Makaranta duniya chapter19

Makaranta. DuniyA

            Chapter19

yasa take daga murya,‘ba tare da ta saniba  da dariyar mugunta, kana’ ta nu’na .shi da yatsa tace kaci sa,a har yanzu banji motsin wani ba Da Wallahi tallahi babu-‘abida zai hana  aiwatar da :abinda na  kudurta cikinraina damanTunda “na jiyo sallaman-ka, wannan dabarar’ta zomin Wanda nake ganin ita~ce .damata ta karshe Ka
kuwa babu tabbacin zan iya bari ta kubce min, sai dai in banji motsin wani ba”.
Ya sauke numfashi, har’ yanzu neman tsari yake yi wajan Allah, shi ya sa wasu maganganun nata ma bai ji su da kyau ba. Suka yi cirko-cirko tsawon dakikai biyar. kafin yace, “Ki kyaleni na wuce Hajiya Aliyaa, da sunan Allah nake rokonki, ba dun na isa ba”. ‘ ‘
Tace ‘Hmmm… Yaro baisan Wuta ba sai ya dafa. lna fatan wannan zai zama gargadi na karshe a gareka! Kawai ban son ganinka, ba na bukatar ka kusa da mijina Ka kyalamu mu sarara, wata kila mu manta da fuskar ka, ,mai tsananin muni a zukatanmul ldan  kunne yaji…
Ta wuce uwar “dakanta ta bar shi jiki babu laka, sai dai da saurinsa’ya fice‘ya bar gidan, ba tare da ya nemi’ ganin abokinsa ba. Zuciyarsa cike da godiya ga Allah daya kubutar da shi daga kaidin Hajiya , Aliyaa. Kai tsaye tashar mota ya nufa, ya yi sa’a motar-dake lodin Funtuwa mutane: biyu.kacal Ake nema;  cikin lkon Allah su biyun’suka iso a lokaci guda Don haka bahu bata lokaci mota ta tashi. Alh. Abdul-Rashead zaune yake cikin tashin hankalin da bai taba tsintar kansa ciki ba.
Musamman daya ‘ tuna kalaman Aliyaa.‘ “Wallahi tallahi yaddah na tsane ka zan, Iya iya tsirara in maka ihu kwarto”Ya kan ji kamar ransa zai fita,“‘saboda bacin rai. ‘lta kuwa Hajia Aliyaa‘“ ‘bayan; ‘ ta’ gama nishadinta da farin-cikin da take ciki Tashi ta yi ‘ta nufi’ dakin Alhaj Bara’u; don lekoshi kamar yadda ta Saba; ldan biyu tayi  ta hangoshi wasu hawaye na ‘kwarara bisa kuncinsa, har suna
sauka bisa matashin kansa. ta zauna gabansa,
‘ “Baban ManSur’ka TAshi’ yajikin
ya’motsa maka ne?” Ya .dubeta’da kyau na tsawon ‘lokaci,~ _ tamkar ba’zai ce da ita komai ba; kafin yacé, “Aliyaa
Aliyaa!!’ Kiji tsoron Allah, ki daina biyeWa. abinda zuciyarki ta zo miki da shi’Tace, “Me na yi Baban‘ ManSur’?” Yace “Ni dai na ‘gaya miki. watan kunyarki ya kusan tsayaWa’ kuma‘ zaki yi tagumi; idanuwanki‘ 2a Su zubda. haWaYe
masu zafi‘ ’ ‘ Ta‘muskuta fuska cunkushe tace, “Ban san
me na’yi maka ba Baban Mansur’, ya kamata ka gaya
min laifina. kafin ka gaya min. duk ‘kalaman da ka ke_
son’ fadi”.‘Yace “Duk’ na ji kalaman dake ta fitowa’ dakin ki dazun kUma na tabbata ba da kowa kikeba.
‘ Face aminina Alhj. Maganganunki sun ba ni kunya Aliyaa, kuma‘ sun ,daSa min Wani sabon ciwo a zuciyata Wanda“ na ke ji ‘a jikina a yau zan bar gidan ‘duniya’kamarki A’liyaa alhaj
_ Abdul-Rasheéd. _
da girmanki_da kamai, ‘ki ke cewa zaki iya tsirara! ‘ Tsirara fa?”
Ya kada kai, hawaye suka kara kwararo masa,- wani irin daci ya .mamaye bakinsa,‘ “Ban taba zaton rashin kunyarki ya kai haka ba. Kin ci mutuncin aure kin zubda‘kimar ki. Da wane  bayani zaki. gaban Ubangijinki? ’ Tabbas kin ‘zaUce Aliya’; duk darcewa na san kin’dasa ‘wa~abuloki na tashin hankali; tamkar yadda’na kejiTa yadda na ji takunsa, yayin da yake , fita cikin gidan‘nan‘. Allah kadai ya san halin da yake ‘ ciki_ a yanzu. Amma ba zan bar aboki na ya dauwama cikin bakin-ciki ba, alhalin yana da gaskiya.
‘ Na san ya haneni da fadi, sai dai yau ya zama ‘ wajibinana gaya‘ miki kafinna mutu, dun karki zama mai .alfaharin abinda kika aikata a gareshi.‘ Saboda. ” haka ki bude kunnuwanki’, ki saurare ni
Sannu a hankali ya warware mata kamai Muna- munar ‘da ‘suka shirya- wa‘Alh. Abdul-Rashee’d ‘shida~ Mr. Balugun. Bai boye komai ba, har da sirrin‘dausuka ‘ yi’a asibitii inda shi Alh. Abdul-Rasheed din yace wa Alh. Barafu’ karya gayawa iyalansa ..komai game da zance’ A karshe yace “Dama’nasha gaya miki wata ‘ ‘rana za kiJi kunya Haukar banza kikeyi akan hujjar da ba ta da dalili. da tun farku kin  girmamani kin
dauki shawarata da baki yi nadama ba.
. – Amma ‘da yake kwakwalwar kifi gareki, sai kika kasa gane habaicin da na rinka yi miki. Babu abinda ‘ke zuciyarki, sai son ki dauki fansa. Wa ya gaya miki ciki da gaskiya wuka na‘ huda shi?‘ Wa ya ‘gaya miki ,
“ fadan da babu hujja, akwai riba?” ’
‘ ‘Ya dan jima yana sararawa, kafin ya ci gaba,
Wallahi kin min abinda zan’ sallama ‘aurenmu, abu ‘ daya yataimakeki, komai kin‘yi shi a cikin duhu ne,
amma tunfarkoda’ naCeki  bari, me ya sa ki ka ka‘sa
bin;umarnina?”Hakan yana nufin’ban isa dake ba?” Ya yi shiru yana
duban‘ yadda ta’ muzanta tashi guda,ta Fara kuka-_.ta kasa cewa komai. .
jimawa kadan ya katse shirun. “Kuka ba zai yi‘ -‘
miki-ba; domin ni ma na yi shi,’ kuma’ bai yi min magani ‘ba, .sai- dana rike hannun abokina na. bayyana
na nemi gafara gareshi sannan na samu sassauci
‘Saboda’haka na bar miki wasiyya, idan har ya samu
zuwa jana’iza ta. ‘Ki gaya masa ya yafe min, ,don ‘tona sirrin da yace bai yafe ba, muddin na gaya ma wani. Ba da gangan na ‘yiba,  ita kadai ce mafita, don ban san me zaki aikata a nan gaba ba bayan raina. Wata kila ki fiddo‘Murja‘ daga‘ gidan‘mijinta. Laifi mafi muni a gareni, wanda ba zan’taba yafe miki ba”;
Yana sa aya, ta mike da sauri ta fice cikin kuka mai razanarwa. Dakinta ta fada ta yi kukan da ba adadi. Lallai kam yau ta gane abubuwanda mijinta yake gaya mata. Hasalima ta gani zahiri, duk wanda baiji bari ba. zai ji hoho
gashi tsananin kunyar da yake gaya mata, ta sa’shi kansa ta kasa‘ kallonsa, balle ta furta wata kalma. Da wane ido za ta kalli Alh. Abdul-Rasheed? A yadda take ji a halin yanzu, har’ karshen’ rayuwarta ba ta fatansake hada ido da Alhj Abdul-Rasheed.
La’asar’ ta wuce, ba ta ma‘san ta wucan ba saboda tashinhankalin da take ciki. ldanuWanta sun kumbura, tunaninta kawai ‘ta wacce siga za‘ ta fuskanci mijinta zuciyarsa ta sanya‘ya? Wannankalma za ta gaya masa, ta’shafe duk kuncin dake zuciyarsa?
Kamar saukar’ aradu ta ’jiyo muryar Mansur yana kwala mata kira. Ta mike ‘a firgice ta yo waje. kiris! Ya rage, su gwabza karo. “umma kin ga Abba kuwa’?”
A tsorace tace, “Me ya yi’?” Ya juya da gudu, yana fadin.’zoki gan shi fa Umma” llahiirin jikinta rawa yaka yi, suka shige, ciki. Idanuwan sa kafe suna‘ kallon sama 
Ta yi tsaye ta ‘zuramasa ido, yayin da Mansur ya zube gabansa, ya kamoshi “Abba!” gaba daya ya ‘ biyoshi sharaf! Ido waje. ya dube ta, “Kingani ko?” Tace, “Bari asa masa ruwai, ka san ya saba-yin haka”.
‘ Ta juya ta nemo ruwa suka yi ta shafa masa, amma shiru ka ke ji.
Mansur ya natsu, ya kara kunnensa bisa kirjinsa, bai ji alamar’ numfashi ba. ‘Ya tattaba ko’ina inda akejin tafiyar numfashi, sam ko alama babu. Ya koma dirshan! Ya zauna yace. “Shi kenan! Shi kenan Umma!!” ,
Tace “Kayi shiru Mansur, ba mutuwa.ya yi ba, ‘Mutumin da muka gama magana da ‘shi yanxu Ka’ san ya saba irin wannan doguwar sumar”. Ya yunkura— ya mike—ya yi Waje, ya’ bar ta nan ido waje
‘Tana kallon ikon Allah; Hawaye na sauka, amma zuciyarta ta kasa amince mata mutuwa ya yi. shi ya sa take ta  fadin, “‘Yanzu fa muka gama magana Baban Mansur”;
_ Kafin”wani lokaci,’. mutuwar‘ Alh. Bara’u ta yi ‘tambari a gari, yayin da ‘yan-uwa ke ta hada-hadar yi masa: sutura. Hajiya Aliyaa ganin abin take‘tamkar mafarki take yi. ‘
: Kuka wurjanjan! Take yinsa, babu abinda yafi _ damunta, face yadda ta bar. dakinsa ba tareda ta – rake shi gafara ba, duk tsawon lokacin da ya kwashe
yana karanto mata tarin laifukanta.  .Shi yasa ta rasa ina za ta tsoma ranta, Sai ‘kuka takeyi tana faman fadin. “Ka yafe min Baban Mansur!” _ .
_ Kwakwazonta ya yi -yawa har ta fara‘ ba mutane haushi, saboda tana wa Mamaci kukan daya
take hakkin shari’a. don haka manya suka yayyameta da masifa dole. ta lafa, ta shige uwardakan ta, amma Allah kadai ya san halin da zuciyarta ke ciki. .
Bayan an kammala hada shi. aka rarraso ta dun ta zu tayi. masa addu’a. Tana Zuwa.ta kuma zubewa, ta ci-gaba da .fadin. “Ka‘yafemin Baban Mansur Babu shiri aka fita da ita. ‘
Take ta” fara jefa zargi cikin zukatan mutana?
suka fara tunanin‘ wane irin neman gafara ne
wannan? kowa yaSan ta wahaltu wajan jinyarsa har ‘
ana mata hasashen-samun lada wajen Allah. To me zai kawu wannan gigicewa, tana neman afuwa? Tuni wasu’ suka samu amsar’. musamman
matan gidan, dan sun san rashin mutuncin’da ta, ‘zubda lokacin bikin Murja. Ba’yan wannan ma Alhj‘
Bara’u na yawan kuka da ita akan kin bin umarninsa akan: abinda yakaso
Wata kila shi ne take Wa ihu. bayan hari? To al ko banza ‘ta ga darasi dan duk wanda taurin kai ya.
zama abokin mu’amalarsa.
» Tabbas haka ne. domin Hajiya Aliy‘aa ta ‘ji babu ‘ dadi, tunda, ta fara .tunanin itace silar’ mutawar‘
mijinta. -A yanzu .ta ‘gane duk lokacin da ta sabawa abokinsa. da kyar suke samun ransa. Ga shi yau anyi
mai gaba daya, shi ya sa take ganin babu zato
ldan aka ce ita ta kashe shi. ba ciwonSa ba
Humm …… ! To koma dai menene. Allahu-A’alam. kuma ya raba gardama. Sai dai shi Alh. Abdul“ Rashaed ba shi da masaniyar halin da ake ciki. Ransa cunkushe ya iso gida gab da sallar magariba._
Kallo daya Hajiya Suwaiba ta yi masa ta gane akwai matsala. Amma basuyi maganar ba, saida suka zauna cin abincin dare. kuma cikin dadin rai. ya gayawa Murja iyayenta na gaisheta. . ‘
lta kanta Hajiya Suwaiba ta kwashe lokaci mai tsawo bata iya cewa komai ba, saboda tsabar alhini. Hannunta a kunshe tace. “To, mace ce shaWarar da ka
yanke?”
Yace, “Dole na hakura da wannan zumuncin. Koda ace Aliyaa ba za ta aikata abinda ta furta ba, kunnuwana bazasu sake jin’ wadannan munanan kalaman ba. Ina mai tabbatar miki ko mutuwa Alh. Bara’u ya riga ni, ba zan je Kankiya ba.
Zan dai yi masa addu’a anan inda na ke, na
kuma tabbata‘ za ta jé gare shi. Na yi rantsuwa ba zanyi kaifara ba. Ni da Hajiya Aliyaa har abada, ba na fatan Allah ya sake hada ni da ita. ba wai kuma ban yafe mata bane. .Wallahi na gafarta mata duk abubuwan da ta yi min, dun ko a lahira ba na ‘son Ubangiji ya tsaida mu tare”.
Ta sauke‘numafashi mai karfi tace. “Hakan “shi ne daidai, kuma tun farko da wannan hukuncin‘ka yankse Aliyaa ba za ta samu damar- cin-zarafinka ba;
Allah ya sani, nikam tuni ‘na kulle babin Hajiya Aliyaa.
Tunda kai ma ka gane. shi kenan, sai mu ce Allah ya shirye ta”. Yace ‘Amin”.
Kwanaki uku ana ta zaman makokin Alh. Bara’u, ba tara‘ da labari ya zo Kaduna ba.Suna zaune
biSa tabarma. bayan addu’ar’ uku. Malam Sallau ya kira
Mansur ya matso yace dashi yace. “gani Baba'”. Yace “Wai ‘kuwa an alikawa.‘ – Murja da surukinta?” Ya girgiza kai,.yana fadin “A’a”. da saur‘i ya tambaya, “Meya sa?” YaCe “Ban ji Umma‘ ta yi magana ba, kuma ni banda kudin mota”, Ya ” numfasa yace. ,’Kwata?kwata abin ya shige ‘min- duhu; sai yanzu maganar‘ ta ‘fado min.’ ‘ba’a yi shiru ba, yarinya ta rasa mahaifinta,_ a kasa’gaya mata.,Tunda akwai kudaden’da aka samu na sadaka; kawai kayi amfani dasu kaje ka’ gaya masu.-‘A- yau ya’kamata ka tafi, saboda lokaci ya wuce”. Yace,””To, bari in je in gayawa Umma”.Yace, “Shiga’ka’ fito; ka amshi kudin”. Ya mike ya shiga wajen Ummansa. Tana makuré ‘uwér dakanta. gaba daya ta je‘mance ta rame kamar ba ita ba.  ‘ya shaida mata yadda sukayi da Malam Sallau. ‘ Ta girgiza kai tace, “Ai ni_ma ina sane da su, amma tunda ka ji ban ce komai ba, ‘ka san akwai_ dalili”. Fuska yamutse yace, “Ina ganin .ya kamataua gayawa Murja’Umma,’ dun ta, san ita marainiya ce”. .
“Na fi ka‘ sani Mansur, saboda haka-ka koma kawai kayi zaman ka”.
Ba wani jan gardama ba, ya; tashi ya kama gayawa Malam ya mayar masa da abinda Ummansa tace Ransa ya baci .ya‘ hau fada” “yace Dun Allah karbi kudi, ka~wuce Ai mu ba mahaukata bane. da za ta ce kar a gaya’ wa yarinya mahaifinta ya mutu”; ‘ ” :
‘ Ya mika masa’kudi yana ‘Cigaba da fada. “Tashi maza ka wuce. Allah ya sauke ka lafiya in ka ga dare zai maka, ka na iya kwana gobe ka taho da ‘yar-uwanka ka Ya amshi ‘kudi; ransa bai soba, dun sam .baya son sabawa mahaifiyarsa sai dai shi kansa ya San ya dace Murja ta san cewa Baba ya rasu. Kai-tsaye ya wuce ta’sha ‘da silifas ,a kafarsa. Shi kuwa Malam Sallau cikin gidan ya .shiga’,‘ yasa aka yo masa; magana da Hajiya Aliyaa, ta‘ fito ‘ta ?same“shi,gefe guda Suka kebe, yaCe, ,Wai ke me yake damunki? Ya zakice a kyale, ‘yarinya kar’ a gaya mata mahaifinta ya’mutu? Mecece hujjarki?””Ta yi shiru .idanuwanta suka tara kwalla. “Haka kawai, dun durawa kai fitina! Ashe duk‘shurun da ki ka “rinka yin ri banza‘ ,ne dama. ba ki saduda ba?”
‘ To’ Allah ‘ya ‘shiryéki; ni kamna ba‘Mansur kudin mota ya kuma tafi, don mu ha mahaukata bane”- Ya juya ya yi waje ya bar ta tsaye.
ldanuwanta suka tara kwalla, ta tashi a hankali‘ ta koma daki. Shiru ta ci-gaba ‘da zama. tunaninta Alh. Abdul-Rasheed zai zo kenan? Da wane ido za ta kalle
shi?” Ta gage hawaye, wasu suka sake kwarara shikenan bakinta ya yanka mata waya. Sarai tana sanida cewa ba’a gayawa Murja zancen mutuwa ba, kawai ta yi shiru ne.
Dun’ ta’tabbata Alh. Abdul-Rasheed zai zo gaisuwa. A yadda take ji. cikin ranta. gara ta makance data hada ido da shi. Kuka ya dawo ‘maté sabo~da kyar ta samu mata biyu masu ba ta hakuri. ‘
Shi kuwa. Mansur, yana shigowa layin gidan, ya tsaya wani shago ya sayi fallae takarda. (-Puls-Scaf) hade da biro. Ya zauna bisa benci nan kofar shagon, ya rubuta wasika zuwa ga Mur‘ja,~ ya ninke, ya karasa kofar gidan Alhj  Abdul-Rasheed.
‘ Anan ya samu yaro,‘ya’ba shi yace wai aba Murja. Yaran’ ya shiga, ya juya yai tafiyar’sa. Yaro ya shigo ya iske su zazzaune tsakar’ gida. Mur’ja na kwabin kalallabar’ fulawa. ‘
Imam ya ta so ta kamar zai afka robar kwabin. ‘ Ya yi’tsayeda ‘takarda a hannunsa, yace, “Wai inji wani a waje yace aba Murja”. Gaba .daya suka dubi yaron. SulEman’ya’ fara magana, “Wani?” ‘
Ya taso a fusace, ya fige takardar ya yi waje da sauri, yana fadin, ‘.’Muje in gan shi don ubansa’. Tuni tsoroya- lullube Murja, ta shiga zare ido tana
cewA Ni wa na sani?” Hajiya .Suwaiba tace Kwantar da-hankalinki, bari ya dawo muji ko waye Wannan mai karfin halin?” Tana sa aya. Suleman ne ya Shigo da kumfar baki.
“Ba kowa a wajen! Ya gudu dan iskan! Amma Wannan akwai matsiyaci”. Ya’yi kwafa kafin ya ci‘ gaba, “Da ya bari na ganshi, da anyi kare jini, biri jini!”‘.Hajiya ‘Suwaiba tace; “Gaskiya kam. To in Mur’jar ma ta je, hér ya ganta?”
“Uhn”. Ya amsa yana Warware takardar nikan zafin kishi kama zuciyarsa ta tsage, rubutun’ma dishi-dishi yake ganinsa kuma‘ duk girman takardar rubutan‘ léyi daya me. to marar’ zuciya idan kinga dama kixo Gida baba ya rasu
Ya kara Ware ido sosai, ya kara maimaitawa. ‘ ~ ’
‘ A salube yadubesu, dama su shi‘suke kallo kuma ‘tuni haWaya kate zuba kuncin Murja. “Inna- Lillahi’wa-lnna-ll‘aihir-Raji’un! Mamanmu. ina Baha?”‘ Gabanta ya kara ,faduwa, tace “‘Menene Na gaya maka Kauran Juli ya tafi dubo gona”. Yace .”Taso ki ji”. Ya wuce dakinta, ta bi bayansa a tsorace.
Nan take Mur’ja ta sha jinin jikinta, don hakata taso ita ma ta biyo su ta labe jikin bango, dun haka tana ji‘ Saleman yana faidin -“Abba ‘ne ya rasu Mamanmu”; ‘ ‘
Ta-dafe kirji ta dau salati. Suka karaSa ‘tare “wa zai iya gaya wa-Murja wannan labari? Ni kam bazan iya ba”. lnji Suleman. ‘
Tace “Ai dole a gaya mata Sulaman, me za ta yi banda hakuri? Hukuncin Ubangiji wa zaija da shi?” Kawai ganin Murjar suka’yi ta karasa shigowa ta zube kasa tana shasshakar kuka.
Mama ta nufota da sauri, ‘ta rungume,”‘Yi hakuri Murja, haka Allah ya so. Addu’a kawai za ki yi masa. Allah ya sa jinyar da ya yi, ta zama kaffara. Yi hakuri kin ji’?” Haka ta yi ta rarashinta. ,
Sulaman na kallonsu cike da tausayinta, kukan da take yi, shi ke kara ratsa masa zuciya. Da ya ga ta kasa daurewa, sai‘ya mike ya damki hannunta yace “Taso muje
Mama ta mikar’ da ita’, tana fadin, “Yauwa, ku je don Allah ka rarrashe ta’_’. Ya ja ta har dakinsu, suka bar Hajiya Suwaiba da juyayi
Ta jima zaune, sannan ta fito tsakar gida ta~ iske Imam ya dauki_,ruwa ya tsula shi cikin kwabin da Murja ke yi, shi ma yana ta juyawa.
Ta mammake ‘masa hannu ta kwace, kwabi kam ya riga ya lalace,_ sai zubarwa ta yi. lta kanta mai son ta soya kallabar, tana can ta Zama kalallabar kanta, Suleman na ririta ta kamar kwai.
Yamma ta rufa susai, lokacin da Alh. Abdul- Rashead ya dawo don-gab ake da kiran magariba. Daga shiguwarsa ya gane akWai damuwa cikin gidansa, don haka ya tambaya. Nan take Hajiya Suwaiba ta shaida masa rasuwar abokinsa.
Jikinsa ya yi mugun la’asar, ya jima shiru ya zauna, yana yi wa Allah tasbihi cikin zuciyarsa, kafin ya tashi ya leka dakin Murja, ya yi sallama suka amsa. ya shiga ya zauna a kujera, ya yi wa Mur’ja ta’aziyya tare da nasihohi masu taushi da dadin saurare.
Nan da nan zuciyarta ta kara naba’a, ta dauki dangana. Yana karewa, ana kiran sallah, dun haka ya fito suka yi alwala da Imam; suka fita masallaci, sannan Suleman ya bi bayansu. ’
Bayan ya natsu a falonsa, an gabatar masa da abincinsa. Ya yi shiru yana kallon kayan abincin, can ya numfasa yace, “Akwai kudi a hannu na, Wadanda na ‘gaya miki Suleman zai fara juyawa. Allah ya sa ban siyo kayayya kin ba. Na gaya wa Suleman din su shirya gobe su tafi, idan kuma ke ma za ki, sai ki bi su ki yo gaisuWa”.
‘ Ta dan yi shiru, kafin tace, “Kaime ka gani game da tafiyar‘ tawa?” yace “Zan ji dadi‘idan har ki ka samu zuwa Amma babu dole, idan ba ki da ra’ayin hakan”.’
Ta gyara zama tace, ,”Haba Alhaji, ai ba sai ka ba ni zabi ba, tunda zuwan nawa zai sa’ka farin-nikam ai ina ganin banda zabin daya wuce hakan, dun farin- cikinka shi‘ nafiso a kullum”. ‘ ‘
.Ya yi dan murmushi ‘yace, “Allah ya yi miki _albarka, ‘ ya kai mu goben lafiya. Idan kun je, duk wandaya tambayeni. ku gaya masa bana jin dadi ne
Tace”Shi kenan”. Abincin nan kadan ya ci shi dun ma Hajiya Suwaiba tasa baki ne.
Washa gari da sassafe suka bar Kaduna. :saboda Hajiya Suwaiba tace ba kwana ita zatayi ba. Suka bar Alhaj shi kadai a gida, inbanda tunanin Alh. Bara’u ba abinda yake yi. Rashin zuwa ta’aZiyarsa ba karamin kona masa rai ya yi ba. Ta kowana bangare cikin zuciyarsa cunkushe yake da takaici, shi yasa yake ta ajiyar zuciya tare da fadin “Allah ka jikan A‘lh. Bara’u”. –
Tun isowarsu. Murja keta ruSar kuka kamar ranta zai fita, musamman da ta ji cewa yau kwana hudu kenan da ra’suwar‘ mahaifinta. Haka shima Suleiman y yana jimami. ace mutuwa kwana uku ba su da labari, lallai wannan kiyayya ta kai ’karshe. ,
‘Malam. Sallau ya tambayi Alhaji, Sulaman yace bayajin dadi ne. Amma yace idan yaji Sauki, zai zo. Malam‘ Sallu ya “yi ‘ mesa ‘addu’a’r samun‘ sauki cikin gaggawa. Da‘ga nan ya shiga cikin gida. ya yiwa ‘ kowa gaisuwa har da Hajiya Aliyaa, kuma ta’amsa ba kamar yadda ya yi zatu ba.
Haka Hajiya Suwaiba ka mamakin yadda ‘ Aliyaar’ ta amsa gaisuwar ta, ba yabo, ba fallasa. Amma duk da haka bata zauna wajentaba  sasan Malam Sallau  zauna’cikin matansa. ‘Suka yi ta ‘rawan ‘jlki da ita Bayan sallar azahar taYI‘ shirin komawa, sannan takoma sasan
Hajiya Aliyaa. ta yi mata sallama, ta fito ba tare d ta tambayi Alhj. Abdul-Rasheed ba. lta ma ba ta yi mata maganarsaba,‘balle tace yana mata gaisuwa. lta kuwa Aliyaa ba ta tambaya bane. sabuda kunya. tunda Allah ya: taimake ‘ta‘baizoba, shi kenan ta kubuta, ‘ kara kwantar :mata. da- hankalisannan tayi mata sallama ta fita nan ma tasallami su Malam Sallau. Yana kara jaddada. mata ta mika gaisuwarsa ga Alh. Abdul-Rasheed ‘ Ba- ta ga Mansur aWurin ba; dun ‘haka ta tambayi Suleman.‘Yace “Aitunda muka gaisa, .ban  sake ganinsa ba”. Tace “To shikenan; ka gaya masa ina masa gaisuwa. ‘. Yace “Zan” gaya , masa. Muje in raka ki‘tasha”. Ta wuce‘ tanakara ban kwana da Malam Sallau. ta gayama  Alhj Abdul-Rashaed yayi matukar mamakin jin céwa‘yau kwanan Alh. Bara’u hudu da mutuwa.’Kenan tun ranar da ya je. Allah ya yi ikonsa? Ya kada‘ kai yace “Allahu-Akbar! Allah ka- dauki ranmu muna masu .tsananin imani ‘ Haka ‘yaci-gaba dajuyayln’rashin abonkinsa. Haka gwaggo ‘da‘lnna Mairo su kai ta‘yi masa addu’ar samun rahmar Uhangiji. Alhj. Abdul-Rasheed bai sani ba, suka shirya tafiya Kankiyar, don ya dace auje gaisuwa. Ba. su gaya wa Alhajin bane. dun karsu dora masa nauyi.
Ranar’ sadakar bakwai, sammaku suka yi, sai dai Suleman ya gansu ba tsamamni, sudin ma shirin komawar suke yi, saboda haka’ suka jinkirta su Gwaggo suka huta, zuwa azahar. sannan suka dungumu tare.
Duk tsawon kwanakin da su Suleman da Murja suka yi. Hajiya Aliyaa ba ta zaunar’ da su ta nuna masu kuskurenta ba, balle ta gaya ‘masu komai ya wuce, ko sa ji-dadi a zukatansu._Rashin azanci ne ko wauta? oho! Ita a tunaninta bata so ta nemi shiri da su, don kar Alh. AhdUlRasheed yazo inda take.
Shi‘ ya sa-ko Mansur ba ta’nunawa tayi ‘ nadama ba, balle’shi ma ya san gaskiyar lamarin. Wannan shirme da yawa yake, bayan kuwa ta bar maganar cikin‘ ranta ‘tana ta faman yi mata ciwo a zuciya. Kai! Lallai duniya makaranta ce, idan ba ka yi sharar masallaci ba, ka yi na’ kasUwa.
can gida Kaduna kuwa su ma har yanzu cikin jimamin ‘mutuwar’ suke.-Musamman Murja da ta hada taura biyu a bakinta. ga mutuwa, ga rashin samun‘ hadin kan mahaifiyar’ta, shin da wane za ta ji? Dadinta daya kawai; mijinta na sonta kuma yana‘ matukar kulawa da ita. Sannan duk abinda takeso, shi take samu wajen surukanta, muddin baifi karfinsu ba‘.
. Sannu a hankali komai yabi jikinta, ta rage jin radadin mutuwar’ mahaifinta. Rayuwa ta cigaba mai dadi, saboda akwai kwanciyar’ hankali har sakamakon
jarahawarsu ya fito.
Alhaji ya yi fadi tashi, ya sama‘.mata makarantar ‘yan mata ta jeka ka dawo. Nauyi “ya qayi masa yawa, ko kudin motarsu na Zawama aikine yau da gobe sai Allah. Amma da yake Alhaji jarumine” sam baya gazawa balle ya koka, yaushe
zuciyarsa a dake take cikin yiwa Allah godiya, ‘
.                  **********
Daminar bana ta yi kyau‘sosai, an samu amfanin gona ba kadan ba, gaba daya gonakin Alhajin guda biyu. Domin kuwa buhunann ‘masara har’ sun kai rabin zakka, kuma take nan ya fidda zakkar kafin ya ware na ci a gida.
Saura ya -kai kauwa ya‘siyar, ka na ya siyo buhunan shinkafa ‘da wake, ‘daWa hade da gero sabuda yin kamu. Abinci sosai ya aje a gida, kamar yadda ya saba, wannan kokarin koda yaushe.
Ha’ka wajen gwaggo ita ma ya aje mata komai na bukata. KaiAlhaji bai tsayanan ba, har dinkuna ya yi masu, kowa ya samu karin’ sutura. SaUran abinda ya rage a hannunsa, sai ya sa aka bugaWa. Suleman dan karaminkiyos ya‘ aje kofar gida. .i ,.
Ya zuba masa.’yan abuhuwan masarufi, kuma ba laifi shagon ya cika da kaya. Kullum idan ya dawo gida, ciki yake zama akan dole. Domin shi ,cikin zuciyarsa shagon ‘ya yi maSa kadan.‘ ‘
Ya kamata ace babban shagone Alhaji yasa- aka yi ha karami ba. duk da’ haka yana samun taro da‘ sisi. Sai dai a dogun burinsa yake ganin abinda yake samu ya yimasa kadan. ‘
Ga kwadayi, sauda yawa ‘in baya muradin‘ tuwo, sai ya dauki kifin gwangwanin’Sadin ko Geisha da biradi in yatashi da daddare ya shige daki su bare su cinye da ‘yar’ ‘ lelensa.‘ Shi’ kuWa‘ Alhaji saboda tattalin kar a cinye shagon,‘ hatta biskit idan Imam na
so, kudi yake badawa a bashi. A haka shagon ya rinka tafiya, wata rana ya rame, Wani lokacin ya dan yi kiba.
Shekaru biyu Suleman ya kamala Difilumarsa, yayinda  Murja ke ~shekarar karshe  ta kammala babbaar sakandiranta. A tsawon shekarun nan, babu_ abinda ya sauya a zaman ‘doya da majan da ake yi tsakanin Hajiya Aliyaa da iyalan Alh. Abdul-Rasheed. Amma duk hutu Murja ta kan je ta kwana biyu ta dawo
Sakamakon Suleman ya yi-kyau, kuma Alhaji na sha’awar ya néma masa ABU, dun ya yi ‘Digiri dinsah Sai’dai a _halin.yanzu babu kudi’a hannunsa. Saboda. haka Suléman ya ci-gabada zama shagonsa.
ldan ya gaji da zaman ya kulle ya shige daki, ya. yi _kwanciyarsa. Alhaji ya yi ta fada, yana, ganin Suleman‘ya fiye sun jikinsa, maimakon ya zama namiji mai fafutikar neman na kansa. Koda takardun sa ya rarraba na neman aiki, wata kila Allah ya taimake shi ya samu.
A’a sai ya yi kwance‘ yana jira komai Alhaji ya je ya nemo Wai ma har yaji haushi, yana ganin kamar da gangan Alhajin ya ki name masa makarantar.A b u haka ya kusan shafe shekara’a zaune, ko gona baya raka Alhaji, idan bashi yace masa‘yazo sujeba.
A wannan‘ karon kam Alhaji yana ganin Suleman zai Samu shiga makaranta, domin akwai alamun amfanin gona zai yi kyau.‘ Kwatsam! Hajiya Suwaiba ta kwanta, .ciwu, kamar wasa; abinya kaita ga‘kwanciya asibiti. Sai ‘da bincike ya tsanantafa ka
ga shigar ciki ke damunta. Wani iko sai Allah! Murna da farin-ciki wajan Alh. Abdul-Rasheed. abin ba’a cewa komai. Ita kuwa Hajiya Suwaiha ta ma rasa me zatace? Har wata kunya ta rinka ji, saboda yawan shakarunta. Amma cikin zuciyarta fari yake sol Tare da dimbin godiya ga Allah. .
Kai ‘ba su kadai ba, kowa ma ya samu lahari murna yakeyi. musamman gwaggo zuwa tai ta zauna da ita a asibitin har zuwa kwanaki goman data yi a can. Bayan  sallamanta.
gwaggo ta koma. Murja ta ci-gaba da hidimar gida, domin Hajiya Suwaiba ba-ta iya komai. gaskiya wannan cikin ya zo mata da lalura susai, ba kamar cikin Imam ba‘. Kodon jiki ya kara taushi ne’? Allah dai ya raba lafiya..
Wata uku tsakani, shi ‘ne satin karshe da su Murja zasu kammala (WAEE) dinsu. Yau tun a dakin jarabaWa, ciwon ciki ya ta sa Murja ya hana ta sukuni. Ayamutse ta gama jarabawa ta dawo gida, ta iske Hajiya Suwaiba kwance tana ta faman lasar lemon
tsami. Tun daga fuskarta ta gane akwai wani abu.
‘ “Yaya dai Murja’? Kamar idanuwanki sunyi ja?” Tace “Wallahi Mamanmu ciki na keta ciwo, da kyar na rubuta jarabawa yau”. Tace “Assha! Toki gaya wa’ mijinki ya nemo miki magani”. Tace To, yau me za’a dafa Mamanmu?” Ta-ce “Kar ki damu da ni, ki dafa duk abinda kukeSo.
Tunda ba kya jin dadi, ki yi mai sauki, wanda ba zai dauki lokaci ba”. ,
Tace, “Ai saboda Baba ne, kin ga shi ya fi son tuwu”. Tace Hakane. amma dun kin yi wani abin, ba Zai ce komai ba, ci zai yi”. Tace “Shikenan, bari inyi Taliyar Hausa da manja
“Ki cédai kwadayi za kuyi ke’ da ‘Imamunki”. Ta yi ‘yar- dariya ta. mike-tana fadin, “Bari in canja kaya Tace “Maza., ‘amma ki Sha magani ko (Mistmagne), ya siyo miki ki sha”. Ta sake fadin. “To Ta fice. Kwanciya ta yi tana jiran Suleman ‘ya shigo.‘ta ‘gaya masa har barci ya kwashe ta. ‘
Alwalar sallar la’asar ya shigo yi, daga nan ya tasheta don ita ma ta yi sallar‘. Nan take ta gaya masa ya siyo mata (Mistmagne), idan ya dawo masallaci. Ya dubeta da kyau yaCe. – ‘
“A’a Bebina, kodai kemA cikin gare ki?” Ya ba ta kunya, ta ruga bayi tana fadin. “Ni ba ruwa na”. Ya fice yana yar, dariya. Da kudin aljihunsa ya’siyo mata maganin, ya kawo mata, ta sha. cikin ikon Allah kuma ta ji sauki, har’ ta kama aikin‘ abinci. Kafin wani lokaci ta gamA Taliyar, ta ji daddawa,
‘Tun- a tukunyah take.cinta,saboda ta yi mata dadi sosai. Karfe shida Imam ya‘dawo ISlamiyya yana’ sallama. Lokacin‘ tukunyar tana ‘ta faman kankarar kanzon tana ci. ”
Wajen‘ta ya nufa yana dariya, “Me’ ki ke’ci. Anti?” Tace “‘Dadi yaro” Ya ‘tSUqunna’
yace. “Lah Taliya Dan Allah Anti ,samman. Tace”Yaro na cinya”. Ya cunna baki “Kai don Allah Anti shi ne ki ka ki raga mln? Shl kenan Ya
fadi yana wani marairaicewa.
Ta kyalkyale da dariya, “Ba ka Ji yadda ta yi dadi ba”. Bakin nan a ture ya sa hannu cikin tukunyar. ya wawusu wanda ta ‘kankaro ta tara. Ta yi wuf Ta kama hannunsa. ‘ .
“Al kuwa ba ka lsa ba, In kankaro. ka kwasha? Sannu”. Kamar zai yi kuka yake cewa, “Haba Anti Haba AntI’dan kadan’fa’na diba
Tace, “Zuba dai a tara da yawa. sal mu raba”. Ta ci-gabadakankara tana masa dariya..dun ta san- ya kusa yaci shl ya  take ta faman ja masa rai  ya shammace ta, ya wawusu‘ya ” ruga da gudu daki ,yana turawa baki Da wa Allah ya hadata,inbada shl ba? – 1 ,
Ta bishl ltama da gudun. Yafada jikin Hajlya Suwaiba yana kira. “Mamanmu!” Tace Kash! Haba Imam, ya ka ke naman ka karasani?” , .Murja ta yi tsaye’, tana dariya, “Mayen tsoho“ kawai, al tana nan cika da ~kula ka lashe ba za ka cl ba”. Mama tace. “Kin lsa, al- dama dun ki tsokana . ya sa ki ka.ce Taliyar za kl yl. Tashl ka Je tazuba maka . Ya taso. yayin datake fadin.
“lnka biyonl, sal na yanka ka na’soya”. Da saurl kuwa ya biyota ya kama hannuntA
“yi hakurl’Antina …… ” Ta jawo kafadarsa, suka fice‘ Mama na masu dariya.
Bayan sallar lssha’i, suka baje ta a tire Ita da Imam, suna ta sharba. Sulaman ya zuba mata Ida. Tace, “kai kallo ka ke yi. ba zakaciba. Yace, “Allah shi kyauta, wa zaici ci wannan abin? Kin ‘wani zabga uwar daddawa, baki ya yi ta wari Dama ki tabbatar’ kin yi burush, kafin kizo kusa da ni”. ‘ Ta dubi Imam tace, “Dun ‘Allah ya ka ji Taliyar nan?” Ya kar-kada kunna, yace “coi!” Suka? kyalkyale da dariya har da tafawa. Suléman yace “AI wannan . bakin na ka wagege, shi na coi din”. ‘
Ya mike yana fadin, “bari In fita duk warin daddawa ya lshenl, kar ya sumar da ni”. Ta kama’baki ta bi shi ‘da kallo. “Ah Iya,yi Imam ,ya hau darlya. Sukayi ta ci suna kari, sai’da suka ga byan kular;
Da kyar Imam ke motsawa saboda kosho. haka ita ma Murja. Nan’suka baje tsakar daki suna tayi wa juna dariya, anyi cin haram  Ba’a
jima ba. Nepa suka kawo wuta. Ta kunna’ masu kallo anan barci ya kWashe shi.
Karfe tara da rabi Suleman ya kulle dan shagon  ya dawo gida da cinikinsa hade da gwangwanin geisha da biredl. Duk a cikin cinikin ne, ya gangara kan layinsu yaa siyu lemon kwalba guda’biyu masu sanyi. Ta amsa’sallamar da yayl, sannan ta tasa ta‘karbi abinda me hannun nasa tana masa sannu da zuwa. Tun ’kafin tazauna, yace ta dauko min-
Ta nufa kicin ta dauko, ta ‘
JUyE masa Geishan ya . bare biredi ya hau ci. lta kuwa zuciyarta-ce keta tashi haka ta zauna tana yatsine yace bismillah tace wlh amai ke tasomin amai kafin ya sake bude baki tuni aman ya taso gadan gadan
lol

Karna cikaku DA lbr said muyima alhaj barau fatan samun can
mu hadu a next chapter

naku har kullun

The. (O I C )OF LITTafan Hausa zallah@fcb page

www.Facebook.com/abdullahi.Ismail.salanke

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE