Makaranta duniya chapter18
Makaranta duniya
Chapter18
“Zakakan kalaman Alh. Abdul-Rasheed sun dade ‘suna shagaltar: da zukantanmu. Dasu ya yi amfani ya yaudaremu ya ci amanarmu! Kowa ya gani, ba sharri ‘ na yi masa ba. Har yanzu da wadanann kalaman yake sake bibiyar mu
.Sai dai ni anyi walkiya na ga fuskar munafuki. maci amana, ba zan sake yarda da shiba. Har kwanan gobe, ina jin radadin rashin ‘yan-uwanka, ina kuma kallon yanayin da’muka koma‘abin‘tauSayi.’ Sannan’ .. har abada ‘bazan daina ganin cin fuskar da ya yi min’
ba,’ka ga maganar yafiya ma bazata taba tasowa ba”.
Suka yi shiru. Hajiya Aliyaa tana maida numfashi. Bayan ‘yan dakikai Mansur yace “Umma ki yi hakuri, duk abinda ki ka lissafa, ni ma ina jinsu cikin raina. Amma ……
ta katse shi, “‘Ka . cire. amma Mansur dun kalmar zata aje’“maka-wasi wasi. Kanka‘ tsaye ka- zama mai kishi. Wannan shi ne tabbacin da na halas!‘ Ka ji ni da kyau? Shi dai da zuciyarsa ta‘mutu akan Alhj Abdul-Rasheed, ya yi ta sauke
Numfashi mai karfi ya sannan yace, “Allah’ya bi mana .hakkinmu. TaCe .”Amin! Haka nakeso kullun ’ inji daga gareka, Ma kazi da shi a leda’?” Ya jawo ledar ya mika’mata, yana fadin. “.Wallahi ban sani ba ni ma’ gwaggo Saude ce tace in kawo miki”.
Ta fidda kular ta bude, tuwon shinkafa ne Miyar zogalle. Tace “An godé mata. Bari in kai, inji ko‘zai ci. Kaima zaka cin ne?” Ya kada kai kawai. ba tare daya amsa ba. Ta yunkura ta tashi da kular ta shige cikin dakin, ta bar Mansur’ a wajen kamar yayi‘ ta kwarma ihu.
lta’ kuwa‘ kujera ta ja~ ta ‘zauna. “Abban. Mansur”. Ya .yi shiru bai tankaba, bai.,.kuma bude idonsa ba. Ta yi jim,‘ tana kallonsa kafin tace
“Tuwo na kawo maka Alhaji. Ka daure ka ci‘, kodan kadan ne”. Ya bude ido fuska daure. yace “Bana
bukatar’komai daga gare ki Aliyaa, da zaki koma daga
waje. kiyi zamanki,da zan fi shakar isasshiyar iska mai amfani gare ni”.
Haushi ya kamata, ta sakar masa ’yar harara tace. “Babu komai Alhaji, ai dama ba’a bakin komai ka daukeni ba. Amma ina, soka sani ni na ‘san muhimmancin ka a gareni…” Ya tari numfashinta, “Ba ki sani ba Aliyaa, da kin sani da kin bi umarni na. da ba ki dubi tsabar idona ba, kin ci wa aboki na ~ mutunci ba, amma ga hanya nan, idan abinda ki ke yi akwai riba, za ki tsinta a gaba
Ranta bace take kallonsa, wata zuciya” na zugata da ta tashi kawai ta fice ta ba shi Wuri‘. Wata kuma na tausaya masa kan lalurar da Allah ya saukar -‘ masa. Ta kada kai cikin damuwa, tace. . ‘
“Ni dai ban ce dole ka yarda da ni ba Abban Mansur, maganar da na yi, in ta bata maka rai, ka yi, hakuri. Ni yanzu bukatata, ka amshi abinci ka ci, don ya taimaka wa magungunan da ka sha su yi maka aiki
Ya yi shiru bai tanka ba. Hakan yaba ta damar ‘ zubo abincin ta ci-‘gaba da rarrashinsa har’ ta samu ya yarda ta gyara masa kwanciya, ta yadda zai:ji dadin cin abincin. . ‘
Ta ciyar da shi, sannu a hankali har ya koshi” ba tare da ya tanka mata ba, duk da cEWa shi kansa yana jin tausayinta, saboda ba ta kosawa wajen kula
da shi, kuma ya san duk abinda take yi.
Kokari take yi ta kare mutuncin iyalinta. kamar yadda ta fadi. Amma laifinta, kin yi masa biyayya akan umarnin daya ba ta. Me zai sa yace ta
bari, ta ki bari? Kenan ba ta ganin girmansa kuma bai isa ya hanata ba, ta hanu? Wadanannan tambayoyin kan sa shi yake ganin aibunta har’ ya kan ji baya bukatar taimakonta.
Kwanansa uku, ya dan murmurse Suka dawo gida saboda karancin kudi. Yanzu damuwarsa. yadda za’a samu ayi wa Murja kayan daki, koda gado da katifa ne kawai da ‘yan kayan za ta yiwa mijinta abinci. Hankalinsa tashe yake, tunda Baba Sallau yayi masa ‘ bayanin yadda aka yi da kudaden nan dole.
Shi ya sa yake kara ganin bakin Aliyaa, dun ita~ ce silar tafiyarsa asibiti. Kwana biyu tsakani. Malam Sallau ya kora san sa guda daya daya rage masa yana yi masa aikin gona.
Kai tsaye kasuwa ya kai shi, ya karbi kudin, saboda ya taimaki Alh. Bar’a’u, ganin yadda ya shiga damuwa akan kayan daki.
Ai kuwa ba karamin farin-ciki ya yi ba, kamar zai zubda hawaye saboda murna. Matan gida aka ba kudin suka tafi Katsina suka yo mata siyayar’ duk abinda ya dace, tun daga kan gado da katifa da kayan
kicin daidai gwargwadon kudinsu.
can cikin sasansu Malam Sallau aka ajiye kayan. Ko da wasa Aliyaa ba ta yi marmarin ganin kayan ba, balle ta sanya masu albarka.
Babu wanda ya kula saboginta, kowa neman yadda za ayi a fita kunya yake yi. Bayan kwana goma da fitowar Alh. Bara’u daga asibiti Murja ta dawo gida. lta ma ta shiga shire shiryen bikinta. Abinda ta, lura da shi. ‘
Ummanta ta kara tsanar ta. ko gaisuwa da kyar take amsa mata. Har dama-dama Yaya Mansur. shi ya sa ta fi zama tare da Abbanta. tana sauraraun hudubar da yake mata, akan zamantakewar aure
Haka zalika shirye-shirye sun yi nisa ‘ a bangaren ango. Duk da dai can ma akwai matsala ta kudi, sai dai su da sauki akan bangaran amarya.’ domin Alh. Abdul-Rashed ya jajirce wajan neman kudi.
Kuma Allah da ikonsa, duk inda ya aika masu da goron gayyata, sai an kawo masa gudummawa har zuwa yau daya rage sauran kwana daya daurin auren.
sancewar anan Kaduna za’a yi taron gidan dankare yake da mata har’ daga Dutsan Abba sunzo. Daidai gwargwado ana ta dora tukunya ana saukewa ma’ana abinci, bai yanke ba. ‘
,Washe gari jama’ar Alhaji suka taru da sassafe, wasu sunzi da motocinsu har sun kwashi wasu mutanan, ga kuma bus biyu da Alhajin ya dauka
shata, saboda kwaso ‘yan rakiyar amarya.
*********
Abu kamar wasa. ga shi ya tabbata an daura auren,
Suleman da Marja. Sasan Malam Sallau kam cike yake da ’yan-uwa da abokan‘arziki, domin can bikin yake.
Ta bangaren Hajiya Aliyaa kuwa, babu wanda ta gayyata, tun daga danginta har abokan mu’amalarta. Duk wanda yazo, ya zo don kashin kansa ne. Ai kuwa ta sha cancagwadi, musamman ‘yan-uwanta, amma hakan bai sa ta sauka daga tudun da ta hau ba. Babu Wanda ya sake kallonta, safgoginsu kawai suke yi, har aka daura auren, ‘
‘ Mansur kuwa Katsina ya tafi abinsa, dun kar’ ma ya ga yadda taron zai ka sance. Shi kuwa angon bakinsa, kamar zai tsage biyu, saboda murna .
Bayan daura aure, baki suka ci abinci, sai maganar tafiya da amarya. Anata kwaranniyar tafiya, shi kuwa Alh. Abdul-Rasheed yana tare da Alh. Bara’u. Farin-cikin zukatansu ba’a cewa komai.
“Burina ya cika Alh. Abdul-Rasheed, ko yanzu Allah ya dauki raina, na yi masa godiya, don ya gama – min komai, tunda ya nuna min wannan rana da na cika alkawarin da na dauka”.
Alhaji yace, “Haka zalika nawa farin-cikin baya faduwa Alh.‘ Bara’u, domin ,ni, kaina auren Suleman da Murja, shine cikin raina dare da rana.
Koda yaushe zullumi na ke yi kar a samu akasi. Ban
san me zai faru da Sulaman ba, saboda son da yakewa Murja. To Alhamdulillahl. Zullumi ya kare, abinda nake roko gareka, ‘shine kaci-gaba da rike min sirrin da na baka. Sannan ka taya mu addu’ar Allah yasa mu rike amanar da aka bamu.”
Yace “Ba na haufi Alhj Alad‘ul-Rashaad. in dal rikon amana ne, ina da tabbacin Murja ta yin sa’a. Sai
dai ku, ku yi hakuri da yarintar ta. Komai ta yi maras kyau, ku’ hukunta ta ko ina da rai, ballé’idan na‘ mutu. Murja ta zama taku har abada da yardar‘ Allah, Ni rokon da zan yi a gareka, shi ne don Allah da.Manznnsa, ko bayan‘raina Aliyaa ta bijiro da wasu.” halaye akan wadanda take nunawa yanzu, kar ku biye mata”. Yace “Me zai sa? Ai fatan ganewa muke mata a koda yaushe. insha-Allahu za ta gane nan gaba’”. Suleman‘ ya yi sallama dakin tare da wani abokin karatunsa Abdul-Salam, suka shigo. Shigowar tasu ce ta katse hirar tasu,-suka tsugunna gabansu. Alh. Abdul-RaShead na zolayarsu. “Angwaye Angwaye” ‘baki kamar- gonar auduga.
“Sannu Abba”. Ya-ce “An gaisheku angwaye. To mun gode_
Allah, tunda alkawari ya cika..Sai a kula a kiyayaye a kuma lura da yadda iyaye ke ta iya kokarinsu wajen tarbiya. Na san daga kai har Murja yara ne, amma ka fita hankali. Saboda haka sai ayi ta hakuri da ita, idan
ba daidaiba. ga Babanku nan, ba sai ka taso zuwa inda nakeba. Ka ji‘ko Suleman?”
Kansa sunkuye ‘ya amsa, “Na ji Abba, kuma lnsha-Allahu zan kiyaye. Na gode Allah ya kara maka lafiya”.,Duk suka amsa da ‘Amin”; “To yaya?” inji. Alh. Abdul-Rasheed. Abdul Salam ya amsa ‘Duk an gama shiryawa Baba, kowa yana mota”
Yace,”To bari mu zo mu‘yi harama. Alhaji mun barka lafiya, sai an kwana biyu Zan dawo‘lnsha Allahu”. Yace- “Ba laifi. Allah‘ya tsare. “Ya- sauke ku lafiya”. Suka amsa da’ “Amin”, Su Suleman suka yo gaba, suka bar su suna kara musabaha.
Motoci suka mika da amarya tare~da ‘yan rakiyarta, ko ‘dama tun safe motar kaya_ta fara yin gaba. Kuka kawai Murja,.ke ta faman yi, musamman idan ‘ta tuna harta baro gida mahaifiyarta bata sa mata albarka ba. ‘
A. lokaci guda kuma tana yiwa kanta tambayoyi. “Yaushe Umma za ta gane? Yaushe za ta bi Abba, ta yi.yafiya ga Alh. Abdul—Rasheed?” Taci-‘gaba da sharankwalla ana rarrashinta dun kar kukan ya jawa mata ciwo ” _
‘isowar amarya bayan sallar magariba, gida ya kara rincabewa. Akasanya amarya dakinta. ciki da falo ne manyan gaske ne, ‘ka na ga bayi a cikinsa. Gaba daya dakunan manne suke da tayles‘din roba, domin shi ‘ake yayi a wancan lokacin. Shiya sa ma” ledar dakin da aka‘siyo mata ba ta yi amfani ba.
Dai dai gwargwado dakinta ya. kayatu. Shagali ya ci-gaba har zuwa washe garin lahadi. Aka ,koyi budan kai, zuwa azahar suka‘gama shirin komawa gida. Ba tare da bata lokaciba Alhaj ya samu mota madaidaiciya, ta kwashe su, suka bar amarya na kukan rabuwa da ‘yan uwanta; ba don‘ba ‘ta farin-ciki da gidan data shiga ba, sai don sabo.Sannu a hankali, gida ya‘ rairaye, babU’saUran baqi daga gwaggo, sai su Raliya da Asabe kannen Suleman. Sune ma ke ta hidimar taya’ Hajiya Suwaiba gyaran gida, yayin da gwaggo ke tare da Alhaj Abdul— Rasheed’a falonsa. lta dince’ke fadin. ‘
“Tuntuni na keso na tambayeka,~~ban samu sukuni bane. Na ga har aka yi sha’anin nan ‘aka ‘gama ban ga motar. ka ba, me yafaru da ita?
Ya dan ‘dUbEta,” yayi murmushi,’ “Gwaggo kenan”. Tace “Akwai magana, ba’ka son fadi ko? To ai na’gane”. Ya-ce “Me ki ka gane? Ta-ce “Ka siyar, ka yi hidima ko?” ‘”Murmushi yake tayi‘ Ta kada’kai, tana masa duban tausayi.‘ “Me yasaba _ka shawarce ni ‘ba?‘ ‘Yar motar da ta rage maka take‘rufa maka asiri, ita‘ka kama ka’siyar’?” ” ‘ Yace ‘”Ki daina tone~tone Gwaggo, mota’kam ta rufa asiri,’ tunda ,an fita ‘kunya.’ Fanta’mu kawai ‘ Allah ya zaunar’ dasu lafiya
A sanyaye tace. “Ai shi kenan, amma ka san ka karowa kanka aiki ko? Sanin kanka ne Sulaiman baya aikin komai.
Ga karatunsa, ga na matarsa. a cire batun Ciyarwa, w. Ni da ka Shawar ceni da nace ka bar motar nan. shi Suleman din Ya rinka kabo kabo da ita. duk lokacin da ba shi da. karatu”. ‘
Ya ‘numfasa. yacé gaskiya ne, duk, abinda habba ya hango Yaro baya taba ganinsa yace ida nuna ne ya rufe. bana ganin komai, face in ba Aliyaa kunya akan kayan lefe.
Shi yasa na siyar da ita, na. yi maganin abinda ke damuna. Kar ki damu gwaggo shi komai na Allah ne, cike da tausayi tace, “Haka
‘ ;Allah yai maku alharka. amm da ina ‘ganin da ka
‘, koyama Suleman sana’ar hannu. Dale ya san yaddé Zai nemi na kansa”. _Yace “Kin ‘fadi gaskiya gwaggo, da yardar Allah zan san abinyi”. Sun jima suna’tattauna abubuwa masu dama.
‘ Shi kuwa ango sharholiyarsa yakeyi, tun lakacin da ‘yan rakiyar amarya suka wuce, yaketa zar’ya ‘ wajen amaryarsa, Zuciyarsa kamar gonar auduga, gani yake tamkar mafarki yake yi. Bayan sallar’ isha’i. Hajiya Suwaiba ta yisallama dakin
amarya, suka amsa ita da ango. Ta shigo cike da
fara’a. “Ango kenan! To a taso Babanku ke bukatar ganinku”. Kanta sunkuye ta amsa da “To”, Shi ma angan hakan ya fadi.
Ta wuce, Murja ta dauki mayafi ta rufa. Angon
nata yana gyara mata, ya’ rufe mata fuska, “Haka ku kayi ko? Ku na ganin hanya kuwa?” – ‘ Ta dan dube shi tana murmushi, ta wuce ya
biyo ta, yana ‘yar dariya. Shi ya fara shiga falon, duk suna zazzaune ‘har’ da kannensa. ‘.
Asabe ta yi azama ta mike ta kama maYafin amarya, tana fadin. “Dadi na dake‘gwaggo kin faye kishi. Maimakon ki tashi da gudu, ki. kamo ‘mana amar’yar‘ mu? Sokike ta fadi ko?” .
Gwaggo tatabe baki tace, “Au ai ban san makauniya bace”. Duk suka’fara dariya. “.Haba ‘sai‘ka’ ce wata ke?” lnji angon Maganar gaskiya, idan ba makahoba, wa akewa jagora?” ‘
“Zancen ki dutse ‘gwaggo Har dake Mamanmu” lnji Suleman, Alhaji yace, “Ita ma ta” dana ne. To’Alhamdulillahi, kowa ya dube mu, ya‘ san muna cikin‘ farin‘ciki, saboda haka mun kara ‘yiwa Allah godiya
Daganan zarce wa_ yayi ‘da nasiha garesu, watau angon da amarya, inda ya fi‘jawnlo hankalinsu akan rikon amanar juna. domin idan amana ta tsaya. tsakanin ma’aurata, tabbas zaman lafiya.zai samu wanzuwa kwarai da gaske. ‘ ‘
Hajia Suwaiba ma tayi nata jawabin” akan girmama na gaba da biyayyar miji. Sannan gwaggo ta fi bada karfi akan Suleman ya koyi sana’ar hannu, dun tallafawa kansa, kafin aga makomar‘ karatunsa. Kowa ya jinjinawa shawarar‘ gwaggo, har da angon kansa. amma Shi tunaninsa ba karamar sana’a ba.
Kamar’ yadda Gwaggo ke tunani, koda ta kawo maganar da an bar motar nan, ya rinka yin kabo kabo. dariya ya yi cikin rainsa yace, Sai dai ya siyar da ita. ya .bude wani katon shago.
“Uhm… Suleman kenan, baYan’ kowa ya gama tofa albarkacin bakinsa. Suleman ya yi godiya kuma ya yi alkawarin kula da matarsa, don ba mara’da kunya’
Sun jima nan Sana hira. sannan suka koma dakinsu koWa ma makWancinsa ya nufa don hutawa. Suleman ya baje wa amarya kaji da Yugot masu sanyi.
Ya yi ta rarrashinta da‘kalaman kauna, har ta danci kadan, ya bata Yugut ta sha ruwa. ‘Komai cikin kunya take yinsa. kamar ta’ shige cikin kasa. Shi kuwa dan gogan, kunyar ma kara burge shi ta yi, ta kara’ masa shaukin. sonta.
Ya kuwa nunar mata tsatsar’ yadda yakeji cikin ransa, bai iya boye‘mata komai ba, har ita kanta ta
fara jin tsoron kar angonta ya haukace a daran yau. lol
Amma sai ta ga ya tashi tangaran! Da asuba yai wanka. ya yi sallah. Shi yasa ta yi ta satar’ kallonsa. yana ba ta mamaki, zuciyarta na kara son angonta.
Bayan hada-hadar- karin safe, misalin karfe goma su Gwaggo suka yi ‘niyya. Nan ma Alhaji bai bata lokqciba , domin mota ya dauka masu har gida ta kwashe su. kuma har kofar gida za ta aje su.
. cikin yardar Allah sun sauka lafiya. Su Raliya sai da suka tsaya suka gyaraWa gwaggo gida, suka wanke mata kayayyakin da suka yi kura, tare da sauya mata ruwan randunanta dake cikin gidan kaf Sannan suka wuce gidan Innar su, tana ta sanya masu.
albarka: ’-
Inna Mairo ta yi ta murna, nan take suka bude . mata faifan biki. Ta zabga tagumi idanuwanta taf! ‘da kwalla jin news aShe har motarsa Alhaji’ya‘ siyar – saboda hidimar bikin. Ta numfasa tace, “Me zance wa Yaya a duniya’?
Kai! Allah na gode maka da ka ba mu Dan-uwa’ mai kaunar mu”. Ba ta iya jurewa ba, hawayenta shar! suka zubo bisa kuncinta, .tana fadin “Allah ka yi masa sakayya da alkhairi”. r,
‘ Su kansu su Raliya jikinsu ya mutu kwarai’da ‘ gaske. A raunane‘ suka amsa “Amin Inna”. Ta ,goga kwalla tace; “Kuje akwai abinci ku zuba har da gwaggo sai in kai mata, idan na dawo, kowacce ta kama hanyar gidan mijinta’”. ‘
Suka amsa da “To”. Asabe ta kawu abincin Gwaggo cikin langa. Inna ta yafa gyala, ta dauka ta ‘wuce gidan. Har barci ya fara dibar ta. ta tsinkayi sallama, ta amsatana tashi zaune. “Lale da ‘yan biki”. Tana murmushi. tace “Mairo ce?” “Ni ce gwaggo”.Ta karasa shigowa Cikin dakin. “Su gwaggo amare”.
Ta yi murmushi tace,» “Na bar mata amarcin, na ci girma”. Inna -tace Ya kamata. To an dawo lafiya? Ya taron? Ya aka baro su’?” ta amsa; “Duk lafiya lau”. Tace Allah saka wa kowa da alkhairi, ya bar mana zumuncin mu””Amin””. Ta tura mata kwano gabanta. “Ga abinci gwaggo. dambu ne”. ‘ –
Tace “Shake ‘mai hadama”. Ta bude kwanon ta sa-hannu da Bissmillah! Ta fara‘ci, “Ai kuwa- yaii “ gyada”.‘ Tana murmushi ta debo mata ruwa’ta‘aje gabanta. Bayan ‘yan’ dakikai. Inna tace, Yaya yayi kokari. Allah ya bar mana shi’.
Tace, ““Amin -. Ta kara gyara zama ta sake fadin “Ashe har motarsa ya sayar Gwaggo?” Ta dube ta da kyau.tace. ‘
“Uhm ….. Ni ma ban sani ba WaIIahi’, ashe tun lnkacin hada lefe ne Ni kam daya shnwarce ni, da bai
siyar ba, daya barwa Suleman din ya nemi kudi da
ita
Tace “Wallahi kuwa, yanzu ‘shi ga mata. ga ‘bahu sana’a, nauyi dai ya kara yawa. ga-Yaya, Saidai mu yi ta ta ya shi addu,a; Allah ya dafa masa”. Gwaggo tace, amin
Alh. Abdul—Rasheed ya dawo cike da farin-ciki, ya zauna gaban kudin. Ya sa hannu ya dauka. ya jujjuyasu, yace a ransa “Alhamdulillahil Kudin tafiya Sun samu”. Yana shiga gida, ya labarta wa Hajiya Suwaiba cewa ya samu kudin tafiya, saboda haka nayi niyya, idan Allah ya kai rai gobe zan tafi.
Ta yi masa fatan alkhairi da addu’ar Allah ya – ‘ kai shi ya dawo da shi lafiya. Washe gari ya yi shiri‘ tsaf Yayin Ida shi kuma Sulemar ya gama shirin tafiya makaranta. – ‘
Ya shigo tare da sallama, ya gaishesu. Ya yace Baba yau fa ta kulle”. Ya dube shi yana murmushi. ‘Tafi Ai kuwa kai kadai‘ta‘ kulle mawa. ni aljihuna tab yakE”.
Suna dariya’ yace, “Don Allah a bani ba mota Babana”. Ya zurahannu aljihu ya fiddu bandir“ daya. ,Suleman‘ya ware ido yace,’”‘Lallai, Baba’ cikin kudi kake
‘ Yace “Ni ma jiya na same su albarkacin aurenka. = Tsohon’ ‘ Sakatare na ya kawo min gudumuwarsa. Dama ina‘tunanin idan Allah ‘ya dawo da ni lafiya, dan abinda: ya rage a hannuna’zan ba ka. ko ‘yar ‘tire’da ce ka fara juya kudi. ka na samun taro,da sisi. Ko kuwa?”
Yayi wani bazawarin murmushi yace, ” Hmm! Baba kenan,_‘ina laifin kace a hada ‘ min dan “kiyus madaidaici a , cika -shi ‘da ka’yan, masarufii’, ai za’a fi samun. riba”.~ dukkansu baki bude
suke kallonsa, kafin Hajiya Suwaiba ta riga magana! “Me ya kawo dogon buri Suleman?”
Alhaji ya amsa. “Ni ma dai shi na gani. Ka na nufin ba za ka iya zama gaban tebur ba, sai cikin shago?” _ . . Ya mirgina kai yace. “Ba hakana ke nufi ba Wai na ga in zaka roki Allah; aka ce ka rokai da babban masaki”. “Idan ka na da babban masakin ko?” Hajiya Suwaiba ta tambaya, ka na ta nunu shi da yatsa.
“Suleman! Suleman kar ka dauki wani kaya, ka dora wa kanka wanda nauyinsa zai dameka har ya yi maka illa. Ai sannu ba ta hana zuwa’kuma’guntun gatarinka, yafi ,sari, ka ba ni. Ka gane hausa‘ ta?” Fuska yamutse yace, “Ni faba wani abu nace’ba Mamanmu…” ‘
Alhaji ya cafe “Mun ji, tunda ka gane kuskurenka, sai ka’ tashi ka tafi makaranta. Ungo wannan Naira dari Ce, na san za ka kwana biyu, idan har. ka na lallabawa. Amshi”,
‘ yasa hannu ya karba,‘ fuska babu walwala yace, “Na gode, amma ku yi hakuri,idan maganata‘ ta bata maku rai. Sai ka dawo ka gaida mana Abba da kyau”. a sanyaye ’Alhajin ya amSa, “zai ji”. Suleman ya mike ya fice. Hajiya SuWaiba tace “Yaro dai, yaro ne,‘ in banda abin .Suleman ba da rarrafe kowa ya yi tafiya ba?” Yace,._’-‘Kyale shi, na. gane Suleman da sauransa. Raina sana’ar yayi.
Ya dan kada kai. “Matsalar ‘ya‘yanmu kenan. da zarar sun fara Jami’a, sai girman kai ya hau masu. Su rinka ganin sunfi kar’fin kananan sana’o’l, alhali abinba haka yakeba”. Tace “idan shi baya so a siyowa matarsa ita ta rinka yi a cikin gida. Ko kuwa?”
Yace “Haka ne, babu shakka yarinta na damun Suleman. Amma kin’ san wani abu? Zan siya kayan tiredar kuma dole ya zauna”; ‘ Ta yi dan murmushi tace. ‘ . ‘
“To, Allah ya bada sa’a”. Yace “Amin”. Ta. mike ta kawo masa abin karinsa. Imam ya zosuka ci tare. Ba su kareba. Suleman ya sake shigowa yayi masa sallama, ya wuce makaranta,
Bayan‘sun ,kammala cin ‘abincin, ya sanya ‘ babbar» rigarsa, ya dora hula, ya‘ zira _takalmansa, yayin da ~shi ma Imam yake tsaf! Cikin kayan makaran‘tar sa, don haka tare suka fice daga falon. Alhajin ya dubi Imani yace, “Shiga ka kira min Antinka”. Ya ruga Ya kirata, suka fito tare.
Ta tsugunna ta gaishe shi, ya ‘amsa cike‘ da fara’a. “Zan wuce Kankiya lnsha-Allahu, meza’a ce wa mutan gidan?”. Fuskarta kamar gonar auduga tace, “Ina gaida su duka. Acewa Abba ya jikinsa?’ Yace “Zasu ji. Ina fatan ba kya bukatar’ komai?” .
Ta kada kai _tace, “Babu komai Baba . A dawo ‘lafiya. Allah ya‘tsare”. Ya amsa da “Amin”. Daga nan ya wuce rike da hannun Imam. Hajiy‘a Suwaiba na biye
da su, tana fatan alheri har suka fice. Ta juyu gida, shi
kuwa makaranta ya aje Imam. sannan ya nufi inda zai samu mota.“ Ya iso Kankiya karfe daya da kwata. sai da ya
shiga wani masallaci, ya yi sallar-azahar ya fito, ya wuce kasan wata katuwar bishiya. Jama’a ne birjik! Fulani na ta damun fura.
Kusan wajen hada hadar fura da’nono kawai akeyi. Alhaji ya yi‘ masu sallama, suka amsa, Sannan ya yi maga‘na da masu furar’, yace ‘a dama masa ta Naira ashirin. ” .
Ya nemi wuni ya zauna, yana jira. ‘Kafin wani‘ lokakci an dama_ masa furar da lafiyayyen nono. Ya’sha. ya dura ruwa, ya yi hamdala, kafin ya shiga cikin gari, ya karasa gidan abokinsa da ‘ kafa. _ ‘ ‘
Yai sallama kofar sasansu’ sau ‘uku. ‘kamar dirar minkiya, yaga Hajiya Aliyaa a gabanSa, fuskarta ba yabo,- ba fallasa take amsa’sallamarsa. Sai da gabansa ya yi mugun‘faduwa, har ya kaiga’ya zura mata ido. ’
“Sannu da zuwa, shigo mana”. Mamaki cike da fuskarsa ya shigo, ta wuce yana biye da ita; Tun yana zancen zuCi ‘har ya fito fili. “Hajiya Aliyaa? “dan Allah!” Ta waigo ta dube shi, “Ka na mamaki ko?” Yace “Ba dole ba”.
Ta dan kada kai, “Ai komai na iya sauyawa Alh. Abdul-Rasheed, musamman idan’mutum yayi dogon tunani, ya gano kuskurensa. ‘Kar’ in- jaka da tsawo.
shigo daga ciki don maganar bata tsaye ya numfasa gamida yinma Allah godiya cikin ransa dakin Nata ta shige – tana fadin “Bimillah. mutumin naka ai ya dawo nan ne tunda yai mubaya,a yace ai haka akeso ‘ Ya ‘shiga dauke da’sallama yace “Ina Alhajin ? Ta sanyaya murya tace “Tsakani da Allah Baban Mansur na dakinsa yana barci. amma so nake mu yi magana ta fahimta akan abubuwan DA suka faru. Ya dubeta ido waje’ -yace daman kina jiran zuwana ne? Ban yarda da keba Hajia Aliaa sai dai Ki sani Allah ha zai bari ki cimma burinki a kaina ba, Aimu ba yara bane. duk maganar DA kikeson fadi muje Ki fadeta a gabansa ya Kama hanya yana shirin fita Tasha gabansa
. ldanuwanta duk sun juye. donta tabbatar DA ya fahimci manufarta innalillahi wa inna ilaihirrajiun ya dinga karantowa a zuciyaraa don ya tabbata ya fada hannun Hajiya Aliyaa. Allah ne kadai
zai iya fidda shi. Da ya ga ta yi tsaya, ita ma tana tunanin mafitar ta, sai ya kwantar da murya yace.
“Ki ji tsoron Allah Hajiya Aliyaa, ki sani sharrin da ki ke kokarin kulla min. ba shi ne mafitar ki ba, illa ya tara miki dalar zunubin da ba zaki lya saukewa ba a gaban Ubangiji. ‘ ‘ _
Na yarda,~ na amince wa kaina, na riga na fada tarkon ki, tunda gani cikin dakin ki, amma ina rokon ki don girman Allah ki kubutar da ni, ni kuma na yi miki alkawarin ba zaki’sake .ganina cikin gidanki ba.
Ta yi‘ dan murmushi tace, “Me yasa kayi saurin karaya? Ina cewa kai namijin duniya ne Wanda baya gezau ga duk! wata barazana ‘a rayuwarsa! Amma ka ban kUnya. “Magana kawair nace zamuyi duk ka rude ka na ‘yar‘ murya, a zatonka wasa na ke yi? Ka na gani kamarba zan iya aikatamaka komai ba ko? Wallahi ka yi kuskure. yadda na tsane ka, zan iya tsirara in maka ihun kwarto da rana tsaka!” ya runtse’ ido, ya fara fadin ,”Inna-LiIIahi’WH- lnna-llaihin-Raji’un!” Farin-cikin abinda take’aikatawa, yasa take daga murya,‘ba tare da ta sani ba. Ta kece da dariyar mugunta, kana ta nunashi DA dan alhaj abdurrasheed yau ka shigo hannun uwar shaidanu hajia aleeeeeeeeeeya
hehehehehehehe DA alamun akwai rikici kenan donjin yaddah lamarin zai kasance saimu hadu later
naku har kullun
The (O I C ) of littafan Hausa zallah @fcb page
www.Facebook.com/abdullahi.Ismail.salanke