ma Tudun Wada, babu wanda ya runtsa, sannan ba’ su sami jin su .Sulaiman ba, saboda an yi masu allurar barci, don su kara samun saukin radadi.
Ana sallar asuba‘ suka dauki hanyar Zariya. Shi ya sa karfe bakwai daidai ‘a a‘sibitin ta yi» masu. Sun tsaya sun dauki Inna Mairo da su Raliya, suna kwance aikin imajansi, gwanin tausayi, amma bakin su bai daina sharara karya ba
Likita ya bada shawarar su wuce da su asibitin kashi na Kano, saboda kasusuwan guiwar su sun yi
dameji kwarai da gaske, suna bukatar ganin masana ‘
fannin kashi cikin gaggawa.
, ‘ Hankalin kowa ya kara tashi, take Imam ya cake kudin aikin da aka yi masu na gaggawa dubu goma sha biyar su biyu. Sannan ya dauki motar asibiti aka kwashe su zuwa Kano. Dole mata suka koma Kaduna, aka bar Murja kawai, suka bi bayan motar da ta kwashasu. Domin ko. sun‘je, babu abinda za su yi da ya wuce dan karan kuka. _ ‘
,- Wannan abin al’ajabi- da yawa yake.’ Sun kuwa tsunduma cikin mamaki da jimamin wannan al’amari, yaushe suka gama fargabar barayi? Ashe har yanzu suna nan suna bin su?’Wannan abu kamar cinne? Babu abinda ba sa sakawa cikin zukatansu, amma a karshe
dole suka bar wa Allah. .
duk Imam ne ya biya kudaden, sakamako ya yi ta yawo tsakanin likitoci, suna ta muhawara;’daga nanne suka zauna da su Imam ‘suka yi masa bayan’ ma’ haka. “A hakikanin gaskiya akan kasusuwansu
An yi hotuna kusan kala uku—uku kowacce kafa
ta
lalace da yawa kuma ga shi kashin guiwa, watau mahada zai yi wuya ba sai an yanke su ba …..
ldo waje Imam ya katse su, ‘haba Likita? Ya ce eh to, za su iya zama dukkan su,‘ amma ita kafa daya ta fi lalacewa. Za mu yi iya’kokarin mu, mu yi mata ‘yan dabaru a dayar kafar, idan Allah ya taimaka abin ya zauna.
Shi ke-nan, ita za ta iya samun kafa daya, ita ma ba za ta iya lankwasuwa ba. Amma shi namijin gaskiya hakuri za ku yi a yanke,don ko an bar ta rubewa 2a ta . yi, ta zame masa matsala, wanda a karshe dole a dawo a yankewa din.”- . .
Imam ya yi wuf Ya tashi ya fito waje, kawai ji ya” yi cikin zuciyarsa wani abu ya soketa fadi yace, “Inna- Lillahi‘wa-lnna-llaihir-Raji’un! Bai san lokacin da hawaye suka goce masa ba, wani tsananin tau‘sayi ke ratsa shi, bai taba sanin har yanzu yana son Jamila ba, sai yau. Ji yake kamar kirjin sa zai tsage. .
Mudansir ya zauna kusa da shi a sanyaye ya ce, ‘Yaya.’ Ya dago ido ya dube shi, “Yaya hakuri za mu .yi da kaddarafa Ya gage fuska ya cé, “Na yarda da kaddara Muda,amma tabbas’ muna yawo tare da makiyanmu, akwai matsala wani wuri,— dole ni da kai mu yi taka tsantsan tare da kara kaimi wajen addu’a.
Domin wannan alama ce ake’ nuna mana cewa kiris Ya rage azo gare mu, in ban son mugunta ba, . menene na nakasa mutane ba su ci maku ba, ba su sha maku ba? Kai Allah kai ne ishashshe. Ubangiji~ ka wargaza shirin duk makiyan mu.”
Ya ce‘ “Amin Yaya amin, amma don Allah ka kwantar da hankalin ka komai zai wuce, kuma babu wanda yake tsallake kaddararsa‘ in ta zo. mu yi masu fatan Allah ya sa wannan abu ya zama kaffara a gare ” su.” _Ya ce amin, yana goge fuska~ da hankici, ya numfasa ya ce, “Mece ce shawarar karshe? Ya ce
Kafafuwan za’a yanke dole. kamar yadda suka fada
tunfarko.” “Har da ta Jamila? Ya zura masa ido ya ce‘Yaya “na san ka na son Jamila kuma na tabbata hawayen da “ke zuba bisa fuskar ka na tausayin ta ne, amma babu wata dabara da ta wuce wannan. Hakuri kadai zai yi mana magani.’ .
Ya kada kai, ya ce “Hakika ina son Jamila, kuma na so ta natsu‘ ta yi aure ita ma ta dandana dadin gidan miji. Ban san me ya ’sa zuciyata ta ki karbar ta ba? Wata kila da tana gida na a killace. da ba ta zo yawon kWana a hotel ba,-har barayi su-far masu, su nakasa ta haka. Tabbas ina da ‘laifi .ina da hannu a cikin wannan al’amari, dole in roki Jamila ta yafe min.”
Mudansir ya sauke numfashi ya‘ ce, “K0 kadan ba ka da laifl Yaya. ai  Jamila ta yi maka laifin da za ka yanke’mata wannan hukuncin. Abinda na ke so da kai, shi ne‘ka tsaya a tausayinta kawai.kar ka zurfafa  binciken sanadin faruwar wannan al’amari, ina ‘mai tabbatar maka za ka kasa daukar kaddara.” Ya, dube shi yana kada kai ya ce, “Gaskiya ne. Allah ya ba su lafiya.” Ya ce, “Amin.” _
‘ Haka suka_ yi: ta zama jugun-jugun! Sai dai musayar waya da mutan gida.’Karfe goman‘ dare aka rubuta za’a yanke kafafuwan Sulaiman, amma an rasa wanda zai ‘gaya ‘masa. lta kuwa Jamila sai tara na safiyar gobe. Can gida Kaduna ma koke-koke ake ta‘yi, ina ga shi kansa. wa zai tunkare shi da wannan mummunan labarin? Balle Jamila da take ganin yanzu ta fara lokacin ta? ‘ .
-Alhaji ne ya‘yi ta maza ya yi karfin hali ya ja kujera gaban gadon da Sulaiman ke kwance, ya .yi masa nasiha mai ratsa zuciya, ya tuna masa imani da Allah da kaddara mai ‘kyau ko maras kyau‘. Sannan ya gaya masa abinda ke faruwa. Wata irin razanada ya yi, bai
san lOkacin da ya zabura ya tashi zaune ba, tare da fadin “Me? ~
Bakinsa ya kage, bai iya kara komai ba, tsawon lokaci Suna kallon juna da Alhaji, jiri ya soma dibarsa ya tafi yuu…. Ya koma da baya ya fadi bisa filo, take nan idanuwansa suka kade, hawaye ya cika su.
Alhaji ya kara matso shi ya ce, “Kar ka damu da yawa Sulaiman, wani ciwon ya sake kama ka. Ka yarda da…. Da sauri ya fara magana, .“A’ a Babe. Wallahi ban yarda ba, babu wanda zai yanke min‘ kafafuwa, kawai daga harbi? Ya ce “Ai ba kawai bane Sulaiman. Likita zai kawo hoton ka gani da idon ka, yadda kasusuwan guiwoyinka suka dawo…. _,
“Ni ban yarda ba, ban yarda ba, a bar min kafafuwan haka.” Cikin damuwa da tausayi yace, “Barin na su ba shi da amfani Sulaiman, sun ce rubewa za su yi ……
…Su rube din, babu ruwan kowa. Ai gara su rube in mutu da a maida ni musaki Atabau fa Sulaiman ya ki amincewa da shawarar Likita, kuka yake kamar karamin yaro, cikin zuciyarsa yake zargin kansa tare da tambayoyin da suka sanya masa hawan jini nan take, shi ya sa ma ba a gaya wa Jamila ba.
Shi namiji ma ya kasa daurewa balle ita? Menene abin yi? Gaskiya su Alhaji sun rasa na yi. lokacin na cika ana gwada BP din sa, jinin ya yi mugun hawa, don haka Likita ya ce babu damar a taba, sai jinin ya sauka.
can bangaran Jamila haka abin yake, ita ma jinin na ta ya hau, saboda tsabar shiga damuwar da ta yi, tun kafin ‘ma a gaya mata yanayin da kafafuwan nata suke ciki, haka suka kwana babu madafa. Kowa cikin
‘.tashin hankali.
Karfe bakwai na safiya, wayar Imam ke ta
bugawa. Bakuwar lamba ce, a gaskiya gabansa ya fadi,
dan daman can ya na samun kiran’ sababbin lambobi, amma tunda wancan al‘amari ya »faru, yake tsoronsu Haka nan ya‘ yi ta maza, ya dauka ya yi sallama aka amsa masa. ‘ ‘
Nan take ya dan ji sanyi‘ a ransa. “Ina fatan’da Alhaji Imam Yusuf nake magana? Ya ce, “Eh shi ne.” Aka sake tambaya “Mai kamfanin (Imam Farm Nigeria Limited)? Ya ce‘“Kwarai shi ne; ko lafiya?
Ya ce “Ka‘na magana da D.P.0 na yankin Zariya, akwai Wani case na wasu barayi da sojijin da ke shingen bincike suka kama su da manyan kudade a daran jiya, sun bada’ labarin kudaden ka ne, wanda aka ba su wata kwangilar sace mahaifinka…
Jikinsa ‘ya fara rawa, da sauri‘ ya katse, shi, “An ‘ kama, su? Suna ina yanzu? Ya ce “Suna ofishin ‘Yan sanda na hedkwata dake Sabon Garin Zariya, muna bukatar ganinka cikin gaggawa, domin su suka ba mu – lambarka kuma suka ce akwai bayanin‘da suke so su yi a gabanka.”
Ya ce “To ina Kano yanzu, amma Insha—Allahu zan taso ba tare da bata lokaci ba.” “Allah ya kawo ka lafiya.” Ya ce, “Amin, amin, na gode.” ,
_ Kowa a wajen kallonsa yake yi. Ya daga hannu sama ya ce “Alhamdulillahi! Allah mun gode maka.’ Ya dube su baki har kunne, “An kama su, an kama barayin da suka sace ka Baba.” Duk suka tashi da murna “An kama su? A ina? Ya ce “A Zariya, suna headkwata na Sabon Gari, zan tafi yanzu. D.P.0 ke nema na, don‘ ya ce an kama su da kudadaen.” ”
Mudansir ya ce “Ai sai mu tafi tare in yi maka rakiya. Baba da Anti sai su zauna.kafin mu dawo.” Ya ce “Ba laifi, mu je wajen Antin.” Suka bar wajen mota gsu suka nufi dakin mata, in’da Murja take tare da Jamila daki na musamman take. ‘
Nan lmam ya sa aka ba ta, shi ma Sulaiman din daki ‘na musamman din yake a bangaran maza, suka tura kofa tare da sallama. Jamilar na zaune jingine da filo tana wanke baki da burosh. Murja na rike da wata ‘yar roba tana zubawa a ciki.
Ta amsa sallamar su tare da fadin, “Imam kun iso? “Mun iso Anti, ya kwanan masu jiki? Ta ce, “Mun gode Allah. Baba ina kwana.” Ya amsa “Lafiya lau Murja, ya masu jiki? “Sun ji sauki Baba.”
Ya ce, “To Allah ya karo sauki.” Tace “Amin. Jamiia ma ta gaishe su, sannan Baba ya ce, “Wani labari mai dadi muka samu yanzun nan, wai ankama barayin da suka Sace ni, a Zariya.”
Ido waje ta ce “An kama su. Kai Alhamdulillahi”, Haka idanuwan Jamila ke hawaye ta daina wankin bakin, ta ,zubo’ masu ido, ta kalli wancan ta kalli wannan. “YaUshe aka kama su Baba?
‘ Ya‘ce “Tun shekaran jiya k0 lmam? Ya amsa, “Haka D.P.0 ya ce.” Alhaji ya ci-gaba, “Kuma an yi sa’a ba su taba kudaden ba. Ya ce suna hannu ofishin . Yanzu za su wuce Zariyar ne don gani da ido,” Fara ar Murja ta karu.
“Kai mun gode wa Allah, to shi kenan lmam sai kun dawo. Allah ya tsare.” Suka amsa da amin. Ya sa hannu aljihu ya ciro dubu goma ya mika mata, “Ki rike ,wannan Anti, koda za’a bukaci wani abu. Idan mun dawo za muci-gaba da shawara akan maganar nan.”
Ta ce,‘ “Shi kenan, an gode. Allah ya tsare.” “Amin. Jamila ki kwantar da hankalin ‘ki  Kuma sannu a hankali za’a kama wadanda suka aikata ma ku wannan abu. Kin ji? Hawaye suka goce mata, saboda ta kasa daurewa‘tsananin tashin hankalin da ta shiga.
Bakin gadon lmam ya zauna, ya zuba mata ido, “Haba-Haba don Allah me ya Akawo kuka‘? So ki ke jinin ki ya ci-gaba da hawa a kasa yi maki aikin? Bai kamata
ba, ki sanya imani a zuciyarki, na yi miki alkawarin sai inda karfi na ya kare wajen neman lafiyar ki, kin gene? Ta sunkuyar da kai, kwalla na diga. Ya sa hannu ya dago fuskar, ya goge mata hawayen, “Ya isa kin ji? Na ’ce ya isa haka, kalle ni ‘ Ta dube shi, ya yi dan murmushi ya ce ‘Akwai maganar da za mu yi, sirri ce, sai mun dawo za mu yi ta.” “Ok?. Ta amsa da ka, “To yi murmushi mana.” Ta
sunkuyar da kai .ba ta iya murmusawar ba. Ya inumfasa ya dubi’ saura ya ce.
“Za mu wuce.’ Ya tashi bai saurara ba; suka fice suna masu fatan sauka lafiya. lta kuwa Jamila hannu ta dora a kai, ta kara barkewa da kuka. Bakin—cikin ta daya, babu kafafuwan gudu, da ba su dawo suka same ta ba, don ta tabbata asirinsu ya gama tonuwa

naku har kullum

www.littafanhausane.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE